Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk da haka ta bi bayanta, ta juyo don ganin ko Bintu ta taso, saidai ga mamakinta kamar bata san wainar da suke toyawa ba, k'arshe ma talabijin ta nufa ta kunna ta dauki remote ta zauna ta soma controlling. Aisha ta shige kawai ta kyaleta.
Hankalinta ya tafi a kallon wani series wai Saloni(gwalo) wayarta ta d'auki k'ara.
"Suhail." Shine sunan da ta gani
Saurayi ne k'arami wanda koda zai girmeta bai fi ga bata shekaru biyu ba, aboki ga k'awarta, Maijidda. Ta dubi k'ofar da Ma'aruf ya fito d'azu, babu alamun fitowarsa yanzun, hakan yasa ta d'agawa.
"To sarkin takura rayuwa, kaidai bansan wane irin saurayi bane. Babu kud'i sai afkin kiran waya ka cikani da 6a6atu."
Suhail daga d'aya 6angaren ya kyakyace da dariya, yana son bugowa Bintu ko don abin dariyarta.
"Amma kin raina ni wallahi, haba 'yanmata, a cikin samarinki goma da wuya ki samu biyu irina."
Ta yamutse fuska kafin kuma ta saki dariya.
"Waya gayamaka ina da samari da yawa? Kai d'aya ne na k'arfen."
Farinciki ya mamaye Suhail. Sun jima suna hira da wasa da dariya kafin tace ya kyaleta ya isheta da zuba. Bayan ta ajiye wayar tayi magana a fili.
"Banza, yaro da shi sai karambanin tsiya. Ni dama zai aikomin kati ya fiyemin wannan zantukan marasa alkibla."
Tana d'ago kanta sukayi ido hud'u da Ma'aruf tsaye, saidai bai k'arasa fitowa daga d'akin ba. Sanye yake cikin shadda fara tas. Ya d'ora' bak'ar hula a kansa. Kallonta yakeyi kallon tuhuma, gaba d'aya ta tsorata. Ta had'iye miyau.
"Yau babban yaya da la6e." Ta fad'i a ranta. Ya k'arasa fitowa ya zauna a gefenta kafin ya sanya hannu ya d'auki wayarta. Ya gama bincikensa a contact, abin mamaki sunayen da ta sanyawa samarinta ya bashi dariya sai murmushi kawai yakeyi. Akwai Banki, Malam K'eya, Sarkin Nanaye, sai Suhail 6a6atu. Ya dubeta.
"Abinda kikeyi kenan a makarantar? Duk a ina kuka had'u?"
Ta sunkuyar da kanta tana wasa da zobunan yatsunta biyu kamar wata saliha.
"Ni babu wanda na janyo."
Kamar yayi magana sai kuma ya barta, ya ajiye wayar ya d'auki remote.
"Ina Aisha?"
Ta tsuke baki. "Tana taya Ma'u girki."
Cikin tsananin mamaki ya dubeta.
"Ma...what?"
Sai lokacin ta tuna a inda take.
"Su6utar baki ne wallahi Yaya. Ina girmamata ai, Anti Ma'u."
Baice komai ba har ya kamo Al-jazeera. Ta yamutse fuska, ta mik'e. Ta gwammace ta koma kicin wajen su Aisha da dai ta zauna kallon wani Al-Jazeera.
"Zo nan."
Ta tsaya kafin ta juyo ta dubeshi. Shima ita d'in yake kallo. Gaba d'aya sai yayi mata kwarjini, ta tako a sannu ta zauna saman kujera inda ta tashi.
"Gani."
Ya k'ara murya kad'an.
"Zauna, ki dunga fassaramin abinda suke fad'a naji ko da gaske yanzun kin iya (English)."
Ta d'an dubeshi. Amma Yaya Ma'aruf ya raina mata wayo, lallai ma.
"Ina jinki."

[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<10>>
Ta muskuta tana duban talabijin. Yau zata rainamishi wayo tunda abin nashi hakane.
Tayi tsai bayan ta gama fahimtar inda labarun ya dosa. Akan yara masu (kwashiorkor) ne, har gasunan ana nunosu ana jawabinsu. Ta turo d'ankwalinta gaba, kafin ta soma magana.
"Ana magana akan wad'anda k'iba tayi musu yawa ne, da ace duk zasu koma kamar wad'annan da kwarai sun ji dad'in rayuwa kuma..."
Ba zato ya sakarmata rankwashi a tsakar kanta.
"Banga amfanin karatunki ba. Tashi ki bani wuri kafin na kwasheki da mari. Dak'ik'iyar kawai."
Ta mik'e da saurinta ta nufi kicin d'in, tana shiga ta kwashe da dariya, Ma'u da Aisha na tayata kasancewar suna jin abinda ke wakana tsakaninsu.
"Baki da kirki wallahi. Kin raina mijina Bintun Mami."
Bintu tana 'yar dariya ta amsa.
"Atoh, ya cigaba da takurawa rayuwata ya gani."
Sukayi dariya. Sun riga sun kammala, ta ja kujera ta zauna tana dubansu yayinda suke jerawa saman babban faranti.
Tana ta afkin girgiza k'afa, d'abi'ar da Mami ta hanata. Ma'u kawai take k'arewa kallo ganin yanda fatarta ta murje ta k'ara k'iba sosai.
"Tab, Anti Ma'u wallahi ki rage k'ibar nan, nan gaba zaki iya illah."
A mamakince suka dubeta.
"Illa wace iri kuma?" Cewar Ma'u.
"Yanzu misali, Yaya Ma'aruf ya k'ara aure tsab zaki tomasheta,wannan duka d'aya da wannan mulmulallan hannun naki kin kasheta."
Aisha ta ji hanjin cikinta sun kad'a. Yau Bintu ta janyomusu, mai fitar da ita sai Allah. Ma'u tayi murmushin yak'e.
"Hum, ballantana ma bana tunanin Mijina na sha'awar k'ara auren. Sam, ba shi da wannan ra'ayin. "
Ta d'auki farantin ta fice. Dukan da Aisha ta d'aka mata a cinya ne ya maido da idanunta gareta ga barin kallon Ma'u.
"Kinsan abinda kike fad'a kuwa? Wallahi naga alama kina neman sanyamu cikin blacklist d'in anti ma'u. Yau mun shiga uku."
Bintu ta tsayar da ita ta hanyar yarfamata hannu.
"Ke dallah can kyaleni, ta sanyamu mana sai me? Nifa ba tsoranta nakeji ba. Ai duk laifinku ne, saida nace bazan zo ba kuka matsamin. Maganin kar ayi kar a soma."
Aisha dai tayi lamo kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.
"Aisha!" Muryar Ma'u ya katse mata tunani. Ta zaro ido
"Shikenan, ta sanarwa Yaya."
Bintu ta ta6e baki ta bi bayanta suka fito.
"Kuzo ku karya mana."
Bintu ta girgiza kai.
"Nidai na k'oshi, Mami fa cikamin..."
Kallon da Ma'aruf yayi mata ya sanyata yin shiru.
"Toh Aisha fa?"
Aisha ta girgiza kai.
"Na k'oshi Anti, mun karya kafin mu fito."
Zama sukayi suna duban TV. Bintu sai afkin satar kallonsu takeyi. Sai hirarsu sukeyi akan abinda ya shafi ambaliyar ruwan da ake nunowa anyi a wani gari a Aljazeera.
Can kuma tayi magana.
"Yaya zamu wuce."
Ba tare da ya dubeta ba ya jefo mata tambaya.
"Daman ba yini kuka zo ba?"
"Eh, gidan Yaya Rufa'i zamuje."
Sai lokacin ya d'ago ya dubeta.
"Ba zaku bar gidannan yanzu ba tunda ba a kurkuku kuke ba, idan na dawo anjima da rana sai na saukeku."
Ran Bintu ya 6aci, ta daure dai ta had'iye 6acin ran sannan ta koma ta zauna.
Aisha bataso furucin Yayan ba, don gaba d'aya ta tsorata da Bintu, tana tsoron kato6arar da zata k'ara yi musu.
Saidai Bintu ta bata mamaki, sakewa tayi kamar batace komai ba, itama Ma'un bata nuna komai a fuska ba. Saidai har zuciyarta ta ji ta tsani yarinyar, ta lura tantiriya ce ta bugawa a jarida. Dole tayi takatsantsan.
Sai bayan da Ma'aruf ya dawo suka tafi. Bintu zaune a baya. Tana ji yana tambayar Aisha ko itama tana kula samari. Tayi kamar batasan wainar da suke toyawa ba.
Can ta d'ago kanta, suka had'a ido, ta sauke nata tana murmushi kawai. Ba koyaushe takeson magana ba.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<11>>
Yana saukesu yayi gaba bayan ya basu dubu d'ad'd'aya. Sukaui godiya.
Hajara uwar surutu, nan suka had'u sukayita zuba kamar ruwan famfo. Yaya Rufa'i baya gidan bai dawo daga ofis ba. Nan sukayita kyakyata dariyar abinda Bintu ta yiwa Yaya Ma'aruf da matarsa.
"Ke dai Bintu zanso naga mijin da zai kwashi shiriritarnan ta ki." Cewar Hajara. Bintu tayi dariya irin ta rainin hankali.
"Mijin Bintu? Tab, yana k'asar waje yana karantar masters yanzu."
Suka gwalalo ido.
"Waye?" Suka tambaya har suna had'a baki.
Ta dubesu kafin ta cigaba da rainamusu wayo
"Yana nan, kulkum muna waya. Duk randa ya zo k'asar nan, zaku ganshi."
"Mts, mak'aryaciya kawai."
Aisha ta fad'a bayan ta d'agota.
"Ina batun k'arya anan?"
Aisha tayi murmushi tana duban Hajara.
"Ai nasan halinta ciki da bai. 'Yar iska kawai, wallahi k'arya takeyi.'
Bintu ya kyalkyale da dariya.
"Ho ni, ranar aurena akwai rawa da gira d'aya." Suka dara.
Ranar sun jima cikin nishad'i har dawowar Rufa'i. Shima ya biyemusu sukayi tayi, saida Mami ta kira wayarsu sannan sukayi azamar tafiya, Rufa'i da kansa ya kaisu gidan.
* * *
Bayan watanni Bintu ta soma zuwa jami'a, business take karanta. Aisha lokacin ta shige level2, ita kuwa, Accounting take karanta. Alokacin Hajara ta haifi d'anta namiji, wanda ya ci sunan kakansa Abba, wato Umar suke kiransa Sadauki. Cikin iko da hukuncin Allah itama Ma'u ta samu ciki saidai bisa matsalar da likita yace mahaifarta tana da shi, ya sanya aka k'ulle mata bakin mahaifar da fatan samun cikin ya zauna.
To fa! Bintu kai ya k'ara wayewa, an shiga jami'a. Kwalliya take ci har da na ban mamaki, a lokacin ta k'ara sanin rayuwa, tasan lallai ado shine mace. Hijabi idan ba don sallah ba, ko kad'an baya daga cikin suturunta na sanyawa ta fita, a cewarta yafi dacewa da gidan malamai. Aisha kuwa jefi-jefi takan sanya wataran ta fita makaranta.
Abinda zai burge mutum da Bintu, ko kusa bata da kula kulan samari. Idan kuma ka matsawa rayuwarta, toh fa alokacin zatayi maganinka ta hanyar cin kud'in da k'arya-k'aryacen ankon biki da na katin waya. Ga duk saurayi mai hankalin da ya fahimci ba don Allah take sonshi ba, nan take yake yanke mu'amalarsu. Idan kuma ta gane da iskanci kazo, ta zageka tas ta kuma gargad'eka da babbar murya.
A haka rayuwar ke tafiya.
Watarana tana zaune a baranda, sanye da T-shirt ja da zanin atamfa, kanta babu ko d'ankwali, ta bararraje tana shan rake tana kallon wata wak'a a wayar d'an dolo dake zaune gefen kujera shima yana fisgar rake. Sai dariya suke 6a66akawa da hirar duniya, Mami batanan ta fita, Aisha kuwa tana kwance a falo tana jinsu.
Babu zato Ma'aruf ya iso, sam basuji k'arar motarsa ba kasancewar a waje ya fakata.
"Kai bari na tura wak'ar nan wayata, tayimin kyau."
Cewar Bintu wacce hankalinta kacokam ya tafi akan wayar, gaba d'aya batasan da tafiyar d'an dolo ba. Hakanan batasan da zaman Ma'aruf ba a wajen.
Kallonta yakeyi a matuk'ar fusace, yana takaicin wannan taurin kai irin na Bintu da bata da aiki sai hira da d'an dolo.
Ya warce wayar kafin ya kai mata hauri da k'afarsa ya had'a da kai mata mari, da sauri ta kauce.
"Don ubanki bana hanaki mu'amala da mutumin nan ba? Ina rantsuwa da Allah sauran k'iris ya bar gidannan!"
Tuni ta soma hawaye, ranta ya 6aci, kamar ita k'atuwar budurwa wai Ma'aruf ke duka?
"Ai ba hira mukeyi ba, wata wak'a yake gwadamin."
"Wak'ar banza da wofi kai! Shashasha kin zauna kanki babu ko d'ankwali kina wagewa gardi baki. Zan sa6amaki wallahi!"
Ta mik'e ta tattara wayoyin ta nufi ciki tana kuka, bata tsaya a falon ba ta zarce zuwa d'akinsu. Yaya Ma'aruf ya tsani ganin walwalarta, tun tana k'arama ya takurawa rayuwarta. Lallai zata bar gidan nan idan har ba zai kyaleta ba. Ta yi kwafa kawai.
Mami koda ta dawo, bata goyamata baya ba, haka tayi mata fad'a ita dai a ganinta kowa ya tsaneta ne kawai.
Hakan yasa ta dauki fushi da mutanen gidan. Daga gaisuwa bata k'ara cewa uffan ga kowa. To gidan ya koma babu dad'i garesu, daidai da ma'aikatan Mami suna jin dad'in zama da Bintu, da wuya kuyi hirar mintuna uku bata sanyaka dariya ba. Abba da kansa ya rarrasheta don kuwa samunsa tayi tace zata tafi Rano. Mami jikinta yayi sanyi, tana son Bintu, wannan ne dalili babba da ya sanya ta d'aukota daga wajen k'anwarta Dije.
Nan ta shiga nan nan da ita har ta ware. Washegari ran Mami yayi fari k'al ganin Bintu ta shirya ta nufi makaranta, don har makarantar ma yaji tayi masa.
* * *
Bayan watanni tara, Aisha ta koma gidan Yayanta Ma'aruf domin taimakawa Anti Ma'u. Gaba d'aya daman an hanata aiki mai wahalarwa, cikinta ya girma cikin hukuncin Allah saidai a yanda likitan ya fad'a, cs zasuyi mata, har an sanya (Date).
Suna samun hutu Aisha ta koma gidansa. Bintu ko daman Rano takeson zuwa, rabonta da Rano tun kafin ta soma zuwa jami'a. Saidai zuwa yanzun tana matuk'ar tausayawa Ma'u musamman yanda ciki ya sanyata ramewar dole. Har mamaki Aisha da Mami kai harma da Hajara sukeyi idan sun ga yanda Ma'u da Bintu ke d'asawa. Kodayake, Bintu bata da raini a zahiri, barta dai idan ta so zata kwa6a maka magana a wasa. Tana da fushi amma bata da rik'o. Sannan a gaban Ma'u ta sha fad'amata. Ta k'i jinin mijinta, tafi k'aunar zuwa gidan Yayanta Rufa'i akan Ma'aruf. Da Ma'u ta fahimci halin na Bintu haka yake, sam bata da 6oye abinda ke ranta, yasa ta bar damuwa.
Kwananta uku a Rano, aka yiwa Ma'u aiki.
Suna zaune tsakar gida suna hira da yayanta Saifullahi, sai kannenta, Habib da Habiba, da Innarsu sai 'ya'yan abokiyar zaman innar, wacce suke kira Umma .
Wayarta tayi k'ara ta duba. Ganin sunan A'i yasa ta d'agawa da sauri.
"Me muka samu?"
"Baby Boy." Cewar Aisha cikin tsananin murna.
Ihu Bintu ta saki tana mai tsananin farin ciki.
"Ta haihu! Ta haihu!!"
Haka ta hau fad'i. Nan su Inna suka shiga murna da hamdala.
Washegari kuwa wajejan tara na safe, Inna da Bintu sai Saifullah suka nufi Kano.
Tunda Bintu ta shaidawa Mami sun taho ta kashe wayarta. Basu jima sosai ba a hanya (inji ni..lol) suka iso Birnin Kano.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<12>>
Gida Saif yaso su soma nufa, saidai Bintu tace ita kam asibiti ya kamata su je su ga lafiyar baby da mamansa. Inna ta goyi bayanta. Bintu ta bud'e wayarta a lokacin da motarsu ta shigo harabar asibitin. Layin Aisha ta soma nema. Saidai yana ta k'ara ba'a d'aga ba. Ta kira lambar Mami, cikin sa'a ringing uku ana hud'un Mami ta d'aga.
"Mami gamunan a asibitin, a wane 6angare kuke?"
Ta ji shiru kafin ta ji muryar Mami a sanyaye.
"Ku dawo gida mu ma gamunan a hanyar gidan."
Kafin Bintu tayi magana Mami ta katse. Ta dubi wayar da mamaki.
"Ya akayi ne?" Cewar Inna da ke tsaye tana jiran shigarsu. Bintu gaba d'aya jikinta yayi sanyi.
"Bansani ba, wai an sallamesu, tace muje gidan. Mamin ce ta sanyayarmin da jiki, duk muryarta ta chanja."
Inna tayi shiru tana ambaton innalillahi a zuci, tasan ba k'aramin abu ke sanya yayarta shiga wani hali ba. Ta soma kokarin shiga mota.
"Ai sai mu k'arasa."
Suka hau sai gida.

Cikin fad'uwar gaba, suke duban k'ofar gidan ganin motoci fin uku.
"Wannan motocin duk na barkan ne?"
Cewar Bintu.
"Ina tunanin haka."
Baba maigadi ya bud'emusu kyauren suka shiga, anan ta ga su Abba tsaye tare da mahaifin Ma'u wanda ya kasance k'anin Abban, sai sauran 'yan uwansu.
Suka gaisa sannan suka k'arasa ciki, Saifu ya bisu da akwatin Bintu. Gaba d'ayansu jikinsu a sanyaye. Kuka kawai kakeji daga falon Mami. Ai da gudu Bintu ta k'arasa, duk taron jama'ar dake a falon, bata kasa hango Aisha ba. Itama a guje ta k'araso ta rungumeta.
"Munyi rashi Bintu, Anti Ma'u ta rasu."
Ai ji tayi kamar an bugamata guduma a k'irji sakamakon wani bugawa da yayi.
"Ke kina da hankali kuwa? Haka mutuwar take?!!"
Ta fisge jikinta da gudu ta nufi wata 'yar uwar Ma'u da suke uwa d'aya uba d'aya.
"Anti Zainab, ina Anti Ma'u?"
Cikin kuka Zainab ta k'ara jaddada mata lallai babu Asma'u, Asma'u ta rasu."
Kai Bintu ta ga tashin hankali. Da wayonta, batasan mutuwa ba. Kuka takeyi tana tambaya.
"Haka mutuwar take? Innalillahi."

Suna ji suna gani aka tafi da Ma'u makwancinta na gaskiya. Ko ta kan jaririn bata bi ba ballantana ta sanyashi a ido.
Har magrib bata saki ranta ba, babu abinda take tunanowa sai yanda Ma'u ke hak'uri da dukkan abinda take fad'amata duk furucin da ya zo bakinta akan mijinta.
"Allah Sarki, halinki na gari ya biki. Allah Yayi miki rahma. Aisha, ina Yaya Ma'aruf?"
Aisha ta ja majina.
"Yaya Ma'aruf yana asibiti, amma naji Mami tace sunyi waya da Rufa'i, yanzu zasu taho. Shi fa yana ganin an fito da ita bayan an shiryata ya suma. Har zuwa yanzu, bai k'ara sanin inda kansa yake ba sai yanzun. Yaya Ma'aruf ya ji mutuwa Bintu, yana son Anti Ma'u kamar ransa."
Bintu hawayenta suka k'ara zubowa. Ta tunano baya, ta jinjina kai. Ita tasan yana k'aunar Ma'u.
"Ina Bebin?"
"Yana wajen Anti Amina. Ta amince zata shayar da shi, mijinta bai hanata ba."
Tausayinsa ya mamaye Bintu. Ta mik'e ta fito zuwa wajen da Anti Amina take. Saidai ta tabbatar mata yana d'akin Mami yana bacci. Batayi k'as a gwuiwa ba ta nufi d'akin Mami. Can ta hangoshi cikin gadon jarirai yana baccinsa lafiya lau.
Ta bud'e (net) d'in ta rik'o yatsunsa. Yaron sak mahaifinsa, babu abinda ya bari. Hawaye kawai take shatatarwa na tausayinsa. Shikenan ya zama mara uwa. Abin akwai tausayi. K'aunar yaron ya shigeta kwarai. Nan ta kwanta tana dubansa har bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita itama. Don jiya batayi baccin kirki ba sakamakon d'oki da son ganin Ma'u da bebinta da takeyi.
A haka Mami ta shigo ta iskesu.
"Wani abun sai Bintu, kya bud'ewa yaro (net) sauro ya cijeshi?"
Bintu batasan ma tana yi ba. Mami ta gyara mishi rufin net din ta fita.
* * *
Washegari da asuba Bintu ta farka babu yaro a gefenta. Inna ke sanarmata yana can wajen Amina a d'ayan d'akin. Suna cikin haka Mami ta shigo.
"Mami don Allah kada a d'auke baby daga gidannan."
Mami ta sauke ajiyar zuciya jin k'orafin Bintu.
"Shi kansa uban yaron bai amince ba, yace a samo mai shayarwa ko nawa ne zai biyata da dai yaron yayi nisa da shi."
"Haka ma yafi wallahi Mami. Idan ya koma gidan Anti Amina ba zamu k'ara ganinsa ba fa. Kema nasan bazaki so ya bar nan ba."
Mami ta d'auki hijabin sallarta wanda shi ya maidota d'akin daga d'akin Abba.
"Bani da iko, sai abinda Abbanku ya fad'a. Bari dai muga yanda za'ayi."
Daga haka ta fice. Bintu ta fad'a bandaki tana fad'a a fili.
"Banda mutuwa ma, me zai raba d'a da uwarsa? Kai, Allah Ya bamu kyakkyawan k'arshe."
Inna daga saman darduma ta amsa da amin.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

©Rufaida Omar
(July...2016)

<<13>>

Bintu bata samu yiwa Yayan nasu gaisuwa ba sai wajejan sha d'aya na safe. Shi d'inma, aikenta Mami tayi akan yazo Abba yanason ganinsa, don gaba d'aya wayoyinsa a kashe suke.
Da sallamarta ta tura k'ofar, ba'a amsa ba. Kansa kawai take iya hangowa kasancewar ya juyawa k'ofar baya, ta tako sannu kad'an yanda take iya hangen fuskarsa. Fuskarsa ruwan hawaye ne kwance yayinda ya zubawa k'aton enlargement na hotonsa da Ma'u tun ma na lokacin da aka d'aura musu aure yana duba. Ta dubi hoton, ma'auratan sun dace matuk'a da juna. A dai fari da kyau, babu na yar wa. Allah Ya basu, kodayake jini d'aya ne.
Tunda take a rayuwa, bata ta6a jin tausayin Yaya Ma'aruf ba sai a wannan karon da Anti Ma'u ta tafi ta barshi. Ga duk wanda ya zauna da Ma'aruf da Asma'u, zai gane irin tsantsar so da kaunar da sukeyiwa juna. A yau ga mutuwa ta yi musu YANKAR K'AUNA. Ta zauna a gefensa, ina ruwan Bintu, maimakon ta rarrashe shi sai kawai ta had'a kai da gwuiwa ta fashe da kukan itama.
Sai a lokacin yayi niyyar motsawa. Ya ji shigowar mutum, saidai bai san ko wanene ba. A yanzu kuwa da ya ji muryarta, ya ganeta.
"Nayi rashin madubi abin dubawa. Na rasa wani 6angare na jikina. Asma'u ta kasance wata fitila mai haskaka rayuwata, har abada bazan daina jin ciwon rashinta ba. Bani da tamkarta, a yanzu kuma bani da tamkar abinda ta haifamin."
Yayi shiru sakamakon hawayen da ya haneshi k'ara magana.
Bintu ta tsaida kukanta ta dubeshi cike da tausayawa.
Kawai sai ta k'ara rushewa da ihun kuka. Ya tsayar da hawayensa ya dubeta a mamakince. Wai daman tana da tausayi har haka? Ikon Allah.
Sallamar Mami da Abba ta katsesu. Itama jin shirun yayi yawa ne ya sanyasu biyo sahu don Abba har ya fito da zummar ganin abokansa da sukazo musu ta'aziyya.
"A'a, menene kuma haka? Ke ba kiranshi nace kiyi ba?"
Bintu ta mik'e tana sharar majina.
"Kuyi hakuri, kuka ya sanyani."
Abba ya girgiza kai sannan ya nufi wajensa ya zauna. Bintu ta fice daga d'akin. Nasiha mai ratsa jiki Abba yayi mishi. A k'arshe Mami ta d'ora sannan Abba ya umarceshi da yin wanka ya kimtsa ya fito amsar gaisuwa. Ya amsa da toh.
Ita kuwa Bintu kan gadonsu ta nufa kai tsaye bayan shigarta d'aki. Ta kwanta ta soma rusa ihun kuka.
"Allah mun tuba, Allah ka ji k'anmu ba don halinmu ba."
Aisha ta amsa da amin.
"Haba ke kuwa, ya dace kibar wannan kukan, duk masoyin Ma'u na hakika kamata yayi ya bita da addu'a koyaushe. Wannan kukan ba abinda zai rage mata."
Bintu ta zauna sannan ta share hawayenta.
"Hakane, Allah Ya jik'an Anti Ma'u."
To a k'arshe dai bayan anyi sadakar bakwai kowa ya watse, lokacin itama Inna ta wuce Rano. Gidan ya zama daga su sai su, sai ko Ma'aruf wanda Abba ya k'i amincewa da komawarsa gidansa adalilinsa na tsoron halin da zai jefa kansa saboda damuwa. Sai kuma Malama Atine wacce ita ke shayar da Hanif, yaron Ma'u.
Babu wanda ba ya ji da Hanif, daidai da 'yan uwan mahaifiyarsa sukan lek'oshi. Da wuya ayi sati batare da wani cikinsu yazo ganinsa ba. Bintu da Aisha kuwa, d'akin da yake nan ne wajen hirarsu tare da Atine muddin basu da karatu.
Tsakanin Bintu da Ma'aruf kuwa, raina mishi wayon da ta saba yi, ta rage sosai ganin yanda shi kansa ya sanyaya.
Saidai bayan watanni biyu ta fahimci ashe lam6o yayi ba wai ya chanja bane. Abinda ya had'asu kuwa shine.
Tana bacci gefen Hanif yaro mai watanni biyu, wanda saboda gata da kulawar da yake samu sai ka rantse d'an watanni hud'u ne. Cikin magagin baccinta ta d'ora mishi hannu a wajen hanci, ai kuwa yaro ya hau numfarfashi, Allah Ya taimaka Ma'aruf yayi sallama ya shigo wanda sam Bintu bata ji ba, Allah Ya yi ta mai nauyin bacci. Atine suna falo suna hira da 'yan aiki. Lokacin k'arfe uku na rana. Babu zato ya kai mata wawan duka a k'afa. Ta mik'e a gigice tana sosawa.
"Tsabar iskanci kashemin yaron zakiyi?! Atine! Atine!!"
Ai da sauri ta yo d'akin. Nan yayita bud'emata wuta. Ya kuma gargad'eta koda wasa kada ta k'ara yarda Bintu tayi bacci a gefen d'ansa.
Bintu ta turo baki tana dubansa. Ya danna

1 Comments On BINTU
avatar
ikleemah

11 months ago

Reply

The novel is good and sweet

Please Login or Register in order to submit comment