Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

(two pocket)
Yaci zanzaro sai kace wani tsohon hedimaster,
" mj ya akai ne"
"Dai dai wallhi kasan meye?"
Ya tambayeni
"A'a"
"To Dangado fa yana ta nemanka don yanzu na hadu da shi, malam ranshi ya baci,ya tambayeni kai
nace mai ban ganka ba,"
Nayi murmushi kafin nace
"Dan Allah kyaleshi"
"Wai me ya hadaku da shine" mujahid ya tambayeni
Ban boyemai komai ba na fede mai biri har wutsiya dan gane da abun daya faru da wayan dangado,
Mujahid ya fashe da dariya bayan daya gama sauraran labarin,
,
Dariyarsa bata bani haushi ba don mun ruga da mun saba haka da shi
"Kai amma 99% yarinyar nan ta raina maka hankali wallahi"
Na dubeshi cikin rashin fahimtar yanda zancen nashi ya nufa
"To wani rainin hankali ne taimun "
Na tambayeshi
"Ta boye waya tace maka an sata kai kuma ka yarda, wallahi ni banga ranan da zaka wayeba 99%,
ga ka dai kaman wayayye"
Kirjina yaba dumm sakamakon jin abunda mujahid ya fada
Na dubeshi nace "to kai ya akai kasan cewa ta boyene"
Ya sake fashewa da dariya akaro na biyu
Wannan karon kam ya bani haushi, naja tsaki nace "kaga malam tambayrka nake fa "
"Yo kai 99% sai kace kwakwalwanka bayaja, haba, tayaya za'a ce barayi sun shiga gidan Alhaji
Kawu sunyi sata anma mutanen angwa basu ji labari ba har yanzu, ai kaima kasan inda da gaskene
har Gidan rediyon N B S sai sun san da labarinnan "
Na jinjina maganarsa kafin nace "tabbas maganarka abar dubawa ce, amma yanzu yaya zamuyi mu
amshe wayar din a wajenta"
Yayi murmushi yace
"Ai maganin biri karen maguzawa,allah na tuba mu yanzu har wata tayi mana wasa da hankali, ka
ganni nan Na mijine ni, nasan mata sosai duk wani takunsu a kaina yake, dun haka zo kaji"
Na matso kusa da shi ya kitsamin
********************
Kofan tangamemen gidan ne ya bude
A yayinda kyakkyawar budurwan ta fito daga ciki ba wata bace face safiyya tana sanye da rigan
kanti da wando ta yafa wani dan bingilallen gale iya kirjinta,
Turus tayi tana kallonmu cikin razana
Yayinda bakinta yafara rawa "shuri-shur-shuraihu me a faru"
Nai murmushin mugunta kafin nace
Bakinki ne safiyya
.
Mu hadu a part na gaba

,
Toh wasu baki kenan

MAZAN KO MATAN
Rubutun Shuraih Usman
@shuraih 99%
Part 5
KARSHE
Cikin matukar razana da daburcewa ta ce
"Bakina kaman yaya?"
Tayi maganar tana mai kare masu kallo sama da kasa
.
Mu biyarne tsaye a gabanta, yayinda ni da mujahid muke gaba gaba
,
Na lura da yadda safiyya ta tsorata sosai,
Bisa ganin mutanen ukun dake bayanmu
,
Kattine majiya karfi, kowannensu ya hakimce hannuwansa, sai muzurai suke tamkar saci babu,
Ransu a bace tamkar wayanda aka aiko masu da sakon mutuwa,
,
Kallo daya zakai masu ka gane ko su waye, sakamakon kayan dake jikinsu,
Na lura tunda muka iso angwan jama'a ke binmu da ido ,
Suna sanyene da dogon wandon uniform nasu da kuma riga mai gajeran hannu, a kafadun rigan
akwai wasu kore koren layuka,
Sun saka hullana kafiya naci, wacce take dauke da tambarinsu na bindigu guda biyu, an rubutta
VIGILANTEE gROuP OF NIGERIA a kasan tambarin
,
Nai murmushi sakamakon ganin yadda cikin kankanin lokaci har safiyya ta razana da ganinsu,
Na fara magana bayan dana sauke ajiyan zuciya
"Wato ainahin safiyya kinsan hausawa sukace ranar wanka ba a boyen cibi, "
Ta kankance kai cikin rashin gane inda maganata ta dosa
,
Koda mujahid yaga na kamo wata hanyar wacce ba haka mu ka tsara ba sai yai maza ya amshe
maganar
"Malam ba zakai mata bayani ba ko, so kake yanzu nasa su GAJIMARE sui ta labtarka"
,
"Safiyya dama wayan dana baki jiya ba wayata bace, wayan abokina ne, na dai shirga maki karyane
kawai, don ki kulani, Tun jiyan yake nemana na bashi wayansa, sai dazu muka hadu, shine dana
fada masa wayan ta bace yanuna shi sam bai san wannan zance ba, shi isa ya hadani da vigilantee ni
kuma ayanzu gaskiya bani da kudin da zan iya biyansa, shi yasa nace da su muzo wajenki tunda ke
ce ki ka salwantar da wayar, "
Nayi shiru ina mai saddar da kaina kas
,
"Yo kai shuraih haka mukai dake "
Cikin mamaki na dago kaina mukai ido hudu da ita "nace haka mukai dakai" ta sake tambayata
,
Nai kasake nama rasa amsan da zan bata
Ta dubi mujahid tace mai "malam kaine mai wayar"
"Eh nine" ya bata amsa yana wani shan kunu
"Dun Allah kaji mani maganar nan, jiya fa yazo wajena da waya a hannunsa na karbe wayar ina
danne danne, saboda da doki ya tafi ya manta da wayan a wajena,
Da sanyin safiya sai gashi ya zo wajena in bashi waya, na lallaba na bashi hakuri nace mai ya dawo
an jima ya karba saboda akwai wakokin dana ke son turawa wayata,! Toh kaji yadda mukai amma
yanzu kuma ya kwaso min ku, toh mai zam maku ni?"

.
Ta karashe maganar tana ware hannayenta
Tsaban mamaki ma sakin baki nayi gala lala ina kallonta sakamakon jin abunda ta fada, lallaima
yarinyarnan ta cika yar rainin hankali na fadi haka a zuciyata
.
Mujahid ya jinjina kai yace "ince dai wayar din tana nan"
"Eh tana ma cahji yanzu" ta bashi amsa
Mujahdi ya dubeni sannan ya dubeta yace
"Dauko min wayar din toh"
Ta juya ta shige cikin gidan
,
Shigewanta gida keda wuya mujahid ya fashe da dariya ni kaina me zanyi inba dariyan ba,
Sai da mukayi mai isanmu sannan nce"kai mj amma ka kawo shawarafa, yanzu badon kaiba da
shikenan, yarinyarnan ta cimin waya kenan"
,
"Hmm ai na fadamaka mata saide ka barsu kawai, don sun wuce tunaninka yanzu duba kaga yadda
ta kare kanta, wai ita batace an sata ba"
"Barta kawai bari ta kawo wayan yau MAZAN KO MATAN"
Nai kwafa ,
Karar Kiciniyar bude kofa da mukaji shi ya ankarardamu tana zuwa hakan yasa muka tsuke
bakinmu mukai shiru,
Mujahid ya bata ransa in ka gansa kamar ba shi bane mintukan da suka wuce ya runga dariya har da
buga kafa ba
,
Ni kuwa dama fuskarnan tawa tafi kamaa da na tausayi,
Safiyya ta fito wayan na rike a hannunta, na dama
Ta mika ma wa mujahid wayan, ya karba yadan dudduba sannan ya miko mani,
Cikin zumudi na karba a nan take yanayina ya canza, na dudduba wayan gaba da baya sama da kasa
gefe da gefe naga babu abunda aka cire a ciki, daga nan sai na kunna wayar na shiga camera, na
ware murya nace ma mujahid selfie na daga wayar sama yan bangan bayana suka washe baki,
mujahid kuma yai murmushi, nima dai murmushin nayi kafin na capta mana selfie din,,
.
Cikin mamaki baki bude safiyya take kallonmu yayinda muke antaya selfie,
Na dubeta bayan dana zura wayar din cikin aljihuna, fuskata na dauke da murmushi "malama
safiyya, wai da wani suna ya kamata na kirakine ,MAI WAYO,YAR RAININ HANKALI ko kuma
BARAUNIYA"
Ta dubeni cikin tantama "kaman yaya ban gane nufin kaba"
Na dubi mujahid nace "mj kaji wai bata gane ba dun Allah taimaka ka ganar da ita"
,
Mujahid yai murmushi yace "malama BARAUNIYA, toh ai wayansa ne, kawai dai plan muka hada
maki, YAR RAININ HANKALI, wai ita MAI WAYO har da......"
Tun kafin mujahid ya karisa maganarsa ta juya da gudu ta shige gida, ta banko kofan gidan
.
Mun dan jima a tsaye a kofan gidan muna sharara dariya, kafin muyi tafiyanmu
Bayan mun sallami yan bangan da dari biyar
,
Tafiya nai na samu dangado na bashi wayansa a inda ya hauni da masifa ta inda yake sgiga bata nan
yake fita ba,
,
......

Yammaci ne mai dauke da ni'ima , domin tarin ababen kayatuwar da suka lullube yammacin, garin
ya danyi duhu alamun hadari a yayin da iska mara karfi mai matukar dadi ke yawo a cikin
yammacin,
,
Mutane da dama sun dan tsorata da wannan hadarin har ta kai sun fara gudu domin isa masaukinsu,
Cikinsu har dani dana fito gangaren tudu wajen sahibata sadiya, inda muka sha hira sosai tamkar
kar mu rabu da juna
,
Sa'I sa'I nakan kalli hannuna mai dauke da wani koren zobe nayi murmushi,
Bawai hannunan bane ke sanya ni murmushi a'a Zoben dake sakale a dan yatsana shike sanyani
nishadi har murmushin yake fita batare dana sani ba, zoben da masoyiyata kuma abar kaunata
sadiya ta sanya mani yau,
A hakan na runga murmushi har na iso Gida,
Ina Tunanin yadda na hadu da sadiya,
Da farkon haduwana da ita,
Koda na tuna sanadiyar haduwata da ita sai na tsinci kaina ina mai fashewa da dariya,
"Ba'asamu safiyya yar karya ba an samu, sadiya sanadiyar karya?" Na furta a fili
.
.
Alhamdulillah
Anan na kawo karshen wannan gajeran labarin na wa,
Dafatan ya nishadantar
,
MAZAN KO MATAN
Shuraih Usman
********************
,
Zaku jini a cikin tsohon littafina mai taken
A RANAR SALLAH
Nan bada jimawa ba
,
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment