Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*ZAƁINSHI NE..!*

🪂🪂🪂🪂🪂🪂

_Zainab Habib(Mom Islam_




*Bismillahair rahmanir rahim*

*_Ina miƙa godiyata ga Allah daya bani iko dakuma aron rai ,na sake rubota wanan littafin mai suna a sama ,ina roƙon Allah ya baki ikon kammalashi lafiya  amin_*




______________________💕

1-2

Gida ne madai-daici wanda ya kasance mai ɗakuna biyu , ɗaya na mama ɗaya kuma namu nida yayana haidar , gefe kuma kicin ne sai bayin mu dake can hanyar fita waje .
Zaune nake a kan kujera ƴar tsugunno fuskata tasha hoda kasancewar bana rabo da kwalliya koda wane lokaci, mama dake zaune kan tabarma ta kalleni tare da cewa "Umaimah kitashi ki zuba shinkafar a kula mana kina ganin har ƙarfe goma da rabi 10:30am "miƙewa Umaimah tayi tana ɗan turo baki kana tace "mama gobe zan huta "mama ta harari Umaimah dak kwashe shinkafa da ludayi tana sawa a babbar kula , bayan ta gama sawa ta kawo murfin kular ta rufe , tare da gyara mayafin dake rataye a kafaɗarta tace "mama har yanzu almajirin bai zo ba "mama na shirin magana almajiri ya shigo ya gaishe su ya ɗauki kular mama tayi musu Allah ya bada sa'a ,Umaimah ta ɗauki bokiti mai ɗauke da robobi da baƙaƙen leda da cokula a ciki suka fita , sunyi tafiy mai nisa kana suka iso gidan mai , inda ƴan mata ke zaune ko wacce da abin siyarwa a gabanta , Umaimah na zuwa samari suka fara tasowa kowa na cewa "zai siya ,bayan ta zuzzuba musu ta hau wanke robobin da wasu suka gama ci , cikin ikon Allah abinci ya ƙare har ana nema "ƴan matan dake kusa da ita sukace "Umaimah ki jiramu mu tafi tare "Umaimah tace "wlh baba na ganin na daɗe zai biyo sahu na, kuyi haƙuri sai anjimanku " taɓe baki sukayi ,Umaimah ta ɗibi kularta da bokiti tayi gaba , tana cikin tafiya taji kamar ana binta , da ta tsaya sai taji an tsaya ,cikin mamaki taci gaba da tafiya ,tana zuwa wani lungu da ba kowa ke binsa ba taji ana cewa "maza ku toshe tacan ni zanbi tanan "juyawar da zatayi taga samari ne su biyu ƴan shaye-shaye , cikin tsoro ta wurgar da kular da bokitin kafin ɗayan ya zagaya ta falle da gudu , tana gudu suna binta sai da suka ga sun iso gurin mutane sanan suka koma ɗayan yace "idan kere na yawo zabo na yawo wata rana zasu haɗu ,Allah ya kaimu gobe wlhi ko ban tareta a lungu ba sai na mammatse na shannunta "ɗayan dake layi kamar zai faɗi yace "ai kai ka kira da sauƙi baabaa ni inhar Allah ya haɗani da ita wlh sai na yi mata zigidir "suka sheƙe da dariya .
Tsabar gudu Umaimah kamar zata kifa har wani duhu take gani ,tana zuwa dai-dai gurin wani mai shago ta faɗi tana mai sakin kuka sbda jiri days ɗauketa ,mai shago ya fito yana salati ya duba fuskarta yace "ai Umaimah ce "sai kuma yayi bismilah ya ɗagata yana ce mata sannu "dafe kai Umaimah tayi ta kalli kuɗin dake damƙe a hannunta ta kalli mai shago tace "nagode "murmishi mai shagon yayi mata kana yace "yau babu abinci ne ?"Umaimah tace "eh "tare da cigaba da tafiya , tana tafe tana saƙa da warwara a zuciyarta har ta iso zauren gidansu , tsayawa tayi tana nazarin me zatace wa mama idan ta shiga , Yaya Haidar ya shigo da sallamarsa , ganinta tsaye a zaure ya sashi cewa "Umai ya akayi ?"Umaimah ta shagwaɓe fuska kana tace "yaya an sace kayan abincin "dariya yayi mata kana yace "idan bakison talla sai ki ɓoye kayan abinci yau kuma da wanan salon kikazo ? Umaimah tace "wllahi yaya babu kular wallahhi wasu ne suka tareni ƴan iska shine nabar kular na gudo "mama dake  zaune tana haɗa miyar dare ta fara magana cikin ɗaga murya tace "wlhi Umaimah idan bakije kin ɗaukomin kayan ba Allah ranki zai ɓaci "yaya Haidar yace "Umai muje ki ɗauko inyaso gobe ki huta da tallan "mama dake tsaye tana kallonsu  tace "Aliyu kana ɗaure mata gindin zama ko ?"kana sane mahaifinku ba kuɗin cefane yake bamu ba "cikin ƙosawa Umaimah tace "yaya Haidar mu tafi ", da fitarsu suka miƙi hanyar da zata sadasu da gurin da samarin nan suka tareta , koda suka kusa gurin yaya Haidar ya shige gaba ita kuma ta koma bayansa , tun da su Umaimah suka taho samarin ke hankalce dasu ,sai da suka zo dai-dai lungun  yaya Haidar na shirin shiga yaji an rufe masa fuska ana tafiya dashi , Umaimah dake ihu tace "na shiga uku na lalace zasu kashemin yayana "samarin na ɗazu sukace "babu kisa ki bari mu kwashi kayan daɗi zamu dawo miki dashi "gaban Umaimah ya bada rasss ta fara waige-waige tana neman agaji ,shirin gudu take amma ina sunfi ƙarfinta ,suka sanyata a tsakiya tare da riƙe hannunta tana yaƙushinsu amma ko a jikinsu , wani ɗaki suka nufa da ita wanda babu kowa a cikinsa , da'alamu ɗakin na kwanan su ne ,su biyun suka rufe ƙofa tare da....!


*Wanan littafin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙi, zaki turo da kuɗinki ta wanan account ɗin 3175689751 👉Zainab Habibu first bank ,screen shot ta wanan number 08141799224, idan kuma kati ne na mtn. ga yadda tsarin yake 👇*

NORMAL #300
VIP 500
SPECIAL 800

Mom Islam
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*ZAƁIN SHI NE..!*

🪂🪂🪂🪂🪂🪂

_Zainab Habib(Mom Islam_








*Bismillahair rahmanir rahim*

*_Ina miƙa godiyata ga Allah daya bani iko dakuma aron rai ,na sake rubota wanan littafin mai suna a sama ,ina roƙon Allah ya baki ikon kammalashi cikin ƙoshin lafiya_*

_NOTE_  *_Bance dole ki karanta min littafi ba ,kuma wlhi duk wacce ta zageni a wanan littafin  bazamu wanye lafiya ba👌duk abinda kuka gani anayi ne shiyasa na rubuto ,ban saki dole ki karanta ba love and romantic ne_*

___________________________💕

Free page 3-4

Matsowa gabanta ɗayan yayi ya fara  cewa "dan kinga kin cika shine kike neman raina mana hankali koh ? to wlh yau ɗinnan zanga wanda zai hanamu jin daɗi dake "suna tsaka da magana Umaimah ta ƙwalara ƙara a tunaninta ko akwai wanda zai zo wuceww ya taimaka mata , sai taji shiru .
Ƙokarin cire belt ɗin wandonsa  ɗayan yayi shi kuma ɗayan ya tsaya a bakin ƙofa , wanda ke tsaye a gurin Umaimah yace "ki gama zagaye zagayenki babu inda zaki "Umaimah ta miƙe jiki na rawa tayi hanyar ƙofa taji gam ta fashe da kuka , mai sauti  .
Cafko mata nono yayi tare da cewa "wayo laushi "ihun data kuma saki ne yasa suka ihun abokin waanda ke gurin Umaimah ,cikin ɗaga murya suka jiyo ihunsa , a lokacin da wanda ya riƙe Umaimah ya buɗe ƙofa wando a sakwar kwace ,lokacin ita kuma ta samu damar gudu idonta na ci gaba da tsiyayar ƙwallah , ɗayan abokin na fita sukaji an rufesu da duka , suna ihu suna cewa "dama Baabaa baka kulle Haidar ɗin ba ?"Haidar dake dukansu yace "wlhi da kunyiwa ƙanwata wani abu da sai na zamo ajalinku "ya juya ya tafi , yana tafe yana tunani , a fili yace "Allah sarki Umai gani nazo taimaka miki ,kin wuce baki lura dani ba .
Umaimah kam gudu takeci sosai dan ko bayanta bata dubawa ,wani azababben horn taji wanda ya karaɗe kunnuwanta ta tsaya cak tare da juyowa "wata mota ta gani sabuwa fil mai numfashi ,sai kuma ta ci gaba da gudunta , jin motar tasha gabanta yasata fashewa da kuka tace "kukuma me kukeso a gurina ?"wani dattijo ne ya fito hannunsa riƙe da key ɗin motarsa a ƙalla zaiyi shekara 58") yace "ƴan mata mai ya sameki tun ɗazu naga kinata gudu ko wani abun kike nema ?"Umaimah da kuka ya kuma ƙwace mata tace "malam dan Allah ka ƙyaleni "taci gaba da maganar tana kuka ,cigaba tayi da gudu har ta iso gidansu ,tana shiga  ta faɗa jikin mama dake zaune ta zuba tagumi Haidar na bata labarin abunda ya faru da ya riga Umaimah zuwa gida kasancewar ba hanya ɗaya sukabi ba "Umaimah tace "mama kinga abin da nake gudu da tallah ko kince dole sai nayi "ɗago kanta mama tayi kana tace "Umaimah  insha Allah bazan ƙara cewa "ki ɗauki tallah ba "cikin tausayawa yaya Haidar yace "mama in Allah ya yarda zan fasa asusuna yau dama nace kuɗin aure nake tarawa yanzu ko na fasa "mama da hawaye ya wanke mata fuska tace "a'a Aliyu bazaka fasa ba ,kaci gaba da tarawa Allah zai kawo mana mafita .
Suna tsaka da magana sukaji sallamar baba hannunsa na riƙe da akwatin gyaran takalmi ya ajiye tare da cewa "wash wlhi na gaji ace tun safe ina yawo iyakacin ɗari da ashirin nayi "babu wanda ya kulashi har sai da yace "ku kuma me ya faru kun wani yi durun-durun sai kace anyi muku mutuwa "yaya Haidar yai ƙarfin halin cewa "baba muna shawarar sana'ar data dace ne "to yayi "baba yace "ya shige ɗaki "ba tare da yaya Haidar ya jira mai mama zata ƙara cewa ba ya miƙe ya nufi ɗakinsu na matasa dake can ƙofar gidansu ya ɗauko jakarsa dake saƙale da ƙaramin ƙwaɗo ya buɗe ya tura hannunsa ƙasan jakar ya ciro asusun ,ya mayar da kwaɗon ya rufe ya fito ya dawo gida .
Da ganinsa da asusun mama tace "Aliyu  ba nace karka fasa ba ?" ba tare daya saurari ƙarashen maganarta ba ya sanya wuƙa ya cicire ƙusoshin asusun ya zazzage kuɗin ,dama baba na leƙe  da wundo yana ganin kuɗaɗe sun zubo ya fito kamar mai jin yunwa yace " wai baku gama abinci bane ?"mama tace "ka bada cefane ne ?"baba bai ce komai ba ya waro ido tare da sanya hannu a baki yace "Gadanga dama kanada kuɗi haka ka barmu cikin talauci ?"ran yaya Haidar ne ya ɓaci yace "nima ba nawa bane na Kamalu ne da muke kwana ɗaki ɗaya yau zai tafi gida yace "in shirya masa "cikin gamsuwa baba yace "to ai na ɗauka naka ne ?"babu wanda ya sake kulashi ,ya kalli Umaimah da har yanzu kuka take yace "ke kuma sangartacciya me akayi miki ?"babu komai Umaimah tace "sbda sunan yana mugun ɓata mata rai ,komawa ɗaki baba yayi ganin ba'a kulasa ba  ya ciro awara a cikin aljihunsa ya fara ci ,yana gama ci ya nannaɗe ledar ya mayar aljihu .
Bayan yaya Haidar ya gama fito da kuɗin duka suka ƙirga dubu ashirin ne dai-dai ,ya ciri dubu uku ya miƙawa mama dubu goma sha bakwai yace "gashi ta saro wani abun "godiya mama tayi masa tare da sa albarka ,Umaimah dake kwance cinyar mama tace "ga ragowar cinikin da nayi "yaya Haidar ya karɓa yace "nawa ne ? Umaimah tace "dubu biyu da ɗari biyar "mama tace "ai dole dasu zamuyi cefanen dare baza'a haɗa da wanan kuɗin ba "yah Haidar yace "daga yau a dinga aikana mama wlhi fitar Umaimah hatsari ce "baba dake ɗaki yace "idan bata fita ba ka gayamin waye zai aureta munafukai kawai "tsit sukayi ,mama tace "ka siyo taliya leda biyu ka siyo manja na ɗari da hamsin da magi na hamsin munada kayan miya da gawayi "ficewa yaya Haidar yayi ya tafi cefane Umainah kuma ta fara haɗa kayan miya .

Fitowa baba yayi hannunsa riƙe da riga da wando masu datti ya miƙawa mama yace "a wanke min su yau "to mama tace "har ya juya tace "kuɗin omo fa ?baba yace "kin ɗauka banji abin da kukeyi bane ?to ki ɗauka a wanan kuɗin "daga haka ya fice .

Haƙuri Umaimah ta shiga bawa mama -mama tayi murmishin yaƙe tace "Umaimah ko kaɗan raina baya ɓaci dane ", bayan yah Haidar ya dawo ya miƙa cefanen Umaimah ta karya taliya tasa kasancewar ta gama haɗa komai , jin ana kiran sallahar magrib  yasa su tashi shi kuma yaya Haidar yaje masallaci , Umaimah na idar da sallah tazo ta ƙara juya taliya sbda da farko ta jujuya ,zuwa wasu mintuna abinci ya dahu aka sauke ,  aka zubawa baba  da yaya Haidar Umaimah ta zuba musu ita da mama takai ɗaki ta ɗora ruwan wanka a gurin ragowar abincin takai kicin.
Bayan sun gama ci anyi isha'i suma sunyi yaya ne ya fara dawowa yana shirin zama baba ya shigo  yana cewa "Umaimah yau me kika dafa  ?"Umaimah tace "taliya "baba yace "a kawo masa nasa ,kwanan silbar da tasa masa ta ɗauko da cokali da ruwa ta miƙa masa ,mama da ta mance da wankin baba ta miƙe tana fita taga yaya Haidar na wankewa "wani sanyi taji a ranta tace "Allah ya baka maiyi maka "ta juya ta koma ciki kar baba ya fahimta ya fara yi mata faɗa .

Washe gari bayan kowa yayi sallah misalin ƙarfe takwas baba ya kira mama dake cikin ɗaki a kwance ya kira Umaimah dake ɗakinta , fitowa mama tayi ta zauna tare da cewa "au na mance bamu gaisa ba "baba yace "dole ki mance tunda kin ɗauki ƴa'ƴanki sun fini "sunkuyar da kai mama tayi batace komai ba , Umaimah ta shigo  da sallama ta gaishe da baba ta gaishe da mama ,ta nemi guri ta zauna ,baba yace "Umaimah dama dalilin kiranki shine ki fito da kiji ayi miki aure tun wuri "mama tace "idan mijin ya fito kanada kuɗin yin kayan ɗaki da abincin da za'aci "yaya Haidar dake shirin shigowa yaji maganar mama yama mance baiyi sallama ba yace "mama ki daina haka komai Allah ne meki duk talaucinmu akwai wanda ya fimu...!

*Wanan littafin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙi, zaki turo da kuɗinki ta wanan account ɗin 3175689751 👉Zainab Habibu first bank ,screen shot ta wanan number 08141799224, idan kuma kati ne na mtn. ga yadda tsarin yake 👇*

NORMAL #300
VIP 500
SPECIAL 800

ƴan Niger suyimin magana inyi musu bayanin yadda zasu turo .


Mom Islam

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*ZAƁIN SHI NE..!*

🪂🪂🪂🪂🪂🪂

_Zainab Habib(Mom Islam_



*Bismillahair rahmanir rahim*

*_Ina miƙa godiyata ga Allah daya bani iko dakuma aron rai ,na sake rubota wanan littafin mai suna a sama ,ina roƙon Allah ya baki ikon kammalashi cikin ƙoshin lafiya_*

_NOTE_  *_Bance dole ki karanta min littafi ba ,kuma wlhi duk wacce ta zageni a wanan littafin  bazamu wanye lafiya ba👌duk abinda kuka gani anayi ne shiyasa na rubuto ,ban saki dole ki karanta ba love and romantic ne_*








Free Page 5-6

Baba yace "gaya mata dai Gadanga "Umaimah dake zaune kanta a ƙasa bata furta ko uffan ba ,har suka gama maganar , baba yace "nidai na gaya miki .

Bayan an ɗora abin karyawa sun karya ,baba ya ciri kayan da aka wanke masa yasa yace "idan na dawo nayi wankan , kallon agogo mama tayi kana tace "babansu ƙarfe sha biyu fa 12:pm har zakayi wanka "baba yace "ke ƙyaleni idan da kuɗi zan samu da nayi amma ko sisi bazan samu ba gara in tafi haka , ya ɗauki akwatin gyaran takalminsa kenan zai fita sukaji yaro yayi sallama , wlkslm sukace tare da fitowa dukkansu , baba ya kalli yaron yace "ya akayi ?"yaro yace "wai ana sallama dakai  ,gaban baba ya bada rass yace "Allah yasa ba wanan mayen mai gidannan bane "yaron yace "wani mutumi ne a galleliyar mota "da sauri baba ya ajiye akwatin tare da cewa "Allah yasa masu raba zakka ne ya fice ,mama da yaya Haidar da Umaimah suka bishi da ido.
Baba na fita ya samu mota ƙatuwa tsaye a bakin ƙofar gidansu ,jiki na rawa gaba na faɗuwa ya ƙarasa gurin motar yace "yallaɓai ance kana sallama dani "murmishi dattijon yayi kana yace "eh wlh baba inba damuwa ayimin izini da'akwai maganar da nakeso muyi "jikin baba na rawa ya leƙa gida ya ƙwalawa Haidar kira yace "maza fito da tabarma "cikin bin umarni yaya Haidar ya fito da tabarma ,baba yace "shimfiɗa a zaure "inda baba yace masa haka yayi bayan ya shimfiɗa ya durƙusa har ƙasa ya gaida mutumin harda cewa "baba ina yini "bayan ya amsa Yaya Haidar yabar gurin , dattijon ya gaishe da baba bayan baba ya amsa dattijon yace "wlhi wata yarinya na gani fara doguwa tana da ɗan jiki ta shigo gidannan "washe baki baba yayi kana yace "Umaimah kenan itace ai "mutumin yayi murmishi wanda ya baiyyana haƙoran makkansa guda biyu farare masu kyau , yace "ni sunana Alhaji Naira "kafin mitumin yakai ga ƙara magana baba yace "kana nufin kaine wanda ake nunowa a T V wanda yakeda gidaje dubu a cikin garin Jos "gyaɗa kai mutumin yayi alamun eh shine , baba yace "ikon Allah ashe zamu haɗu "mutumin yace "dan Allah baba idan ƴarka ce ina roƙon arziƙi da alfarma inasonta wlhi tun ranar dana ɗora idanuna a kanta na kasa kwanciyar hankali "washe baki baba yayi kana yace "ai ka kwantar da hankalinka naji labarin halin kirki irin naka mai zai hana in baka ɗiyata ,ai ka can canci a haɗa zuri'a dakai "godiya Alhaji Naira yayi kana ya miƙe yace "ni zan koma baba "baba dake jira a miƙo masa yace "Allah ya ƙara girma ,Alhaji Naira ya ciro rafar ƴan dubu ɗaya guda biyu ya miƙawa baba tare da cewa "zamu dawo da magabata na amma dan Allah ina son magana da ita Umaimahar "to..to...to baba yace "tare da godiya ya juyo takalmansa silifas yasa ya shige gida shi kuma Alhaji ya koma mota .
Baba na shiga ya zauna a tsakar gida yace "kowa ya fito "mama da Yah Haidar da Umaimah duk suka fito ,baba ya fito da kuɗin rafa ɗaya yace "kunga arziƙi har gida ashe ma mijin naki yana tafe nake ta yi miki magana ƴar lele ,yau shinkafa da miya da nama za'ayi dan ya jiƙani da nera "Umaimah da mama da yh Haidar da basu gane maganar tasa ba cikin haɗe murya sukace "baba me kake nufi ?"yace "kafin in fara magana Umaimah jeki waje ana sallama dake "Umaimah na turo baki tace "baba waye ?"baba daya zuciya yace "ubanki ne maza ki fita karya gaji da tsayuwa ki jaza  mana fitinar talauci "badan taso ba yaya Haida yayi mata magana da ido akan ta tashi ta fita , ɗaki taje ta ɗauko mayafinta ta yafa ta fice , tana fita taga mota irin ta jiya ,har zata wuce taji ance Umaimah yaki "da sauri ta juyo a zuciyarta tana cewa "mezan maka ?"zo mana Umaimah "Alhaji Naira yace "da sigar rarrashi , baba daya leƙo yace "tun daga gida nakeji ana kizo Umaimah kin fiya taurin kai au bazakije ba ?"Alhaji Naira dake murmishi yace "baba karka damu wlh , Umaimah yanzu kam ta gane me baba yake nufi amma ko babu komai zataje taji dame yazo "motar ya buɗe mata gidan gaba ,ta shige tare dayin bismillah  , zama tayi tare da gaishesa ya amsa yace "Umaimah tun jiya dana sanyaki a idona na kasa bacci wlh koda ƙwaƙƙwaran abinci na kasa ci "uhm "Umaimah tace "tare da taɓe baki tace "ai kai sa'an babana ne aure bazai yiwu dani dakai ba "dariya Alhaji Naira yayi kana yace "insha Allah aure ma ya yiwu ya zaki dinga cewa "haka ?"Umaimah ta murguɗa masa baki kana tace "bana sonka "Alhji Naira yace "a sannu zaki soni kuma in koya miki sona "ficewa tayi daga motar ta barshi yana murmishi.

Washe gari da yamma Alhj Naira ya turo waliyansa ,bayan anyi magana baba shima da nasa waliyan aka yanke kuɗin aure dubu ɗari biyu ,a take a gurin iyayen Alhaji Naira suka biya kuɗin , kasancewar a zaure akayi komai yasa baba cewa "to Allah ya saɓar mana da mafi alkairi suka buƙaci sa rana ,wani ɗan uwan baba yace "kamar zuwa yaushe kuke ganin asa ranan yayi ?"da aka kira Alhaji Naira yace "wata sati biyu "kaf cikinsu babu wanda ya musa ,kunsan ance wai idan da kuɗinka kaine alhaji koda bakaje makka ba "bayan an gama komai sukayiwa baba sallama suka wuce ,baba ya kalli ƴan uwansa biyu dake gefensa yace "yanzu wanne abu kuke ganin za'ayi ?"yayan baba yace "kamata yayi a fara bawa masu aikin gado kuɗi su fara da kujeru "baba yace "eh naji bayan nan fa ?"ƙanin baba yace "ka ɗibarwa mahaifiyarta wani abun sbda hidimar biki "sai da suka gama kawo shawar warinsu baba yace "ƙwaƙwalwarku bata ja wlhi ,bazan fara bada aikin komai ba ,sbda ina sa ran Alhaji zai iya cewa mubar kayan ɗaki zaiyi "cikin mamaki ƴan uwan baba suka jinjina kai kowa na saƙa a zuciyarsa .

Zuwa dare baba yazo wa dasu mama kuɗi da kuma maganar sa rana ran mama ya ɓaci sosai a ganinta itama tana da haƙƙi akan maganar amma yakeyi iya ƴan uwansa.
Yaya Haidar dake zaune ya kalli baba daya mimiƙe ƙafa yasa kuɗi a gaba yace "yanzu wanan kuɗi da kuke gani zan ɗauki dubu hamsin ana bina bashi kuma munsa biki sati biyu "da sauri mama tace "haba babansu meyasa kake mana haka wlhi wanan ba adalci bane ,ka tambayi ita yarinyar kaji tana sonsa ?cikin faɗa baba yace "dama ke kike hanata aure wlhi da kin barta da tuni tana da budurwar ƴa dan Umaimah yanzu zatayi shekara 20 ashirin , wanan maganar ta yiwa mama ciwo sosai yah Haidar ko ficewa yayi dan bazai iya jurarar wanan abin da babasu yake yiwa mama ba ,  Umaimah da tun da baba ya fara magana batace komai ba idonta ke fitar da hawaye ta shige cikin ɗakin mama  ta faɗa katifa tana kuka .

Rabon Umaimah da abinci tun na safe shima na safen da a lokacin akace

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment