Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

RUDIN SHAIDAN
Littafin Shuraih Usman
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com

RUDIN SHAIDAN
Gajeran labari
Marubuci
Shuraih Usman
© Shuraih 99% - 2018
Part 1
.
"Uztaz"uztaz"uztaz" tayi kururuwa yanda wayanda suke
nesa da ita ma sai sunji muryarta
.
Kyakkyawar budurwace take tafiya sauri sauri don ta
cimma wani mutum dake gabanta,
Da ganin fuskar budurwan kasan tana dauke da abu mai
muhimmanci, wanda ya shafi rayuwarta
.
Azuciyan budurwan nan kuwa ta tabbata komai zaiyi
sauki muddin ta samu suka tattauna da wannan bawan
Allah din
.
Da Sauri sauri gudu gudu ta karisa har wajen wannan
mutumin , kuma bata daina kiran sunan sa ba Uztazz
.
Mujahid yana cikin tafiya akan hanya a yayin daya ke
nazarin wata littafin Addini , kaman daga sama sai yaji
ana kiran sunansa
.
Nan ya juya don ganin mai kiransa , toh anan ne yayi
arba da wata budurwa tana sauri don ta iso wajen da
yake .
Kallo daya yayi mata yasan ba lafiya take ba dole akwai
wani abun dayake damunta
.
Koda ta kariso gabanshi sai ta cigaba da maida numfashi,
duk tabi ta jike da zufa a dalilin gudun da tayi
.
"Ina yini yallabai ,nasan na takuramaka bisa tsareka a
hanya da nayi ,ina baka hakuri Uztazz,
Ina da wasu batutuwa danake son mu tattauna dakai izan
ban takuramaka"
Budurwar ta fada a lokacin da take tsaye agabanshi,
.
"Babu damuwa ina sauraronki" uztaz ya fada
"Suna na Rufaidah, nasan baka sanni ba , Ni dalibace a
makarantar Mu'azu bin jabal ,
Satinnan nayi rigestration" rufaidah ta fadi
.
.
Mujahid ya dubeta da kyau sannan yace "toh malama
rufaidah ina sauraronki shin wata maganace kike son mu
tattauna akai,
Shin maganar da zamuyin magana ce wacce zamu iya
yinta a tsaye, ko kuwa sai mun samu wajen zama"
mujahid ya tambaya
.
"Uztaz gaskiya yana da kyau mu samu wajen zama domin
kuwa , dogon zance ne zamuyi, domin kuwa bazan taba
runtsawa ba muddin ban fadi maka ba"rufaidah ta fada a
lokacin har hawaye sun fara zuba daga idanuwanta
.
Yafara waige waige ko zaiga wani dan inuwa ,
Cikin sa'a kuwa sai ya hango wani dakali a kofan gidan dake nesa da su, rufin gidan ya yayiwa dakalin inuwa
Ya dubeta yace "toh mu karisa can sai kiyi mani bayanin "
"Toh "
.
Suka nufi dakalin
Bayan sun zauna sai mujahid ya dubi rufaida yace "malama rufaida ina sauraronki"
Rufaida wacce hawaye suka bata mata fuska ta goge da mayafin jikinta ta budi baki tamkar ba zata iya magana ba ta fara bada labarinta kamar haka
"Sunana Rufaidah...........
.RUDIN SHAIDAN
Gajeran labari
Marubuci
Shuraih Usman
© Shuraih 99% - 2017
Part 2
.
"Sunana Rufaidah ina zaune ne a lafiya, mahaifiyata ta rasu tun ina yar shekara goma sha shida,
Babana yana matukar sona,
Hakanne yasa ya karo aure don ya samu wacce zata runga kula dani,
,
Nayi zaman kadaici lokacin da mahaifiyata ta rasu, duniya tayi mani baki kirin sanadin rashin mahaifiya, akullum nakan zauna nayi shiru ina tunanin mahaifiyata da duk wasu abubuwan da suka wakana tsakanina da ita
,
Matar da babana ya auro inna ladi, ta tsaneni matuka tana azabtar dani sosai,
Arana in ban sha bulala ba kenan tayi mani dari,
,
Kwanan kullum wuni takeyi tana azabtar dani na zama abun tausayi , a wajen mutanen angwanmu kowa yana matukar tausaya mani
,
Nasan zaka yi tambayar ina mahaifina yake lokacin da take gana mani irin wayannan azabobin,
Tunda mahaifina baba sallau ya auri inna ladi shikenan duk wata kauna daya ke nuna mani ta rikide ta koma kiyayya sam baya kaunar ganina cikin gidansa don kuwa bazan taba mance wata rana ba ranar da itace ta janyo mani duk wannan ukubar dana ke ciki,
,
Bana fatan irin wannan ranar ta sake zuwa cikin rAyuwata,
Wata rana da safiya Na futo daga cikin dakina daga ni sai wani yamutsatsen shimi da wani kodadden zani, buta na rike a hannuna
Na je na bude randar gidanmu na debi ruwa
Na nufi bayi, ina shiga bayin ta kurma mani ashar
"Ke dan uwarki ina cikin bayin shine har zaki shigo"
Da guduna na fice daga bayin,nazo na rakube a gefen dakina jikina sai makyarkyata yake, a tsorace nake dun nasan yau sai naci duka sosai,
,
"Yau zaki ci uwarki dani, sai na kure rashin kunyarkin nan"
Inna ladi ta futo daga bayin tana fadin haka,
Ta harbeni da butan dake hannunta, butan ya sameni aka tsinin bakin butan ya sokeni cikin kaina, sai ganin jini nayi yana bulbulowa daga kaina,
,
Maimakon inna ta razana sai ma kara harzuka tayi ta nufoni gadan gadan, tana zuwa ta wankeni da mari, nayi kokarin sanya hannuwana na rufe kuncina, nan ta hau jibgata tamkar tarin dawa, tun ina kururuwa ina bata hakuri har nayi lamo , bakajin sautin komai sai nishi na dake tashi a hankali,
,
Saida tayi mani likis sannan tayi shigewarta cikin daki,
Ina nan a kwance akas ina nishi sama sama, har baba sallau ya dawo daga wajen aiki,
Kallo daya yaimani ya watsar, daga nan yayi shigewarsa cikin dakin inna ladi,
.
Ina jin muryansa yana tambayar inna me yafaru dani,
"Shegiyar yarinyace, dubifa ina cikin wanka a bayi ta shigo kanta gade, shi yasa na lakada mata wannan duka"
,
Baba sallau yace "ai kaji irinta saida nace maki duk randa yar iskarnan tai maki abu, kiyi mata dukan da bazata ma iya motsa koda dan yatsanta ba yo gata can har ta fara mikewa",
Fuu ya fito daga cikin dakin hannunsa rike da dorina mai baki hudu, ina kallonsa ya nufoni, nayi kokari na mike don na ceci rayuwata amma babu hali sakamakon ji dana keyi tamkar an dora mani mirginenen dutsene a bayana
A Haka ya cimmini ya dunga tsala mani dorina a bayana, tun ina iya bashi hakuri har na fara ganin dishi dishi, daga nan ban san abun daya biyo baya,
Abun da zan iiya tunawa shine kamar naji muryan makwabcinmu malam buba yna cewa "haba sallau kasheta zakayi, wannan wani irin jahilci ne , yarka ce fa ta cikinka"
"Toh ba gwamma na kasheta na huta da irin bakin cikin datake kunsa mani ba"
**********
Bani da farkawa ba sai a gadon asbiti inda nayi arba da malam buba a gefena, sai wani doctor fari dogo yana sanye da rigan asibiti (lab coat)
Na daga kaina don ganin rufin dakin anan ne naga ledar ruwan da ake karamani
,
Kwalla ne ya fara gangarowa akan kuncina,
Ji nayi na tsani mahaifina, na tsani kishiyar babata, inna ladi,
Na kasa yarda cewa mahaifina ne yai mani wannan dukan,
Duk irin kiyayyar da mahaifina yake nuna mani ban taba tsammanin takai ga yana neman ya kasheni ba,
.
Malam buba ya dafa hannuna yace "rufaida kiyi hakuri, kinji Allah sai ya sakamaki, akwai ranar kin dillanci"
Nayi shiru ban ce masa kala ba ya mike yace min "ina zuwa rufaida bazanje gida na dauko maki abinci na dawo, kinsan uwargidana tayi tafiya"
Ya dubi likitan dake gefensa yace "likita daga nan zanzo da cikon kudin "
Likitan yace "ok ina jiranka a ofishina "
Dukkansu sukai ficewarsu ,
.
Bayan fitar malam buba sai na daddage na daure na mike zaune, na cire ruwan da ake karamani, na ajiye a gefe,
Na mike na shiga tafiya ban san ina na nufaba, ko kadan bana kaunar komawa gidan mahaifina
Bayan na fito daga cikin asibitin sai na wuce tasha, anan ne na hawa motar keffi,
,
Acikin motar na hadu da wata mata , wacce na lura tun shigata motar take kallona,
Cikin kankanin lokaci matar ta gama shawo kaina na amince zan zauna wajenta a garin keffi,
Matar me suna jummai itace ta fara dora ni a turban KARUWANCI,
Tun daga wannan lokacin karuwanci ta zama sana'ata da ita nake ci da ita kuma nake tufatar da kaina,
Na tsinci kaina cikin wani yanayi, wadda cikin sati muddin namiji bai kusanceni ba toh banajin dadin jikinah,
Sai a kwanakin baya ne nayi wani mugun mafarki wanda ya rikita mani kwalkwalwa nan take naji nadama tazo mani,
Naji na tsani kaina da kaina, naji ina kyamar irin rayuwar danayi a baya,
Nayi yunkurin na kashe kaina, daidai zan sha guba shine naji WA'AZINKA a gidan rediyon maloney fm,
Shi yasa na fasa kashe kaina,
Uztazz ! Shin Allah zai iya yafemani wayannan laifukan nawa kuwa?"
.
Mujahid wanda tun lokacin da rufaida ta fara bada labarinta yayi shiru ya kuma natsu sai yanzu yayi gyaran murya sannan yace "malama rufaida hakika Allah maji roqon bawansa ne.....
RUDIN SHAIDAN
Gajeran labari
Marubuci
Shuraih Usman
© Shuraih Usman - 2018
Part 3
.
Mujahid wanda tun lokacin da rufaida ta fara bada labarinta yayi shiru ya kuma natsu sai yanzu yayi gyaran murya sannan yace "malama rufaida hakika naji dukkan labarinki na kuma tausaya maki bisa ga halin da kika tsinci kanki abun dana ke son ki sani shine Allah maji roqon bawansa ne, muddin kinyi imani kan ba zaki koma ki sake dulmiya cikin wannan sabon ba, toh Allah zai yafe maki shi kansa Allah yana son bayinsa masu Tuba, kuma a kowani lokacin Allah yana amsar tuba"
.
"Uztazz yanzu me da me yakamata na dunga aikatawa na wanda zai nisantani daga alfashan dana bari"
"Ki yawaita yin Azumin litinin da alhamis da yin Sallah akan lokaci,sa'annan ki yawaita karatun al'qurani da yaddar Allah zaki ga rayuwa tazo maki da sauki sannan kuma akwai darasi na musamman da ake dauka a makaranta ranan asabar da lahadi, na matan aurene kiyi kokari ki runga zuwa"
.
Ta mike tsaye yanzu kam fuskarta sai sheki yake tayi wa uztazu mujahid sallama, ta yi tafiyarta
,
Uztazu mujahid
Asalinsu mazauna kaduna ne daga bayane lokacin da aka yi wani rikici a kaduna shine sukai hijra suka zo keffi, jihar nasarawa
Mujahid ya taso a gidan mutunci, tun yana dan shekara biyar mahaifansa suka sanya shi a makarantar islamiya na mu'azubin jabal,
.
Wannan yasa yataso cikin tarbiya da sanin ya kamata, gashi fasihi da an biya masa karatu yake dauka,
Wani lokacin sau daya yake karanta abu ya haddacesa akansa,
,
Malamai da mutanen angwansu suna yabonsa , bisa matukar kokarinsa,a haka har ya sauke alqur'ani,
,
Mujahid dogone baki mara duhu, fuskarsa a shimfide take, dararan idanunsa gami da dogon karan hancinsa, da dan mitsitsin bakinsa, su suka karawa fuskarsa kyawu,
,
Arayuwar mujahid bai damu da mace ba, babu ruwansa da neman mata, haka kuma bai cika magana da mata ba, gaba dayan al'amuransa ya karkatasune ga karatunsa,
,
Ahaka har Allah ya sanya ya zama malami , yana koyarwa a makarantar mu'azu bin jabal makarantar data fara haska kwalkwarsa,
.
Haka kuma yanayin program da dama a gidajen talabijnin na garin keffi,
Kaf mutanen keffi babu wanda zaka tare shi ka tambayeshi wanene Uztazu mujahid yace maka bai sanshi ba,
,
Ayanzu haka yana 100 level zangon farko a karatunsa na jami'a wanda yake a jami'ar NSUK
,
Bayaune karo na farko da mujahid yake haduwa da mutane masu matsaloli a rayuwarsu ba
Shi ya sa ma bai nuna damuwarsa sosai ba ga labarin da rufaida ta bashi,
,
Ya mike ya nufi gida,
********
Wa she gari mujahid ya shirya ya nufi makarantar mu'azu bin jabal,
Yana karisowa ana kiran Sallan La'asar,
Bayan ya ja sallah ya idar lokacin mutane sun fara watsewa daga masallacin,
Ya mike ya fita daga masallacin ya nufi wani lungu wanda yake cikin makarantar,
.
Gajeriyar Tafiya yayi takawoshi ga wasu ajujuwa guda biyu,
Ya nufi ajin dake farko ya bude kofar hade da sallama, sannan ya shiga
"Wa'alaikassalam" matan dake cikin ajin suka amsa masa
.
Babban ajine wanda ya isa akirashi da falo,
Ajin ya kawatu da ire iren kayayyakin da ake bukatan agansu cikin ajin makarantun islamiya,
,
Zazzaune akan kujerori, sanye da bakaken hijab mai hade da nikab,
Matane burjik
Mujahid ya samu kujera ya zauna sannan ya mika hannu ya dauko abun daukan sauti Microphone,
,
Anatse yake masu karatun, yana kawo masu hujjoji, cikin hadisai da qur'ani,
Fuskarsa yana kallon littafin dake ajjiye akan teburin gilashin dake gabansa,
,
Bayan ya iddar da darasin, sai ya daga kai ya dubesu yace
"Masha Allah mun iddar da darasin wannan satin, in Allah ya yarda sati mai zuwa zamu yi bayani akan Jinin NIFAS , amma kafinnan dakwai mai tambaya akan wani abu da bata gane ba"
.
Ajin yayi shiru, ya dade yana kallonsu koda zaijji mai tambaya a cikinsu,
Dayaji shiru sai yace "tun da bakwada tambaya ina ganin lokacin tashi ma yayi sai kuyi mana addu'a?"
Dukkansu suka hada baki sukai Addu'a
.
Ya fito daga ajin lokacin da hayaniya ta fara gauraye ajun,
Da sauri ya nufi bangaren da zai sada shi da masallacin makarantar,
"Uztazz" yaji an kirasa daga bayansa
Ya juya da sauri saboda ya gane mamallakiyar muryan
,
Rufaidace a gabansa sanye da wani murgujejen bakin hijabi har kasa, ta yaye nikab din dake fuskarta sama,
Hakanne ya fallasa asirin zunzurutun kyawun dake tattare da fuskar, wanda sam mujahid bai lura da shi jiya ba
.
Kyakkyawace fara doguwa, ta mallaki faffadan fuska ma'abocin sheki,
Mujahid na kallonta yaji zuciyarsa ta buga,
Tunda yake bai taba kallon mace zuciyarsa ta buga ba sai a wannan karon
.
Yasha arba da kyawawan mata wayanda suka dare rufaida kyawu, amma bai tabajin hakan ba sai ayau da suke tare da Rufaidah
,
Cikin takun nutsuwa ta kariso inda yake yadda take tafiya sai ka rantse mara lafiyace,
Murmushine dauke akan fuskarta,
"Inayini uztazz" ta fada lokacin data kariso
"Lafiya malama rifaida? Ya karatu da makaranta"
"Lafiya lau ?dama uztazz tambaya nake so nayi game da darasin yau"
.
"Mai yasa dana tambaya ko akwai mai tambaya baki tashi ba" ya tambayeta fuskarsa na kallon kasa
"Kunyar mutane naji ? Amma kai hakuri"
Ta bashi amsa
Ya jinjina kai yace "malama rufaida in har kina so ki karatu ki san addini sosai dole sai kin cire kunya da tsoro acikin zuciyarki, ya kasance kina yawan tambaya akan dukkan wani abun da baki gane ba, ko baki sani ba, Tambaya mabudin ilmine, dafatan dai kin gane"
Ta gyada kai
Yacigaba
"Yanzu ina sauri da kwai inda zani izan mun hadu gobe cikin aji sai kiyi tambayan"
"Toh uztazz sai anjima" ta fada cikin marairaice murya,
Mujahid ya juya yacigaba da tafiyarsa
******
.
Alkalamin 99%
RUDIN SHAIDAN
Gajeran labari
Marubuci
Shuraih Usman
© Shuraih 99% - 2018
Part 4
.
Tun daga wannan rana sai ya kasance rufaida ta zage dantse sosai kan karatunta, a kowani rana akayi darasi sai ta yi tambaya akalla goma
.
Sosai mujahid yake jin dadin yadda take da matukar kokarin ganin tayi tambaya kan duk wani abun daya shige mata duhu,
.
Ta hakanne mujahid ya gane cewa rufaida mace ce nutsatsiya bata cika son magana da mutane ba,
Haka kawai yaji tana burgeshi, duk da kasancewar magana bata cika hadasu ba sai in ana dau kan darasi
,
"Malama rufaida ina jin dadin yadda kike da kokarin fahimtar darasi sosai,
Ki cigaba da aiki mai kyau sannan a kullum ki runga rokon ALlah ya yafe maki zunuban ki na baya, "
Mujahid ne yake fadawa rufaida haka wani lokaci da suka hadu bayan an fito daga daukan darasi
Rufaida tayi murmushi tace "nagode uztazz, ina matukar godiya ga taimakon ka, Allah yayi maka sakayya da kyakkyawan karshe, kuma in sha Allahu bazan gaza ba wajen karatuna, da halayyana,"
.
*******

"Rufaida wata shawara nake so na baki mai matukar muhimmanci? Wacce nasan ba za ki yi nadama ba muddin ki kayi aiki da ita "
Mujahid ya fada yana kallon. Teburin gilashin dake gabansa,
Rufaida wacce take tsaye a gabanshi tana sanye da burgujejen hijab dinta fuskarta na boye cikin nikab,
Kwayoyin idanuwanta ne kadai a bayyane
Tace "ina saurarenka uztaz dun na san baza ka taba sani a hanyar da zanyi danasani ba"
.
Mujahid ya dago kanshi ya dubi rufaida a karon farko kwayan idonsa ya ci karo da nata
Nan take yaji zuciyarsa ya buga da karfi,
.
" mutuncin ko wacce ya mace shine tayi aure tta samu kanta a Gidan mijinta,
Alokacin da akace maki mace tayi aure, kimarta yana karuwa a idon mutane, darajarta yana daukakuwa a wajen ubangiji, sam bai kyautu ace mace kamarki tana zama babu aure ba, kiyi nazari sosai ki duba maganata zaki ga cewa gaskiya nake fada maki"
.
Rufaida tace "nagode uztaz da shawarar daka bani ni kaina abun dayake cimin tuwo a kwarya kenan, bana da wani buri da ya wuce nai aure , toh amma bana da yadda zanyi don shi aure nufin Allah ne shi yasa na fawwala dukkan lamurana ga Allah"

.
**********
"Kwankwan! Kwankwan!! Kwankwan!!!" Sautin Karan kofan dakin ya gauraye dakin
Yana zaune akan kujera yana nazarin wani karamin littafi
Sai ji yayi ana kwankwasa kofan dakinsa
Yana daga zaunen yace "waye wannan, "
Maimakon abashi amsa sai aka cigaba da kwankwasa kofan dakin
"Ina zuwa " mujahid yafada yana yunkurin mikewa
.
Cire sakatar dake jikin kofan yayi sannan ya bude
Cikin matukar mamaki ya ce "malama rufaida kece a gidan namu, "
Rufaida wacce take tsaye a jikin kofan dakin, sanye da burgujejen hijabi ruwan kasa, hannunta na rike da Kulan zuba abinci,
Tayi murmushi tace "eh wallahi uztaz nice "
"Shigo daga ciki mana" yafada lokacin daya juya ya koma cikin dakin,
Ta shigo cikin dakin tana duban yanayin dakin
Komai na dakin cikin tsari yake,
Ta zauna akan tangamemen katifarsa wanda ya kusa mamaye dakin,
Shi kuwa mujahid sai ya zauna nisa da ita sosai akan kujeransa,
Har alokacin zuciyanshi yana bugawa,
"Dafatan dai komai lafiya malama rufaida
Mujahid yafada
.
Rufaida tace "komai lafiya ustazz dama abuncine na girka na kawo maka"
"Na gode rufaida , Allah yabar zumunci "
Sun danyi hira sosai kan batun karatu, kafin ta mike ta tafi
.******
Tun daga wannan rana sai ya kasance kusan kullum sai rufaida ta girka abinci ta kawo ma mujahid,
.
Aduk lokacin da ta kawo abuncin mujahid yana kokari yaga ya nisance ta, saboda gujewa RUDIN SHAIDAN,
.
Rufaida ce a tsaye. A bakin kofan dakin mujahid wanda dakin ya kasance a wani gefe daban na gidan na su,
,
Tana sanye da riga da siket, wayanda sukayi matukar dame ta, ta yafa dan fingilallen mayani, inda mayanin ya samu nasarar rufemata daga kan kirjinta zuwa cibiyarta,
,
Sake-sake take a zuciyarta na ganin ta samu cikar burinta,
"Wannan daman itace dama ta ta karshe ba zan taba yin sakaci da ita ba"
Rufaida ce take fadin haka cikin zuciyarta,
Ta dade a tsaye kofan dakin tana saka abubuwa cikin zuciyanta,
Kafin daga karshe ta fara kwankwasa kofan
.
Kwankwasawa biyu tayi taji alamun ana zare sakatar kofan,
Da sauri ta gayra ttsayuwarta,
Mujahid ya bude kofan dakin,
lokaci guda numfashinsa ya tsaya sakamakon Ganin irin shigan da rufaida tayi
Ita ko rufaida koda taga haka sai tayi murmushi sannan ta wuce cikin dakin ,
Kai tsaye kan katifarsa ta nufa tana zuwa ta zauna akan katifar,
.
Mujahid wanda abun ya matukar rudashi, ya juyo ya dubeta lokacin daya dan bata ransa yace "menene ya faru"
Ganin irin yadda yayi maganar shi ya sanya rufaida ta sha jinin jikinta, mikewa tayi ta matso inda yake a bakin kofa tace
"Farin ciki nazo ka tayani" tana maganar cikin wani irin salo
"Na me" ya tambaya
Batare data bashi amsa ba sai ta rungumeshi,
Ya fara kokarin ya bambare jikinsa daga nata, sai ji yayi ta kama kanshi ta hada bakinsa da nata
,
Duk yanda mujahid yayi don ya hanata abun datake kokarin sashi aikatawa amma ya kasa,
Ji yayi gaba dayan lakar jikinsa sun mutu, yanaji yana gani ta tureshi kan gado sannan tabi bayansa,
,
,

RUDIN SHAIDAN
Gajeran labari
Marubuci
Shuraih Usman
© Shuraih 99% - 2018
Part 5
.
.
Cikin magagin barci ya farka,
Mikewa yayi daga kan katifarsa , ganinsa da yayi a tube babu ko singeliti shi ya tayarmai da hankali,
.
Sai a sannan madaukin kwalkwalwarsa ta fara haska mai duk abun daya faru baya tamkar a majigi,
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'uun"
Shine abun dayake ta furtawa a fili,
Kafin ya fashe da kuka
Ya dau lokaci yana kuka shi daya a cikin daki
Zuciyansa na tuna mai da abun daya aikata ji yayi ya tsani kansa da kansa,
"Shike nan na biyewa son zuciyata na gurbata rayuwata, da wanne irin ido zan fuskanci mahaliccina ,"
Mujahid ne yake fadin hakan cikin zuciyarsa
,
"Rufaida TA CUCE NI ta bata mani rayuwa, "
Waige waige ya farayi yana neman wani abu, ya dau lokaci yana tsaye
Yana kare ma dakin kallo zuciyarsa na ci da wuta,
.
Wani farin takarda ne ajjiye akan katifarsa ya dau hankalinsa, ya mika hannu ya dau takardan,
Gajeran rubutu yagani, ya fara karanta rubutun
"Assalam social Uztazz, burina ya cika , na dandani abun dana ke kwadayin dandana wanda yake tattare da kai, daga wannan rana baza ka sake ganina ko jin labarina ba,
Daga Rufeeeee."
.
Katon makwallaton hushine ya tokare mai makogwaro, shakka babu da zai hadu da rufaida a wannan lokaci da babu abun da zai hana bai kasheta ba,
.
hankalinsa ya dugunzuma ransa ya baci,idanunsa suka yi jajur da su kamar garwashin wuta. Da kyar yake numfashi kamar kumurcin maciji,
Ya yayyaga fallen farin takardar
********
Tun daga wannan rana mujahid ya dena futa daga gida hatta makaranta ya dena tafiya babuu inda yake zuwa kullum yana kulle cikin daki
.
Lokaci daya ya fara ramewa ,babu irin dabon duniya da mahaifiyarsa batayi ba don ya fadi mata me ke damunsa amma yaki,
A kullum babu abun dake ci masa zuciya face zullumi, da tunanin irin babban sabon daya aikata wa ubangiji,
.
Ga duk wanda yasan uztaz mujahid, kallo daya zai mashi ya gane cewa da kwai abun da ke damunsa,
Rufaida kuwa tun daga ranan da wannan abu ya faru, aka daina ganinta a makaranta, ko duriyarta an daina ji
.
**********
.
.
Motace kirar peogeut ta faka a gaban dan kareren Asibitin
Daya daga cikin masu bayarda tsaro a sibitin ya na sanye da uniform din aikinsa ya mike daga kan kujeransa ya nufo wajenda da peugeot din ta faka, koda ya kariso sai ya karkato da kanshi kasa ta yadda zai iya ganin mutanen da suke cikin motar,
.
"Sannu maigida"
Mai bada tsaron yace
"Yauwa sannu"
Mutumin daya ke cikin motar ya amsa
Mai bada tsaron ya sanya hannunsa aljihu ya ciro wata karamar kati ya baiwa ya mika wa direban motar,
Direban motar ya sa hannu ya karfa yana mai kallon katin wanda yakasance korene ajikinsa an rubuta, F M C passing card,
"Nagode "direban ya fada
A daidai lokacinne mai bada tsaron ya daga wa dan uwansa wanda yake nisa da shi hannu,
.
Aka
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment