Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba kafin yasake nad'a maki wani dukan?"

Dai dai bakin shiga rumfar tasu ta tirje tana kuka had'e da fad'in. "Ni bazan fita harkarsa ba Ina sonsa, kuma ai keda baffa kunce zaku kaisa wajen malan bakada imani asa mashi soyayyata ya akayi har yanzu baya sona, ni bazan yarda ba kawai yau akaishi wajensa a d'aura mana aure gobe bana son aurensa qarshen shikarar nan don wallahi waccan munafukar zata iya aura masa fadeela gashinan sai faman tura masa ita akeyi tana shisahige masa.."












*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___29πŸ’Ž

Bayan tagama tayi gyatsa had'e dayin hamma sannan yace.

"Habiby bacci?"

"Kuma?" Yafad'a yana kallonta, kashe electric d'in tayi sannan tajuyo ta d'ora kanta saman qirjinsa tana sake sakin wata hammar akaro na biyu ta sake cewa."bacci nakeji."

Muje nima shi nakeji, Nuraddeen yafad'a tare da sunkutarta yanufi d'aki da ita, cikin muryar dake nuna baccin takeji sosai tace. "Habiby jiyafa tsoro aka bani a falon nan!."

"Kamarya habibty, tsoro anan falon Kuma? to sai Kikayi qaqa." Yafad'a tare da direta saman gadon, Saida tasaki wata hammar sannan tace. "Addu'a nayi."

"Shine baku tasheni ba yafad'a yana kwanciya bayanta tare da jawo masu mayafin lullubinsu ya lullub'esu, cikin nauyin baccin dake d'ibarsa take basa labari shikuma yana isar da saqonsa ba tare daya fahimci sauran abubun da take fad'a masa ba har ya cimma burinsa, gyara kwanciyarta tayi yace. "Yihaquri Bari muyi wanka tukuna saikiyi baccinki" daqyar yasamu ta tashi suka tsarkakikke jikinsu sannan suka koma sukayi kwanciyarsu.

Kamar yanda Nuraddeen ya fad'a haka akayi, ya sanarwa baffa da cewa ya samoma Rashida maganin macijin ciki dana basir take fama dasu, da baffa yasamo yazo ya gyarasu Inna Bilkisu na gefe tana gyaran ayarta ya miqo mata, "ungo maganin nan ki kaiwa yarinyar nan Rashida tun shekaranjiya Nuraddeen yafad'amun tana fama da matsalar macijin ciki da basir asamo mata, to bansamu shiga dajin ba sai yau, wannan ganyen dafashi zatayi tasha, shi kuma wannan sassaqen ta dakesa sai tarinqa sha tare da hura ko kunu, yarane basuda aiki sai cin maiqo ALLAH dai ya kyauta."

Dariya tafaryi had'e da cewa, "yanzu shi nuran yafad'a maka cewa tana fama da basir da macijin ciki?"

"Haka yace mun mana tunda tana yawan bacci da cin abinci sosai bini bini yace taji yunwa, ai kinga wud'an matsalolin ke damunta ko kuwa.?"

"Ikon ALLAH, malan kenan sake dai tunani, ai akwai d'ayansu dake iya haifar da irin wud'an matsalolin koma fiye dasu, be cemaka yaga tana haskeba ka had'o mata da maganin shawarah ba?" Inna Bilkisu taqarasa maganar dariya na kuccikke mata cike da mamakin Nuraddeen daya kasa gane matarsa nada ciki, kodon yaga ALLAH yabata lafiyayyene, shiru baffa Usman yayi na tsawon mintota kafin yagano inda zancen Inna Bilkisun ya nufa, murmushi yayi irin nasu na manya sannan yace. "To.to..to haka ankayi? Masha ALLAH, ubangiji ALLAH ya inganta, ja'iri zaisa in tafkawa kaina b'arna."

"Ai kuwa dai, Ina ruwan malan Nuraddeen, to bai d'au hannu ba shiyasa." Tafad'a tana dariya.

Daidai lokacin Nuraddeen yafito sashensa yayo inda Inna Bilkisu take a hirgitse,

"Inna Bilki Rashida ce ba lafiya tun jiya da daddare take fama da zazzabi mai zafi yanzu haka gata can sai amai take faman yi ko za'a kaita asibiti ne?" Kallonsa baffa Usman yayi had'e dayin murmushi cikin xolaya yace. "To ko dai macijin cikinne yataso mata Nuraddeen?"

"A'a inaga dai wannan karon qila shawara ce ko?" Inna Bilkisu tafad'a tana kallonsa, "Inna Bilki inaga itace ko akwai sauran maganin da baffa ya d'ebowa fadeela kwanakki abata har zuwa anjima inga ko zamu samo aron mota muje asibiti..."

Bai qarasa ba Inna Bilkisu tace "Kai don ALLAH rufemun baki, ba don dai nasan kayi boko ba da nace maka takkwali kuma Mai qaton kai" tana gama fad'a tanufi sashen nasa baffa Usman na dariya ya shige d'aki suka barshi tsaye yana bitar kalaman Inna Bilkisu, can ya zaro idanuwa cike da mamaki har yana rufe baki yabi bayanta da sauri don samun qarin bayani cike da jin dad'i.

Kwance ta iskota saman kujera mai zaman mutum uku cikin bargo sai rawar sanyi takeyi, sannu tayi mata sannan tajuyo ta kallesa tana fad'in, "yanzu kai Nuraddeen kan shirin zama baba amma har yanzu akwai wauta atare da kai, tana cikin wannan hali tun jiya ko ince kwanakin baya amma ka kasa kaita koda nan chemest ce adubata sai kira mata basir da macijin ciki kakeyi?"

Cikin jin kunya yashiga sosa k'eyar kansa yana sissinne kansa qasa, murmushi tayi kafin suga Rashida tamiqe tayi waje da gudu da d'an sauran qarfin da take dashi, da sauri yaje ya kamata tana kwarara amai tamkar zata amaye hanjinta, ji yakeyi kamar yayi kuka ko ya maido da ciwon ajikinsa saboda tsantsar tausayinta, rungumota yayi gaba d'aya ajiki yana zuba mata sannu jikinta duk yayi yaushi, ruwan daya ajiye gefe abokiti ya d'iba ya wanke mata bakinta sannan ya d'agota tamkar 'yar baby ya maidota d'aki tana sakin lumfashi da qyar, gaba d'aya ya mance da zancen Inna Bilkisu awajen sai daya gama gyara wajen yakoma cikin d'akin tace.

"Idan akwai 'yan ruwan zafi ka d'ebo mata ka lallab'ata tasha ko kad'anne in sha ALLAH Aman zai tsaya, bari naje nadubo maqwabcinnan namu idan motarsa nanan kayi masa magana kuje asibit, sannu Rashida sai hanquri Kuma yanzu har lokacin da ALLAH yarabaku dashi lafiya, ALLAH ya inganta kuma yaqara sauki."
Tana gama fad'a bata jira me zaice ba tafito tazari hijab d'inta, baffa Usman ta tarar bakin gida zaune ta sanar dashi halin da ake ciki, cikin sa'a mutumen nana yajawo motar Inna Bilkisu ta taimaka masa aka fito da Rashida, har zata bisu baffa Usman yace a'a tadawo taje can cikin gida ta sanar masu da halin da ake ciki, su kuma yace su wuce idan akwai buqatar wani yazo to yakira sai Inna Bilkisu tabiyosu a baya tunda nan cikin garine ba nesa ba.

Suna isa nan take aka d'ebi jininta don ayo mata gwajin ciki bayan an bata taimakon gaggawa irin nasu na qauye, tashin farko ana aunawa a kaga tana d'auke da ciki har na tsawon wata hud'u da sati d'aya, duk da Nuraddeen yasan da haka tun gida da Inna Bilkisu tafad'a masa Amma bai gasgata hakan ba sai yanzu da likita ya tabbatar masa, tsabar farinciki ji yakeyi yau tamkar ya take kan jariri sai faman washe haqora yakeyi yana yiwa yiwa likita godiya, likita kam abun har dariya ya soma bashi ganin yanda gaba d'aya murna da farinciki suka rud'ar dashi,.
Girgiza kai yayi yana dariya yace "malan Nuraddeen wanna irin farinciki haka inaga haihuwar farko ce za'ayi maka ko?" Murmushi yayi yana sosa kai likitan yaci gaba da cewa

"Ahhh.. Masha ALLAH Ina tayaka murnar zama fresh baba, ALLAH ya inganta."

"Amin Dr. nagode sosai" Nuraddeen yafad'a yana miqa masa hannu cike da farinciki.

Takardar magani da ruwan da za'a qara mata da allurai ya miqa masa yana fad'in. "Amma zakuyi haquri zuwa nan da anjima koda za'a sallameku don tana buqatar qarin ruwa sosai, ALLAH yaqara sauqi"

"Amin Dr mungode" Nuraddeen yafad'a tare da ficewa daga cikin d'an office d'in nasa.
A can gida kuwa koda Inna Bilkisu ta sanarwa da Yaya hawwa dasu Inna ruqayya babu wacce ta nuna tadamu acikinsu don duk a tunaninsu aikin bokansu ne yafara aiki, tana fita sashen Yaya hawwa ta kece da dariya tana fad'in. "Wani aikin sai malan bakada imani, ba kince ke taurin kaiba yarinya, anturo maki su mutsibbata da janjabilu su tsorataki yanda bazaki iya zama a d'akin ba sunce kinfi qarfinsu, anturo maki ashiq ya shiga jikinki amma yayi duk shawaginsa da dubarunsa shima ya kasa, na dasa na binne don ashiga tsakaninki da d'ana ya dakeki muhuta duka shima mun kasa nasara saboda baqin naci irin naki, shiyasa nace ayi maki mai kankat aturo maki mugun ciwon da zaisa kidinga wari kina sakin quraje dole ko baiso ya gujeki, kuma da dukkan alamu malan bakada imani yasa munyi nasara a kanki wannan karo, shegiya tsigitsila sai kinbar gidannan tunda bana ubanki bane, ba inda zanje ALLAH ma yasa kimutu.
Haka kuwa akayi har marece yayi aka sallamota babu wanda yatafi daga cikinsu inba baffa Usman dasu Aysha da fadeela ba saboda Inna Bilkisu ta tsaya yin girki da gyara gidan sai Kuma yusuf d'an baffa Ali,
Allah sarki baffa duk ji yayi ba dad'i da aka sanar dashi halin da take ciki, yaso ace lafiya take da babu abunda zai hanashi kai jiki asibitin, duk da yanzu sanadiyar addu'ar data bashi yanayi wata ran kuma tayi masa ko kuma baffa Usman yayi masa yafara samun sauqi sosai, Yaya hawwa kuwa sai yakwan biyu baiga ko qwayar idanuwanta ba, Inka gata tazo wajensa to wasu tarako cikin 'yan uwa dake zuwa dubasa ko intake karb'ar kud'in da zatayi abincin da zataci duk da kuwa ko yaushe Rashida na kai mata idan tayi.
Addu'a yayi mata sosai akan ALLAH yabata lafiya yanajin wata irin qaunarta na ratsa zuciyarsa musamman ma da akayi masa albishir tana d'auke da juna biyu, sai yaji kamar ya taka saboda tsantsar farinciki, nan yasa aka kira masa Nuraddeen yace kada yasake yafad'awa kowa cewa tanada juna biyu koda mahaifiyarsa ce har sai cikin yafito, haka ma Inna Bilkisu da baffa Usman duk ya roqesu su b'oye wannan sirrin na jikansa domin komai zai iya faruwa dashi idan har wani abun ya Sami yarinyar da abunda ke cikinta. Baffa Usman dama ba mutumne mai surutu ba ita kuma Inna Bilkisu tafi kowa son a b'oye zancen cikin gudun kada acutar da ita.

Bayan an sallamosu sun dawo gida baffa yasa su baffa Usman suka riqasa yaje har d'akinta yayi mata ya jiki, akunya ce ta amsa yayi mata addu'a tare da gargad'inta akan cikin sannan suka mai dashi, yanda take d'an miqewa yana d'an aza qafafuwansa a qasa shi zaisa kana kallonsa kasan ya samu sauqi sab'anin da dako tashi tsaye baya iyayi balle har ya iya aza qafafuwansa a qasa, dudduqe yake kuma bai iya miqewa tsaye koda an riqasa, Amma yanzu cikin yardar ALLAH yana miqewa yayi tafiya idan anriqasa saidai baya aza qafafuwan da kyau ya taka qasa shiyasa mutanen gidan keta kallonsa cike da mamaki suna jero masa sannu.

Satinta d'aya cikin d'aki tunda aka salla mota bata fitowa ko bakin qofa tana jinyar jikinta don har yanzu bai koma daidai ba bata son cin komai sai fura da kwad'on zogale hakan yasa tadena girki don ko qamshinsa bata so, Inna Bilkisu kullum cikin sayen ganyen zogale take a b'oye tana aika mata dashi haka baffa duk yafita sai ya sawo mata damammiyar fura tasha nono, abunka da qaramar yarinyar dake taka matakin farko na cikar girmanta mace nan take suka karb'i jikinta ta murmuje tayi haske abunta, bata aikin komai saboda fadeela da aysha keyi mata share share da wanke wanke, shi Kuma Nuraddeen shike kula da gyara mata d'akinta da wankanta, sosai yake bata kulawar da baya barin kowa shigowa sai idan aikowa akayi ko kuma cikin matan gidanne sukazo dubata da jiki shima d'in sai ya tabbatar ya saka mata hijabi tukuna yake cewa su shigo.

Yaya hawwa kam ranar tunda safe ta shiga sashen daga tsakar gida tana qwalla masa kira da sauri yafito had'e da duqawa yana gaisheta, kallonsa tayi tun daga sama har qasa ta mere baki had'e da cewa.

"Sannu bawan mata, wai ita har yanzu bata warke bane?"

"A'a innar mu da sauqi dai."

"Mtssa to ni nagaji da d'ora sanwar nan Ina jiran aminci don yau zanyi baqi, sai ka sanar da ita don kada ab'ata mani lokaci."

"To innar mu."

Yafad'a jiki a sanyaye yana mamakin wannan hali na mahaifiyarsa, tun ranar da abunnan yafaru tsakaninsa da muneera har zuwa ciwon Rashida bataxo sashen ba balle tazo ta dubata, amma yanzu rashin kai mata abinci na sati d'aya yajawo tazo tana qorafi akai, muryarta ya tsinkayo daga tunanin daya tafi tana fad'in. "Kaji ko."

"E.eh innar mu."

Nuraddeen yabata amsa da sauri cikin i'ina, Jan tsaki tayi tare da kallon qofar d'akin Rashida ta cije baki had'e da girgiza kai sannan tabar wajen, jiki sanyaye yabar wajen shima yakoma cikin d'aki yana kallon Rashida dake baccinta hankali kwance batare da tasan ma wainar da ake toyawa ba,

K'arar wayarta dake ruri yasa ta motsawa had'e da bud'e idanuwanta suka sauka akan fuskarsa, murmushi yayi tare da mik'a mata hannu yariqota ta tashi zaune sannan ya d'auko wayar dake sake ruri akaro na biyu ya miqa mata, murmushi ne ya bayyana a fuskarta lokacin da idanuwanta suka sauka saman screen d'in wayar ta kalli Nuraddeen tace.

"Laaaa..Habibi baba ne."

"To kid'auka mana kada ta tsinke." yafad'a tare da miqewa yabar d'akin yana tunanin abunda yakamata ya dafawa Yaya hawwa tunda ko kad'an Rashida bata son qamshin girki shiyasa ta denayi, shi kansa saidai yanemi ruwan tea yasha ko kuma yaci abincin da Inna Bilkisu ke aiko mata dashi.

Cikin jin dad'i Rashida ta d'aga had'e da gaisheda mahaifin nata da tuni labarin tana da ciki ya isa kunnensu...






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

_Hi fan's am so sorry akan yanda kuka matsu mukoma asalin labari, Karku manta ita SANNU SANNU bata hana zuwa..no matter how matuqar ALLAH yabani aron lumfashi da kuma rayuwa zan sadaku da farkon labarin da muka faro, karku manta *baku san ko waye Abu sumayya ba?, bakusan asalinsa ba? taya ya had'u da matarsa batool shima baku sani ba? meya jawo batooul tabar iyayenta har na tsawon shekaru bakwai? Shin Abu sumayya ya cancanci mutuwa adaidai lokacin da yakamata yasan ko waye mahaifinsa?, meyasa mahaifin batoul ya sheganta shi, Shin batool itama ta cancanci ta fuskanci jarabawar da take ciki adaidai lokacin da take d'okin sake had'uwa da iyayenta?* πŸ˜…Inada yaqini akan shima baku sani ba kuma bakuda duka amsoshin wud'annan tambayoyin, wannan waiwayen tushen labari da mukayi shi kad'ai zai amsa maku duka wud'annan tambayoyi kuma da sannu ya sadaku da farkon labarinku, saboda haka kujuri zuwa rafi na tabbatar ranar da tulun zai fashe na nan zuwa🀣Ina matuqar godiya bisa yanda kuke qaramun k'warin guiwa ta hanyar comment d'inku, nakanyi farinciki kuma na nishad'antu da hakan akoda yaushe, FILLAH INA SONKU OVERπŸ’‹πŸ˜_


Page___31πŸ’Ž

Har Nuraddeen zai wuce yadawo yayi tsaye yana jin maganganun dake fitowa daga bakin muneera, tun daga farko har qarshe babu abunda baiji ba yafito ransa a'bace yana watsawa Inna ruqayya da tayi tsuru tsuru da idanuwa tana 'yan kame kame wani irin mugun kallo da yasa cikinta murd'awa, nunata da yatsa yayi yace.

"Wai ni za'a kai wajen wani malami ko boka don in so wannan abar?" Yaqare maganar yana nuna muneera sama da qasa da hannu, murmushin gefen baki ya saki cike da takaici kafin yaci gaba da cewa. "To wallahi Inna ruqayya koda matan duk duniya zasu qare bazan tab'a auren muneera ba Kuma badon bana sonta ba sai don kawai kinzamo mahaifiyarta, duk da 'yar uwata ce ita bazan iya aurenta ba har duniya ta nad'e don haka idanma mafarki kukeyi to wlh kufarka kunema mata mijin daya dace da ita, wannan Nuraddeen da kike gani in sha ALLAH mallakin Rashida ne ita kad'ai, zuciya da kuma ruhi gaba d'aya natane bana tunani ko a mafarki kwakwalwata zata aminta da shigowar wata azuciyata ko wacece ita ciki kuwa har da muneera d'in da kuke qaqabar 'yar uwata ce domin bare tagama mani komai aduniya.." wata irin qara muneera tayi had'e da ciyo kwalarsa tana kuka, "wallahi ya nura baka isa ba, don ka kawai aka halitto ni bazai yuyu na auri wani inba kaiba.." Bata qarasa maganar sanadiyar wani zazzafan mari daya d'auketa yana kallon wuyar rigarsa data riqo, qafa yakai zai hankad'ata tayi saurin duqewa wajen tare da riqe masa qafafuwa tana kuka, "don ALLAH ya nura karka damu da inna, kafita batunta da halayenta ni kai nake so, zan zauna da kai ko mata nawa zaka aura amma karka yimani hukunci akan halin Inna ita da baffa sune basa son matarka haka ranar naji suna fad'a wai Inna hawwa takaita wajen malan bakada imani za'a dinga turo mata aljanu suna tsoratata, yanzu haka ciwon da takeyi sune sukasa yaturo mata shi.." baya baya Nuraddeen yayi kamar zai fad'i saboda tsorata da kalaman dake fitowa daga bakin muneera, duk da dai ciwon da Rashidarsa keyi ba irin wanda take nufi bane amma maganarta akwai qamshin gaskiya aciki idan yayi la'akari da tsoron da Rashida kecewa ana bata da Kuma yawan firgitarta acikin barci, kasa cewa uffan yayi har saida Inna Bilkisu dake tsaye cikin rumfarta tana sauraronsu ta matso wajen ganin yanayin daya shiga ta dafashi tana fad'in. "Karka kuskura ka amince da wannan soki burutsun na muneera kasan halinta da shirme, idan kuma har gaskiya take fad'a to kada ka tsorata domin da wannan tsoron naka za'ayi amfani wajen cutar da kai da kuma matarka kayarda ba mai yimaka sai ALLAH kuma Babu wanda ya isa ya cutar da kai sai abunda alqalamin qaddara ya rubuto akanka, maza kawuce kaje wajen iyalinka ba abunda zai sameku in sha ALLAH tunda kun riqe ALLAH, sharri shi Kuma d'an aikene duk inda kaje zai dawo ya sanar maka."

Taqare maganar tana kallon Inna ruqayya da tsabar kunya tasa tayi wuri wuri da idanuwa tana faman susar wuyanta.
Wasu zafafan hawaye yaji son zubo masa wai ace qiyayyar da mahaifiyarsa keyima matarsa har takai ga za'a iya had'a baki da ita acutar mashi da ita don d'ai cikar burin wasu, cikin zafin rai ya dubi Inna Bilkisu yace. "Inna Bilkisu me yarinyar nan tayi masu da suke nema su cutar da ita, nine fa d'ansu duk wani abu na mataki daya kamata su d'auka akaina ya dace ba itaba." Girgiza kai Inna Bilkisu tayi had'e da cewa.

"ALLAH dai ya kyauta, kawai kashiga ciki in sha ALLAH babu abunda zai sameta."

"Munafuka! aikin kenan ko yaushe sa ido, to Ina ruwanki tunda duk abunda akayi d'in da sanin mahaifiyarsa ita data haifesa, meye naki nasa baki, ke kuma shegiya mai baqin baki kamar aku da yaushe akayi haka? wato ke uwar soyayya zaki qaqaba mana sharri tsakar rana, tashi muje yau sai kin gane kurenki" irin borin kunyar nan Inna ruqayya tafara wud'annan suruttan had'e da rufe muneera da duka tana janta,

"Dakata Inna ruqayya! ku gaggauta zuwa kusa a kwance qullin da akayi maku akan matata idan ba haka ba duk abunda yafaru da ita to sai nayi shari'a daku.." kafin yarufe baki yaji saukar wasu zafafan marora har biyu a fuskarsa, Yaya hawwa ce da tun d'azu da taji muneera ta sako baki tana zuba tafito tayi tsaye tana qare masu kallo ta sakar masa wud'annan marora bazato ba tsammani, cikin d'aure fuska da rashin tsoron duk abunda zaije yadawo tace
"Don buhun ubanka dake kwance anyi qullin kuma baza'a kwance ba kayi duk abunda ka iya, inkaga dama kaje koton duniya ni hawwa bana tsoron uban kowa akan wannan tsigalalliyar yarinya bare daka auro mani, Kai nifa nagaya maka natsani matarnan tun wuri ka rabu da ita ko agaban idanuwanka insa ta walaqanta, shashashan banza da wofi har kace zakayi shari'a damu akan bare." tunda Nuraddeen ya soke kai qasa bai d'ago ba sai hawaye dake faman kwarara daga idanuwansa, yarasa wannan wace irin qiyayya ce mahaifiyarsa keyi ma Rashida da har Bata shakkun kowa akan zata iya illatata.

'Dago kansa yayi yana kallon Yaya hawwa yace. "Innar mu kiyi hak'uri, aurena da Rashida muqaddirine daga ALLAH, Ina sonta sosai shiyasa nakasa haqura da ita tun farko, don ALLAH ko donni ki daure kisawa zuciyarki soyayyarta, inada yaqini akan zakiyi alfaharin samunta a matsayin suruka, kigujewa wannan mummunar al'adar da kike tunanin daidace kada ta jefaki cikin fushin ALLAH."

"To saketa idan kana so kada nashiga cikin fushin ALLAH, idan bahaka ba nayi maka baki ka lalace." Taqarasa maganar tana gyara tsayuwarta da d'aurin zanenta,

"Haba Yaya hawwa meyayi zafi haka keda d'anki, ai idan kikayi kuskuren yimasa baki damuwar akanki zata fad'a, don ALLAH da girmansa kiyi hak'uri kibar yaronnan tunda yana son matarsa, yaran zamani da kike gani bad'ai suke dana da ba zaifi kibarsu suyi rayuwarsu yanda sukesu ke Kuma iya naki kibisu da addu'a," Inna Bilkisu tafad'a tana kallon Yaya hawwa cike da girmamawa.

"Bilki."

"Na'am Yaya hawwa."

"Bilki." Yaya hawwa ta sake fad'a akaro nabiyu tana kallonta, itama ta sake amsa mata kamar d'azu.

"Ya isheki haka babu ruwanki da d'ana, kifidda bakinki a wannan maganar saboda ba huruminki bane, ni nahaifi d'ana baruwanki ko yankasa zanyi shishshigin naki ya isa haka kina jina, idan kuwa ba haka ba zan zageki tass awurinnan nayaga maki rigir mutunci ba abunda yadameni, ke kike da abun fad'i agari bani ba don haka bar wajen nan tun wuri kinaji na ko?"

"ALLAH yabaki haquri." Inna Bilkisu tafad'a tare da barin wajen zuciyarta cike da tausayin Nuraddeen, wata irin gud'a Inna ruqayya tasaki had'e da cewa, "su uwar gulma andaiji kunya idan ansanta, sai aja tsomakaran qafafuwa asani inda akayi yau shishshigi baiyi rana ba." Bata tankata ba tawuce abunta Yaya hawwa tajuyo tana kallon gefen da Inna ruqayyace take tace.

"Ai kece babbar uwar gulmar kuma zan dawo ta kanki."
"Kai nadawo gareka zaka saketa ko kafiso sai naga walaqantata agidannan."

"Innar mu don ALLAH kada kirabani da Rashida Ina matuqar sonta."

"Maida son akan waccan mai idanuwa kamar na mujiya koba komai 'yar uwarka ce" Yaya hawwa tafad'a tana nuna muneera dake jingine ajikin k'arfen rumfa ta takure waje d'aya, wani irin shu'umin murmushi Inna ruqayya ta saki tana ayyana abubuwa aranta, cikin katsa tsawa taji tace masa.

"Ka saketa nace.." duqewa yayi agabanta yana fad'in "innar mu kiyi hak'uri bakina bazai iya furta wud'annan kalaman agareta ba."

"Bazaka sake tab'a saina tsine maka?." Tafad'a tana qoqarin bud'e baki ta tsine masa, da gudu Rashida dake lab'e tafito ta durqushe agabanta itama tana hawaye.

"Don ALLAH kada ki rabamu innarmu, kifad'i duk abunda kike so zamuyi amma kada kirabamu ko don albarkacin abunda ke cikina."

Rashida tafad'a tana kuka, wani irin mugun kallo yaya hawwa tabita dashi tana kallon yanayinta da d'an cikin daya taso kad'an ajikinta kafin tace....





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___32πŸ’Ž

Buhun uba mezan gani haka?, Munafukan ALLAH dama cikine dake ake yimani rufa rufa agidan nan? tirqashi to idan tunaninki yabaki cewa wai cikin dake jikinki nada wata kima ko daraja awajena da har zai iya dakatar dani daga qudurina to kinsha qarya, dake har wannan abun dake cikinki bana sonku bana qaunar ganinku, don haka kai kasaketa kaji nafad'a maka kafin raina yab'aci" Yaya hawwa tafad'a cikin zaro idanuwa tana kallon Nuraddeen da izuwa yanzu gaba d'aya qasusuwan jikinsa sunyi sanyi, ga wani irin zazzab'i daya ji yana shirin taso masa, a hankali ya d'ago kai bakinsa na rawa yace. "Innar mu kidubi girman ALLAH kada kirabani da Rashida, wlh zan iya mutu idan kika rabani da ita, nayarda bakya son Rashida amma abunda ke cikinta bai kamata ki k'isa ba saboda jinin kine kuma jinina."
Tana bud'e baki tayi magana taji muryar baffa da tun d'azu yake yaqar

Please Login or Register in order to submit comment