Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg1⃣

KATSINA

Duk wanda ya san Jami'ar Umaru Musa Yaradua dake garin Katsina yasan wajen gari take, a k'alla ba a kasara ba tafiyar minti arba'in da biyar (45) ne zuwa cikin gari.
Daliban aji d'aya, na (Department of MicroBiology) ne suka fito a gajiye daga aji misalin karfe shidda da minti biyar (6:05) na yamma kasancewar sunyi lectures 4-6.
Mimi tayi wujiga-wujiga don tsabar gajiya, ta kalli kawayenta biyu tace
"Wayyo Allah! da alamun zamu kwana a Hostel yau, ji yanda garin ya hade rai, ko dai ruwa zaayi?"

Usheey cikin damuwa tace "kai! dole captain ya nema mana sauki gun lecturer nan, a yi rescheduling lectures din, ko wednessdays ne da safe, don bala'i 4-6 ran saturday?"
Dayar me sanye da nikaf tace
"Don Allah ku mu daga kafa, kar su cike bus din, kun dai san mazan nan ba hakuri zasu yi ba, balle yanda suka ga hadarin nan kowa so yake ya tafi gida." Miemee tace "nikam i dont have dat strength."
Usheey tace "aikam tafiyarmu zamu yi mu bar ki, suka cigaba da tafiya.

Mai sanye da nikaf din tace "laahhh! kun gani ko, school bus2 sun tafi." Miemee tace "wallahi kina da damuwa, mu kadai ki ka ga bus din ta bari?"
Mai nikaf din ta dauke kai don tasan da ta sake bude baki tana iya fashewa da kuka. Usheey tace
"Ai ke Mimi ko karfe nawa zamu kai na san ko a jikin ki."

Daga nan ba wacce ta kara magana, ko da suka karasa Student center duhu ya fara yi, kuma matan da ke gurin daidaiku ne, wasu an basu lift. Miemee tace "ko mu zauna a kujerun SUG kafin bus ta dawo?"a Usheey tace "chap sabod gamu gantaIallu ko?"
Dayar tace "to ya zamu yi? ko mu karasa gate kila mu samu ko commercial a chan?"
Mimi tace "chap wallahi bazan iya tafiyar minti ashirin ba."
Usheey tace "toh bari mu barki nan."

Tafiya su ka fara yi miemee tace "bala'i wlh ba za ku barni nan ba, ta bi bayan su da sauri. Tafiya su ke yi suna fira jefi-jefi, dare kam har ya fara yi ga hadari ya kara haduwa, Agogon wayar ta karfe7 saura minti 15, Idon mai nikaf ya ciko da hawaye, tsiraran motoci suke wucewa, miemee tace "wlh a ruwa muke, dama mu samu lift. Usheey tace "eh wlh".

Ba su rufe baki ba sai ga wata bakar mota mai bakin gilashi ta danno a guje, har ta dan gifta su, sai kuma motar ta fara dawo da baya da baya. Miemee tayi saurin gyara zaman rigarta, tace "yauwa ai nasan na annabi ba sa karewa, ga lift nan na zuwa" usheey tace "Barkan mu Allah ya takaita mana wahala ba sai mun je gate ba" me nikaf cike da mamakin kawayenta tace "yanzu motar nan mai tint zaku shiga? Kuna jin sauti na tashi kamar ba dare ba?" Usheey da miemee suka buga tsaki a tare, Usheey tace "kinga dai Besty idan muka bar motar nan ta tafi, ba mu san lokacin tafiyar mu gida ba, daga cikin makaranta ta fito balle mu ce sace mu za ayi, " Miemee cikeda takaici tace "Abu mai sauki, idan ba ta shiga sai mu yi tafiyar mu mu barta nan" kafin tace wani abu motar nan ta iso ta tsaya daidai su.

Ido suka zuba ma bak'in windon motar, a hankali glass din ke sauka, idanuwan 'yan matan nan 3 tsam cikin halittun da ke zaune gaban sits din motar, Su biyu ne, daya na zaune sit din direba, dayan kuma na zaune a kujera me zaman banza, da alamu abokai ne, Mimi da fara'arta tace "sannun ku fa, please, cikin gari kukayi"? Me tuk'in motar ya dan yatsina fuska, a tak'aice yace "Eh" dayan ko kallon su beyi ba, ba tare da bata lokaci ba mimi ta sa hannu ta bude baya, zata shiga kenan me tukin motar yace "ba dai da Ninja din chann za a shigar min mota ba?" Mimi ta kalleshi da mamaki, tace "ninja kuma"? Yace ehmana wanchan me Nikab din, Ushee a hankali tace Seebi daga nikab dinki, wacce aka kira da Seebi ta kalli Ushee cike da takaici tace bazan daga ba, ba zan kuma cire ba, sai a sannan Abokin ya juyo don kallon mai nikab, itama ta dago kai kenan suka hada ido, sun dauki kusan seconds goma suna kallon-kallo, yayi saurin dauke kai, ya maida kallon shi ga Abokin shi, murya kasa-kasa kamar bai son magana"yace Maalesh donAllah mu tafi" wanda aka kira da Maalesh ya kalli miemee yace "Malama kulle min kofa ko?" Miemee za ta yi mar magiya kan yayi hakuri mai nikaf tayi saurin kulle kofar, Maalesh ya ja motar sa a sittin ya bar gurin.

Mimi cike da fada tace "Haba SEEBI menene haka?" kin wargaza mana damar da mu.ka samu na tafia gida, Ushee tace aa fa mimi, shima ya sa wulakanci a alamarin shi, menene abun ce mata Ninja? kuma har sai ta cire nikab zai taimaka ya dauke mu?
Mai nikab din tace "Dama chan basuyi niyyar daukar mu ba". Ushee tace Seebi kin lura da na gaban motar? Side view din shi kadai nagani, amma nagane Azababben guy ne ko kallo fa ba mu ishe shi ba, Uhm kadai Seebi tace a yayin da ta tuno kallon-kallon da suka yi da shi, Miemee cike da masifa tace tunda dai sun tafi ai shikenan, Seebi ta mana Bukulu, kila da ko numbern mu sun amsa, Usheey ta ce ke kuma matsalarki kenan sun amsa number? Harararta mimi tayi Seebi me nikab ta sa daria don ta saba ganin haka gun kawayen ta biyu, yanzu ba wannan ba burin ta a yanzu be wuce ta bude ido ta ganta a gida ba.

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg2⃣

Haka suka cigaba da tafiya har suka fita gate, suka tsallaka titi, a lokacin kuwa dare yayi don bakwai ta gota. Zuciyoyin su ya fara karaya, tsoro da fargaba ya mamaye su, barin ma mai nikab din da ta fara hawaye a cikin nikabin ta.

Sunyi nesa da gate Ushee tace "idan ba so kuke mu karasa cikin Gari a kafa ba ku tsaya mu samu mota ko daga cikin wadannan masu wucewa ne" Miemee please ki taran mana lift, Miemee ta tabe baki, tace "ba zan tsaida ba" donAllah mana miemee inji Mai nikab, in tsaida ki k'i shiga? Da sauri ta zame nikabin fuskarta, tace "kinga na cire gabaki daya" Miemee tayi murmushi tace "eh lallai dagaske kike" ta dan matsa bakin titi ta sa hannu, motoci goma suka wuce da karfi ba tare da sun tsaya ba, Mimi tace ba fa zasu tsaya ba, ni na gaji. Ushee tace "Dont give up" Miemee ta wurga mata harara tace malamai kuzo ku sa hannu kila mu samu wani ya tsaya. Ushee tayi daria ta matso kusa da mimi suka sa hannu.

Daga nesa suka hango wata Jan Mota ya doso da full light dinsa, suka dage wurin daga hannu yanda za a gansu daga nesa, Motar ta cigaba da dosu har ta gifta su, Ushee da karfi tace "kaii yau mun shiga 3" Seebi da ke gefe hawaye kadai ke zuba daga idanuwanta.

Horn suka ji ga baki dayan su ka kallo inda suka ji horn din,Miemee tace "lahh ga wata BMW na na zuwa da baya da baya, mai jan motar nan ne ya dawo, ushee tace muyi sauri mu karasa gunshi kafin ya chanza ra'ayinshi, sauri-sauri suka nufe me motar nan.

Mimi ce gaba suna biye da ita a baya har suka iso inda mutumin yayi parking motarsa, ta window miemee tace Assalamu Alaikum, mutumin ya sauke glass din motar sa, hade da amsa sallamar Mimi, Waiyo Allah! Mimi bude baki tayi tana kallon mai motar, don ya hadu iya haduwa kamar shi yayi kanshi. Ganin kallon da Mimi ke mishi ne ya sa shi cewa "Cikin Gari zaku?" Ushee da ta lura kwatakwata hankalin kawarta mimi be jikinta ya sa ta matso kusa, itama kusan abun da ya faru da Mimi ya kusan faruwa da ita, amma ta dake tace ina wuni? Cikin gari zamuje, donAllah ko zaka rage mana hanya? Yace Bismillah, Ushee tace Mungode, tayi saurin zunguran Mimi, Mimi ta wayance tare da saurin shiga gaban motar, Ushee ta bude baya ta shiga tare da kallon kawarta da ke tsaye waje, tace "Seebi shigo mana" cikin sanyinta ta shigo da Sallama, ya dan waigo ya amsa sallamarta ya dauke kai, bayan ya kwashe takardun da ke bayan sit din.

Gaishe shi sukayi duka ya amsa musu, yace Students ne ku, suka amsa mishi da eh, amma a hostel kuke ko? Ushee tace No day, cike da mamaki yace Day students kuma?ya akayi kukayi dare haka? Mimi cike da yanga ta bashi bayanin dalilin su na yin dare, ya jinjina kai, yace ya kamata a san nayi, in rescheduling lectures din za'ayi tok, idan kuma Buses za a karo don tabbatar da an kai kowa gida, is very risky a bar dalibi mara abun hawa a nan, balle ku mata. Allah shi kyauta suka amsa da Amin. Haka ya cigaba da tukin shi, Ba wanda ya sake magana, ba kajin komai sai karatun Qurani mai Girma kira'ar Sudais.

Dif-dif sukaji, Alamun shigowar waya, mimi ta lek'a wayar kirar Iphone 6s da ke jone jikin radion mota (AUX) taga Meema jikin screen din, Mutumin yace ma mimi dan taimaka ki min swiping, da sauri mimee ta yi yanda yace.

Ba tare da ya kanga wayan a kunnesa ba yace "Hello Assalam Ailaikum" wata Zazzakar murya su Ushee sukaji ta cikin speakers ba cewa "Hello Uncle Zaid kanajina?" Yayi murmushi yace "Ohh Meema, so nawa zan miki maganar amsa sallama? Oh sorry Waalaikum Salam, Uncle Zaid baka iso bane har yanzu? Meema ina cikin katsina, but sai naje masauki, idan na huta zuwa anjima ko da safe sai na zo gidan ko? A shagwabe tace "haba mana Uncle Zaid, You promised to come see us immediately you arrived" Ya sauke ajiyar zuciya, yace "toh bani 30mins zan karaso InshaAllah" tayi dariar murna, yay Uncle Zee Thanks, u d best" yace "erhm, Rafeek na gida?" tace "No be dawo ba ko" ya danyi shiru yace "toh sai na iso" kafin tace wani abu ya latse wayar.

Ushee ta kalli Seebi, sukayi murmushi, matuk'a wanda aka kira da Uncle Zaid ya burgesu, daga jin wanda su kayi waya da ita sun san yar gata ce, don yanda take shagwaba da magana, a hankali ushee ta rada ma Seebi 'kila diyar yayar sa ce' seebi gyada kai tayi.

Zaid ya dago wayarsa, ya dan rage gudu, ya shiga neman layin nephew dinshi, callertune din yazo karshe ba amsa, ya sake redialling, yanzun ma kamar ba za'a dauka ba, a ka dauka ba tare da ance komai ba, Zaid yayi gyaran murya, yace "Rafeek" chan kasa sukaji ance "Barka da yamma" Zaid yace "lafia lao, Kana ina?" kamar bazai tanka ba, yace "Gani nan Maalesh zai saukeni gida" yace"Okay toh, ku je ku min booking Liyafa hotel" Ok kadai yace ya kashe wayar, Zaid ya murmusa a baiyane yace "Rafeek ikon Allah"..

_Bibilicious Biebee_

👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg3⃣

Zaid ya kallo Miemee yace"Ina kukayi?" mimi ta yi far da ido tace"dukkanin mu unguwanni daban muke, ka ajiye mu a National, sai mu hau keke napep" yace "Junction din bus? No, kubari na sauke ko wacce a unguwar su" mimi ta yi murmusi mai sauti tace "ji fa nayi ana jiranka" yace kar ku damu, ya kalli mudubi daidai saitin Seebi, yace Malama wani unguwa kuke? Seebi baki ya fara rawa ta kasa magana, da sauri ushee tace mu muna ta Wurin Gidan Masari, Miemee kuma na GRA wurin motel. Zaid ya jinjina kai yace wace Miemee? Miemee na murmushi tace "nice nan" ya sake kallon madubi yace kece wa? Ushee tace nice Ushee, wannan kuma Seebi, Zaid yayi murmushin da ke kara ma fuskar sa annuri, yace "inyee!, sunan yan gayu ne daku, Miemee, Ushee da Seebi" sukayi daria duka, yace toh bari mu fara sauke Miemee, ku ta unguwarku nayi.

Da taimakon Miemee na nuna mai hanya Zaid ya iso har kofar Gidansu, yayi parking, miemee ta sadakar zaid zai tambayi numbern ta, sai wannan yanga takeyi, amma shiru takeji, a ranta tace kila zai tambayi su Ushee, ta bude murfin kofar tace "Thanks So much Uncle Zaid" ya yi murmushi yace bakomai, ta juya ta kalli kawayenta tace "toh kar dai a manta a fito da wuri gobe don muna da GSP karfe takwas (8:00)" Ushee tace "InshaAllah" Seebi tace "ki gaida Mummy" Miemee tace "Zataji, dayanku ya dawo gaba" Ushee ta bude murfin motar ta koma gaba. Mimi ta daga ma Zaid hannu, Ya ja motar ya bar layin ita kuma ta shige gida.

Shiru ba wanda ke magana, sai da yazo unguwar yace ta wurin ina kuke? Ushee tace "ka ajiye mu a wurin Makarantar Salamah" ba wanda ya sake magana har suka zo daf da makarantar Salamah, yayi parking, Ushee tace mungode sosai, Seebi ta bude murfin motar, tace"Jazakallahu khair" Allah ya biyaka yanda ka taimake mu" da sauri ya waigo don yaji dadin adduar nan, duk da be samu ya ga fuskar yarinyar sosai ba yace "Amin Nagode" Suka rufe kofar ya ja motar sa yayi cikin unguwan, Ushee tace toh Seebi sai da safe, Allah ya kaimu Ushee, ko wa tayi hanyar Gidansu.

Sai da tayi tafia sosai kafin ta iso gida, ta na ture kofar gidan ta ga Nenen ta tsaye, da sauri Nene ta rungumota tare da matse kwalla tace "Nasiba, ina kika tsaya haka? Duk kin tashi hankali na, ince dai lafiya ko?" Nasiba ta kalli kakarta cikin tausayawa, tace "Nene kiyi hakuri, darasi mukayi 4-6, ko da a ka tashi ba mu samu abun hawa da wuri ba, sai da ma mu ka tako har wajen gate kafin muka samu wani bawan Allah ya kawo mu har gidansu ushee" Nene tace bakiji yanda na tada hsnkali na ba, don naga baki taba kai wa haka a makaranta ba, na ci kuka na ni kadai, na fi minti 30 gaban gidan nan, ga shegen unguwar nan, ba wanda zaka aika. Da na hana babanki ya sai man waya, amma saboda irin haka, dole xai siyo min, Seebi tayi daria tace bari na shiga ciki in watsa, ko Laasar banyi ba wlh" Nene tace "yi maza, ga abincin ki chan a madafa" ta amsa tare da shigewa cikin gidan.

Assalam Alaikum yayi sallama a kofar falon gidan, mamimakon a amsa mai, sai jin ihu yayi, yayyy!!! Ga Uncle Zee oyoyo, wasu yanmata biyu suka zo suka rungumeshi, takaici ya cika Zaid, be da yanda zaiyi sai dai k'irk'iro murmushin dole wanda hausawa ke cema Yak'e kafi kuka ciwo, Babbar ta ja hannunshi zuwa dinning area, tace "Uncle Zaid, i know u must be hungry" murmushi yayi yace "Aa meema, ciki na a koshe yake" ta marairaice tace "donAllah kaci, ni da kaina na girka maka, wallahi na dade ina yi, please" Ya mata murmushin da ke kashe ta yace "Meema i'm full wallahi, some other time ko?" be bari tace komai ba ya kalli dayar budurwar yace "Aneesa Yaya na nan? Tace "eh Uncle Zaid yana sama" mikewa yayi ya hau sama.

Ya shiga da parlorn yayan sa da Sallama, Yayan ya amsa mishi cike da farin cikin ganin danuwansa, Barka da Yamma yaya, yayan ya amsa mishi da "Sannu da zuwa Engr. Zaid Ibrahim Lema, Zaid yayi daria, yace ka fara ko yaya? Nan suka fara fira irin ta wa da kani cike da aminci da kaunar juna, suna cikin firan ne Hajia Saude tayi Sallama ta shigo dauke ta tray, tana kwarkwasa kamar wata yarinya, "Ahh! Zaidu, ka iso kenan? Ya amsa mata ba yabo ba fallasa, ta dire tray din gabn mijinta ta na tsiyaya mai ruwan zafin shayi a dan karamin kofi, tace" Kaima a zuba maka Shayin ko Zaid? Ya mike da sauri yace "aa nagode, bari inje masauki nagaji" ya kalli yayanshi yace "Yaya bari na tafi zan shigo da safe in Allah ya yarda", Alhaji Habib Ibrahim Lema yace "Allah shi huta gajia Zaidu".

A parlorn kasa ya iske meema da alamun jiran shi takeyi, tana ganinshi ta nufo shi da sauri, Uncle Zee har ka gama da daddy? Yace eh nagaji ne, zan tafi na kwanta, tace yanzu ba za kaci abun da na girka domin ka ba ko? Yace "sorry Meema" sai da na ci abinci kafin na karaso. Ba haka taso ba sai dai ba yanda zatayi da shi tace "toh munje in raka masaukin naka" yace wa zai dawo dake? Don ni bazan sake fitowa ba sai gobe, ta mai fari da ido tace"ba sai na kwana chan ba" ya zaro ido, yace ke bana son shiririta, ta wayance tace "haba, kasan wasa nakeyi" ya wuceta ta bi bayanshi "mai zan dafa maka da safe?" Yace "Nothing". Ta juyo a fusace tare da fashewa da kuka haye sama..

Daidai haraban gidan mai gadi ya wangale gate, wata bakar mota mai bakin gilashi ta shigo, Uncle Zaid ya tsaya kallon motar har tayi parking, bangaren kujeran direba a ka bude, na cikin ya karaso gun zaid da sauri yace "Uncle Zaid sannu da zuwa, ya Kaduna? Zaid ya amsa cikin sakin fuska lafiya lao Mahmud. Dayan ya fito cikin takun kasaita, kamar be son taka kasa, ya karaso gun da su Zaid ke tsaye, sai da ya zo daf da su, ya tsaya ya cire baki da kyar yace "ka zo lafiya?" Zaid yayi murmushi yace "lafiya kalau Rafeek, ya karatu? Maimakon ya amsa shi, hannu ya sa a aljihu ya zaro makulli ya bashi, yace " room 108, Allah huta gajia" ya maida duban sa ga abokinshi yace "Night Maalesh" ya juya ya bar Zaid da Maalesh a gurin. Zaid yayi murmushi ya tsaida shi ta hanyar kiran sunan shi "Rafeek Lema " Chak ya tsaya.

_Bibilicious biebee_
👧🏽KE ALHERI CE🙇🏼‍♀

NA

BIEBEE ISA

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)

Pg4⃣

Uncle Zaid ya tako har gaban shi ya, yace "kana da matsalan wani abu? Do u need anything?" girgiza kai rafeek yayi, yace No, nothing, Zaid yace "nawa aka kama min daki? Rafeek yace "na riga na bada" kayan abincin ka fada kudi? Rafeek yace "akwai saura" karatu fa? A takiace yace "Lafiya " Zaid yayi daria yace "baka tambayi Mami ba" Rafeek ya dago jajjayen idon sa ya kalli kawun shi, Zaid ya fara daria don ya san ya kure hakurin shi, tunda har ya sa shi magana haka, yace to "ka tafi ko?" kamar jira yake ya fara tafia part dinshi, Zaid ya juya gun maalesh, Mahmud ya abokin na ka? Maalesh yace "Uncle Zaid, akwai improvement, don yanzu yana zuwa lectures, daga chan muke wai yayi lectures 4-6", Zaid ya kalleshi yace "good, kai yaushe kake gama service din? Maalesh yace"karshen wata" Zaid yace yayi "kyau copper, ka kawo min CV dinka kafin na bar katsina" Maalesh yace nagode Uncle Zaid.

Kamar daga sama yaji muryan Rafeek nace wa "erhm, nace ba?" Zaid da Maalesh suka kallo shi, Zaid yace "naam, kace mene?" Rafeek ya danyi guntun tsaki yace " kace ma wannan yarinyar ta daina shiga harkata, ta daina kula ni" tsaf Zaid ya gane yarinyar da ya ke magana, amma sai yace "wace yarinya kenan?" Rafeek ya bata rai yace "Aneesa" Zaid ya dan murmusa, yace "haba Rafeek, ya zaayi ta daina kula ka? Ai ko ba komai zumunci ya hada ku, ba wani abu bane don ta kula ka, besides ai kanwar ka ce, duk da ba a saba ganin fuskar shi da murmushi ba, amma kallo daya zaka mishi yanzu kasan ranshi ya baci, ya daure fuskar nan tamau, zuciyar sa na tafarfa sa, da karfi yace " she's not my Sister, she's Nothing like my sister" Maalesh ya tsorata da yanayin abokin sa, don ya dade be ji ya daga murya haka ba, kuma uncle Zaid ya ke ma ihun nan? Kai Rafeek be cikin hayyacin sa"

Rafeek ya runtse ido gam, Zaid ko sai daga baya yayi da na sanin cewa Aneesa kanwar Rafeek ce, tunda ya ga haka, ya san ran shi ya baci, kwata kwata be son ganin tillon dan yayan shi a damuwa.Rafeek ya bude ido a hankali ya sauke su fes kan Zaid, dan gajeren tsaki yayi yace "I am sorry" Zaid yayi murmushi yace "je ka kwanta Rafeek" Maalesh kai ma ka wuce gida Allah ya bamu Alheri" ya fada motarsa, Maalesh ya shiga motarshi ya tada, a ka bar rafeek tsaye yana kallonsu, maigadi ya bude gate Maalesh ya fara fita, daidai Rafeek uncle Zaid ya tsaya, yayi winning glass ya miko mishi takarddun Kilishi guda 2, yace a hanyar K'ank'ara na siya " Rafeek ya amsa yayi murmushi da gefen bakin sa, Zaid yace "Baka tambayi Ayman
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment