Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin wani daban, the way yadda takira sunan yamasa dadi, yace "yes "
Rumaisa tace "baka sallah, sannan kuma baka tunanin lahirarka, kadauki duniyar nan kamar wani gidan jindadi, kamanta cewa a koda yaushe zaka iya mutuwa kuma kakoma ga Allah, mezaka fada masa idan kaje garesa, zaka fada masa cewa shan giya da neman mata shiya hanaka yin salla, bazaka iyaba, a ranarma bakinka bazaiyi magana domin baki zai iya shirya karya, sassan jikinka sune zasuyi magana wadanda kasan dacewa kana aikata barna dasu, fahad kaiba yaro bane, kamallaki hankalin kanka, yakamata kagyara zamanka da uban gijinka" nadai tashiga karoro masa nasihohi daban-daban...

Jikinsa yayi sanyi sosai, ajiyar zuciya yayi sannan yace "shikenan naji, zan daina komai, indai har hakan zai sakaki farin ciki, ya kara kallonta yana murshi kafin yace "amma namanta komai kikoyamun yadda zanyi"
Dadi sosai rumaisa taji,

Acen kasar zuciyarta tace yes my mission started,...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10:43am, 09/08/2016]
_Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

45 and 46
Via *OHW*
_A love story_💝

kallonsa tayi tay murmushin tace "shikenan zan koyama"

Shima murmushin ya mata,

Zafin kafarsa yakai masa ko ina yayi yunkurin tashi, sai a lokacin rumaisa ta lura da jinin dake fita a kafarsa,

Tace "subhanallah, jin ciwo kayine" ya girgiza mata kai,

Oh sorry" tafada tana kokarin taba masa kafa, da sauri ya janye yana kallonta yace "babu kyau macce tataba kafar daba ta mijintaba"

Rumaisa ta kallesa tayi murmushin tajidadin maganar har cikin ranta tace "babu shamaki gaduk wadda zai tamakawa musulmi dan uwansa a duk lokacin da yake cikin neman taimako, dan haka idan har taimakonka zanyi babu laifi idan natabaka"
Fahad yayi dariya yace "ok shikenan" ya miko mata kafar ta kama ta matse jinin daya taru a ciki sannan tamike taje toilet ta dibo ruwam zafi a heater tazo tana gasa masa kafarshi, tana dan kara yimasa bayanin akan addini,

Haka dai harta kare, sannan tatashi taje tashirya musu breakfast, bayan sun gama suka dawo falo suka zaune tafara kowayar abubuwa, ranar tasaki jiki sosai dashi,

A ranar babu inda yafita yana gidan har yamma tayi, kuma ya koyi abubuwa dadama daga gurin rumaisa,
****** ***** ****
Allah sarki majnoon,
Majnoon nagani a rakube a gefen tati yana kakkarwar sanyi, duk ya rame yakara fita hayyacinsa,

Duk da babu hankali a tatare dashi amma dai yaji rashin zuwan rumaisa gurinsa, yashiga da muwa sosai amma babu wadda yadamu dashi balle yasan damuwa sa, yanzu yama soma daina yawan wasar nan da yara, burin shi kawai shidai yaga Rumaisa. ..

ALLAH SARKI SOYAYYA...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:43 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

47 and 48
Via *OHW*
_A love story_💝

*Bayan kwana biyu*

Zarah ce zaune akan gado, tadafe kanta tana hawaye, edonta duk sun kumbura, tasha kukanta mai isarta,

Turo kofar d'akin nata akayi akashigo da gudu, bata d'ago kantaba ballema tasan waye yashigo, illadai taji shigowar mutum,

Yarinyace yar kemanin shekaru 10 tashigo d'akin tana murna, tafada kan gado inda zarah take, "anty zarah, kingafa abbanmu yasayimun game boy" tafada tana nunawa zarah game din,

Zarah ta d'ago edota ta kalleta tace "Feena kije nagani banason damuwa" tafada a kasale

Feena tana kallon zarah, tagane kuka take tadan bata fuska tace "anty zarah kuka kike, me akayi miki, mamace ta miki laifi ko Abby"

Zarah ta share hawaye ta tadan langawabe kanta kadan tana kallon feena "basu bane, kidai nace kije kibari anjima zamuyi magana"

"Faisal ne koh?" Feena tafada tana kallon zarah, zarah ta zare ido tana kallon feena cike da mamaki, tayadda akayi tasan faisal, saikuma ai bazatayi mamakiba domin tana yawan bata labarinshi, bata san lokacin da data girgiza mata kaiba, feena ta tsuke fuska "waishi faisal dinnan duk lokacin da kikaje gurinsa saiya sakaki kuka, ni gaskiya anty zarah kidaina zuwa gurinsa, kima rabu dash.." bata karasa maganar ba zarah ta toshe mata baki, tana girgiza mata kai a lokacin har hawaye sunzo mata ta dora kanta akan feena tana fadan "bazan iyaba feena, wlh bazan iya rabuwa dashi ba, kee bakisan MIYE SO ba, shiyasa kike fadan na rabu dashi, I lov him feena, I lov him...." takarasa maganar tana kuka,

Feena ta tausaya mata sosai. tasa hannu ta share mata hawaye sannan tace "anty zarah malamin islamiyarmu yace duk abinda mutum keso toh yakai kukansa a gurin Allah insha Allah allah zai shere masa hawaye, anty zarah mezai hana kifadawa Allah damuwarki"
Zarah tayi murmushin yake tace "ngode sister na, nagode sosai, tashi kije inason na kwanta"

feena ta mike daga kan gado tanufi hanyar fita tana tana juyo tana kallon antynta, harta fita tabar dakin, zarah takara fashewa da kuka....

**** **** **** ****
Kwanan umma biyu kenan a station tayi baki dukta kode, tasha wuya sosai,

Yanzu dai kam abba yagane ba umma bace ta sace rumaisa, domin da ace ita tasaceta data fito da ita kodan wahalar datasha,

Abba duk ya fita hayyacinsa, 'yarsa k'waya daya tilo tabata, anyi nema har an gaji, dole akaje aka bawa malamai adu'a akan sutayasu da adu'a ko Allah zaisa aganta, tafito a duk inda take ,

Abba kullum yana station idan baya station to yana gida amma kwata2 yadaina aikin komai, komai nasa yatsata cak, tashin hankali yashiga sosai, zuciyarsa cike da danasanin abinda yayiwa rumaisa,

Yauma Yana zaune a station yana tunani2

Zunbur ya mike kamar wadda aka tsigala, dasauri yafita yabar office din, yashiga motarsa, ya kunna yahau hanya gudu yake sosai, harya karasa unguwar da ya saba ganin rumaisa....

wace unguwaceee...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:44 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

49 and 50
Via *OHW*
_A love story_💝

Unguwar da majnoon yake zaune, daidai gurin daya zo yasami rumaisa ranar anan yaja birki, yana tsaya yana kallon unguwar, yana jan nunfashi,

A gefen wani gida ya hangi majnoon a rakube, yayi wani irin zama kalar tausayu..

Dasauri abba yafito daga cikin motar yanufi gurinsa, yana karasawa ya gurkusa yazauna kusa dashi edon abba sunyi ja sosai, yadube majnoon sai kuma yasaukar da kansa, yanayinsa yabashi tausayi cikn sanyi murya yace " ina rumaisa"

majnoon yayi saurin dago kansa yana kallon abba, saikuma ya mike tsaye yana kokarin barin gurin, abba yayi saurin shiga gabansa " magana nake maka ina rumaisa" majnoon ya ture abba daga gabansa yacigaba da tafiyarsa, ran abba yasoma baci kara shiga gaba majnoon ya runtumo kwalar rigarsa yadaga murya sosai yace "kai inaima magana ka kashareni, ina kakaimun rumaisata, wallahi saika fito mun da ita saboda komai yafaru da rumaisa kaine sila, abba yakara jinjiga kwalar rigar majnoon yana fadan " ina rumaisa..." yafada yana hawaye, nan take mutane suka taru a gurin suna kokarin babbare majnoon daga hannun abba, shidai majnoon uffa baiceba, sai mazurai yake da edo, abin tausayi duk ya rama,

Abba yana kuka yake fadan " karku barshi yatafi wlh 'yata yasacemun, 'yata tana wurinsa kuce masa yabani 'yata" mutane suka rirrike abba, wasu kuma wasu kuma suka rike majnoon..

daya daga cikin mutanen yace " haba Alhj yazakace mahaukace yasacemaka yarinya, meyasani waddama koshi kansa baisaniba ballema harwata 'yarka, kaidai kaje kanemi wadda yasacema 'yarka amma ba wannanba"

nan kaji mutane gurin sunce "gaskiyane wannan bazai iya sace maka 'yaba " wani matashi yana rike da majnoon yace " wannan mahaukacin yau kwanansa biyu kenan ko wasa yadainyi da yara, kullun yana rakube a gefen titi ko agefen unguwa, gaskiya wannan bashi yasace maka 'yarka ba, kaje cen kanemi wadda yasace maka 'ya"

Abba yace "wlh shine.. wannan ne " yanuna majnoon, mutane suka ce a fa bashi bane, abba kuwa yayi juyin duniya suka koki bashi gaskiya, mutane suka rikesa suka kaisa har bakin motarsa suka sakashi, sannan ya kunna motar yabar unguwar yana kuka, soyayyar 'ya da mahaifi kenan....

**** *** *****
Faisal kuwa duk ya rame abincima kadan yakeci bai wuce a yuni yaci abinci saudayaba, koshi dandai momy na matsa masa ne, ammashi kwata kwata bayajin dadin abinci,

Faisal yana zaune a falo yana kallo bayan dawo daga gurin aikinsa dagashi sai singlet da 3cutr yadora kafarsa kan dani table dake tsakiyar dakin ya jingina jikinsa a jikin kujera, kallo yake amma hankalinsa kwata2 baya gurin yana gurin tunanin rumaisa, gaggar jikinsa ce kawai zaune a gurin amma zuciyarsa bata tare dashi,

Momy ce tafito daga cikin dakinta, ta ganshi saune yayi kuru da edo yana kallon tv, tayi murmushi sannan takarasa gurin tazauna tana kallonsa takira sunansa har sau biyu taji yayi mata shiru, bubbuga kujerar tayi sannan ya zabura yana kallonta " momy" yakira ta yana kikarin yin murshi, yaushe kikazo nan "

momy tayi ajiyar zuciya tana kallonsa tace " taya za'ayi kasan nazo, tunda kadauki damuwa kasaka kanka aciki, wai mekakeson kazamane faisal akan soyayya duk kabi ka susuce, jibi yadda karame sai kace bakaiba"

Faisal ya tsuke fuska, shiko yawan magana yanzu bayaso, shidai yafison kummul abarsgi alone, yace " menayi kuma umma, nifa ba ita nake tunaniba, kawaidai ina kallone"

Momy taja nunshi tace "duk yadda kaso kaboye damuwarka, bazaka iyaba domin fuskarka da jikinka zasu bayyana hakan, kiyi kokarin saita kanka faisal"

Faisal yasaukar da kafafun daga kan dani table di yana kokari saka takalminsa, yace "nifa babu abinda ke damuna momy, ni baccima nakeji " yamike tsaye momy ta bishi da kallo haryabar falon, ta girgiza kanta zuciyarta cike da tausayin yaronta, akan soyayya duk yabi ya susuce...
****** ******** ******
_One day later_

Rumaisa ta koyawa fahad abubuwa sosai kuma sun shiga kansa, yanzu yasan yadda zaiyi sallaj aduk lokacin dayaji ankira sallah,

hankalinsa yasoma dawowa kansa, rumaisa tasakashi harda siyo littattafan addini, (kujimun samun guri irin na rumaisa) yanzu kam tasake dashi sosai,

Yauma suna zaune a falo, tana koya masa adu'oi, tasaki jikinta da gidan kamar gidansu, daman cen a gidan nasu ba wani farin ciki take samuba, yanzu kuwa tasamu freedom,

Kallonta yakeyi kamar zai hadiyata ita kuwa kanta na kasa tana karan ta masa littafin dake gabansa,

Saidai ta lura da hankalinshi baya gurin sannan ta dago kanta tana kallesa taga ita yake kallo, ta kida masa masa hannu da sauri ya zabura, yana murmushi, itama murmushin tayi tana kallonsa tace " littafi zaka kalla baniba"

Fahad ya girgza kai "tohm malama" murmushi tayi sannan taci gaba da karanto masa,

Shidaikam yagaga daina kallonta domin akoda yaushe kara shiga masa rai take, sha'awarta makil take a duk wani sassa na jkinsa..?...aha

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:44 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

51 and 52
Via *OHW*
_A love story_💝

Da yamma fahad yakira duk wani ma aikacin gidan suka taru a falon, rumaisa tana zaune a gefen kujera tana jiran taji maizaice, kowa a falon yayi tsit yana jiran yaji me fahad zaifada,

Fahad yayi gyaran murya yace "daga yau nabawa rumaisa damar shiga ko ina agidan nan amma banda fita, dan haka karkowa ya hanata zagaya gidan nan, yana kallonsu yace " ina mai gadi " mai gadi ya leko.kansa daga cikin taron ma aikatan yace "gani oga "

Fahad yace "toh kaji abinda nace ba, karka kuskura kabarta tafita" mai gadi yace "toh"

fahad yanisa yace "toh shikenan kowa yatashi yakama gabnsa" nan falon ya watse rumaisa dake zaune duk tasha jinin jikinta, a zuci take fadan watoshi wannan baya mada niyar sakina nan , lallai kuwa akwai matsala, bazan dawwama anan ba yazama dole inje inga majnoon, shima wannan zaman danake dan kaina nakeyi, kuma domin in gyarawa fahad rayuwarsa ta yadda zaiji dadin rayuwa koda bama tare dashi..

Maganar sace ta katse mata tunani yana fadan "yanzu kinsamu freedom a gidan nan dan haka saikiyi abinda kikeso"

kai kawai rumaisa ta daga masa sannan tatashi tanufi dakinta yabita da kallo, tafiyartama burgeshi take,

Sai da tashige dakin sannan ya furzar da iska, yatashi yanufi dakinsa, yazauna bakin gado zuciyarsa cike da wasu wasi kalla2 , dafe kansa yayi sha'awar rumaisa tasoma fin karfinsa ta yadda bazai iya hana kansa aikata abinda yaso akan taba,

Yana zaune cikin wannan yanayin yaji anturo kofar dakinsa, dasauri yadago kansa yana kallon kofar, rumaisa ce tashigo dakin da littafi a hannunta, murmushi ta sakar masa suns kallon juna tace " kamanta da littafin nan ne a dakina shine nace bari nakawoma ko zakayi bitarsa, murmushi yayi yace "ok kawomin"

Taku takeyi tana kokarin karasowa gurinsa, shikuwa edonsa na akan kirkijinta, tana karasowa ta mika masa littafin, da sauri ya cafki hannunta, ya lumshe edo, yana sosar hannun
Jikin rumaisa yadau rawa, taga edonsa sun fara rikidewa, murya na rawa ta furta " sakeni na wuce daki "

Fahad ya dubeta a lokacin duk tsigar jikinsa tatashi, dasauri ya mike ya tsaya daf da ita kamar zasu hade fuska yace " rumaisa kinunamin soyayya mana, a koda yashe kece muradain raina"

Yafada yana kokarin sanyata jikinsa, rumaisa ta na kokarin kwatar kanta tana fadan "meye kuma haka Fahad ko kayi haukane"

Fahad yace " eh rumaisa nayi hauka indai akan kine, rumaisa I need you, plcxx" k'akk'ameta meeta sosai yayi a jikinsa yana shakar nunfashin ta, rumaisa ta soma kuka " dan Allah kasakeni natafi"

fahad yan nishi yace " rumaisa bazan iya bane sha'awarki zata illatani rumaisa kiyi helping dina plx dan Allah kosau dayene muyi sex"
rumaisa ta tureshi daga jikinta,

Tana kuka take fadan "bazan iyaba fahad, nayi zaton karatun damuke da zaman da mukayi dakai yasa kacanza halinka ashe bahaka bane, makeson zamane fahad, nidai wlh bazan iya baka kainaba amma nasan banada karfi dazan iya hanaka abinda kake sonyi dani, a duk yunkurina so nake naga na gyaraka koda Allah zaisa sonka yashiga zuciyata, amma kai baka gani wlh fahad tir dakai" ta tofar da yawu tana kuka,

fahad yayi tsaye yana hawaye, bazai iya gujewa sha'awar dayake yiwa rumaisa ba, cikin muryar kuka yace " sau dayafa rumaisa, daga wannan wlh bazan karaba sai idan munyi aure plx"

Rumaisa ta dafe kanta tana mamakin wannnan wane irin mutum ne, baya tsoron Allah ko kadan, baya tunanin makomarsa a gobe jiyama, cike da hargowa tace "bazan aminceba fahad, kuma walh bazan aureka matukar baka gyara halayen kab.. kuka ya hanata karasa maganar, kuka take sosai, cikin kukan taci gaba dacewa " matukar ina raye bazan barka kakusanceniba, ta nuna kanta da dan yatsa tana kuka tace " kazo kakasheni fahad, kazo kakashine dan ka sami abinda kakeso a gurina" takarasa maganr tana kuka sosai,

Fahad ya fa juye2 a cikin dakin kamar wani mahaukaci yayi ihu yadaki ganin dakin yana fadan " bazan iyaba rumaisa, bazan iya kashe kiba Rumaisa, kece hasken idanuwana"

yana gama maganar ya juya gefen gado ya hangi makullan motarsa karasawa yayi yaje yadauko makullan sannan yafice yabar dakin yana hawaye,

Baifi minti biyu da fitaba taji kukan motar sa yafita yabar gidan, dasauri tatashi tana kuka tanufi dakinta, tashiga tamayar da kofar dakin ta rufe tasa key, saboda tana tsoron kar yaje yasha giyarsa yazo yasameta,

Sannan tafada kan gado tana kuka, Zuciyarta cike da bakin ciki yanzu duk abinda ta koyawa fahad tayi abanza kenan, lallai kuwa wannan bazai taba shiryuwaba, yazama dole ta dauki mataki, tayi kokarin barin gidan tun kafin ya cimma mummunan kudurinsa akanta,

Tambayar kanta take to ta inama zata fara ...

Oho...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:44 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

53 and 54
Via *OHW*
_A love story_💝

A ranar kaf har dare fahad bai dawo gidan ba, haka ta kwanta tayi baccinta cike da fargaba,
Washe gari
Tatashi bataji motsinsaba, tafito taje har dakinsa bata ganshiba, hankalinta yasoma tashi, ta zurawa lamarin Allah edo,

Haka har yamma tayi baidawo hankalinta yatashi sosai duk ta sukukuce, takasa yin komai, sai taji gidan duk baya mata dadi saboda baya nan,

Misalin karfe 10:03 na dare tana rakube akan kujera cikin falo tana jiran dawowar fahad, amma taji shiru, gangadine yafara dibarta, bata ankaraba bacci yayi awon gaba da ita,

11:00 fahad ya dawo gidan, yanayin bude motarsa kawai nagani nace akwai matsala domin kuwa da karfi tsiya ya turo kofar,

Sai kuma naga yana fitowa a hankali, yana tangadi kamar zai fadai ko ba a fadamin ba nasan giya yasha yayi mankas domin ko tsayi gagara yi yayi yana tangadi yafadi sai kuma yagagara tashi,

Bodyguard dinda ke tsaye a bakin kofar suna kallonsa sukazo gurin, " oga lfy"

Cikin murya irin ta yan maye fahad yace " kudaukeni kukaini ciki"

Yadago musu hannayensa, ba musu suka rika hannayen suka dagashi sama suka sark'afahi suka nufi cikin gida dashi,

A falo suka sami rumaisa tana bacci, duk da acikin maye yake amma hakan bai hanashi ganin rumaisa a kwanceba, yacewa bodyguard din "ita wannan metakeyi anan" dayan bodyguard din yace "bacci take oga" fahad yayi gyatsa kamar zaiyi amai sannan yace " bacci,,, bacci, ya fada cikin salon kasala, sai kuma yace "to kuma kuje kuyi bacci, ni kubarni anan nima anan zan yi bacci"

sukace "toh oga" suka karasa dashi bakin kujera daya suka ajiyesa sannan suka fita suka wuce dakinsu, koba komai yau zasu Huta da tsaron wannan mashayin...

Yadade a kwance kafin yayi yunkuri iya karfinsa sanna yasamu ya mike,
tangadi yake sosai da kyar ya iya yakarasa gurin rumaisa, yayi gyatsa kamar zaiyi amai,

Sautin gyatsar yaratsa kunnen rumaisa da sauri ta farka ta ganshi a kanta, yana mashalo, cike da zafin nama ta mike, edonta duk suncinciko da kwalla, tana kallonsa, wannan bazai taba shiryuwaba, a zuci tafad'a, duk ta firgita, yazu kam tsoron fahad take domin yazamo ibilis, mutum bayajin nasiha,

fahad dake tangadi yace "zonan Rumaisa" rumaisa ta makale kafad'a tana shirin yin kuka,

Fahad yace" bazaki zoba, toshikenan bara nazo ni" yayi taku daya zuwa biyu yana kokarin karasawa gurinta tangadi ya hanashi sandin cafet din yajasa yafadi rakwassss a gurin daidai dani table din da ke tsakiyar falon yafadi, dani table yarabu gida biyu,
Rumaisa ta toshe bakinta takara tsorata ganin fahad kwance cikin glass,

A hankali takira sunansa, taji shiru, dafe kai tayi ta rosa kuka tace na shiga ukku"

Dasauri ta nufi hannyar fita domin yanzu ba bodyguard ko daya agurin, takara bakin gate tana kuka a lokacin mai gadi yafito, da fitila a hannunsa" hajiya lafiya, yana fada yana dalla mata fitilar

Rumaisa tace " fahad zai mutu yana ciki" takarasa maganar tana kuka,

Mai gadi ya tsorata sosai, dasauri yace " hajiya yana ina" rumaisa ta nuna masa kofar shiga falon " yana ciki"

Mai gadin baijira takara magana ba ya zura da gudu yanufi cikin falo,

harta daga kafa zata bisa, saikuma ta tsaya cak, zuciyarta na harbawa tara2, yau gata a bakin gate, kuma ita kadai, ai kuwa bazata watsar da wannan damar ba, dole tabar gidan da sauri takarasa wurin key din kofar tana kokarin budewa, cikin sa'a kuwa yabude, ta tura kofar tafita waje, unguwar shiru kake jinta, tsoro yakata jitakeyi kamar ta koma cikin gidan, wata zuciyar tace "ina ai komai tsoron da zataji gwara tatafi" tayi tsaye a bakin kofar tana kuka.

tambayar kanta take, to ina kuwa zata je, kalaman mahaifinta ta tuna nacewa zai mata aure da faisal kotanaso kobataso, hakan yasa taji batason zuwan gidan, toh ina zataje,

Kakarta tafadi mata a rai, mahaifiyar abba, gurinta zataje domin tana da tausayi sosai kuma tana son rumaisa,

Tohm amma kuma ba'a garin takeba a sokoto take, taya za a yi tasamu motar sokoto a yanzu cikin daren nan, ta tsaya tana nazari...

jin mai gadi yafito yana kiran hajiya! hajiya!! a cikin gidan ta kara firgita, mai gadine yana kokarin fitowa waje..

Rumaisa tace kafa menaci banbakiba, nan ta famtama da gudu tsiya tabar kofar gidan ta ratsa unguwar cikin duhun dare...

Mai gadi na fitowa yaga babu hajiya, kuma kofar gidan a bude abin, yadafe kansa yafashe da kuka, domin yasan dacewa gudu tayi, yafito waje yaleka yaga babuta babu alamarta, kuka yafarayi....

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:45 PM] ‪+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*😃

55 and 56
Via *OHW*
_A love story_💝

*NOTE* _ina mai baku hakuri, saida nayi typing ya goge hakan yasa nayi wannan a gurguje, sai kunyin hakurin ganin correcting mistakes, ngd_

"Nashiga uku, yanzu idan oga yatashi yasan dacewa hajiya ta gudu wlh zai iya illatani,wlh bazan zauna a gidan nan ba, dole inje innemota, idan kuwa ban sameta bazan dawo gidan nan ba" mai gadi yafada, Dasauri yashiga dakinsa yafara hada kayansa yana kuka,

saida yagama hada kayan kaf sannan yafito, cike da tsoron kar wani yagansa, ya sulale yafita yabar gidan,

Rumaisa kuwa sharara uban gudu kawai take, ita kanta batasan inda takeba, ballema harta samu hanyar zuwa sokoto,

Daidai wani layi ta karyo kwana, karnuna na kwance a gurin sunaji gudun mutum, suka tashi suka fara haushi, a daidai kwanar tayi kicibus dasu,
Cike da tsoro da fargita ta famtama ihu, daman dai tuncen rumaisa tsoron kare take,

karnukan sukaji ihu ta, ai kuwa nan suka biyota, cab bata mayi guduba yanxu tafarashi domin wani masifaffen gudu danaga rumaisa nayi, nikaina banzaci zata iya yinsaba, gudu take tana kuka, Wani irin sabon karfi yazo mata, su rumaisa anga mutuwa... lol😝

Karnukan na biye da ita suna mata haushi, ita kuwa tana gudu tana kuka ratsa unguwar kawai take bata masan inda takeba, tana cikin gudun kawai jitayi tafada ciki wani rame fancamm!!! saida bakinta yadaki gabar ramen, bakin ya fashe da jini, duk jikinta ya goge, ta duke a kasan ramen tana maida nunfashi,ta toshe bakinta duk da zafin dayake mata amma a haka tadaure, saboda batason karnukan suji kukanta,

Karnukan sukazo gurin sai haushi suke amma basu gantaba, suka yi tsaye a gurin suna sintiri, saida suka gama zagayensu sannan suka bar gurin, saida taji gurin yayi shiru sannan ta saki bakinta shanshekar kukanta kakeji sannu2,

Sai a lokacin tasamu natsuwar duba ramen data fad'a, da kyal ta mike tsaye tana hawaye, duk jikinta ciwo,

Irin ramun nanne na gefen titi, (lamba 2) tana daga kanta kuwa sai taga titi, wata irin ajiyar zuciya tayi tana nishi,

Da gyar ta iya kama bakin ramen, tafito tahau titin tayi tsaye, tana kallon titin gefe da gefe, tsif kakejin tati babu ko motsin lade, a hankali tafara

2 Comments On MAJNOON
avatar
hafsat-muhammad-5

11 months ago

Reply

Amazing

avatar
hafsat-muhammad-5

11 months ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment