Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take gaya masa sunyi bak'uwa shima Khalil d'in yanason tuno inda ya santa 'amma ya kasa , da fara'arta tace ”brother yakake lpy kawai Khalil yace ”sbda in yana kallonta kuwarjini take yimasa gashi sai yadingajin wani iri."


Khalil ya mance da Nancy ko zancenta bayayi ,tunda Nussy tazo komai nashi ya sauya ita ce abincin sa komai ma gashi kosu momy nasan yin magana babu hali saidai subita da ido.


Yau Bikin Humaira sati biyu kenan shiri tayi dan zuwa gidansu Nancy dan tagane abinda tayi bata kyauta ba , tare da mijinta suka tafi , bud'e get din gidan sukayi suka shige ciki da sallama, Umma na bedroom Nancy kuma na parlor , ko amsa sallamar tasu batayi ba tafara zazzago musu bala'i , Humaira kinzo ne ki had'ani da nahaifiyata kokuma kinzone ki k'arasani da sauran kwana na ? wlhi nayi dana sanin saninki a rayuwa turr , hayaniyar da Umma taji ne yasata fitowa ganinsu Humaira a tsaye yasata cewa mekuma ya faru ne nakejin hayaniya , Nancy da kuka ya k'wace mata tace ”Umma karki yarda da ita wlhi ,umm ita ta rabani da Khalil tana kuka tana nuna Humaira ran Humaira ne ya 6aci sosai ,tace ”tunda ke ba kida fahimta munzo baku hak'uri ne shine zaki fara cimana mutunci ?"mijin Humaira ne yace ”zomutafi kawai ,Umma na cewa kuyi hak'uri Nancy da idanunta ya rufe tace ” wlhi wlhi Humaira ku fice mana a gida tana nuna musu hanyar waje , Humaira da ranta ya 6aci tace ”ank'i fita d'in kiyi duk abinda zakiyi banza kawai , Umma ganin abinnasu ya girmama yasata yiwa mijin Humaira magana akan ya tattarata su wuce , mota ya wuce tunda yayi mgna sunk'i jinshi , Umma tana kuka tace ”wlhi DUDUWA inbaki shige d'aki ba wlhi ranki zai 6aci ,Umma na magana Nancy na magana Humaira ma na magana ,maruka Umma ta wankawa Nancy dukda hakan batayi shiru ba ,tana cewa anty Humaira meraba masoya , Humaira da haushi ya isheta tace ”menene amfanin mak'aryaciya bazakiyi rayuwa a inda Allah ya ajiyeki ba kind'auki burin duniya kin d'orawa kanki ,garama da Khalil din yasani ba dukiyar momyn mu bace kikecin arzik'i ke banda butulci harzaki iya yimin rashin mutunci ,karki manta kwaliya a gurinmu kika koya kuma iya tafiya da magana ba a gurinmu kika koya mungama miki komai ai dole muzamo abin wulak'antawa , wawuya jaka kawai har mahaifiyarki kika dauko sbda san duniya kina tunanin soyayyarku da Khalil zata d'ore gashinan kinga k'arshen karya yazamo saniyar tatsa a gidan ku ,mahaifiyarki ma sbda San abin duniya tabiyoki kuka kama gida wani wawan mari Nancy ta tsinkawa anty Humaira nanfa fad'a ya kaure Umma ko tun d'azu tafad'i sumammiya ,Humaira ko kallon inda Umma take batayi ba ta wuce waje gurin motarsu ."


Da shigarta mota mijinta yafara surfa mata bala'i yana cewa”koma me akayimiki keka jawa kanki da bakizo gidansu ba da hakan bai faru dakeba , yaja mota suka wuce gida .



Yau kwanan Nussy goma a gidansu Khalil babu mai cemata komai kowa na gidan tsoron 6ata mata rai yakeyi , kuma bata ta6a nuna musu tana taraiyya da maza ba kasancewar tunda tazo bata fita koda k'ofar gida ba ."

Khalil ne yakira KB wato mijin Humaira a waya yace ”masa ganinan zuwa cikin murna KB yace ”Allah ya kawoka lpy mekakeso a dafa maka ?"Khalil na dariya yace ”ai kasan cimata farfesun kifi OK suka kashe waya , Nussy na bakin k'ofa tanajin hirar tasu , cikin kulawa tace ”brother nima zani , zaice a'a ta kafeshi da idanuwanta baisan lokacin da yace ”jeki shirya ba , saida ta tafi yashi haushin kansa shin wanan wacece dazata dinga yimasa shishigi ? bashida mai bashi amsa hakan yabashi damar yin shiru✍️.



Gaskiya jiya banga sharhi ba 😫😉.



~Mom Islam ce~✍️.
💖🌷NANCY YAR KARYA 🌷💖.


*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

Zainabhabibu713@gmail.com



_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_



71_72

,,,,,,,,,,, Nancy na kuka ta yayyafawa Umma ruwa , ajiyar zuciya Umma ta sauke daganan tafara kuka Nancy kuka Umma kuka babu mai bawa wani hak'uri , Umma ce ta mik'e taje tayo alwala ta dawo tafara sallah ."

Misalin k'arfe 2:pm Khalil da Nussy suka isa gidan KB wato gidansu Humaira , Nussy na sanye cikin riga da zani da hijab ba k'aramin kyau tayi ba , horn yai maigadi ya lek'o ya bud'e masa gidan , da shigarsu KB ya lek'o yana cewa ”wata sabon gani ,fitowa sukayu a motar suka nufi ciki ,anty Humaira ta cika musu tirai da kayan motsa baki gakuma farfesun kifin a kula , hira sukeyi sosai , anty Humaira ce kejan 'Nussy da hira amma batason yin mgna , saida sukayi sallar la'asar sanan suka wuce , yana shirin d'aukar titin da zai sadashi da unguwarsu ,Nussy tace ”my lovely brother please muje shoppin mana ,kasa yimata musu yayi yajuya motar suka nufi super market , suna sauka ta kamo hanunshi ta rik'e , Khalil kuwa wani bak'on yanayi ne yaji ya ziyarce shi haka suka wuce ciki tana ta jidar kaya , Khalil ne ya wuce gurin turaruka wata kyakyawar budurwa tazo kusa dashi tace ”barka handsome zaro ido Khalil yayi saikuma yace barka yakk lpy suka gaisa , tace "masa inba damuwa kabani number ka mudinga gaisawa kayimin kama da brother na ,bakomai Khalil yace yana cikin fad'a mata number Nussy ta k'araso ta wankawa budurwar nan mari ,nanfa fad'a ya kaure aka yiwa Nussy duka harda kumbura baki bayan le6enta dake fitar da jini
Haka Khalil yasata a mota suka nufi hospital akayi mata treatment aka basu magani amma a gefe dariya yake kwasa ,da komawar su gida momy taga fuskar Nussy tambayar Khalil meya faru tayi cikin in insa Khalil yace ”fad'uwa tayi ,badan momy ta yarda ba ra k'yalesu , ranar dai Nussy tasha bak'ar azaba dan idanunta sun kumbura sosai ."



Ragowar dubu goma ne a hanun Nancy , damuwa da tashin hankali sun shiga sbda daga ita har Umma suna tunanin halinda ,zasu shiga idan kud'innan ya k'are tagumi suka zuba suna tunanin hanyar data dace , Umma ce tace ”DUDUWA zani k'auye ko Allah zaisa insamo mana wani abin kuma a d'akina ma inada buhun masara , 6ata rai Nancy tayi tace ”amma dai Umma inkin kawo masarar za'abada canji ne subamu shinkafa ? dak'uwa Umma tayi mata ,kana tace ”ke bakya tunanin abinda zaije ya dawo ko ,baki tunanin halin rayuwa ,ko sokikeyi wataran mud'auki kayan kallo ko gado da katifa musiyar gashi me hayan ma yakusa wai_wayar mu , Nancy dai bata k'ara magana ba taja bakinta tayi shiru."


Yau kwanan Nussy biyu da zuwa gidansu Humaira gashi haryanzu ido yak'iyin sauk'i , kwance take idanunta nayi mata wani azabar zafi gashi babu dama ta kalli mudubi sai taji kamar an zuba mata barkono , washe gari dady ya dawo daga tafiya ya cewa Nussy ta shirya suje wani hospital din , rabonta da wanka tun jiya haka tasa hijab suka nufi hospital itada dady da Khalil , sunsami ganin likita aka wuce da ita d'akin masu larurar ido , doctor ne yace ”sai anyiwa idon aiki , hak'ik'a ciwon idon Nussy ya gir giza su momy amma basu isa suja da ikon Allah ba, doctor yace ”musu suje sudawo gobe insha Allah sai ayi aikin Nussy ko ba haka taso ba sbda wanan ciwon idon yasa Khalil bayajin maganarta ko kad'an ."


Yau Umma taje k'auye mutane da ganinta suka hau gulmarta wasu na cewa aikatau tajeyi wasu kuma na cewa tuwo tuwo tajeyi kowadai na tofa albarkacin bakinsa ,duk maganar da umma taji dole take shanyewa sbda batada bakin mgna , kwananta d'aya ta tattaro abubuwan da suke dashi buhun masara da daddawa da kuka da ku6ewa da wake na shinkafa ,mak'otansu ta shiga tayi musu sallama ta fito ,bataji dad'in gulmarta da akeyi a garin ba alma dole ta hak'ura ,ta hau mota ta nufi Abuja ,mai motar da ya kawota ne ya temaka mata suka shiga da kayayyakin Nancy kuwa batanan ,kasancewar key kuda biyu ne d'aya a gurin Nancy d'aya a gurin Umma , kud'in shigo da kayan ta biya tayimasa godiya , je jera kayantayi taje tayo alwalah tayi sallah , tana idarwa ta nufi kitchen hango plet tayi cike da taliya da kifi , girgiza kai tayi dan tasan yarinyar tata tayi nisa batajin kira , Nancy ce tashigo tana cewa oyoyo Umma kinsha hanya seda Umma taci abinci sanan suka fara hirar k'auye



Yaune za'ayiwa Nussy aikin ido an shige da ita d'akin ,🤷‍♀️sedai muyi mata fatan fitowa lafiya."




[02/02, 3:13 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 🌷💖.


*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)





_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_



73_74

,,,,,,,,,,Khalil ya koma gida , yabarsu momy da Dady a Hospital d'in ,

Kwance yake a makeken gadonsa tunanin Nancy ne ya yafara ziyartar shi cikin azama ya mik'e ya na shirin fitowa , kome ya tuna oho saiya koma ya kwanta zuciyarshi babu dad'i ,tunanin farkon fara soyayyarsu dakuma yanzu daya gano gaskiyar lamari gameda Nancy , wayarshi ce tafara ruri sunan momy ne ke yawo a fuskar wayar cikin azama ya d'auka tare da sallama ,Khalil kazo yanzu cewar momy , Khalil da hankalinshi ya tashi yace ”to ganinan zuwa , tunani yafara kodai jikin Nussy ne kokuma ba'ayi nasara bane oho bashida mai bashi amsa ya mik'e batare da ya sauya kaya ba ya fice , yanufi mota ...



Tunda su Nancy sukazo Abuja basu ta6a yin tuwo ba 'amma gashi yau ,umma shitakeyi , tarasa inda zatasa rayuwarta gashi batada kud'in kayan kwaliya bare akai ga cikinta dan tafi buk'atar kayan makeup , lek'owa kitchen d'in tayi taga Umma na kad'a miyar kuka chii ,Nancy tace ”tana toshe hancinta da gefen d'ankwalinta ,ko d'ago kai Umma batayi ba bare ta kulata , d'aki Nancy ta koma tanata juyi sbda wata azababbiyar yunwa takeji ,sallama Nancy tajiyo ,da sauri ta fito dan taso tagane masu muryar , hango su Jamila da Karima tayi aikuwa ta buga tsalle suna dariya d'akin bak'i dake can wani part daban ta kaisu dan batason suga Umma na tuwo , Umma ko taji zuwan bak'in kuma taci alwashin kaimusu tuwon ko Nancy zatayi menene ,hira sukeyi sosai ,d'auko musu exotic tayi dama jiya ta siyoshi tana burin yau tasami biscuit taci dashi tunda Umma nayin tuwo , to gashi yanzu anyi manyan bak'i ,zuzuba musu a cup tayi sukaci gaba da hira , suna cikin hira ne Umma tayi sallama , cikin girmamawa suka amsa suka gaisheta , Umma ce ta ajiye musu tuwon leda a plet da miyar kuka da taji daddawa da citta sai k'amshi take zubawa , cikin farinciki sukace kai mungode Umma wlh kamar kinsan munason tuwo a gida ko munaso basayi mana kuma bamu iyaba dariya Umma tayi tace ”zaku iya a hankali Allah yabaku miji nagari ,suka amsa da amen Nancy kuwa kamar ruwa ya cinyeta, Umma na fita su Jamila suka janyo plet d'in tuwon suka fara ci suna santi Nancy ce kallonsu takeyi ga bak'ar yunwa data gallabe ta ."

Da isarshi hospital din yasami momy a barandar asibitin a zaune parka motarshi yayi ya k'araso da sauri mik'awa momy abincin daya buya hotel yasiyo yayi ,kar6a momy tayi suka gaisa , Khalil ne yace "momy ya mai jikin ?" da sauk'i momy tace ”ammafa idanuwan nata duka sun rufe yanzu bata gani , zaro ido Khalil yayi tareda jan dogon salati yace ”abu kamar almara innalilahi momy daga mari ?!! haka Allah yaso cewar Momy , mik'ewa my tayi tace ”tashi muje ka ganta ku gaisa tun d'azu take kuran sunanka , mik'ewa Khalil yayi jiki babu k'wari , suka nufi cikin hospital d'in ,da shigarsu Nussy tajiyo sallamar Khalil dariya takeyi tana d'aga kai alamar inda makafi sukeyi, rung d'in wayar Nussy ne ta katse dariyar tata , batasan mai kiranba saidai ta d'auki murya , jiyo muryar bokanta tayi yana ihu yana d'ura mata zagi had'i da wasu dariyaku kamar na mahaukaci , hankalin Nussy ne ya tashi sosai dan tasan su momy sunji komai angama , ajiye wayar tayi ta maida kai ta kwanta , mik'ewa Khalil yayi zaije gurinta ,momy tayimasa alama da hannu akan yadawo , bahakan yaso ba amma dole yadawo ."



Bayan su Jamila sungama cin abinci suka mik'awa Nancy wata leda cike take da kayan makeup dasu chocolate da biscuit ,aiko ba k'aramin murna tayi ba , labarin fad'an dasukayi da Khalil tabasu amma bata basu labarin cewar su talakawa na harda k'arya ta shirya musu , sukadinga zagin Khalil , saida akayi magrib driver n su yazo ya tafi dasu Umma nata yimusu godiya , d'akin Umma ta nufa da kayan Umma tayiurna sosai Nancy ko abin nema yasamu lol."


Yaune aka bawa Nussy sallama taji sauk'i saidai matsalar ido, sbda likitoci sune jijiyar idonta sun mutu ko ina zasuje a fad'in k'asar nan saidai suyi asarar kud'i , da isarsu gida kowa ya zarce part d'insa , momy ko tunani takeyi anya wanan yarinyar ba da wata manufa tazo gurinmu ba ,dan tasha mafarkin tazo mata da daddare zata caka mata wuk'a ,
Shima Khalil a nashi 6angaren ya tuno inda yasan Nussy a gidan shi babbar k'awar Suhailat ,amma meyasa kwanaki kowa kejin shakkarta
[02/02, 6:36 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 🌷💖.


*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

Zainabhabibu713 @gmail.com

Whattpad Momislam2021

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_



_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_



75_76

,,,,,,,,,, Washe gari da sallama momy tashiga d'akin Nussy ,samunta tayi kwance a kan gado idanunta tabb da hawaye dajin motsin shigowar momy yasa Nussy goge fuskarta , momy nuna mata tayi kamar batasan tana kuka ba , ta gyara zama tace ”Nussy waye kukayi waya dashi a hospital , uhm im am ,momy ta dakatar da ita dacewa wato mu munrik'eki da zuciya d'aya kekuma kinna nufinmu da mugunta ko?" bajinayi mutumin 'na zaginki ba mekika aikata masa ? hawayen da take k'ok'arin tarewa ne sukayi nasarar zubo mata tace ”momy ku gafarceni momy ku yafemin 'niba marainiya bace kamar yadda Na fad'a muku inada iyaye yawon duniya ne yasa na watsar dasu rabon da iyayena susani a idanunsu nayi shekara bakwai , momy ni ce silar mutuwar Suhailat!!! Innalilahi wa inna ilaihirraji'un momy tace ”tana k'arewa Nussy kallo ,kenan kece kika kasheta , cewar momy Nussy na kuka tafara bawa momy labarin lesbian d'in da sukeyi dakuma bin boka da sxx da boka yayi da ita komai saida ta fad'awa momy tace ”ita ba y'ar Nigeria bace , amma iyayenta haifaffun kano ne amma basa zama a Nigeria suna London ,cikin 6acin rai momy tace ”kinga irinta nan ai shiyasa akafi so mutum ya aikata alkhairi , to wanan rayuwar taku ishara ce ga y'an baya masu biyewa zuciya ,wlh da har unayiwa Khalil sha'awar auranki yanz kam banajin son muhad'a zuri'a dake wlh dole kikoma gurin iyayenki , kuka Nussy takeyi ta sauko a hankali ta dafa gado ta durk'usa gaban momy tana bata hk'r momy ko saurararta batayi ba , tace ”barinkira Khalil gobe yau yaje ya shirya komai a airport gobe ki wuce ai bazaki kasa sanin iyayenki ba , cikin kuka mai ban tausayi Nussy tace ”momy kitausayamin mana kema mace ce ,momy ce ta k'i kallonta dan batason fasa niyar da tayi ,zakutafi tare da Khalil daganan ta fice. "




Nancy taga batada gaba batada baya dole ta zage tana kwasar tuwo gashi duk tayi bak'i ta rame yanz kam ko tunanin Khalil batayi sbda tama cireshi a ranta ,
Wata rana suna zaune da umma tace ”mata ke bazaki fito da mijin aure bane ?"rau_rau da idanu Nancy tayi tace "Umma wazan fitar babu mai zuwa gurina ina adu'ar za6in Allah ko mai amalanke ne yazo zan aureshi , dariya Umma tasa tace ”nagodewa Allah daya amsa adu'ata dakuma ya cire miki girman kai Alhmdulilh."


Washe gari Khalil da Nussy jirginsu ya d'aga zuwa London , gidansu Suhailat yafara zuwa shida Nussy sunyi sa'ar samun momy suka gaisa tare da k'ara yimata gaisuwar rasuwar Suhailat ,ganin Nussy yasa momy tuno wa da itace shu'umar k'awar Suhailat , momy zatace Allah ya is....Khalil ya dakatar da ita da cewa makauniya ce tazo neman gafarar ki ne itama kinga inda Allah ya maidata momy Suhailat na kuka tace”na yafe miki Allah ya k'ara shirya mana ku amen."



Nancy ce taje gidan anty Humaira tabata hak'uri anty Humaira mace ce mai fahimta suka zauna sunata hira kaya tabawa Nancy masu kyau da hijab da gyale Nancy tayi murna sosai suka yi musayar number ,Nancy tayi mata sallama ."


Da fitarsu Khalil daga gidansu Momyn Suhailat anguwarsu Nussy suka wuce da isarsu Khalil ya hango wani tsararren gida ,yafara tunanin to har me Nussy ta rasa take yawon karuwanci alhali iyayenta sun mallaki dukiya , shiga gidan sukayi da sallama wata mata fara ta fito da fara'arta ta taresu ,da ganin Nussy yasata fara zubda hawaye , tace ”NUSAIBA dama kina duniyarnan ?" Nussy bata ganin mahaifiyarta ta durk'usa tafara kuka tana cewa Ammi ki yafemin dan Allah , Allah sarki uwa kome d'anta yayi bazata gujeshi ba ,rungume ta Amminta yayi suka shige ciki Khalil ko said a ya zubar da hawaye , nayafe miki NASIBA ,Nussy ce tace ”Ammi nazamo makauniya wani razanannen kuka Ammi ta saki had'i da fad'uwa kasa sumammiya , da sauri Khalil ya d'auko ruwa a fridge ya shafa mata a fuska ,ajiyar zuciya ta sauke tafara adu'oi , bayan Khalil yaci abinci yayi sallah yayi musu sallama , Ammi godiya tayita masa ,yau zai kwana a hotel gobe ya wuce Nigeria
[03/02, 12:56 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 🌷💖.


*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_



_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_



77_78

,,,,,,,,,,Bayan Khalil ya sauka 'a Nigeria drivern gidansu yazo d'aukarshi , gida suka wuce inda yasami momy da dady a zaune suna dinner ,shima zama yayi akayi dashi albarka momy taketa sanya masa hakama dady , dady ne yace ”yakamata kaje kayi wanka kashirya zuwa gobe kaje gurin surukarmu , Khalil da baigane zancen da dady keyi masa ba ,yasashi cewa dady wacce surukar taku ?"dariya dady sukayi shida momy yace ”au bakada budurwa to momyn ka ta fad'amin komai , kanshi a sunkuye ya wuce part d'inshi batare da ya k'ara magana ba , wanka yayi ya sauya kaya shadda fara yasa sai takalmi da hula bak'i ,wow Khalil yayi kyau sosai kamar kasaceshi ka gudu ."



Gidansu Nancy ya nufa ganin get d'in a bud'e yasashi parking d'in motarshi a nesa ya fito ya shiga gidan da sallama , lokacin Nancy na kwaliya Jamila ta kirata zata rakata bikin wata k'awarta Umma dake tsakar gida tace ”barka da zuwa , durk'usawa Khalil yayi cikin girma mawa ya gaishe da umma , bayan sungai sa ne yake tambayar Nancy , umma ce tace ”yashiga parlor bari taje ta kirawo ta shiga yayi ya zauna dakin tsaf tsaf kasancewar Umma mace ce mai tsafta batason k'azanta hakama Nancy halin Umma tabiyo , shiga umma tayi ta tarar da Nancy tanasa kaya ,cikin fara'a umma tace ”ga Khalil nan yana jiranki , umma ta fice tayi d'akinta , sanya gyale Nancy tayi ta fito fuskarta cike da fara'a , barka da zuwa tace ”tana k'ok'arin zama a kujera , ywwa beauty barka ya garin ya kwana biyu lpy tace ”a tak'aice , gyara zama Khalil yayi yace ”nasan dukkan mu bamu kyautawa junanmu ba 'amma dawoda gaba baya bashida amfani , yanzu dai muyafewa junanmu , murmushi Nancy tayi wanda yakuma baiyyana kyawunta tace ”babu komai , Khalil ne yace ”dady na yanason zuwa gurin iyayenki akan maganar auranmu , Nancy ta girgiza amma bata nunawa Khalil ba , tace ”yaushe zezo , Khalil ne yace ”am inaga nanda 5 days yace , to Allah ya kaimu ,nan sukayi sallama ya mik'a mata bandir d'in y'an d'ari biyar biyar tak'i kar6a ya ajiye a kan kujera ya fita ."



Da fitarsa Nancy ta buga tsalle tace ”umma adu'armu ta kar 6u yanzu Khalil yace ”wai dadynsa zaizo to umma gurin wa zaizo alhali mahaifina ya rasu kuma y'an uwanmu na k'auye , Umma ce tace ”zankira yaya Ubale a waya sai atura masa kudi yazo ,rungume Umma Nancy tayi yaudai tayi kwanan farinciki."




Yanzu momy batada zama itada wata k'anwarta kusan kullum a hanyar kasuwa suke saboda momy a ganinta tayi dacen surukar kirki yanzu Khalil zaisan yayi aure wasu mahaukatan kaya ake jidowa kamar ba'asan zafin kud'i ba sosai momy takejin auran Khalil da Nancy alkairi ne saboda ta yaba da hankalinta ."




Nancy ce ta k'irga kud'in da Khalil yabata dubi ishirinne 20k taji dad'in wanan kyautar sosai dan haka ta mik'awa umma kud'in dukka , umma ta cire dubu biyar ta tura garinsu saboda d'an uwan mahaifin Nancy yazo ya tsaya akan maganar auranta , ta ware dubu goma ta ajiye dubu biyar ,tace ”yau Nancy ta rakata kasuwa , bawani tsayawa shiri sukayi ba sbda umma najin labarin bikin yan birni basa sashi da nisa , da isarsu umma ta hango abubuwan buk'ata

Wato tanason fara gyara Nancy 💖🌷.


Aya
Dabino
Kwakwa
Rid'i
Mazar k'waila
Minannas
Shinkafar tuwo
Gyad'a
Kafi malam
Asuwakin mata


Duk umma tasa aka had'a mata su takoma gurin masu saida saiwoyi please👏kuyi hakuri zan wuce but nasan kunsani ."


Dawowa gida sukayi umma tafara wanke aya ta shanya ta surfa rid'i ta wanke ta wanke shinkafar tuwo da sauransu , tana jira subushe ta dakesu inta soya ayar sama sama
[03/02, 12:56 pm] Mom Islam ce💃: 💖🌷NANCY YAR KARYA 🌷💖.


*STORY AND WRITING*
_BY_

*ZAINAB HABIB*
(Mom Islam)

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

Ina mik'a godiyata ga masoyana masu karanta littafin NANCY YAR KARYA gaskiya inajin dad'in faranta min da kukeyi Allah yabar zumunci masu sharhi ina godiya Allah yasaka muku da alkhairi🤙.


_Allah ya had'amu a sabon littafina mai suna *JININ ABBANA!!*

SHAFIN KARSHE👋.





________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_



Page 79 _80

,,,,,,,,,,Yau kwana biyar da zuwan Khalil kawun Nancy harya zo Su
Su Umma sun shirya wa su dady tarba ta musamman da ragowar kud'in hanunsu , hak'ik'a dady ma ya yaba da karamcin da su Umma sukayi musu ,a take a gurin suka biya dukiyar aure dubu d'ari biyu ,aka sa rana wata d'aya dan sunce basason ad'au lokaci mai tsayi , daganan sukayi sallama cikin mutuntawa ."


Parking yayi a k'ofar gidan su Nancy ,yanzu ko kunyar Umma bayaji kai tsaye zeshige suyita hira , tambayar Nancy yayi dame _dame take buk'ata zatayi ,Nancy ce tace ”gara munemi albarka ayi walimah kawai kuma a raraba 'alqur'ani hak'ik'a Khalil yaji dad'in hakan saboda yasan yaza6awa y'ay'ansa uwa ta gari , samun Umma yayi yace ”karta si komai saboda ya zuba komai a gidan, godiya Umma tayita zuma mai tare da sa albrka , cewa ”nancy yayi tazo suje ta kar6o kaya a mota , tare suka fice bayan yayiwa Umma sallama , da isarsu ya bud'e motar ya ciro wata k'atuwar leda cike da kaya ,godiya tayimasa tare da cewa Allah ya k'ara bud'i amen yace ”yana yimata murmishi ."





Riga da skirt na na atamfa sai swiss less da material ,d'inkin yayi matuk'ar yin kyau Nancy tayi farinciki hakama Umma tana ganin yarinyarta tayi sa'ar miji."




*WEDDING*💖🌷.


Allah ya yarda 'a yaune asabar dubban mutane suka shaida d'aurin auran IBRAHIM KHALIL da amaryarsa AISHA akan sadaki dubu d'ari biyu ,daurin auran dayasami halartar manyan mutane daga 6angaren dady Khalil , momy kuwa kamar anyimata bushara da aljanna , ango ni kaina ban ganeshi ba bare kuma amarya Nancy da gidansu yake cike da yan garinsu da mak'otan anguwa , Khalil ne yadauki nauyin abincin da Umma suka dafa kayan miyane bai

Please Login or Register in order to submit comment