Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzun dan dare yayi shiyasa." cewa tayi."To zan gaya mata, sai da safe, Allah ya kara lafiya." Fadil yace."ban ji ba gaskiya princess, abunda zaki ce man kenan."? Gwalo tayi mashi sannan ta ruga da gudu tana yi ma Fadil gwalonta." a hankali yace."Hmm yarinya zan kama ki, zaki shigo hannu ne." Murmushi yayi kawai.
Bayan su Fadil sun koma gida, wanka yayi yaci abinci, sannan ya samu suka yi waya da Abdullah, bayan sun gama waya, yaje mosque, suna fitowa , ya biya yayi ma su Umma sai da safe nan ya wuce part din shi, ya buga ma Rumaisa waya...
"Hello princess, ya gajiya."? A hankali tace."Alhmdulh princes, ya jikin ka princes."? Rumgume pillow yayi sannan yace kamar maiyin raɗa. "to da sauki sai da ina ta tunanin sauranniyar zuciya ta, baki ji yanda nayi missing dinki ba." daga can bangaren ta, itama kara kashe murya tayi sanan tace."Nima nayi missing dinka princes, nidai ka rage yawan wannann tunanin pls princes, bani son nayi asara." Murmushi yayi sannan yace."to shikenan, zan rage, ni fa na kosa naji ansa mana baiko, inda so samu ne anyi bikinmu cikin wata nan."
Dage kirji tayi sannaan tace."haba princes wani rawar jika har haka."? Cewa yayi."Naji din idan akan sonki to akirani *MAJUNUN* , princess na fi son ayi mana aure na nun maki kallar son da nike maki physical, sannan zaki yarda da Son da nike maki." cewa tayi."Tom princes Allah ya kaimu lokacin.".."Amin, ki gaya ma Mama zani zo na gaida Baba, dan inason manya shigo cikin maganar mu, dan gaskiya cikin shekarar nan nike son na ganki a dakina a matsayin mata." cewa tayi."to zan gaya mata." cewa yayi."yauwa, fatan zaki shigo gobe ko."?.."Eh zan shigo, prices bacci, yanzun har 12 tayi. Cewa yayi."ok bari na barki, amman ba dan na gaji ba, byee iluv you."...."byee luv uh too."
bayan su princess sun gama waya, Fadil sai da ya tura mata text messages kamar haka

_I cannot imagine a day without you my love. I feel insane with you. Nothing ever is the same. You touch my heart with your very presence and when we kiss it takes me to my soul. I am so madly in love with you princess.._

Bayan Rumaisa ta karanta message din Fadil itama ta maida man da nata

_As I lay_
_As I lay on the bed this night,_
_I was thinking about you so strong,_
_I want to come and hug you tight,_
_I know to me you belong,_
_My love for you my_ _feelings are that strong,_
_I so love you my love,_
_Have a lovely night,_
_And yes do sleep tight_ _my princes.._

Haka suka kama tura ma junansu sakonnin soyayya sannan suka yi bacci cikin farin ciki da annashuwa.

Washe gari...

*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls


🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      

            

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_49&50

Washe gari tun da safe, Rumaisa ta tashi, ta shirya sannan ta wuce gidan aiki..
Bayan taje, ta gama yin komai part din Umma suka shiga kitchen suka yi white rice with kayan lambu...

'''shinkafa,  carrot,green beans (pies''' )

_Yanda ake hadawa__

'''Da farko zaki samu tukunyarki mai tsata, ki daura a saman gas, sai kisa ruwanka wada tace, indan ya tafasa sai ki wanke shinkafarki sosai ta wanku, ki zuba a cikin takuya, kafin ta dahu ki samu carrot dinki ki yanka shi kanana sai ki wanke shi sosai, ana sauran bai fi 30min ki sauke shinkafar ba, sai ki zuba carrot din da green beans dinki, sai ki juya su yanda zasu hade da junansu sosai, in sun yi kamar 20min sai ki yi per boiling din shinkafan,  Kinyi per boiling water din da kamar 5min sai sauke ki sa a cikin cooler...
'''
Sai tayi miya....


'''tittasai (pepper),tarigu,albasa,curry,thyme,seasoning,kayan dan'dano
Mai,  jan Nama,  garlic (tafarnuwa)'''

'''Da farko dai uwar gida zaki wanke namanki ki sa  a tukunyarki, sai ki daura tukunyar a kan gas, ki dan sa kayan dan dano kadan da albasa da garlic da yar citta kadan(kun san dai citta tana fidda karnin nama), sai kisa dan ki shirinki shima kadan....'''

'''uwargida, zaki samu pepper dinki ki gyara shi sosai,  shima tarigun ki gyara shi sosai, albasa ma ki gyara ta, ki hadasu ki wanke su sosai, sai ki yanka su kananu ki zuba a cikin blender dinki ki blending su sosai, ki samu container din ki ki zuba shi markaden kayan miyar..
'''
'''Sai ki dauko tukunyarki ki daura a gas dinki, ki sa mai dinki ya dan soyu kisa yar albasa kadan gun soya man, sannan kin dauko kayan miyar da kika blending ki sa a cikin tukunyar,  in kayan miyar sun fara soyuwa, sai ki dauko dan'danonki ki zuba, ki gyara garlic din ki kasa a ciki, sannan ki yanka albasarki itama ki zuba, ki dauko tafashen namanki shima ki zuba, da roman tafashen da ki ida miyarki, inta dahu sai a sauke..

'''

Bayan ta gama yin shinkafa sai tayi lemun cucumber da danyar citta

_Abubuwan hadawa_

'''Kukumba (3) Citta (4), Suga,Lemun tsami (5),

Yanda ake hadawa'''

'''Da farko zaki sami kukumbarki ki wanke ki yanka kisa a blender.
Sai ki wanke cittarki ki goga da abin goga kubewa ko ki yanka kisa a blender ki hada da kukumba ki markada.
Sannan sai ki tace ki sa suga da lemun tsami.
Daga karshe, sai ki sa a firinji ko kisa kankara'''
Bayan ta gama hada komai ta kanshi a dining lokacin 1:00pm tayi, sallah taje dakin Fadila tayi, sannan suka fito, suka zauna aka kira Fadil yazo suka yi lunch  din...
Bayan sun gama yin lunch , Umma ta tashi tace ita ta tafi gidan su Rumaisa zasu yi magana da Mama, bayan tafiyar Umma, Fadil ya kalli Rumaisa sannan yace."Princess." Kallonshi tayi sannan tace."Naam prince." Dafe zuciyarshi yayi, dan sosai maganarta ta soki kagon zuciyarshi, murmushi yayi sanann yace."tashi ki shiga room din Fadila ki shirya kaya nan can na bata tun da safe, zamu tafi shan ice cream." Cikin salo mai tafiya da imani tayi magana,tace."to shikenan prince bari naje na shiyar tom." Kallonta yayi sannan yace."Princess kinsan me."!? Girgiza kai tayi sannan tace."Aa princes sai ka fadi." Matsowa yayi kusa da ita sannan yace."muryarki tana da dadin saurare, yanda kikasan ana busa sarewa dan dadi, ilove you Princess." Cikin dadi tace." Hakima samun masoyin gaskiya yana da wahalar gaske, ni kuma Rumaisa ba tare da nasha wuya ba Allah ya bani, Prince ina sonka nima kuma ina kaunarka." Tashi Fadil yayi yana hura mata iskan kiss, dafe kirji Rumaisa tayi alamun sakon kiss din Fadil ya iso gareta, itama maida mashi tayi da zanan heart bisa iska, rufe idanu Fadil yayi shima sakon ya iso, sannan yace."iluv uh will all my heart." Wucewa suka yi dan su shirya, Rumaisa shiga room din Fadila tayi tana cewa."Fadila, muga kayan da princes ya baki,ki bani."cire wayar kunnanta Fadila tayi sannan tace."ok ga sucen, red laces ne, shiga kiyi wankan ki fito na ta ya ki shirya wa."


"Assalama Alaikum."...."Aminwa'alaikumus sallama, Aa sannu da zuwa Hajiya Maryam, anzo lafiya."? Cewa Umma tayi."Lafiya lau Maman Rumaisa, sannu da hutawa, mun anshe maki abokiyar fira."dariya Maman Rumaisa tayi sannan tace."laa bakomai, mun gode sosai,bari na kowa maki ruwa."zaunawa Umma tayi sannan tace."to shikenan." Zuwa Maman Rumaisa tayi ta kawo mata ruwa tana cewa."gashi." Ansa Umma tayi tana cewa."nagode sosai, Alhmdulh ruwan randa yana da sanyi da dadin kamshi." Zama Mama tayi tana cewa."Ai shi da man haka Ruwan randa yake, dan yanzun freezer yazo, sai ya danne randa." Cewa Umma tayi."ai haka zamani yake,da man Maman Rumaisa zuwa nayi muyi magana a kan yaranan, tunda suna son junansu, ammn ya kika ce."? Murmushi Mama tayi, tana cewa."Eh hakane gaskiya Hajiya Maryam, amman wani hanzari ba gudu ba, mu bamu da kudin aurar da Rumaisa, sai nan gaba, dan ko jiya munyi maganar da Babanta." Shiru Hajiya Maryam tayi na wani dan lokaci, sannan tace."Eh to, kun kawo uzurinku, kuma abun dubawa ne, amman ni banda niyar na bari Fadil ya zauna wani gidan daban ga gidan da muke ciki, in ma yace yayi mashi tsufa, sai mu chanza gida in anyi bikin su, dan haka bamu bukatar komai naku, ai ko ba Fadil Rumaisa, zata aura ba hakina ne nayi ma Rumaisa kayan daki, na dauki Rumaisa tamkar yar cikina, dan haka mubar yin maganar kayan furniture." Numfasawa Umma tayi sannan ta cigaba da cewa."Naso na tadda Babanta amman, bakomai kin gaya mashi yanda muka yi da ke, sai naji ansa daga gare ki." Cewa Maman Rumaisa tayi."To Hajiya Maryam, mungode sosai, zan gaya mashi yanda muka yi da shi."Murmushi tayi sannan tace."to Maman Rumaisa, bari yau dai nayi maki wuni, nan suka kama fira, kamar sun dade da sanin juna.



Woow masha Allah, wata zugegiyar budurwa ce na gani tana murmurshi tana tafiya cikin kwanciyar hankali da natsuwa, Fadila tace."masha Allah, Rumaisar yaya Fadil, kinyi kyau sosai, sai kace ke kika yi kanki, gaskiya dole yaya Fadil ya rude." Bugu Rumaisa ta kaima Fadila sannan tace."Kin fara ko? Kinji matsalarki kenan, ina kyau anan nida ba wata uwar kwaliya nayi ba, duka daga poder sai lipstick, sai fa dan kajal da shafama ido na, kuma ba wani dauri nayi mai kyau tunda old style ne nayi *MARYAM* *BABANGIDA* , shine kyau? Mai karama miya gishiri." Rike baki Fadila tayi sannan tace."Wallahi kinyi kyau, sai kace wanda zata gasar kyau." Tashe jikinta da turare Rumaisa tayi sannan tace."indan babu ke a gurin ko."? Latsa wayarta Fadila ta cigaba dayi, dago kanta tayi sannan tace."Ai duk kyau na kin fini kyau ai Rumaisar Mama." Cewa Rumaisa tayi."to naji ni bani gyalen, kin san prince baya son jira, kuma tun dazun ya ce man yana wajen mota." Mika mata gyalen, fitowa tayi, tafiya take kamar bata son taka kasa, sosai ta tafi da imanin Fadil, kallonta yake sake da baki, baison ta iso ba, sai dai yaji tana cewa."Hy prince." wayyo Allah na😱, Wani handsome guy ne yayi firgigi yana cewa."gaskiya princess na zaunu,amman ji nike inama ace yau din nan an daura mana aure, wallahi, Hmmmmm, nadai yi shiru."murmushi Rumaisa tayi, ta basar da maganar Fadil tana cewa. "afuwan prince, Woow gaskiya prince wannan boyal din yayi maka kyau sosai." wani black boyal ne ya sa, da black hularshi yar maiduguri, ga wata Gucci watch daya daura a hannu shi, ga sumar kan shi Lub-Lub, tasha gyara kamar mai, cewa yayi."princess, ai kin fini kyau sosai ma."shiga cikin mota Rumaisa tayi sannan tace."thank princes, amman sai dai muzo daya." Fadila ce ta fito tana cewa."dan Allah lovers of the world, ku tsaya nayi maku pictures pls." Rumaisa ce ta fito daga cikin, ta tsaya nan fa Fadila ta kashesu da hotona, har guda uku, sannan tayi ma Rumaisa ita daya, bayan ta gama suka tafi..
"Umma sai yanzun kika dawo."?..."Eh wallahi Fadila,  tsayawa nayi muka yi fira da Maman Rumaisa, gaskiya tana da mutunci sosai." Cewa Fadila tayi." hakane Umma, ai gunta Rumaisa tayi gado."

Kallon Rumaisa Fadil yayi sannan yace."Princess, ina kike so mu fara zuwa, shoprite ko kuma Mudansir and brother, kuma mu fara zuwa Zoo."!?cewa Rumaisa tayi. "Eh mu fara zuwa Zoo, sai mudansir daga nan sai mu biya shoprite din."
Haka ko akayi, su Rumaisa sunje zoo, sunga su zaki da giwa 😁, Sannan suka biya mudansir, suka yi sayaiya, amman komai uku Rumaisa take dauka, ita da su Umma, daga nan suka wuce shoprite daga shoprite suka je suka sha ice cream sannan suka wuce gida.. Cewa Rumaisa tayi."Wai Fadila duk na gaji wallahi."..."ai dole Sannunku, ga wannan uban tsaraba duk ankawo mana, mun gode Sosai." Cewa Rumaisa tayi."kinji ki wai mungode, sai kace wani abu, kinga bari naje na hada ma prince tea na wuce gida."
Bayan taje part din Fadil direct kitchen ta wuce ta hada mashi tea din na'a-na'a zallah, sai ta dan ta mashi karanfani da chita kadan, bayan ta gama ta juye mai a flask, ta zuba wanda zasu sha, ta dauko ta shigo parlon lokacin yana zaune yana hutawa ya fito daga wanka....
"Prince, muna kwarya."cewa yayi."to princess, nagode sosai, princess har yanzun baki bukaci kije wanene Fadil ba, to gobe insha Allah zaki ji wanene." Cewa tayi. "to prince, Allah yakaimu gobe."
Bayan sun gama sha tea, ya dauke ta ya kai ta gida, da dare kuma su kayi wayarsu, bayan sun gama waya ya tura mata text messages 
_A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa_ _sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa_ _gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji._ _Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke_ _har abada. Ki kwana_ _lafiya princess, iluv uh_
Bayan ta gama karanta itama ta maida mashi murtani😎
_Farin ciki mara_ _misaltuwa kan ziyarci_ _zuciyata a dukkan_ _lokacin da na ji sautin_ _muryarka, murmushinka_ _babban abu ne da yake yayen damuwa, bana kasancewa dai dai da, shakar nimfashi ba tare_ _da tinaninka ba a cikin zuciyata, kaine d’aya tilo da na damkawa ragamar_ _zuciyata. Ni taka ce har abada, Ina son ka sosai prince..._
Bayan sun gama soyayarsu ta kashe waya, tayi addu'a sannan ta kwanta bacci...


*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING BY_
        
_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*



*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      

*BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*wannan page din nakane Yayana Muhammad Kareem kayi yanda kake so dashi, kaba wanda kake so ka hana wanda kake so Yayana na kaina🤗*

Page_51&52

Bayan Rumaisa ta tashi tayi duk abunda zatayi ma Mama sannan ta wuce gidan aiki, bayan ta gama aiki sukayi girki ita da Fadila sannan ta wuce part din Fadil, sallama tayi ta shiga zaune ta iskeshi yana danna laptop, kallon shi tayi na wani lokaci tana murmushi dan ji take sonshi na kara fisgarta cewa tayi."Good morng Prince." dago kanshi yayi yana kallonta fuskarshi cike da annuri, dan baisan ta shigo ba, hankalinshi yana kan aikin da yake, cewa yayi."oyoyo Princess, sai yanzun kika shigo kiga masoyinki? Bayan tun tuni nike zuba ido naga shigowarki."
Ida karasowa tayi ta zauna tana kallonsh nuna tayi mashi da ido ma'ana kar ya damu yasan komai takeyi cikin ranta tana tunaninshi, murmushi yayi ya cigaba da aikinshi, itama gyara mashi ko ina tayi ta hado masu tea sannan ta zo ta zauna ta zuba mashi ta bashi tea din sannan ta kwashe laptop din ta kai daki ta dawo ta tana kallon shi sannan tace."Prince ina sauraren ka yau dai ka bani labarin waye Price." Murmushi yayi sannan yace."tom karkaɗe kunnanki yanzun zakiji ko waye Fadil."
Gyara zama tayi tana kallonshi  shima kallonta yayi sannan ya fara cewa."Ni suna na *FADIL* *KHAMIS MAI DAKO* , mahaifina haifafen dan jihar Kano ne, iyayenshi talkawane sosai, dan ba ko da yaushe suke cin abinci ba."
Numfasawa yayi ta kurbe tea din shi sannan ya cigaba da cewa."Sunan mahaifiyarshi *FADILA,* Sunan Mahaifinshi *MUHAMMAD* , Babana su biyu iyayensu suka haifa, shine babba, sai kaninshi Fadil, duk da Khamis ya girmi Fadil da shekara shidda, amman shakuwa da soyayya tashi ga tsakaninsu, sosai dan Khamis babu abunda ba zaiyi ba akan Fadil."
"Talauci yayi ma Muhammad katutu, wanda baida abincin da zai ciyar da iyalenshi, wannan dalilin yasa Khamis ya shiga kasuwa ya fara sana'ar *DAKO* , lokacin Khamis yana da shekar 16,shi kuma Fadil yana da shekara 10."
Rayuwa kenan, dama haka take Princess dan talauci baya dadi ko ya yake ko, dan ko idan Khamis yayi dako, sai ya raba kudin da yayi ciniki gida biyu, ka so daya yake boyewa, sai kaso daya ya sawo masu abincin da zasu ci shida iyayenshi."

"Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Khamis shi ke ciyar da iyayenshi, watarana ya samu da yawa, watarana kuma aka shin haka."

"Kinsan ance hannu daya baya daukar damai, aiko haka maganar take Princess, dan ko Khamis ya gaji da ciyar da iyayen shida yake duba da karancin shekarun shi, kuma ba wata sana'a mai karfi yake ba dakon nan dai shine yake yi har ya ciyar dasu, to kasuwar Dako ta tsaya sai suyi kwana biyu basu ci abinci ba, kuma Baban shi na kwanciya yayi ba shima yana nema amman baya samu, sai dai Khamis yayi bara ya samo abincin da zai ba kaninshi Fadil yaci, sai Fadil yaci ya koshi sauran da Fadil ya rage Khamis yake ci."
"Kawai watarana aka wayi gari, babu Khamis babu labarinshi, haka malan Muhammad ya sha neman dan nashi, amman bai sa mai shi ba, haka ya dawo yana kukan bakinciki."

"Tunda Khamis ya gudu gun iyayenshi, ya shiga sabuwar rayuwa, ya maida hankalinshi wajen neman kudin shi, a rana Khamis sai yayi kunsan 1000 duk rana indan ya shiga kasuwa yin Dako."
"Watarana a kwana a tashi, Khamis ya hadu da ubangida Alhaji Nurandden, shine mahaifin Ummana."
"Alhaji Nurandden, sunyi sabo da Khamis sosai, tunda ya lura Khamis mutun ne mai zuciyar neman na kai, bai dogara da abun wasu ba."
"Alhaji Nurandden, yaso  hana Khamis yin dako, amman Khamis yace ya barshi ya nemi kudin kanshi, ba dan yaso ba ya kyale Khamis yana dako kasuwa, Amman duk da haka sai da yasa Khamis a makaranta."
"Khamis, yana makaranta, yana zuwa kasuwa, lokacin yana da shekara 18,ya gama makarantar secondary school, ya cigaba da dakonshi, Alhaji Nurandden yaso ya shiga jami'a, amman Khamis yace shi daga secondary ya gama."
"Cikin ikon Allah, Allah yasa ma kasuwar Khamis albarka, dan Khamis yayi suna a wajen dako a kasuwa, dan yanzun Khamis ya saya motoncin da suke yin dako cikin ko wace kasuwar Kano, ko wace mota ansa mata suna *KHAMIS DAKO* ."


"Khamis, yayi suna cikin garin Kano, yana da shekara 25,ya gina gijajen haya, sanann ya saya *KEKE-NAPEN* , ya raba ma mutane ya suna ba shi balance."
"Soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Khamis da Maryam, lokacin maryam, tayi degree din ta affanin Likita, ba su dade suna soyayya ba, Alhaji Nurandden yayi masu aure."
"Bayan aurensu da shekara biyu aka haifeni, naci sunan kanin Khamis wato Fadil, bayan suna na, Khamis yaje wajen mahaifanshi, amman sai kash ya tadda basu nan, da ya tambaya aka ce mashi tsawon shekaru rabon da a san inda mahaifanshi suke ba, sun tafi sun bar kaninshi Fadil."


"Khamis ya tambayi ina shi Fadil din yake, suka ce yana wajen kanwar Babanshi, ya nemi gidan Ba'bar tashi amman bai samu ba, dan itama ta chaza unguwa, da man gidan haya take zaune."
"Khamis, yayi kuka, ya na da ya sanin tafiya da yayi ya bar iyayenshi, ba inda bai bada cigiyarsu ba, dan harda gidajen radio duk a je, ya sa kudi masu tsoka ga wanda yaga yan-uwanshi, amman shiru kake ji ba'a gansu ba."
Khamis yayi hakuri, ya barma Allah lamarinshi, ina da shekara 7 aka haifi Fadila, mun taso cikin jin dadin rayuwa, dan a Dubai mu kayi karatun mu baki daya, tun daga kan primary school har zuwa university, dan ni sai da nayi *M. S. C* a dubai, lokacin Fadila tayi degree din ta, ta karanci *B.S. C* *NURSING* , ni kuma nayi karatun *BARRISTER* , sannan muka dawo Nigeria."
"Bayan mun dawo Nigeria, Abba ya bude ma Umma hospital ita da Fadila, amman ita fadila tace ba dan tayi aiki tayi karatu ba, sai Umma Kawai take zuwa sunan hospital din *DOCTOR* *MARYAM PRIVATE* *HOSPITAL* , ni kuma ina yi ma gwannati Aiki."
"Yanzun haka Abba, ya tafi neman yan -uwanshi a wudil nan Kano, dan ya ji labarin suna wudil da zama, amman jiya nayi waya da shi yace ya kusa dawowa cikin satin nan ma, dan Allah bai sa ya gansu ba." kallon Rumaisa Fadil yayi sannan yace."Princess kinji Labarin Barrister Fadil Khamis Dako."numfasawa tayi sannan tace."eh Prince, naji labarinka, Kuma Allah yasa Abba yaga yan'uwanshi, Kuma Allah yasa suna cikin koshin lafiya." cewa yayi."Amin ya Allah Princess, da nafi kowa farinciki idan Abba yaga danginshi, amman Princess  tunanin ke yar kanin Abba  ne, amman ni bansan kanin nashi ba da na biki na gan shi ba Wanda ya sanshi mu duka gidan nan, sai dai labarinshi, dan haka in dan Abba ya dawo yaje gida ya ga Babanki, tunda da man zaije ya nema man aurenki, dan tunda kika ban labarinki nikeji yayi shige da wanda Abba ya bani akan yan'uwanshi." shiru Rumaisa tayi tana tunanin maganar Fadil, tabbs labarinsu yayi shige dan itama Babanta ce mata yayi iyayenshi da yayanshi sun gudu sun barshi shi daya sai Ba'ba Rumaisa data rikeshi, numfasawa tayi sannan tace." Allah yasa muji alkhari Prince." Murmushi yayi yana mikewa dan yaga marece yayi cewa yayi."Amin Princess, taso na maida ki gida, kinga dare ya fara yi." "to, mu tafi."
Bayan Rumaisa, ta gama abunda take ta kwanta, nan fa as usual suka yi wayar da su ka saba sanann suka tura ma juna text massage..

*Nisa tsakanin zukata biyu baya nufi shinge face yana tuna mana da kyakyawar alakar dake tsakanin mu. Ina kewar Ki princess 💖*

Bayan ta karanta ta maida mai da haka🤪

*Farin ciki mara misaltuwa kan ziyarci zuciyata a dukkan lokacin da na ji sautin muryarka, murmushinka babban abu ne da yake yayen damuwa, bana kasancewa dai dai da, shakar nimfashi ba tare da tinaninka ba a cikin zuciyata, kaine d’aya tilo da na damkawa ragamar zuciyata. Ni taka ce har abada, Ina son ka.💞*
Washe gari, bayan Rumaisa, ta gama yin aiki, Baba ya kira ta..
"Rumaisa.".."Naam Baba." Murmushi yayi sannan yace."naji komai daga bakin Maman ki, a kan maganar yaron nan Fadil, ta gaya man yanda suka yi da Mamanshi yaron, naji dadin haka sosai, amman dan Allah Rumaisa ki kula da mutuncin ki kinji."? cewa tayi."Eh Baba nagode sosai."


'''Wayyo Allah, Wallahi na gaji sosai😢, typing ba sauki, gashi kunce dole sai anyi maku read more 🙍‍♀️, ni kuma wallahi ban son ya wan typing sosai☺️, amman ai bakomai book ya zo karshe dan bai fi sauran yan pages ba, ya kare baki da'ya😍..
'''
'''Ina yinku my fans I love you wujiga-wujiga, dan comment din ku shi ke sa man kwarin giwar yi maku yanda kuke so 😁
'''
*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey_

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_53&54

A haka rayuwa, ta cigaba da tafiya, soyayya mai karfi ta kunnu tsakanin FADIL DA RUMAISA, da kuma FADILA DA ABDULLAH..
Soyayya wanann masoya suke babu kama hannun yaro, zumincin tsakanin Umma da Mama, suma abun sai gaba yake, wannan dalilin yasa Umma ta ba su Rumaisa wani part a cikin gidan.
Kallon Mama Rumaisa tayi sannan tace."Mama wai yaushe zamu koma gidansu Yaya Fadil da zamane? Kinga Umma batajin dadi ace ta bamu wani bangare mu zauna a gidansu amman har yanzun bamu koma ba."
Kallon Rumaisa Mama tayi sannan tace."ba haka bane Rumaisa, nidai sai naga kamar bai dace ba, ace mun tare a gidan surukanki muna zama." Kamo hannun Mama Rumaisa tayi sannan tace." Mama su Umma ba irin wannan mutanan bane, su zasuyi ma mutun abu kuma ba gori har abada, amman yanda kika gani Mama." Suna cikin maganar Baban Rumaisa yadawo, yaji komai suka tautauna akai, zaunawa yayi,sanna yace." Hadiza kuyi sallama da mutanan gidan nan, yau da dare zamu koma gidansu Hajiya Maryam da zama, tunda ba tambayarsu muka yi ba." Murmushin murna Rumaisa tayi da Baba ya amince, itama Mama taji dadi cewa tayi." Shikenan insha Allah zaniyi duk yanda kace." Tashi yayi ya dauko abunda ya maido shi gida dauka sannan yace masu." Ni zan koma." A tare suka ce." Allah

Please Login or Register in order to submit comment