Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ayarin tawagar sun doso inda suka boye mutanen biyu
sarakan barayi suka dubi juna lokaci guda kuma suka hangi inda makwaro yake make daga inda
suke zaune suna iya hango rungumemen kan makwaro wanda ke zaune yayi dani baya ko motsi
kamar gunki.
Allah yasa kada lalataccen can ya harbi yaran nan biyu...zangeru yace batareda ya dubi mai masaba
ba domin tuni har sun fara jiyo hayaniyar mutanen suna hira.
Ai kuwa in ba wata sa'a ba da nisan kwana sai ya kashe su kaga dai sana'ar mu daya dashi amma
wallahi ni kaina tsoron rashin imaninsa nakeyi.
Zangeru yaji wani gumi yafarayi masa sartu a doron baya harga Allah bashi son abinda zaisa a
kashe kyawawan 'ya'yan sarkin nan domin shi dukiyar ce kawai agabansa ba kisan kai ba.
To sai fa garemu gasu nan sun matso mai masaba yace da zangeru sannan cikin zafin nama na ban
mamaki sai ya gyara danin kibiyar dake jikin bakansa sannan ya cilla harbi cikin ayarin ta tsakanin
duwatsun ba'a dade ba sukaji an kwalla kara mai tsanani sannan sai sautin fadowar wani abu mai
sauti irin na buhun sumunti.
Na sami daya kafiri. Mai masaba yace cikin karaji.
Zangeru jiki na rawa ya shafi gefen tsafaffen bantensa inda ya kulla duwatsun nan da balbale ta
bashi ya tabbata yana nan sannan sai shima ya cilla harbi cikin ayarin nan da nan hayaniya ta barke
da hargowa da ife ife cikin razana da kaduwa daga cikin duhu zangeru ya hangi makwaro ya fara
cilla harbi cikinsu har sau uku duk harbin dayayi sai ya jefa mutum daya kasa.
Ba'a dade ba sai wajen yayi tsit bakajin komai sai gurnani da motsin dawakai mai masaba ya dubi
zangeru jikinsa na rawa yana haki yace Munci Nasara... Lalataccen duk ya kwantar dasu.
Zangeru bai ko dube shi ba jikinsa sai kyarma yakeyi abinda ke damun zuciyarsa shine kyawawan
yaran ya'yan sarki ko shakka bayayi makwaro duk ya harbe su yakuwa tabbatar kibiyar makwaro
tsafaffiya ce bata sukar mutum ya rayu ga mamakin zangeru sai yaji a karo na farko ya tsani kansa

ya kuma tsani makwaro don me? Don me awane dalili zai kashe wannan kyakkyawar budurwa ita
da dan uwanta bayan shi kuma nasa dan Amadi yana can gida lafiya kalau babu ko kwarzane
ajikinsa?
Wayyo Allah na shiga uku na lalace Hassan ihun hussaina ya ratsa cikin dajin amsa kuwwar ta
watsu cikin duwatsun sarakan barayin biyu suka dubi juna sannan lokaci guda suka dubi inda
makwaro yake kwatsam sai sukaga ya mike tsaye ya zaro kibiya daga cikin kwari ya danata sannan
sai yayi awon cikin duhun inda sukaji ihun farko.
Zangeru zuciyarsa ta harba domin yasan abinda makwaro yake nufin yi cikin zafin nama na mamaki
sai zangeru ya dana kibiyar ya saita wuyan makwaro ya harba kamar wasa sai kibiyar ta sami inda
aka yi nufinta makwaro ya kwalla ihu sannan sai yafi agurin.
Mai masaba ya dubi zangeru cikin kaduwa yace Haba zangeru kanka daya kuwa meyasa zaka harbe
shi?
Zangeru ya harari mai masaba acikin duhun yace a fusace meyasa zai kasheta bayan kuma da
sauran kwananta a duniya? Ko ya dauka shi kadai yake da tsafin harbi? Yau kunama ne shi nakawo
karshen karyar banza.
Mai masaba cikin kaduwa ya mike tsaye a fusace bazatayi ba zangeru dole ne mu kashe yarinyar
nan tunda sauran sun mutu dole ne itama ta mutu idan kai bazaka iya taba ta ba bari ni in tafi kasa
na karasa ta.
Yana gama fadin haka sai yafara gangarawa kasan dutsen ya nufi inda suka jiyu ihun budurwar
adaidai wannan lokacin ne zangeru yaji kamar wani abu na sukansa a kugu cikin sauri ya yakai
hannu gurin sai yaji ya taba tsinken kibiya jikinsa na rawa ya zare kibiyar daga kugunsa ya dagata
sama cikin duhun daren ko shakka bayayi daga cikin kibiyoyin da baraden sarki suka sami damar
harbowa ce ta huda bantensa ta kuma dan soke shi kadan a kudu babu mamaki tashin hankali ne ya
hanashi jin sukar kibiyar tun farko.
Zangeru yayi kamar ya jefa da kibiyar daya zare daga kugunsa can kuma sai ya fasa lokaci guda
kuma yaji wani zazzafan gumi ya fara wanke masa fuska yasha jin labarin cewa duk kibiyoyin dake
kwarin baraden sarki a shurbune suke da masifaffen dafi wanda duk wanda yasoka bazai rayu ba.
Daga inda yake tsaye yana iya hangen faffadan bayan mai masaba wanda ke gangarowa ahankali ta
tsakanin duwatsu
Kyakkyawar budurwar yarinya ce karama bai kamata ta mutu tun yanzu ba ni kuwa tawa ta kare
kamata yayi mu wuce lahira nida babban abokina. Zangeru na gama fadin haka sai ya shafi kugunsa
inda kibiyar ta same shi baiyi mamakin jin gurin tuni har ya fara kumbura ba yaji wani zafi ya soki
kugun kamar ana hura masa wuta yanzu kam ya tabba dafi ne ajikin kibiyar.
Zangeru ya jinjina kibiya ahannunsa sannan ya dana ta ya daga bakan sama ya saita faffadan bayan
babban abokinsa Mai Masaba sannan sannu ahankali batareda wata nadama ba domin yasan ceton
rai yakeyi sai ya saki Kibiyar CUL.
** ** ** ****** ****** ***** *****
Lokacin da zangeru ya dawo bakin katuwar koramar ta danmusa tuni har ya gari yagama wayewa
yayi sa'a bai hadu da kowa ba sai wata tsohuwa mai sammakon tsiya dake bayan gari a musissika
dake daf da koramar tana shikar gero.
Sannu da zuwa bawan Allah tsohuwar tace da zangeru sa'ar data ganshi tafe bisa katon doki dauke
da akwatin karfe yana tafe yana layi kamar zai fado daga kan dokin sakamakon dafin kibiyar dake
daukarsa.
Baiko dubi tsohuwar ba ya wuce kai tsaye zuwa can cikin koramar jikinsa na ta rawar dari
sakamakon mummunan zazzabin dake addabarsa lokaci guda kuma zuciyarsa na ta tunanin halinda
hussaina take ciki.
Lokacin da zangeru ya tabbata ya harbe babban abokin satarsa mai masaba sai ya gangaro daga kan
dutsen yana layi yashigo har inda tawagar baraden sarkin suke duk a kwankwance kuma a marmace
bayan ya tabbatar babu mai wani sauran numfashi sai ya fara laluben inda Hussaina take ya dade
yana lalube kafin ya ganota karkashin wani lankwasashshen dutse mai siffar bil'adama tana kwance
a sume zangeru ya jujjuya ta na dan lokaci ya tabbatar suma tayi ba mutuwa ba sannan saiya data ta
yayi abinda rabonsa dayayi tun yana karami -- ADDU'A.

Allah sarki kyakkyawa Allah yasa fatake su tsince ki yana gama fadin haka saiya nufi inda dokin
akwatin dukiyar yake ya yunkura ya haye bisa dokin ya juya ya kalli gawarwakin kallon karshe
sannan sai ya karkata linzamin dokin yabi takan gawar babban abokinsa Marigayi Mai Masaba
yakoma da baya.
Don haka ayanzu da zangeru yazo bakin korama sai ya hangi wata doguwar bishiyar giginya dake
gangare ba'a nan yaso ya tsaya ba to amma dayake jikinsa yagama yin rauni sai ya sauka agurin
baiyi mamakin jin kafafunsa sun kasa daukar nauyinsa ba ahaka yafadi a gurin zaman yan bori bai
damu ba domin tuni ya shirya abinda zai acikin zuciyarsa jikinsa na rawa ya lalubi inda ya kulle
farin dutsen nan acikin bantensa ya kunto dutsen sannan saiya sa dutsen tsakanin tafin hannunsa
biyu ya murza.
GANI ZANGERU ME KAKE SO MASOYINA?
Farar balbelar tace sa'ar data bayyana agabansa
zangeru ya dubi balbelar yana haki bakinsa na rawa yace dan lokacin daya rage min aduniya kadan
ne shiyasa na neme ki domin kiyimin taimakon karshe kuma muyi sallama kafin na mutu
''Me kake so?
Zangeru ya dubeta yace kai tsaye so nake ki sa yan uwanki su tona rami yanzun nan su binne min
akwatin dake kan dokin nan inason kuma ki kawo min warka(takarda) da alkalami.
''An gama balbela tace sannan ta bace ba'a jima ba saita sake bayyana ita da wani dankareren aljani
dauke da tawada da waraka.
'Binne akwarin nan agindin bishiyar giginyar can balbelar ta umarce shi.
Kafin kiftawa da Bismilla bakin Aljanin ya daki saman akwatin da karfi akwatin ya nutse acikin
kasa
Ga tawada da takardar balbelar tace da zangeru
hannunsa na rawa yayi rubutu mai tsayi ajikin takardar da AJAMI sannan ya yiwa takardar nadin
laya ya mikawa balbelar yace ga wannan ki kaiwa matata kice da ita ni na mutu kuma wannan
takardar tabaiwa dana amadi sakone aciki shine kadai gadon da zan iya bar masa aduniya tari ya
shaqe zangeru nan da nan yafara bakin amai na dafi ba a dade ba sai idanunsa suka kakkafe akaro
na farko arayuwarsa sai zangeru yaji nadama tazo masa to amma duk da haka saiyaji gamsuwa
tazowa zuciyarsa tun da dai wai atunaninsa yayi abin kirki akaro na farko ya ceci rayuwar Hussaina
da wannan tunanin ya MACE.
Balbelar ta dubi gawar zangeru saita dubi katon bakin aljanin tace zauna anan kayita gadin wannan
akwatin daga yanzu har zuwa abinda hali yayi
''An gama ranki ya dade bakin Aljanin ya daki kasa wata katuwar kujera ta hudo kasa ta fito aljanin
ya hau kai ya harde sannan yace
YI TAFIYARKI RANKI YA DADE KARKIJI KOMAI NI INA NAN KAFIN ALLAH YA
DAUKI RAINA.
Balbelar tayi fir da nannadaddiyar takardar abakinta.
** ** ****** ****** **** ***** ****
Har zuwa lokacin da Amadi yafara hango dogayen duwatsun hawaye bai daina kwarara akan
fuskarsa ba abinda yasashi kuku wiwi shine mutuwar mahaifansa guda biyu duk lokaci Guda.
Amadi ba zai taba mantawa da safiyar jiya ba dawowarsa gida kenan sai ya tarar da mahaifiyarsa
kwance tana murkususu da tsohon ciki taci uban kuka idanunta sunyi jawu cikin kaduwa taga
Amadi yayi tsaye akanta sai yaga kawai ta miko masa wata nannadaddiyar takarda tace ga Wannan
ka riketa da kyau Amadi ni ma mutuwa zanyi Mahaifinka zanbi.
Amadi ya dubeta cikin Kaduwa da kuka
Amadi babanka ya mutu...
Awajen sata wannan ma inajin.....Amadi ya dubeta cikin kaduwa da kuka.
Amadi babanka ya mutu....awajen sata wannan ma inajin laya ce ya baiwa Aljanar balbelar nan tasa
yace ta baka ina jin maganin tsautsayi ce da yake amfani da ita yau rana ta baci ka rike layar da
kyau Amadi inayi maka fatan alheri Allah rabaka da sana'a irinta mahaifinka tana gama fadin haka
sai itama tace ga garinku nan.
.

Wannan shiyasa amadi kuka sa'ar da ya nufo duwatsun ya shafi layar dake makale awuyansa sannan
ya kara fashewa da kuka wannan laya ita kadaice abinda zai ke gani yana tuna iyayensa hakan
shiyasa shi tun a safiyar ranar bayan an binne mahaifan nasa sai amadi ya baiwa wani baduku ya
dinke masa ita da fata ribi uku. A yau da sassafe ya kamo hanya domin bashida sauran wata sha'awa
ta kara zama agarin tunda dai bashida kowa... Sai ko hussaina yace acikin zuciyarsa.
Amadi ya dada sauri yana tafe yana share hawaye lokaci guda kuma yana tunanin cewa lokacin da
sukayi zasu hadu da masoyiyarsa hussaina agarin sarki lurwanu ya karato.
Sa'ar daya shiga tsakanin duwatsun ne to yayi gamo da wani babban tashin hankali Amadi yayi
turus ya tsaya cak a tsakanin duwatsun a tunaninsa mafarki yakeyi to amma wani katon kuda daya
fada cikin kunnensa yana guda shiya tabbatar masa cewa idanunsa biyu.
A zaune tayi kuka ta gaji ta hada kai da gwiwa ta sallamawa mutuwa kanta....
Hussaina ce tasa gawawwakin baraden mahaifinta da dan uwanta agaba tana cin uban kuka.
.
Hu...hussaina ya kira sunanta a razane hussaina ta mike da kyar jikinta na rawa sannan ta nufo inda
yake ta rumgume shi tana kuka
Amadi...Amadi don Allah ka mayar dani gida kada ka bari wani abu ya sameni.
Amadi ya banbareta daga kirjinsa sannan ya dubeta yakuma dubi gawarwakin dake kwance awurin
yace bakinsa na rawa kada kiji tsoron komai masoyiyata in Alllah yaso daga yau kinyi sallama da
duk wani tsautsayi ya dan dada janye jikinsa daga inda take Hussaina...me...ya faru haka?
Wallahi yanfashi ne suka taremu wayewar garin yau da kusan asuba kaga har sun kashe hassan dina
ta sake fashewa da kuka sun dade tsawon lokaci awurin Amadi yana kokarin lallashinta bayan wani
lokaci hussaina ta dawo cikin hayyacinta kadan.
Amadi ya dubeta yanzu ina kike son nakai ki?
Cikin sauri tace mayar dani gida wajen mahaifina
Amadi ya dubi kyakkyawar fuskarta cikin tausayi sannan sai ya cire layar dake wuyansa ya mika
mata yace Hussaina ga wannan layar ki riketa da kyau maganin tsautsayi ce mahaifina ne yabar min
ita gado shima jiya Allah yayi masa rasuwa inason ki riketa da kyau koda Allah bai kaddara aurena
dake ba ina son idan kin haifi 'ya ko 'da kema ki basu layar domin na fada miki maganin tsautsayice
sosai don da ita mahaifina yayi amfani iya rayuwarsa.
.
Hussaina ta dubi amadi a razane don jin abinda yace lokaci guda kuma ta dubi layar da yake mika
mata tace Meyasa kake irin wadannan maganganun?
Waya ce maka bazaka aure ni ba?
Amadi ya dubeta cikin damuwa ke kinsan abin ne da wuya Hussaina.....
Ta katse shi amadi shiyasa nace ka mayar dani gida domin idan munje zan ce da mahaifina kaine ka
ceci rayuwata a hannun barayin....nasan tabbas idan yaji haka na nuna ina kaunar ka babu abinda zai
hana ya aura min Kai.
.
Tabbas maganar data fada tayiwa Amadi ma'ana to amma duk da haka sai ya dada mika mata layar
yace to gashi dai ki rike layar awurinki idan Allah yasa kin aureni din idan mun sami 'da basai mu
saka masa ba.
Me yasa to kai bazaka rike layar awurinka ba? Saboda maganin tsautsayi ce nafi son naganta
agurinki bari nasa miki ita
kafin ta rufe baki Amadi ya rataya mata layar a wuya sannan sai ya dubeta yace ZO MU TAFI.
Hussaina ta juya hawaye na zuba akan fuskarta tayiwa gawar dan uwanta ganin karshe sannan saita
juya gami da dafe layar dake makale a wuyanta tabi shi abaya
koda suka fara tafiya sai sukaji haniniyar doki abayansu hussaina ce ta fara juyawa cikin mamaki
dokin yayi haniniya sa'ar daya fito daga cikin duwatsun sannan ya nufo inda suke
Lahh Allah sarki ashe kaima Allah bai kari kwananka ba?
Amadi ya juya ya dubeta yace wanene?
Hussaina ta nuna masa shi da hannunta dokina ne danazo akansa.

Amadi yaji wani dadi ya lullube shi a kawo na farko domin babu abinda ya tsana irin yaga hussaina
ta taka a kasa har zuwa garinsu mai nisan tsiya daga gurin.
Nagodewa Allah daya kawo miki abin Hawa
Kaifa bazaka hau ba?
Amadi ya girgiza kai yace kada ki damu dani kedai dake layar dake wuyanki kada ki jefar da ita
idan kinzo hawa dokin me yiwuwa kice na cika mita akan layar nan ni kuwa abinda nake ta
nannago akanta shine nasan maganin tsautsayi ce.
.
** ** **
KASHI NA BIYU
2004
.
BIYAR.
Ga doki har doki amma kofaton na sakaina yar budurwar tace cikin zuciyarta a sanyaye sa'ar data
dubi kanta ajikin agogon madubin dake fuskantar ta.
Bawani abu ne yasa ta fadi haka ba sai hadin bautar ban haushin data gani ajikin madubin
.
Gashi dai budurwar kyakkyawa ce doguwa mai tsukakkiyar mara fatar jikinta a mulmule tana sheki
kamar kwalba arana ga dara daran idanu farare sol firgita samari ahaka nan dan iskan can da
akullum ya gallabeta a makaranta yasha cewa da ita.
Ke bebe wallahi ina bala'in son skil din nan taki gata dai ita ba fara ba ita ba baka ba kuma baja ba...
See your eyes kyawawa juyayyu masu firgita lakcarori yayin daukar darasi ga kuma fatar bakinta
looks very soft tausasa shi yasa kullum nake kaunar ki wallahi idan ace ni malamin jami'a ne da har
kigama bake ba faduwa
to amma duk da irin wannan kyawun nata sa'ar data dubi kanta jikin madubin saitaji duk ranta
yagama baci badon komai ba kuwa sai don yaroki yarokin tsummokaran dake jikin ta bana fita
kunya a farfajiyar jami'a bane ga dai atamfar dake jikinta ba wata mai tsada bace kamar buhun
busassun zogale ta kode ta jeme kamar labulen laburare haka nan dan siririn kallabin dake dafe akan
kyakkyawan gashin kanta shima duk yaji jiki yayi shara shara kamar buhun algarara ga kuma uwa
uba abinda ke dada bata mata rai akullum kwanan duniya wata Bangwaleliyar LAYA dake makale
a dan siririn wuyanta mai kamar na Barewa.
.
Wannan laya tana matukar bata mata rai ta tsani layar nan kamar yadda ta tsani dan iskan saurayin
can na makaranta mai takurawa rayuwarta a kullum.
Yar budurwar ta sake nazarin kanta jikin madubin sannan saita shafi tsohuwar layar dake wuyanta
wacce a cewar masifaffiyar marikiyarta wai
LAYAR GADO CE KUMA TA DADE A DUNIYA DOMIN TUN DAGA CAN KAKANNINTA
NA BAYA AKE TA GADON LAYAR HAR ZUWA KANTA. KUMA WAI LAYAR MAGANIN
TSAUTSAYI CE.
.
To ko ma dai layar mecece ita kam budurwar ta tsani wannan laya.
Gashi dai daman ita ba wata suturar kirki ce da ita ba kullum taje makaranta a rabe rabe take bata
iya shiga cikin kawayenta tun da dai su a kullum tsaf tsaf suke cikin sutura mai tsafta amma ita
kullum cikin tsumma ga kuma wannan masifaffiyar laya da aka makala mata a wuya
to yanzu in ba son a muzantani ba wacce budurwa yar jami'a wacce ta kai matsayin karatun jami'a
awannan zamani za'ace wai dole saitasa laya?
Budurwar ta tambayi kanta hawaye ya fara sartu akan kyawawan kumatunta sa'ar data fara kokarin
tura layar cikin rigarta domin ta boye ta.
.
Kukan me kikeyi AISHA?
Wata fikakkiyar murya tace da ita daga baya aisha ta juya firgigit ta dubi uwar rikonta jikinta na
rawa

Ma...ma ba komai
babu komai kamar yaya? Amma kuma bakomai kike kuka kedai wallahi aisha kin shiga uku da
gulma shegiya masifaffiya uwar jaye jayen magana wato yanzu tsakanina dake ma har abinda yakai
sharri ko? Yanzu idan wasu dangin namu suka shigo gidan nan ai sai suce cutar MARAINIYA nake
toh Allah yagani dai tsinanniya tun da iyayenki suka mace na daukeki inata faman wahala dake ashe
bakar jaraba na dauko toh kyaci kanki ba dai ki cinye ni ba.
Zaki tashi ki tafi makaranta ko kuwa saina karaso naci ubanki anan inyaso kiyi kuakn da dalili?
Aisha ta mike a tsorace sannan ta dauki jakarta dake kan kujera cikin sauri ta fice daga dakin tana
goge idanu
saura kuma ki dawo naga kin jefar da wannan layar wallahi na lahira ma sai yafiki jin dadi shegiya
uwar kinibibin tsiya in banda layar wacce tsiya iyayen naki suka bar miki matar tace da ita tana
Bambami
aisha batace kala ba tafice tana kuka.
.
Karfe tara da kwata ta isa jami'ar tuni tasan an fara daukar darasi kuma tana tattare da masaniyar
cewa muddin dalibi ya kara mintuna goma sha biyar to bashi ba shiga dakin darasi musamman idan
dakta bashir ne ke koyarwa.
Tunanin hakan dakuma gudun kada tashiga ajin karatun dakta bashir ya muzanta ta agaban dalibai
shi yasa Aisha ta karkata tabi ta cikin inda ake ajiye motocin dalibai domin anan ne kawai zatabi ta
iya zuwa dakin kwanan dalibai mata dake jami'ar
ko banza dai aisha tace cikin zuciyarta na wanke fuskata na dan gyara kwalliyata kafin dakta bashir
yafito daga ajin inyaso saina halarci darasi na gaba.
Aisha ta kutsa kai tsakanin tarin motocin burjik kamar fari dake farfajiyar makarantar wadanda mafi
yawa daga ciki motocin na dalibai ne adaidai da wata bakar marsandi mai budaddiyar kofa ne to taji
caraf an rike jakarta ta baya ta juya a fusace.
Sannu da zuwa aisha kema a makare kikazo? Wata sassanyar muryar namiji ke magana
Aisha ta dubi saurayin mai magana cikin takaici tace a fusace don Allah meyasa ne kullum kake son
takurawa rayuwata?
Ki gafarceni aisha wallahi so kawai nake mu gaisa don nasan idan muka shiga aji ba saurarata
zakiyi ba
kuma don kana son mu gaisa saika rike mun jaka? Kai bakajin kunyar mutanen dake kallon mu?
Dubi fa can da nan ko ina duk dalibai ne amma saika....
Aisha stop ita please kada ki zama kamar wata yar sakandire mana remember fa yanzu a jami'a
muke inda ba ruwan wani da wani kowa nada yancin irin rayuwar dayaga dama don haka idan inaso
ma ayanzu I Can Kiss You I Dont Care.
Allah yayi min tsari dakai aisha tace a tsorace sannan tafara ja da baya zata wuce shi
Aisha saurayin ya kira sunanta a tausashe
ta murtuke fuska tace dashi cikin shishshika don...Ta murtuke tace dashi cikin shishshika
don Allah don Annabi ni ka kyaleni na huta ka takurawa rayuwata tun danazo makarantar nan kake
ta damuna da maganganu marasa ma'ana na rashin kunya to ni naji kaje ka nemi daidai dakai ni ba
yar iska bace dubeni fa.
Ta daga hannu ta nuna masa tsummokaran kayan dake jikinta menene abin sha'awa ajikina?
Tsummokaran ko me?
Saurayin ya zura mata idanu na tsawon lokaci yana kallon bangwaleliyar layar dake wuyanta baya
ko kiftawa tamkar malamin kimiyya mai nazarin kwayoyin halittun cikin ruwa.
Aisha diresin kawai suka fi ki ba kyau ba amma ni tunda nake ban taba ganin wacce nake kauna
kamarki ba amma ke kin tsaneni kullum ina lura dake danayi miki magana sai inga kin hada rai
kamar kinga mutuwarki. Sai kuma kiyita wulakanta ni.
Gaban aisha ya fadi sa'ar dataji ance tayi wulakanci a'a kayi hakuri ni ban iya wulakanci ba.... Ni
irin maganganunka ne bana so
to daga yau ban kara yi miki su amma kauna ban iya dainawa Aisha kin shiga rayuwata har abada.

Aisha ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta sannan sai ta daga kai matasan biyu suka dubi juna
na dan lokaci
saurayin ya sake kurawa layar dake makale a wuyanta idanu zuciyarsa cike da mamakin dalilin
dayasa wannan kyakkyawar budurwa yar jami'a guda take yawo kullum da laya a wuya tun shekarar
karatunsa ta farko a jami'ar yake ganinta da bangwaleliyar laya da yawa daga cikin abokansa sun
sha cewa dashi. Kai bebe din nan karshe ce duk fakalti din nan babu mai kyaunta amma rashin
diresin da katuwar layar nan dake wuyanta shi ya bata lamarin bayaninta.
Aisha tayi sauri ta rufe layar da tafin hannunta sa'ar data lura da irin kallon da saurayin keyi mata
sannan saita juya tana cewa dashi.
Sai an jima ko? Saurayin yayi murmushi cikin jin dadi domin tun da yake bata cewa dashi sai
anjima ba.
Aisha... Adawo lafiya idan an tashi kuma zanso kibani labarin wannan layar dake wuyanki fuskar
aisha ta sauya launi sa'ar dataji abinda yace.
Babu ruwanka da layata aishata tace dashi batareda ta tsaya ba tana gama fadin haka saita dada
sauri ta nufi dakin kwanan dalibai wanda dole ne saitabi ta tsakanin wani dan karamin daji daji
kafin takai dakunan.
.
Lokacin da aisha ta biyo yar siririyar hanyar kusan ita kadai take tafiya domin duk kusan dalibai
suna dakunan karatu suna daukar darussansu na ranar.
Adaidai lokacin data kawo kusa da wasu dogayen bishiyoyin turare ne to taji anyi kiran sunanta
Abaya.
AISHA
cikin sauri ta juyo a tsorace domin muryar batayi kama data mace ba haka nan kuma shakka babu
muryar batayi kama data namiji ba sautin muryar yafi kama da bututun Roba.
Aisha ta dafa kirji sa'ar data juyo tana waige waige cikin fargaba domin bataga kowa ba abayanta
sai wani famfo dake zubar da ruwa da ruwa shi kadai acikin tarin ciyayin dake karkashin bishiyoyin
turaren gami da wata kyakkyawar BALBELA fara mai dogon wuya da tsinin baki tana karkada
fuffuke cikin Nishadi.
Aisha tayi sauri ta gyara jakar dake kokarin subucewa daga kan kafadarta domin duk ilahirin jikinta
rawa yakeyi kamar mazari sannan lokaci guda kuma ta fara waige waige a rude.
.
Shin ko ba sunana naji an kira bane?
Tace cikin zuciyarta daga inda take tsaye tana iya hangen dalibai mata acan nesa da ita a kofar
hostel din haka nan kuma tana iya jiyo hayaniyar dalibai sama sama acan cikin makarantar inda
dakunan darussa suke.
Lallai kam me yiwuwa kunnena ne yake fada min karya aisha ta sake cewa azuciyarta don haka
saita sake juyawa gami da yiwa kanta murmushi aisha yar yarinya kedai kin cika tsoron tsiya
wallahi Tace da Kanta.
.
Tana juyawa gaba ta fara tafiya sai taji an sake cewa abayanta AISHA DAKE FA NAKE.
Aisha tayi mutuwar tsaye domin ko shakka batayi tasan sunanta ne aka kirawo awannan karon.
Wa...ne.. Ne? Ta juyo tana fadi a razane domin haryanzu bata ga mai kiran ba sai farar balbelar nan
dake kan famfon nan mai tsiyayar da ruwa tana dubanta
Nice Aisha kada kiji tsoro na ni mai kaunarki ce farar balbelar ce ke magana da aisha ko shakka
babu.
Aisha tayi tsalle gefe guda a razane ta dubi balbelar idanunta kamar zasu fado a kasa saboda tsabar
kaduwa balbela da magana
na shiga uku aisha tace cikin zuciyarta
hannayen aisha suka dauki rawa kar kar kar jakar dake kafadarta ta kwace ta fadi a kan ciyayin nan
da nan iska ta fara fatali da yan takardun da kuma littattafan Aisha cikin a ciyayin.
Dauki Jakarki Aishata ba cutar ki zanyi ba tsakanina da duk danginku sai kauna nasan tuni kin fara
tunanin ko ni aljana ce to tabbas hakane ni aljana ce kuma na dade ina tare da danginki yau kusan

SHEKARU DARI DA ASHIRIN 120YRS kenan don haka ki saki jikinki Aisha so nake nabaki
wani dan bayani agameda Layar dake wuyanki domin naga kina cikin wahala da tsananin rayuwa.
.
Aisha ta dubi balbelar tace baiwar Allah dan Allah kiyi hakuri ki barni na koma da baya zuwa cikin
makaranta wallahi bansan cewa nan hanyarku bace da bazan biyo ba
kada kiji tsoro Aisha ba laifi kikayi min ba inason kuma ki kwantar da hankalinki ki daukeni
amatsayin yar uwa kamar yadda wani daga cikinKada kiji tsoro Aisha ba laifi kikayi mini ba inason
kuma ki kwantar da hankalinki ki daukeni amatsayin yar uwa kamar yadda wani daga cikin
kakanninki na can baya ya daukeni shekaru dari da ashirin da suka wuce Balbelar tace tana
mimmike dogon wuyanta.
.
Toh baiwar Allah yanzu me kike sonyi dani kuma? Aisha tace jikinta na kyarma.
Abinda nake so dake aisha shine idan kinje gida yau ki shiga

Please Login or Register in order to submit comment