Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo Mata daukin wannan azabar da takeji
Cikin ikon Allah kamar da kiftawar ido sai gata a zaune"

Idanun ta sunyi jazur sai kerma jikin ta keyi da kallo tabi gurin da ta take zaune tabi wa"innan ruwan da suke ta komawa" tsutsotsi daga tsutsotsi zuwa qwqri da kallo.sai ta Mike bako tsoron ganin su a ranta ta nufi toilet ta fidda kayan jikin ta tabi jikinta da kallo ganan ruwan Nan a jikinta har sun bushe wanka tayi yafi aqirga ta darje jikinta zuciyar ta nata Mata barazanar tarwatse wa alwala dauro ta fito Dan Babu lokacin tunani a Yanzun bari ta Gama da abinda ke gabanta"

Da kallo ta bi dakin Ina zata Fara ?
Hijabi take nema ganin zata wahala yasa kawaii tajawo wani
Mayafi ta Dora Kan wata gown da ta fiddo tasaka ta kabbara sallah ta Dade tana. Addu'ah tana kuka sannan ta koma toilet din ta debo wasu ruwan Nan ma ta Dade tana addu'ah tana tofawa a ruwan sannan ta karanta ayoyin karya sihiri duk ta tofa aciki
Ta tashi ta nufi wajen kwarin Nan da sukai yawa ga kananun tsutsotsi Nan tayi busimillah ta kwara musu ruwan
Haba ikon Allah yafi gaban wasa sai ga wajen ya Kama da wuta hayaki ya turnuke dakin
Dakin har wata jijjiga yake babu tsoro a tare da ita tana Nan tsaye tana ambaton sunan Allah cikin abinda baifi minti biyar ba hayakin ya dauke " babu komai ba tsutsotsin bare kwarin babu Kuma wannan green din ruwan
Sai a lokacin taji wani kuka ya kwace Mata tanayi tana. Ambaton sunan Allah
Da ya sassauta Mata tuquqin da take ji cikin zuciyar ta


_yan uwa addu'ah ba karya bace" ki jaraba ki gani idan wani Abu ya shige_
_Miki duhu me kuke tunani zai faru adaidai wannan lokacin da aikin_ _boka ya Karye daga jikin umayma inda ace Bata rike addu'ah ba?_

_Na Tabbata da karfin addu'ah Allah yasa duk wata cuta dake marar ta ta fice Wanda wadannan tsutsotsin sune aka cusa Mata a mara da sun cije ta to duk inda zata samu namijj sai ta samu ya biya mata buqatar ta" sune makaman aikin da aka dasa Mata a mara_ _yanda indai Bata samu namijj a time din ba to tabbas zata it's rasa ranta sabida tsananin Sha"awa. Allah ya rabamu da mugayen abokai_


Wai Ina zeena ne?
🤣🤣🤣🤣🤣🤣
Ai mutuniyar taku ashe duk abin nan da ake ta fece Dan tun sanda umayma ta Mike tashiga toilet taso ficewa" to sai ta fasa ta tsaya ta qara ba idon ta abinci
To sanda wuta ta kama kwarin Nan hayaqi ya turnuke dakin tayi tunanin gobara ce ai har fitsari ta saki sanda take gudu hhhh
_bariki Babu amana_


Biki fa ya zo hidima ta kankama daga kowanne bangare" dangi sun Fara hallara daga gidansu ango har gidan su amarya
Shagulgula akwai suke

Events uku kadai suka tsara zasuyi
Arabian night
Bridal shower
Sai dinner in ankai amarya...


**********************
"badiyya badiyya wai bazaki Fito bane? Dan ubanki ki shige daki ki ta faman kwakule kanki ubanwa ya hanaki zaman gidanki? AI da Babu gwara ba dadi kince mijinki Baya isarki Shiyasa kika kashe auren to ai yanzun Gashi nan kinzo kin kare da zurmuka wa kanki Dan yatsa naga ubanda Dan yatsa zai miki yanda kike jarababbiyar nan Toni ki Fito kizo kije ki karbo min tsumi na wajen wajen ille yar sokoto Kinsan Yau malam anan yake so nake mu kwana muna kashe arna a gidan Kinsan malam karshe ne wajen iya harkar nan"
ta karasa maganar Tana nufar bakin rariya Tana tsiyaye wasu ruwa daga cikin wani Dan bowl Mai cike da wasu sauyoyi

🤣🤣🤣🤣 _hodijam gamu a wani gidan yan shagalin Kuma tosu Kuma komeye tasu matsalar?_

Comment
Share
08038541511
[1/27, 9:11 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA*
_kalubalenku Iyaye_


*na*
*Zahrabukar*

*exquisite WRITTERS forum*



*masu himma tuni sun fara subscription kui maza ku hanzarta fa kar ayi baku Tafiyar Mai tsawo ce Akwai rikita rikita da bankade bankade cin amana daukar fansa Mai zafi yaudara zamba cikin aminci kawata matso kusa da yan kudinki kalilan ki kwashi garabasar wannan daddad'an labarin*

Normal group #300
VIP #500
special #600
_duk tsarin da kike bukatarku zaki samu Akwai banbanci yawan posting a kowacce rana akan kowanne tsari_
ki biya yan sulallan ki ta wannan account number din *6035968908 keystone bank umma yusif* Sai ki Turomin shaidar biya akan wannan number din 08038541511. Sai insaki paid group


*25*

___________Kuka take kamar ranta zai fice ta Ina zata Fara?
Menene yashiga kanta har ta manta ubangin ta ta aikata Zina? Zinar ma Mai Muni Dan batai nadama ba sai ma Kara dulmiya da tayi cikin harkar karuwanci ita dai? Ita umayma itace wannan murdaddiyar kaddarar ta afka wa?

Tsaf duk wata rayuwar da tayi tundaga ranar da fateema tazo gidan su har yanayin da ta tsinci kanta aciki bayan tafiar ta da yanda ta bawa sageer kanta a mota da yanda ta watsa rayuwar ta ta hanyar bin maza har wata uwa DUNIYA tsaf ya dawo cikin kanta babban tashin hankalin ta ma shine bakin cikin da ta saka iyayen ta
Shin ita wacce iriyar ya suka Haifa? Bata saka musu da farinciki ba sai kishiyar hakan? Me ta tsinta a rayuwa'?
Lallai ta tafka babbar asara,
Amma yanzun Ina ta Dosa? Me yakamata ta farayi?

Inuwar mutum ta hango da alamun lek'e ake '
Murmushi Tai da ta hangi kan zeena
Dake labe sai ta leko sai ta koma
Duk da kuncin da zuciyar ta kemata Amma tana buqatar shawara
Har ga Allah bata san me yashiga kanta ba har tayi wannan rayuwar Amma Yanzun mafita take nema

Cikin sando ta tashi ta lallaba
Ahankali a hankali ta cafko hannun zeena da ta d'an juya

"Wayyo nashiga uku Dan Allah kar ki mun wani Abu karki manta fa ni taimaka miki nayi ban cutar dake ba" ta fada Tana zazzaaro idanuwa waje

Murmushi Mai hawaye umayma tayi tace
'Matsoraciya to ai sai ki shigo in kin Gama laben "

Da kallo tabi umaymar lallai tabbas zargin ta ya tabbata umayma nada iskokai yo in ba Mai iskokai ba duk wannan abin da ta gamayi dazun yanzun Kuma dariya take
Dazun fa ta Gama cewa wacece ita ni dan tsabagen wulaqanci ma cewa tai Bata sanni ba take ta fada a zuciyar ta

Harara ta wulla Mata tace "baran shigo ba yar wulaqanci inshigo kice Baki ma taba gani na ba kenan
Irin na dazun"

Batace komai ba ta jawo hannun ta tace "haba aminiya meyayi zafi haka Ashe Zaki iya guduna?
Kada fa kisa maganar Nan ta tabbata na cewa
_bariki babu amana_"

Biyo ta tayi tana cewa "yo ai kema dince kinzo da raini sense"
Ammafa abin da mamaki pls bani insha

Zama sukai saman gadon kusan a tare zeena na ta kara kallon dakin Dan fa ita har Yanzun kusan a tsorace take


Hawayen fuskar ta ta share sannan ta ce "ta Ina zan fara?
Wani juyayyen Al'amari ne ya faru dani bansan yanda Zaki dauki abin ba amma fatana ki min kyakkyawan fahimta ki kuma bani shawara ko ince ki tayani warware wannan murdadden Al'amarin dake barazanar tarwatsa min kwakwalwa"

"Inshallah inajinki zan Kuma fahimce ki" su zeenah an Zama serious

Tiryan tiryan ta bata labarin komai tundaga haduwar su da sageer har zuwa ranar da qaddarar ta ta juye" da irin duk irin shedancin da ta aikata sai da ta fadawa zeena
Ta karashe da wani kuka Mai cin Rai
Tana cewa "nayi asarar rayuwa'ta nikam banzo a sa"a ba a DUNIYA"

Da sauri zeena ta katse Tana share hawayen da majina jin itakuma umaima irin tata kaddarar da cewa "kull ki daina fad'in haka
Kowa da kaddarar shi nikaina baki san wace iriyar kaddara ta raboni da gida ba Har tasa na jefa kaina cikin yanayin nan da muke Kai a yanzun bana son tuna Baya bana son tuna wace ni idan natuna cewa nice sanadiyyar mutuwar mahaifiya ta cikamakin farin cikina Amma wani al'amari Mai girma da daure Kai da mamaki ya gifto a rayuwata, amma bari in baki labarina kiji wacece zeenah na tabbata zaki tabbatar da cewa kaddarar ki Mai sauki ce akaina"


"Sunana zeenatu aminu d'an jirgi
Haifaffiyar garin Kano gaba daya na rayuwa'ta a Kano nayi ta mahaifina ya rasu tun Ina yarinya dalilin haka yasa muka koma gidan kakannin mu da zama nida kqnne na biyu da maman mu muka koma gidansu maman mu da zama kakan mu shi ne cinmu Shan mu sitirar mu rashin lpyr mu ke komai har ta skull fees shi ke biya mana bamu da matsalar komai domin Kaka malam ya tsaya mana akan komai

A haka muke ta RAYUWAR mu babu ruwan dangin baban mu da duk wata lalura tamu
Dangin mamana sune komai a kan gaba a haka dai muke rayuwa har sanda nai candy a lokacin Kam na girma babu laifi Dan duk wasu alamomiin yanmatanci sun gama bayyanar mun

Samari ko ta Ina"
Inason auren kasancewar tun sanda na fahimci wacece ni Allah yasa ina da wata irin fitinanniyar Sha"awa hakan yasa nakeson aure tun ina jss Amma ba amin ba kaka malam ya kasa ya tsare ya hanani kula duk wani saurayi acewar shi ni marainiya ce so dole zanyi karatu Mai zurfi kodan in tallafi rayuwa ta da ta Yan uwana anan gaba

Maman mu da sauran dangi suka goya mishi baya
Aka samomin wata private uni naci gaba da karatu na a duk da a gefe daya kullum na tashi sai nayi wankan tsarki
Domin kullum sai nayi mafarkin ana saduwa Dani kuma idan natashi sai naga alamun hakan ajikina

Haka dai tafi tafi har nashiga level 2

Watarana wace Ina tunanin har in koma ga Allah bazan manta da ita a gajiye na dawo skul kasancewar ranar har shida muna makaranta
Wanka kawaii nayi nayi alwala nayi sallahr magrib
Ban ma jira aka ci abinci a tare ba kamar yanda aka saba na je na d"ebo nawa na dawo daki nazo naci inaci nai sallar Isha naje naiwa su mama sai da safe'

Bacci ne a ido na fall hakan yasa ko dakin ban rufe ba na kwanta

Can cikin bacci naji ana ta lalube na na gyara kwanciya ta inajin dadin abin Dan ni duk a tunani na ko acikin mafarkin da na Saba yi ne"
ta saurara tanayin wani murmushi dake nuna tsantsar ciwon da take ji a zuciyarta ta share hawaye ta Kalli umaima tace
"Hmm Ashe wannan a zahiri ne a zahirin ma abin yayi Muni wanda tun da uwar da ta haifeni na fado duniya ban tabajin Wata ya mace da aka taba yiwa irin abinda aka min ba"
Kuka ne yaci karfin ta kamar ta shide umayma dai na kallon ta
Sake da baki
Bata hanata kukan ba sai da tayi har ya ishe ta sannan ta ci gaba da cewa
" da sauri na lalubo bed side lamp na kunna Umayma kinsan me na bude ido na gani?"
Girgiza Kai umayma tayi cike da jimami

"To umayma kakana kaka malam shine dai Wanda na bude ido nagani zigidir Yana wani shasshafa gemu Yana murmushi "
wayyo wata hantsila wa umayma tayi jin wata iriyar cakudaddiyar magana
Gefe ta koma tana zare ido

Murmushi zeena ta saki Mai ciwo taci gaba "Ashe dama kullum idan na rufe dakina sai yazo da spare key ya bude duk abinda nakeji ana mun nake tunanin mafarki ne Ashe umayma kakana ne wanda ya haifi mamana
Shine ke zuwa kullum ya sadu dani ba tare da sani na ba"

Wani kukan ta Kuma fashewa dashi tace
"Ranar ne Allah ya tona asirin shi
Shaf a ranar bansha ruwan dake fridge din dakina ba Ashe aciki duk yabi ya zuba mun mqganin bacci Mai nauyi to a ranar na dawo da ruwa a jaka ta daga makaranta gajiyar danayi tasa Ina Gama cin abincin na jawo jakar na fiddo su nasha duk da rashin sanyin su

Wallahi umayma la"annen tsohon Nan idon shi kyas Dan Babu alamun nadama ko kunya a tare dashi bare ince idan namishi ihu ya tsorata
Sai ma karfi da yasamin ya juya bayana ya sadu dani ta bayana inaji Ina gani sannan ya faffala min maruka Babu bakin kuka har ya gama yasa wani kyalle ya kwashe kazantar da ke bayana wacce ya zuba min sannan ya zura kayanshi

Ko kallo ban isheshi ba bare yamin gargadin kada yaji ko ya gani na sanar da wani abinda yamin ya bude kofa ya fice ya barni Nan yashe

Abin bakin ciki da takaici na kasa magana"l kukan ma gashi fa inayi Amma babu sauti sai hawaye haka na tashi da karfin hali nqje na wanke jikina na fito bacci ya gagare ni na kosa gari ya waye in sanar wa da mamana abinda yafaru mu tattara kayan mu mu bar gidan haka na zauna zuru har gari ya waye na lallaba na fito"

Da qanena Ahmad na faracin karo yace min "Aunty gud morning Baki da lpy ne idanun ki sun kunbura ko
Ko wani ne ya doke ki kikai kuka in rama Miki?"

Ya fada cike da yarinta

"To fa wata sabuwa umayma na bude Baki da niyyar in bashi amsa magana tace daukar ni inda Kika ganni Dan ga fa maganar inayi Amma ba ajin me nake cewa Baki na ma bai nuna alamun Ina maganar balle a fahimci me nake cewa Kiri Kiri a ranar umayma nazama bebiya muna Nan tsaye ina share hawayen fuska ta Dan abin narasa ma me zanyi sai ga kaka malam ya shigo da sauri Ahmad ya ruga yana cewa.......


_tsokaci akan labarin zeenah kacokam labarin zeenah true life story ne asali ma Saboda labarin na tsara sauran labaran nasan da yawa zasuce karya ne_ _so bazan bata lokaci wajen rantse muku ba Wlh inajin zeenah Har cikin Raina sannan bana gajia da bibiyar labarinta Sanda ta bani labarin wallahi na girgiza matuka Tana nan cikinmu Kuma Har gobe Tana rayuwa labarinta Akwai manyan darussa aciki yanzun zamu nausa_

*akwai sabon labarin da nafara a jiya free buk ne short comedian story wato haihuwar fari ku nemi naku kusha Dariya ga Oum nurain ga abu nurain gakuma nurses da dakin kwadago wato labour room karki bari wannan nishadin ya wuceki nemi naki da zafi zafinsa*

Comment
Share
08038541511
[1/28, 9:14 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA*
_kalubalenku Iyaye_


*na*
*Zahrabukar*

*exquisite WRITTERS forum*



*masu himma tuni sun fara subscription kui maza ku hanzarta fa kar ayi baku Tafiyar Mai tsawo ce Akwai rikita rikita da bankade bankade cin amana daukar fansa Mai zafi yaudara zamba cikin aminci kawata matso kusa da yan kudinki kalilan ki kwashi garabasar wannan daddad'an labarin*

Normal group #300
VIP #500
special #600
_duk tsarin da kike bukatarku zaki samu Akwai banbanci yawan posting a kowacce rana akan kowanne tsari_
ki biya yan sulallan ki ta wannan account number din *6035968908 keystone bank umma yusif* Sai ki Turomin shaidar biya akan wannan number din 08038541511. Sai insaki paid group


*26*

"Kaka malam kalli wani ya doki aunty idanun ta duk sun Kun bura da tayi kuka Kuma nace ta fada min wanene in rama Mata taki ta yi magana"
Cike da yarinta Yana tattabe baki ya karasa maganar

Murmushi kaka malam yayi "yace to Parrott akun gidanmu Mai magana idan ka Fara magana ba comer bare full stop
Ita tace maka wani ya dake ta ne?"
Ya maida kallonshi gareni "ke umayma tsohon banzan Nan sai kanne min ido daya yayi Wai shi d'an duniya"

"Zo Nan zeena inji wa yadakar min Mata kodai bulalar manya taji?"
Ahmad sabida yarinta Bai fahimta ba Amma ni tsaf nasan inda ya dosa zuciya ta namin wani irin suya ga wata qundumemiyar ashariya danake fatan ta fito daga bakina in maka wa wannan tsohon najadun Amma wlh magana taki fita"

Kukan da nake fatan inyi ko ya ragemin zugin zuciya ta shima ya d'auke diff

Muna haka mamana ta fito

Cikin girma mawa taje ta gaida mahaifin ta
Ahmad ya ruga ya rungume ta Yana fada Mata dsame abinda ya fad'awa kaka malam da kallo ta bini sannan ta qaraso wurina

Tace "Baki da lafiya ne?",
Girgiza mata Kai nayi Tana tattaba goshina tace "to me ke damunki?"
Nan ma ba Amsa kallo na takumayi tace "Wai bazaki min magana ba Sai na cicci ubanki anan?"

Kallona na maida direction din da kaka malam yake ina fashewa da kukan da Babu sauti balle Amo
Wayam Babu kowa sai a lokacin naji wani tukukin baqinciki ya taso min na samu kukan da nake neman Yi tundazun ya fito

Ido ta zuba min cikin mamaki tace

"Zeena meye? Bazaki min magana ba?"

Kukan nake sosai ga maganar fa inayi umayma
Wallahi mamana itama sai ta Kama kukan ta rungume ni muna ta yi

_luv u so much my luvely momy_

Salati mukaji a bayan mu hajia ce tace "Kai lafiyar ku? Tunda farar safia kuzo falo kui zaune kuna kuka?"

Mu duka Babu amsa karasowa wurin mu tayi ta ce "hadake bintu sai ki biyewa yarinya kui ta kuka yaushe zaku rungumi kaddara ne Wai? Akan ki a ka fara rashin miji? Ta kalleni tace ko ke Akan ki aka fara rashin mahaifi?"

Cikin hasala take fad"an wanda batasani ba ni wani tsumin tashin hankali take bankado min tuna min da mahaifina da tayi

Na tabbata da Yana rage bazan ga wannan wannan masifar ba badan mutuwa ba da yanzun kaddara bata kawo mu Zama gidan wannan wannan la'anannen ba da yanzun muna gidanmu tare da mahaifinmu kilan ma da yamin aure tuni Amma mutuwa ta yanke wannan zaren kaunar ya tafi ya barmu cikin yan uwanshi da Basu kula hakkin zuminci ba dangin mama da kowa Ke ganin sun mana gata da hallacci shi Kuma jagoran gidan ya tarwatsa min rayuwa ya rushe dukkan burina da Wata sauran fata na a gaba kaicona!
Su duka kuka suke umaima na Kara girmamawa lamarin ubangiji da yanda son zuciya da burin duniya Ke halakar da mutane Ashe Akwai wacce tafita kunsar bakinciki? Me yafi wannan kazantaccen aikin muni?
Babu mai rarrashin wani acikinsu ,
Can zeenah ta tak'aita kukan taci gaba da cewa,



Comment
Share
08038541511
[1/29, 9:36 AM] Zahrahbukar: *KARSHEN DUNIYA*
_kalubalenku Iyaye_


*na*
*Zahrabukar*

*exquisite WRITTERS forum*



*masu himma tuni sun fara subscription kui maza ku hanzarta fa kar ayi baku Tafiyar Mai tsawo ce Akwai rikita rikita da bankade bankade cin amana daukar fansa Mai zafi yaudara zamba cikin aminci kawata matso kusa da yan kudinki kalilan ki kwashi garabasar wannan daddad'an labarin*

Normal group #300
VIP #500
special #600
_duk tsarin da kike bukatarku zaki samu Akwai banbanci yawan posting a kowacce rana akan kowanne tsari_
ki biya yan sulallan ki ta wannan account number din *6035968908 keystone bank umma yusif* Sai ki Turomin shaidar biya akan wannan number din 08038541511. Sai insaki paid group

*2️⃣7️⃣*

"wasa wasa magana taki yuwuwa an rasa dalili kaka malam Sai kawo rubutu yake Ana duramin na rame na lalace Haka mamana tashin hankali bai sa natuna cewar Wata uku rabona da period ba Sai da na fara laulayi laulayi na gasken gasken hankula suka tashi aka kwashemin zuwa asibity awon farko yanuna ina da ciki umaima ranar naga masifa da bala'i tun a asibityn Abba kabir Kanen umma yafara duka na Hajia na tayashi hankula sukayo kanmu ina kallo su bayan an kwacen a hannunsu suka ja motar suka tafi suka barni"

Na Dade agun ina jinjina wannan lamari dama banyi mamakin cikin ba Tunda nasan ta inda aka sameshi mamakin yanda lokaci daya jarabawo wi masu wuyar ci keta jerin gwanon kunno wa rayuwata Haka na tashi na nufi hanyar gidan zuciyata namin zafi
Inajin jiri ga rashin sanin me zan tarar na karaso

Kwata kwata mani kaina a kulle yake nakasa yin wani tunanin .meye mafita a gareni.

Haka dai jiki a sabule na tura kqaramar kofar gidan na shiga"

Direct babban falon na wuce inda acan nake jiyo hayaniya da sheshshekar kuka'
Zuciya ta naji ta fara dake min Naji na shirya karbar duk wani abinda zai biyo Baya kamar sukar mashi Naji wani Abu yabi ta kunne na nauyin day baki na yayi Naji Babu na jaraba yin magana da kaina Naji inaji kuma maganar ta Fito abin murna ne wannan tsawon lokaci magana ta dauke min Kwatsam Kuma ta dawo a lokacin da bazata amfane ni ba

na zura qafana bakina had'e da sallama

Duka mutanen falon suka zuro min ido ban iya d'aga kaina na dubesu ba zan Kuma d'aga kafa kenan
tsawar abba rabiu ta dakatar Dani yace "dakata daga Nan fandararriya kada ki kuma kokarin tako kafarki a cikin falon Nan"

Cakk na tsaya kaina a qasa nakasa d'ago kai ban ankara ba naji wasu tagwayen maruka
Mama na ce kuka take sosai ta kasa furta wata kalma duka na take aka rasa mai hana ta Har ta gaji ban motsa ba Sai huci take ta dafe kirjinta bansan me suka gaya mata ba Amma nasan bazai wuce zancen cikin na. Ta dafe kirjinta Tana ambaton sunan Allah

Can taja wata gajeriyar ajiyar zuciya ta hadi'iyi wani abu
Qutt take ta fad'i agun"

Tana zuwa Nan kukan ta ya tsanan ta tace
"Umayma ranar naga bala'I tsantsa har kullum Ina bawa kaina cewa nice silar mutuwar mamana"

"Faduwar Nan da tayi ashe zuciya ce ta hadiya da sauri akazo kanta mamana ce fa amma kowa tureni yake a kanta
Yan uwan ta sukai dafifi a kanta
Aka duba aka tabbatar rai yayi halinsa"

Wallahi inajin ana cewa innalillahy wa Inna ilayhirraji un" bintu rai yayi halinsa
Wlh bansan sanda na fasa wata qara na fad'i agun ba dama
A ranar bakina ya bude"
Suma nayi umayma amma rashin imani tsantsa aka nuna min haka aka tsallake ni akaiwa maman sutura aka kaita makwancinta

Ina a halin suma sai da aka dawo daga janaza sannan aka kwara min wasu ruwa masu azabar sanyi,

Kamar ba Yan uwana
Ba haka na farfado
Babu tsoron Allah ba komai ga yan gaisuwa akai ta yayatani cewa na kashe mamana sabida nayi cikin shege ta hadiyi zuciya ta mutu Ina kuka ina su tsaya in musu bayani Basu saurareni ba' suka tarka Tani nida kayana suka wullo ni waje"

*Bazan bata musu sunan zuria ba inje duk inda zani abinda ya had"a ya raba"*

Kalmomin Nan har gobe suna amsa kuwwa a kunne na kinsan wake fad'ar hakan?"

Umayma ta girgiza

Please Login or Register in order to submit comment