Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Umma ta nufa ta sami Umma na rabon abinci tace "Umma yau Abdull zai zo kuma yace "daga wanan zuwan sai maganar auranmu "cikin farinciki Umma tace "to ki zuba shinkafa da miya ko zai shigo "yamutsa fuska Saudat tayi kana tace "kalan ya raina mana wayo miya babu ko nama a ciki "Umma da abin ya bata mamaki taja baki tayi shiru ba tare da ta ƙara cewa "uffan ba , ƙarfe takwas wayarta ta fara ring , babu ko jan ajin nan ta ɗauka da sauri har hannunta na rawa tace "babyna har ka iso ?"  sai kuma ta fice zuwa ɗakinta.

Mayafi ta ɗauka ta fice da sauri ta nufi ƙofar gida , tana fita ta gansa tsaye a jikin motarsa ,da murmishi ta ƙarasa inda yake shigar da yayi ba ƙaramin kyau tayi masa ba ji take kamar ta rungumesa , murmishi Abdull yayi yana dariya yace "wanan murmishin duk na farincikin ganina ne ?rufe fuska Saudat tayi da mayafinta tace "ba kayimin rowar zuwa ba sai yau "ah-ah Abdull yace "yana dariya kana yace "to yau ba gashi nazo ba " daga nan suka gaisa Abdull yace "ya su Umma ?"Saudat tace "lafiya lau wlh suna gaisheka "bayan sun ɗan taɓa hira Abdull ya buɗe motarsa ya ɗan shiga , fitowa yayi da bandir ɗin ƴan dubu ɗaya guda biyu , (a tunanina kuɗin zasuyi 100k ya miƙa mata , tsalle ne kawai Saudat batayi  ba tsabar daɗi tayi masa godiya tana kashe masa ido , fuskar Abdull ce ta sauya i'zuwa ɓacin rai kasancewar da hasken wutar lantarki yasa  Saudat kallonsa tace "baby lafiya kuwa ?Abdull ne ya kalleta idanunsa sun kaɗa sunyi jajir yace " mu shiga mota akwai maganar da nakesonyi dake "gabanta ne ya bada rass ,a zuciyarta tace "Allah yasa ba wani abun bane ya faru "shiga gaba yayi ita kuma ta shiga baya Abdull ya rufe ƙofar motar kana ya fara tafiya ,sai da suka kai bakin titi kana yayi tsayar da motar yace "SAUDAT !! a inda ya kira sunanta sai da gabanta yayi mumunan faɗuwa tace "na'am "Abdull yace "nasan kina sona so na tsakanj da Allah nima naso ki zamo matar da zan aure sai kuma Allah baiyi ba ,sakamakon zaɓamin ƴar abokin Abbana da akayi ,kuma a halin da ake ciki ma yau saura kwana bakwai biki "tunda ya fara magana Saudat tayi ɗiff bata ko motsi sbda gabaki ɗaya jikinta ya mutu ga kanta dake sara mata ,ganin batace komai ba yasa Abdull tallafo haɓarta yaji bata nunfashi ,hannunta ya kama yaji tabbas suma tayi , a firgice ya ɗauko ruwan gora ya kwarar mata kasancewar yana da sanyi ta motsa a hankali tana cewa "shikenan Abdull dama yaudarata zakayi ? nagode "zata fice ya riƙo mata hannu yace "haba Saudat ki fahimceni mana ,kamar inda kike sona haka nima nake sonki , ke bakisan halin dana shiga ba akan maganar auran nan ko ?"nidai ina mai baki haƙuri akan dan girman Allah karki ɗaukeni maci amana "Saudat da sai yanzu hawaye ya sami damar zubo mata tace "na yarda tabbas iyaye ba abin wasa bane amma ka sani soyayyarka na cikin raina har abada "kasa magana Abdulla yayi sbda tuƙuƙun da yaji zuciyarsa keyi masa ,daga ƙarshe dai yace "Saudat ina yi miki fatan alkairi dakuma samun miji wanda ya fini "Saudat data koma kamar wata zautacciya ta buɗe murfin motar tace "fatan alkairi zata tafi ya kuma kamo hannunta a karo na biyu ya damƙa mata 50k kuɗin ya koma dubu ɗari da hamsin yace "Allah ya baki wanda ya fini "ba tare data wai wayesa ba ta nufi gidansu tana shiga ta sami babanta a zaune kan tabarma shi da Ummanta , kurma ihu tayi sbda ta kasa samawa kanta nutsuwa dan batayi niyar tonawa kanta asiri ba ,tace "na shiga uku wayo Allah na "baba daya ruɗe ya kalli Saudat yace "lafiya kuwa "Umma ma tambayar da tayi mata kenan , sai da Saudat tayi kuka ya isheta sanan tace "Umma Abdull ya taƙaitani na shiga uku wai anyi masa mata shine ya bani waɗannan shegun kuɗin dubu ɗari da hamsin "zabura Umma tayi tare da dafe ƙirji tace "dubu hamsin kuma ?kai wanan wane irin dukiya garesu ?baba da yayi mutuwar zaune yace "ai ni wanan rabuwa tayi mana rana harda maƙudan kuɗaɗe ?Saudat kam babu magana ganin iyayen nata sun nuna son kuɗin dake hannunta , barinsu tayi a gurin ta shige ɗaki tare da faɗawa kan fale falen katifarta ta kuma fashewa da kuka , gashi bataci abincin dare ba haka ta kwanta bacci ɓarawo ne yayi awon gaba da ita.

Abdull na komawa gida kasancewar kowa da ɗakinsa ya sashi wucewa nasa ɗakin , zama yayi kan haɗaɗɗen gadonsa tare da zuba tagumi ,a fili yace "nayi dana sanin amincewa da auran Fati wlh nayi dana sani "sai kuma ya tashi ya fara zagaye ɗakin yana huci kamar zaki , ya daɗe a haka daga ƙarshe ya kalli agogo ƙarfe goma na dare dai-dai , alwalah yayi yazo ya kwanta tare da adu'a , washe gari da asbha Abdull yayi alwalah ya tafi masallaci ya gabatar da sallah ,ba shi ya fito daga masallaci ba sai ƙarfe bakwai na safiya ,lokacin gari yayi haske sosai , miƙewa yayi daga zaman da yayi ya shafa adu'a sanan ya nufi gidan su  ,yana shiga ya sami Abba da hajiya zaune a palo suna hira ,durƙusawa yayi har ƙasa yace "barka da safiya hajiya "kana ya kalli Abba ma yayi masa barka da safiya , bayan sun amsa ne Abba ya nunawa Abdull gurin zama , zama Abdull yayi tare da jiran zantukan da zasu biyo baya  "Abdull" Abba ya kira sunansa a hankali "na'am "Abdull yace "yana duban Abba ,Abba yace "kasan yau bikinku saura kwana shida ko ?"mudai ta ɓangarenmu an gama komai ,kaima ya kamata ka ƙoƙarta ka kammalah "eh na gama "Abdull yace "jiki a sanyaye ,Hajiya tace "to jeka auta "ya miƙe ya basu guri ransa babu daɗi.

Tsohuwa dai taƙi zuwa karɓo magani kuma likitan yaƙi kawowa ,Ramu tunda taji zancen aure ciwo ya warke.

Washe gari tsohuwa ta gyara gidanta tayi wanka ,tana fitowa ta shafa mai ta ɗauko ƙure adakanta tasa ta yafo gyalenta tare da ɗauko takalmin soson da bata sashi sai zata anguwa ,mudubi ta ɗauka tana kallon fuskarta tace "Ramumu nayi kyau kuwa ?Ramu dake ta ƙunshe baki tana son yin dariya tace "kinyi sosai Allah ya haɗaki da bazawari "turɓune fuska tsohuwa tayi kana tace "ke zanje nemowa saurayi ai garama ki nutsu ,ni zan tafi ki gyara shinkafa ko mai da yaji ki ɗora "to Ramu tace "tare da yiwa tsohuwa Allah ya tsare , tsohuwa na fita Ramu tai tsalle kai tsaye cikin ɗaki ta shige ta buɗe madara ta dinga hambaɗa tare da ɗibar suka , ta haye gado tana dariya sai kuma ta miƙe zaune tace "oh ni Ramatu idan nayi aure sau biyar zan dinga cin abinci a rana sai kuma tasa dariya har da shewa.

Kasancewar ba wata tafiya bane sosai yasa tsohuwa tafiya a ƙafa tana tafiya tana zancen zuci , tana isowa ƙofar gidan su likita ta gyara mayafinta tare dayin sallama , wata farar mata ce ta leƙo tace "sannu baba "bakinta na ɗauke da haƙorin makka wanda ya ƙara fito da kyawunta ,baba dake kiciniyar shiga ba tare data amsa sannun da ake mata ba yasa matae bata guri , sai da tsohuwa ta shige ta fara ƙwaɗa sallama ,sai da tayi sau biyu sanan taji muryar Alhajin gidan ya amsa , washe baki tsohuwa tayi kana tace "faɗi yazo dai-dai zama ayita ta ƙare "kallon rashin fahimta da hajiya da alhaji sukayi mata ,ita ko sai ɓaɓatun surutu take , ita bata shiga ɗaki ba ita bata nemi guri ta zauna ba sai magana take ,su kuma basu gane inda ta dosa ba , alhaji yace "tsohuwa bismillah sai yanzu na ganeki naga kin dawo ƴar caras ne "washe giɓib bakinta tsohuwa tayi kana ta kutsa kai zuwa cikin ɗakin Hajiya ma ta bita ,zama tsohuwa tayi a kan kujera tare da gaishe su ,bayan sun amsa tace "nazo akan maganar wanan ɗan naku likita waye ma sunansa ?tsohuwa ta fara kame-kame    sunansa "Zaiyyan" hajiya tace "a taƙaice , kuma washe baki tsohuwa tayi kana tace "dama nace "tunda yaga ƴar gurina wato jikata yace "yanaso sai ayi ƴar gida ai ko ?"cikin farinciki Hajiya tayi murmishi ta wuce kitchen ta ɗibowa tsohuwa dambun nama da lemun kwalba guda biyu ta ajiye gabanta , sai da tsohuwa ta gama shirya ƙarya da gaskiya sanan ta ɗauki kular da aka zuba mata    dambun nama ta riƙe ta kwashi lemon kwalba tace "Ramu zata kawo kayan "Alhaji ne yace "to hajiya kam sai binta da ido da tayi.

Tsohuwa na tafe tana sambatu tana cewa "dama ance idan arziƙi ya kiraka babu makawa sai ka samu ,yanzu gashi nayi samuwa dama Bashir ya daina ɗan siyomin gidan ma yamin yajin aiki ,tana tafe tana surutan ta har ta iso gida , sallama ta ƙwaɗa.  in kaji muryar tsohuwa sai ka rantse anyi mata bushara da aljannah ne , Ramu dake zaune a kan bishiyar gwaiba ta amsa tare da durowa ,kallon hannun tsohuwa tayi kana tace "sannu tsohuwa "yawwa ƴar albarka kinyi ƙoƙari gidan ya gyaru sosai gashi kinyi wanka kinyi fess kamar ba keba "murmishi Ramu tayi kana tace "ai saboda zan fara samari nayi " tsohuwa ta nemi guri ta zauna bayan ta ajiye kular hannunta da kwalaben lemu tace "yau fa samuwa mukayi "da sauri Ramu tazo ta buɗe kular , ganin dambun nama yasa ramu washe baki tace "wayo tsohuwa kin iya zuwa anguwa yasin ,nima barin kawo miki abin da na yi miki "tsohuwa dake hambuɗar dambun nama a baki tace "bari mu gama da wanan "tsohuwa da Ramu suka fara ci kamar kamun yunwa ,sai da suka cinye kowa ya ɗauki lemon kwalba ya kora .

Zuwa yamma abin da akaci ya zazzage tsohuwa tace "Ramumu mai kika dafa mana ? da sauri Ramu ta shiga kicin ta ɗauko kwano mai murfi ta shiga dashi ɗakin tare da direshi a gaban tsohuwa tace "gashi "bismillah tsohuwa tayi ta buɗe ,abin data gani ne yai matuƙar firgitata tace "....!

Afuwan fans ina matuƙar ƙaunarku daga grps grps ina ganin shar'inku insha Allah zanyi ƙoƙari inci gaba da faranta muku kamar yadda kuke kwararo min adu'a .

Pls kuyi following ɗina a wattpad momislam2020 sanan kumin vote a page sbda ganin cigaban labarin .

MOM ISLAM
[29/01, 10:11 PM] Mom Islam Ce: 🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️
   
*NI DA   YARINYA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂

Zainab Habib/Mom Islam

P 7-8

Farfesun kaza ta gani yaji manja ,waro ido tsohuwa tayi kana tace "Ramatu a gidan wa kika samu nama ?"naga kinje nemo min saurayi ne ,shine farinciki ya kamani nakeson nima in saki farinciki shine nace wani almajiri ya yankamin wanan babban zakaran naki "rakwab tsohuwa ta mayarda murfin kwano ta ajiye har idonta na ruwa tace "dan kutumar uwarki dan bazan zagi uban ba tunda nawane mun haɗa kuɗi da Lami ne ?"Ramu dai tana ta kallon tsohuwa tana ɗura mata zagi, tsohuwa ta ɗauko cinya ta lashe romon dake shirin zubewa a ƙasa tana cin naman tana faɗa , bayan ta cinye na hannunta ta kurma ihu ,Ramu tace "tsohuwa mai ya faru ?tsohuwa dake ci gaba da cin nama tana kuka tace "wlh Ramu kin taƙaitani wlh kinci bashi ,duk inda zanyi dan bikinku ya kan kama sai nayi ,saboda inje in maido kuɗin zakarana a gurin Zaiyyanu "ita dai Ramu babu bakin magana tana gudun ta cika magana tsohuwa tace "zata fasa shige mata gaba akan saurayin , sai da tsohuwa ta cinye na kwanon tass ta shanye romo ta suɗe hannu sanan ta kalli Ramu tace "ina ragowar ?"Ramu dake shirin miƙewa tsohuwa ta bita da ido , Ramu na fita tsohuwa tace "ai duk wanda  fito daga tsatson Lami dole sai yayi kwaɗayi ,badan kwaɗayi irin na Lami ba da tuni Bashir ya gina gidan sama mai hawa dubu "shigowar Ramu ne yasa tsohuwa yin shiru da maganarta ,sakamakon tukunya data gani an ɗauko , ajiyewa a gabanta Ramu tayi ta buɗe ,tsohuwa da kwaɗayi ke tunzurata ta leƙa tukunyar abin data kuma gani a karo na biyu ne yayi matuƙar firgitata har sai da nunfashinta ya ɗauke ta ɓingire a gurin sumammiya ,salati Ramu ta doka tana shirin kuka taje ta ɗibo ruwa a randa cikin kofin silba irin manyan nan ta sheƙawa tsohuwa duka a jikinta tana cewa "sannu "ajiyar zuciya tsohuwa tayi kana ta kalli kofin silban gabanta ta tureshi gefe tace "wanan ruwan ko mutuwa nayi ai dole na farfaɗo sbda wanka da kikayi min "murmishi Ramu tayi ta nemi guri ta zauna , kwararo amai tsohuwa ta fara kamar ,zata amayar da kayan cikin nata ,sai da tsohuwa tayi mai isarta sanan ta jijiga kai   tace "naci wahala Ramu zaki kasheni "Ramu dake tsaye me zatayi banda dariya ,ta dinga ƙyal ƙyalewa tana tafi , kwanciya tsohuwa tayi kan ledar tsakar ɗakinta tana murƙususu alamun ciwon ciki ,sbda bata yarda da wanan abin da taci ba kuma a tarihin rayuwarta bata taɓa cin wanan abin da Ramu ta dafa ba sai yau , ganin tsohuwa na shirin margayawa yasa Ramu zaro ido tana shirin kuka ta fice da gudu , kai tsaye kemis ta nufa ta samu shi kaɗai ne a ciki , ko sallama batayi ba ta faɗa tare da cewa "dan Allah kazo ka duba tsohuwa wlh ciwon ciki ke damunta "Zaiyyan dake sarrafa system ɗinsa ko ɗagowa baiyi ba bare ya kalleta yadai ji ance tsohuwa , ihun data kurma ne yasa shi ɗagowa idonsa yana cikin siririn farin gilashi mai kyau  yace "ku kullum damuwoyi sunyi muku yawa ita me taci kuma ?nama mana "Ramu ta bashi amsa idonta shaɓe shaɓe da hawaye  ,Zaiyyan da mamaki ya kamasa a fili yace "ikon Allah ku kuma nama ne ke lalata muku ciki to lu daina ci mana dole ne "kai naman Mage ne fa nayi mata farfesu saboda taje nemomin...sai kuma tayi shiru ta juya da gudu , komowa gida tayi ta sami tsohuwa kwance tana ta mutsitsikuwa ta shiga uwar ɗakinta ta ɗauko wayat tsohuwar ta danna number babanta , ring ɗaya baba ya ɗauka yace "baba ina yini ?Ramu dake shirin ƙara fashewa da kuka tace "baba nice tsohuwa babu lafiya "waro ido baba yayi kana yace "to gamu nan tahowa ".
Da sauri baba ya fito tsakar gida ya sami Lami tana haɗa wutar da zata soya waina , cikin firgici yace "Lami baba babu lafiya maza tashi muje "cikin ko  ɗarr Lami tace "jeka ina nan biyoka kana gani wutar taƙi kamawa "baba bai jira jin mai zata ƙara cewa ba ya fice , sauri yake kamar zai tashi sama ,tsabar ruɗewa gani yake mashin bazai fishi sauri ba shiyasa ma bai hau ba  , cikin ikon Allah ya iso gidan ,tura ƙofar yayi kana ya faɗa gidan ,yana shiga ya sami Ramu a zaune a tsakar gida ta rafka tagumi , baba dake mayar da nunfashi yace "ina take ?Ramu ta nuna ɗakin tsohuwa ,baba na shirin buɗe labule yaji sallamar likita    ya dawo da baya ya miƙawa likita hannu suka gaisa ,likitan ya shige ciki .

Da shigarsa yaga tsohuwa na kwance ido ya kakkafe ,ya nemi guri ya zauna tare da ciro abin gwajinsa ,zai gwadata ta kamo hannunsa ta riƙe muryarta bata fita sosai ta ɗaga kai ta kalli  baba tace "Zaiyyanu ka riƙemun amanar Ramu ko bayan raina kaine mijinta ,kai kuma Bashir ban amince a aurawa Ramu wani ba inba Zaiyyanu ba wlh inko ba haka ba banyafe b...baba yai saurin rufe mata baki idonsa ya kaɗɗa yai jajur yana ganin kamar tsohuwa bazata tashi ba , wani irin tari ne ya sarƙeta cikin ƙanƙanin lokacin jikin likita yai sanyi dana baba , hannun tsohuwa dake riƙe da likita yaji ya faɗi ƙasa ,a razane ya ɗago kai ya kalli baba ,baban ma shi yake kallo yace "ta mutu "ta mutu?"baba yace " innalilahi wa inna ilaihir raji'un "baba ya rushe da kuka ,Ramu dake waje ta kurma ihu tana shure shure tace "wayoo tsohuwata  na shiga uku "irin kukan da takeyi
[29/01, 10:12 PM] Mom Islam Ce: 🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️

    *NIDA YARINYA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂

_Zainab Habib/Mom islam_


P 9-10

Aslamu alaikum ,amsawa Fati tayi murya cike da farinciki ta miƙe da gudu ta rungume Abdull ,cireta yayi a jikinsa kana yace "ba wanan ne ya kawoni ba "kallonsa tayi tana murmishi tare da haɗe hannayenta guri ɗaya tace "to meye ?"tsaki Abdull yaja yana shirin ficewa Fati ta janyoshi suka faɗa gado tare ,waro ido Abdull yayi tare da tureta yace "wlh karo na farko kuma na ƙarshe da zaki kuma yunƙurin yimin haka ko ance miki haka nake ? sam maganarsa bata ɓata mata rai ba ko kaɗan hasali ma samun ƙwarin guwaiwa tayi kuma tabbas yau ɗinnan sai ta ƙwaci haƙƙinta ko ta halin ƙaƙa ,cikin azama Abdull ya miƙe ta kuma ruƙosa ya ɗaga hannu zai kwaɗa mata mari ,ko me ya tuna oho sai ya fasa  ya fice .

Abdull na fita Fati ta fashe da kuka dan wanan tulin maganin da Hajiya ta dinga ɗirka mata ya fara aiki ,gani take idan burinta bai cika ba komai zai iya faruwa , tana saƙa da warwara har ƙarfe goma na dare yayi .

Abdull na dawowa ɗaki ya fara tambayar kansa shin wai dama mai ya kaika tafiya ɗakinta sarai kasan halinta , yana tsaka da tunani yaji ta faɗo ɗakin ,a zabure ya miƙe dan shi a halin yanzu ma tsoronta yake ji , daga ita sai pants ta shigo tana tafiya tana karkaɗa jiki ,Abdull ya fara ja da baya kai kace shine amaryar ,ganin ta ritsa dashi a bango yasa shi dakewa yace "ke dallah ɓacemin anan me kuma ya kawoki ɗakina ? ba kince aure bane to gaki a gidan sai kuma me ? hannunta tasa ta zagaye masa kafaɗa kana tace "ai kaine angon ƴar kazar ma da ake kawowa baka siya bane brother ?"wani yawu na wahala Abdul ya haɗiya muƙut duk da yanayin inda ta shiga yasa shi jin jikinsa ya mutu amma  baiyi  inda zata gane ba , Abdull dake ƙare mata kallo yace "abinda na sani duk cikakkiyar mace wacce ta amsa sunanta mace ,ba ita ke neman miji ba shike nemanta "batare data kula maganarsa ba tace "to ai ni gani nayi mijin na gudun matarsa ina tunanin matsoraci ne "tasss Abdull ya wanketa da mari tare da jefata bed ya rabata da komai na jikinta ,shima ya cire nasa ,bai tsaya sarrafata ko kaɗan ba ya faɗa mata .
Fati ta raina kanta dan sun raba dare a abu ɗaya Abdull yakai wajen awanni a kanta harda neman yafiya tayi amma yaƙi kulata kuma yana jinta ,sai da ya gama wususukata sanan ya miƙe tare da ficewa yabar mata ɗakin ya nufi toilet ɗin palo yayi wanka ya duba rigar bacci a ciki yasa ya kwanta room ɗin dake palo mai toilet ɗin a ciki , washe gari tun safe ya tashi bai tsaya wanka ba ya nufi ɗakinsa samu yayi bata nan yayi murmishin mugunta ya ɗauki wayarsa ya danna number kukun gidan lokacin ƙarfe takwas, ɗauka kukun yayi Abdull yace "black tea da egg "ok kukun yace "Abdull ya ajiye wayar , ba'a ɗauki wasu mintuna masu tsayi ba sai ga kukun ya kawo ya ajiye a dining , fitowa Abdull yayi ya zauna ya fara ci ,yana cikin ci yaji tafiya yasan mutuniyarsa ce , ganin tana tafiya tana ɗingisa ƙafafuwa yasa shi tuntsirewa da dariya yace "madam ga abinci fa "Allah sarki Faty bata fushi ta zauna ta cika cikinta ,bayan sun gama ci ta kallesa tana gudun karta yi magana yace "tayi masa rashin kunya yayi mata irin na jiya , amma bari ta gwadasa tace  "yah Abdull ina kazata ?"Abdull dake dariyar mugunta yace "kaza ko ?zakici kaza tabbas ya sureta sai ɗakinta ya rufo ƙofa ,dama iya doguwar riga ce a jikinta ,shima ya cire nashi ya fara wajigata ,yau kam kuka take sosai da sosai dan har haɗashi da iyayensa tayi sbda gani take kamar zai cire mata rai gashi ko taimako babu , yaumafa sai da yayi niya ya ƙyaleta sanan ya wuce bedroom ɗinsa yayi wanka ya sauya kaya duk da yasan ba cikakkiyar budurwa bace ta bada kanta a waje bai hanashi jin farinciki ba ,dan ji yake kamar ya dinga kasancewa da ita kullum .

Yau akayi sadakar bakwai na tsohuwa har mutane zasu watse ,alhaji wato mahaifin Zaiyyan ya kalli baba dake zaune yace "dama yau juma'a inason a ɗaura auran Zaiyyan da Rahma "cike da farinciki mutanen gurin suma amince hatta shi baban yaji daɗi sosai sbda burin mahaifiyarsa kenan kuma an cika mata shi , cikin ikon Allah aka fara shirye shiryen aure ,dama mutane na kusa dana nesa sun halarci gurin taron ,aka biya dukiyar aure cikin ikon Allah aka ɗaura auran Zaiyyan da Rahma akan sadaki mafi albarka dubu hamsin .

A take a gurin alhaji yace "bama buƙatar komai daga gurinku dama munata yi masa shirye shiryen aure to wacce yake son ma ba sonsa take ba ,jiya tazo har gida taci mana mutunci ,mun gama kayan aure har gidan ma duk an kammala gyara sa gobe insha Allah sai kawo amarya "kowa ya tashi da tsananin farinciki baba ko baki yaƙi rufuwa haka ya shigo gidan ya dami ƴan uwansa mata da suka zo yake sanar musu da Lami , duk sunyi farinciki Ramu dake rakuɓe a gefe sai binsu take da ido ta miƙe ta fice , tana fita taga dandalin sa'aninta a ciki ,ƙawarta mai suna Khadija tace "shikenan Ramu gobe sai gidan miji "dariya Ramu tayi kana tace "ni so nake ma ana kaini wllh in dafa shinkafa da miya mudu ɗaya in cinye ni kaɗai ,tunda nake ban taɓa ƙoshi da shinkafa a gidanmu ba in kunga abin da naci na ƙoshi sai dai tuwo "dariya suka sa wata a gefe tace "shikenan zaki dinga kwana a bayan ƙato 😂"Ramu tasa dariya tace "ke ai ba ɗakinmu ɗaya dashi ba ,kin mance abin da malam yace "?dariya suka saka dukkansu tare da cewa "wa gaya Ramu da ciki "Ramu ta hau shure shure tace " ai bazai naje naci dankali ba shine cikin mutum yake ƙato ai "daga nan dai ko wacce tayi gida Ramu ma tayi gidansu .

Zaiyyan da yaji wanan maganar ta auransa ya tsorata ,sbda a inda yake da wanan rayuwar tasa yana ganin Ramu tayi masa yarinya ace NIDA YARINYA zanyi rayuwa ?wlh zan cuceta ko kuma ta cutar dani....!

Afuwan fans yauma babu yawa fa 😂naga comments a grps grps ina godiya insha Allah na gobe sai ya baku mamaki 😍.

Tofa ga littafin daya doke na NIDA yarinya daɗi ,sunsn littafin MACEN SIRRIN  kunsan akwai cakwakiya fa ,duk wanda ya nuna min soyayya ta  hanyar siyan littafina bazaiyi nadama ba ,littafan guda biyu ne ,da ƳAR DAMFARA da kuma MACEN SIRRI .

MACEN SIRRI 300 Vip 500
ƳAR DAMFARA 300 tabbas inason ganin yawanku masoyana karku manta akwai cakwakiya ,littafan zasu fara zuwar muku idan har akayi rabin payments wayo biya .
Domin neman karin bayani 08141799224  abari ya huce duk wacce bata karantaba ina tayata da jimami aradu 😂.

Mom Islam
[29/01, 10:12 PM] Mom Islam Ce: 🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️

    *NIDA YARINYA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂

_Zainab Habib/Mom islam_

P 11-12

Washe gari bayan anyi sallahar asbha ,iyaye suka duƙufa aikace -aikacen biki , Lami kam komai ya cukurkuɗe mata sbda babu abin data siya duk da ance iya amaryar ake buƙata amma ai gara dai ace akwai nata ,zuwa ƙarfe tara maƙota sun shigo aka fara yanke yanken kabeji dasu karas da sauransu , masu ɗora tukunya nayi masu gyara shinkafa nayi , amarya kam Lami ta kaɗata gidan wata mata ana ce mata Hajiya Nafisa , Hajiya Nafisa gogaggiyar yar duniya ce sana'arta shine sai da magungunan mata  a garuruwa da dama , kasancewar ta fara manyanta yasata dena yawo amma ana zuwa gida ana siya , kuma ƙawar

Please Login or Register in order to submit comment