Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Auntu Husy ce tace ta sayi hannun amarya naira
million daya cash ta zubesu a table din da suke zaune ...
Duk da hakan kasa bashi tayi ...hannuta ya kamo ya kai
bakinshi saitin fuskarta ...
"Ba kya sona Hudah? .....ya fada a hankali ...
Dagowa tayi da sauri tana kallonshi kafin ta girgiza
mashi kai a hankali ...hannuta ya kama ya debo abincin
sannan ya saka a bakinshi yana lumshe ido ....gurin ya
dauki tafi da ihu ...abokan wasanshi kuwa cewa suke wae
amaryar bata sonshi tunda har ta kasa bashi abinci ...
A hankali ya dago da fuskarta yana kallon ..."Prove it
Hudah ...ki nuna masu kina sona ...ko bakya sona .?..
Ba tare da tace komae ba ta kai hannu ta debo
Muhassimba ta kai bakinta ta b'alli kadan sannan ta sa
mashi sauran a baki ....
Ba karamin burge mutane sukayi ba ...Aunty hanne
kam na can cikin gida bata san wainar da ke toyawa ba
...Yayar Mamanshi ta bata yan shila tace ta gasa masu da
ruwa ruwa idan zasu tafita a tafi da ita..dan haka bata
gani ba.. bare ta kwashi takaici .....
••°°••
Bayan Magrib ne akace a fito da amarya ....sae da
sukaje falon Abbah suka masa bankwna tare da Mama
sannan Uncle Mahmoud din ya jata har harabar gidan
inda aka ajiye motoci ....Daga ita sae Aunty Hanne da
Aunty Husy kadae suka shiga motar ...dan Aunty husy
cewa tayi bara su shiga mota dashi da Amarya ba tunda
baida kunya .....
Sae da aka fara tafiya sannan ya masu gyaran murya
lokacin Aunty Husy tana karawa Hudah nasiha ..Hudah
kuwa kuka take a hankali ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_83 to 84_*
"Aunty Husy dan Allah ki barta hakanan ...kinga zaki
ja ta bata kwalliyar tun kafin na gani ...kuma duk abunda
kike fada mata Allah yau zan fada mata ba tare da tayi
kuka ba " ....ya fada tare da kunna fitilar motar ...
Sake da baki aunty Husy ke kallonshi "∆mma
Mahmoud baka da mutunci ...ashe dan Ubanka sae da ka
biyomu ....shine ka karbi driving din ko?....ya maka
kyau!! ....
Dariya yayi kasa kasa tare da kallon Hudah da ta
kwantar da kanta sanan cinyar Aunty Husy tayi lamo
kamar maijin bacci...
Hanne ta saka hannu ta kashe filitan ...ba tare da tace
komae ba ...har suka isa gidansu ...sannan aka shigar da
Amarya Part dinta ...amma ba asalin wanda take ciki ba
da ...aa saman bene aka kaita ...dama kuma gurin rufe
yake ...
Kamar yarda addini ya tsara bayan kowa ya watse ya
tarasu falonshi tare da masu nasiha mai ratsa jiki
...sannan yace kowa ta fadi bukatarta ...
Aunty Hanne tace ...Idan da hali ya taimaka masu da
jari saboda ita tana so ta dinga fita kasashe tana dauko
kaya ... tasan ko ance ta koma karanta bara tayi abun
kirki ba ....
Yacce .."kamar nawa suke bukata ?
Hanne tace " ko nawa yake da hali ..."
Hudah kam jinsu take ..don bata da wani guri da ya
wuce tayi karatu domin cika gurin Yaya Sa'arta !!
Leda da ya shigo dashi yace Hanne ta je ta dauko
masu plate ..
Aa tace ...yafi kyau suje can su ci abunsu kamar yarda
akewa ko wace amarya ...sannan ta mike ta daga Hudah
tare da daukar basket din da ta shigo dasu suka nufi part
din Hudah ....bawae bata jin kishi bane sae don ganin ko
tayi kishin a banza tunda bata da abunda zata iya biya
mashi bukatarshi ..
Part dinshi ya shiga ...yayi sallah tare da wanka sannan
ya shiga part din hanne ya mata bankwana tare da
hugging dinta yana mata godiya ...don ba karamin
burgeshi tayi ba a hidimar bikin ...bai tafi ba sae da ya
dan bata farinciki ta hanyar romancing dinta sannan ya
fita .... _Ajiyar zuciya ta sake ta bishi da kallon ..wannan
ne karo na farko da ya taba kai hannunshi a jikinta da
niyar faranta mata..kwallah da suka taro idonta suka
gangaro mata ...._
Hudah kam inda hanne ta barta nan ya isketa ....ko da
ya shigo sae da ya kura mata ido ..duk da tana lullube da
maroon din saree hakan bai hanashi ganin kyauwun da
ta yi ba ....bakin gadon ya zauna tare da yaye mata fuska
yana lumshe ido ...
" Tubarakallah ...Masha Allah ..Alhamdulillah ya Allah
.."!!!.ya fada tare da dago fuskarta yana kallonta ...kasa
tayi da idonta har sae dae ya kai bakinshi yana gogawa a
dukka fuskarta ....
"Tashi kiyo Alwala" ...ya fada kasan makoshi ...har
lokacin bakinshi na saman fuskarta idonshi a lumshe ...
Ganin bata da niyar tashi ya sashi daukarta cak ya dire
ta cikin toilet din tare da zuba mata ruwa har ta gama
alwala sannan ya janyo hannunta ya shinfida masu
darduma ....ya gyara mata zaman saree din a jikinta ta
yarda baka iya ganin komae a jikinta ...sannan ya jasu
sallah ...bayan sun ida ..ya dafa kanta Kamar Yarda Allah
ya umurce mu ...ya dinga kwararo mata aduu'a sanna ya
janyo basket din da hanne ta shigo dashi ...ya fito da
foodflask da waterdesndr ....tare da plate da spoon ...
Yan shila ne da sukaji kayan yaji ya juye masu .sannan
ya tsiya mata lemon da aka hada da
kankana,gwanda,dabino da kwakwa ya tsiya a cup ya
kafa mata a baki
.
Wani bala'in kunyarshi take ji...duk da ba wannan bane
first time da ya bata abinci a baki ....kin karba tayi sae da
ya daure fuska sannan taci kadan tace ta koshi ....
Ledar ya janyo ya juye mata kazar dake ciki yana fadin
.."Zauna kici kinji..bana so ki man irin na meenalle kice
ban kawo maki kaza ba My Hudah!! ....dan hararanshi
tayi sannan ta mike ...
Shima mikewa yayi ...yana kwance saree dake nannade
jikinta ...rike kafadarta yayi yana juyata har ya gama fitar
da gyalen ya barta daga ita sae siket da wata yar rika
wanda iyakar jibi da karamin hannu ....Sae kwalliyar
stone dake jikin rigar ....
Wani asirtaccen kamshi ke fitowa daga jikinta ...bai ga
bukatar saka wasu kayan bacci ba ...ya dauketa cak tare
da direta saman gado ...sannan ya koma ya kashe wutar
dakin ...
Cikin dubara har ya rabata da kayan dake jikinshi
...anan ne ya kusa zaucewa har bai san sadda ya kunne
fitila ba yana kare mata kallon ...da sauri ta rugumeshi
ganin haske ya gauraye dakin tana niyar kuka ...
Da kyar ya iya kai hannu ya kashe fitilan yana mayar da
numfashi ..cikin kunnenta yace ..
"Allah ya ma lubna Albarka ...yanzu zan gane idan
abunda take ba dawa yayi amfani..don bana son wannan
rakin ya tafi a banza" ...ya karashe maganar cikin zolaya
....wani uban duka ta kai mashi a kirji tare da ko ma wa
can karshen gado ta kwanta ..
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_85 to 86_*
Mirginawa yayi ya hadeta da bangon yana fadin
.."Sorry na daina kinji ko "...Sannan ya janyota jikinshi
yana gentling ko'ina na jikinta
••°°••
Barister shehu kuwa bayan sun kaishi asibiti aka
tabbatar masu da barin jikinshi bara ya taba amfani ba
_paralysis_ ...domin faduwar da yayi ga lokacin jininshi
ya hau ....Hajiya da dad kuka suka sake ...yayin da take
tsinewa Hudah Albarka tare da ja mata alkaba'ai kala
kala ...
lokacin ne maganganun hudah suka fara mata yawo
...cutar Kanjamau kawae take tunawa ...Dad din ta kallah
taga duk yayi yaushi ga kuraje da suka fara cika mashi
jiki ....
Ba tare da tayi shawara dashi ba ta je laboratory tace su
mata gwajin HIV ....jininta suka diba bayan mintuna suka
tambar mata positive ce tana dauke da cutar ....
Kamar mahaukacya ta koma ...ta shakari wuyan Dad
tana dura mashi ashar ...da kyar ya kwaci kansa ...
Doctor yace shima a mashi gwajin ...baa dauki lokaci ba
aka tabbatar mashi da shima positive ne ....
Doctor din ya basu shawara da su rufawa kansu asiri su
zauna tare ba tare da wani ya sani ba ...sannan ya daura
su kan magani ..
Bayan shehu ya farfado ..ya tabbatar masu da ya sayar
da gidan da suke zaune ...amma ba Hudah ya sayar
mawa ba ...wani makwabcin su Hudah ne amma ba
mamaki ita ta turoshi .. ....
Dad din yace bai yarda ba wallahi zai shigar da ita kara
...amma sae barister Shehu yace ...babu wata kotu da
zata karbi gidan daga hannun Hudah tun da "ka sayar ya
rabaka da abunka" ..sannan takardun gidan ma na
gurinsu ....Ba karamar nadama barister shehu yayi ba a
ranar ....gashi a kwance rabin jiki a mace ...sannan har
lokacin akwai soyayyar Hudah a ranshi ....wanda ya
tabbata bara ta taba gushewa ba ....
••°°••
A hankali ya kai fuskarshi tare da kissing lips dinta
...sannan ya sake murmushi ...bai taba tunanin rakin
huda ya kai haka ba ....Ihu ta dinga mashi kamar ita
kadaece macen aure a unguwar ....
Blanket ya ja mata ya mike ya fada toilet yayo wanka
tare alwala ..
har sae da ya gama sallah sannan Hudah ta bude
rinannun idonta tare da dallah mashi harara ...
Murmushi ya sake mata tare da fadin ..."Ni kike
harara" ...
Kafarta ta sauko zata mike tsaye ta koma da sauri...tana
fadin ..."Allah ya isa wallahi .Lubna..ban yafe ba ..kema
zaki samu wanda zai maki irin hakan ...Shegiya
kawae !!! ..ta saka bayan hannu tare da share kwallah ..
Dariya sossae ta bashi ...bafa Lubnar ta tsareta ba tace
dole sae tayi amfani da abunda ta bata ...aa itane har da
boyewarta ma dan kar wani ya ganta ....amma kuma zata
zagi yar baiwar Allah tana can gida tana bacci abunta...
Cikin zolaya yace .."Wae Hudah me lubna ta maki tun
jiya kike mata Allah ya isa ..? ..Gaskia ina neman mata
gafara kinji ...!!
Harara ta balla masa tana fadin "...Ban sani ba ...ka
shafa kaji ..."..
Tasowa yayi yana dariya ..
"Abu mai sauki ..muje toilet idan na hada maki ruwan
wanka sae na shafa da kyau naji ....!!
Daukarta yayi tana harbe harbe ya direta cikin ruwan
zafi yana mata dariya ....sae sa ya tabbatar ruwan zafin
sun ratsata sannan ya canza mata wasu ruwan zafin yace
"Kiyi wankan tsarkk kinji Hudah ...bara na gyara dakin
kafin ki gama ko!! "...ya barota cikin ruwan tana lumshe
ido..
Kusan Minti Talatin yana jiran ta fito amma shiru ko
motsinta baya ji ....toilet din ya leka tare da sakin
murmushi ganinta kwance cikin ruwan zafi tana bacci
hankalinta kwance .....
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_87 to 88_*
Girgiza kai yayi ..sannan ya dauko katon towel ya
nadeta ciki ya kwantar da ita saman gado tare da shafa
mata cream kadan ....
Cikin kayanta ya dauko wata doguwar riga mara nauyi
ya saka mata...sannan ya shafa mata powder ...wasa
wasa kwalliya ya mata sosaae tana baccinta don lallabata
yake kamar kwae ....
Fita yayi ya leka part din hanne ga mamakin shi ya
tarad da ita kitchen tana hada masu break ....sai da ya
tayata suka hada komae sannan ya koma dakin Hudah
....
Lokacin ta tashi amma tana kwance idonta na kallon
sama ....Tana jin shigowarshi ta maida idonta ta rufe ..
"Hudah ....baki tashi ba har yanzu ....!!ya fada tare da
shafa wuyanta ...
Da sauri ya janye hannunshi ...yana kallon fuskarta
...."Subhanallah ...Hudallah...ba dae baki lafiya ba ? ...ya
fada a rude ...
Dagota yayi tare da rungumeta yana mata sannu ......
Sae da taji duk ya rude sannan ta bude ido tana
hararanshi ta kasan ido ...
"Bakya lafiya ne Hudah .?..sorry fada man kinji ...!! ya
sake tambayarta a rude ..
Banza ta mashi na tsawon lokaci sannan tace ..."Lafiya
na lau "
"Amma jikinki zafi Hudah "...ya fada tare da dago
fuskarta ..
Haka jikina yake fa Uncle ...!
"Kin tabbata lafiyarki lau ? ...
daga mashi kai tayi tare da mikewa a hankali ta bar
dakin ...ba tare da yace mata komae ba ya bita da kallo
har ta bar dakin ....
*_4 month_*
"Uncle wallahi wannan rito ne ...kuma baran yarda ba
.."..ta fada tare da rike guiwar kafarta ..
"Ga Auntynki nan ta mana shari'a ...ai ta gani tsabar
rigima ne irin naki ...kuma kema kin san ni nayi winning
ba ke ba....."
Kusa da hanne ta koma tare da dafa
kafadarta ..".Aunty hanne dan Allah ba sae da ya'yan
wasana suka shiga ba sannan ya saka nashi? ...
Cikin dariya Hanne tace .."kinga Hudah ba ruwana da
rigimarki ...kufi kusa...idan kin gama kya sameni kitchen
....
Gwalo ya mata tare da mayar da kudinshi aljihu ....
"Wallahi Uncle sai ka bayar dasu ...tun da bani nace ka
sa kudin ba" ...
Ta fado jikinshi tana kokarin karbar kudin ...fito dasu
yayi tare da yin sama da hannunshi yana mata dariya ....
Kokowa sossae take sae ta karbi kudin ...hannuwanta
duka biyun ya hade tare da matseta a kirjinshi yana
mata cakul kula ...
Zuciyar ta ji tana tashi ...ta fara kokarin fita daga
jikinshi saboda bata son kamshin turaren dake jikin
kayanshi ....bai lura da yarda take ba ...ya rike ta gam ..
Ganin ta fara kakarin amai ne, ya sashi dagota da sauri
...kafin yayi wani kokari ta wanke mashi jikinshi tsaf da
amai ...
Sam Aman bai dameshi ba ..."sorry" kawae yake fada
tare da rike fuskarta da duka hannuwanshi ...
Sae da Aman ya lafa sannan ya dauketa ya shigar da ita
toilet din dakinshi ya wanke mata jikinta tare da mata
wanka sannan ya fito da ita ya zaunar da ita gefen gado
...ya koma yayi wanka ya canzo kaya ...
"Sorry Hudah ....." ya fada a hankali kamar zaiyi kuka
....
daga mashi kai tayi a hankali ...sam bata kaunar
kamshin turarenshi amma barata iya gwada mashi ba
...rungumeta ya sakeyi sossae ...yana shafa fuskarta ...
A hankali hawaye suka fara bi mata fuska ...lokacin da
yake kokarin kwantar da ita sossae a jikinshi lokacin
zuciyarta ke kara tashi ....cikin dubara ta zame jikinta
tana mashi murmushin yake ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_89 to 90_*
Da daddare ta kwashe duka turarukanshi ta boye ....da
ya tambayeta sae cewa tayi "ta gyara dakin ne ta manta
inda ta ajesu" .....
da yake ranar ba gurinta zai kwanta ba ...sae tayi
baccinta lafiya .....
Ranar da ya dawo dakinta kuwa ...kwana tayi tana amai
gashi ta kasa fada mashi shine silar aman nata ...tun da
safe ya kaita asibiti ...
Doctor ya tabbatar mashi da matarshi tana da ciki wata
2 ...farinciki sossae ya nuna ...shi kanshi doctor din sae
da ya sami kyauta ta musamman ...
Kasa Hakuri yayi ya wuce da ita gidansu ...acan yake
gayawa Mamanshi wae Ya kusa zama Abbah ...dariya
maman tayi cike da kunya ta barshi ....Haka Hudah kasa
ko da motsi tayi saboda kunya .....
Tun da suka shiga Mota taki ko da kulashi ..ya sani
sarae fushi take dashi .....Hannunta ya kamo ya rike tare
da kallon Fuskarta ...ganin sam hankalinshi ba ga hanya
yake ba ya sata kwace hannunta tana hararanshi ...
" Uncle ka kalli gabanka mana "..ta fada tana
hararanshi ..
"Taya zan kalli gabana bayan kina fushi dani Hudah
.?...to naji nayi laifi kinji ko ...kiyi hakuri, farincikin da
nake cikine bara ya boyi ba ba ...!!
Turo baki tayi tana kallon taga ba tare da tace komae ba
...hannunta ya sake kamowa ya hade da sitiyarin motar
yana murzawa a hankali ...
Dan satar kallonshi tayi taga yarda duk ya damu da
fushin nata ....kwantar da kanta tayi saman kafadarshi
tana shafa gefen fuskarshi ...
"is ok Uncle ..Hudah barata taba fushi da Uncle dinta ba
....!! ...ta fada cikin kunnenshi
"Are you sure !...ya fada a hankali tare da parking
motar kasan wani icce ...
Daga mashi kai tayi tare da sake mashi murmushi
...."Me zamuyi nan Uncle?
"Na gaji ne nake so na kwanta bisa k'ashin matata na
huta for some minutes ...!!
Turo baki tayi .."Lallae Uncle ni ce k'ashin ? ...wallahi
zaka maimaita ...!! Ta fada tare da girgiza kai..
" Oho dae ...Lokaci da zaki bukaci na maimata ke kanki
rokona kike na barki .."..ya fada tare da kwantar da
kanshi saman cinyarta ...
Wani uban ihu ta sake jin kamshin turaren nashi ya cika
mata hanci ..ga har zuciyarta ta fara tashi ....yayi saurin
tashi zaune yana tallabo fuskarta ...
"Menene Hudah "..,.Ya fada a rude ...
"Uncle Kaza ...Ji Uncle dan Allah ka sayar man zanyi
kiwo ko guda Daya ce please",..ta fada don bata so ya
fahimci wani abu ... _a tunaninta duk yarda na miji ya kai
ga sonka bara ya ji dadi ba kace baka son wani abu daya
dangance shi_
"Ohoo Hudah Wae meke damunki ..?..duk wannan
ihun na kaza ne ...?..Allah ya shiryeki !! ....ya fada tare da
bude motar ya fita ...
Gurin da yaga kejin kaji ya nufa ...ya iske saura kaza
daya da zakara ...kudin ya biya aka saka mashi su cikin
kwali sannan ya sayar masu buhun abincisu daya ....
Harde Hannayenta tayi tana watsa washi wani
wahalallen kallo ..."He's such a cring person ....!! ..ta fada
a hankali tare da bude mashi motar ya shiga ...suka saki
murmushi lokaci guda ...
Duk lokacin da Uncle dinta zai kwana dakinta sae ta
sami kerosine ta shafa a wani hanky ta riga sinsinawa ba
tare da ya lura ba ...hakan da take yi ya mata rage yawan
aman da take ...
••°°••
Kamar yarda ta fadawa su barister Shehu ...wanda ya
sayi gidan a hannunsu yaje yace su fitar mashi daga
gida..daga farko dad din yace bai yarda ba ...sae da
mutumin ya nuna mashi takardun gidan tare da shaida
...sannan ya kalli Shehun cikin bacin rai zaiyi magana...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_BONJEN muyitda bueda...Aunty sis , Jeedah
Aliyu,Ummi A'isha, Asy khaleel , Pherty ,Khaleesa ,Afra
,Hajja ce , Queen Mermue ,Nafee Anker, Asmy B, Billy B
,Billy G, Candy, Classic, Aisha Muhammad ,Maman
khadija ,😘😘😘_*
*END...*
Sae yayi shiru ganin ba amfanin maganar domin shehu
kamar gawa yake sae tarda akayi dashi ....haka suka
tattara kayansu suka bar gidan ...Allah ma ya soshi guest
house dinshi yana nan ....suka koma can ...
Cikin Yan watanni kudin magani suka fara cinye duk
wani abu da ya mallaka...ga shehu akwance paralysis ya
gama dashi kullun abun karuwa yake ..sannan shi da
Hajiyar kullun suna neman magani amma abun ba saa
••°°••
Hudah kuwa Uncle Mahmoud soyayya yake nuna mata
kamar ba gobe ..sannan shi da kanshi yace ta bari ta
haihu sae ya maidata makaranta ...
Suna zaune cikin garden lokacin ta daina jin warin
turaren da yake sawa ....lafe take a kirjinshi yana karanta
mata wani novel .. _Tears drop at the sunset_ Zakaran da
ya sayar mata ya biyo kazarta tibi tibi ...suka zo suka
wuce ta shinfidarsu da gudu ...
Kallonta yayi yana fadin ..."Umhum ...dama barewa
zarayi gudu ne danta yayi rarrafe ..."
Sam bata fahimci inda zancenasa ya dosa ba ...ta dago
tana kallon kajin tare da fadin .."Uncle sun yi girma ko?
"Dole suyi girma man ...tun da mamansu ma ta kara
girma ...sae dae ya kazar ya mamanta ...!!
" Uncle ban gane ba ?...ta fada tare turo da baki ...don
ta fara gane magana ya fada mata ...
Huh ...yarda kazar ke gudun zakara haka mamanta ma
ke guduna...kin fahimta sossae ko ?
Dan duka ta kai nashi a kirji tare da fadin ... "Kai uncle !!
" Ba haka bane ? ...ya fada tare da kafeta da ido ...
Kara shigar da kanta tayi a kirjinsa ... "to yi Hakuri ai
kaga bana lafiya ne ?
Ko ? ....Ya tambaya tare da saka hannu a yana shafa
jikinta ...
Bata ce komae ba sae turashi da tayi ya kwanta ta
daura kanta saman cikinshi tare da lumshe ido ...
••°°••
Tun safe ta sakashi gaba tana masa kuka ...tambayar
duniya ba wadda bai mata ba amma taki bashi amsa ...
wajen sha biyu ya fito daga wanka ya iske still inda ya
barta tana sharan hawaye ...
Hannu ya mika yana fadin ..".Haba Hudalliyar Yaya Sa'a
zo nan ki fada man me kike so kinji ko .!!...ya mikar da ita
tare da zagaye kugunta da hannunsa ...
Turo baki tayi tana fadin ...
"Uncle ina indomie din da ka dafa man ranar da ka
daukoni daga gidanmu ? ..
Ido ya waro ..."duk da dai ya manta amma Bai isa yace
bai tuna ba ...sae cewa yayi " Na ma isa na manta ta
Hudah ..ya akai ?
" Ita nake so ka sake dafa man yanzu " ...ta fada tare
da kwantar da kanta a kirjinsa ...
" Hudah!! ....ya fada da sauri .."Over 6 years fa
kenan ?
" Bara ka tuna yarda ka hada ta ba ? ..ta tambaya a
hankali ..
" Haba Hudah ..taya zan manta ...bani 30mints yanzu
na kawo maki kinji ko ....? ..ya fada tare da shafa kanta
Peck ta mashi a kumatu cikin jin dadi....har ga Allah
bawai don ta bashi wahala ba ...aa ta tashine kawae tana
son cin irin indomie din ...duk da itama ta manta koda
kalar taste din bare shi da ya dafa ...
Kitchen ya shiga kasancewar Hanne bata ban ...tana
gurin kasuwancinta ...rasa abunda zaiyi yayi ...Hudah ta
riga ta shagwabashi in banda yankan albasa da zuba
maggi a abinci babu abunda ya iya ..hana rantsuwar tana
bashi ya mata taste yaji idan abincin yayi dadi da kuma
zubawa a coler ....
Lumshe ido yayi a hankali ya bude fridge dauke da
addu'a ...ya fito da fura da youghurt da inibi da kwakwa
ya zuba a blender ya dama mata ...sannan ya saka
kankara kadan ...
Sae da yayi addu'a sannan ya shiga dakin ...cikin fara'a
ta mika mashi hannu ..tana ganin fura ta bata fuska
zatayi kuka ...
Dukawa yayi gabanta tare da dafa guiwarta .."
"sorry Hudah ...wallahi da zan iya tuno yarda na dafa
maki ita babu abunda zai hanani kare rayuwata a
matsayin kukunki ...Kin sani duk wani abunda zai sakaki
farinciki nima shi nake so Hudah ...Kiyi Hakuri kinji ko
..ki sha furar kafin naje kitchen din na dafa har Allah
yasa zanyi wadda zata maki dadi kinji ko ...!!
Hannunta ta kai ta karbi furan tare da rike hannunshi
da cup din guri guda ...sannan ta saka gudan hannun
tana shafa sumar kanshi ..tare da kissing din goshinshi ...
"Nagode Uncle .!!....ta fada cikin kunnen shi tare da
hura mashi iska a hankali ..
" Zan sha wannan din ka ji uncle dina ...wallahi
indomie din ma ta fita raina karka damu ...kayi hakuri
idan na bata maka rai ...!!.
°°••°°.
Cikinta na cika wata tara ta haihu santaleliyar diyarta
mai kama da Babanta ....Murna gurin family din ba'a
magana ...kudi kuwa kamar suke nomansu ...
Ranar suna diya taci Sunan Sa'adatu ...ana kiranta da
MUNIFFAH ( _Sabon farinciki.._ ) ...ita kanta Hudah bata
san sunan Mahmoud zaya saka ba ...sae daga baya take ji
gurin wanda suka shigo ....
Tana zaune tana bawa babyn mama ya shigo cikin
mayan kaya yayi mata masifar kyau ....dagowa tayi ta
zuba mashi ido har ya iso kusa da ita ...tare da dukawa
ya sumbacin babyn sannan ya kai lips dinshi saman na
Hudah yana kallon cikin idonta
Lumshe ido yayi yana fadinn .."Wannan kallon
fa? ...baki san kin haihu ba ? ko

Please Login or Register in order to submit comment