Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kam dan Allah
Baku yarda dani bane baba? Yai mata dakuwa"
ungo naki,,yar kota,, kimin bayani ya akai kika
samu motar nan mai tsada haka,tace "Baba bafa
abun mamaki bane dan dan siyasa yai kyautar
mota,, wlh ba abunda akai,,kuma bari na kira a
gaban ka kaji komai,. Taje ta dakko waya,,ta
bugawa Alhaji tasa a hands free,,"Assalam
Alaikum.. ya akai Sa'a,, ta gyara murya,,dama
godiya na bugo na maka,,yai murmushi, " kinfi
gaban nan Sa'a, ina son halin rike alkawari,,
tace"Wlh ban San haka kawai za'a Iya min
kyautar mota sukutum ba ba tare da nayi wani
aiki ba,,yai dariya,"ke kwa kikai aiki,,tunda kin
gyara min Matan gida na,, sannan kun tafiyar da
abun campaign bisa amana,kar ki damu,,.yi wa
kai ne,,sai dai ina fatan baki samu matsala a gida
ba??ta kalli su baba,,"Alhaji na samu,,dan basu

yadda da wannan kyautar ba ta fisabilillahi,,Yace
"kar ki damu,gobe da dare zan samu baban naki
da maganar,, tace" aa ba sai kazo ba,gashi a
kusa.
Baban ya karba,ya mishi bayani,shi saboda Allah
yai,da kuma ta gyara tsakanin iyalin shi,.sannan
shi wannan bai dauke ta a wata kyauta da Sa'a
ta fi karfi ba..dakyar ya yarda da Sa'a ta rike
motar,da sharadin babu gantali sosai a mota..
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/27, 2:01 PM] Feenat Ja'afar.
BARIKI...IYAWA
19_Lalle Sa'a, yarsu tana daga cikin wayan da
suka zo Duniya cikin Sa'a,, fatan shi Allah ya
cigaba da kare mishi Sa'adatun shi..Lalle kam
taci sunan masu sunan nata "SA'ADATU SA'AR
MATA..(na Damary en Feenat)..
Washegari gidan su Ummi aka fara sauka,, dan
tunda ta sa rai da mota tai joining class inda ake
training, cikin 4 days kwa ta Iya mota,,da
mamakin ta data shiga taji tana zugar ta..."
Wayyo dadi..da gudu ta shiga gidan su Ummi, ba
ko sallama "Qawata...Ummi.,woo fito kisha
kallo..ta fito daga kitchen da mamakin
sammakon Sa'a yau,,,dan sai 9 suke da
lectures,,suka ci karo" Sa'a,. Lfy?maman Ummin
ma ta fito,,jin sun wani kwalla musu ihu a cikin
gida.."Lfyn Ku kuwa yaran?ina ai har sunyi
waje,.ta girgiza kai "Allah ka shiryi Sa'a da
Ummi,.. Tai kitchen dan duba abinda Ummin ta
bari a wuta..da karadi suka shigo gidan"kai
shegiyar gari..kin Faso mu da yawa,yau dole mu
tada kura a schl..
"Duk dan uban da bai tayamu celebration ba
bamu bashi,..suka kyalkyala dariya., mama ta
fito,," zanga ranar da zakuyi hankali yaran nan..
Suka kallo ta,kan ta gaida ta, tace"oh Wai murnar
ta meye wannan? Da sauri Ummi tace"Mama
mota fa mukai?wanda zai aure ta senator nan ne
ya siya mata..da sauri Sa'a ta kallo ta, sai ta
kanne mata ido, "tace mama karya take wlh,,ni
saboda Allah ya ban dan na mishi campaign din
partn su..ta kallo Ummi, " kullum sai na ce miki
ban son karya,,ta kalli mama"mama nasan kin
yarda dani tamkar wacce ta Haifa ko? Maman ta
kada kai, ta kallo Ummi tare da Harar ta"ni zuba
mana abinci in kin gama,,ta kalli mama tare da
mata murmushi.. Sukai kitchen.
Tuni karya ta karu wajen Sa'a,, ansa bikin fadeela
itama,,tuni suka hau shirye shiryen biki,.za'a ai
nata kan nasu Ummi,,
Ranar ta fito a gida, tabi layin su Aminu a kafa
sukaci karo dashi,,da abokin shi,, tuni ta hade rai,
Shima yana ganin ta ya hade rai yaja ya
tsaya,,tai mai wani kallo kan ta dawo kan Aminu,
"angon mu,,ya akai? Yai murmushi bayan ya kare
musu kallo duka,," lfy lau,, yau ina motar na ganki
a kasa?ta yatsine fuska,, tana chan gidan da ake
ajiye ta,, Da sauri Hafeez ya kallo su,ta maka
mishi harara tare da kawar da kai..
Duk yana kallon su Aminu.. Hafeez yai dan

tsaki,,"malam kazo mu wuce ni,,ta tabe baki "ai ni
ban tsayar da wani ba anan., ta murguda baki ba
tare da ta kalle shi ba,,ya kalli layin yaga ba
jama'a kan ya dawo kanta" dallah rufen baki a
wajen,,ke har kin kai ki tsayar ni da?.tuni ta
kankance ido ta nuno shi da hannu "kar ka kara
ce min dallah chan..ya zaburo kamar mai jira,"
ance dallah din,,mey zakiyi?ta matso itama"kaima
Dallah chan toh,,Aminu mai zai inba dariya ba,,Bai
san mey yasa jinin su bai hadu da juna ba,tun
haduwar su ta farko,,kuma yasan duk din su ba
masu son fada da jama'a bane.."sarkin yan tusa
kai a mutum, ban damu da kai ba ka bi ka damu
dani,yai murmushi "ke a fada miki tusa kai,,
macen da tsabar rashin kamun kanta ba wanda
bai Santa ba,,da sauri ta kallo shi,zata tanka
Aminu ya shiga tsakanin su,," Wai Ku hala kuna
ganin hanjin juna koh??taja baya,, "kaci Sa'a wlh
yau Dana fada maka wacce har ka mutu bazaka
manta ni ba..
Taja tsaki tare da daga wa Aminu yatsun ta ta
wuce,,tuni ya cije lebe tare da rintse ido,, ya
bala'in tsanar tsaki,,kan ya bude ido har tai
nisa,," amma ya kamata kasan ba abu mey kyau
kuke ba,,ache kullum kuka hadu sai kun bar abun
fadi?kwanaki naji mey ya faru a super market ai a
wajen Ummi,,na rasa mey ke damun ka kwana 2
nan..ya kallo shi,shi kanshi bazai ce mey ke
samun shi ba,, shida maganar bakin shi ma
gagarar shi take,,amma ya rasa indai suka hadu
da Sa'a in basui ba baya ma jin dadi..
Haka akai bikin fadeela sukuku da ita,, idan ta
tuno kalaman Hafeez,, ta tsani a sha da ita a
rayuwa, gashi bata rama ba yazo abu na damun
ta..
Sun samu hutun makaranta a dai dai lokaci,dan
yau suka fara shirin biki,ranar Aminu yazo Yace
suzo suje rakasu zabar kayan taron,ta tambayo
mama suka fito,,da ganin Hafeez tace ta fasa
zuwa,,Ummi ta kallo Aminu,, da sauri ya fito,,"kar
ki mana haka Sa'a pls,,kin San dole sai da ke a
lamarin nan,, ya kamata ace abokin na da ta
Ummi sun hada kai a bikin nan,dan kusan kune
kan taron nan,ya kallo Hafeez "Dan Allah Ku
taimake ni a gama lfy,, ta hade rai kan ta
shiga,.ya sauke ajiyar zuciya..
A wajen masu decoration tai tsaye taki zama
ganin kujerar kusa da hafeez,,duk suka zauna aka
kawo musu drinks,Hafeez ya dau mai
strawberries da blue barriers,sai kallon shi take
tana yatsina fuska kamar taga kashi,,yai
murmushi kan ya tashi,,yazo zai wuce ta gaban
ta ta Matsa tana tsaki,ya kar kada kwalin yaji da
ragowar guntun,ya saita bayan ta ya watsa mata
kan yai waje,,taje ta zauna..
Sun gama kenan zasu fita Matar cikin da mijin ta
suka tsayar da su Sa'an, Aminu yai gaba" kinyi
staining ta bayan ki fa,,ta nuno Sa'a, take gaban
ta ya fadi,,tana mai rokon Allah yasa Aminu baiga
ba da Hafeez, yau da karyar ta ta kare..,toh
amma da mamaki fa,a satin nan ta gama period
dinta,kuma a zuwan farko baici har ya bata ta
haka ba,,Ya ilahi.,,Ummi ta juya,ta kalla,.kan ta
kada kai, dan tana ganin lokacin da Hafeez din ya

watso mata Jan lemon,,tace"Ke kwantar da
hankalin ki,lemo ne fa,,da sauri ta kalli Ummin,
"Lemo kuma?ta rintse ido, "wlh Hafeez ne ya
zuban,indai lemo ne,, tai kwafa,mu zuba indai
nice...
Allah yaso ta Ummi after dress ta dauro,, ta kallo
ta" bani abayar ki ki karbi gyale na..da sauri suka
kebe a cikin shagon sukai musanye..dan kunya
koh masu shagon bata kalla ba tai waje..a dai dai
windown shi ta tsaya tana huci..kan ta nuno shi
da hannu"wlh ka dau bashi ..ta bude mota tana
ta huci,,Aminu ya kallo shi yaga sai murmushin
mugun ta yake,,toh mey kuma ya faru? Dan yana
zaune baiga mey Hafeez din yai ba..Ummi ta
shiga tana kallon Aminu,,ta daga mishi kafada,,ya
kada kai tare da cewa.. "Allah ya shirye Ku
wlh,,kui ta abu kamar wasu yara kanana,, yai
tsaki,,.har akaje gidan kunshi ba wanda ya tanka
wa dan uwan sa,,basu suka gama ba sai kusan
5,aka karbo head din su da kayan sawa a wajen
mai guga na sawar gobe..
Hafeez tunda yazo kwanciya yake tunanin abinda
yai wa Sa'a dazun,sai yaji bai kyauta ba,,shi dan
tsokana yai mata badan tozar ci ba,, duk da tana
bashi mugun haushi in sun hadu amma yana son
yaga sunyi fada..sai dai yai alkawarin bazai
kulata ba gobe bare suyi abun fadi a wajen
partn..
Yau tunda suka tashi aka shiga busy,,sunsha
gyaran amare sai kyalli suke,, hannun nan yasha
kunshi,, tamkar duk dun sune amaren,, qawayen
su suma duk sunsha kyau,,tun 4 ta koma gida ta
kira Ali mai kula da motar ta ya kai mata ita
Wanki,tai latti bata bashi da wuri ba,ya karbi
mukulli jiki na bari yai gaba,dan yasan zai fadata
yau da motar da yamman nan,,ta buga wa Ummi
waya cewar a gida zata shirya,,tace " Dan Allah
toh Sa'a kar ki latti,,8 sharp,pls.ta kashe
waya,dan tun jiya take ji da fada.
By
Feenat Ja'afar
[10/27, 12:07 PM] 💍🛍🍬Salma🍬🛍💍: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afarSalma🍬Salma🍬🛍💍: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar🛍💍: FEENAT JAAFAR'S MOBILE BLOG

JUST ANOTHER BLOG

BARIKI IYAWA 3

[10/2, 5:57 AM] Feenat Ja'afar: BARIKI...IYAWA
20_Har yau da abun da ya faru a party,,sai da tai kuka mai Isar ta kan ta tashi
ta cire kayan ta,, tana mai kara tsanar Hafeez a rayuwa.. Mari??wlh ko uwar da
ta haife ta bata taba mata ba,,ta Shafa wajen,, a hankali ta furta"Allah ya isa
wlh,,badan ta nuna masa yau BARIKI ba da tuni an sha da ita ta warke,,wa ta isa
gaba tai wa fa fa kuma??

Shima yana zuwa gida ya tarar da su Hajiyan tashi a parlour,Tasleem da Zahra,,
gaba daya gefen rigar shi ya jike,,yai sallama ba wal wala a fuskar shi,,suka
bishi da kallo har ya shige dakin shi,,. Direct bandaki ya shiga ya cire ya
watsa ruwa,jikin shi har ya fara dankon exotic din,, ruwa na sauka a a kanshi
kawai hasko yadda take ta kuka yake da kokarin tada mota,,"Anya kana da hurumin
takura wa baiwar Allah nan kuwa Hafeez? Jiya ka mata 1,ta rama,mai ya kaika da
Marin ta??Ba halin ka bane wannan,, ya kada kai,,shi kanshi bazai ce ga dalilin
da yasa yake biye wa Sa'a ba har haka,, a Schl din su da mata da suka take Sa'a
a iskanci, toh amma mey yasa yafi jin zafin nata??ya kada kai,. "Dis is d
1st,and InshaAllah d last,,ba zai kara yadda makamancin hakan ta kara hada shi
da Sa'a ba kuma,tunda an gama biki, toh Alhamdulillah..
Hafeez Shehu Umar yan asalin Jigawa ne,,kakan su aiki ya kawo shi Kano,, anan
yai aure mata 3,har ya haifi yara bai waiwayi komawa Jigawa ba,, Allah ya bashi
yara guda 11,,Baban su Hafeez shine na 5 a gidan,,yana da kanne mata 4 da Yayye
maza 6,,Familyn suna da matukar hadin kan da bazaka gane wannan dan wane daki
bane,,duk Matan Sun zauna lfy cikin Aminci da juna,,sai dai dan abinda ba'a rasa
na yau da kullum ba,,duk gidan mutane 2 ne sukai boko,sauran duk muhammadiya
sukai,, Shehu da Sadiya aurar gidan..
Shehu yanxu da ya zama Alhaji Shehu,yana da mata 1 da yara 4,,Aunty
Maryam,Umar,Hafeez da autar su Tasleem,, Su gidan su Hafeez gidan yan boko ne
kamar yadda baban su yai boko har ya mallaki kujerar perm sect,,saboda haka
rayuwar su ta tafi cikin waye wa,,kowa na kaunar kowa,,Haj Fati itace Maman su
Hafeez,,Mace ce mai fada,musamman akan gaskiyar ta,,shi yasa yaran sunfi shayin
ta akan baban su,, dan shi kam mai sanyi ne,, Hafeez tun tasowar shi ba mai
shiga shirgin jama'a bane,asali ma Aboki 2 gare shi,daga Aminu sai kwa Zunnu,,
Musamman mata basa gaban shi,,tun kan ya tafi makaranta a indai, cikin birnin
Hyderabad,,Artist ne,, tun a secondary yake da burin zama,,Allah ya taimake shi
akai wa Baban shi hanya a a Sarojoni Naidu school of Arts and Communication,,.
Tunda ya dawo aka Matsa mishi da zancen aure,,ai shekaran shi 34,meye
meye,Yace"shifa bai da Matar aure,,tuni Hajiya Maryam tace ga Zahra,yar gidan
kanin Baban shi,,amma fir Yace "shi batai mai ba,,Haj Maryam tace kwa an gama
magana,,tunda zance yaje gun Zahra ta kasa sukuni,,dan Allah ya zuba mata dama
son shi,,komai nashi burge ta yake,, shikam a nashi bangaren baiga kalar
mafarkin shi a Zahra ba,,duk da su duk dangin su ba laifi suna da kyau,musamman
gidan su Hafeez din,,dan Baban su a Yola ya samo Maman su,,kakan su kuma fulanin
Jigawa ne,,.
Ranar ya samu baban shi da zancen Zahra, shifa batai mishi ba,, baban Yace yai
hakuri,dan zance har ya shiga family.. Tun daga lokacin ya dauke kafa a gidan su
Zahra, sai sai ya gaida baban su a waje ya arce,, ko kula tai da hakan,haka
kawai sai ta wanko kafa tace tazo wajen Tasleem, ko bata ganshi ba sai ta kwana.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/28, 1:18 PM] BARIKI...IYAWA
21_Washegari ma bai fita ba sai 11 Aminu yazo ya raka shi da abokan shi Gaisuwar
Sirikai,,.Aminu yai mamakin yadda yaga ya sau rai,tuni ya dawo Hafeez din shi na
da,, sunsha shadda sai kamshi suke suka shiga,,Aminu Yace su fara zuwa gidan su
tukun,.dai zasu karya kwana suka ga Hafeez ya tsayar da mota,, sanye take cikin
hijab dogo kusan kasa ruwan kasa mai hannu, da nikaf,amma ta dage shi saman
kanta,,rike take da Qur'ani da littafai na addini,tafe take fuskar ta babu
walwala., ido ya kara kar kade wa,, Aminu ya kallo shi"kai ma wa Allah kar ka
kulata, muje dan Allah tunda bata ganmu ba,..da sauri ya kallo Aminun, kan ya
kalle shi da mamaki"Wai da gaske Sa'a nake gani??Aminu yai karamin tsaki,."Dan
Allah ja muje,da wace in ba ita ba,,sauran abokan da basu San komai ba suka fara
"ko dai ta tafi da shine? Aminu ya kallo shi, sai dai da mamakin shi yaga Hafeez
din yai murmushi kan ya tada mota,.
Sun dawo daga gaisuwa ya tsare Aminu da tambaya., " Wai dan Allah da gaske Sa'a
na gani dazun??ya kyalkyale da dariya,,"Aa yan biyun ta ce,,.ya hararo shi, "Bar
zancen wasa, Allah da gaske nake,, Wai ina amaryar ne?? Aminu yai murmushi, yana
fatan abinda yake zai faru.. Ya kada kai yana murmushin mugun ta..dakwa wannan

drama zatai dadin gani,.Ummi ce ta fito ita da Kanwar ta,. Da murmushi take musu
sannu da dawo wa.." Yauwa amarya,. Itama da mamaki take kallon shi,, ganin jiya
a wajen Dinner irin rabuwar da sukai,, Aminu ya kanne mata ido,,ta sukui da kai
tana murmushi,, ya kallo ta,,"Amarya,dan Allah na tambaye ki man?ta kallo shi,,
"ok, Allah sa na Sani,,ya gyara zama,, kan ya kallo Aminu," ba ruwan ka,,tashi
ma ka bamu waje,,.yai murmushi,, "indai Sa'a ce,kasan ko Ummi bazata fada min
ita ba...zaka neme ni nasan..ya tashi yai daki cire babbar Rigan shi,, dariya
take ta ciki ciki," kufa haka kuke keda mijin kin nan,komai ma dariya ne,ta
kunshe baki tana"I am sorry,, ina ji, ya kada kai "Wace Sa'a? Sai taji tambayar
tazo mata a bazata,, tace" me kace pls¿? Yai murmushi,, "cewa nayi wace ce
Sa'a?? Tai murmushi,." Sa'adatu.. BARIKI.. Oh whatever Dana Sani ta qwarai
ce,,.Hafeez, kai ne baka San BARIKI ba, baka San rayuwar ta ba,,ni dai abinda na
Sani Sa'a mai Sa'a ce cikin mata,,nan ta fara bashi lbrn ta wanda ta Sani,karaf
kaf bana sharri,,"abu 1 na Sani da Sa'a, bata barin ta kwana,, sannan mace ce
mai amfani da baiwar da Allah ya bata,,amma fa ta hanya tsaftachaciya Hafeez,,
ya kada kai da gamsuwa da bayanin ta,,"Amma mey yasa ta zabi sunan BARIKI da
kuma wannan sanaar? Ta kada kai "na fada maka tana amfani da baiwar ta wajen
Gina kanta..bayan wannan ta girgiza kai" Ban San komai ba,,ya kada kai,, "dama
Sa'a tana zuwa islamiya??what I mean,dama ta saba ko yau ta fara??dai dai Aminu
ya fito,"Har yau tambayar nan ake?yau fa ka sauya abokina? Yau ranar hala ta
Sa'a ce?
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/28, 3:45 PM] BARIKI...IYAWA
22_Tai murmushi kan ta tashi tai kitchen tana kiran Qanwar ta.. Ya kallo
Aminu"Dan Allah kaban naka details din da ka Sani a kanta,,ni kaina bazan ce ga
abinda yasa na damu da ita ba a yau kadai ba,,Aminu yai dariya"Ba yau kadai ka
damu da ita ba,.ina kula da kai,,har Allah Allah kake Ku hadu da Sa'a I know u
fa..Ya kada kai,, duk abinda Ummi ta sanar mishi haka Shima Aminu ya sanar
mishi,,"tun zuwan su Sa'a unguwar mu na Santa,, a lokacin bata fi yar 7 to 8 yrs
ba,,tun a wancan lokacin ina ganin ta a islamiyar unguwar mu har yau din nan
Hafeez,, en u know what?? Ya girgiza mishi kai,, a shekara 6 ta gama tai
sauka,,sannan ta haddace littafai da dama da kake ganin ta haka,,sosai tasan
abinda take yi,,yanxu haka ta gama amma bata daina zuwa hadda ba da daura wa
wasu duk ran weekend, shine yau lahadi ka ganta,toh chan ta nufa,,nayi imani
Hafeez ba haka ka dau Sa'a ba,,shi yasa yana da kyau ka kyautata niyar ka akan
mutum,,
Ya kada kai,, tare da rintse ido,, bai son a daina bashi lbrn Sa'a, Dan yana
sashi nishadi,,take yaji wani abu na yawo a kwakwalwar shi zuwa jikin shi..
Ya bude ido ya kalli Aminu da wani yanayi,, "yaushe take tashi a makarantar? Ya
kallo shi ya kyalkyale da dariya,tuni ya kule,, "kaifa dan iska ne wlh,, ni ka
fadan nai gaba malam,.ya tsagaita dariyar kan ya fada mishi lokaci,, tuni ya
kalli agogon hannun shi ya mike,," sai mun hadu,,ya kwalawa Ummi kira"na
wuce,,,ta fito tana dariya,"sai ina?ya hararo Aminu,kan Yace mata"inda kuka aike
ni,,ya dau key din shi ya fita,,suka sheke da dariya,,sun San wataran za'a Rina
haka,.
Tana woo wa kwanar ta dage nikaf din ta,,sauri take dan wata irin yunwa take
ji,,daga kan da zatai ta hango shi yana fito a mota yana tahowa wajen ta, da
sauri ta sauke Nikaf din ta juya bayan ta tana salati da faduwar gaba..ta shiga
3 indai ta bari Hafeez ya ritsata a gun nan sai dai wata ba Sa'a ba,, gashi a
ka'idar ta in zata islamiya ba mai Binta a baya a masu take mata baya,,ta waiga
taga gidan su Tj a bude da sauri ta kule tare da turo kofa,,d sauri ya bita yana
kira,, "Sa'a ki bude dan Allah,, magana zamu yi,,cikin tsiwa tace" ba a bude
ba,,kasan dai ramako nai ai,,wlh kama kauce kan na Tara maka yaran unguwa suma
Atule,, yai murmushi,, toh na tafi bude,,wlh ba abunda zan miki,,tace"waxaka
maida Yarinya,,na San ka ai,,ka tafi kawai,ba maganar da zanyi da kai,,taji
shiru,,sai da ta kusa minti 10 taji shiru kan a hankali ta zare sakata a hankali
zata leka ya turo kai ciki da sauri,,taja baya tare da kwala ihu,,zatai cikin
gidan da sauri ya ruko hijab dinta,,ganin hijab din zai matse mata wuya yasa ta

tsaya,. "Cikan hijab,yai murmushi tare da sa dayan hannun ya cire nikaf din da
sauri,,ido ta zaro kanta nuno shi da hannu" wani salon wulakancin ne wannan
komai?ya girgiza kai, "ka cikan hijab toh,ban son iskanci,, ta warce nikaf din
ta,.jin ihu yasa Tj da kanin shi suka leko,," su waye?,,ta dallah musu
harara,,"Jisu a gun,,toh Aljanu ne,,kallon bakin ta kawai yake,,akwai Iya fadan
gan gan ga tsoro,, Tj ya murguda baki, itama ta murguda mishi,,Yace"Kuje ba
komai,,suka kada kai,, ya juyo kan ta da take hararar shi,, yai murmushi, duk da
haka yaki sake mata hijab,, bata nufa kawai sai ganin shi tai ya zube mata a
kasa yai kalar tausayi,, da sauri taja baya tare da zaro ido cikin mamaki,,. Da
sauri tace "meye haka?ya kada mata kai,," I am really sorry Sa'a,,wlh Sa'adatu
believe me,, ban taba daukar hannu na taba wata da sunan duka ba,,koda kwa
Qanwata ta ce,,but thank God, ba wanda ya gani,daga ni sai ke,sai Ummi da
Hafeez,, tuni ta fara hawaye,,dan tuno yadda taji a jiyan,,tare da rintse ido,,
take wani karfi yazo mata ta kwace hijab din ta da karfi,, cikin kuka tace"how
could you? Ko kasan ko iyayen da suka haifo ni basu taba mari na ba a rayuwa,,ta
goge hawayen ta,,"no bama haka ba,, Hafeez, duk da ba wanda Ya gani, amma zubar
mutunci nawa ne,,da sauri Yace,"I know,, but pls I am so sorry,,nasan na miki ba
dai dai ba, amma in kin duba duk mun ma juna pls,,ta girgiza kai, "ka Sani
kuka,ka Sani a bakin ciki,ka dauran tsanar da ban San lefi na ba,. Ta goge idon
ta tare da nuno shi da masifa,."Ban waje na wuce kawai,,tashi yai,dan yasan ba
kula shi zatai ba yanxun., yana kauce wa ta fita tana daura Nikaf.. Ya bita da
kallo har ta sha kwanar gidan su.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[10/2, 6:02 AM] Feenat Ja'afar: [12/29, 3:39 AM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
23_Tana zuwa kofa taga mota a kofar gidan wata mai kyau,, da mamaki yau kuma
wata samu haka??ta shiga,suna tsakar gida an shimfida taburma a inuwa,,harda
Baba da a ka'ida iyanxu baya gida,,ta cire Nikaf din tare da sallama,,baban
Yace"Kaga yar halak, walaikum salam,ta kalli bakon, tuni ta hade rai,, baba
Yace"kin dawo mama ta?ta daga kai,"Baba lfy?yau nagan ka a gida?da fara'a
Yace"a, baki gane bakon namu bane?ta kallo shi, dan jaraba kuwa kirrr ya kafe ta
da ido,."Ban gane shi ba Baba,, bakon yai murmushi,, "lalle Sa'a,, Duniya da
alkawari kuwa?ta harare shi a takaice,, ta basar,, baban yai murmushi," shekara
3 kam baici ki manta Ali ba,,dan wajen mai gida na da ya tafi kasar waje
karatu,,naga har gidan nan yana zuwa kan ya tafi?tace"au, na gane,.bari na shiga
ciki,,baban Yace dama fita zamuyi yazo gaida su Maman ki ne,,ta kada kai, Baban
yai waje,,zata shiga Ali ya bita da kallo,,lalle Sa'a ta sake girma da kyau, wlh
karan nan bazai bi ta kanta ba,,baisan dame ya ragu da Sa'a take kinshi ba?ya
girgiza kai lokacin da ya tuno rabuwar su ta karshe da ta furta mishi ba aure a
gaban ta yanxu,..yai murmushi, yanxu kam yasan akwai,,shi a yanxu gani yake irin
su Sa'a ne kadai ajin auren shi a garin,,gashi Wai dan tsabar takaice Wai bata
ma gane shi ba..yai kwafa,yasan ta inda zai bullo mata ai,, inta San wata,bata
San wata ba.
Shi kwa Hafeez tunda dare yai ya nemi nutsuwar shi ya rasa,, jin wannan abun da
ke yawo a jikin shi sai karuwa yake,,ya kasa sukuni sai tunanin Sa'a,,. Duk da
bata yafe ba,but at least ta gano yai nadama,, ya hasko lokacin da ya cire mata
Nikaf dinta,, Ya salam,Ashe Sa'an karshe ce,amma mey yasa da bai kula da kyan
nutsuwar ta,,ga ba karamin kyau hijab din ya mata ba,, yai murmushi, "Hafeez mey
ke kanka ne yau 4d first time?? Sa'adatu.. Kamar an tsikare shi ya tashi tare da
lalumar wayan shi,, ya kalli agogo 9 ma batai ba,, Aminu ya kira,,bugun farko ya
dauka,,"Nifa tsiyata da gauron mutum baiya sanin dare yayi masa,. Dan tsaki yai"
commot ni temako zaka min,,ka nemi gauro kuma,dan nima na kusa aure,.ya
kyalkyale mishi da wannan dariyar da take kulal da Hafeez,, kan ya tsagaita,
"kai shegen kaya,har an dai daita da Zahra ne??Hafeez yai tsaki, "wace haka?dan
Allah be serious, numbern Sa'a nake so kaban..yace"eyeee?mey kace?ya kara
tsaki,"kai fa dan wulakanci ne,zakace bakaji mey nace bane? Aminu ya ci mur
kamar yana kallon shi, "meye dan na tambaya, nasan mey zaka karta mata,haka
kawai kasa gobe tazo ta sauken kwandon bala'i a gida..toh da sake,.ji yai kamar

ya bishi ta wayar ya rufe shi da duka..sai dai yasan halin Aminu,sai ya hana shi
tsaf,,tuni ya dawo lallami,," no wlh ba abinda kake tsammani bane pls, gaisawa
kawai zamuyi,,pls,.ya kara kecewa da dariya,, "lalle Sa'a tai zarra,a takaice
dai tai wining kenan?da sauri yace "eh,duk ya matso ya bashi,amma dan wulakancin
sai ja mishi rai yake,." Ni in zaka ban kaban malam,,Yace"kai,wlh kai
ladabi,tam,,lalle Mutumi na da magana a kasa.,bani 2mints yazo zan turo,,tuni ya
sauke wata ajiyar zuciya,.kan ya kashe. "Toh in na kira ma mey zan fara ce
mata??ya salam,,Wai mey hakan ke nufi ne dashi da ya kasa sukuni?kadai wannan fa
shi ake kira da so?dan ya San ance so a zuciya yake,gashi shima tashi zuciyar
sai tsanan ta bugawa take,,tun a ganin shi na farko da Sa'a Saida yaji haka..yai
murmushi,, da ya tuno yadda in sun gamu suke rabuwa,,in tana zazzaga fada bakin
ta kawai yake tuna wa, komai da gaske take yin shi,,.. shigo war text ne ya
katse shi, da sauri ya duba,,editing kawai yai ya danna calling,ya sata a kunne
tare da komawa da baya ya kwanta rigin gine,,caller tune ya fara ji na sheikh
sudeis na Allahumma Aslihlana Duniyall....take ya lumshe ido,,a hankali ya
furta" Sa'a "bai tsammani ba yaji ance " Yes,who's this? Ido ya lumshe,dan baima
San ta dauka ba,,ita kwa ta bangaren ta tuni ta fara kulewa,,a tunanin ta ko yan
iskan samarin tane yan naci,,tuni ta fara sababi"Malam in baka da tace wa bacci
nake ji,,yai murmushi kan Yace" am sorry,, Hafeez din ki ne..tuni taji abun wani
bankwara kwai,Wai Hafeez din ki,,"Hafeez dina?tace"Toh daga wace jahar?yai
murmushi mai sautin da ya ratsa ranta,duk da ta gane wake magana kuwa..ya katse
ta "Sa'a,tace" umm,,"nasan kin gane mai magana,,kiyi hakuri again,na nemi afuwa
pls,,,ta lumshe ido,, ya cigaba"Sa'a,, da baki juyar da Marin nan kaina ba da
bazan taba yafe wa kaina ba,, amma ki tsimaye ni gobe,zanzo in tsaya a titi ki
Tara kema jama'a ki rama Marin ki,,Kila in munyi 1-0 nima nawa mutuncin ya zuba
sai ki yafen.. Pls,,ta ja numfashi,"ni bance ba,,Yace"meye baki ce ba?tai shiru,
Yace"Ok,yanxu kin yafe ni ba sai kin rama ba??cikin kaguwa tace"eh..yai
murmushi, "Ok,tnks, bari na barki,. Sweet dreams,,.. Kit ya kashe,,tabi wayar da
kallo,,har kwakwalwar ta taji Kalmar" sweet dreams din nan..samun kanta tai da
murmushi,, kome ta tuno take ta keme fuska kamar yana ganin ta.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/29, 4:35 AM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
24_Yau kwana 2 da faruwar haka,Ummi ta kira ta harda fadan su,, dan wulakanci
batazo an kawo ta da ita ba,sannan har yanxu taki ta leko ta,,toh wlh zata
fadawa mama,, tana jin tace mama ta hau bata hakuri,,zata zo yau,,"uwar jaraba,
ta ce"na kai ki?saura ki min lattin zuwa..sukai sallama, ita kanta tasan bata
kyauta ba,,.
Da yamma misalin karfe 4 kwa ta dau wanka cikin wani dakakken Orange din les da
blue, yai bala'in mata kyau,tai ado da blue sarka ta fashion,,batai wata
kwalliya ba,amma sai kyalli take na dilka,ga kunshin biki kamar yau akai
mata..Mama ta kalle ta,,"ah gaskiya baki kauta ba,amma kunfi kusa,,tai murmushi,
"mama zan wuce,ba sako?dan gidan fadeela zan fara zuwa,,tai murmushi," babu,Ki
gaida ta kawai.,ta gyada kai kan ta fita,,.
Tuki take tamkar bata so,,duk da tana dan gudu,,bata San meya sa haka kawai take
jin nishadin yamma
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment