Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace " to wanene?

Yarima yayi shiru

Jin yayi masa shiru yasa yaci gaba da tambayarsa

"Sau nawa kataba Kusantar ta?

Nan ma yayi shiru kansa akasa yahau fidda xufa

Ganin haka sarki yace " tun anan alamu sun nuna cikin kane Dan haka bazaka wulakanta Rayuwar yarinya kaci riba ita ta wulakantaba Dolene ka Aureta....

"bazai yiyuba!

Cewar UMMAH tafada ranta abace

" don ci baya sai D'ana ya Auri KUYANGA gaskiya da sake

Mai marmataba yanunata da yatsa "kishiga taitayinki Fulani idan Dan kine nima nawane nama fiki iko dashi danhaka magana dole abita in anason zaman lfy dani

YARIMA yadukar dakansa yana magana ahankali " Ina Neman Alfarma ayimin rai walh bana sonta akwai wacce nakeso mun mayi alkawarin yin Aure atsakaninmu ayimin kowanne irin hukunci amma banda wannan

Galadima yayi Gyaran murya yace "kwantar da hankalinka Yarima Munanan ma baza.ai hakaba kaidai katsaya da gaskiyarka inhar bakai kayi cikin nan ba Ai jini zai nuna dazarar ta haihu za a auna jininka da abinda ta haifan agani

Galadima yadubi *KUYANGA* duk don yakamata da laifi sbd yana goyon bayan Yarima yace mata

" Ke Wanene shaidarki akan wannan lamari?


Tadago dakai ahankali tana tace "SAHABI shine Shaidata domin shine yadawo dani daga kasar waje

YARIMA yazaro idanu yana mamakin lafazinta wato Ashe SAHABI munafukin Sane?

Galadima yace mata " wanene kuma SAHABI?

Tace "Abokin Yarima tun acan yasan wasu abubuwan

Nan tahau bada labari tiryan tiryan Har takai karshe tana fidda kwalla a idonta

Kowa agun yaji labarin KUYANGA me taba zuciya Wanda masu tausayi agun harda hawayensu irinsu MAMAH da FAATU

Haka LAMIDO yacika da tausayinta zufa taringaa karyo masa agoshi yana gogewa

Sarki yakalli Yarima daya sunkui dakai alamun rashin gaskiya yace masa "Maza kira SAHABI awayarka kasaka handsfree kowa

Jiki asanyaye yakira wayar SAHABI yabarta a bude sunajin tana ring

Saida takusa katsewa kana Sahabin yadaga

Sarkine dakansa yahau masa magana

SAhABI yanutsu awaya jin martabane dakansa

Duk yanda ake ciki dai da mai martaba yazayyane masa kana yakara da koro masa Tambaya

SAHABI yakadu dajin hakan tabbas yasan abin babbane
Nan yagyara zama yafede masa biri hr wutsiya bai rage masa komai ba na abinda yasani duk domin yaga yafutar da *KUYANGA*

Yarima yaita mamakin SAHABI nayanda yake zayyano bayanai

Da sarki yagamaji yaiwa SAHABI godiya yakashe wayar

Ran sarki yagama baci akan musantawar da Yarima keyi

Yarima yahau sose sosen kai jin Sarki yace masa " kaji abinda abokinka yace anyi hakan?

Yagyada kansa

Sarki yace "Kasan da saninka Inta haihu zan daura muku Aure da ita sannan ayanzu Alhakin kulawarta yadawo kanta sbd abinda ke jikinta

YARIMA bai yi maganaba

UMMAH Ranta yabaci sosai da jin sannan hukunci

Take Sarki yasallami kowa aka watse

Kwana biyu da faruwar hakan YARIMA yabar gidan batareda Sanin kowaba ckn dare yagudu ko UMMAH bata saniba

Yahada kayansa yasilale cikin dare yatafi inda yafito

Da labarin yashiga ckn gidan ba karamin tashin hankali mahaifiyarsa tashiga ba Don hartahau zargin waiko Asiri akai masa dahar yabar gida


Abu kamar da wasa saida yakwana hudu labari ya isa fada

Tabbas Sarki ya guntsi bakin ciki awannan ranar yasan Yarima yanason yakun yatashine kawai tun aranar yakara tabbatarwa kansa cewar Yarima bai cancanci yaxama sarki ba

Tuni aka hadu kowa da kowa afadar Sarki domin shi yakira taron

Inda yabayyana musu bakin cikin dayake ciki

Yace da *KUYANGA* dafarko inaso kizama me daukar kaddararki haka Allah yatsara miki naso inga yarima ya aureki domin Asirinki yarufu kedashi dinma

To gashi Allah baiba yanunan ban isaba yawatsan kasa a ido yagudu yabar kasar


Dan haka inaso kikwantar da hankalinki da zarar kinhaihu zan karbi abinda kika Haifa hannu bibbiyu nayi miki Alqawarin baxaku wulakantaba ke dashi Dan haka wanene kike so ackn gidananna fadawa ko ckn BAYI xan muku Aure domin inwanke miki zuciya

*KUYANGA* tayi shiru kanta nakasa

Ayayinda MAHBUB dake ckn mutane nesa da ita yadago dakanta yana kallonta gashi dai har ynzu yana sonta to amma wani Abu ma sukar ransa inya tuna ta yaudareshi duk da azaman farko da akayi babushi ankawo masa Rahoton cewa Ba da saninta komai yawakamaba Yarimane ya cuceta

Yana so yafurta kalma abakinsa ya gagara jiyayi mai martaba yayi masa kwarjini bakinsa yayi masa nauyi

Yaso yafurta shine maaoyinta na asali na gaskiya da akai musu kutse arayuwa aka rushe musu farin ciki

Allah cikin ikonsa MAHBUB saiya kasa magana Allah yanufi LAMIDO Da maganar data furgita kowa harni

Hannu LAMIDON ya daga yana fadin "Ranka ya Dade ka Amince min Na Aureta domin inraya sunnar manzan Allah nakuma shiryi taimaka mata kota halin kaka domin naji zuciyata ta kwanta da ita....

Kallon kallo UMMAH suka hauyi da Jakadiya hakama MAMAH takalli FAATU yayinda FAATUN takalli Mai martaba domin jiran Abinda zai yanke akai....



To muma fans da writers sai mubi layi afada domin jiran tacewar Sarki Abdallah


πŸ™‡πŸ™‡πŸΌβ€β™€πŸ§–πŸΌβ€β™‚πŸ‘©β€β€β€πŸ’‹β€πŸ‘©πŸ‘¨β€πŸ‘¨β€πŸ‘¦β€πŸ‘¦πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘¦πŸ‘©β€πŸ‘§

Muje zuwa
[8/1, 3:17 PM] Ummi Tandama: πŸ“Ώ *KUYANGA...* πŸ“Ώ




*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*Nabilancy Luv* πŸ’˜
(Auntyn S&S)



60-65



AFIRGICE *KUYANGA* ta dago dakanta takai kallonta ga LAMIDO daya furta wannan kalami wanda azatonto ko karya kunnenta yajiye mata saitaga da gasken ne jin Abinda Mai martaba yace

"LAMIDO da gaske zaka Aureta? Har zuciyarka ka Amince?

LAMIDO da fuskarsa ke cike da Murmushi da Annuri yace "Na Amince har ckn raina babu wasa ko yaudara zan Auri *KUYANGA ZEENATU* ko domin inga asirin gidannam bai buduba kuma don itama inrufa mata Asirin Amma inhar kaida mahaifiyata kun Amince

Mai martaba yayi murmushi yace "Nidai na amince nakuma yi farin ciki kafitarni kunya domin banzamo me kyamatar talaka ba ko bawa na duk daya muke mu dasu gun ubangiji Saidai ko mahaifiyarka xamuso muji ta bakinta domin bata hakkinta.

FAATU tayi murmushi tace "Tunda har ka amince TAKAWA ainima dole in amince akullum Allah nakewa Godiya akan yanda mukai dace da samun D'a nagari wanda akullum burinsa shine yaga ya kyautata mana ya kuma bi sahun masu bin tafarkin ubangiji burinsa akullum yasami lada arayuwarsa kaga dole muzamo masu bashi goyon baya Allah yasa hakan yazamo Alkairi arayuwarsa

*"AMINNNN*"

Kaf Al,ummar gurin suka furta banda mutum biyu

MAHBUB da xcyrsa ta cika da kishi

Da kuma UMMAH da hakan bai mata dadiba

Mai martaba yadubi *KUYANGA* yace mata "Dazarar kin haihu za,a daura muku Aure da LAMIDO kigodewa Allah sannan duk abinda kika haifa mace ko namiji zamu karba da hannu bibbiyu Zansoshi kamar yadda nake son iyalaina tunda jinina ne za.a bashi kulawa sosai bakuma nafatan yataso cikin tsangwama ko bayan raina dan hakan ki Kizama me mika lamuranki ga Allah

*KUYANGA* Ta ckn ladabi ta Amsa tana godiya

Sarki yadubi LAMIDO yace "Asakamakon Wannan farantawar da kaimin ina me yi maka Albishir da cewa kaine zaka haye kan karagar Sarauta idan nayi murabus nan ba da dadewa ba Halayanka sunnuna kaine zaka iya rike masarautar nan ko bayan raina kacancnta babu haufi kaine adalin Mutumin da akullum ake nunamin amafarki wanda zai zamo sarkin garinnan Kadauko halayen kwarai na iyaye da kakanninmu kwarai ina godiya da Allah daya bani kai amatsayin D'a

Yadubi Tarin jama.ar da suka cika fadar maza da mata na gidan yaci gaba dacewa "Inaso kusheda daga yau LAMIDO Shine wanda zaizama jagoranku nan bada dadewa ba LAMIDO shine xai xama sarkin gobe da yardar Allah.

Take Gurin yahautsine da sowa da murna fadawa Suka hau Kabbara

Bayi mata tsoffin da manyan suka gau guda

Yayinda MAMAH ta rafka guda tareda cewa sarki "TAKAWA Allah Yaja da ranka muna taya LAMIDO murna kuma muna tayashi yin Godiya da wannan kyauta

Maimartaba yagyada kai yana murmushi

Dayake anyi tsit ana sauraren maganr MAMAH

Saijin kukan UMMAH Akayi ta dora hannu aka tana fadin "Shikenan burinku yacika kun raba D'ana da gidan ubansa kunyi kutunguilar da D'anku zai zama sarki kuma walh baku isaba

Sarki yadaka mata tsawa

Amaimakon tayi shiru saita mike tana fadin "walh baza,a dakeni ahanani kukaba. Tafuce fuuu tana kukan bakin ciki


LAMIDON da kansa yanuna godiyarsa ga sarki

Maimartaba yahau shafa kan LAMIDON yana fadin "Kacancnci hakan LAMIDO fatana harkullum Abinda kayi min na Farantawa to ubangiji Allah yafaranta maka kaima

LAMIDO ya amsa da "Amin, Aminn


Saida Sarki yabada umarnin tafiya sannan kowa yatashi yayi nasa guri


Jakadiya har sashin FAATU tabisu tana Rangada guda

Tareda fara yi masa kirari na sarakai

Saida tafaranta musu rai
Da kalamanta garesu masu dadin saurare sannan tafuta


Jakadiya
Tana barin Bangaren FAATU ta wuce sashin UMMAH Domin tayata Jimami da Alhini tunda tafi kowa sanin yanda UMMAH take da burin taga Yariman yazamo sarki

Ta tarar UMMAH tana waya da Yarima tana bashi labarin komai daya faru sannan Tabashi ixinin akan yadawo Gida maza maza akwai abinda take shirya masa akai


Yarima ya amsa da to zaidawo nanda kwana uku ko
biyu

Kai UMMAH ta hada da guiwa tareda dayin shiru na minti Talatin

Jakadiya na gefe taa jiran tafara kawo gulma da soki burutsin karya Data saba donta sami fada agun Fulanin

UMMAH tadago takalleta tace mata

"Jakadiya jeki kya dawo anjima ayanzu baxan iya maganaba ina ckn wani hali banda lokacin zanta wata magana kibari nahutawa bakin cikin dana dauko afada

Sum sum jakadiya ta tashi tafuce guiwa asage


Itako *KUYANGA* Kwana tayi ba ci basha Sai dakyar Akwana na biyu da Yin abun sannan Zulaihat data matsa mata taci abinci kadan duk tasaka damuwa ackn ranta

Zulaihat tace mata "walh kigodewa Allah ma ayanzu ji nake dama nice ke kuma nasan bani kadai ke wannan tunanin ackn bayin gidan nanba domin kin xama "yar baiwa tunda gashi Allah yakusa "yantaki

Zaki zamo matar sarki Surukar Sarki.……

"Uwar Shege ko Shegiya kuma ba.

Cewar Zeenatun tana matsar kwallah

Zulaihat tace "kibar fadin hakan domin inma shegene ko shegiya duk kafin yafito duniya ne ko tafito duniya domin Kinji ta bakin Sarki yakarba kuma za,a bashi kulawa zai zamo tamkar d'a ko "ya me "yanci to balle LAMIDO natare dake kinyi matsayin da bakowacce zata iya takashiba ackn mu *KUYANGIN* Gidan kema kinsan hakan

Zeenatu tace "hhhmmm ke kike ta wannan tunanin ni tunani na yatafi ga masoyina MAHBUN tausayinsa nakeji yanzu shikenan ……

Zulaihat ta daga mata hannu "saurara niarki dameni da xancensa domin banga yayi hobbasa yanuna soyayyar da yake mikiba agun dan da,a ce sonda yake miki har zucine da kafin LAMIDO yace wani abu akai tuni shizaice

Dan Allah kicireshi aranki tunda yanzu bake kadai bace ba,bafa ason me ciki da shiga damuwa balle kuma abinda zaki haifa me matsayine agidan

Zeeatu tace "Zulaihat da alama bakisan radadin soyayya a zuciba Ni LAMIDO baya gabana Mulkin gidannan baya gabana ko arzikinsu kawai Matsayina nake tunawa ayanzu


Zulaihat tace "ke nifa Allah nagodewa da bai nufi MAHBUB da magana akan kiba agun natabbata da tuni LAMIDO baice komai b.……

Sallamar Wata yar matashiyar yarinya ce cikin bayi tashigo dakin nasu takatseta tashigo musu da ladabi tagaidasu

Zulaihat tace "Laminde ya akai akwai wani abune?

Laminde tace "Ustaz ne yace Zeenatu taje yana waje.

Da sauri Zeenatun tace mata "kije maza kice masa ina zuwa

Ta xira hijab tabi bayan Laminde data futa da mintina uku

Yau ya canxa gurin tsayuwa can gefen hanya yaja tunga yatsaya yana jiranta

Tun daga nesa yakura mata idanu yana kallonta tayi haske fuskarta taxamo yar kuyas tayi kyau saidaita rame

Takasara gareshi da sallama tagaidashi

Ya amsa yana kallon yana fadin "ZEENAH ina sonki amma dole inbarki, yanzu kinmin nisa kinfi karfina.……

takatseshi dacewa "kadaina fadin haka komai nufin Allah ne matar mutum kabarinsa saikaga muna tamune Allah na nasa zai iya kuma canza lamarin aduk sanda yaso bamu zataba kaifa malamine kasan hakan kazama me tawakkali mana kana fa da Sani....

Yace "Duk na susuce Zeenatu ayanxune akwanakin nan biyu da faruwar lamarin naji kaunarki ta karu araina tamkar ana kara rura wutarta ma

Kokinsan YARIMA yadawo Gida adaren jiya labarin yakarade gidan nan. Sarki ko kallonsa baiyiba haryanzu yayi fushi dashi kuma duk akan ne "yar baiwa

Duk da gabanta yafadi jin ya ambaci sunan yarima sai bata nunaba a fuska ta dake tareda kawar da maganar ma tace masa

"Ko awane hali nake bazan manta dakaiba bakuma zan daina son kaba kaine kadai wanda naso a afarko da karshe ackn Duniyar nan ……


Adaidai lokacin da *KUYANGA* Ke furtawa MAHBUB wannan daddad'an kalma ar daidai lokacinne Allah yakawo yarima yazo xai girfta ta gun yahangosu yabiyo ta jikin katangar da suke tsaye kunnansa yadebo masa wannan kalami da muryarta yawatso akunnansa

Yaja da sauri yatsaya baya so su ganshi domin dan ita kawai yabiyo ta gurin

Rintse idanunsa yayi wani abu yaji yana masa yawo akirjinsa

Tabbas yau yakara aminta da zargin dayake mata na soyayya da MAHBUB duk da ta taba tabbatar masa amma kalaminta na yau yakara bashi haske

Ya dafe kansa domin Wani hali yashiga Akanta yadawo adalilinta tun daya hada kayansa yabr kasr yakoma turai yakas sakat Allah yajarabceahi da azababbiyar kaunarta dayaji batun da mahaifiyarsa ta gaya masa na LAMIDO zai Aureta bakaramin tashin hankali yashiga ba domin yasan shirinsa yagama baci

Nemanta yakeyi ido arufe ruwa ajallo Donsu keb'e yanuna mata nadamarsa ya amshi cikin nasa domin ta yarda dashi yakuma roki alfarmar tarakashi gun Sarki Ta tayashi neman yafiya
Yasan ita din me hkr ce da biyayya bazaisha wahalar taba

Waishin ma tawace hanyar zaisamu hakan? Anya bai makaro ba kuwa hhhhhh fans kufito ku gaya masa πŸ˜†πŸ˜…πŸ˜‚πŸ€£




Muje zuwa
[8/2, 5:04 PM] Ummi Tandama: πŸ“Ώ *KUYANGA..* πŸ“Ώ




🌈 *KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*
{United We Stand and succeed;Our Ambition is to entertain & motivate the mind of reader's}



*Nabilancy Luv* πŸ’˜
(Auntyn S&S)


*KAFIN AYI NISA KAI TSAYE INA MIKO GAISUWA DA GODIYA GA D'AUKACIN "YAN CIKIN GIDAN NABILA'S ONLY 4 STARS WRITERS MA,ABOTA KARANTA KUYANGA MUSAMMAN MASU COMMENT*





65-70


A SANYAYE Yarima yajuya da baya don gara yakoma kada wani cikinsu yaganshi su rainashi

Yakoma sashen mahaifiyarsa ya tararta tana Safa da marwa atsakar dakinta tana buga hannunta daya cikin daya tana kwafa da alamar har yanzun ranta abace yake tana kuma ckn halin damuwa

Tana ganinsa tahau fadin "Ya Akai yarima kasame tane?


Yazauna akan kushin yana fadin "Bansami ganawa da itaba UMMAH natarta ne da wani Kazamin bawa da take so..,UMMAH Takatse shi da sauri

"Au dama ackn gidan nanma akwai wanda take soyayya dashi ? Ashe haka tazama yarinyar to da alama ma cikin agida tayishi kenan

Yarima yadago da sauri yadubi mahaifiyarsa da jajayen ido yace "A,a UMMAH tunjiya Dana dawo nagaya miki cewar Wannan cikin fa nawa ne kada ki kakabawa wani makaskanci mana jini na karba.... " Dakata!

Ta dakatar dashi da daga murya ranta abace

"Wai bazaka daina kiran cikin jikin *KUYANGA* da sunan mallakin kaba,walh inkai ka karba to ni ban karb'aba domin bazan yarda da shege ace shine jikanaba jikanma ajikin baiwa Allah yakiyaye dama ajikin wata baturiyar ne ko " yar sarauta da sauki

Yarima yace " Amma ai u UMMAH shi .mahaifina
yakarba ballantana ke da kike mace kikafi sona.

Tace "Dan babanka yakarba be dameniba domin yakarbane da wata manufa aransa tunda bayason azageshi bakuma yaso Dan daza,a haifa yatashi yarasa madafa amma nasan ba har zuci yakarba

" kidaina fadar haka UMMAH.

"Saina fada din kaida bakasan inda yake mk ciwo ba baka ma damu da kyautar kujerar sarauta da Aka baiwa LAMIDO ba

Yarima yace "Ni wannan kam baya gabana fatana dai ayanzu *KUYANGA* zeenatu ta Amince da abinda nazo dashi sbd Allah yajabceni da kaunarta UMMAH kitaimaka kiyi wani Abun walh sonta nakeyi sosai har cikin raina

UMMAH ta maka masa wata harara tace "Shima LAMIDOn daya Amsa yana sonta zai Auretan nasan badan Allah yayiba a to.

Yarima ya shiga tunani

Kai Yadafe don kan nasa ke bugawa dolene yasamo mafita akan MAHBUB Domin irin kalamin dayaji tana watsa masa na soyayya tabbas su yake muradin yaji wataran tagaya masa

Toshin ta wace hanyar? Ta Yaya?

Yakasa samo amsar tambayar domin kansa yakulle Dole saiya nutsu

UMMAH bacin ran abinda Yarima yaxo mata dashi baisa tasami nutsuwa ckn rantaba tabbas dolene tasami mafita akai rana zafi inuwa quna knn domin wannan shine ana wata ga wata can Hukuncin da sarki ya yanke nabaiwa LAMIDO sarauta nacinta arai saigashi Yarima yazo mata da wani batu wai yana son *KUYANGA* to tawace hanyar ma zaisameta Alhalin LAMIDO yakarba kowa yashaida hakan lokaci kawai ake jira

Yarima yadago dakansa yaga mahaifiyarsa ta hada kai da guiwa
.yasauko kasa Yakama kafafunta yana fadin

"UMMAH kitaimaka mini kije ga mai martaba kinemamin yafiya sannan kifada masa batuna na karbar cikin *KUYANGA* da zanyi kice nayi nadama sharrin shaidanne inasonta yadaina fushi dani

Wani dunqulelen abune yatsayewa UMMAH a maqoshi na takaici da bakin ciki

Taki jinin jin Kalmar nan dayake furtawa na son *KUYANGA* dayake fada mata yanayi domin ita ji takeyi tana kara tsanarta ma tunda itace tazamo silar rushewar Burinta ayau,tayi nadamar amincewa da tayi tun farko daya yatafi da ita kasar waje tasan da bata yarda sun tafin ba da tuni hakan bata faruba tunda gashi akan Yariman yak'ita yaki cikin ne LAMIDO yashirya manaqisa yakarba don abashi sarauta kuma anbashin kamar yadda sukeso kuma bazata taba bari suji Dadin yin mulkinba indai daranta saita zame musu masifa a ckn gidan

Wannan tunanin tane

UMMAH dai taga Yarima da Gaske yakeyi domin shirin kuka yake mata akan bukatarsa

Dabara ce tafado mata tace masa "kwantar da hankalinka shalele zansan abinyi agun Takawa

Yace " to agun ZEENATUN fa?


Tahade rai

Yamarairaice mata Taga dai da Gaske ne lamarin nasa saitahau tunanin anya kuwa ba Wani abun akaiwa D'an nataba mutumin dayaqi Abu futuk kuma cikin "yan kwanaki saiya haukace akai

Lamarin Allah nefa UMMAH πŸ˜ƒAllah yakara inji fans πŸ˜‚


Takama hannayensa itama ckn marairaita tace masa "YARIMA kai D'ane D'an fari abin so aduk wani gidan sarauta baikamata ka lanjare a son BAIWA ba kafi karfin Auren *KUYANGA* ajinka da kimarka da izzarka na Dan sarki zai ragu inhar ka Auri *KUYANGA* inaso kayi hakuri kabarta ni dakaina zansamo maka ko ackn gidan sarautar mune akwai mata masu kyau adangina mahaifina kafin ya mutu yayi sarki yanzu babban yayana shine sarkin garinmu kasan da haka Babbar masarautace datafi wannan munada mata kyawawa yan boko wayayyu sai wacce kazaba babu me kinka walh kanada cikar da namiji kaidin gwarzone me tattare da mazan taka gaka kyakkyawa kafi LAMIDO kyau da kwarjini Meye naka na damuwa da Baiwa Alhalin kafi karfinta shi din dayace abashi ita ya Aura kabarsu dama da ita yadace

Yarima yakyabe fuska yace " UMMAH bazaki ganebane

Tace "tayakuwa zangane kaki amsar batuna

Dayaga da Gaske takeyi baxata sakkoba saiya rushe mata da kuka yasan lagontane bata son damuwarsa balle ganin hawayensa

Nan take kuwa ta rude tace masa yayi shiru zata duba lamarin yaje zuwa gobe kafin tasan abinyi

Yana Fita ta aika aka nemo mata jakadiya


Jakadiya na zuwa tagurfana gabanta

" gaisuwa nakeyi Uwar dakina barka da warhaka gani ckn ladabi mezan miki ?nasan bukatace babba tasa kk kirani

UMMAH tagyada kai tace "tabbas kuwa jakadiya domin Yarima yaxo min da banzan zance wai yanzu shi *KUYANGA* yakeso kuma ya amince da cikin jikinta nasane

Jakadiya tadafe kirji tace " wannan Abu bai Dadin jiba kamar Wanda akai masa surkulle

UMMAH TACE "Maza kije kishirya kije min gurin GOGAL matsafiya kice inaso acire masa son yarinyar ckn kwana daya

Da sauri jakadiya tace " angama uwar dakina.

UMMAH takawo kudi tabata jakadiya tafuce da sauri

Amma kafin ta tafi gurin matsafiyar tasu dake bayan gari saida tafaki ido tashige Sashin MAMAH Takai musu Gulmar wai ga Yarima can yarikicewa Mahaifiyarsa waishikam yanzun *KUYANGA* Yakeso kuma ya amince cikin jikinta nasane

FAATU DA MAMAH sunyi mamakin wannan Abu sunkuma Daukeshi arainin hankali yariman yazo dashi sunsan kuma TAKAWA bazai daukaba


Yo muma ba dauka zamuyi ba 😑

Muje zuwa
[8/3, 11:13 AM] Ummi Tandama: πŸ“Ώ *KUYANGA* πŸ“Ώ





*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*Nabilancy Luv* πŸ’˜
(Auntyn S&S)




*wannan shafin Sadaukarwace ga Binta kabir Auntyn Yasmin Mrs ibrahim R/k quarters* πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ Kawata inayinki Ina godiya da tayani posting a grps



70-75


JAKADIYA tana isa cikin Dajin tayita shiga cikin Ko tsoro babu atare da ita haka har tazo gindin wani tsauni ta haye daf !daf!!daf!!! Ta nufi wata babbar bishiyar Kuka dake kan katon Dutsen

Tana isa ga bishiyar saita cire takalmanta ta tsaya gaban bishiyar tana fadin "Gafaranku dai manya da kanana na fadar GOGAL ga jaririya tazo tazo Neman taimako da cin Albarkaci ayi min iso gurin Hakima mandiya shugabar matsafa

Wani kuka taji yana tashi na muryoyin yara daga ckn bishiyar taitaji harna tsahon minti talatin can kuma taji shiru sai kuma ga amsa kuwwar Babbar murya tana fadin

" SANNUNKI DA ZUWA HATSABIBIYAR JAKADIYA GAMANDI ME HADA WANDA TASO

Jakadiya ta hadiyi yawu domin kirarin nan bai mataba tasaba yi matashi

,"Barkanki da isowa GOGAL

Cewar Jakadiya

GOGAL da ba,a ganinta saijin muryarta ta jikin bishiyar tace da jakadiya

"NAji zuwanki angayamin tunkina afarkon daji nasan meke tafe Uwar Dakinki ta aikoki akan Acirewa D'anta son da yakewa *KUYANGA* Daga zuciyar sa ko?

Jakadiya tace " E kwarai hakan yake.

Jakadiya taci gaba da cewa "Hakan data tsara nikuma incanza salon abun yazamo amaimakon ancire masa son yarinyar saidai ma akara masa don ya axabtu sosai

Yakasa sakat yashiga damuwa akanta sakamakon yanda yasaka yarinyar adamuwa

Wata bunsurar dariya aka sheke da ita dg jikin bishiyar kukar

Daga can kuma akace da jakadiya " ko baki fadaba hakan za,ayi domin Baxan iya cire wannan soyayyar dake ransaba na duba naga ajiyar Allah ce ban isa in girgizata ba Dan haka zankara da Dora aikinki da kika bukata domin nima ayaune zanrama abinda YARIMA yataba yiwa Jikana yafita rangadi suka hadu ahanya YARIMA yabuge minshi da doki yafadi ko kulaminshi YARIMA baiyiba harya suma agun

Jakadiya tahau gyada kanta

Tana mamakin jin wannan labari na GOGAL duk da tasan zai aikata din

Jakadiya tahau godiya tareda ajiye kudin da uwar dakinta tabata agindin bishiyar ta mike da niyyar tafiya

Sai taji ana mata magana da muryar tsohuwa ta jikin bishiyar

"Kema kibi lamuranki na gidan nan a sannu domin a irin zaqewar da kikeyi wataran zaki girbi kashinki ahannu domin akwai abinda zaki aikata zaija miki babban aiki da kuma danasani HAHAHAHA

Aka rufe da katuwar dariya

Jakadiya na kyarma tace " Ataimaka agayamin ko mene wannan Abu da zaijamin danasani don inkiyaye

Dariyar dai akaci gaba dayi mata babu wani Karin bayani

Tana kallo kudin data ajiye yabace sundauke

Difff! Taji anmata tasan bakuma xasu karace mata kanxil ba shiyasa ta tafi da baya kamar yadda ta saba

*******

Yarima Yana kwance akan makeken Gadonsa yanata juyi yakasa controlling din kansa akan soyayyar *KUYANGA* Da take azabtar dashi arai

Hotonta ke masa gixo alokacin dayake kanta a time din suna Turai

Tabbas Yanda takeda tarin baiwa bazai iya barin taba saiyayi yanda yayi ya mallaketa baxai taba barin LAMIDO ya Aure taba


Can kuma saiya mike da sauri ayau saiya ganta kota halin kakane koda zai karya billensa yashiga ckn gidan bayin bazaiji wani Abu aransaba Sontane yaja


Yazira kaya ajikinsa dama dagashi sai gajeran wando da singilet

Yafito farfajiyar gidan yatsaya yana karewa kowa dake wucewa kallo duk Wanda zai wuce ta kusa dashi saiya kawo masa gaisuwa

Da ka kawai yake amsawa

Sarkin gida ya hango agurin ajiyar dokuna yana baiwa wani farin doki da LAMIDO kefuta dashi abinci

Matsawa yayi kusa da Sarkin gidan tareda kwalla masa kira

Da sauri yabar abinda yakeyi yataho gurin Yariman

Ya mika gaisuwa tareda tsayawa ckn ladabi agefen yarima yanajiran abinda zaice masa


Yarima yace "Sarkin gida Inaso kaje ka kiramin *KUYANGA* Zeenatu

Sarkin gida yace " Tana tareda MAHBUB acan bayan Gamji da suka saba zama

Yarima yadaka masa tsawa yace "To intana tareda wani bazatazo ba ko Yaya?shi wanin yafinine ?mijin tane ko waye dinta?

Sarkin gida yahau fadin " kayi hkr ba nufina kenan ba sanar maka nayi dai bata gida agarceni bari aje can akirata

Yatafi da sauri inda yasan zaisametan

Yarima yahau cizar yatsa jin wai tana can tareda MAHBUB tabbas dole yadau mataki akan

Please Login or Register in order to submit comment