Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zainab bata yaddaba tadai k'yaleta batace kumiba.




Haka sukayi tafirarsu har magarib sukayi sallah sannan sukayimusu sallam to fah na Fateema tafar rikice musu da k'ir tabarsu suka tafi tafiyar suke da wuya ta fara San arta sai da tayi mai isarta sannan tayi shuru .





Toilet taje ta sakar ma kanta ruwa sannan ta ɗoro Alwala tayi sallah sannan tafara aikin ta na tunani .




Daddy tunda yafita aiki ya hanashi fitowa Yana tason ya dawo Amma Babu hali shi ai bai samu kan saba sai dab da magarib .


Ya fito koda yafito anata kiraye-kirayen sallah masallaci ya wuce bayan ya angama magarib bai fito ba sai da akayi sallahe Isha'i.



Sannan yayo gida Yana shigowa part Ɗinsa ya wuce bayan yayi wanka yana fitowa rik'e da towel yana gogar jikinsa Mummy ta shigo taci kwalliya tayi kyau sosai tak'arasa tana "cewa Alhaji kadawo "yace kinganni sai yanzu. "ta ce Allah tun dazu mu ke ta ji ran dawowar ka.



Tana karb'e towel d'in dake hannusa tana Ƙarasa goge masa jikin sa.


cike da duniyan ci bayan ta kammala ta shafe shi da mayuka masu Ƙamshi ta Ɗauko mishi kaya marasa nauyi .


bayan ya kammala sanya kayan parolurn yaje yazauna ta kawo mi shi abinci ya d'an ci ba sosai ba "yace ya Ƙoshi.



Dan shi ba abincin ke gaban shi ba .


Burinshi yaje ya ganta ko zai samu natsuwa.


Nan Mummy tayi tajansa da fira Amma duk abunda take zuciyar shi naga haskin idaniyarshi .



tana tayi masa fira wata yana fahinta wata ko sai yace eh.


Haka har su ka kai goman dare ba tare da ya samu yagan taba.

Daya ga abun ba mai Ƙarewa bane "yace wai ina yaran nan?".


"Tace tunda akayi sallah suka shege Ɗaku nan su ban kuma Jin motsin suba".

yace "Ok".


"Yace bari na tashi naje naga Ƙanwarki".

Yana faɗin haka sai da gabanta yafad'i amma tada ke tayi mumushi tace "to muje na raka".


Yace "kidai haɗa min ruwan lipton kafin nafito"



Tace "to dan ba haka ta soba".
tace "zan haɗa"

yace "ok" yafice ..





Tunda ta kammala sallah take kan sallaya tayi kuka, tayi tunani har bacci ya ɗauketa a haka.



Daddy ya same ta ya ƙaraso wajan ta a hankali yakai hannun shi yana shafar fuskar ta.


Ji tayi kamar wani abu na shafar fuskar ta da sauri ta buɗe ido .



Suka had'a ido da sauri ta miƙe zaune jikin ta sai rawa yake "tace Daddy ina wuni sai da ya lumshe ido yace "kina lafiya".


tace "lafiya k'alau"





kanta na Ƙasa tashi yayi yazo dab da ita ya zauna yana "cewa "mi kika ci yau?".



yana kallon ta ba tace komai ba tashi yayi yaje wurin Mummy yasa ta haɗa mishi tea ya kawo ma.



ya kawo mata mik'a mata kofin yayi ta karb'a.



Ahakali ta ke sha har ta sha sosai.


Sannan ya zuba mata abinci yace "kici" tace "Daddy na Ƙoshi"



Yace "kici ko kad'an pls" saboda kunyar sa da ta keji a hankali ta soma ci taci ba sosai ba tace "ta Ƙoshi" ruwa ya kawo mata tasha yace ko ke fa.




sunda ɗe bai tashi ba ita ma bata ce komai ba a haka har bacci ya ɗauke ta.




Ya maida ta saman gado ya gyarama ta Kwanciya ya rage mata hasken wuta yajawo mata Ƙofa ya fitowar sa.




Yakoma part Ɗinsa Koda yakoma Mummy tana nan tana jiransa tace "ka dawo?" yace

"eh"




Lafiya take ko yace "eh" Dan Shima bacci yakeji ko lipton bai tsaya shaba ya kwanta bai jima da kwanciya ba bacci ya ɗauke shi......


















Muje zuwa






*Commet*
Nd
*Share*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦




*K'AWAR* *'YATA* *CE*




®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION?*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼







*Story & written*
By
*Sumy*


*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*





*page 6*





Kiran sallar farin Daddy yafarka da addu'a a bakinsa.


Tashi yayi ya shiga toilet ya watsa ruwa ya d'uru alwala yafi to



sai da yayi na fila yakai kukan shi wajan ubangiji bayan ya kammala ya tashi Mummy.




Cikin magagin bacci tace "natashi"



Fita yayi yayi part d'inta Koda yaje akan sallaya yagan ta karasowa yayi yace "Ashe kin tashi?"





Tace "eh"

Daddy wucewa yayi masallaci bayan ankamala sallah bai shigo gidaba sai da gari yayi haske .



Yadda yabar Mummy haka yasameta.




Da sauri yak'arasa wajan ta.

Yana cewa" Hajiya baki tashiba? kitashi gari har yayi haske"




Ahankali take b'ud'e idonta ta sauka kan gado part dinta takoma sai da tayi abunda takeyi sannan tayi sallah .





Koda Fateema takamala sallah tayi azkar ta gyara komai na part d'inta tayi wanka tashirya bai laifi tayi kyau kwance take saman kujera tana Tunani umman ta.





Da Baban ta da k'anneta kewar su ,dok, ta addabe ta.




Kuma gashi yanzun ko waya bata da ita bale taji 'yan gidan su.





Jitayi yau tana sun jin muryar Ummn ta taji bazata iya hakura ba tashi tayi waje zata je dakin Zainab.




Steps day ta taka suka hada ido Daddy shima yazo wajanta .





Da sauri ta kuma ta zauna bisa kujerar falon hankali yataku zuwa gareta.




da sauri ta ce Daddy ,"in kwana?" kallon ta yayi yace "lafiya k'alau sannan yakara da cewa "ina zakije kamar ba zatayi magana ba tace "wurin Zainab"




"Yin me i Yana kafeta da ido .



Tace "wayar ta zan karb'o nak'ira Umman ta tana fad'i kamar wadda akayima tilas.





Fita yayi bajima da fitaba yadawo riki da kwalin waya a hannunsa mika mata wayar yayi ta karb'a





Yace akwai slm aciki yakuma yace "Dan Allah Fateema kiyi hakuri kinji wllahi sonki ne ya rufemin ido bana ganin kumai sai ke.






" Dan Allah inason kiba ni had'in Kai muyi Zama na amana wllahi Fateema ba dan naci zarafinki ba na aureki.



" Nasan ni ma laifine gareki Amma "Dan Allah ki yafemin .




Kamar wani karami yaro Daddy dok ya rakicema ta.


Ita abun nashi yanzo har tsoro yake ba tace "Daddy dan Allah kaje kada Mummy tashigo please"



Kamar tayi kuka yace "ko tashigo mizatayi ?

ta "a'a Daddy wllahi kunyar ta nakeji tana mafashewa d kuka,




Yace "naji daina kuka yanzo zan tafi Amma kishirya a kowani lokaci zakimin rakiya bai jira mizatace ba yafice



Da kallo tabishi tana koma Mai Mai tawa rakiya Kuma tanasheri hawaye wai yau daddy ne a ma tsayin mijin ta .


Wayar tadauka ta kunna ta taga akwai slm tunani tayi akwai kude a wayar kowa.



Number daya ce kuma tasan ta Daddy ce.

Ganin tayi k'ila ba kud'i a ciki Kuma gashi tanasu jin Ummanta .




Tashi tayi taje wajan zainab takar b'o wayar dan wannan ba Kati aciki .



Sauka tayi taje dakin Zainab koda tasau ka taga falon dok ayamutse tayi mamaki Amma ita dai yau Ummanta takesun ji shiyasa bata bi takan sa ba.






Ta wuce d'ikin Zainab knocking tayi taji ba'a yi magana ba takoma wani knocking da yake d'a kin su d'aya da anty Nabila.




Afusace tafito tabud'e k'ofa a tunanin ta Zainab ce tana b'ud'ewa zatashi ga da sauri ta tunku d'e ta ba wani shiri tajita k'asa daf .





Da sauri Zainab dake toilet tafito ganin Nabila bakin k'ofa yasa ta k'arasuwa da sauri.



Fateema tagani tana k'ukarin tashi Amma tagaza da hanzar tayo wajan ta tana mik'ar da ita.



Tana cewa "baki ji ciyoba ko? ta ce"eh"



Nabila ta karasu wajan su tana huci da yatsa take nuninta tana cewa "kada ki kuskura ki Kuma d'auku kazamar k'afarki ta ma cuta ki zo dak'in nan .




Wllahi kika K'ara sai kinyi dana sanin.

muna fukar banza muna fukar yaufi.



Mai fuskar muna fakai Ida aka ganta kamar ta Allah.


Kamar haya niya Mummy taji dasauri tafi to tana kallon su bakin k'ofa Amma kumai batace ba.




Asalima dadi taji abin da Nabila ta yi ma Fateema Zainab data ga cin mutuncin bama k'arewa ba ne.






Ta ce "haba anty Nabila Dan Allah kibari kin tureta yanzo da ta jiciyo fa? mizaki ce ?



Nabila tace "Oh har yanzo kinan Baki rabu da itaba Kena Koh?



"Amma anyi asararriya awajin nan dok abunda tamiki bazaki bartaba kenan?"kin fison ta d uwari ki.?


Tana mai janyo Zainab tana Sanya ta ad'aki .




Taci "ke kuma kafin na k'irga uku kin bar wurn nan tana kuka kasa kasa zuciyarta na Kuna tafa ra takawa sannu sannu.







Har zata far hawa steps din farin Mummy tayi sauri tace "amarya mu Fateema yau ya akayi akabar falon kaca kaca haka.




Tsayi tayi bata ce kumai ba Mummy tace "fateema kobakijiba ne.



Dan Mummy nuna tayi kamar bata San miya faro ba .



A hankali tace "yanzo nakesun nayi Mummy" .



Tace to "a yi sauri pls" dan yau muna da baki ta ce "to Mummy.



A haka tafara gyaran gida tanayi ta goge kwalla har ta gyara falon tsaf.



ta San ya turarin hayaki masu kamshi gaske bajimawa gida yadau kamshi .





tana kammalwa kitchen ta wuce ta hada break fast ta jera a dinning sannan ta wuce part dinta .





shigar ta keda wuya tafashi da kuka tana mai tausayi kanta tajima a haka daga baya tashi tayi tayi wanka takwan ta




Wayar da Daddy yakawo ma take ta juyawa tana tunani yazatayi tanasun jin iyayin ta wani hali suke ciki Amma bata samuba tana haka har bacci ya dauke ta.






Daddy baima San wanasn da ake tuyawaba Dan Yana ko mawa part dinshi anty shi tayimishi Kiran gaugawa shiya sa ko breakfast ba tsaya yi ba yafita


Ita ce bata farka ba sai sha biyu saura cikinta yafa suwa alamun yauwa takeji Dan rabunta d abinci tun darin da Daddy ya tsareta sai taci.








da sauri tayi kitchen d'inta ta had'a tea tasha sannan taji dama koshi da k'ir ta iya Sha .






Tana zaune saman kujerar falon kulsum tazo da gudunta tana cewa "anty Fateema dake zaune tace "na am" kulsum .

Ta fada jikin ta tace "anty mummy nakiranki gabanta sai da yafadi acikin ran ta tana ta fadin Allah kasa lafiya.



Tashi tayi suka sauku ita d kulsum tun kafin takarasu suka fara antayama ta hararar datasa hanjin cikin juyawa.







Na take jikin ta yadau rawa haka takarasu wajan su su uku ne zaune cikin shiga ta alfarma kuwace naji d nira da gayo kallo daya zaka musu kaga suna kama da Mummy.




Koba a fad'a ba dagani family d'in Mummy ne.



Hajiya Asma' u data daka mata tsawa bata san lokaci da kuka Mai k'arfi y kub'ucema taba .



Dan ita gaba d'aya tsoron su takeji

jikin ta na karkarwa ta k'arasu gabansu

Dan gaba d'ayan su ba alamun Wasa atari dasu kafin takai wajan su ta dur kusa tafara kuka,


Hajiya karima tace "baki mayi kuka ba wllahi sai nan gaba.






Mutukar kikace Zaki ciga ba da Zama gidannan wllahi ko kukan jini sai kinyi.



Bata ce musu komiba kuka take mai ban tausai sai dayar tace "ina mai baki sha wara tun ba aje ku anaba kibar gidan.




Wllahi ku kiyi Dana sanin zuwaki duniya.



Suna gama fadar haka Nabila tace "kuma kije ki duramuna abinci rana kuma idan kin gama kije d'akina ki gyaramin.




Kuma kije ki gyaramin Wanda anty Mimi zata zauna dan nasan kowa ni lokaci zata zo.




kuma wllahi dok bakiyi min dai dai ba jikin ki zai gayamiki jikin ta nakar karw tatashi ta tafi kitchen tana kuka.




Zainab ko dok tanajinsu Amma Mummy ta hana tace kumai .


Sai dai tashige d'aki tayi ta kuka tana mai tausayi teemar ta .



Haka tawuni aiki ita abba ta samu kanta ba sai daf da magarib Dan Koda tagama aikin d akasata Mummy tace ta "dura na dare .

Daddy kiran Mummy yayi yace mata tafiya takamashi tayi mashi addu 'a tace adawo lfy .

Tana kwance wayar da Daddy yakawo mata ta fara rura tayi mamakin mai kiranta Amma dan tasan bawan da yasan ta da wannan slm .




dauka tayi taga mekiran ta har wayar ta tsinke aka Kuma Kira .



Haka tad'a ka takara a kunninta batayi magana sai da yayi a jiyar zuciya sallama yayi mata sai yanzo tage ne. kowaye .




kenan daddy ne kamar bazata ammasa ba amma ta "amsa yace "kin wuni "lafiya

tace "lafiy kalau


Yaci "kin ga ban dawo ba ko tafiya takamin yanzo Amma kiyi hakuri kwana hudu ne zanyi insha Allah.


Zan dawo aiyi min addu a.



Kamar bazatayi magana ba tace "Allah yaka lafiya yamai daku lafiya.


Wani dadine yaziyarci zuciyarshi Yana Kiran "amen ameen.




yace "kuma dok abuda kikesu kimin magana kuma anty sa' a zatazo kowane lokaci zaki iya ganin ta.





Kinji kiyi hakuri idan nadawo har wajan su Umma zankai ki kinji ko.




Tace "to yace "mikika ci ta ce "abinci yace "nasan bakici komiba.

" Amma Dan Allah ki tausayamin kici ko zan samu sukuni.

Gajiya da wayar tayi tace "to yanzo bari naje na ce.


Yace
" yauwa Bata bari ya koma magana ba ta yanke wayar .




Tunda Daddy yatafi kullum ciki aika ce ai kace take Zainab tayi kuka har tagaji watarana takan fake idon su Mummy taje ta tayata.




Haka taka shanan wuyar aiki har lokacin dawowar Daddy.



Ranar da Daddy zaidawo tun wuri Mummy ta aika a kirata .





*Muje zuwa*



*Commet*
Nd
*Share*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦




*K'AWAR* *'YATA* *CE*




®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION?*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼







*Story & written*
By
*Sumy*



*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*



*Page7*






Tashi tayi dan ta fara aiki tana sau kowa Mmmy itama ta fito.



Gaida Mummy tayi tamsa tana cewa "kinsa yau Alhaji zai dawo dan haka ayi sauri a gyara gida Sannan ashiga kitchen basai nafad'i miki kalar abinci da yake soba kin sani ko?"




Bata ce komai ba sai da Mummy tak'ara cewa "kinyi shuru kamar badake nakiba?"



Tace "eh" nasani"



Mummy wuce war ta tayi batari da tace komai ba.


Tana ganin Mummy ta wuce ta fara tsaf tace gida har zata fara morping taji ana sallama.



Amsawa taiyi tana mai juyuwa dan taga wake sallama.


Marmushi tayi tana mai k'arasuwa gare ta tana cewa

"gwaggo "in kwana?

Bata karb'amata ba tambaya ta jefu mata.

"Waya saki aiki da sassafin nan?"

"Ko masu aiki basa nan"

"Ina mutanin gidan suke?"

,Dok, a jere taje famata su kuma ba wanda ta k'arb'a .

Shuru tayi bata ce komai ba dan bata san mizata ce ba dan tasan halin yayar Daddy akwai iya fitina.



Tana cikin tunani taji tace "Fateema dake na ke fah?"


D'ago kanta tayi a kasa tace "Mummy na d'aki".

Batama bari tak'arasa fad'a ba ta wuce part din Mommy.


Knocking tayi mata Mommy tace "waye?

"Hajiya sa'a ce kisameni falon.


Batsaya jin miza tace ba ta wuce warta.


Inda tabar ta anan tasame ta kallon ta tayi da kulawa tace "kije kishirya fita zamu yanzo .

Tace "to kamar mai koyun tafiya haka takeyin tafiya har taka part dinta.


Hajiya sa'a zaune tayi saman kujera ta d'ura k'afa d'aya kan d'aya tana karka d'awa.


Haka Mummy ta same ta ta k'arasu ta zauna tana mai cewa "Hajiya kece da safen nan?"



Sai data yima ta kallon sama da kasa ta "eh nice"


Tace "wayasa Fateema aiki da safen nan?


"Shin ma ina masu aiki ne? Ko "Ina yaranki?


"Ko kin dauka aiki yakawo ta "eh"

Tace a'a "Hajiya ban sanya ta ba ita ce dai tasanya kanta"


Tace "naji ,dok, da haka akiyaye gaba,




Suna cikin hakaFateema ta k'arasu gabansu

Hajiya sa'a taci "kin fito tace "eh nafi to",

Hajiya sa'a tace ma Mummy "wai Ina yaran nan suke?


Mummy tace "suna d'aki"

Hajiya sa'a tace" kice suna can suna hutu ga baiwa ankawomuku mai yimuku aiki ko?"


Tace" a'a Hajiya

Tace to bari kiji daga yau wallahi kada akasake sata akin in dai ba dan ra'ayi kan ta tayi ba."

Indai ba haka ba ni da kaina zan dau mataki tana mai mikewa tsaye tace "Fateema muje,"


Da ido mummy tabisu zuciyar ta na kuna tana cewa "wannan matar tanasu tazame mata matsala,


Suna fita cikin wata mota suka shiga direban yatada mota suka bar gida.



Inda zai kaisu Hajiya sa'a ta fad'imishi bai zame dasu ko inaba sai wata unguwa gaban wani ma dai_dai cin gida suka tsaya .






Bala laifi shima gidan yana da kyau dan shima ginin zamanine.




Fitowa sukayi cikin mota suka K'ara sa cikin gida da sallamar su .



Suna shiga wasu yan mata su gaishe su kai tsaye Hajiya sa'a falon gidan suka wuce suka zaina,




Wayar ta ta d'auku takira wata number bajima sai ga wata mata tafi to .




Zata Kai sa'a r Hajiya sa'a da fara'ar ta ta k'arasu suka gaisa da Hajiya sa'a .



Nima na gaisheta ta amsa tana fara'a bayan an gama gasawa .





Hajiya sa'a ta gyara Zama tace "inason agyaramin gatan tanuna Fateema ayimata ,dok, abunda akema amare ,



"Sannan inason akoya mata abubu gyaran jikin da yadda akeyin su ke duk abunda kikasan mace zata nema wajan gyaran jikin a koyama shi."


Tace Hajiya kada kidamu idan wannan ne kamar angama kud'i mausu yawa Hajiya sa'a ta bata tace gasu afara dasu.




Har tamik'e tace "Hajiya a kula sosai dan cikin manyan mata za'a kaita dan haka abata huru mai kyau."




Tace "Fateema ni zan wuce i dan inkwana biyu zan dawo kinji kuma ,dok Abu da akace kiyi kiyi kinji kiyi hakura please"


Har zata wuce Fateema tace "Hajiya ta juyu tace 'Fateema ko kinasu wani abu ne?"


Kanta tad'aga mata
Tace "to miye?"

Tace "inasun nayi waya da Umma ta
tace "badamuwa yanzo zan ba direba ya kawo miki tace to."

Tace "Hajiya Ummu zan wuce Amma zan ba direba yakawo mata sakon ta tace to "Hajiya sai kinji mu tace tom nagude sai anjima",



Tana fita mota ta shiga direba yamai data gidan ta taba shi wata leda tace yakoma yakai ma Hajiya Ummu a ba Fateema,





Tunda suka fita Mummy take tunanin akan Hajiya sa'a dake sun kawoma cikas dan haka dole taje suzauna da group7
dan bazata zuba ma Hajiya sa'a ido ba


Tashi tayi taje d'akin su Zainab dan sutashi ak'arasa aiki kafin Daddy ya dawo .






*Muje zuwa*






*Commet*
Nd
*Share*
1/23/20, 11:48 AM - +234 706 211 8047: 💦💦💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
💦💦




*KAWAR* *'YATA* *CE*




®?
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION?*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }


🎐 ```G•W•A```🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼







*Story & written*
By
*Sumy*



*Page 8*




Kai tsaye d'akin su tawuce Koda taje kowace su kwance ta tasame ta Nabila tana rik'e da waya ita kuma Zainab na karatun wani novel,


Mummy magana tayi musu Sannan masuka san ta shigo d'akin,


Tace "kutashi kuje ak'arasa aiki kunsan yau ne Daddy ku zaidawo ko.?"


Zainab tace "da gaskey Mummy?"

Mummy tace "zan miki karya ne?"

Tace "a'ah".

Tace to "kutashi kuyi sauri "

Nabila tace "Mummy Ina ita waccan Fateema komu zamuyi mata aiki ne?"


Mummy tace "hmmm kedai bari yanzo akanta Hajiya sa'a ba abunda bata cemin ba yanzo mahaka ta jeta sunfi ta."


Nabila tace "mekika ce Mummy."


Tace "abunda kunneki yajimiki" .

Nabila tace "Mummy yanzo Ina suka je?"


Tace "nima bansani ba."

Kowanin su kallon Mummy yakeyi ba wanda ya koma cewa komai,


Nabil tace"wai yaushe Hajiyar Mufida tazo Gidan nan"

Mummy tace "da safen nan tazo."

Mummy tace "kutashi lokaci natafiya ba ayi komai ba."


"Suka ce to"

Tashi sukayi ita dai Zainab tunda Mummy ta ke magana bata ce komai ba asalima ita tausayama Fateema takeyi,


Nabila tace "mubari tadawo wallahi ,Dok, bata fad'amuna ida suka jeba sai tayi kuka a gidan nan."


Zainab ita dai fita tayi tafara aiki ita Kuma Nabila sai da tagama cin fitinar ta San nan tafi to ,

Tace wai "yaushe Hafsatu mai aiki zata dawo?"

Mummy "tace satin nan idan suka gama biki zata dawo."

Dan ita Nabila ba gwanar aiki ce ba shiyasa komai bata iyaba Zainab ce keyi ko girki ita ce Amma Nabila shara da wanke_wanke kad'ai takeyi Amma koshi ba koda yaushe ba,


Haka saka cigaba da aiki Mummy ko takoma d'aki tana tunanin mafita,



Sai da Hajiya sa'a ta tafi Hajiya Ummu takai Fateema wani d'aki tace "gashi nan ki zauna kafin mugama aikin."


Tace "to"


Bayan tafita Fateema tabi d'akin da kallo karamin d'akin ne mai had'i da toilet d'auke yake da gado da k'ara mar wardrobe d'akin yayi mata kyau sosai tana cikin haka Hajiya Ummu tazo takawao mata sakon da Hajiya sa'a tabama direba yakawo,


Karb'a tayi sai da tabari Hajiya Ummu ta fice Sannan ta bud'a tana b'ud'ewa waya tagani mai kyau kunnawa tayi ta duba ta ga akwai slm Kuma aikwai kud'i aciki cahji tasanya dan ba cahji aciki sai takira Umma ta,


Tashi tayi tashi ga toilet tayi wanka tana fitowa gyara jikin ta tayi ta kwanta ba ita tashiba sai da akayi sallah azahar tashi tayi tayo alwalla tayi sallah bayan ta kammala ta d'auku wayar ta kunna tasa number Umma ta takira,




Sai da takusa tsinkewa aka d'aka ajiyar zuciya tasaki mai k'arfi shuru tayi batayi magana ba sai data ji ana sallama

Muryar kanen ta taji yana sallam da sauri tace "Nasir Ina Umma?"


Yace "Anty kece ?"

Tace "eh nice"

Yace "ga Umma"

Ta ce "to"


Umma yamik'ama sallama tayi tanajin muryar Umma ta fashe da kuka,


Acan b'agarin Umma shuru tayi sai can tayi k'arafin halin cewa "tunda kuka zakiyi to sai anjima" ai da sauri tace "Dan Allah Umma kada ki tsinke kitsaya tana share hawayin ta.

Umma tace "waye cemiki kuka, na magani da ace kuka na magani kin san da ba ayi auren nan ba, dan haka kisama

Please Login or Register in order to submit comment