You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
idanunshi suna rufewa a hankali har suke rufe baki ɗaya, dr ta kalle mamani da takw kuka, tace.
"Madam kibar kuka haka nan gaba zai tashi ba tare da kome ba normal zai farka kedai kicigaba da bashi kwarin gwiwa, haka zai bashi damar fuskar wata rayuwar sai anjima."
Godiya tayiwa dr sannan tafita daga ɗakin, kiran Daddy Asad tayi a waya bayan sun gaisa nan ta labarta masa ya tashi amma cikin damu, sai dai sunasa Allura bacci,
Sun jima suna magana kafin sukayi sallama da ita........
♡
*Liverpool state*
Kuka nake tare da rike marana ina birgima a kasa, duk ihun da nake yana jina, duk ya ruɗe, ya rasa yanda zayi dani abinda yazo masa kawai ya fasa kofar aikuwa ta gurin mukullin ya fasa, sai ga kofar ta buɗe, da sauri ya shigo inda nake,yana faɗin" subhanallah, A'isha mike damunkine haka,"
Cikin razana da mugun tsoro nace.
"Yaki fitowa ne fitsarin, don Allah ka taimaka min zan iya mutuwa"
Jikin shine ya ɗauki rawa yafito falo motar asibiti ya kira a wayar da take cikin gidan ko mintuna goma ba'a ɗauka ba sai ga motar Hijab yasaka min sannan ya ɗauke ni ya ɗaurani a gadon, inda suka gurgurani zuwa asibiti,
Tare da shi kuka nake tare da nishi amma yaki fitowa har muka isa asibiti, dukda nice me ciwon amma shine mai damuwar, muna zuwa aka wucce dani zuwa emergce room, nan aka shiga duba dan bai ɓoye musu ba yace shi baya bukatar namiji likita ya duba masa matarshi, kuma dake can suna da doka da oda take aka nime wasu likitoti mata ɗaya yar naija ce, Dr Halima Omar da Dr Hudallah Aswad, yar pakistance, tare suka shigo ɗakin nan suka rufu akaina tare da wasu nurse mata su uku, ita dr halimar ce ta tambayeni haka nake tunca ko lokaci guda abin ya faru, nan na shiga musu bayani, adaidai lokacin da Dr Hudallah tare da taimakon nurse suka saka min, injin sukar irin wannan matsalar suka zuko min fitsarin ajiyar zuciya na sauke, kallon Dr Halima dr hudalla kafin tace.
"Mi kike ganin zamu yi mata nan gaba dan fitsari wajibine ga ɗan Adam"
"Eh babu abinda zamu mata sabida ai ba halitta bace, ki gani mana, mu fara bincike me ya haifar da matsalar tukun, domin ina da shakku akan tushewar gab..........
*_Happy Honey Moon Mr&Mrs Usman S Usman♥_*
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳
*Na:Mai_Dambu*
*Wattpad:Mai_Dambu*
*_Godiya da fatan alkhairi mai tarin yawa Ubangiji yasa yanda kika fara Ajalin So ki gama lafiya Mungode da pagen sukuntu amma hamzari ba gudu ba da alamu Mrs Mohan zata bawa Banafsha ciwon kai dan naga tahau bishiyan kace akan Mohan muna biye dake sai munga kwal uwar daka_*💋
_Rigima ta ɓarke a zauren Mai_Dambu fa jama'a Ummu Ilham,Maman minal, Phatyma, and As-min, tsakanin team ɗin Imamu da Team ɗin Asad wannan nacewa ya gaji wannan nacewa dama yake jira yaseen duk na diririce kuma dan kusani a uku nice wai alkalin gaku ga Mommy Sayyed da Aunty A'isha ai su kaɗai zasu iya raba wannan rigima ba sai na shigo ciki ba_🙆
Not edit≥﹏≤
*:~•33*
"Mikike nufi da cewa kina da shakku akan ciwon nata." jefa mata tambaya tayi haɗe da zuba mata idanun, ita kuma dr halima ko ajikinta cire hand glove ɗin tasa take cikin nutsuwa kafin tace.
"Muje ki gani da idanunki mana."
Gaban wani na'ura aka turani nan aka nan bakin kofar ya buɗe suka turani nan suka shiga bincike abin ya ɗaurewa Dr huda kai dan babu kome fito dani akayi suka maidani gefe, inda ita kuma dr halima ta cigaba da haɗa bayananta suka fita yana tsaye ta kalle shi sannan tace.
"Zaka iya biyo ni office."
D'an tafiya kaɗan suka ya, sadasu ga office ɗinta, ɗan madaidaci, zagayawa tayi gurin xamanta ta zauna sannan tace.
"Zaka iya zama."
Zama yayi amma hankalinshi a jagule yake, yan rubucce rubucce tayi sannan ta ɗago ta kalle shi sannan ta kauda kanta gefe, tace.
"Mr Usman matsalar matarka bata asibiti bane, ta gidace dan ko zaku zauna a asibiti babu abinda zasu iya muku,ni yar bauchi ce iyayena malamaine, kuma ina da sani akan wasu abubuwan, abinda ya dace yanxun kafin nan da wani lokaci ka nimo mana, magungunar islamic, ka kawo irin ha."
"Karki damu ba sai kin lisafo ba. Zanyi kokarin haɗowa na kawo miki. Dan nima masanine akan wannan ɓangare nagode." cike da mamaki take kallonshi ai ya bari ta idar kafin ya katseta.
Ko bin takan baiyi ba yafita daga asibitin wayarshi ya ciro daga aljuhu, ya shiga browse islamic medical center, abin mamaki sai gashi yasamu har kusan gurare shi da, wanda yafi shahara na wani ɗan china amma musulmine, sai na biyu na wani ɗan India, bai damu da wanda yafi shharan ba shidai wanda yake kusa ya nima, kuma ba karamin tafiya bane na kusan wanda yafi shaharan kuma sai kayi tafiyar awa biyu, ajirgi kasa,
Cikin sauri ya tafi, inda ya haɗo, *Ambar,Safarjal,Kusdul Hindi,siitira, black seed oil& garin, olive oil& garin,sai zam zam, da sukansu y'ay'an olive oil*
Yana zuwa yaje office ɗin dr halima ya zuɓe mata su, kallonshi tayi da mamaki sannan tace.
"Ƙana ji da Y'arkan nan fa"
Shafa sajenshi yayi sannan yace.
"Matata ce, muje ki sallamemu."
Kasake tayi sannan suka tawo zuwa gurina, nan aka sallamemu zuwa gida muna na zuɓe a falon dan bacci nake ji,
Wani kwantena ya ɗauko ya shiga haɗa maguggunar, Ambar ya hada da man olive oil da oil ɗin black seed, ya haɗa su guri guda,
Sannan ya ɗauko safarjal, shafin aljanu ya mika min yace.
"Wannan gashi kina shafawa a jikinki, koda yaushe. Wannan kuma ya zama man shafawarki, amma ban kamala dasu ba, sai siitir shi zaki shane sabida abinda ya toshe miki wajen fitsarinki, wannan kuma kusdul hindi xan haɗa miki da man zaitu kina saka auduga kina goge gurin, sai wannan zam zam shima zan miki addu'a a ciki, kina sha kullun safe da maraici,"
Zama yayi sosai yasani nayi alola nazo na zauna ina jiranshi addu'o'i Yayi sosai ya tofa a ciki daga ciki akwai ayatul shifa, kallona yayi cikin nutsuwa sanan yace.
"Ki ɗauki wannan abinda ya faru a matsayin jarrabawarki, sannan A'isha kina kuskure sosai a rayuwarki, ban taɓa ganinki da koda hisnul muslin ba, balle kuma alqur'ani, ita kanta sallar idan kiyita baki zaman cikakke minti biyar da sunar addu'a kina tashi zaki kwanta sabida son jiki irin naki, A'isha ita kanta rayuwa bata yuwa sai kanemi yardan Allah a cikinta amma ke kin shagala ke ba azkar ba ke ba tasbihi ba..."
Mikewa nayi cikin kuka nace.
"Toh kace min kafura kawai, mana ka huta da kwana kwana da kake min,"
Zuba min ido yayi na gama rashin kunyata na bar mishi maganinshi a gurin ni nayi fushi sabida ya faɗa min gaskiya, tattara maganin yayi ya kaimun ɗaki, ya ajiye sannan yayi min bayanin yanda zanyi amfani da shi, sannan ya fita zama nayi na cigaba da kukana.
Tun daga ranar yafita harkana baki ɗaya, cikin ikon Allah da natashi fitsari ya fita babu ciwo dan murna narasa wa zan faɗawa sai na fashe da kuka, hankali abubuwa suka canza wanda nice mafarin faruwarsu, Allah ya gani Imamu yafita hakkina, ina jiran yazo ya lallaɓani ashe gefe guɗa Hauwa ta kutsu min, kaman tasan bama shiri da shi tafara masa kiran safe daban na rana dabam ga na dare, tun baya damuwa har ya fara biye mata suna waya karshe suka ɓige da whatsp da Imo ga vedio call, bayayi a gabana sai ko idan yana ɗakinshi zasu jima suna hira ko wanka tayi sai takirashi, kai hatta idan tasa kayan bacci haka zata ɗauki hotonar ta turo masa, kuskuran da Wauta yaja min dame hauwa tafini, amma once ta tafi da imanin mijina, dukda matarsa ce,
Ana haka ranar sai ga Dr halima tazo duba ni, abinda yake burgeni da bariki kenan koda kai ba dan jahar wani bane matukar akace kai ɗan naijane toh take zumunci yake kulluwa, musaman A naija matukar kuka fito jaha ɗaya amma gari ya bambantaku toh ana ganin junane kamar ciki ɗaya aka fito,
Shi ya buɗe mata kofa ni kuwa ina kitchen ina kuka, kwana biyu nan akan idanuna yake wayar babu abinda ya dame shi, gaisawa suka tashigo nuna mata mazauni yayi sannan ya biyo ni, kitchen ya rumgumeni ta baya, cikin tsiwa da ɗaga murya nace.
"Malam sake ni kaje ita wacce take turo maka tsiraicinta ka rungumeta but not me."
Yanda nayi maganar ita kanta dr halima taji, marai raice fuska yayi yace.
"Muna da bakuwa a cikin gidan nan karki ɓata mata rai tafita dr halima tazo"
Ajiye wukarda nake yanka albasa nayi na kashe gas, nafito ina share kwallae idona, murmushi na kago a fuskana naje cikin fara'a zan zauna sai naga wayarshi tana ruru ina dubawa kuwa naga hauwa ce take kirashi zasu vedio call bansan lokacin da na ɗauki wayar na rutsa da kasa ba wayar +2 cike take da abubuwanshi, yana kallona ni kuwa tsuru tsuru nayi ina kallon wayar ban zata abinda zai fito bakinshi ba na ɗauka zaice ya gajine abin mamaki sai naji yace.
"Allah ya shiryeki Nana A'isha"
Yana gama faɗar haka ya tattara wayar, ya juya zuwa ɗakinshi nan ya sake kaya ya ɗauki katin bankishi ya fita yayiwa Dr Halima sallama bari yaje wani super mkrt ya sayo wayar, tace.
"Toh Mr Usman sai an haɗa da hakuri fa."
Dariya yayi yafita abinshi. Yana fita banyi aune ba naji saukar mari a fuskana cikin kiɗima zan ɗago takara min cikin ɓacin rai take magana take sai tayi min kwarjini.
Tace" Banda ɓatar basira har zaki ɗaga murya akan mutumin da ya damu dake ki godewa Allah da ba ciki ɗaya muka fito ba wallahi da sai na takaki, kinsan girman darajar wanda kike tare dashi dan ya damu dake shine zaki masa hauka, wallahi da mijina ne sai ya miki abinda gobe bazaki sake masa wannan ɗanye kan ba, ba dole wata tashigo rayuwarki ba kiɓ zauna kina shashanci, banza wallahi kikayi sake ya daina sonki kin kaɗe har buzunki,"
Sassauta faɗarta tayi cikin sanyi murya ta ɗagoni ta zaunar dani inda tashiga rarrashina da min nasiha sosai jikina yayi sanyi sannan ta tambayeni ya jikin nawa nacw mata da sauki ta jima sosai kafin kara min nasiha da bni hakurin marin da tayi min ɓa in raine,
Godiya nayi kuma na ɗauki aniyar gyara kuskurena ba dole ba nasha sanbaɗa, hmm duk yanda naso na bawa imamu hakuri ya toshe kofar haka horon da ya shiga min shine baya dawowa gida sai nayi bacci idan zai fita kuma da asuba yakw fita, amma abin farin cikine zai ci abincina da na ajiye masa, idan ya rage yayi mana ɗumame ya wanke filet da kular abinci ya kifa ni kuma ya dafa min ruwa zafi da kayan kamshi.
Wasa wasa sai da muka kwashe wata uku babu jituwaa tsakaninmu kuma bama haɗuwa ranar hana idanuna nayi bacci ina jiran dawowarshi gashi ciwon jikina nata warkewa xance, dan ina kome babu matsala sai dai wani abu da ya dameni a gurin kaman kari, shima dai yana motsewa kuma Yanzun na maida hankalina sosai gurin gyara alakata da mahaliccina kuma Alhamdulillah ina samun nutsuwa, sosai.....
Ina zaune rike da yar karamar qur'ani me ɗauke da suratul Kafh suratu-Arrahama, me ɗauke da manyan sururri haɗi da addu'o'i sam yanzun ko bana sallah kullun cikin alola nake, toh ba dole ba ai nima naji daɗin yanzu har wani nutsuwa nayi ba kamar daba wato *birkita bani* duk nabirkita kaina birkita abokin zamana kai Allah karabamu da shagala.
Kallon agogon gefena nayi cikin nutsuwa na cigaba da karatuna jin dirin mota yasa na ɗago idanuna ina kallon kofar, a hankali ya ɓuɗe a jiye alqur'ani nayi naje amshi jakarshi,kaina a sunkuye rufe kofar yayi ina rike da hannunshi har ɗakinshi, na ajiye jakar na taimaka masa yayi ya rage kayan jikinshi sannan na haɗa masa ruwa yayi wanka, duba wardrob ɗinshi nayi babu kananun kaya tsaki nayi na ciro masa jallaɓiyar dan yayi imani da sakasu, a hankali nace.
"Wallahi ka dole ka koyi saka kananun kaya Allah ya kaimu gobe xan baka mamaki."
Gajeran wando na ɗauko masa na ajiye nafesa masa turarren Bint hoor, turarena ne fa, amma dake kamshin da daɗi kuma naji yana yaba kamshi kafin muyi rigima. Dariya na fita tuwon miyar kuka nayi wanda Aunty Halima ta kawo min har da garin kuɓaiwa garin daddawa, wani zuwanta da yaranta har da masar bauchi, nayi murna sosai ga gefe gidanmu ma akwai wata Yar kebbi Maman husna daga ita har mijinta duk yan kebbine, itama ba karamin shiri muke dasu ba, gashi haɗa min kayan hidima suke su sunzata yar hannunce ni🙈🙊 nan kuwa ko bakin gefe ba akai da zuwa ba,
Ina gamawa na fito da abinci na kaimasa har ɗaki ganinshi ɗaure da towel sai ya bani kunya na ajiye zan fita, shan gabana yayi, yasaki, buga kafana nayi cikin sakalci nace.
"Nikan zanje na kwanta."
"Hmm humm ahh waya koya miki, kulawa da miji,"
Hararar shi nayi nace.
"Inda ake koyarwa mana"
Buge min baki yayi yace.
"Har ynx baki horo ba, amma bari nayi gwajin takalmi, inji maza da."
Ainkuwa kafin nasn nufinshi ya cillani gado, yabi bayana yana min cakulkuli dariya har da rike cikina muna cikin haka wayarshi ta fara kara, ɗagowa yayi yaga nombe hauwa tsaki yayi ya ajiye kiran naji ba daɗi, amma sai nayi fuska nace.
"Ka ɗauka mana"
Zaro ido yayi yace..
"Wani Shehu ɗan shehu, jikan Usman ban shirya sayan saya sabon waya ba a ynx."
Dariya nayi na gudu nabarshi a ɗakin koda ya gama cin abinci ya biyo lokacin ina ciki da amfani da magani na mikewa nayi na koma ban ɗki na karasa, ina fitowa na kwanta kashe wutar ɗakin yayi yaxo muka kwanta, hira muke cike da farin ciki, wanda jikina ya mutu da irin hiranmu, sosai muke tarairayar juna, cike da so da kauna, wanda ban taɓa tsamani zan iya nuna masa ba, a ranar saura kiris abubuwa su faru, amma da kanshi ya hakura da haka badan kome basai dan lalurata. Rungume ni ya muka cigaba da bacci,
Can wajen karfe biyu da wani abu na farka afirgice, kuma a tsorace addu'a nayi na zare jikina daga nashi nashige banɗaki wanka nayi tare da alola nafito na tadda sallah, ra'a biyu nayi na zauna na cigaba da addu'a na rasa gane mi ya tsoratani alqur'ni na ɗauka a side bed na fara karatu, sautin karatuna ne ya ɗaga shi yaga alamun sallah nayi shima tashi yayi yaje yayi wanka da alola sannan ya fito, sallah ya gabarta ina a takaice bamu tashi a gurin ba sai da asuba yai mukayi sallah sannan muka koma,
Bamu tashi ba sai bakwai saura a gurguje muka tashi nayi na da niyyar haɗa masa abinci karyawa rike hannuna yace.
"Kiyi min ɗumame da tea sun ishani."
Toh kawai nace naje nayi masa yanda yace na kawo masa,tare muka ci sannan ya fita na rakashi har bakin kofa.
Dawowa nayi na kwanta a kan kujera jikina a mace na rasa meke min dadi a rayuwa, har kusan karfe ɗaya na tashi na haɗa abincin rana fried rice da zoɓo wanda na haɗa da fruit nayi blender dinsu bayan zoɓo ya nuna na juye a ciki abinci kuma nasaka a micro, sai kifi nasoya bayan na markaɗa kayan miya tattasai albasa,da green chill, bayan na soya miyar sauce ɗin na zuba masa, magge da kayaɓ spices na juye akan kifi na zuba ruwa cikin cokalin miyar na yanyanka albasa na watsa akai, na rufe na rage karfin wutar gas ɗin sannan sallar azahar nayi ban fito ba har sai sanayi la'asar sannan nafito, na kuma kitchen ɗin nan na tacce zoɓon sai kamshin su citta yake da fruit musaman cucumber da abarɓa, sachet ɗin tiara na saka guda ɗaya brown sugar nasaka, a zoɓon yayi dai dai yanda imamu zaisha.
Wayata na kunna na buɗe data na shiga google inda na shiga niman wani babban super mkrt dake kusa dan banda gidan Maman husna, ban taɓa zuwa ko ina ba, aikuwa dan gaba damu tafiyar minti shabiyar zai kaika a bus inda da kafane tafiyar minti talatinne babban jacket na ɗauka nasaka bayan na ɗibi zoɓo, na zuba a wani goran ruwa na ɗauko kuɗaɗɗen da yake bani na shiga dakinshi, na shiga auna tsayinshi da nariga da na wando, da sauri na fita, daga gidan na mikawa Mmn husna zoɓo da abincin da nayi nace ta bawa husna.
Tafiya kaɗan ya kaini bus stop, daga nan na faɗa masu inda zan sauka, aikuwa bamu jima ba muka isa sauka naga shagon nan nashiga duba kayan ina zaɓa masa, riguna da wanduna, kusan kala biyar biyar naje gurin takalma na ɗiba masa, irin boot ɗinan na maza kala uku, da face cap nifa dole wai mijina sai yayi gaye gaye(😂 lolx baby maryam kiyi hakuri na bar miki Baban waleed dukkanshi kema kije canti ki sayo masa kaya.)
Ina gamawa naje gurin biyan kuɗi na biya nafito bansamu bus ba sai taxi shi nashiga ya kawoni har bakin unguwarmu dake najima a shagon har yamma yayi dan kusan six na dawo nan nashiga niman hanyar gida amm Ban gane layin mu ba tun ina ɗauka wasane har duhu ya fara mamaye garin kuka nasaka dan abinda na fahimta shine na ɓata..........
Tohfa Ana wata ga wata.......Naiha taɓa Maman sadiq da Sister Hadnoor na Musha karatu saiku bazana niman naiha......
*_Mr & Mrs Usman S Usman Happy Honey Moon_*♥
[5/4, 06:19] Me Dambu: 🌹🌹👳
*MATAR MALAM*
🌺🌺👳
*Na:Mai_Dambu*
*Wattpad:Mai_Dambu*
*:~•34*
Dafe goshi nayi cikin da nasani mara amfani, kuka nake sonyi amma na gaza yinshi, ga garin ya fara duhu fa sai wutar layi.
«»
Karfe biyar da rabi ya dawo gida kararawar kofar ya latsa gar sau biyu ban buɗe ba sai ga Husna da kaninta Ra'if, gaishe shi suka sannan suka kalleshi alamun tambaya da cewa.
"Kawu Aunty bata dawo bane ko?."
Maida hankalinshi yayi gurin yaran yace.
"Tafita unguwane?"
Dake mamarsu tana kaɓarsu akan babu kyau kome aji abakinsu, sai husna tayi maza ta gyara,zance da "ai muma bamu sani," tsagal Ra'if yace.
"Kawu naji Amminmu tana cewa sai tadawo, ita kuma Aunty tace super mkrt zata."
Murmushi yayi ya musu ya shafa kanshi ita kuwa husna sai aika masa da harara take, sallamar yaran yayi ya koma cikin mota ya zauna. Tun yana saran ganina, har lokacin sallah yayi,ya tafi masalaci bayan dawowarsu yake faɗawa Baban Husna ban dawo bafa yana tsoron kar na ɓata,
Ai basu zauna ba suka nime yan sanda da suke patrol a area suka shaida musu, hankalin Imamu idan yayi dubu ya tashi, kaman zaiyi kuka, kasan ranshi kuwa wutar ɓacin rai kawai yake ruruwa.
Nan su da Yan sanda suka shiga bin hanyar da taimakon, sadarwar Cctv, sunga fitana har zuwa super mkrt, abin mamaki dawowata ne basu lura dashi ba dan babu camera a guri.
Tsananin ɓacin rai da Imamu ya shiga kuwa har jijiyar goshinsa sun fito raɗa raɗa,
«»
Ni kuwa ina tsakanin unguwarmu, sabida ruɗu da ɗimuwa yasa na ɓata nabi hanyar gater ɗinmu yafi sau goma amma banyi tunanin shiga ba, gani nake unguwar wasune, kuma ina rike da kayan da nasayo.
Ina cikin tafiya na hango wasu gungun yan iska sai shaye shaye suke abinsu, tsoro da fargaba yasa kafafuna suka fara harɗewa dakyar na isa gurinsu na ratsa tsakiyarsu zan wucce, aikuwa suka kewayeni suna dariya, sabon tsorone ya cikwikuyeni, bansan lokacin da na sake kayan hannuna ba, na fashe da kuka, ina niman hanyar guduwa,yunkurin guduwa nayi babban cikinsu ya fisgone ya falla min mari ya haɗani da bango, wani marayar ihu na fasa tare da zuɓewa kasa ina dafe keyawa,.
Jin ihuna yasa Imamu ya nunawa Yan sandar dake tare dasu inda yajiyo ihun basu masa gardama ba, suka tawo inda muke da sauri,dai dai katon ya kai hannunshi zai buɗe gyalena da nayi rolling ɗinshi yaji an rike masa hannun cikin ɓacin rai ya ɗago, ganin waye yayi masa wannan shamakin, sai yaga yan sanda akewaye dasu hannunshi kuwa Imamune ya rike, sabida kishi irin na imamu sai da yakifa masa mari wanda yaja hancinsa ya fashe,(😎lolz)
Kamasu yan sandar sukayi Baban husna ya tattara min kayana shi kuma ya ɗauke ni cak zuwa mota, koda muka isa gida hakuri Baban husna ya bashi sannan ni kuma yayi min Allah ya tsare,
Baban husna nabarin gurin ya buɗe motar ya fincikone zuwa cikin gida dan ya cire key a jikina,muna shiga ciki kuwa ya kifa min mari sannan yafita kayan ya kwaso ya watsa min a fuskana yace.
"Kai Subhanallahi ke kan wacce irinyar mutunce haka, mi kike so nayi miki a rayuwa wanda ban miki ba,ok ynx na fahimci matsalar baki sona kuma bazaki taɓa sona ba,"
Cacumoni yayi ya haɗi da bango, yana hucci yace.
"me kika ɗauke ni lusari dan kinga na zuba miki ido, shine zaki maidani mutumin banxa, da girmana da mutuncina Yau da wani abu yasameki me zancewa Iyayenki." Cikin tsawa yayi maganar, kifa kaina nayi a