Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har sau uku
.
Ba komai bane ya sanya ni farin ciki ba face ganin alert cewa mahaifina ya turo mani naira dubu goma sha biyar #15,000.
.
Ai atake awajen na shiga gida na mayar ma mahaifiyata da dubu biyun ta .
A gurguje naje unity bank na ciro kudaden duka sannan na dauki hanyar EMIR PALACE
.
Tana zaune bisa wata kujerar roba sanye da wata tsadaddiyar atamfa dinkin riga da siket ta yafa wani mayafi wanda launinsa yazo daidai da launin takalminta, shi ko jakanta launinsa ya zo daidai da launin kayan dake sanye ajikinta
.
Irin zunzurutun kyaun datayi bazan iya misalta shi acikin wannan gajeren labarin ba ,
Koda na iso gareta sai nai mata sallama take ta amsa da muryatta mai dadin sauraro
Sai na saki wata murmushi mai dauke da sakonni kala kala sannan nace da ita "maganar gaskiya itace a kowani lokaci kara kyau kike gimbiya kursiyya"
.
"Lallaima wato abin ya zama yar zolayace ko" tafadi
Nan take nasa hannu na jawo wani kujera sannan na zauna ina mai fuskartarta
Hira mukai da ita sosai,amma ko kadan babu wata kalma ta so ko kauna dana bari ta subuce daga bakina
Bayan mun idar da hirar ne muka tashi muka nufi bakin titi don tsaid abin hawa
Toh anan ne nace da ita"kinga ma na manta ban tambayeki ,inda zamu fara zuwa ba"
Tayi mani fari da idanuwa tace " ai kafini sanin garin don haka kai zan tambaya ina muka dosa"
.
"Ok tunda haka kikace sai ki saka io,sannan kija bakinki kiyi gum, ga duk wajenda na kaiki"
.
Napep na tare sannan dukkan mu ,wato ni da ita muka dunguma izuwa ciki, na dan matsa gaban direban na rada mai akunne wajenda zai kaimu
**** ****** *****
Kayataccen wajene wanda iya tsaruwa ya tsaru, tamkar gidan gona haka yake ,
Kujerune makare a wajen an masu wani irin salo
Salon kuwa shine kujerune guda biyar ake ajiyesu yadda zasu fuskanci juna (cycle) a tsakiyar kujerun kuwa wani dankareren teburne na gilashi.
.
Zaune take a daya daga cikin kujerun a yayin da ni kuma nake fuskantarta yayinda wata dankareriyar teburi ta gilashi ta raba tsakaninmu
.
A makare a saman teburin kayan makulashe ne da tande tande sai lemuka iri iri
Duk kuwa ni nai ordansu wa kursiyya duk da kuwa wasu daga cikin kayan makulashen ban taba ganin suba sai yau ARANAR SALLA.
.
A tunanina na riga na gama sace zuciyan kursiyya tun da gashi ta kirani izuwa yawon bude ido,
Ta danci kayan tande tanden kadan sannan ta kora lemo sai ta dubeni tace itafa so take taje gida, dariya nayi sannan nace "keda kika fito yawon bude ido , tun ba'aje ko'inaba har kin fara sarewa "
.
"Ba sarewa nayi ba yanayin garinne bai min ba "
Anan dai na shiga lallabata har na ci nasara na shawo kanta ta amince zamu karisa yawon bude idanuwanmu
.
Wani ma'aikacin wajen ne ya kawo mani bill na dauki bill din da hannun hagu alokacin da na dau lemo zan kora da hannun damana
.
Ai koda na kalli bill din bansan lokacin da kofin gilashin dake hannuna ya fadi akasa ba
Sakamakon ganin irin makuden kudaden dana kashe yanzu yanzu
.

.
Warnin:- Ina fadi ina sake fadi, da kwai wasu da suke Editin mani post suna cire sunana sannan su saka nasu, wato ina nufin SATAR FASAHA
Ban hana copy ba amma ban yarda a canja mani tsarin labari ba
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%
https://facebook.com/Shuraih-99-296485144050085
.
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 9
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
Naira na gugar naira har naira Dubu biyar #5000
Ni dana ke tunanin duk wannan lodi danayi baifi na dubu daya #1000 ba amma ashe hadin manyan mutane nayi ,
"Dubu biyar " na fadi acikin raina
"Wainine nan na kashe dubu biyar cikin mintuna kalilan akan wani abin banza wanda bama zamu'iya cinyewa duka ba.
Ai da badin muna tare da kursiyya ba da babu abin da zai hanani kwashe duk wannan kayan tande tande na zuba su acikin leda,nayi gida
.
"Ina ganin ya kamata mu wuce"
Muryar kursiyya naji kwatsam acikin raina
Tashi nayi naje na biya su kudinsu ba tare da son raina ba haka ina kallo muka tafi muka bar damin abinci da lemo bisa tebur.
Godewa Allah na sake yi daya sa mahaifina ya turo mani da kudi. In badan haka ba da yanzu haka ban san irin ukubar dana ke ciki ba
**** ****** ******
Kishingide nake acikin daki na bisa katifa nayi daidai da kafafuwa kai kace dan kaciya ne ,
.
Babu abin da na ke tunani sai abinda ya wakana tsakanina da kursiyya
A wanni biyu da suka wuce lokacin da muka bar wannan restaurant din bamu zame ko ina ba sai wani wajen chasun Salla anan ma muka dan shafe wasu mintuna sannan aka tatsi lalitata har naira dubu biyu #2000
Kai in takai ce maku wannan labarin, saida muka ziyarci wurare akalla sunkai biyar, akowani waje kuwa sai an tatsi lalitata.
.
Bazan mance lokacin dana sauke kursiyya a kofar gidansu ba, alokacin ne ta fito daga cikin kafi babur din da muke zaune dukkanmu, fitowa nima nayi daga cikin kafi babur din, sannan na sallami mai kafi babur din yai tafiyarsa
.
Kursiyya ta matso dab dani yadda zamu iya shakan numfashin junanmu ,tace dani
"Shuraih" yadda ta kira sunan sai naji tamkar ita ce ta rada mani sunan sannan taci gaba da cewa
"Agaskiya na godema abisa wannan halaccin daka nuna a gareni"
"Ai nine da godiya bake ba gimbiya kursiyya"
Nace da ita yayin dana dan ja da baya
"Toh ni zan shiga gida. Shuraih". Tafadi mani lokacin data nufi hanyar da zata sada ta da kofar gidansu
"Bakiji ba" nafada
"Baka fadi ba" ta bani amsa
"Gimbiya kursiyya yanzu a wani matsayi kika ajiyeni acikin zuciyarki"
Tayi murmushi sannnan tayi mani wani kallo wanda ke nuna ta dago jirgina
"Shuraih lallai zan baka amsar wannan tambayar taka amma ba yanzu ba,
"Sai yaushe "na tambaya cikin kaguwa
"Zan kiraka a waya da karfe 9:00pm na dare. Sannan sai in sanar dakai inda zamu hadu" tanagama fadin hakan sai tai tafiyarta
.
Sa'o'i biyu kenan da faruwar wannan al'amarin
Yanzu dana ke kwance bisa katifa acikin dakina, babu abin dana ke jira face karfe tara na dare tayi, duk kusan minti daya sai na duba a gogo haryanzu dai karfe 8:30pm ne
.
Sautin budewar kofa naji daga gefena hakan yasa na maida dubana bakin kofa, mujahid ne ya shigo. Yana zuwa daidai wajena sai yace" baba kafara shirin cin kasa fa"
Na dubeshi cikin mamaki nace mai name kuwa
Yayi murmushi sannan yace
"Ai dazu da muka dawo masallaci, na kira kursiyya awaya mukai ta hira , nace mata zanzo gidansu, nan take ta bani adreshin gidan
Ina zuwa kuwa na dauketa ,muka je sabon gari gidan su Anas daganan kuwa muka zarce zuwa karofi na kaita gidan hajiya suka gaisa, kai in takaice maka labarin har cewa tayi zata kirani yau misalin karfe taran dare izuwa wani shagali"
BADAKALA KEnAN
Warnin:- Ina fadi ina sake fadi, da kwai wasu da suke Editin mani post suna cire sunana sannan su saka nasu, wato ina nufin SATAR FASAHA
Ban hana copy ba amma ban yarda a canja mani tsarin labari ba
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 10
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
Take na tashi daga kwancen danake sannan cikin alamun mamakin maganar mujahid. Nace mai
"Yaushe kenan duk wannan al'amari ta kasance tsakaninka da kursiyya alhalin yau throught out muna tare da ita ne"
Nan na zayyane ma mujahid dukkan wani al'amarin daya faru tsakanina da ita.
Koda mujahid ya gama sauraren labarina sai ya kama habar bakinsa sannan yace
"To yanzu wannan yarinya me take nufine damu"
"Ni ba wannan ne yafi damuna ba ,shin me yasa ta ce zata kiramu da karfe tara" na fada
Girgiza kai mujahid yayi sannan yace"ni ma abin dana ke tunani kenan"
.
"Kodai zata kiramune don ta zabi wanda take so a cikin mu" nafada
"Tabbas maganarka hakan take kiranmu zatayi don ta nuna wanda ta keso atsakaninmu" mujahid ya fadi
"To amma..." Karar ringing din wayar mujahid ce ta katse mani zancena "
Ciro wayar yayi daga aljihunsa sannan yai sallama , tsayawa yayi da wayan akan kunnensa har tsawon wasu dakiku ,sannan yace "toh ganinan zuwa"
.
Yana sauke wayar daga kunnensa ne nima tawa wayar ta fara ringing ,ina dubawa naga nomban kursiyya ne
Na daga tare da doka sallama, ta amsa sannan tace
"Shuraih ka saurareni da kyau yanzu haka ina (U.CENTRE) , Bikin salla ake don haka ina jiranka a wajen yanzu, dan Allah kar ka wuce mintuna biyar " tana gama fadin hakan ta kashe wayar.
.
Na dubi mujahid nace "kursiyya ce ta kirani tace dani wai na sameta a.."
"U.centre ko" ya katseni da fadin haka
"Toh amma kai ya akayi kasani" na tambayeshi
"Kiran da akai mani yanzu itace ta kirani take sanar dani wai na sameta a U.centre" ya bani amsa
***** ******
A tsaye muke abakin titin muna neman acaba , can sai ga wani dan acaba nan ya sulalo, tsayar da shi mukai, sannan muka hawa muka cemai U.centre zai kaimu
.
Gudu acaban keta shararawa,
Babu tunanin danake illa irin cakwakiyar da zata faru izan har kursiyya ta zabeni a matsayin masoyinta, hakanan wani irin cakwakiya za'a diba izan har ta zabi mujahid ,
Can sai ji nai dan acaban ya taka burki, take babur din ta tsaya cak a gefen titi
Na duba gefen dama na , sannan na duba gefen haguna banga wani mai mota yana ko masu babur suna giftawa titin ba.
Duk da kuwa a cikin duhu ne amma hakan bai hanani gane A DOKAR DAJI muke ba.
.
Mujahid ne ya fara saukowa sannan yace "ya malam mun ce maka ka kaimu U.centre ne bawai DOKAR DAJI ba "
Juyowa dan acaban yayi sannan ya dubemu, duk da acikin duhu muke amma hakan baisa kwakkwal din dake kanshi ta daina kashe idanu ba, haka kuma hakan bai sa na kasa gane wannan bakar fuskar tasa ba
Kamar dazu dai fuskar nanan babu walwala bare annuri a tattare da ita ,
Koda nai arba da fuskar nan tashi sai naji gaba daya gabban jikina sunyi lakwas, alamun razana suka bayyana akan fuskata ,
.
Na juyo dabi mujahi na ce mai "kasan ko wanene wannan dan acaban din"
Girgiza mun kai yayi alamar bai ganeshi ba
.
"BA WANI BANE FACE BAMAGUJEN DAN ACABAN DA MUKA CUTA DA SAFE"
Na fadi mashi
.
Hausa wa suka ce inkere na yawo zabo na yawo wataran sai an hade
.

Warnin:- Ina fadi ina sake fadi, da kwai wasu da suke Editin mani post suna cire sunana sannan su saka nasu, wato ina nufin SATAR FASAHA
Ban hana copy ba amma ban yarda a canja mani tsarin labari ba
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%
https://facebook.com/Shuraih-99-296485144050085
.
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 11
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
.
Koda dan acaban ya fuskanci mun ganeshi sai ya fashe da dariya marar dadin sauraro sannan ya fuskance mu yace
" Mu maguzawa ,ba a cutarmu sakamakon wanda ya cucemu kuwa itace mutuwa"
.
Ai yana gama fadin hakan sai ya zaro wata narkekiyar wuka daga kugunsa ,kafin ya yunkuro ya juyo
Tuni har mujahid yayi tsalle daga kan babur din , take nima na mara masa baya,
Bamu tsaya duban gabanmu ba sai kawai muka ari na kare
.
Wannan bamagujen kuwa sai ya buga wutan babur dinsa sannan ya cigaba da binmu.
.
Fadawa mukai cikin daji sai gudu muke
A yayin da mujahid yake gabana ni kuma nake bayansa
.
A duk lokacin dana waiga bayana sai naga wannan bamagujen ya kusa cimmini hakan ce tasa na dage sai gudu nake
.
Muna cikin wannan gudun ne muka shigo wani gona wanda kunyen doya ne birjik a ko'ina ,ban ankara ba sai ji nayi wani kututturen itace ya tsarge mini kafa,
.
Take na fadi shirim bisa kunyen doya ,
Na yunkura kenan zan mike in cigaba da gudu , kawai sai ji nai an ciccibeni an buga da kasa , sannan aka hawa ruwan cikina aka danne ni
.
Ashe dai bamagujen nan ne ya cimmini, wukar dake hannunsa ya daga sama sannan yace
"Kai yaro babban kuskuren da kuka aikata agareni itace karya da kukai mani, a rayuwata na tsani karya , kaine mutum na goma sha uku da zan kashe ata dalilin karya"
Yana rufe bakinsa sai yadaga wukan sama da nufin ya caka mani, kawai sai ji nai ya kwarara ihu, sai hannunsa mai rike da wukar ta fara yo kasa tana kusan toni,
Nan take bamagujen ya bingire kasa sumamme
.
Abin daya bani mamaki kenan , sai dana mike tsaye sannan na lura da mutum agabana .
Mujahid ne rike da wata zabgegiyar katako a hannunsa,
Sai yanzu nagano abin dayasa bamagujen nan ya bingire akasa sumamme .
.
Nan take muka dauki babur dinsa muka hau mujahid yajamu.
.
**** ******
Saukarmu kenan abakin dankareren hotel din wanda a samansa anyi rubutu da wata na'ura mai haske rubutun cikin manyan haruffa suke(U.CENTRE)
.
Nan take muka kutsa kai ciki, bamu sha wahala ba wajen ganin kursiyya ,
Azaune bisa kujera kursiyya ce
Sannan wani saurayi kyakkyawa yana fuskantar ta koda muka kariso sai muka gaisa da shi sannan muka nemi kujeru muka zazzauna
.
Tun lokacin dana hada ido da wannan saurayin naji gabana ya fadi,
.
Akaron farko kursiyya ta dubemu tace "shuraih ,mujahid, wannan shine saurayina ANAS, kuma mijin da zan aura "
.
Ai bansan lokacin da kaina yafara juyiba ,kunnuwana suka kurumce ,
Nidai naga kursiyya na motsi da baki amma bansan me take fadi ba ,take na tashi naje na nemo ruwa nasha sannan ne hankalina ya dawo jikina
Kursiyya ta dubi waNnan saurayin tace "Anas wayannan Abokaina ne kuma yan'uwana "
Nan dai muka sake gaisawa da anas
A sannan ne take sanar damu cewa bikinsu saura sati biyu kuma zata aikomana da katin gayyata .
******
Nida mujahid muka fito daga cikin hotel din rai a bace ,
Dukkanmu da abinda muke tunani acikin zuciyarmu,
.
"Sannunku dan Allah tambaya nake "
Wata zazzakar murya ce ta katse mu,
Waigowar da zamuyine mukai arba da ita,
Farace tas,mai matsakaicin tsayi hade da faffadan fuska, dauke da haskakkun idanuwa , dan siririn karan hancinta shi yataka muhimmiyar rawa wajen bayyana kyawunta.
.
Koda mukai arba da wannan kyakkyawar budurwa sai muka rugo izuwa kanta
Da saurina na matso gefenta na dama shi ko mujahid ya matsa gefenta na hagu,
.
Rike mata hannu nayi sannan nace wa mujahid
"A'a fa mujahid kar mui haka dakai kasan ni nafara ganinta"
Shima ya rike mata hannun hagu gam yace dani
"Karya kake ni nafara ganinta"
Nan dai muka cigaba da jayayya da shi, izan naja hannun damanta sai kaga shima mujahid ya janyo hannun hagunta, yadda kasan zamu ballata
Ita ko inbanda ihu da karaji babu abinda take
.
Wani mai shayi dake dan nisa damu, yana kallon duk wannan badakalar,
.
Sai ya wangame katoton bakinsa sannan yace"jama'a ina kuke ga wasu yan banzan yara can suna neman su lalata yarinyar mutane" cikin bude murya ya fadi hakan
.
Ai koda mutane suka ji haka sai suka nufo inda muke
Daga mai katako 2 by 2 sai mai icce da gora
Kai hardama masu Adduna da fafale
Suko yara kankana na sai suka debi duwatsu.
.
Koda muka hangosu sai muka saki wannan yarinyar sannan mukace kafa mai naci ban baki ba
.
Muna cikin gudun ne kawai sai naji saukan wani katon abi a goshina , nan na kwarara ihu, ina taba goshin naji danshi danshi a goshina wannan shi ya tabbatar mani da an fasa mani goshi
.
ADUK LOKACIN DANA KALLI TABON DAKE GOSHINA A MADUBI SAI IN TUNA
DA RANAR SALLAH
.
TABBAS BAZAN TABA MANTAWA DA IRIN CHAKWAKIYA DA BADAKALAR DATA FARU DANI ARANAR SALLAH BA IYA TSAWON RAYUWATA
.
Tammat alhamdulillah
Kagaggen labari daga Shuraih Usman
Na godewa Allah daya bani ikon kammala wannan labari
Duk wani kuskure dana tafka acikin wannan labari Allah ya gafartamani
Sannan ina mika gaisuwata ga dukkan masoyana da masu bani shawarwarin alkhairi
Allah yabar zumunci
Daga karshe nake cewa sai kunjini a cikin wani sabon littafina mai suna TUHUMA
.
ARANAR SALLAH
Shekarar rubutawa:- 2017
Hakkin mallama (m) Shuraih Usman
Company:-Shuraih 99%
Tel.08133209890
Tel.09086261484
.
Warning. | Gargadi
Ban hana copy ba, Amma duk wanda ya canja mani tsarin labari , ko ya cire sunana yasa nasa toh Allah ya isa
.
LITTATAFAN MARUBUCIN
1.TAKOBIN JINI 1-2-3
2.LABARINA
3.NAMIJIN GASKE 1
4.ARANAR SALLAH
LITTATAFAI MASU FITOWA
1.TAKOBIN JINI 4-5
2.NAMIJIN GASKE 2-3
3.TUHUMA
4.SADAUKI UBAN SADAUKAI
Coming soon.......
.
Sadaukarwa ga
Mal.Usman
Haj.Maryam
Mujahid hamza
Zainab Usman
AAmina Usman
Abdul'aziz Usman
BAN MANTA DA KUBA
Dahiri Usman diffusion(D.U.D)
Anas Aliyu katuka(bin maleek)
Suleiman ishaq(big army)
Abdullah(B.O.C)
Dafatan kuna cikin koshin lafiya


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2

Please Login or Register in order to submit comment