Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KIBIYAR AJALI
Na
Nazir Adam Salih
Ebook creator Shuraih Usman 99%
.
Zaku iya downloading wasu da dama daga cikin ebook namu ta hanyar ziyartar babban shafin mu na Hausaebook akan wannan adireshin www.shuraih.waphall.com
Wannan ebook din an sake shi ne A matsayin Happy Sallah ga daukacin Al'umman musulmai baki daya ,
Asha karatu lafiya

Karar Abinda Ban taba zato ba ta ratsa kwakwalwata da
farko na dauka karar aradu ce barcin da idona ya zama
tarihi a halin yanzu na tabbata karar bindiga naji nan da
nan na nufi kofar dakin da gudu a daidai lokacinne naga
wani ya nufi kasan benen da gudu sanye da bakaken
kaya. Cikin kaduwa na juya zan koma dakina sai naga daki
mai lamba uku 3 a bude banyi wata wata ba sai na fada
cikin dakin na lalubi makunnin lantarki na kunna sannan
na ganta a kwance gaban farar rigarta ya rine da JINI.
Babu Alamar tsoro a fuskarta duk da cewa ta mutu hakan
bai hana ZAINAB yi min murmushi ba.........
.
KIBIYAR AJALI-01
.
NAZIR ADAM SALIH
(Nas)
.
KASHI NA DAYA
Lamarin yafaru ne tun yammacin wata lahadi misalin
karfe hudu da rabi bazan taba mantawa da lokacin ba
domin kuwa lokacine da ya zamo wani bangare na tarihin
rayuwata ina zaune a kofar gidan mu sai ga wani yaro fari
siriri yana sanye da fararan kaya da bakar hula hana
sallah a kansa yaron bai wuce shekaru goma sha uku
aduniya ba ya jingine kekensa a jikin bangon gidanmu
.
"Ina wuni yaron yace dani
lafiya lau na amsa
wai kaine Fadil yaron ya tambaye ni
eh nine na amsa
ya miko min wata farar jakar wasika an zaneta da furanni
tun kafin na buda na gane daga inda wasikar ta fito
wannan itace wasika ta uku dana karba a cikin kwanaki
biyu hakika ina tausayin rayuwar amina sai yanzu ne
nagane irin son da take min amma ni haryanzu allah
baisa min kaunarta ba ko kadan kada kayi zaton wai ko
don ba ta da kyau ne shine yasa bana kaunarta ba kada
kayi mamaki idan nace ma ina kyautata zaton tana daya
daga cikin matan da zasu cinye gasar sarauniyar kyau da
za'ayi anan kano.
.
Nafito da wasikar na karanta sannan nace da yaron kaje
kace mata ina zuwa yanzu yace toh sannan ya hau
kekensa yatafi tausayin rayuwarta ne ya sake dawo min
amma badon inasonta ba kyakkyawar tafiyar minti
ashirin takai ni unguwar
gidan
KANAL A. MUKHTAR
yana daya daga cikin manyan gidajen dake sultan road
kanal mukhtar tsohon soja ne wanda yayi ritaya shekaru
goma da suka wuce ganin wasu sojoji biyar masu jajayen
ido da tarin gashin baki shiyasa ni na kafe babur dina tun
kafin na karaso kofar gidan na tako a kasa har na karaso
kofar gidan na tsaya cak ina shawarar abinda zanyi shin
sallama zanyiwa sojojin ko kuwa sannunku zance musu?
Sannan kamar daga sama sai na ji anyi kiran sunana tana
zaune akan wata farfanda nayi mamakin yanda akayui
ban ganeta ba.
.
Sannu da zuwa tace dani naji ance gobe zaka tafi kaduna
hutu shine nace bari na kirawo ka muyi sallama
tausayinta yakara kamani akaro na farko kenan tun
lokacin da muka fara haduwa da AMINA a wajen wani fati
da akayi a unguwarmu sainaji ta fara karya zuciyata...
**
Kina nufin kice wani yazo nema na?
Na tambayi yarinyar adaidai lokacin da zan bude kofar
dakina dake DABA OTAL kaduna kwanana biyu a cikinta
kuma naji dadin zama babbar otel ce mai dauke da kayan
jin dadin rayuwa ana jita jitar cewa duk najeriya babu
irinta in ka dauke guda daya wacce basai na fada ma ba.
Ke menene sunanki? Na tambayi yarinyar dake gabana
tayi murmushi sannan tace sunana ZAINAB kuma ni
ma'aikaciya ce anan otel din sannan ta sake yin
murmushi na dubeta sannan nace don Allah kinsan
abinda zakiyi? Tace a'a
idan ya dawo kice masa yabar miki sunansa ko kuma ya
jirani har na dawo.
kamar yaushe zaka dawo in yazo na fada masa ?
Zan dawo kamar kamar bakwai da rabi na dare.
Nagode kinji ko don Allah menene sunanki? Kin fada min
amma na manta na tambayeta,
Sunana Zainab idan kuma kana son ganina zaka iya zuwa
hawan benen nan na uku ofis mai lamba(6).
Nagode nace da ita sannan ta tafi tabarni nan cike da
mamakin wannan bako nawa wanda bana tsammaninsa
yanzu haka ma bani Fadil din yake nema ba nace cikin
zuciyata sannan na fitar da maganar daga raina na tura
kofar dakin na shiga.
.
Sanyi ya bugi fuskata a yayin dana ga dakin babban daki
ne wanda ke dauke da gado daya, kujeru biyar da kuma
tebur daya mai dauke da wata karamar bidiyo da
talabijin mai fadin fuskar da ta wuce fadin bangon sinima
ba zaka iya kiran dakin aljannar duniya
ko kuma in ce aljannar najeriya saboda tsabar
tsaruwarsa nidai awajen hudu na kira shi.
Duk zuwan bakon mutumin nan bai dameni ba har yanzu
ni ina murna da hutuna dana fara anan jihar kaduna
kullum fatana shine idan nagama makarantar gaba da
firamare wato sakandire na tafi kaduna na kashe lokacin
jiran da zamuyi na fitowar sakamakon jarrabawar mu.
Yayana wanda nake wajensa acan jihar kano baiso na tafi
hutun ba saboda babu wanda na sani a kaduna amma
dana takura masa sai ya amince yakuma kama min
wannan daki dakuma wa'adin wata daya zanyi bayan
wata guda yace kada na kara koda kwana daya na koma
gida.
Na zage labulen tagogin biyu dake dakin sannan na cire
rigata da wandona na daura kyallen tsane ruwa na shiga
wanka bayan na fito na dubi agogo naga karfe hudu
saura minti biyu sannan na buda akwatina na dauko wata
riga baka marar nauyi mai budadden hannu na kuma
dauko wani farin wando shima nasa na tsefe kaina na
daura agogo na kuma na kwama takalmina na shiga duba
littafina dana rubuta.
Bayan lokaci kankani na gano inda na ajiye shi shida
alkamin rubutuna sannan na fito na rufe dakin har zan
tafi saina dawo da baya na sake budewa na shiga domin
na tabbatarwa da hancina abunda ya shaka adaidai
lokacin danake kokarin rufe kofar na mika kaina ina daga
waje na shaki iskar dakin nidai nasan bansa turare ba
nakumayi mamakin yadda akayi harna shigo nayi wanka
banji kanshi ba saida nazo fita.
Hakika wani yashigo dakin dazun bayan fitata na tabbatar
da hakan ta hanyar kula da tsarin inda takalmana suke
daga bangaren arewa amma yanzu sun dawo bangaren
kudu
Na tabbatar da hakan ne ta hanyar kula da tsarin inda
takalmana suke daga bangaren arewa amma yanzu sund
awo bangaren kudu na dakin akwatin kayana ma ba'a
barshi a baya ba.
.
******* ******* ******* ******* ******
.
Idan ka dauke wajen danake zaune ko ina cikin lambun
shakatawar otal din cike yake da mutane makil wadansu
na wanka wasu kuma suna wasa da jajayen ya'yansu a
bakin ruwa wannan shine daya daga cikin abinda yasa
jama'a suke zaune a otal din na dauki birona da littafina
na dora akan tebur sannan na jingina da kujerar na fara
tunanin abinda zan fara rubutawa.
.
Idan baka sani ba yakamata ka sani nazo hutu kaduna ne
da niyyar rubuta littafi akan soyayya kamar yadda
abokaina keyi anan kanon dabo a duk lokacin danayi
niyyar fara rubutawa sai naji duk na rasa ta inda zan fara
wannan shine babban abinda yasa na nacewa yayana
yabarni nazo kaduna hutu
domin idan ina ni kadan zanfi bada kwazo da nutsuwa.
Don haka ma danazo wajen shakatawar otel din sai na
zabi bangaren arewa da lambun dana jikin katanga wacce
zaiyi wuya ka gane cewa katangar bulo ce saboda
korayen furannin da ganyayyakin fulawowin da suka yi
yado akanta gaba da baya abin ba'a cewa kome domin
duk inda ka taka a otel din kore shar yake da ciyawar nan
mai kama da kilishi.
Saura kadan biron dake hannuna ya kwace ya fado kasa a
sakamakon firgitar danayi na tabbatar da cewa lokacin da
na zauna babu kowa a kusa dani sai wata bishiya taku
biyu daga inda nake to amma yanzu juyawar da zanyi sai
naga wata yarinya tana zaune akan wata kujera mai
kyaun gani da dukkan alamu ita tazo da kayarta
.
Sannunka tace dani cikin wata murya lallausa muryar da
bazan taba mantawa da ita ba har abada.
zuciyata da kwakwalwa ba zasu iya jure irin kyawun
wannan yarinya ba.
Yawwa sannunki dai kyakkyawa na amsa mata
WANNAN SHINE FARKON RIKICIN
sa'adda na juya na tafi daga wajen da duk wannan bai
faru a kaina ba.
Na mike tsaye yayinda tabar kujerar da take zaune ta
matso kusa dani sannan sai tattausan lebenta ya fadada
izuwa murmushi fuskarta na kyalkyali hakoranta kamar
nono tana sanye da riga suwaita baka da kuma jan
wando jeans da bakin takalmi kambos ta daure mararta
da wani faffadan belt mai kyalkyali ga sarka mai kamar
walkiya nata kyalkyali a wuyan. Sai bayan datayi
murmushi ne na kula da wani digon baki a kumatunta na
hagu wanda shi dai ba digashi akai ba halitta ce kawai.
.
Yan mata da dama suna da kyawawan fuskoki da kuma
halittar da zaka dade kana sha'awarta ka kalle su sama da
kasa ka gane wa kanka cewa lalle wadannan sune irin
matan da duk wani saurayi ke burin mallaka sannan da
zarar kun rabu saika manta dasu da dai kamar ba'a
halicce su ba amma wannan yarinyar bazaka taba
mantawa da ita ba kada ka tambayeni me yasa akwai
wani abu dake tattare da kyawunta ita dai daban ce daga
cikin mata kamar yadda kalanzir yake daban acikin ruwa
.
Kina bukatar taimako ne? Na tambaya cikin muryar dana
kasa ganewa ko tawa ce ko kuma ta wani. Ta girgiza kai
sannan tace A'a daman dai naga kai kadai ne shine nace
bari nazo na debe maka kewa.
Kasan nima ban cika son surutu da hayaniyar jama'a ba.
Toh ai shikenan nace cikin rwar jiki
ta janyo kujerarta tazo gaban tebur dina ta zauna a duk
lokacin data kalleni sainaji kamar na dauketa na hadiye
don kauna na tabbata yanzu na kamu da ciwon SO
wanda bansan maganinsa in dai har yarinyar nan
bataamince min ba.
Menene sunanki Yan Mata ? Na tambaya
sunana BADURA tace dani cikin lafazi tattausa hutu kake
anan ne naga alamar kamar kai bako ne?
Kwarai kuwa nace da ita yau kwanana biyu kawai anan
kuma sunana FADIL
Badura ta kalleni na kalleta mukayi shiru na dan tsawon
lokaci wajen yayi tsit na dan tsawon lokaci wajen yayi
domin alokacin mutane sun fara watsewa ta dan duba
agogo ta mike tsaye zan tafi Fadil sai kuma yaushe kenan
.
Haba Badura tun yanzu nace, ki bari mana shida ta karasa
yayinda nake bin ta da kallo
akwai abunda zanyi ne gobe ma ranace zamu iya haduwa
kamar wannan lokacin sannan nan da nan ta dafa
kafaduna guda biyu ta kura min ido nasan ta gane na
kamu ciwon sonta ta kuma san nima nasan ta kamu da
ciwon SONA.
.
Fadil! Tace dani cikin rarraunar murya kamar zatayi kuka
kar kaji komai don Allah idan na bata ma rai kayi hakuri
zan dawo gobe kamar yau kaine mutum na farko da na
fara jin son sa acikin zuciyata kafin na farga har ta saki
kafaduna ta fada motarta taja kamar hayaki ta nufi kofar
lambun.
.
****** ****** ****** ******* *******
.
Karfe uku tayi hudu tayi banga alamar Badura ba na tashi
na fara hange hange amma ban hango kome ba sai masu
hannu da shuni ne suda ya'yansu keta shagali a bakin
ruwa
tun misalin karfe biyu na sauko daga dakina zuwa
lambun na zauna zaman jira amma har yanzu shiru
kakeji biyar tayi shida tayi sannan na fitar da rai na
tabbata yau ko bacci bazan iya ba,
haka na kwana ina tunani jiya ga dukkan alamu yau ma
haka zan kwana na mike na nufo kofar lambun ina dube
dube shiru kamar na tsaya na sake dubawa sai dai na
hakura na hau sama na shiga dakina na bude tagogin
dakin sannan na kwanta amma barci ya kasa daukata
Na duba agogona naga karfe goma saura kwata hakika
tunani da begen badura sun mamaye duk wani sashe na
zuciyata abin dayafi tsoratar dani ma shine yadda akayi
har na kamu da ciwon sonta cikin dan kankanin lokaci a
yanzu kam babu wani abu da bazan iya ba wajen ganin
na mallaki abar begena badura kada kaga laifina abin da
ido ya gani zuciya ta amince masa dole ne rai ya so shi.
Na juya da niyyar na gyara kwanciyata sai naji kamar ana
kwankwasa kofar dakin na yunkura na tashi tsaye cikin
mamakin ina tunanin ko zainab ce ta kawo min abinci to
amma kuma ai na sanar da ita cewa yau a waje zanci
abinci na dai bude kofar.
A tsaye a bakin kofar fuskarta tana walwali kamar madubi
tana sanye da riga ruwan hoda da wondanta akwati mai
taya baka a hannunta kanta babu kallabi BADURA CE.
Cikin mamaki da kaduwa na matsa ta shige cikin dakin
batareda ta ko dubeni ba abin dana tabbatarwa kaina
shine wannan zuwa nata bana kwanciyar hankali bane na
kara tabbatarwa da kaina haka alokacin dana kunna
lantarkin dake dakin haske ya gauraye ko ina sainaga
fararen idanuwanta sunyi jajur kamar ta wuni tana kuka
ko kuma bata sami cikakken barci ba
.
Me yafaru badura nayita jiranki bakizo ba? Na tambaya
lafiya kuma na ganki haka cikin wannan lokacin?
Tayi ajiyar zuciya sannan ta dago kai muka hada ido
Wallahi Fadil wani abune yake bani tsoro tace dani tun
jiya da safe wani mutum yaketa bina abaya abaya duk
inda nayi sai ya bini da farko nayi kokarin bace masa
amma na kasa sai na hakura na kyale shi na dauka irin
samarin nan ne masu bin yanmata agindi toh sai kuma
jiya muna zaune a lambun nan naganshi yanata kallon
yana muzurai nayi niyyar na fada maka sai tsoro ya
hanani shine nace maka zan tafi kaga idan natafi sai ya
bini domin bana son abinda zai tayar maka da hankali
'kamar yaya yake? Na tambaya cikin mamaki.
Baki ne dogo kakkaura yana sanye da koriyar riga da farin
wando' tsoro ya kamani cikina ya kada tun sa'ar data fara
bani labarin sai yanzu ne na gane abinda take nufi
mutumin kenan dayazo nemana bana nan shine yake bin
Badura
.
Bayan wannan fa? Shi ya hanaki zuwa wajena? Na
tambaya
'A'a ba hanani yayi ba nice dai na hana kaina domin bana
so in jefaka a cikin bala'i gara in wani abu ne ma ya
sameni ni kadai na tashi na matsa kusa da ita na kura
mata ido.
Kada kice haka nace da ita ni masoyinki ne kifada min
duk abin dake damunki gobe zanyi maganinsa abinda
nake fada nima kaina ya bani mamaki domin maganar da
tayi ta dada tabbatar min da kaunar da take min.
Jiya da daddare.....
Taci gaba da cewa naganshi yazo hotel din nan a wata
mota kirar Alfa Romiyo amma bai shigo ciki ba daga waje
ya aje motar ya shigo da kafa danaga haka sainayi sauri
na rufe dakina ina lekensa ta tagar dakina.
Yana nan yana ta dube dube har sha dayan dare danaga
haka saina kulle tagar dakina nayi kwance toh sai kuma
can dare naji ana taba min kofar daki amma idan na leka
saina rasa kowa da haka dai har gari ya waye da yamma
tayi yau kenan nayi shiri domin na same ka a lambu sai
na ganshi a hawa na daya benen nan yana jira na nafito
don haka sainayi zamana har dare yayi ban fito ba shine
yasa kaga banzo wajenka ba
.
A wanne daki kike? Na tambayeta
daki mai lamba uku 3
nayi mamaki don jin cewa dakin a kusa da nawa yake
amma ban sani ba daki mai lamba hudu shine nawa ta
dago kai muka hada ido sai tace dani
ina fata ban takura maka ba don nazo nayi ma bayanin
abun da yafaru kaga jiya wallahi banyi barci ba tsoro
kuma yau ma na kwanta kenan sainaji an fara gugar
kofar dakina shine na ganka kana bude kofar dakinka
shine nace bari nazo na kwana anan da safe saina tafi.
.
Ki tafi ina?
Na tambayeta
kano mana ai canne garinmu daman a kano kike nace da
ita da sauri
Eh mana zakayi mamakin yadda akayi ban tambayi inda
take zaune ba a kano bankuma tambayeta abinda ya
kawota kaduna bahakika al'amarin ne ya rikitar dani
yakuma bani tsoro don hakan saina kyaleta ban kara
tambayarta komai ba.
Saiki kwanta da safe ma tattauna akan maganar nace da
ita ban kuma ce mata nima dan kano ne ba
.
Ahaka muka kwanta tana gefena daga bangon dakin
nikuma ina kwance a gabanta wato a bakin gadon karfe
hudu da rabi na dare agogon bango ya buga otel din tayi
tsit bakajin komai sai saurar ruwan sama ajikin tagogin
dakin kamar da bakin kwarya idona biyu tun karfe goma
sha biyu sai yanzu ne naji idona ya fara lumshewa na
juya na zubawa abar kaunata ido ina kallon kyakkyawar
fuskarta har dai barci ya daukeni.
.
Karar Abinda ban taba zato ba ta ratsa kwakwalwata na
tashi firgigit!
Na miko kafata kasa sannan na tashi tsaye barcin ya fice
daga idona nan da nan kamar daman idona biyu da farko
na dauka karar tsawa ce amma daga baya saina kasa
gaskata hakan na tabbata karar BINDIGA naji nan da nan
na nufi kofar daki da gudu na bude na leka a daidai
lokacin danaga wani kokuma ince wata ta nufi kasan
benen da gudu sanye da bakaken kaya zaiyi wuya ka gane
mace ko namiji ne saboda rashin isashen hasken dake
kwararon benen saida me gudun yazo shan kwanar da
zata kai shi hawa na karshe....
Saida me gudun yazo shan kwanar da zata kai shi hawa
na karshene na gane macece na tabbata ko wacece bata
so a ganeta a matsayin mace
.
Cikin kaduwa na juya zan koma dakina sai naga dakin
badura mai lamba 3 a bude banyi wata wata ba na kutsa
kai cikin dakin na lalubi makunnar lantarkin na kunna
dakin ya gauraye da haske sannan naganta a kwance akan
gado gaban farar rigarta ya rine jawur da JINI tiriri na
tashi daga ramin da harsashin bindigar yayi a kirjinta.
Babu alamar tsoro a fuskarta duk da cewa ta riga ta
MUTU hakan bai hana Zainab murmushin karshe ba.
**
Mintuna biyu suka shude ina tsaye akan gawar zainab
bana ko motsi kamar an dasani rigata ta jike shakaf da
gumi duk da yake ana san danyi saboda ruwan da ake ta
ketawa kamar da bakin kwarya A halin yanzu ruwan ya
dan tsagaita nayi zaton karar bindigar zai tashi jama'ar
dake kan benen otel din amma koda na mutum daya
baizo ba na dan bude kofar dakin na leka sosai ko zan ga
motsi amma banji motsin komai ba sannan na juya
nayiwa zainab kallon karshe na fice daga dakin nakuma
maida kofar na rufe nasa hannu zan tura kofar dakin
kenan sainaji wata murya irin wacce zakaji idan kaje
makabarta da ake fatalwa tace min
.
Barka da asuba
nayi firgigit na jya a rude abinda idona ya gane min ya
ban haushi dakuma dariya wani tsoho ne fari mai
motsatstsiyar fuska kamar matsatstsen lemon tsami yana
sanye da shudayen kaya a kirjin rigar an rubuta cikin
harshen turanci
(DURBA HOTEL)
wato sunan hotel din da nake ciki kenan
barka ka dai na amsa masa cikin wata murya da batafi
tasa dadi ba girarsa mai kama da ta biri ta daga sama
ayayinda yaga fuskata ta hadu da gumi
Lafiya dai malam kobakajin dadi ne ya tambaya nayi
murmushin da bai kai idanuna ba nace dashi wallahi
wani abinci jiya kuka bamu a otel dinnan wanda ya rikita
min ciki shine yake murda min ciki yanzu ma naje wajen
makwabciyata ce ko tanada magani ta taimaka min dan
yi shiru sannan ya kalle ni yace Allah sawwake nace amin
.
Har zan shige dakina sainaji yace zainab ta tashi kuwa ko
har yanzu bacci take? Saura kadan in kifa masa mari
fuskata ta chanza kala jikina ya dau rawa lallai in tsohon
nan yasan zainab tana cikin dakin nan to kashina ya
bushe domin babu abunda zai hana a dora min laifin
Kisanta
Malam kaga karka bata min lokaci nace dashi cikin fushi
ni bansan wata zainab ba Badura dai itace mai dakin ita
kadai kuma nagani aciki in babu sauran wani abu kuma
ya kamata ka kyaleni da shegiyar tambayarka kaje kayi
aikin da aka saka ka
Allah baka hakuri mallam motsatstsan tsohon yace dani
daman abinda yasa na tambaya jiyane kafin mu tashi
daga aiki tace min idan aiki yayi mata yawa a daki mai
lamba 3 zata kwana wai saboda idan dare yayi ba'a
samun motar zuwa unguwarsu.
.
Jikina ya sake daukar rawa kamar anayi min kidan gangi
awace unguwa take? Na tambaya
A Unguwar shanu take yace dani
menene aikinta a otel dinnan?
Aikinta shine bada dakunan kwana dakuma kula da
wadanda ke ciki
sai anjima kaji ko nace dashi ba tare dana jira wata amsa
ba sai kawai na shige daki na janyo kofar na rufe sannan
nasa sakata
.
Badura na zaune akan gadonta tana shafa mai koda ganin
fuskata saita tashi tsaye ta dafa kirji
lafiya fadil na ganka haka duk ka canja nan da nan ?
Kada iya kayan da kika san zaiyi miki amfani kisa cikin
jaka nace da ita batare da na kalleta ba domin nasan
kallonta alokacin zai iya kara tsoratar da ita nayi
tsammanin zata tambaye ni wani abu amma saita bani
mamaki nan da nan naga ta fara hada kayanta kamar
yanda na umarceta na wuceta nabarta anan tana ta hada
kayanta ni kuma na shige bandaki
na duba kaina sama da kasa acikin madubin dake like a
dakin abindana gani yaban tsoro fuskata tayi sharkaf da
gumi kamar wanda yaga fatalwa karkayi mamaki dajin
haka domin kuwa wannan shine karo na farko dana taba
ganin gawa kiri kiri kasan kuwa ko jana'iza naje a lullube
nake ganinta na dauke kaina daga madubin sannan naje
gindin famfo na shekawa kaina ruwa ahalin yanzu bana
bukatar wanka itama badura rashin sanin abinda ya faru
ne yabata damar wanka shin data san da gawa a dakinta
me kake jin zai faru? Na shashshare ruwan dake kaina da
wani kyallee sannan na sake duban kaina ajikin madubin
abinda nagani yanzu yafi na da kyaun kallo da kadan a
kalla dai bazan tsorata yara ba na bude kofar bandakin na
shigo dakin tana zaune akan kujera tana kuka
menene kuma ya same ki na tambaya tayi ajiyar zuciya
sannan ta dago kai muka hada ido da ita sannan tace fadil
don Allah in laifi nayi maka saika fada min bai kamata ace
kana korata don kawai kaga ina SONKA.
.
Banga laifinta ba domin kuwa ko kaine ka kwana dakin
wani yazo yace maka ka hada kayanka batareda wani
karin bayani ba dole ranka ya baci saidai kuma shirin shi
yafi amfani ahalin yanzu ba sai na gaya ma ba halin mata
ina fada mata zata rikice har tasa shirin da nake a halin
yanzu ya ruguje ya zama dole na bar otel din kafin a sami
zainab a mace.
Kada ki damu masoyiyata nace da ita cikin kalami mai
dadi idan munje gidan zan fada miki abinda ya faru
sannan naci gaba da nade kayana tana zaune batace dani
Uffan ba
Na hada kayana masu amfani a jaka daya sannan na zuge
nayi shirin gudu kenan ko ban fada maka ba zaka fahimci
bala'in dana fada a halin yanzu gawar ma'aikaciyar hotel
din dake ciki dakin masoyiyata kanajin idan aka same ta
matacciya wa za'a fara nadewa? Masoyiyata badura kasan
kuma ko ban fada maka ba bazan taba barin wannan ta
faru a kanta ba sannan abinda ya dada dagula al'amarin
shine idan yan sanda suka fara bincike matsatstsen
tsohon nan zaice
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment