Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

 DAJIN FARAUTA
Littafi na daya(1)
Complete book one
Typing. Suleiman zidane kd
Whatsapp 08161272634

page 1 Daji ne mai dauke da sarkakiya,duhuwoyi,tsaunika,manyan duwatsu da manyan bishiyoyi gami da koramai iri-iri.komai yawan ayari kuma komai jarumtakar mutum idan ya shigo cikin wannan daji wanda akayi masa lakabi da DAJIN FARAUTA dole ne zuciyarsa tayi rawa,saboda kwarjininsa,da kuma irin dabbobi da tsuntsayen ciki.dajin yayi tsit ba a jin sautin komai face na tsirarun tsintsaye da kuma manyan dabbobi dake nesa ko cikin surkuki.A wannan lokaci wata jaruma ita kadai jal ta ratso cikin wannan daji,tana bisa kan doki,tayi shigar bakaken tufafi na yaki,ta goyo wata zabgegiyar takobi a gadon bayanta.Abin da xai fara baiwa mutum mamaki shine,tana ta ganin kananun dabbobi irinsu barewa,gada da sauransu amma ko kallonsu batayi sai dai ma ta ratse ta basu hanya su wuce abinsu.hakan ne ke nuna cewa bata shigo cikin wannan daji domin yin farauta ba. Kuna so ko mu canja wani?Comment pls. Anatare
.DAJIN FARAUTA.Littafi na daya[1]. Page 2. A kodayaushe tana ta hange-hange da dube-duben nesa da kusa kuma tana duban kan hanya ko zataga sawun mutum.tun safe jarumar ta shigo cikin wannan daji,kuma ga shi har rana ta fadi ba ta ga ko alamar abin da tashigo nema ba,al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalinta kenan,ta rasa abin dake mata dadi.ita dai wannan jaruma tafito ne daga wani birni da ake kira SAMLAK wanda tazararsa da wannan dajin farauta bata wuce tafiyar kwana uku ba kacal.ta fito neman dan sarkin garin maisuna YARIMA KAMSUS,wanda ya bata tsawon sati guda bisa umarnin mahaifinsa akan cewa,idan har ta sami nasarar samo shi zai bata ladan sarautar sarkin yakin birnin samlak.wannan jaruma ana kiranta da suna NASIRA,sarkin yakin birnin samlak ayanxu wani sadaukin jarumi ne mai suna HUBAS,kuma shima ya shigo dajin farauta domin neman yarima kamsus.abin dake faruwa shine an sanya gasa tsakaninsa da jaruma nasira cewar..? #Anatare
DAJIN FARAUTA LITTAFI NA DAYA (1) PAGE 3.cewar dull wanda ya samo yarima kamsus yaxo dashi,to shine zai ci gaba da sarautar sarkin yaki a birnin.tsakanin sarkin yaki hubas da jaruma nasira gaba ce mai tsanani,tun usulin iyaye da kakanni.asalin sarautar sarkin yakin agidansu nasira take,ma'ana kakanta ne sarkin yakin sai rigima ta hadashi da kakan hubas wajen neman aure,har ta kai cewa suna farautar rayukan juna.watarana sai kakan nasira ya kwanta rashin lafiya,akayi ta magani ba sauqi.a karshe sai ciwon ya zama sanadin ajalinsa,daga wannan lokaci ne gaba mai tsanani ta qullu tsakanin zuri'arsu jaruma nasira da zuri'arsu sarki hubas.duk da cewa sarautar sarkin yaqi na gidansu hubas,sai zuri'arsu nasira suka fara kokarin karbe ta da karfin tsiya,har takai ana shirya musu gasa akan hakan,amma kodayaushe su hubas ne ke samun nasara.yanxu an sami shekara talatin da hudu kenan ana yin wannan gaba da gasa don haka wannan karon jaruma nasira taci alwashin.
DAJIN FARAUTA. Littafi na daya{1} Page 4. Sai ta sami nasara ta kowone hali,saboda sai data shafe shekaru biyar tana ta neman sa'a a wajen bokaye kuma tana ta baiwa kanta horo na yaqi da jarumtaka na musamman.a zuciyarta bata da wani buri wanda yafi ta dauki fansar ran kakanta.aqalla anyi asarar rayuka na mutane goma sha hudu a tsakanin dangi biyun,hakan ne ya kara tsananta wannan gaba.wani abin mamakin shine duk wannan tsananin gaba ta tsawon shekaru allah ya jarrabi sarkin yaki hubas da tsananin son jaruma nasira,amma bai taba nuna mata yana sontaba,sai dai ita kanta akwai wani abu da ya taba faruwa wanda ya daure mata kai har sau uku.karo na farko akwai watarana daya ganta acikin daji ta fada cikin wani mugun tarko na masu farautar bayi,babu yadda zata iya kubutar da kanta.ana cikin haka sai ga masu tarko sunzo,kimanin mayaka dari.koda suka ga tarkonsu ya kama jaruma nasira sai suka kamu da matukar farin ciki suka yunkura da nufin su kamata su tafi da ita.?#
. DAJIN FARAUTA Littafi na daya{1} Page 5. Nan take hubas ya afka musu aka ruguntsume da yaki,ya kashe na kashewa sauran suka tsere.Maimakon ya kwance jaruma nasira daga cikin tarkon sai kawai yayi tafiyarsa ya barta awajen yana waigenta yana mata murmushin mugunta,harya bace mata da gani.Dakyar da sidin goshi nasira ta samu ta kwance kanta daga cikin wannan tarko.Abu na biyu daya faru shikuma wani yaki aka fita ya zamana cewa shi da itane kadai suka tsira da rayuwarsu,ya zamana cewa an kashe gabadayan dakarun garinsu.Suma din sai aka biyo su da gudu izuwa cikin daji,suka rinka gudun ceton rayukansu.Duk da cewa tsakaninsu gabace mai tsanani,sai gashi sun hada kan dole,domin idan basu hada kanba babu yadda za'ayi dayansu ya rayu.sai da suka shafe kwanaki tara acikin daji suna gudu da buya,ana farautarsu.Yunwa da kishirwa sun addabe su,ya zamana cewa ganyen bishiya da jinin kananan dabbobi ne abincinsu da ruwan shansu. #Anatare.Littafin akwai dadi kuwa
. DAJIN FARAUTA. Littafi Na Daya(1). PAGE (6). Sai da kowannensu ya sami raunika a jikinsa suka jigata ainun,har takai cewa dakyar suke iya gudu da buya.Ana cikin hakane kuma aka harbi nasira da kibiya a kafarta ta dama kan cinya.Nan take ta fadi kasa magashiyan jini na zuba.A daidai wannan lokaci ne suka hango tawagar abokan gabar kimanin mutum dari bakwai daga can nesa sun rugo izuwa kansu rike da muggan makamai suna ihu da kururuwa.cikin zafin nama sarkin yaki hubas ya suri nasira ya goya ta a gadon bayansa ya falfala da azababben gudu izuwa cikin daji.shi kansa yayi mamakin yadda ya iya wannan gudu haka alhalin agalabaice yake. Tun abokan gabar na hangosu sai da suka bace musu da gani,haka dai hubas yayi ta gudu ta cikin kwazazzabai da duwatsu har sukayi nisa sosai suka shige cikin wani kogon dutse.Anan ne ya taimaka mata ya cire mata kibiyar kuma yayi mata magani,sannan ya tafi neman abinda za suci.#Anatare.mungode.
DAJIN FARAUTA. Littafi na daya (1). Page (7). Bayan kamar rabin sa'a sai ga shi ya dawo dauke da wani katon tsuntsu,ba tare da bata lokaci ba ya fige tsuntsun ya gasashi ya ajiye a gaban nasira yayi mata tayi.In ba don nasira na matukar jin yunwa ba kamar zata mutu da ba zataci naman ba,don haka sai ta dauke naman ta kamaci,tana mai daka masa harara.Ko da ganin haka sai hubas ya bushe da dariya ya dube ta yace:ni fa ban taimakeki don ina tausayinki ba ko don ina sonki ba sai saboda bana son na rasa abokiyar gaba.Lallai ina son na ga karshen wannan gaba tamu,dalili na biyu kuma shine ni dake ne kadai muka tsira a wannan yaki da muka fito tunda an kashe gabadayan mayakanmu.Ina son mu koma gida tare domin ki bayar da labarin irin gwagwarmayar da muka yi da kuma jarumtakar da muka yi a yakin.Tabbas ke jaruma ce ta kwatance kamar yadda nima na kasance jarumi abin misali.Sa'adda hubas yazo nan a jawabinsa sai jaruma tayi masa dan guntun murmushi na wulaqanci tace.#anahadefa.
08161272634
DAJIN FARAUTA. Littafi Na Daya(1). Page(8). Tace:"kada ka taba zaton cewa duk wannan abin dakayi zai burgeni ko zaisa na daina gaba da kai,burina kawai muyi fito-na-fito ni dakai,dayanmu ya kashe daya".Ko da jin haka sai hubas ya bushe da dariya akaro na biyu yace:"sau nawa muna kwamarzuwa ni dake batare da dayanmu ya sami nasarar komai ba.A kallah mun yi yaki ya kai sau bakwai babu nasara.Ni ko ke sa'a ce kadai zatasa dayanmu ya ga bayan dan uwansa kuma kada ki manta cewa mun dauke alkawarin cewa babu shammace a tsakaninmu".Hubas na gama fadin haka sai ya koma gefe daya ya kishingida,nan da nan ya kama bacci tamkar a cikin gidansu yake kwance,tamkar ba tare da babbar abokiyar gaba yake ba.Abu na uku daya faru a tsakaninsu kuwa shine,akwai watarana da wata annoba ta rashin lafiya ta barke acikin garin samlak,mutane suka rinka mutuwa sakamakon ciwon ciki da kumallo.Duk wanda ya kamu da wannan cuta baya wuce kwana biyu a raye. #Anatare.mun gode.
08161272634
. DAJIN FARAUTA. LITTAFI NA DAYA{1}. PAGE [9]. Baya wuce kwana biyu a raye.A wannan lokaci sai da aka tara gabadayan likitoci da bokayen garin suka kasa gano maganin cutar.A ranar da jaruma NASIRA ta kamu da cutar ne hankalin sarkin yaki hubas ya dugunzuma ainun.Batare da sanin inda zaije neman maganinba,kawai sai yayi shiri ya fice daga cikin birnin na SAMLAK.Hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace,mai nema yana tare da samu,sai da hubas ya kwana yana tafiya a daji har gari ya waye ya zamana cewa rana tafara hudowa ba tare da ya hadu da komai ba acikin wannan tafiya tasa.Ko daya tuna cewa duk wanda ya kamu da wannan cuta baya wuce kwana biyu a raye sai bakin ciki ya turnuke shi don ya san cewa tabbas NASIRA mutuwa zatayi.A wannan lokaci ya iso gaban wata korama,kawai sai yaja linzamin dokinsa ya sauko.Take dokin nasa yasa bakinsa cikin koramar ya kama shan ruwa.Hubas ya tsuguna agaban koramar ya sanya hannayensa biyu.#anatare.sorry for late post.
DAJIN FARAUTA. LITTAFI NA DAYA{1}. PAGE {10}. Ya sanya hannayensa biyu ya kamfato ruwan da nufin ya watsa a kan fuskarsa,sai ya fasa sakamakon ganin wani katon kifi wanda ya nufo inda yake gadan-gadan.Batare da wani jin tsoro ba sai hubas ya tsaya cak inda yake kuma ya kura wa kifin idanu,har ya iso daf dashi.#Anatare.sorry caji nane ya kare amma gobe zan cigaba insha allah.kuyi hakuri.
DAJIN FARAUTA. LITTAFI NA DAYA[1]. PAGE [11]. Tace.to ni ce wannan tsohuwar.Ni aljana ce ba mutum ba, in da ma ka kyale ni baza a iya kashe niba.Yanzu ka fitone neman maganin cutar annobar da ta barke a garinku,domin ka tserar da rayuwar jaruma NASIRA.To ka sani cewa,ni ce na haddasa wannan annoba agarinku saboda fushin hukuncin da sarkinku ya yanke min,amma yanzu albarkacinka zan bayar da maganin wannan annoba,ka jira ni anan ina zuwa.Aljanar na gama fadin hakan.sai ta rikide ta zama kifi ta koma cikin ruwa.Jim kadan sai gata ta sake fitowa rike da wata battar ruwa ta fata,kawai sai ta mika masa battar tace,"kaje ka jeda wannan a cikin rijiyar nan ta tsakiyar garinku.Duk wanda ya sha ruwan rijiyar zai warke daga wannan cuta,kuma ba zai sake kamuwa da wata ba har abada". Ko da jin haka sai farin ciki ya lullube jarumi hubas,nan take yayi wa aljanar godiya ya kama dokinsa ya haye,ya juya da baya a sukwane yana mai tunkarar birnin SAMLAK.#Anatare.
Posted and typed: Dan Hajiya. Admin 003. No:08081162565. DAJIN FARAUTA. LITTAFI NA DAYA(1). PAGE(12). Hubas bai iso birnin SAMLAK ba sai gefin magriba.Ai kuwa yana isowa ya iske jama'a da yawa sun kamu da wannan cuta,wasu ma sun fara mutuwa.A guje hubas ya karasa gaban wannan rijiya ya jefa battar a ciki,sannan ya debo ruwa ya ruga izuwa gidansu NASIRA.Da farko sai 'yan uwanta suka tare shi don su hana shi isa gareta,amma sai ya banke su da karfin tsiya ya shiga har cikin dakinta inda take kwance magashiyan ya dura mata ruwan rijiyar a bakinta.Ai kuwa tana kurbar ruwan makurwa daya sai gashi ta mike zaune zumbur kamar bata taba yin rashin lafiya ba.Nan fa akayita diban wannan ruwan rijiya ana bai wa marasa lafiya suna sha suna warkewa.Hubas bai tsaya jiran godiyar NASIRA da 'yan uwanta ba,kawai saiya wuce izuwa fada ya baiwa sarki labarin duk abin daya faru tsakaninsa da wannan aljana acan daji abakin korama.Daga wannan rana sarki ya daina yankewa mutane irin wanna hukunci daya yankewa wannan tsohuwa.#ANATARE
Suleiman zidane kd
Whatsapp 08161272634
DAJIN FARAUTA. LITTAFI NA DAYA(1). PAGE(12). Hubas bai iso birnin SAMLAK ba sai gefin magriba.Ai kuwa yana isowa ya iske jama'a da yawa sun kamu da wannan cuta,wasu ma sun fara mutuwa.A guje hubas ya karasa gaban wannan rijiya ya jefa battar a ciki,sannan ya debo ruwa ya ruga izuwa gidansu NASIRA.Da farko sai 'yan uwanta suka tare shi don su hana shi isa gareta,amma sai ya banke su da karfin tsiya ya shiga har cikin dakinta inda take kwance magashiyan ya dura mata ruwan rijiyar a bakinta.Ai kuwa tana kurbar ruwan makurwa daya sai gashi ta mike zaune zumbur kamar bata taba yin rashin lafiya ba.Nan fa akayita diban wannan ruwan rijiya ana bai wa marasa lafiya suna sha suna warkewa.Hubas bai tsaya jiran godiyar NASIRA da 'yan uwanta ba,kawai saiya wuce izuwa fada ya baiwa sarki labarin duk abin daya faru tsakaninsa da wannan aljana acan daji abakin korama.Daga wannan rana sarki ya daina yankewa mutane irin wanna hukunci daya yankewa wannan tsohuwa.#ANATARE
Suleiman zidane kd
DAJIN FARAUTA. LITTAFI NA DAYA(1). PAGE(12). Hubas bai iso birnin SAMLAK ba sai gefin magriba.Ai kuwa yana isowa ya iske jama'a da yawa sun kamu da wannan cuta,wasu ma sun fara mutuwa.A guje hubas ya karasa gaban wannan rijiya ya jefa battar a ciki,sannan ya debo ruwa ya ruga izuwa gidansu NASIRA.Da farko sai 'yan uwanta suka tare shi don su hana shi isa gareta,amma sai ya banke su da karfin tsiya ya shiga har cikin dakinta inda take kwance magashiyan ya dura mata ruwan rijiyar a bakinta.Ai kuwa tana kurbar ruwan makurwa daya sai gashi ta mike zaune zumbur kamar bata taba yin rashin lafiya ba.Nan fa akayita diban wannan ruwan rijiya ana bai wa marasa lafiya suna sha suna warkewa.Hubas bai tsaya jiran godiyar NASIRA da 'yan uwanta ba,kawai saiya wuce izuwa fada ya baiwa sarki labarin duk abin daya faru tsakaninsa da wannan aljana acan daji abakin korama.Daga wannan rana sarki ya daina yankewa mutane irin wanna hukunci daya yankewa wannan tsohuwa.#ANATARE
Whatsapp 08161272634

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Book Chapters

2 Comments On DAJIN FARAUTA Book 1
avatar
mlm

1 year ago

Reply

Next please

avatar
ammar

1 year ago

Reply

N biyu fh

Please Login or Register in order to submit comment