Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba a garin nan. Koda bayan an daura
auren dole ne a nemo ta, dole ne a gano
inda ta shiga."
.
"Haba Alhaji, to amma saboda Allah yaya za a
ce an daura mana aure ba amarya? Kai ma ka
san cewa wannan ba karamin tonon asiri ba
ne a gare ni. Ya kamata dai a san abinda ake
ciki kawai."
.
Siririn mutumin ya share zufa de ke kan
dokin wuyansa. "Wallah ni kaina ban san me
yake damun wannan yarinyar ba. To ka san
bai yiwuwa ka haifi yaro sannan kuma ka haifi
halinsa, wannan hali nata ni ban san inda ta
samo shi ba, domin kuwa daga ni har uwarta
duk mutanen kirki ne wallahi."
.
Gali ya harari mutumin a fakaice, a zuciyarsa
ya ce "Kana matsayin mutumin kirki amma
ka damfare ni kusan miliyan guda, don kawai
za ka ba ni 'yarka?" To amma dai a zahiri
cewa ya yi da shi, "Ni dai ka ji bayanina
Alhaji, in dai har ba a gano mini amaryata ba,
to ina jin mu duka sai kawai mu yi hakuri da
maganar. Domin kuwa jiya aka daura auren
abokina, muna so ne mu hada bukukuwanmu
rana daya da aurenmu, amma kuma ni a ce
wai ba a ga tawa amaryar ba. Wannan ai
tonon silili ne ake nema kawai a yi mini."
.
dan motsattsen mutumin ya yi ajiyar zuciya,
jikinshi ya soma kyarma domin kuwa a yadda
ya lura da kwayoyin idanun saurayin ya san
cewar abubuwan da yake fada har cikin
zuciyarsa abinda yake nufi kenan.
.
"To ni yanzu don Allah me kake son in yi
maka? Ai'sha dai ni na haife ta, kuma ta
kwashe kayanta ta gudu ta bar gidan nan, me
kake so yanzun in yi maka, tunda ka ce ba ka
yarda ba?"
.
Saurayin ya sake hade fuska sannan ya ce da
shi.
"Ai ba wani abu ba ne mai wahala, ina ganin
Alhaji, in dai ban takura maka ba, ai ina gani
ban yi laifi ba idan na ce ka shiga cikin gida ka
tattaro min kudadena da na kashe tun farkon
soyayyata da 'yarka A'isha. Domin kuwa idan
har za ka iya tunawa ka amshi manyan
kudade a wajena, kuma kai ma ka san dai ai
ba kyauta na ba ka su ba, domin kuwa inda a
ce ni talaka ne ba ni da kumbar susa, na
tabbata daidai da rana daya ba za ka taba
barina in zo kofar gidanka har in furta ina
neman 'yarka ba
.
Don haka ni ma na rika ba ka kudaden da kake bukata, na san dai ba ka mance ba da su ba."
Saurayin ya dan yi murmushin takaici sannan
ya ci gaba da shaidawa ramammen tsohon
.
"Tun fara neman auren A'isha na fara lissafin
abubuwan da nake kashewa a dalilinta, kai
hatta man da nake zubawa a motata in zo
wurinta, da kuma kudin da nake baiwa yara
su kira min ita, duk ina rubutawa. A halin
yanzu lissafi ya yi kauri, domin kuwa kullum
sai na ciro doguwar takardata ta lissafi, na yi
bitar kudaden da ke cikin akawun dina da
wurinka
.
Don haka na ba ka awowi goma ka
tattaro min kudadena. In ba haka ba, ka ji na
rantse maka da Allah, sai na dankara ma ka harsashin bindiga,
tsohon banza makwadaici kawai macuci!"
.
Gali ya bude kofar motar a fusace ya shiga ya
tashe ta. Ya juyo ya dubi motsattsen
mutumin, wanda a halin yanzu ko'ina a
jikinsa kyarma yake yi hatta fuskarsa da ke dakon faskeken tabaron
ita ma kyarma take yi, duk da uban kayan da
aka jibga mata,
.
"Kada ka damu Baba, na ga ka rude, ai kudin
ba wasu masu yawa ba ne, miliyan daya da
dubu dari bakwai da hamsin kawai, sai naira
dari uku da talatin da biyar." Ya fizgi motar ya
fice a guje daga kofar gidan
.
Motsattsen mutumin ya bi kurar motar da kallo. A daidai
lokacin ne faskeken tabaron ya kubuce daga
'yar mitsitsiyar fuskar tasa, ya fadi kasa. Tuni
har ya fara tsammanin hawan jini.
.
___________
Shuraih 99%
Iyaye ayi hattara da amsar kudi ko wani abu a hannun siriki kafin Aure
.
Duniya ta lalace da cin hanci wai har MALAMAN ADDINI suna RASHAWA
._____________
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 11
.
____________
Tsawon mintuna biyar mafadaciyar matar na
ta faman yiwa mijin nata banbami. Yana
tsaye kawai yana duban ta, sai zufa ke ta
faman kwararo masa, tana wanke masa
fuska, kamar ana yi masa sakiya
.
Ya rasa da me zai ji tsakanin masifar da kuma gargadin da surukinsa ya zo ya yi masa. Ya san cewar
wannan saurayin dan bindiga-dadi ba hankali
ya cika ba, kamar yadda da ma ya dade yana
jin ana cewa ba duk soja ne ke da cikakken
hankali ba
.
Hakika yana iya aikata duk
abubuwan da ya fada, ga shi kuma yanzu
Juma ta tuso shi a gaba da tata masifar.
.
Duk ya rasa abinda ke masa dadi a duniya.
"Kawai aikin banza Malam, ka jawo min 'yata
kwalli kwal da nake alfahari da ita a duniya ta
tattara kayanta ta gudu, da ma haka kake so
sai ka zuba ruwa a kasa ka sha, burinka ya
cika."
.
Alhaji Dage ya yi shiru, bai ce da ita kala ba,
domin kuwa ya san cewa yanzu ba lokacin
tankawarsa ba ce, don kuwa har ga Allah
matar tasa ta tunzura. Ya san cewa idan ya
biye mata, tana iya kama shi da kokawa,
kuma ba ya kokwanto ya san cewa shi za ta
kayar
.
Shi ya sa ya rufawa kansa asiri ya rabu
da ita, in ta yi ta gaji dai ai dole ne ta bari.
Juma ta sake cewa da motsattsen mutumin
cikin kwarmato kamar za ta hadiye shi.
.
"Wai me kake nufi ne Alhaji, ba ka ce komai
ba. Ko kuwa kana nufin shi kenan, kai ka
cinyewa mutane kudi, ni kuma ka bar ni da
asarar 'yata. To ai sai ka sake tunani, don
kuwa ba kyale ka zan yi ba, duk inda 'yata ta
shiga sai ka je ka kwakulo min ita, in dai kana
son zaman lafiya a duniyar nan, to wallahi ka
nemo min A'isha domin kuwa duk kai ka
jawo mana wannan masifar."
.
Ramammen mutumin ya yi ajiyar zuciya, a
karo na farko ya ga cewar ya kamata dai ya
dan ce wani abu. Don kada ta ga ya ki tabuka
komai, ta sake haye masa yadda ta ga dama.
.
"Ba na son rashin albarka, Juma." Ya ce da
ita, "Ni kike yi wa wannan tsagerancin ko
kuwa kin fi ni son 'yar tawa ce, da kike fada
min wadannan maganganun? Ko kuwa ni ne
zance ta gudu ta bar gidan? Wannan
tsinanniyar yarinya ina amafaninta, duk ba
halinki ta kwaso ba? Ke din a da can me ye ba
ki yi ba? Ba don yanzu an mance, ba a tone-
tone, shi ne har kin samu bakin magana.
Kada in sake jin muryarki a kan maganar nan
Juma."
.
Ya zazzaro mata idanunsa da ke cikin
fasasshen tabarau, a tsammaninsa watakila ta
dan ji tsoro ta lafa. To amma kuma cikin
rashin sa'a sai ya ga ta yi shewa, sannan ta yi
tafi ji kake fas, ta ce da shi.
.
"Lallai yau da tone-tone a gidan nan. Au kai
nan har gori zaka yi min? Ka mance da
abubuwan tsiyar da ka kuntuka a baya? Haka
fa kawai nake zaman hakuri da kai.
.
Shi ne yanzu har ka samu bakin da za ka yi tonon
silili. To ai sai mu fara a ji ni da kai wa ya fi
wani mugun tabo, ba tsoron ka nake ji ba
Alhaji, mu yiyar tonon asiri."
.
Alhaji Dage yayi saurin tsayar da ita, da ya ga
ta sake hayewa.
"Duk wannan ba ta taso ba, ni dai gaya miki
na yi dama don maganar da ya dace ki rika
fada, ai ba cewa na yi za mu yi wani tone-
tone ba, don kuwa mu dai ba yara ba ne, ya
isa a ce mun mallaki hankalinmu a halin
yanzu."
.
Juma ta yi guda sannan ta ce da shi.
"Ashe ka ji tsoro mai gida. Ai na so mu
jarraba tonon silili da kai wallahi da ka ga dan
biki da cika yau a gidan nan. In ana fadin abin
kunya kai har ma ka sa baki a gidan nan. In
ba abin kunya ba mene ne amfanin karbarwa
mutane dukiya don za su auri yarka? Haka
fa ka yi ta yi wa ragowar yayan danginka da
ka rika a gidan nan. Ka aurar da yan mata
sama da biyar duk a bisa zalunci. Yanzu suna
can dakunan mazajensu suna shan wahala ana
yi musu gori da wulakanci, tunda dai ka
saida musu da mutunci. To ni ba mai yi wa
yata A'isha wannan mulkin mallakar, mu
zuba ni da kai a gidan nan tun da kai ba ka
gudun abin kunya."
.
Mutumin ya yi ajiyar zuciya, ba shi da ta cewa
domin kuwa duk abin da matar ta fada
gaskiya ne duk ya aikata. Yana jin ta ta ci gaba
da cewa da shi.
.
"Duk wanda ya sa ranshi a kwadayin abin
duniya dole ne ya ga wulakanci mai gida,
amma ina amfanin a ce a matsayinka na
babban mutum wanda zai yiwa wani nasiha a
ce kana rigima kai da surukanka kana amsar
musu dukiya? Yanzu ga abin da ka jawo
mana, wannan mutunci ne?"
.
Ramammen mutumin ya girgiza kan shi
kamar uwa na wa danta fada "To ai laifin
yarinyar ne ni wannan tsinaniyar yarinyar
wallahi ta cuce ni.."
.
"Ka da ka tsinewa yata a banza domin kuwa
ba ta da laifi, kai ka jawo mana wannan
rigimar muna zaman zamanmu lafiya. Ka san
cewar A'isha ba ta kaunar yaron nan ka nace
a kan maganar nan don ka gan shi da kumbar
susa, ga shi yanzu kana jin tsoron fita waje ka
da surukinka ya harbe ka
.
Ina na taba jin irin
wannan abin tsiya ma a duniya, ni Juma."
Alhaji Dage cikin nadama ya ce.
.
"Kin ga laifina ne a banza Juma, amma a
matsayina na magidanci saboda Allah ba ni
da yanci zabarwa yata mijin da na ga ya fi
dacewa da ita? Wani zamani dai Allah ya kawo
mu inda yara ke kangarewa su fi karfin
iyayensu.
.
Mu a zamaninmu wane yaro ya isa
ya ce shi zai yiwa kansa zabi sai wanda ya ke
so, mu kuma mutane sai mu bar abu ya
lalace da kanmu, mu ce ai zamani ne, da
gangan ake kyale yara suna wannan iya
shegen da fitsarar ana kallon su."
.
"Ba haka ba ne maigida" Juma ta ce da shi
"Ko ka ki ko ka so al'amura suna canzawa,
kuma zamani ya kan zo da abubuwa iri-iri
dole kuma mutum ya bi abinda zamani ya zo
da shi matsawar bai sabawa shari'a ba. Ai ba
haramun ba ne don yaro ya zabi wanda ya ce
yana so ya aura. Kuma da ka ce a naka
zamanin ba haka ake yi ba, kai zamaninka ka
sani, ba ka damu da zamanin yayanka ba. A
zamanin naka ai bante ake daurawa ba sutura
ba, me ya sa ba za ka cigaba da daura bante a
wannan zamanin ba, tun da ka ce ba ka
amince da canjin zamani ba, sai ka koma
tafiya tsirara da bante, don kuwa shi ake
daurawa zamaninka na baya."
.
"Yanzu dai mu bar wannan maganar" ya ce da
ita abin da ya faru dai ya riga ya faru, dole ne
in sanar da jami'an tsaro su shiga cikin
maganar don a kawo karshen wannan rigima,
kafin abin ya kai mu ga kashe-kashe don na
ga alamar abin da wannan mahaukacin sojan
ke nufi kenan, in ya so daga baya sai in sayar
da gidana na sabuwar unguwa in biya shi
kudadensa, ita kuma A'isha sai a nemo ta a
bata wanda take so."
.
Juma ta dan saki ranta ta ce da shi.
"To yanzu da ka yi haka kai kanka ba ka fi jin
dadi a ranka ba? Ai wannan shi ne datattako
maigida, yanzu to ka nemi a zauna lafiya."
Kamar aikin budar idanu cikin yan tsararun
mintuna mafadanta ma'auratan biyu suka
dawo cikin raha kamar ba su ba. Shekaru
sama da talatin kenan, suna wannan halayya,
an ce a cikin minti daya sai su hautsine da
fada, kafin kiftawa da bismillah sai kuma a ga
sun dawo suna dariya.
.
To sai dai kuma a wannan karon da sun san cewar akwai wani
shu'umin saurayin da ya cika bindigarsa da
harsashi, sannan kuma ya saya musu likkafani
jana'iza da ba su sake yin wata raha ko dariya
ba.
_____________
A'isha ta dubi angonta Nazifi cikin farin ciki
sannan ta ce da shi "Nazifi 'darling' yau dai
Allah ya cika mana burinmu, mun zama mata
da miji. Duk duniya babu mai raba mu ni da
kai masoyina."
.
Nazifi ya dube ta shi ma duba na so da kauna
yana kwance a kan doguwar kujerun da ke
cikin tsararren dakin da suke ciki, ya ce.
"Ai ni A'isha ba ma abinda zan iya cewa sai
dai kawai in godewa Allah da kuma wannan
abokin nawa domin kuwa wallahi ni dai ya
gama yanto ni, ya yi min komai na alheri."
A'isha da ke zaune a kusa da shi ta ce cikin
mamaki "Wai da gaske bayan ya ba ka rabin
miliyan har kuma wannan gidan duk shi ya ba
ka, Nazifi?"
.
"To ga zahiri ma kin gani A'isha tun da har ga
shi kuma na shigo da ke kin tare a ciki, ko
kuwa ke a da kin ga na yi miki kama da
wanda zai iya mallakar wannan tsantsareren
gidan?"
.
A'isha ta yi dariya farin ciki.
"Mun gode masa wallahi. Don Allah sai
yaushe zai zo don in gan shi mu yi masa
godiya ta musamman akan wannan abin
alheri da ya yi mana?"
.
Nazifi yace da ita "An jima nan kadan za ki ji
ya zo ya kwankwasa mana kofa domin
kuwa shi ma yau ake daura aurensa da wata
yarinya a nan garin kuma mun yi da shi zai
biyo min ya dauke ni mu wuce wurin daurin
aure tare."
.
A'isha ta sake lumshe idanu cikin murna ta
ce.
"Mun gode wallahi, Allah ya bar zumunci
tsakanin mu da shi. Yaya sunan tasa amaryar
Nazifi?"
.
Nazifi yayi farat ya ce.
"Ai abin namu ni da shi ya zo daya domin
kuwa saboda tsabar shakuwa da muka yi da
shi, har ankon sunan amare muka yi, cikin sa'a
ita matar tasa sunanta A'isha."
.
Suka yi dariya, A'isha ta ce.
"Lallai abin yayi min dadi Nazifi, ka ce kun
samar min kawa kenan ni ma" Suka ci gaba
da dariya abin gwanin ban sha'awa. Suka fito
da naman kaza suka tasa a gaba, dama tun
tarewa su gidan a daren jiya Nazifi ya sawo
dakwalen kaji soyayyu har guda uku. Tun a
jiya suka cikye biyu saura ragowar daya wacce
suka baje a halin yanzu.
.
Ba abin da ya dame su, kudine dai sun samu abin kamar daga sama, dole ne su godewa wannan abokinsu
mai farar aniya.
A daidai wannan lokaci ne Gali ya karaso
kofar gidan fuskarsa a murtuke kamar wanda
aka yiwa albishir da mutuwa. Lokaci-lokaci
yakan kai hannusa cikin aljihu ya shafi
bindigarsa. Kamar yadda ya tsara a ransa,
.
daga nan idan ya gama gaisawa da ango da
amarya, to farauta zai wuce abinsa. Ba
farautar namun daji zai fita ba, farautar
amaryarsa A'isha zai fita da kuma saurayin da
aka ce ya sace masa ita sun gudu. Kuma ya
sha alwashin muddin ya yi ido biyu da A'isha
da wannan saurayi da ya sace ta, to ba wani
bata lokaci duk aikawa da su zai yi barzahu
.
Gali ya yi murmushin mugunta sannan ya
sake mika hannu ya shafo bindigarsa wacce
ke boye a cikin aljihu. Ya daga hannu ya
kwankwasa kofar gidan a sanyaye. A'isha da
Nazifi da ke cikin gidan suna baiwa juna
naman kaza a baki, suka dubi juna cikin farin
ciki a dai dai lokacin da suka jiyo sautin
bugun kofar "Kin ji dan halak!"
.
Nazifi ya ce
"Shi ne yake kwankwasa kofa, Gali ne
abokina. Je maza ki bude masa kofa ki rako
shi, A'isha."
.
Amayar ta ce da angonta a sanyaye.
"Wata kila ma wasu miliyoyin kudin ya sake
kawo mana 'darling'."
Nazifi ya ce "Babu mamaki, A'isha ai na fada
miki abokin nan nawa yana bala'in sona, ke
dai je ki bude masa kofa, ki tarbo shi ya
shigo."
.
___________
YAU KAM RIGIMA ZATaYI KISA
.
Ya kuke ganin zata kaya
Ku biyoni Shuraih 99% a littafin AJALI
Nazifi ya ce "Babu mamaki, A'isha ai na fada miki abokin nan nawa yana bala'in sona, ke dai je ki bude masa kofa, ki tarbo shi ya shigo."
.
A'isha ta mike cikin farin cikin tana rangwada ta nufi kofar gidan.
Hakika sun yi dace ita da angonta Nazifi, Allah ya hada ta da mai sonta kuma ita ma take kaunarsa. Ya raba ta da wannan wahalallen da a da ya nace mata, A'isha ta ce a zuciyarta tana murmushin farin ciki.
.
Ta kama kofar gidan da hannayenta biyu, ba tare da wani fargaba ko zullumi ba TA BUDE MASA kOFAR!
****====******
Dankareren kayataccen gidan ne da ya kai matuka wajen tsaruwa. Jama'a da dama kan dakata don yiwa kyakkyawan gidan kallon tsaf! saboda ginuwarsa.
Mutane da dama kan tuna da kayataccen gidan saurauniyar ingila
dake "BUCKINGHAM PALACE" a duk lokacin da suka dubi tsararren gidan. Wani dadin abin da ke matukar jan hankalin jama'a ga hadadden gidan shi ne daddadan kamshin furanni dake gewaye da gidan.
dan tsamurmurin dattijon maigadin da ke zaune akan bencin a gefen katotuwar kullalliyar kofar gidan mai fasalin fuka-fukan dawisu, ya dan yamutsa fuska gami da gyara rikon jaridar da ke hannusa tamkar mai tsammanin shekowar wani a guje ya wafce ta, cikin zakuwa ya soma bude shafukan cikin ta, a shafi na biyar ya yi ido hudu da labarin da yayi matukar jan hankalinsa mai taken KADDARA KO FANSA!
.
A hanzarce ya muskuta gami da gyara zama, kana ya sake kafa kwala- kwalan idanunsa akan hotunan gawarwakin wasu mutane biyu mace da namiji da ke gefen rubutun, cikin zakuwa ya soma karantawa.
.
A safiyar jiya ne yan sanda suka tsinci gawar
wani saurayi Nazifi tare da masoyiyarsa A'isha.
.
An tsinci gawarwakin ne yashe a cikin wani sabon gida bayan an harbe su da bindiga har lahira.
Tuni jami'an tsaro sun cafke wanda ake zargi da aiwatar da kisan gillar wanda ya kasance wani matashin soja wanda shima yake kaunar budurwar, wanda kuma har an sa ranar bikin su da ita amma kuma ita ba ta kaunarsa.
.
Mahaifin yarinyar mai suna Alhaji Dage ya yi
nadamar afkuwar mummunan al'amarin sannan kuma ya tabbatarwa da wakilinmu cewar dukkan wannan al'amari da ya afku laifinsa ne sakamakon tilastawa diyar tasa da ya yi a kan sai ta auri wanda ita ba shi take so ba. A karshe ya yi kira ga iyaye a kan su dinga mayar da hankali a kan dukkan abin da `ya`yansu ke bukata matsawar dai hakan bai sabawa addini ba.
.
Sannan kuma ya yi doguwar addu'a gami da bayyana matukar alhininsa ga mamatan
.
Don jin yadda zata kaya mu hadu a cigaban littafin nan mai suna A’ISHA don
jin karshen sarkakiyar sarkakakken labarin.
Na gode, naku Shafi’u Dauda Giwa.
.........................
Anan kuma ayau muka kawo karashen littafin AJALI amma da yardar Allah daga nan zuwa wani lokaci zan saka maku cigabansa
.
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing Shuraih Usman 99%
....
JINJINA GA
Shafukan
Shuraih 99%
Zauran labarai
Home of Littatafan yaki and Hausa novels
.
Ina mika sakon gaisuwata ga ahalin kungiyar
TSANGAYAR MARUBUTA
TASKAR GIDAN LITTAFI
.....
Nine naku a kullum da ko yaushe Shuraih Usman
99%
Ku tareni a littafin A'ISHA AJALI
Marubucin littafin
Shafi'u Dauda Giwa
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu [email protected]


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment