You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story & Family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
Wattpad UmmuSubaya
Ina mai bawa SOYAYYA CE fans hakurin rashin ci gaba da banyiba a dalilai na tsaro
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
0⃣1⃣
"MA'U MA'U MA'U pls xo kiban littafina ai bani na hanaki yin assignment dinba, kuma ai kinsan ina baki ki copy idan har ba'a mana gargadin kada a kawo iri dayaba"
Wata yarinya ce da baxata wuce shekara 15 ba takebin wadda ta kira da MA'U itama baxata wuce 15 years dinba, tanata mata magiya
Amma ko a jikin Ma'u sai tafiarta take kamar ba da ita akeyiba hadda guntun dariarta
Palon Amminta ta nufa kai tsaye anan ta taradda Anty Jidda tana bawa diyarta Amal nono, tunda taga Ma'u ta shigo da sauri tasan akwai magana
" wa kuma kika tabo Anty Masifa" bata gama rufe bakinta ba Sukrah ta shigo kamar xatayi kuka
Murmushi Anty Jidda tayi tace
"Nasan xa'a Rina ai, Shukrah me tayi miki?"
Hawayena suka fara ambaliya a fuskar Shukrah
"Assignment nawa ta kwace wai xata kwafe kuma.tacewa Uncle namu nice na kwafe nata baicin kuma yace bayason copy copy"
Kallon bbu wasa Anty Jidda tama Ma'u wadda take tsaye ta kama kumkuminta kamar wata babbar mata
" maxa bata littafinta"
Bani Ma'u ta tura tace
" wlh baxan bataba don ban yiba kuma ban iyaba, da a dake ni daya gwara an dakemu mu biyu"
" xaki bata ko sai na tashi na babbalaki a wajen"
Ganin sarai Anty Jidda xata aikata abunda tace don tasan ba'a kawo mata wargi yasa ta fara kwadawa Amminta kira
Ai kuwa bbu bata lokaci sai ga Ammi ta bayyano
" keda wayene? Sam ba'a barin kuruwarki ya huta sai an dinga daga miki hankali"
Ssai Anty Jidda ta bata rai tasan sarai yanxu Ammi xata goyi bayan Ma'u
"Wlh Ammi kekike goyawa Ma'u baya take duk fitsarar dake, har ta isa na bata umarnin tace baxatayi ba, wlh kada kiga idon Ammi idan bakiyi maxa ki bata littafinta ba bbu Uban da xai hanani farfasa miki jiki da duka"
" uwar ubankine xata hanaki fasa mata jiki da duka kinji ko nace ni nan Asma'u uwar Ahmad ubanki ni xan hanaki fasa mata jiki da duka, littafi kuma baxata bayarba, ke kuma munafuka kinyi fuska kamar wata munina kina jira a amsa miki littafinki to baxata bayarba maxa bacemin daga part
Da gudu Shukrah ta fice tana kuka mai ban tausayi don ta tabbatar littafinta ya tafi kenan forever
A balcony Shukrah taci karo da Zahra, har xata wuceta Zahra ta kamo ta
" keda waye? Waya dakeki"
Cikin kuka Shukrah ta mayarwa Zahra abunda ya faru, ssai ran Zahra ya baci kama Shukrah tayi suka koma Palon Ammi
Nan ma sun sami Jidda nata mitan abunda Ammi tayi
Saura kiris fitsari ya kufce a marar Ma'u ganin Zahra Dodonta, bbu shiri ta koma bayan Ammi
Ita kanta Ammi tasha jinin jikinta ganin Zahra don tasan bbu abunda xai hanata karbar littafin
" to algumguma kinje kin dauko Anty fitsara taxo karba miki, to bari kiji ko uban Zahra'un kika kawo baxa'a bada littafinba"
Inji Ammi tana kara kare Ma'u dake bayanta
Ganin.tsayawa magana ma bata lokaci ne yasa Zahra nufo bayan Ammi gadan gadan don amsar littafin
Cikin karfin hali Ma'u tayi hanxari ta raba littafin gida uku ta xubar a kasa ta juya ta nufi bedroom na Ammi kamar walkiya ta shige ta rufe kofar hadda sa ki don sam bata gigin barin kofar Ammi baki saboda rana irin wannan
Marayan kuka Shukrah ta saka ta fice tabar falon gwanin ban tausayi
Takaicine yasa Jidda sabar diyarta a kafada itama ta fice
Zahra kam tsayawa tayi kamar mutum mutumi don tsabar bakin ciki, dakyar itama ta ja kafarta ta fice daga falon xuciarta na tafasa
Ita kanta Ammi jikinta yayi sanyi kujera ta samu ta xauna tana kuma godia ga Allah dayasa hakan ya faru BATURE baya gari da yau na lahira sai yafi Ma'u jin dadi
"Assalamu Alaikum"
Kamar daga sama Ammi taji Muryan BATURE ya rangada Sallama
A firgice ta juyo tana kallon bakin.kofar falon don.tabbatarda abunda kunnenta ya ji
Ba karamin raxana tayiba dataga BATURE tsaye a bakin kofar falon yana jiran amsa sallamarta
Adan kidime ta amsa tace
" jabbama Gorko amm"
Cikin takunsa na katsaita ya shigo cikin falon yana karantar yanayinta, daria ma ta basa don sarai yasan meya wakana
A bakin kofa sukaci karo da Zahra ta sanardashi abinda ya wakana
Amma ya batsar kamar baisan komai ba, xama yayi kusa da ita
" saukar yaushe BATURE"
Wayarshi ya fito dashi daga aljihun gabar rigarsa ya hau latsawa kan yace
" saukar safe, bandai shigo cikin gida bane ina can company tareda Balarabe"
Murmushi Ammi tayi tace" wato kace nina fara tokali dakai a gidan nan kenan"
Ssai ta kara bashi daria wai a nata xata buga cikinsa kenan
Kamar baxai amsaba yace " eh dake na fara haduwa"
Dadi ssai Ammi taji tana ganin yau Ma'unta ta kubuta daga ukubar BATURE sai kuma gobe wani lamarin ya bullo
Gyara xamanta tayi tace" in kawo maka furane"
Murmushi yayi a xuciarshi yace
" kin kama kanki da kanki "
A xahiri kuma yace
" yanxu kam bana jin yunwa amma kan na kwanta xanso nasha"
Mikewa yayi ya gyara wuyar rigarsa
" xan.shiga cikin gida na gaida su Umma, Ma'u ta dau furar ta kaimin part na tasa a fridge"
Bai jira cewar Ammi ba yasa kai ya fice yana murmushin mugunta
Sanin tsananin wayon Ma'u ne yasashi wucewa part din Ummi duk da bai jima da barin part dinba
Koda Ammi ta fadawa Ma'u sakon BATURE kuka tasa
" wlh Ammi an fada mishine shi yasa yace na kai mishi Allah bani kaiwa"
Rarrashinta Ammi ta shigayi
" bbu wadda ya fadamishi ai da an fada mishi xuwa xaiyi ya balla kofar ya dakaki yau ya fara balla kofarne"
Baki Ma'u ta tura don ita har yanxu bata amince da BATURE bai san da abunda ya faru ba
" to ki kai masa da kanki mana ai baxai gane ke kika kaiba tunda baya dakin"
Da mamaki Ammi take kallon Ma'u tace
"Kinci ubanki ja'ira wato fitsarar taki takai a aikeki ki aikeni"
Kara tura baki Ma'u tayi tace
"To to basai ki bawa matarsa takai masaba"
Mikewa Ammi tayi tace
" kinga rabani fa bala'in BATURE ki mike ki dau furar nan ki kai masa, ko idan ya shigo ya Tara miki jini da majina bbu ruwana"
Bbu yadda Ma'u ta iya taje ta dau furan tana mita
"Shi Ya BATURE kam ubankune da yakeyin duk abunda yaso bbu mai taka mishi birki kodon yaci sunan kakanmune? Ai cin suna ba cin girman mai sunan bane, gani nida naci sunan Ammi amma Sam bbu mai daga min kafa komai nayi sai an takamin burki"
Murmushi tayi
" koda shike nima ina kwatar yancina don bbu mai cemin kule bance ass ba"
Kamar yadda BATURE ya hasaso haka kuwa ya faru sanda Ma'u tabi part nasu Ummi ta leka don tabbatar da BATURE na wajen
Ai kuwa ddi taji data ganshi tare da Zahrarsa suna soyewa a falon Ummi, kwafa tayi ta wuce part dinsa tana cewa
" mutane sai karuwanci ido da ido ko kunyar manya ma basaji, ji inda ta kwanta a jikinsa kamar suna palonsu, suyi su koma inda suka fito ma na sheke ayata bbu kasalanda"
Janye Zahra yayi daga jikinshi ya manna mata peck a check dinta yace
" Habibty bari inje kada ka kufce min kin santa kamar walkiya take"
Daria Zahra tasa tace"
Ok Baby idan kungama dramar Ku ta tom and jerryn sai na kirani don baxan iya tsayawa Ku cikamin ciki da daria ba na kasa nuna maka yadda nayi missing dinka"
Hararar wasa ya watsa mata
" ji kamar xatayi wani abun kirki, yau dai ki shirya 7 hours service na jiranki"
Murmushi kawai tayi shi kuma ya fice son matarsa na kara shiga jikinsa
Cikin hanxari Ma'u ta shiga falon BATURE ta bude fridge taxa Furan data kawo ta juya da Saudi xata fita kawai sai taga kofa a karkabe
A raxane ta fara kewaye falon da kallon, karaf idonta ya sauka akan BATURE yana xaune kan kujera yana latsa wayarsa fuskarsa bbu alamun wasa balle tausayi ya jade cif kamar hadari
Batayi mamakiba dajin dumin fitsari yana bin cinyarta don ban yau aka fara ba
Jin abu na diga ne yasa BATURE dago Blue eyes dinsa ya xuba akan tiles yana ganin yadda fitsarin Ma'u ki diga kamar wata diyar goye
Tirkashi.................
Your
Votes
Comment
Are needed
Ummu Subay'a♥
[23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
0⃣2⃣
" xo ki xauna anan ki fadamin laifinki da bakinki"
Bature ne yayi maganar cike da umarni
Jikin Ma'u har rawa yake ta tako a hankali hawaye sai ambaliya yake a fuskarta, ga kuka nacinta amma bbu hali ta fitar don muddin muryarta ya bayyana na lahira sai yafita jin dadi
Xama tayi a gabanshi cikin rawar murya ta fara koro bayani
"Chemistry assignment book na Shukrah na dauka, da Anty Zahra tare da Anty Jidda suka matsa na bata sai na yaga littafin"
Murmushin mugunta yayi
" bari mu fara da favorite dinki Oyo mike kimin frog jump"
Hawayen Ma'u ne ya kara yawa wajen kwaranyowa, daga gani kasan batason frog jump din amma bbu yadda ta iya ta hau xagaye dakin kamar yadda ta saba, tana kuka mara sauti tana sauke ma Bature Allah ya isa kwando kwando
Mikewa Bature yayi ya nufi bedroom dinshi don kimtsawa kota kanta ma baibi ba
Bbu wani sassauci da barin falon Bature ya kawo mata don tasan akwai security camera a falon
Hawaye, Majina da gumin axaba su suka wankewa Ma'u jiki sai haki take kamar ranta xai fita, tasha wahala iya wahala
1hour later
Bature ya fito cikin shigar jallabiya daga gani shiga yayi ya kintsa kansa sai xabga kamshi yake kamar sabon Ango
Daya daga cushion dake falon ya xauna, ya dau wayarsa ya turawa Zahrarsa short text
" Baby turomin Shukrah"
Knocking da'ake a bakin.kofar falon ne yasa Bature mikewa yaje ya bude kofar
Da sallama Shukrah ta shigo ta xauna akan center carpet dake sakiyar falon tana duban Ma'u wadda anan wannan lokacin mala'ikar mutuwa kawai take jira yaxo ya dau ranta don tsabagen jikatar datayi
Bature daya dawo ya xauna a inda ya tashi
" jeki daukomin dorina a bedroom"
Ya umarci Shukrah bbu musu Shukrah ta mike ta nufi bedroom dinshi
Da rarrafe Ma'u ta iso gaban Bature ta fara rokonsa
" don girman Allah Ya Bature kayi hakuri wlh baxan sakeba, na tuba ka yafemin Allah baxan kumaba"
Shureta yayi da kafa ya watsa mata mugun harara
Bata damu da buguwar da tayi da center table ta kuma dawowa ta rike kafarsa tasa kuka mai ban tausayi
Cikin muryanta daya dishashe ta kuma yi masa magiya
Amma koya kulata ci gaba da latsa wayarsa yayi
A ladabce Shukrah ta mika masa dorinar data dauko
Bbu xato bbu sammani Ma'u taji saukar dorina a bayanta
Wani raxanennen ihu ta sake don tsananin axaba
Bbu tausayi balle imani Bature ya shiga dukar Ma'u kamar aikosa akayi
Tun tana iya ihu har ihun ya gagareta, Shukrah dake gefe toshe kunnenta tayi tana xubda hawayen tausayi
Sanda Bature ya daki Ma'u son ransa kan ya kyaleta ya mikawa Shukrah dorinar
" ki mata bulala goma"
A raxane Shukrah ta dubi Ma'u dake kwance kamar gawa tana fidda numfashi.sama sama
Kai Shukrah ta fara girgixawa tace" don Allah Ya Bature kayi hakuri wlh baxan iya ba"
" ke! Ni joke mate dinkine daxan saki abu kece baxakiyiba oya do as I said"
Shukrah sarkin tsoro jiki na rawa ta amshi dorinar ta daga a hankali ta xane Ma'u
Warce dorinar Bature yayi a hannun Shukrah ya watsa mata
Ihu ta sa tana tsotsa wajen tana kuka
Mika mata dorinar yayi da mugun kallo
Bbu yadda Shukrah tayi illah watsawa Ma'u dorinar kamar yadda Bature ya mata tanayi tana kuka
" kan na bude idona banason ganin ko inuwarku"
Bature ya fada a tsawace bayan Shukrah ta gama xane Ma'u
Da taimakon Shukrah Ma'u ta mike suka fice Ma'u kuka Shukrah kuka
Da sallama Jidda ta shiga falon Alhaji Ahmad Bature (Abba), tare ta sameshi da kaninsa Alhaji Mahmud Bature (Abbu) suna tattaunawa
Da murmushi suka amsa sallamarta, a kasa ta xauna ta kwashi gaisuwa
Shiru falon yayi nadan lokaci kan Abbu yace
" ince dai lfy Hauwa"
Cikin natsuwa Jidda ta fara koro bayani
"Daman wata shawarace naxo da ita"
Sai kuma tayi shiru saboda batasan yadda xasu dau maganarta ba
Abba ne ya katse shirun nata
" muna jinki Jidda "
Gyara xama tayi
" daman akan Ma'u, mexai hana idan Ya Bature xasu koma su dauketa taje can ta xauna a wajensu ko xata samu cikekken natsuwa da kuma tarbiya, am sorry to say a gaskia xamanta a wajen Ammi bbu wani alfanu sai kara ruguxa mata tarbiya datake, Ya Bature da Zahra ne kadai take shakka a gidan nan kuma tunda suka bar gidan ta barjin maganar kowa ta bar shakkan kowa kuma duk sanadin daurin gindi data samu gun Ammine, ina roko don Allah a duba maganata a kira family meeting don a tattauna akai"
Kai Abbu ya jinjina yace
"Tabbas Jidda maganarki dutse kuma yadda kike bukata haka xa'ayi"
Murmushin manya Abba yayi yace"
Wani hanxari ba guduba ya xamuyi da Ammi don kunsan baxata taba yadda a tafi da Ma'unta ba"
"Tun kan naxo nan nasan yadda xa'ayi da ita Abba, upper week su Ma'u xasu fara exam xan jira har su gama sai na tafi da ita a xummar xatamin Hutu, kunsan Ma'u da son yawo xata amince inyaso daga Kadunar sai na wuce da ita Abuja na danka musu ita, ita kuwa Ammi sai dai taji a slow nasan tana shakka Ya Bature baxata je ta dauko ta ba"
Harara Abba ya hurgawa Jidda yace
"Tsabagen kin rainamin uwa har xama kikayi ka tsaro yadda xa'ayi da ita "
Daria Jidda tasa ta mike tana cewa
"Abba Ammin ne sai da haka"
Abbu yace
"Sai.ki sanarwa yan uwanki, mukuma xamu sanarwa iyayenku game da meeting din sa'annan ki tabbatar Ammin Ma'u bataji ba"
Duk daria suka saka Jidda ta fice farin ciki fal ranta
Duk halin tsananin da Ma'u ke ciki bai hanata balbale Shukrah da masifa ba lokacinda taga shukrah tayi hanya part din Ammi da ita
" Uban me xanyi a wajen Ammi baicin yau da ita aka hada baki MUGU ya dakeni, ni ki kaini part din Mami"
Babu musu Shukrah tayi hanyar part din Mami da Ma'u
Mami na xaune tana kallon Sunnah TV sai ga Ma'u da Shukrah kamar daga sama, tunda ta kalli yanayinsu tasan inda xancen yake
" yau kuma meya hada tom and jerryn aka kawomin jinya"
Mami tayi tambayar tana kallon Shukrah
"Nima ban saniba"
Shukrah ta fada tana gudun bala'in Ma'u
A jikin Mami Ma'u ta xube tana kuka mai tsuma rai
Fita Shukrah tayi daga dakin tana tuna arangamar daxa'a sha kan Ma'u.ta fara mata magana don tasan gaba mai tsanani Ma'u xata shigayi da ita
" Mamana Sam bakyajin magana, kin tsan halin Bature Sam baya miki ta wasa idan kikayi laifi ai sai ki dinga kiyayewa, yanxu dubi irin lahanin daya miki kamar wadda aka turawa dan ta'adda ya hukunta"
Cewar Mami tana dudduba yadda farar fatar Ma'u tayi ja dakuma layi layin duka
"Ai wannan tafi Dan ta'adda ma Mami, yanxu idan kin bincika mugun abu tayo aka hadata da Ya Baturen"
Cewar Batool tana dake xaune kan dinning tana dinner
Mugun Harara Ma'u ta aika mata tace
" abunda kukeso kenan yayita dukata kamar jaka, to wlh baxan natsuba sai abunda ya karu, nasan kowa yanxu ya tsaneni a gidan nan Mamita ce kawai take sona"
Baki Mami ta kama tace"
Yau kuma ni Balkisu kesonki Mamata, ina Ammi kuma"
Baki Ma'u ta tabe tace" mun bata da ita don ta ita aka hada baki akamin TARKO"
Daria Batool tasa hadda shewa tace
"Yau kuma Ma'un Ammin ta bata da Ammin"
Kira Mami ta kwadawa yar aikinta Lami, ta umarceta ta kawo mata ruwan dumi a cikin roba
Daga Ma'u Mami tayi ta shigarda ita bedroom Batool kuma sai tsokanarta take don ta samu dama idan da da kafarta baxata samu irin wannan damar ba
Ruwan dumi Mami ta hadawa Ma'u ta kaita toilet tayi wanka
Ruwan duminda Lami ta kawo Mami ta daddanewa Ma'u jikinta tana mitan irin Muguntar da Bature ke mata
Sanda Mami ta tabbatar Ma'u tadan ware taja mata blanket nan da nan kuma baccin wahala ya dauki Ma'u
Idan da sabo Mami ta saba da jinyar nan don duk randa Bature ya samu xarafin dukan Ma'u wajen Ammi to tabbas ita take jinyar
Shiga toilet din Mami tayi ta kintsa kanta tajawa Ma'u kofa ta wuce turakar mijinta
Daria Zahra tasa lokacinda ta shigo falon Bature taga sai feshe falon yake da Room freshner, rumgumeshi tayi ta bayanshi tace
" hala ta aikata maka abunda ta saba"
Takaitacen Murmushi Bature yayi ya dawo da ita gabanshi yayi hugging nata dakyau yace
" ni lamarin Ma'u har ya fara bani tsoro gata da shegen tsoro ga taurin kai, baki ga yadda ya hada mata jini da majina ba kamar baxatayi rai ba amma nasan bbu abunda xai hana gobe ta sake aikata fiye da hakan"
Yana gama maganar ya dauketa kamar yat tsana ya wuce da ita bedroom dinsa
A kan bed ya mata masauki ya fara kissing dinta ta ko'ina
Dakatar dashi tayi tace
" kada na mantar dani Sweety, gobe insha Allah akwai morning meeting"
Tsaki Bature yaja yace
" bai wuce maganar dukan Ma'u bane, Ammi ko Mami suka hada meeting"
Hannunta Zahra ta sakala a wuyarsa tace
" bana tunanin haka don Jidda tacemin kada Ammi ta sani don xata dagula waje"
Baki kawai Bature ya tabe yaci gaba da nemawa kansa natsuwa
For live update follow me at Wattpad Ummusubaya
Ur
Votes
Comments
Are needed
[23/10, 01:08] Frd Din Fatima Saudia: 🏛🏛 GIDAN BATURE 🏛🏛
(Romantic love story& family Saga)
Ummu Subay'a
dedicated to
RUFAIDA OMAR
(GWANATA)
Wani abu sai ka dau wayarka ka nausa Wattpad kaga new updated na TAURARI daga GWANATA Anty RUFAIDA OMAR
Bayan ka sauko daga gajimaren dadin TAURARI sai ka garxaya sashin LAMTANA ka linkaya a kogin dadin ASABE REZA
Kana fitowa kada ka sake a barka a baya sai ka nufi WhatsApp ka shige group don KASHE FITILA na FASIHIYAR marubuciyar nan BATOOL MAMMAN
Idan ka gama KASHE FITALA sai ka Kunna FITILA don kada ka fada TARKON ZAINAB MAKAWA idan ka kuskara ka fada toh TARKON zai kaika karagar dadine daxaisa baxakasan lokacinda xakayi MUSAYAR ZUCIYA da HAJJACE ba don kaga AMFANIN SOYAYYA wajen BATOOL JATTAKO idan ka gama dasu duka xakaga ribar RANA DAYA a alkamin MIEMIEBEE
0⃣3⃣
Tushen Labarin Gidan Bature
Dr Lingard haifeffen London ne, Blue eyes dinshi shi xai tabbatar maka cikekken Baturene gaba da baya
Yaxo Nigeria ne cikin volunteers Doctors da ake dibowa daga England xuwa Nigeria a Congola aka turashi
Bbu xato bbu sammani ya fada soyayya da Asma'u diyar Sarkin Yola
Ba'a samu wani tangarda ko tashin hankali ba Mai martaba Sarkin Yola ya aurawa Dr Lingard aure da Asma'u bayan ya karbi Kalmar shahada
Saboda Mai Martaba ya yaba da kyawawan halayensa
Ta bangaren iyayen Lingard da labari yaje musu nan take suka sallamashi duk da shi kadai suka Haifa
Cikin shekara 10 Allah ya albarkaci Dr Lingard (wadda 'yan uwan Asma'u da jama'a suka lakaba masa Dr BATURE) da Asma'u da yara uku
Ahmad
Mahmud
Muhammad
Bayan Dr Bature yayi retire daga aiki sai ya shiga cikin business gadan gadan inada ya mallaki company da dama kuma ta ko'ina kudade nashigowa
Ba'a jimaba sunanshi yayi shura a Nigeria
Kaduna yaje ya buga tamfatsetsen estate na alfarma xubin gidan turawa wadda a bakin gate akasa BATURE ESTATE
tattara iyalansa yayi suka koma Kaduna da xama
Dukkan yaran kammanin Asma'u (Ammi) suka dauka xubin Fulanin asali ko farar fatarshi fat basu daukaba amma kam fararene farin Nigeria
Rana daya Ahmad da Mahmoud sukai aure kasantuwar sun tashi kansu daya
Ahmad ya auri Fateema diyar kawunshi wan Ammi
Mahmud kuwa Hauwa ya aura diyar Governor Kaduna na lokaci
Fateema macece mai kirki bbu ruwanta,