Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nake (regretting, I'm in need of her)."
Hashim ya ja tsaki.
"Kana da matsala, dole kuma ka sauke wannan ji da kai ko ince girman kan da kake nunamata wallahi."
[7/26, 12:44 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<44>>
Shi kuwa iyakar dauriyarsa kawai yayi, yana son kusantar tafi haka, saidai bayaso yayi gaggawar da zata fassarashi baibai. Watakil ba zata fahimci yanda yake so da kaunarta ba.
Ya ji sadda tayi bacci, shi d'in kuwa ya jima kafin baccin yayi awon gaba da shi hakance ta sanya baiji kiran sallar asuba ba.
Ta k'ura mishi ido tana kallon irin baiwar da Allah Ya bata na samun mutum mai kyau da kwarjini irin Ma'aruf, ba wayonta ba ba komai ba.
Bacci yakeyi hankalinsa kwance, dakyar ta iya mik'ewa ta fad'a toilet.
Saida ta kammala tsarki da alwala ta fito. Har lokacin bai tashi ba.
Ta d'ora zani saman rigar baccinta tayi shirin tayar da sallah tsaf sannan ta tashe shi a hankali ta hanyar bubbuga k'afarsa.
Ya waro ido yana 'yar mik'a. Ganinta da hijab, ya sanyashi azamar mik'ewa.
Saida ya kammala sannan ya fice zuwa masallacin gidan dake kallonsu. Ita d'inma Sarah ta tayar, ta koma tayi nata.
Ta jima da gama addu'o'inta da komai, har rana ta d'an fito, tana son ta d'an runtsa saidai tana tunanin Hanif.
Zata fita sukaci karo zai shigo, ta tsorata, ai ta dauka babu abinda zai maidoshi. Ta gaisheshi ya amsa kafin ta ba shi hanya.
"Ina zaki?"
Ta dubeshi. "Aiki zanyi."
Ya ja hannunta ya rufe k'ofar.
"Aiki da asubar nan Fati? Bari zuwa anjima naga yau dai ba makaranta zaki ba.
Bai bari tayi magana ba ya nufi ciki da ita. Har gado ya ajiyeta ya kashe fitilun ya zagayo ya kwanta gefenta.
Ta runtse ido jin abinda yakeyi. Ya kuramata idanu yana murmushi.
"Fati." Ya kira sunanta cikin sigar da ba zata jura ba. Bata iya amsawa ba.
"Look into my eyes, please."
Ta bud'e idanunta a hankali ta sauke cikin nashi, da sauri kuma ta maida ta rufe. Yayi murmushi ya soma magana ba tare da ya bar abinda yakeyi mata ba wanda ke kunce notinan kanta.
"Zaman da mukayi dake tare yasa na damu dake yanzun, kin samu wani babban gurbi a zuciyata Fati..."
Sai kuma yayi shiru. Ba wannan takeson ta ji bani ta so ba, yanda ya soma bi da ita yasa ta soma fita hayyacinta, saidai da sauri ta mik'e zaune ya dubeta da soyayyun idanunsa. Da saurinta ta mik'e kafin ya ankara ta nufi k'ofa.
"Tsaya!" Ya fad'a da 'yar muryarsa. Ta tsaya cak, ta sa hannu tana m'ara suturce jikinta, a yanzun shi kuma ya shiga matsanancin damuwa, Bintu bata son shi, shine kawai abinda yasa wa ransa.
Hakan yasa shi mik'ewa gami da gyara rigarsa ya nufi inda take.
"D'akinki ne. Baki kamata na takuraki ba."
Daga haka ya fice. Ta bishi da kallo kafin ta lumshe ido tana murmushi. Ta yarda ta kuma gaskata cewar Ma'aruf fa yana sonta yanzun, saidai ta so yayi furucin da bakinsa ba wai yayita kwana-kwana ba.
Ta koma ta kwanta gami da tattaro zanin gadon da filon da yayi matashi tana shinshina cike da jin sanyi a ranta. K'amshin turare Yaya Ma'aruf kawai ke tashi. Wasu ruwan hawaye suka kwaranyo mata. Ko a mafarki idan ance mata zata fad'a wannan hali na soyayya ba lallai ta gaskata ba, sai gashinan daga ita har Yayannata Allah Ya jarabcesu da fad'awa kogi na soyayyar juna, so mai wahalar da zuciya da gangar jiki kuwa.
Shima a can, kasa bacci yayi, idan har bazai samu kan Bintu ba, to zai iya kamuwa da mugun ciwo kuwa don shi kad'ai yasan yanda yakeji a ransa. Yayi amanna cewar bazai iya son wsta ko kusantarta wata d'iya mace ba sai ita. Ita kad'ai yake so yake kuma buk'ata.
Ya lumshe ido yana sakin ajiyar zuciya.
Bintu kuwa har ta kammala komai ta bawa Hanif abincinsa tayi mishi wanka Ma'aruf bai fito ba. Ta gaji da zaman jira ta bar Hanif a hannun Sarah itama ta fad'a wankan. Har ta kammala ta shirya cikin doguwar riga d'inkin buba ta fito falon, shiru babu labarinsa. Hankalinta ya tashi, ta kasa daurewa kawai ta nufi d'akinnasa. Da sallamarta ta shiga, abin mamaki baya dakin, jin motsin ruwa ya bata tabbacin yana wanka ne. Hakan yasa ta fita. Saida ta kammala karyawa ta fiddowa Sarah keken Hanif baranda ta shiga turashi, ita kuwa zama tayi jugum har zuwa sadda ya turo k'ofar ya fito. Tasan yau babu aiki, to meyasa ya shirya cikin manyan kaya.
Zama yayi a gefenta, duk yanda yaso ya nunamata yayi fushi, bai iya hakan ba, musamman ma ganin yanda ta ci ado, duk sai ya raina ajinsa, to ita d'inma hakanne a wajenta.
"Fati." Ta narke fuska. "Nidai gaskiya ka daina kirani Fati."
Yana murmushi ya jefamata tambaya.
"Why?" Ta turo baki "Sunan fa Mami ne, kacemin Bintu na yanda kwa ya sanni da shi."
"Ok, Bintuna, had'amin tea."

Ta dubeshi ido waje sai kuma tayi k'as da kanta don batason kallon da yakeyi mata, irin kallon da Aisha ke gayamata a baya ta k'aryatashi, a yanzun kuwa ta gask'ata lallai akwai shi. Batayi aune ba ta ji ya tallafo ha6anta da hannunsa na dama kafin kuma ta ankara tuni ya soma mata sak'o. Abinda ya keyi zai tabbatar ya mance a inda suke, wannan karon ba k'arfinta ne ya kwaceta ba sai wayarsa da ta dauki ruri.
Alokacin ta ja gefe. Ya duba Abbansa ne, cike da girmamawa ya dauka. Abba ya hau fadan dadewar da yayi bai zo sun wuce ba. Ya bashi hakuri gami da mikewa, a tsaye ya kora tea din kadan sannan ya koma daki, jimawa kadan ya fito cikin yadi maimakon shaddar da yasa a farko. Ta kauda kanta, yana murmushi yace"Saina dawo, zan fita da Abba. Ki shirya tarbata mai karfin mata goma."
Ai a guje ta fad'a dakinta, ya fice yana dariya.





(Nagode wadanda sukamin ya jiki, da ma wadanda basuyiba a rubuce amma sun kirani, da ma wadanda basuyi duka ba amma sun damu da hakan. Allah Yabar zumuncinmu..love oll)
[7/26, 11:45 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<45>>

Tana lek'ensa ta windo har ya bar gidan sannan ta sauke labulen gami da zubewa kan kujera tana dariyar farinciki.
"Na sameshi!" Ta fad'a a fili kafin ta dauki ragowar tea din ta saita daidai saitin da ta ga ya sha ta hau korawa a cikinta tana mai lumshe idanu, wani irin soyayyarsa na k'aruwa a ranta.
Ta dire kofin bayan ta kammala, sai kuma jikinta yayi sanyi. Baifa furta yana sonta ba?
"Sannu bata hana zuwa." Ta ayyana hakan a ranta. Cike da nishad'i ta tattara kayan karin ta mayar kicin domin ji tayi gaba d'aya yunwarta ta kau.
Ranar yini tayi da wani nishad'i marar misaltuwa. To shi d'inma hakan ce gareshi, don har Abba saida ya tambayeshi ko anyimishi albishir da aljanna. Dariya kawai yayi.
Itama a ranar sunyi waya da Aisha, wacce shirye-shiryen biki ya 6oyeta don alokacin sauran watanni biyu da kwanaki. Nan Aisha ta sanarmata lallai a wannan daren tayi kokarin kyautatawa mijinta. Tayi shiri, irin shirin da tasan zaiyi saurin birkita tunaninsa.
Sukayi dariya.
"Kinsan fa har yanzu ya k'i furtamin yana sona?"
Tsaki Aisha ta ja.
"Kedai ki bada kai, wannan kuma sadda zai furta ma bakisani ba, kuma na gayamaki wallahi Yaya yana sonki. Ki bi dai shawarwarina. Na yarda zaki iya fin haka."
Suka k'ara darawa kafin suyi sallama.
Misalin d'aya na rana, ta dauki waya tayi kiransa kamar yanda Aisha ta gayamata. Saida ta kammala dariyar sunan (Angrybird) da ta sanyamishi. Saidai har ya kammala rurinsa baki d'aga ba. Bata sauke wayar data kunnenta ba sai gashinan ya kira. Ta shige d'akinta tana goye da Hanif wanda yayi bacci a bayanta.
"Assalamu alaikum."
Yayi sallama cikin tattausan muryarsa. Ta lumshe ido ta bude tana murmushi.
"Waalaikumussalam, Barka da rana Yaya."

"Bintunaa! Ya dace a chanjawa Yaya suna, a k'ara mishi matsayi please."
Tayi shiru batace komai ba, ya d'ora da fad'in.
"To gayamin ya kike? Ina bebina?"
"Lafiya lau, gashinan yayi bacci."

Ya jinjina kai kamar tana ganinsa.
"Masha Allah. Kinsan ina nake kuwa?"

"A'a " "Gamunan tare da Abba munzo daurin aure Katsina."
Ta zaro ido. "Katsina?"
Yayi 'yar dariya. "Hey, kin tsorata ko? Ba kwana zanyi ba ai, zanzo ki bani karfin mata goma."

Ai tuni ta kashe wayar tana dariya, shima dariyar yayi cikin jin wani irin nishadi marar misaltuwa. Bata motsa daga inda take tsaye ba ta ji shigowar sak'o. Ta bud'o.

"Kina k'ara burgeni Bintuna, miss you! Ayi mana addu'ar dawowa lafiya."

Ta karanta yafi sau biyar da wani, k'arshe ta zauna gefen gado tana cigaba da karatun. Wani sanyi ne takeji yana ratsa zuciyarta, wai kuwa dagaske Yayanta Ma'aruf d'inne kuwa? Wannan Ma'aruf din da suke yawan samun sa6ani har Mami kan kirasu mage da 6era?
Sai kuma ta ji tanason ba shi amsa.
"Miss you too, Allah Ya maidoku lafiya YAYANA."

Ya saki ajiyar zuciya. Wai meke faruwa haka? Da ace ba gida guda suka task da Bintu ba, kuma baisan soyayya ba, zai iya rantsewa ko wani abin tayi mishi ya soma sonta har haka, irin son da babu wacce ya ta6a yiwa sai Ma'unsa.


Ita kuwa Bintu da wuri ta kammala ayyukanta don wajejan hudu na yamma ya shaida mata sun taho. Ta k'ara gyara Hanif ta shiryashi cikin kana kaya marasa nauyi. Itama ta shiga da zummar wanka, ta zaro ido ganin abinda bata zata ba. Tayi shiru, ashe fa tuni aka shiga sabon wata. Hakanan ta hakura ta kimtsa jikinta ta fito.
Batayi wani shiga mai birkitarwa ba kawai ta sanya yadinta marar nauyi mai hannu (3quater) dinkin doguwar riga, saidai ya kamata.
Haka ya dawo gidan har da ledarsa ta kaza a hannu. Dariya ta ciyota alokacin da ta sanya hannu tana kar6ar ledar. Ya matso da ita.
"Ya akayi?"
Ta sunkuyar da kanta tana girgiza kai.
"Bakomai." Tayi furucin a hankali.
Yayi 'yar dariya. "Ashe inada maganin tsiwarki? Lallai nayi sake a baya. Yau dai (the game will be over).
Daga haka ya shige dali yana wani takun kasaita har batasan sadda tayi dariyar mugunta ba


(Kuyi maneji da wannan ..kuyi hkr wlh ba da son raina yake kadan ba.!!)
[7/27, 1:40 PM] ‪+234 806 038 4145‬: ¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<46>>

Bayan sallar Magriba, suna zaune yana wasa da Hanif ita kuwa ta dukufa tana zubamishi abinci kana ganin fuskokinsu kasan suna cike da jin nishad'i. Shi nasa na murnar yau zai samu abinda ya jima cikin tsananin so da bukata, yayinda ita kuma ya had'e mata biyu, ga hirar da sukeyi cike da nishad'i ga kuma na muguntar da Ma'aruf baisan da zamansa ba, har sai kuma ta ji ya bata tausayi.
"Wai Bintuna duk me ya sanyaki wannan fara'ar?"
Ta dubeshi ta kauda kai tana murmushi.
"Bakomai."
Murmusawar shima yayi, zuwa yanzu ya gama fahimtar ita dinma tana sonshi, kawai dai jan aji ne irin na mata.

Misalin goma da rabi na dare, suna zaune daga shi sai ita a falo, Sarah da Hanif sunyi nisa da bacci. Ta mik'e tsaye, ya rik'o hannunta wanda ta jishi har kwanyarta. Ta dubeshi, idanunsa a lumshe.
"Ina zaki?" Ya nemi sani da muryarsa wacce ta chanja sanadin tunaninta da ya fad'a.
Ta kuramishi idanu.
"Zanyi shirin kwanciya ne."

Ya saki hannun bayan ya sauke idanunsa akanta, ta kauda nata da sauri sai kuma ta shige.

Bayan ya shirya ya sanya hannu ya dauki wayarsa ya kirata, tana gani ta k'i amsawa saboda wani nauyinsa da takeji.

Ta zubawa wayar ido yanata ruri, alokacin ne kuma ta ji shigowarsa dakin. Ta mik'e tsaye da sauri, sai kuma tayi k'as da kanta ganin ko riga babu a jikinsa. Ya dubeta daga sama har k'asa, sannan ya sauke ajiyar zuciya ganin irin shigar da tayi wanda shi kadai Allah Ya yarjewa gani.

"Meyasa bakya amsa kirana? Sai ma ido da kika zubawa wayar?"
Ta girgiza kai, baki bari tayi magana ba ya soma abinda ya matsu da shi.
Har saida ta kaisu da zubewa a k'asa. Alokacin kuma ya d'ago ha6anta har numfashinsu na bugun hancinansu da sauri-sauri.
"Tashi muyi sallah."
Shaf, ta mance da batun rashin sallarta sai alokacin. Ta lumshe idanunta, murya na rawa ta amsa.
"Bani da sallah."
Ya saki ha6anta yana murmushi, duk a zatonsa wasa takeyi.
"Bari na gani."

Ya d'ago ya dubeta kamar yayi kuka, sai kuma ya mik'e ya fita kawai. Tausayinsa ya kamata, da kyar ta iya mikewa ta kashe fitilu ta kwanta. Babu jimawa da kwanciyarta, ta ji shigowarsa hakan yasa ta saurin rufe ido. Kwanciya yayi ya juyota jikinsa ya sumbaci goshinta.
"Allah Ya tashemu lafiya."

Ta amsa a hankali. Cikin dare ya kasa saita kansa, haka yayita juyata son rai yana yanda yaso, kafin a karshe ya mike ya bar mata dakin. Ta bishi da kallon tausayi yanda yayi mata da kuma kalaminsa gareta har yana furucin bazai iya rayuwa babu ita ba.
Ta lumshe ido tana murmushi a haka sabon bacci yayi awon gaba da ita.

Shi kuwa tun daga ranar ya rage ra6arta hakanan ya rok'eta da suturta jikinta duk sadda suke tare kada ya sa6a umarnin Mahaliccinsa.
Idan kuma ya fita aiki, ta fita makaranta suna tare a waya, bini-bini ya kirata har itama ta saba da kiransa idan ta ji shiru. Baya dawowa gidan sai magriba, haka zasu zauna suyita hira, gaba d'aya yanzu ya sakar mata har ta daina kunyarsa. Hirarsu a yanzun ya bambanta da na baya don hirar soyayya ce da mutunta juna.
Kamar dai a yau, tana kwance saman doguwar kujera tana lissafa kwanakin period dinta, a goben ne take da kwana bakwai cif wanda a kwanan zatayi wanka. Ta ji shigowar motarsa da tsayuwarsa. Saidai kafin ta motsa wayarta ta hau k'ara, ta dauka ta duba. Tayi mamakin ganin yayannata ne. Ta d'aga da sallama, ya amsa.
"Ki fito, yau zance nazo."
Abin ya bata dariya. Ta amsa da toh.
Dakinta ta shiga ta k'ara kallon kanta. Riga da siket na brown lace ne a jikinta, tayi kyau ya zauna d'as a jikinta. Ta k'ara feshe jikinta da turare ta murza jan baki. Mayafinta ta dauka marar nauyi ta yafa a kafad'arta, sannan ta zura takalminta mai tsini ta fita.
Hanif na tare da Sarah a d'aki, bata bi ta kansu ba ta fita.

Yana sanye da shadda sky blue, hularsa kuma dark blue. Dinkin boda, ya zauna sosai jikinsa, yayi kyau har ya gaji. Kafarsa d'aya ya tankwashe saman kujera, kansa kwance a kujerar ya zubawa hanya ido, a sannu kuma yana sauraron kid'an dake tashi a rediyon motarsa. Ido ya zubamata sadda ta fito tana wani irin taku na jan hankali, bata ganinsa sakamakon gilashin ba haske, saidai jikinta ya bata ita din yake kallo. Yasa hannu ya bud'e mata gaban motar tun kafin ta k'araso. Ta shigo ta rufe. Tayi mishi sallama. Ya sauke ajiyar zuciya don baisan Bintu na da kyau haka ba saida ya soma sonta. Ya amsa yana tambayarta mutan gida
Abin ya sanyata dariya.
"Wai Yayana menene haka?"
Hannunta ya rik'o.
"K'ara'i, sonki ya sanyani Bintuna."
Ta zaro ido tana dubansa, baki ta6a cewa yana sonta ba, zataso a yau ya furta. Ya hura idanun.
"Bakya sona ne? Yau fa baki zaki bude malama, hira ta kawoni, zan bayyana miki sirrin dake raina."

Tayi farr da ido, ya kauda kai yana wani irin murmushi, ya kar6i wannan sak'on.
[7/27, 10:30 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<47>>

"A baya, nayi zaton mace d'aya ce ta dace da ni, mace d'aya ta dace na mallakawa komai nawa. Nayi zaton yanda nake, ni d'in MIJIN MACE D'AYA ne, banyi aune ba, mutuwa tayi min YANKAR KAUNA da matar da na so na kuma fi sonta fiye da kowace mace a duniya."
Ya d'an tsagaita kafin ya cigaba da magana.
"Na zo nayi biyayya bayan da na jajircewa zuciyata na yarda da KADDARA, na aureki."
Ya k'ara matse yatsunta yana dubanta duk kuwa da cewar idanunta baya gareshi.
"Bintun Mami, Bintun Ma'aruf. Kinsan me yafi had'ani dake?"
Sai lokacin ta dubeshi ta girgiza kai gami da turo baki. Yayi 'yar dariya.
"Bakya ji, na lura kina da fitina da tsokanar fad'a. Ba kuma sai na fad'amaki wanene Ma'aruf ba. Wannan shine ya kawo rashin jituwarmu. Kafin kuma na zo na had'u da jarabta ta sonki. Ban k'ara sanin ina sonki ba, sai bayan da na nisanta gareki har na kwanaki talatin da d'aya, zuwana Lagos kenan. Bayan na dawo nayi kokarin soma janyoki a jikina domin nuna miki irin so da kaunar da nakeyi miki a aikace batare da na furta ba."
Ya d'anyi shiru yana mai cigaba da murza yatsunta, ta sauke ajiyar zuciyar tana kar6ar sak'on a sannu-sannu.
"My Queen."
Yayi furucin da wata muryar da ta ji kamar ba ta shi ba.
"Ina sonki, ina kaunar na kasance tare da ke har abada. Kin shirya kar6ata matsayin miji kuma uba ga 'ya'yanki?"
Ta sunkuyar da kanta k'asa. Gaskiya ne, da ba'ason zurfafa k'iyayya a addini, bakasan sadda zaka soma son abinda kake k'i ba.
Ya d'ago ha6anta.
"A'a my queen, you have to answer me."
Ta lumshe idanunta. Murya na rawa ta furta a hankali.
"Na amince, ina sonka."
Haka yayita aika sak'o kafin ya barta yana murmushi ya soma da bud'e kofofin.
"Nagode my queen."
Daga haka suka shiga ciki, ran kowannensu k'al.
Ranar ma basu raba shimfid'a ba.

Washegari kuwa da Magriba, yana shigowa ya risketa tana sallah a d'akinta. Ai baisan sadda ya washe hak'ora ba don farinciko sannan ya juya zuwa d'akinsa.
Abincin daren nan dakyar ya ci. Ita kuwa gaba d'aya ta tsorata da yanda ya soma nunamata. Haka dai ta daurewa zuciyarta ganin ya riga ya gama matowa.
A daren bayan sunyi sallar nuna godiya ga Mahaliccinsu yayi musu dogon adduoi.
DAREN ALKHAIRI KENAN...!

* * *
Kuka takeyi sosai, yana rarrashinta, dole tayi shiru ganin yanda duk ya bi ya damu kansa da kukannata.
Da kansa ya taimaka mata ta tsarkake jikinta kafin ya barta ta k'arasa.
Ranar ya tsinci kansa da wani irin farinciki marar misaltuwa. Lallai Allah Ya mishi babbar kyauta, a yau gashinan ga madadin Asma'u. Yau shi ya taimakawa Sauda da d'awainiyar gidan, ita kuwa kunya ce ta hanata fitowa ma.
Tana jin shigowarsa d'akin tayi saurin ture kanta k'ark'ashin filo. Ya k'arasa yana dariya ya hau yi mata cakulkuli, babu shiri ta hau dariya gami da ture filon.
Ya sumbaci goshinta, ta lura yanason yin hakan kafin ya kwanta ya soma yi mata wasu nauyayyun zantuttuka acikin kunnenta. Zata mik'e cikin zafin nama ya janyota, tayi narai-narai da ido, kwalla suka cikamata idon.
"Don Allah kayi hakuri."
Ya kwaikwayi muryarta.
"Don Allah ki nunamin karfinki na mata goma."
Ai sai ta tura kanta jikinsa tana dariya. Yayi mata kyakkyawan runguma.
* * *
Acikin wannan satin, ba'a cewa komai. Da ka gansu kasan suna cike da more rayuwa babu wata matsala a gabansu. Sai gashi wata muguwar shakuwa ta daban ta shiga tsakanin Bintu da Ma'aruf wanda ta bawa kowa mamaki.
Akwai sadda da yamma suna zaune gaba d'aya a falon Mami ana hira har Hashim da Sally wadanda suka kawowa Mamin ziyara, lokacin sauran kwanaki biyar ya rage bikin Aisha.
'Yar kwarewa Ma'aruf yayi, nan da nan Bintu ta rikice ta mance a inda suke ta hau shafa bayansa tana mai mik'a mishi ruwa. Cike sa tausayawa tace. "Sorry my king."
Ya amsa, gyaran muryar da Rufa'i yayi ta farkar da su. Mami dai kauda kanta tayi kawai tana murmushi, yayinda Rufa'i da su Hajara suka sanya dariya. Ma'aruf ko a jikinsa sai ma ita Bintun ce ta dan ji nauyi.
"Oh, Allah Hakim, yau 'yar Mami ce ke wannan rikicewar akan abin gudunta? Soyayya lallai tana dadi
"
Mami ta mike don sai alokacin ta ji kunya. Daman ita Bintu ke kunyar, ai kuwa tana bada baya ta dubi Yaya Rufa'i.
"To meye? Wasu ma suyi mana."
"Lah, ni kike gayawa haka? Eh lallai, kinmanta sadda yake bulale ki nake yare miki? Aisha kinga halin d'an adam."
Bintu na dariya ta zauna gefen mijinta wanda ke sauraronsu da murmushi dauke saman fuskarsa.
"To ai bulala ce ta soyayya, yanzu ba gashinan tayi rana ba, ai hakane ko my king?"
Suka tuntsire da dariya har Ma'aruf din.

"Yes my queen, ashe kingane. Ku dai ku rike girmanku ba'a shiga tsakaninmu da queen, ko harshe da hak'ori ma haka suka ganmu suka kyale. Ato."
Dariyar aka k'ara. Hashim ya d'ora da fad'in.
"To d'an iska, dadin abin dai..."
"Ya isa." Ma'aruf ya dakatar da shi ta hanyar mik'ewa yana dariya gudun kada yayi mishi iskanci.
"Malam tashi muje ku gaisa da Abba."
Haka suka wuni cike da jin wani irin annashuwa.

* * *
BIKI BUDURI....!

((SAIRAN POST DAYA KO BIYU IN SHA ALLAH..!)






[7/28, 7:00 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<48>>

A yau ake bikin sanya Aisha a lalle. Wannan yasa gidan nasu yake a cike da 'yan uwa, cikinsu kuwa har da mutanen Rano. Wannan karon har Umma abokiyar zaman Inna itama ba'a barta a baya ba wajen halartar bikin autar Mami.
Bintu babu zama, sune wancan babban shagon na kayan kicin, sune acan shagon gyaran gashi.
Ya zamana ta dawo gidan da zama, duk yanda Ma'aruf yaso hanawa bai samu hakan ba kasancewar ta samu daurin gindi wajen Mami.
A daren da akayi kamun Aisha, suna zaune a can d'akinsu tare da su Atika harma da Hafsa kanwar Ma'u wacce itama takanas ta zo kwana adalilin mijinta yayi tafiya, kasancewar gidansu basu da sa ido ballantana har abin ya zama wani babban al'amarin da zai shafi ZUMUNCI A YAU.
Sai hira sukeyi suna kyalkyala dariya. Rabin hirar kuwa Atika ke basu akan matar saurayinta. Yanda yake bala'in shakkar daukar koda wayarta a gaban matar.
Wayar Bintu da tayi k'ara ya sanyasu dubanta suna tsokana.
"Toh sarakan soyayya."
Ta murgud'a baki tana dariya kafin tace suyi shiru ta d'aga da sallamarta.
"My king, fatan dai ka bar fushin?"
"Idan kinaso na daina, zo ki sameni anan d'akina. Ta zaro ido.
"Lah, baka tafi gida ba? Karfe goma fa " Yayi 'yar dariya.

"Kina wasa, ai na gayawa Mami saidai nima na kwana a gidannata."
Ta hadiye dariyarta, suma tasu suka gimtse don kuwa a hands free wayar take.
"Allah Sarki My King, shikenan ai, da safe Dan dolo sai ya mik'o maka kayan karinka. Allah Ya tashemu lafiya."


1 Comments On BINTU
avatar
ikleemah

11 months ago

Reply

The novel is good and sweet

Please Login or Register in order to submit comment