Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

MUN JI MUN GANI
Cigaban Sirrinsu
Na Maje elhajeej
Typing by Shuraih Usman
Ebook creator Shuraih 99%
Ebook publish by http://hausaebooks.cf
.
Zaku iya downloading wasu ebook namu ta hanyar dannan wannan adireshin yanar gizo gizon http://shuraih.waphall.com
.


"Habib daman kai muka kama jiya da daddare"
Kaman daga sama naji muryan sageer daga
bayana ina juyowa kuwa naci karo dashi, Sanye
da kakin yan sanda ya tsaya ajikin karafan da
suke manne da kofar cell din a ak kulle ni aciki.
Sageer abokinane. Munyi secondry tare dashi
har takaimu ga ga jami'a "Sageer" cikin mamaki
nafada . "Ina katsaya jiya har kakai dare haka"
Sageer yafada yana duban fuskana cikin mamaki
shima. Anan dai na ware mai bakin jaka Tun
daga haduwata da farida har jiya dana bisu har
cikin villa guest inn , Na tafi sanar da iyayenta
al'amarin ya kasance akaina . Lokacin danake
fadamasa labarin tattara hankalin sa yayi gareni
bayan na idar sai yayi jugum, kana ya nufi wata
durowar tulin takardu dake jingine a ofishin,
yafara lalube-lalube har sai daya zakulo wata
jarida,sannan ya bude inda yake son budowa ,
kana ya ajiye min agabana . Wanda hakan na
nufin yana bukatar na karanta "A GHOST WAS
MY HUSBAND FOR SIX YEARS WE HAD TWO
CHILDRENS" (Na auri fatalwa har tsawon
shekaru shida,mun kuma haifi 'ya'ya biyu tare)
Abin da idona yai karo dashi kenan ,lokacin
dana fara karanta jaridar.cikin sauri na juya
bayan jaridar. Jaridace mai suna Glow,fitowa ta
goma shatakwas , da ake wallafawa a ikeja dake
jihar lagos , akwatin gidanwaya 10352. Matar da
al'amarin ya faru gareta ga hotonta nan balo-
balo ajikin jaridar . "Lokacin dana karanta
kabarin ban gaskata ba, sai yanzu da ya faru
gareka ,karanta kaji abin dake kunshe cikin
labarin ,daidaine da abin daya faru gareka ,"
Sageer yafada yayin da hankalina ke kan hoton
matar da al'amarin yafaru gareta . *Shuraih
usman* (Labarin yana shafin ishirin da tara na
jaridar kuma agurguje abin dake kunshe da
labarin shine: Maimunat haruna ta hadu da
cletus ne a wajen wata liyafa ,tun daga ranar
taji ta kamar ta hadeyi shi saboda masifarsonsa
da taji tanayi. Kota ina ya kwanta mata
azuciyarta ,saboda kyakkyawane ya kuma iya
kwalliya . A kasancewar da su kayi tare ta
fahimci cewar batare da iyayensa ya keba ,
yakuma rabu da iyayensa lokaci mai tsawo baya
kuma son komawa wajensu . A tunaninta idan
tarabu dashi bazata kara haduwa da namijin da
zai shiga zuciyarta kamarshiba , bata kuma
tunanin rabuwa da shi . Saboda tarairayarta
daso da kauna dayakeyi. A takaice dai har
takaisu gayin auren shekara shida , suka kuma
samu yaya biyu junior da betty. Sannan ne
tarinka matsanta masa akan dole sai sun ziyarci
danginsa ,da kyar da jibin goshi ya amince.
Jihar filato nan suka nufa wata ranar litinin,suna
zuwa wani waje sai ya tsiyar da motar, ya
kwatanta mata gidan yace ta karasa yana tafe .
Babu irin magiyar da batayi masa ba don sutafi
tare , yalallameta akan taje shima yana tafe .
Mahaifiyarsa tana fitowa ta shaidata saboda
kama da sukayi da mijinta da kuma yayan
dasuka haifa. Ita kanta mahaifiyarsa sai ta
kurawa yayan ido don ganin sunyi kama da
danta . Tana shiga gidAn taga hotunansa tun
yana saurayi ,sannan ne tafadawa iyayensa tare
dashi suke. Dukkansu sai suka rinka kallonta
kamar daga wata duniyar ta zo,ita kanta sai data
tsargu akwai wani abu dake shirin faruwa. Kafin
wani lokaci makwabta sun taru agidan ,don
gaiyatarsu da iyayensa suka yi ,anan ne suka
bata tabbacin shekarun wanda ta ce shine
mijinta ,goma shadaya da shekawa barzahu.
(Lallai kam) *Mr: Shuraih 99%* *******
********* ******* "Nasir! nakirawo sunansa
lokacin ina tsayar da motar a kofar
gidansu,shikuma yana shirin shiga gidan . Galala
ya kura min ido ,tamkar fatalwa yake gani . Har
na rufe kofar motar naje wajensa kallona yake
yi, kamar ni, shi kansa kamanninsa sun birkita.
Shakka-babu al'amarn akwai rikitarwa ya
tabbata farida ta mutu sun kuma binneta ,sanna
kiri-kiri ba mafarki yayi ba ya kara ganinta.
"Habib! Yakirawo sunana cikin sanyayyiyar
murya . Na rike hannunsa muka nufi inda na
ajiye motar dana zo da ita ,gindin wata bishiyar
mangwaro dake nesa kadan da kofar gidansu
nasir. "Naseer! Danazo muku da labarin na
gamu da farida ,ta kwatanta min nan gidan ,na
kuma bata zobe kin gaskata ni kukayi. Kaine
kadai ka yarda dani,yayin dana tsinci zobena
akan kabarinta. Yanzu naji matukar dadi da kuka
ganta kai da meenat , me kuma zaka ce yanzu
game da wannan al'amari" Dukkanmu muka yi
shiru na wasu lokuta . "Babu abinda zan iya
cewa game da wannan al'amarin habib. Ni dai
nasan tabbas ya ta farida ta mutu shekaru uku
da suka shude , kuma tabbas na kara ganinta a
kano" (Wasa mafarin aiki*Mr: shuraih 99%*)
"Ranar alhamis da muka ga farida nida kai da
kuma meenat ,kashegari ranar juma'a na kara
ganinta tare da matar dana tambayeka ,kace
baka santaba . Wacce muka gansu tare da
faridar. Nayi kokari na bisu naga masaukinsu
(Villa Guest Inn),dana bincika sai naga kusin
kwana daya suka biya . Abin ya faru ne karfe
ukun dare , nayi yunkurin sanar daku a tarauni
jami'an tsaro suka cafkeni,na kwana a can sai
yau na fito. Ko gida banjeba na koma villa guest
inn din na tarar sun tafi . Ina zuwa ma'aikacin
dana tambaya ya gane ni,ya kuma nuna min 'yar
karamar jakarsu da suka manta ,wacce ya tsinta
a dakin dasuka kwana kaga jakar(nafada lokacin
dana dauko jakar daga aljihuna na nuna masa ).
Kyawawan zararrika ne masu kyan launi guda
tkwas aciki. Irin wanda na gani a hannun farida
lokaci na farko dana fara ganinta. Sai kuma wani
dan karamin kati an rubuta [BBH] ajiki. Shine na
galla masa karyar dama farida ce ta aikoni na
karbar mata jakar. Baiyi min gardama baya ni.
Nakoma tarauni sulaiman ya sanar dani kun
dawo gida .shine na biyo bayanku. *MR:Shuraih
99%* Kuma duba wannan jaridar kagani(na
buda mota na dauko masa jaridar sageer na
mika masa.). Wannan matar maimunat ta auri
mutumin da shekarunsa goma shadaya da
rasuwa,sunkuma haifi 'yaya biyu" "Shin yanzu
ina mijin nata?" Yafada bayan ya gama
karantawa . "Har yanzu bata kara ganinsa ba ,sai
dai 'yayan dasuka haifa " Ina rufe baki sai
mahaifiyarsu rike da hannun meenat suka fito
dga gidan ,wani mutum yana biye dasu abaya .
Basai aniyimin bayanin kowayeba nan take na
fahimci mahaifinsu ne. Meenat na ganina sai ta
kyankyame jikin mahaifiyarta ,yayinda ita kuma
mahaifiyar take yi min wani irin kallo dake nuni
da bata bukatan kara ganina kusa da iyalinta. Kai
tsaye sai mahaifinsu ya nufo wajena. "Bana
bukatar kara ganinka a kofar gidannan har
abada , yaya kake nema kazauta mun ahalina
(iyali munce yarmu ta mutu kace ba ta mutu ba
, to ina ruwanka da ita !koa kai ka haife mana
ita ! Idan nakara ganinka akofar gidna sai dai
kuliya ta rabamu" Wlh abokina ne ya takurani
saina Rakashi wajen budurwarsa. Amma gobe
JLAHADI11 ~ 4 ~ '99Arayuwata ban taba
haduwa da yamacen da cikin kankanin lokaci
hasken sonta yahaskaka ruhina da har nake
tunanin idan na rasata, son wata ya macen ba
zai kara samun sarari a zuciyata irin fareeda
ba.Babban abin dayake firgitani shine rashin
sanin ta-ka-maiman shin farida
mutumce,aljanace ko kuma fatalwa ! Shin
dagaske ta mutu ko kuma tana da rai"Idan har
farida ce ta ajiye zoben dana bata akan
kabarin,farida bata mutu ba.Idan kuma tana
darai menene dalilin kauracewA iyayenta
,bayan tasan inda suke ?Anaya babu hadin bakin
farida ?Idan kuMa da hadin bakinta takunkumin
ala-ka-kai, da'aka gindaya wa rayuwarta fa?Shin
menene hadin farida da wannan mummunar
matar?Kwata-kwata na gama tsarguwa ,da
al'amuran wannan matar.Tun lokacin dana dawo
daga kaduna ina zaune afalon gidan ahmad
.zuciyata fal da tunane-tunane.Ita kanta fatima
tazo ta zauna mu yi hira ,kamar yadda muka
saba kafin inhadu da farida .Amma ganin cewar
babu abinda zai iya janye hankalina daga
tunanin da nakeyi,sai ta kyaleni.*MR:shuraih
99%*"Munce yarmu ta mutu ,kace bata mutu
ba , to ina ruwanka daita!" Natuno da maganar
mahaifin farida ,na tuna lokacin da jikina kamar
ba laka ,natuka motata na bar kofar gidan."Idan
nakara ganinka a kofar gidana ,sai dai kulliya ta
rabamu ...."Shi kansa nasir bai so maganganun
da mahaifinsa ya fada min ba .Ina ganin lokacin
da hawaye suka zubo daga idanunsa,yayin dana
shiga motata zan tafi.Shin yaya za'ayi na
fatattaki saon farida daga zuciyata ?""Shakka-
babu"Naji mauryar mace tafada adaidai lokacin
dana ke tsaye a gaban dogon mudubin ina duba
kwalliyar danayi tun kafin na waiga na san ko
wacece ,domin na kasance da haka ta ke kirana
,kawas yaYata ce fatima ,tana kuma yawan
barkwanci"Habiba " na kirawo sunanta lokacin
dana waiga ita da kawayanta ne su uku
dukkaninsu muka gaggaisa.*Mr:shuraih
99%*"Kinsan mene dalilin daYasa nake kiransa
da shakka babu?"Ta tambayi daya daga cikin
kawayenta."Yawancin duk maganar dazai yi sai
ya fadi shakka babu. Yanzu daza a fasa cikinsa
shakka babu ce taf aciki.idan kuma ka yi musu
yanzu yanzunanmuje asibitin, nabiya a
fedeka"Tafada tan yimini kallon zolaya.Idan
nace zan daka ta habiba , bami lokaci
zatayi,Kuma ni abin dake gabana shine halartar
wasan kwallon kafar daza a gudanar tsakanin
nigeria da kasar ireland.Azagaye na byu na
gasar cin kofin matasa(NIGERIA'99) ko Allah zai
kara hadani da farida a yanzu ma hotonta ne
rike a hannuna ."Kai,kai,kai! Sagwai-sagwai, irn
wannan luntsimemiyar ya sai kace ita tayi kanta
"Habiba tafada lokacin da wuf ta fizge hoton
farida dake hannuna .Tana fizge hoton sai naji
kamar daddaureni tayi.domin babu inda zan iya
motsawa sai ta bani hoton .Kuma babu yadda
za'a yi tabani ba tare data bata min rai
ba.*mr:shuraih 99%*"Sumaza burinsu kawai
ace budurwasu kyakyawace ko kuma yar gidan
masu hannu da shunice, sun manta da fadar
masana sirrin mata cewa mata sirrine ,ba
tukwane bane ballantana akwankwasa agane ta
kwarai ,sai ka ga macen da maza ke yiwa kallon
hadarin kaji ,ita ce kuma zasu samu nutusuwa
da gamsuwa daga gareta "Habiba ke fada yayin
da dukkansu ke kallon hoton.Duk dacewar ita
ma kyakyawace ,na fahimci kishin kyan farida
atattare da maganarta."To ,shin su mazan basa
tunanin cewar ,idan kyakyawa da yar mai kudi
kawai suke hange.suma matan akidatsu zata'iya
komawa ,kyawawan samari da yayan masu kudi
kawai zasu rika soyayya dasu .Su kuma
munanan mazan da yayan talakawan ,sai suyi
yaya?su rataye kawunansu?"Daya daga ciknsu
tafada."Habiba ! Don Allah ia rokonki dAki
taimaka ki bani hoton nan, ba nawa bane
,budurwar wani abokinace suka samu sabani a
tsakaninsu,duk ta mayar masa da hotunansa
,shine ita ma take bukatar ya dawo mata da
nata .Jiya ya dawo mata da nata wannan ne
kadai ya manta,shine ya bani sako na mayar
mata da abinta"*MR:shuraih 99%*Nafada cikin
sanyayyiyar murya , kuma nayi mata karya ne
saboda idan ta san nawane, zata dade tana
jamin rai .tayi far da idanuwanta ,ta dan
rausaya jikinta kana kuma tayi tattausan
murmushi.."Allah sarki habib! Ina ma ace koda
yaushe zaka kasance cikin wannan maganar da
katafi da imanin mata.Domin bakaji inda ka
narkar min da zuciya ta ba"Ba wai dadin yabon
ne banji ba ,domin yamace takan so namiji ya
yabata ,kamar yadda kowanne namiji ke son
mace ta yabe shi.Sai dai buri da doki son kara
haduwa da farida yafi min komai a rayuwata
."Eh wallahi abin tausayi .ko bahijjah"Daya daga
kawayenta tafada ,yayin datake kallonta kusa da
da ita."Don Allah habiba bashi hotonsa"ita ma
dayar tafada.A daidai wannan lokaci fatima ta
shigo falon.*Mr:shuraih 99%*"Fatima shin
wannan budurwan habib ce ,ko kuma da gaske
budurwar abokinsane ?"Habiba ta tambaya
yayin datake nunawa fatima hoton."Bai baki
labarin wacece ke jikin hoton ba,cikin mamaki
habiba ta bukata.A nutse fatima ta labarta musu
komai ,bayan sun zazzauna .Dukkaninsu sai suka
tattara hankalinsu ga hoton farida ,suna masu
cike da matukar mamaki."Habib na taba samun
irin wannan labarin ,amma kin gaskata shi
nayi,habiba tafada.Kanin mahaifiyata Anas,
shine ya sanar dani labarin abokinsa ,da shima
ya hadu da wata yarinya a marhaba cinema.A
lokacin ana ruwan sama ,ita kuma ta fake awani
waje tana ta rawar dari.Ganin haka yasa ya cire
kwat din jikinsa ya bata tasa,Bayan ya je
wajenta sunyi hira ,ta kuma kwatan ta mai
gidansu .Suka rabu akan kashe gari zai je
gidansu,kuma idan yaje ya karbo kwat dinsa
.Karfe taran safiya yamai a kofar gidansu dake
madobi,kamar yadda ta kwatanta mai.
Da
suka bashi tabbacin ta dade da mutuwa ,kin
yarda yayi. Kamar yadda yafaru ga habib,shi ma
sai ya tsinci kwat dinsa akan kabarinta da aka kai
shi don gamsar da shi ce war ta mutu. Da zakayi
kokarin samun Anas ,zai yi matukar taimaka
maka, ka fahimci hakikanin al'amarin. Domin ya
kasance mai yawaita bincike akan abubuwan da
suka shafi taurari da kuma abinda ya shafi
aljanu(Ostrologist) kasan shi,shima ya sanka.
******** *********** ******** A daidai
lokacin da dan'acaban dana ke kai zai gifta
makarantar 'yan mata ta shekara sai na hange
shi daf da makarantar tsaye suna tattaunawa da
wani abokinsa. Na umarci dan-acaban yakaini
inda suke, na biya shi yatafi. "Habib yakira
sunana yayindana mika masa hannu muka gaisa
da shi da abokinsa. Nafada masa cewar dama
wajensa zani.kai tsaye yace mu wuce gidansa a
umguwar yakasai yake da zama. "Habib yanaga
kana ramewa kamar wanda ke hadiyar Allura?
Koduk ayyukane ? Domin na sanku daywan zirga
zirga" Yafada bayan mun zauna a falon gidansa.
*Mr: Shuraih 99%* Yafada lokacin dayake rike
da hannuna ,nayi rungumiyar ajiyar
zuciya,sannan na mika masa hoton farida .
"Tabarakallahu fi Ahsanil khaliqin(hakika
ubangiji shine mafificin tsara halitta kuma ta
tsaru), hakika yarnan ta halittu habib" Yafada
yayin da idanuwansa ke kan hoton. "Kuma
dalilintane rayuwata ke cikin jidali" "Wai kana
nufin tafi karfinka" yabukat. "ranar asbar 3/4/99
ranar da kasar kwastarika tayi wasa da nigeria a
legas,na hadu da ita ta kwatantamin gidansu
akaduna kashegari ranar lahadi 4/4/99 na bita
gidansu,iyayanta suka bani kwararan hujjojin da
suka gamsar dani shakka-babu shekarunta uku
da mutuwa,na kuma tsinci zoben dana bata
akan kabarinta ,kana sau biyar ina sake ganinta
a wurare daban daban" Yayi shiru na wasu
lokuta ,bayan yafita tsakar gida yadaga kansa
yakalli sararin samaniya. "ALLAHU - AKBAR!
ALLAHU - AKBAR!! ALLAHU - AKBAR!!!"

Yafada harsau uku sannan yadawo da hankalinsa
gareni,ya kuma dafa kafadana. "Habeeb! IN
HUWA HAZA SIRIHUN AZIM! Wannan sihirine
babba . Kafin na war ware maka sirrin komai
dalla dalla , ina mai sanar dakai faduwace dai
tazo daidai da zama kuma kayan falke ne sika
tsinke a gindin kaba". "Mekake nufi anas?" "Ina
nufin gobe zamuyi wata tafiya ,tafiyar dazat
budewa rayu warka sabuwan kofa ,kuma itace
tafiyar dazata warkar da lalulurar dake addaban
rayuwarka". "Anas fahimtar dani abinda kake
nufi" "Faridar da iyayenta suka tabbatar maka
da hujjojin mutuwarta,ita ce dai faridar daka
hadu daita a lagos ,itace faridar daka bawa zobe
,haka kuma itace faridar daka hadu da ita a
wurare daban daban" Cikin kaguwa da birkita na
rike hannuwansa . "Shin anas kana nufin faridar
dana hadu da ita mutumce mai rai " "(LA -
SHAKK FI HAZAL AMRI) BABU - SHAKKA ACIKIN
WANNAN AL'AMARIN
K
LITININ 12 ~ 4 ~ 99Jama'a ne makil atattare
wajen kaman duk al'umman kauyen ne suka
hallara a wajen.Duk sunyi da'ira kana kuma sun
tattara hankalinsu ga wani abu dake wakana a
wajen.Kallo daya zakayi musu ka fahimci duk
abin da suke kallo bakaramin jan hankalinsu
yakeyiba .Haka-zalika suna matukar jin dadin
kallon.Daga inda muke ina jiyo tashin sautikan
muryoyin jama'ar wajen gauraye da kuma
sautin kidan ganguna.Na kare fuskata da tafin
hannuna daga hasken ranar dake dimama
kwanyata ,duk da cewar da yamma muka sauka
a garin,har yanzu akwai ragowar zafi atattare da
ranar."Habeeb! Wannan shine garin
bidda,karamar hukuma ce (local government)
dake karkashin jihar nigar.TAFIYA MABUDIN
ILMI, wannan tafiyar,tafiyace da zata mayar
maka da fari ya koma baki, ka kuma yarda da
hakan, bayan ba hakan bane .Duk abinda kagani
ya kuma dada ka da kasa , rubuta domin zakaci
karo da dimbin abubuwan da zasu kara girgiza
tunaninka"Anan yafada lokacin daya rike
hannuna muka nufi wajen taron al'ummar.*mr
: Shuraih 99%*Rike da hannuna ya rinka kutsa
taron .Kuma duk wanda muka ba'a son
ransaba,Sabida wasu tsaki suka rinka yi,yayin da
wasu suka ringa guna-guni da yarensu,wanda ba
fahimtar abin dasuke fada nakeyiba .Wanda
hakan ne yakara tabbatar mini suna kin duk
wani abin da zai janye hankalinsu daga abin da
suke kallo.Sai daya kasance muna ganin wainar
da'ake tayawa atsakiyar taron sannan muka
tsaya.Sakamakon don jama'ar wajen sun zagi
mutum dun kawo musu cikas ga abin da suke
kallo basuyi laifi ba .Wasu mutane ne guda biyu
kowanne rike da takobi a hannunsa ,daga su sai
bantai,gabadaya fuskokinsu sunyi faca-faca da
jini.Gajeran ciki baki mai dankwalelen hanci,ya
kaftawa kuncin dogon mai zungureriyar keya
sara da takobi ahannusa.Kai tsaye takobin ya
ratsA kuncin, fata ce kadai tarike tsokar jini ya
rinka tsattsafowa daga tafkeken raunin.Kiri-kiri
wanda aka sara din ya tallafa tsokar, ya mayar
da ita inda aka sarota. Kamar a shirin film din
al'mara,sai tsokar ta koma ta like tamkar dama
ba a sari wajen ba ,jini kadai ya rage a
wajen.*mr:shuraih 99%*Bayan ya like kuncin
nasa, sai shima ya sari kunnen dogon mai
zungureriyar keyar.Shi ma fata da jijiya ne
kadai suka hana kunnen faduwa kasa.Kamar
yadda dan uwansa yayi shima ya mayar ya kuma
like.Wannan rikitaccen al'amari danake gani
ayanzu shakka babu bashine na farko dana fara
ganin irinsa ba.A shekarar daza a rantsar da
zababben gwamna na farar hula na jihar kano
alhaji kabiru ibrahim gaya,naga wannan wasa
mai suna (SHANCI)Idan ma ka ziyarci balare
cikin ajingi ko falali bangaren sumaila ,ko kuma
fala wajen rano da kibiya,duk maguzawa suna
irin wannan wasan .Bayan su fice daga tsakiyar
taron sai mai zungureruyar keyar ya dawo fes
babu alamar jini.Ya nufi inda wasu gingima
gingiman akwatunan katako suke irin wadanna
zaka rinka gani a wajen masu wasa da miciji.Ya
buda daya daga ciki ya dauko kwalba babu
komai a cikinta,sannan ya kara debo kwayaye
guda uku,kiri -kiri a gabanmu ya ringa saka
kwayayen daya bayan daya har sai da duk
yasaka su cikin kwalbar.Abin mamaki shine ba
wai kwaiba,hatta tsakuwar da bata kai rabin-
rabin kwai ba baza samu damar shiga kalbar
ba.Saboda kankantar karamin bakin kwalban
$Mr:$huraih 99%Ya nunawa mutane tabbas ga
kwayayen cikin kwalbar,ya kara buda akwatin ya
dauko wata zurmukekiyar kayar beguwa,ita ma
yadaga yanuna mana sannan ya rinka zurata
cikin hancinsa sai da ta kule dif.Sannan kuma ya
zarota.Bayan wannan sai yadauko jarida ya
warwareta muna kallo kana ya kanannade
kamar yadda akeyin gurguru."BE"yafada yana
yafito wani yaro,duk da ban taba jin kalmar ba ,
nafahimci(zo)yake nufi.Ya bawa yaron ruwa
yakuma umarceshi daya dura ruwa cikin
jaridar.duk dacewar ruwan daidai da dis ba
digaba .Bayan mutane sun dauka wannan ne
abin mamakin,daya warware jaridar babu
komai cikinta,Da kuma ya kara nada jaridar ,sai
ya rinka zubo da ruwan .Ya yagi takardar ya sa
abakinsa,sai ya ringa fitar da sababbin Allurai da
rezozi daga bakinsa .Duk irin wannan abubuwa
yan bori da masu wasa da majizai sukan yi ire
irensu(ru'ido).Daga karshe bayan yayi abubuwan
al'ajabi da dama .sai kuma tsam ! Aka nemeshi
sama da kasa aka rasa .Daga shi har akwatunan
nsa zuwa masu kade-kaden sun bace
Ganin jam'a sun fara kama gabansu ,anas baice
dani uffan ba ,yawuce gaba ina biye dashi a
baya ,muka rinka shiga cikin unguwar ,har sai da
muka je wani gida ginin gargajiya,sannan muka
tsaya . Bamu dade da tsayawa ba wata budurwa,
dauke da tulu tazo zata shiga gidan. Kallo daya
nayi mata,naga kamannin mai zungureriyar
keyar nan tattare da ita ,kana na fahimci nan ne
gidansu. "Okun".tafadawa anas ,shima yafada
mata wasu abubuwa da yaren ,ni dai kawai okun
na rike ,wanda sai daga baya na fahimci(sannu
da zuwa take nufi) ta kura min ido yayin da suke
magana da anas,bayan ta shiga tafadawa masa
wani cikin yaren,sai takara kura min ido,kana ta
koma gida . Bata dade da komawa ba sai mai
zungureriyar keyar yafito. Bakamar dazu ba ya
sauya kayan jikinsa,ban kuma yi mamakin
ganinsa a nan ba , don ya bace a gabana . Duk
wanda ke zaune a kasar Hausa,yana da labarin
layar zana. Mr:shuraih 99% "Anas! Yafada
lokacin suka gaisa Kana nima yamiko hannu
muka gaisa . Bayan ya kawo mana tabarma mun
zauna ,yakuma kara kawo mana gasassun zabi
biyu da kindirmo. "Dandash ! Wannan
abokinane sunansa habib ,habib abokinane
sunansa dandash, yayi matukar taimaka min
lokacinda nake zaune a nan" anas yafada.
"Dandash! Wannan tafiyar don kai mkayita
kuma abin da ketafe damu shine: Nan anas ya
labarta masa rikitaccen al'amarin daya faru
gareni cikin nutsuwa. Dandash yayi shiru kamar
mai yin tunani ,sannan yayi dan murmushi ,ya
matso da bakinsa kusa da fuskata. "(Kemina
farida tsuwna a ciga ganwa tsu wastu ma an)KAI
MA ZAKA MUTU KUMA ACIGABA DA GANINKA
A WATA DUNIYAR,KAMAR YADDA YAFARU
AKAN FARIDA. (Sarih yan yin gaina).WANNAN
YANA DAGA CIKIN SIRRINMU". **********
*********** ******** SIRRINSU shi ne abin
da yau za'anuna maka" Anas yafada bayan
dandash ya shiga gida . Har yanzu kwalkwalwata
arude take , zanmutu kuma acigaba da ganina ?
Shekaru uku da suka shude, farida ta mutu ta
kuma dawo. Nima yanzu hakan na neman
kasancewa a gareni. A daidai wannan lokaci
dandash ya leko ,yayi mana umarnin mushiga
daga cikin gidan. Har muka shiga muka zauna a
wani kebabben muhalli a razane nake . Na
mutu a kuma cigaba da ganina ? Bawai gani na
da za arikayi bayan na mutune ke girgizani ba,
irin mutuwar dazanyi din. "Habib ! Kafin na cika
maka alkawarin dana yi maka,bari na fara nuna
maka wasu kwararrun hujjoji, don zama
matashiya ga yunkurin daidaita tunaninka dana
ke shirin yi" Dandash yafada yayin daya kwanto
wani guru dake daure akugunsa . Mr:Shuraih
99% "Rike wannan" yamiko min gurun. "Mene
ne wannan " yabukata lokacin dana ke rike da
gurun. "Guru ne"na amsa masa. "Yar dashi
akasa" ya umarceni. Cikin halin kidimewa na
tashi zan cika bujena da iska ,yayin dana iyar da
gurun,ya rikide ya koma maciji yana tafiya a
kasa. "Kada ka tsorata, kamashi!"Dandash
yakara umartata . Ba don na amince anas bazai
kawo ni inda za a cuceniba ,da ba zan kama ba.
Ina kamawa atsorace sai ga gurun rike a
hannuna ,ya karba ya kara daurawa a kugunsa.
"Tabani"ya umarceni . "Wakake tabawa?"
Yatambayeni lokacinda hannuna ketaba jikinsa.
"Kainake tabawa "na amsa masa. Kamar walkiya
sai nemarsa nayi na rasa. "Kana
ganina ?"Muryarsa daga wani waje ta bayyana .
"Bana ganinka " "Kalli saman bishiyar dake kusa
da kai"muryarsa ta kara fitowa. Ina kallon
saman bishiyar sai na ganshi zaune akan reshe.
Kamar dai walkiya sai yakara bacewa ,ban
ankaraba sai ji nayi yana girgizani, yayin dana
tattara hankalina kan bishiyar. Yana zaune inda
yake dazu. Agabanmu yahada kiraruwa ya kunna
Wuta,ya dauki wani dan karamin sanda ya
nannadeshi da tsumma ya jika shi kananzir.
Yana sa shi a wutar takama jikin tsumman da ci.
Mr Shuraih 99% "Cire rigarka"ya umarceni.
Banyi musa ba na cire. "Kai sharifine"? Ya
tambayeni. "Ni ba sharifi bane " Kafin narufe
bakina yafara goggogamin wutar ajikina .
Shakka babu al'amarin da mamaki,kiri-kiri ga
wutar tana taba fatata,amma babu wani alaman
tsafi ballantana na kone. Bayan yakashe wutar
na mayar darigana sai ya zauna kusa dani.
"Kodon gaba, idan kaga mutum ya kirawo
dabbobi suna hira,ko kaga mutum ya shiga tulu,
ko kaga mutum ya shiga ta bakin jaka ya fito ta
farjinta,ko kaga mutum ya mayar da cikinsa
gefensa ko kuma bayansa ko kaga mutum
yadaki bishiya mai rai a gabanka ta bushe
,kokaga mutum yayiwa turmi ko dutse kaho,su
kuma tsotso jini, kokaga mutum yana zuko
ruwa daga hannunsa yana fesarwa,har ruwan ya
taru dayawa,ka kuma rinka ganin kifaye suna
ninkaya acikin ruwan. Ko kuma kaga mutum ya
ajiye kwano babu komi aciki,take agabanka
abinci yazo,ko anuna maka akwati babu komai
aciki take agabanka tacika da kayayyaki iri daban
daban, Ko kaga kan mutum sun zama barkatai ,
koirn wanda nayi maka yanzu a takaice muna
kiransa sihirin damfara,akasar hausa kuwa rufa
ido."Alokacin da mutumin da al'amuransa ya
shafemu ke aiwatar da wani abu,ko yake fada
ko kuma yake tunawa ,alokacin muke sani.
Habib! Koda wasa kada kayi sha'awar wannan
shirmee da mukeyi. Duk wanda keyin shirka
,kafadawa kowa baya cikin da kwancoyar
hankali, Ba ya kuma samun sanyin zuciya. Zaka
sameshi mara imani da tausayi ,haka kuma gasu
da cutar rayuwar al'umma domin duk wani
sihiri idan kaji yadda ake hada shi,ka san aiki ne
na shaidanu . Kuma babu wani amfanarwa
tattare da
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment