Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo sae in masa
magana !!!...
*_MARYAM..._* Diyar liman ce wanda yace bara ya dauki
Huda ba amma asali bashine ya haifeta ba agolace a
gidan ....saboda Mugun Halin Matarshi ya hanashi daukar
Huda !!....Hajiya zubaida itace uwar maryam ...su biyune
ya'yanta ...daga Maryam sae Abdallah kaninta ....Shi
liman Allah bai taba bashi haihuwa ba har yanzu ...kuma
bai taba damuwa ba !!,..Kullun tana sanye cikin
zunbuleliyar hijab ...a fuskarta kamar sahila amma
azuciya sam babu tsoron Allah ...idan ta saka hijab a
unguwarsu tana fita daga unguwar zata kira saurayinta
yaxo ya dauketa ....duk wani club dake garin babu wanda
Maryam bata zuwa ....yar' bariki ce ta k'in k'ari ....
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_41 to 42_*
Duk unguwar kowa zai shedeta mutuniyar kirki ce
....mamanta kadae ta san irin rayuwar da take ...shima
don tana kawo mata tsabar kudine ....ko da rana Daya
liman bai taba fahimtar abunda ke faruwa ba a gidan ...!!
Bayan da ubanshi ya dawo hajiya ta mashi magana aka
fara nemawa Barister shehu auren Maryam ...
Wata Biyar aka saka bikin ...ko da yaje gidansu
Maryama bai samu matsala da Ita ba ...ta amsheshi
hannu bibiyu ...
Lokaci na zuwa aka daura auren ...an kashe kudi
sossae ...don ko lefenta set biyar ne ..Gidansu Huda
Barister Shehu ya saka a rushe suka hade da nasu ...aka
dibarwa Amarya nata part din !!! ...
•• •°°•• •
"Huda kira man Auntynki "...ya fada tare fa sauketa
daga jikinshi ...
Uncle ...
Hannunshi ya saka saman lebenta tare da nuna mata
kofa ...
Ta lumshe ido kamar yarda yayi sannan ta tafi da gudu
...Hanne na kwance tana waya tana fadin ...
"Wallahi kawata na gaji da wannan shegiyar yarinya
...Ni kawae zance ya sawake man na tafi gidan iyayenshi
idan ta tafi ya maidoni"
tayi shiru tana saurarenta ..
kafin tayi dariya tana fadin ..."Haba kawata ya za'ai yanzu
na iya zama kauye ...ai sae dae gidan iyayenshi " ...don ni
da kauye hai hata hai hata ....Ke nifa tunda nazo ba
abunda ya shiga tsakanin mu .....abun har ya fara
damuna kawata "
"Aunty idan kin gama wayar Uncle na kiranki ...amma
dan Allah kicewa shegiyar kawarki ina da baba ...itane
shegiya bani ba ..!! ..idan kuma ke kika ce man shegiya to
...Allah ya isana !!!
Bata jira amsarta ba ta kwasa da gudu ....
Tarota yayi yana fadin "Bara ki bar gudu ba ko
Huda ? ...baran sake goyaki ba !!...
"Sorry Uncle na rantse maka da Allah na daina ..kaji
...!!!tayi rau rau da ido ..
Hannunsa ta kamo ...Uncle wae idan Aunty Hanne ta
tafi kauye tana da tsayayyene? ...
Dariya yayi kasa kasa ..." Ban gane ba Huda !!!
"Yauwa ...Ina nufin tana da wanda zai aureta ...?..
zaunar da ita yayi saman hannun kujeran .."Me ya faru
Hudah ?..
"Kawae Uncle ka saketa mu zauna mu kadae
,,!! ..Kaji ? ...ta fada tare da langwabe kai ..
Murmushi yayi kasa kasa ...kafin ya dago fuskarta yace
.."Idan na saketa ke zaki aureni "..?
"Eh mana ...ko yanzu ma ai ina aurenka Uncle ...tunda
ni da aunty muke tsare maka gida ...kai kuma idan ka
dawo ka dafa man abinci ko ..?
Hanne ta shigo tana fadin
"Wallahi munafuncin wannan Huda kullun k'ara yawa
yake ...banda muguwar fata ni kike fadar a saka ?...Idan
an sakeni Uwarki zaa aura?,..
Look Hanne !! ...ya daka mata tsawa ...wallahi kar na
kuma jin kin zagi wannan yarinyar ..."
Bata ce komae ba ta zauna tana hararan Huda ....
"Ki shirya gobe ..ko kinki ko kinso ..da safe zamuje
kauye a gano kawu ..!!
" To dan Allah yaya ka sawo man wanan safar ta leda
mai kama da takalmi ... "
Cikin Mamaki yace "me zakiyi da ita ?
Dan dukar da kai tayi tana fadin.."Wallahi yaya baran
iya taka dattin gidan mu ba yanzu ...bana son kazanta
...!!!
Dariya sossae yayi ...ba tare da yace mata komae ba
yaja hannun Huda ...Kin tafiya tayi ta tsaya gurin ..
Muje mana !!
" Uncle ba kace zaka goyani ba ?...ta fada a hankali ...
Murmushi yayi ...ai ba yanzu nace ba ko? ...ya dage gira
....
Kafada ta make .."Yanzu mana " ..
"To naji ...zoki hau muje ..." ..duk abunki iyakarki toilet
zan direki !!!
Shegiya ...hanne ta fada a hankali ...
Gwalo ta mata tana hura hanci ..tare da zaro ido ...
a harzuke Hanne tace .."Zanci Ubanki Hudah "...
Mahmoud ya juyo tare zabga mata harara ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_Yaseen mutane ma sun maidani yarinya ...to wallahi
am not a kid ..kyas nake kallonki ...wae na bata un edited
copy taza duba man ..yo Fathern ki ya man typing😂😂😂😂😂_*
*_43 to 44_*
Karfe biyun rana suka isa kauyen ..lokacin anata
haramar shiga masallaci ....Mahmoud alwala yayi ya
shige masallaci ya barsu Hanne zasu shiga cikin gidan ..
Hanne ta tattare Zaninta sama tana yatsina fuska ...ta
shiga gidan ...da gudu kaninta ya taho yana fadin ...
"Ga Hanne Ga Hanne ....."
Da sauri taja baya tana fadin ..."tsaya tsaya boy
...dontu touchi mai wallahi _dont touch me_ "
Sakin baki yayi yana kallonta tare da tsayawa jiki a
sanye ....Hudah ta kura mata ido tana dariya kasa kasa
....Hanne na lura da Hudah ta zabga mata harara tare da
jan karamin tsoki ....
Inno ta fito tana washe baki tare da lale marhabun ...a
dakile hanne ta amsa sannan ta isa tabarmar da inno ta
shinfida ...dank'walin kanta ta cire ta shinfida saman
tabarmar sannan ta zauna....ko da inno ta kawo masu
ruwa a kwano ...cewa tayi Hudah ta tashi ta dauko mata
swan water a mota don bara ta iya shan ruwan randa
ba!!....
Hudah bata amsa mata ba haka kuma bata tashi daga
inda take ba ..!!
Basu dade ba Hanne ta azalzalesu suka fito ...a mota
banda Dariya ba abunda Hudah ke yi ...Hanne kuwa ta
gama k'uluwa don sae Hudah ta kalleta ta madubi
sannan ta tuntsire da dariya ....Shi kanshi Mahmoud ya
fara gajiya da dariyar Huda ...ta madubi ya kalleta yace ..
"Dariyan me kike Haka ne ?
"Ba komae Uncle " ...ta fada tana toshe bakinta ...
ganin ba daina dariyar zatayi ba ya sakashi daure
fuska tare da juyowa ya dan kalleta ...
"ko ki daina dariyan nan ko na bata maki rai Hudah!!!
Sorry Uncle na daina kaji .!!..Benen gidansu aunty na
gani yake ban dariya don yana bukatar Faci ...gudun
zuwan kawayenta !! ...Uncle Na rantse maka da Allah
aunty ba karamar makaryaciya bace ...kasan me take
fadawa kawayenta !!
.
"Bana son ji Hudah " ...ya fada tare da daure fuska
"To uncle baran fada ba ...amma kasan ko ..? Cewa
kawayenta take idan sunzo wae babanta mai kudine
kuma gidansu ya ma fi naka kyau ...kuma kasan?
Kallon da ya mata ne ya sakata natsuwa ....Hanne kuwa
rufe ido tayi kamar mai bacci !!
•••°°••
Rayuwa kenan ..Barister Mahmoud na zaune da
Amarya maryam lafiya kalau ...sae dae kwata kwata
maryam bata ma hajiya magana ...ko gaisuwa bata
hadasu ...kullum tana part dinta ...Idan hajiya ma ta aika
maryam din tazo ...sae dae tace "aje a fada mata ba
zamanta take ba ...don haka bara tazo ba .!!....
Barister Shehu na zuwa zata fada mashi ..
sae dae yace mata. " ai laifin ki ne hajiya ...ta yaya
yarinya na zaune dakinta zaki aika ta zo? ...
Sae dae hajiya ta yi shiru don bata da abun cewa .....
Shekaransu daya dae dae suka haifi diya mace
kyakykyawar gaske mai suna safina....daga barister
shehu har maryam suka dauki son duniya suka daurawa
yarinyar ..haka hajiya ma da dad duka suna kaunar
yarinyar sossae....kullun sae Hajiya ta aiki yaron dake
mata hidima ya dauki Safina ya kai mata ....Tun maryam
na badawa har ta fara fadan bara ta dinga bada
yarinyarta ba ana zuwa a wahalar da ita .....
Ranar hajiya har part dinsu ta shiga tana fada ...ta iske
Maryam zaune bisa cinyar Shehu ...maimakon ta tashi
daga jikinshi sae ma kara shige mashin da tayi ...
Nan Hajiyar ta dinga balai...idan kujeran dake falon ya
amsa to Maryam ta amsawa hajiya ....
Barister Shehu yace "haba hajiya taya zaki zo ki sa
yarinyar mutane gaba kina zagi ....bayan ita ta haifi
yarinyar nan ...gaskia bana son abunda zai bata wa
Honey rai ...don haka kawae ki fita ...ni zan mata magana
duk sati sae a dinga zuwa ana daukar maki ita ...!!!
A fusace ta fita daga part din ...Haka rayuwa taci gaba
duk sati zaa dinga kai safina Part din Hajiya ta wuni a
dawo da ita ..wani sa'in ma hajyar daki take shigewa ta
barwa yaronta yana mata wasa ....
Yarinya bata cika shekara Daya ba cikinta ya fara
kumbura ....tun suna daukar abun da sauki har suka lura
kullun kara hawa cikin yake ...gashi duk abunda diyar
taci sae ta amayar dashi ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_Na Feedohm_*💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_45 to 46_*
Asibiti suka kaita ...duk wani abu daya kamata amata
ana mata ...daga karshe doctor din ya gane cewa ruwan
sperm _maniyi_ ne ya taru a cikinta ....
Daga Maryam har Barister shehu sae da hankalinsu ya
tashi ...
Taya zaa ce ruwan sperm sun taro a cikin yarinyar da
bata kai 1yr ba ...haba doctor bara ta yiyu ba ...ka dae
sake dubawa ...!! barister shehu ya fada a firgice ..
Doctor yace ..."abunda muka gani kenan ..
amma idan baku yarda ba kuna iya sake wani asibitin
sir"..
Kusan asibiti uku suna zuwa amma abunda aka fada
bai canza ba ....kansu ya shiga duhu ...to ina safina ta
samu ruwan sperm ? ...tambayar da kuke ta wa kansu
kenan ...!!
Gida suka dawo a firgice ...part din hajiya suka nufa
...a iya saninsu babu inda ake kai safina sae gurin hajiya
...Barister shehu yayi wa Hajiya bayani ...itama cewa tayi
bata yarda ba , ba yarda za'ace yarinya karama sperm ya
taru a cikinta. ..to ina ta samesu? ...amma a kira yaron da
ke dauko safina din ...don wata sa'in gurinshi take
barinta idan bacci ya dauketa ....
Yaron aka kira ....tambayarshi suka fara yi ...yarda ya
rude ya saka suka gane baida gaskia ...da yaga barister
Shehu ya dauko wuka yace zai kasheshi idan bai fadi
gaskia ba ..
Sae cewa yayi wae ..Stick dinshi yake saka mata a baki
tana tsotsar mashi !!! ...
Kukan kura barister shehu yayi ya makari yaron ..yana
duka tare da fadin Allah ya isa lalata mashi d'iya ...sae ya
kasheta ...da dae yaron ya samu ya kwace daga
hannunshi sae ya ruga da gudu ...dama ba garin yake ba
...zuwa yayi almajiranta hajiyar ta daukeshi ya dinga
mata hidima ....
Babu irin neman da barister shehu bai mashi ba amma
duk a banza ...ko wanda ya sanshi bai gani ....Sae dae aka
cigaba da bata magunguna har Allah yasa cikin ya koma
dae dae ...
••°°••
"Hudah bara ki canza ba "...
" Uncle zan canza wallahi ...kaga nama canza ai .."...
Hanne ta fito zata raka bakuwarta ...Huda ta fara kukan
akuya ...take jikin hanne ya fara kyarma ...don dama
Hudah ta saba mata wannan tozarcin gaban kawayenta
...
Allah Allah take kar Mahmoud yama Hudah magana
...abunda taji yana fada ne ya sa cikinta murdawa ...
Hudah meye Haka ? ..
Sae dae Hudah ta kalli Hanne sannan tace " Uncle kukan
akuyar gidansu Aunty hanne nake tunawa.. wannan
wadda aka daure kusa da bangon toilet dinsu? da
katangar ta kusa ruftawa ? ...ka tuna Uncle? ...
Dariya yayi kasa kasa ba tare da yace komae ba ya
cigaba da karanta newspapper dake hannunshi ..
Kawar ta kalli Hanne tare da tabe baki ...sannan tayi
gaba abunta .....
"Allah Ya Isa Hudah "...ta fada kamar zatayi kuka ...
Mahmoud na dariya ya riko hannun Hanne yana fadin
..."Waya sakaki masu karya?
Hudah ta juyo tana dariya tare da dubarsu ...lokaci
guda ta daina dariyar tana watsawa Mahmoud din
harara dashi kanshi ya rasa ko ta mecece ....
Juyawa tayi ta shige dakinshi ta barsu yanawa Hanne
dariyar Hudah ta karyata Maganin Mai karya kenan
....Zama hanne tayi suka dan taba fira ....dakin ya shiga
zai watsa ruwa ya fita...
Hudah ya gani zaune ta kurawa Window ido ...Duk
tunaninshi bacci ta shigo zata yi ...bai ce mata komae ba
ya shiga toilet yayi wanka sannan ya fito yana goge
kanshi da towel ...
"Hudah !!! ya kira sunanta tare da zaunawa bisa
kujeran dake kallon gadon ..
Bata amsa ba haka bata juyo ba ...kanta ya tallabo yana
fadin "Menene "...?
Da sauri ta buge hannunshi dake saman fuskarta tana
hararanshi ...
"Me naki Hudahta ...fada man kinji ko ..? ...ya fada
cikin lallashi ..
"Kaine ka rikewa Aunty Hanne Hannu mana !! ...tayi
rau rau da ido ..
Ido ya fito cike da mamaki yana kallonta ...kafin yace ..
"Hudah Dan na rike hannun Auntynki shine kike fushi
..matata face ?..
"Nima din ai matarka ce !!! ...ta bashi amsa tare da
kura mashi ido ..
Murmushi yayi kasa kasa ..."Huda ke ba matata ce ...ke
rayuwata ce kinji ko!!..
"Ba wani ! ...ni din matarkace ...tunda tare da aunty
hanne muke tsare maka gida idan ka fita" ....ta fada tana
hararanshi..
Feedohm💞.
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_Na Feedohm💞_*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_47 to 48_*
To wayace maki tsare gida shine aure!!
Bata ce mashi komae ba ta mike ta fita daga dakin
....kitchen ta nufa ..insa yake aje mata dabino da biscuit
tare da sweet ...ta debo sannan ta dawo lokacin yana
shafawa kanshi mai ..
" Karba kaci Uncle "...ta fada a hankali tare da mika
mashi dabino daya ..
Babu musu ya karba ya cinye ..sannan ta bare sweet ta
mika mashi ..itama karba yayi ya shanye yana kallonta
...sae da ta bashi biscuit sannan ta duba aljihun rigarshi
ta fito sa naira dubu ta hankade pillownshi ta aje
...sannan ta dawo kusa dashi tana dariya ...
"Hudallah na me..
Hannunta ta daura saman bakinshi ...
"Yi shiru Uncle ..dama nasan dan ban baka dabino da
sweet ba shi yasa kace ni ba matarka bace ...to yanzu na
baka ..har kudin da ake bawa amare kaga na dauko ko
...To dan Allah Uncle yanzu ban zama cikakkiyar matar
Uncle dina ba ? ...ta langwabe kai tana kyafta idanu ...ita
ala dole fari zata mashi yarda taga hanne nayi idan suna
zaune a falo ..
Dariya sossae yakeyi ...har sae da yaga ta fara bata rai
sannan ya dan rage dariyar ..rasa abunda zai ce mata
yayi ...
Ya juya ya shiga distrnt dinshi ya canza kaya ...still
yana dariyar ...fesa turare yayi sannan ya fesa mata tare
da jan hannunta suka fita...
Ko hanne bai ma bankwana ba ya fita da ita .
Wani katon Moll suka je ya saya mata kaya sossae
sannan suka fito yana janye da hannunta...sae da ya
bude mata motar ya rufe sannan ya zagaya zaya shiga ...
Har ta zauna sossae ..kafin ya kai ga shiga, ta fito da
sauri tana fadin ...
"Uncle yaya Sa'ata !!!..idanuwanta suka ciko da kwallah
..
Barister Shehu ya gani dauke da safina zasu shiga moll
din sae dariya yake yana gaisawa da wasu ...
Da sauri yaja hannunta ya suka shiga motar tare
...gurin driver suka zauna su duka biyun ...tana lafe
jikinshi tana hawaye ....baiyi kokarin tursasata tabar
kukan ba ...sae dae hannunshi dake jikinta yana
bubbugata a hankali ...
••°°••
Hanne me kike so maki dan Allah ? ...ya fada a fusace ...
Haba yaya...me yasaka baka kulani ne ...ko hugging
dinka nayi ka fara ja da baya kenan ...3yrs da aurenmu
amma ko so daya baka taba sauke hakkin dake kanka
ba !!
Murmushin takaici ya sake kafin yace ." Me zan maki
bayan halittar dake jikina ita ke tattare dake ..?
Amma Yaya duk da nake maza mata ai akwae abunda
ya dace kaman naji dadi nima "
"Mace ya kamata ki nema ! ...ya bata amsa tare da
barin daki ...!!
°°••°°
Shekaru nata tafiya ...sam Huda bata da matsala gidan
Mahmoud ...idan tafiyar nesa ta kamashi zai dauketa ya
kaiWa mamanshi har sae ya dawo sannan ya daukota
...wani sa'in ma cewa take gurin maman zata zauna don
tafi jin dadin zama nan ...amma baya iya barinta ko
kadan bai kaunar yin nesa da ita ko na second biyu ...ji
yake kamar yayi loosing Something very important a
jikinshi .....haka zaita lallabata har ya samu ta biyoshi ...
Cikin ikon Allah Huda ta gama secondary school dinta
...lokacin duk wanda ya ganta bara ya taba tunanin
Hudalliyar da bace ...Fatarta tayi fresh da ita ...cikar yan
mata tayi ...kamar ita tayi kanta ...a lokacin shi kanshi
Mahmoud tsoron zama da ita yake su biyu ....yayi baya
sossae da ita ...haka itama ta shiga taitayinta ...!!
••°°••
"Uncle please dan Allah ,yanzu zan dawo wallahi
...please ka ji ? ...ta fada cike da shagwaba ...
Kallonta yayi tun daga sama har kasa ...tana sanye da
gown black ...sannan ta yane kanta da black gyale ...kaf
jikinta ba inda ake gani ...kamar wata balarabiya
...kafarta sanye da plat shoes black ...sae yar jikkar dake
hannuta black itama ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_49 to 50_*
Ganin ya tsaya yana kalllonta ya sakata hade
hannuwata guri guda tare da dan dukawa kadan
"please uncle " ...na tafi ?,...
Da kai ya bata amsa tare da lumshe ido ...wani tsalle ta
daka. tana dariya sannan ta fice da gudu ....ya bita da
kallo..
Gidansu kawarta Lubna dake makwabtansu ta shiga
....ganin ba kowa a falon ya sakata shigewa part din su
lubna ...lubna na kwance tana karanta wani book na
Ummy A'isha *_WANI HASKE_* ...Awayanta ...taji
kamshin turaren Hudah baki kofa...
Da sauri ta juyo tana dariya ..."Zuwa ba alert "...ta fada
cike da zolaya
"Duba phone dinki daga CBN na turo maki shi tun
daxu ..."
Uhm ...ta Uncle Mahmoud ina zuwa wannan irin
kwalliya nasan dai hakanan bara ki man irin wannan
kyaun ba ...
Baki Huda ta tabe tana kokarin cire gown din dake
jikinta ...tare da jefawa saman gadon ...
Lubna ta bude baki tana kalllonta kafin tace ...
"amma wallahi Damsel kin cuci Uncle ...don
munafunci shine kika sanyo wata gown a saman wannan
shedanun kayan .." ina zaki ?
Riga da wandone matsatstsu ...rigar iya karta guiwa
mai gajeran hannu pink ...sae wando pencil black ....
Tabe baki tayi tana fadin ... "dallah ban san gulma ni ki
taso ki rakani ..".
XIna ? ..lubna ta tambayi Hudah cike da mamakinta ..
"Bana son wulakanci ..zan sayar dakene? ...ki taso
mana ...bawae dan kina da mota ba ki tsaya ja man aji
...nasan mama batta nan har mun dawo bata dawo ba
...taso please ..!!! ...ta karashe maganar tare da yin gaba
abunta ...
Da hannu ta dingawa Lubna kwatance har suka isa
tsohuwar unguwarsu ...ta gaban gidansu suka wuce ...sae
da gabanta ya fadi ...inda yaya sa'a ke zama tana awara
ta kalla ...yara zaune gurin sae wasa suke ...take idonta ya
ciko da kwalla tayi saurin juyawa ta goge ba tare da
lubna ta lura ba ..
Gidansu ta kalla an rusheshe an hade da gidansu
barister Shehu ..baki ta tabe ta kauda kai tana kallon
waje ..
Nesa da gidansu barister Shehu tace suyi
parking ...sannan ta duba agogon dake makale a
hannunta tare da fita da sauri tana fadin ..
Excuse me please lubna !!!...
Gidan ta fada cikin sauri ...direct part din hajiyar ta
nufa ...sae da tayi gyaran murya sannan ta shiga ...hajiya
na zaune bisa doguwar kujera..tana amsa waya ..
Sallama tayi a hankali ta harde hannayenta a kirji tana
kallon hajiyar ...
Katse wayar tayi tare da amsa sallamar tana murmushi
...hajiya dama irin mutannan ne masu son mutun mai
kyau ...
"Bak'owa shigo mana "...ta fada dauke da faraa don ta
tabbata da ganin Huda ba diyar karamin mutun bace ..
Dan murmushi ta sake mai burgewa tare da dukawa
kusa da hajiyar tana fadin ...
"Mummy ina wuni " ...ta fada kamar tana rada ..
"Lafiya lau ..yarinya ...Tubarakallah ..daga ina
haka ?,zauna sossae mana".hajiya ta fada tare da fadada
fara'arta ..
Hudah ta dan dukar da kai tana fadin.."Ayyah
Mummyn mu baki sanni ba ..ai kawar Zahra ce ...tana
ma nan kuwa ?
Zahra. ...?...hajiya ta tambaya tana murmushi .."ae ko
nan gidan ba zahra kila dae baa baki adress din dae dae
ba ...
Barister Shehu ya shigo tare da sallama...sallamar ta
katse mashine ya tsaya cak tare da kurawa Hudah ido
yana murmushi ...
Ta gefen ido ta kalleshi ..sannan ta saka hannunta
tsakiyar cinyoyinta tare da matsetsu tana bubbuga
kafanta a hankali .."Oh Mummy ..wallahi na wahala
sossae ,tun dazu fa nake neman gidan duk inda na shiga
ba nan bane ..gashi phone dinta a rufe....OMG ..what
should i do ? ..ta dan wurga idonta tana bata fuska
kamar mai shirin kuka.... Barister Shehu yayi saurin shigowa falon tare da zama
kujeran dake kallon ta Hudah yana fadin .."Mom bakuwa
mukayine ?
Murmushi Hajiyar tayi tare da fadin .."Wallahi kuwa
Shehu gashi sae wahala suke bata har yanzu bata samu
gidan ba !!
Mikewa Hudah tayi tare da dage kafada tana fadin
"anyway!! ..nagode mummy bara na tafi tunda banan
bane .."
Hajiya tace "Ki tsaya ko ruwa na kawo maki mana "
Dan juyowa tayi tana kallonsu tare da lumshe ido
..."thanks ...." ta fada tare da juyawa ta fita da dan gudu
gudunta ...
Har tuntube Barister Shehu keyi gurin binta ...gabanta
yasha yana fadin.."
"Excuse please"
Tsayawa tayi tare da kura mashi fararen idanuwanta ..
"Please wa kika ce ma kike nema "
Murmushi ta sake mashi tana fadin "Zahra Abdullahi "..
"To ko zaki bani phone numberki idan na nemo maki
ita nan unguwar din sae na tura maki housenumber
dinsu please !!...ya karashe maganar cikin ky'arma ...
Kura mashi ido tayi ...ba laifi ya dan manyanta ra fada
a ranshi ..."thanks ...ka barsa" ...ta fada tare da cigaba da
tafiya ...
"Please na rokeki da girman Allah .." ya fada kamar
zaiyi kuka ...
Cak ta tsaya tare da sakin murmushi ...takowa yayi har
inda take ..ya mika mata phone dinshi ..hannunta da
yasha jan lalle ta saka ta karbi wayar ta sa mashi
numberta ...
"Thank you so much beauty" ...ya fada cike da murna
....
gaba tayi abunda ..da karfi yace .."please me zan sa " ..
*_DAMSEL SA'ADAH.._* Ta bashi amsa kai tsaye tana
tafiyarta ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*


Please Login or Register in order to submit comment