Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

cin,, dake gari ne na damuna,, ko ina gwanin ban sha'awa,,
minti 7 ya kaita gidan fadeela,, a waje ta parker motar ta,, kan ta fito tai
bakin gate,,ta tura karamar kofar ta shiga,,ba laifi,gida ne madai dai ci mai
kyau, rabon ta da gidan kusan sati 2,,tunda ta fuskanci kishiyar fadeelan yar
rainin hankali ce,,.a parlour kwa ta tarar ta ta hakimce,,ba kowa sai ita
kadai,tana shiga ta hade rai,, take ta kalle ta ta watsar, ba tasan dalili ba ta
tsani yarinyar nan fiye da yayar tata da take kishiyar ta,,gata da dan banzan
kwarjini bare ta tanka ma Sa'an,, ko kallo bata ishe ta ba daga sallama tai
ciki., ta hada hannu da kumatu tai tagumi halamar tunani,,ta cire gyalen ta ta
ajiye kamin ta tabe baki,, "fadeela,, da sauri ta kalle ta tare da goge
hawaye,,dan bakin ciki Sa'a baki ta sake tana kallon ta,,kan tace" lalle kin
gamu da aiki kuwa,,wlh kinyi asarar kudin Tara fadeela,, tai murmushi, "sannu da
zuwa,,mey nai kuma daga zuwan ki,,Sa'a ta tabe baki kan ta zauna ta daura kafa

daya kan daya,," Fadeela ba karamin haushi kike bani a rayuwa ba,,dama Saida
nace wa mana karki auri mai mata,dan nasan babu abunda zaki Iya dauka a gidan
sai dolanci,,take fadeelan ta hade rai "ke ban San wulakanci fa,,abun harda
zagi?ta hararo ta,"jiki fa,,dan Allah kina kallon mudubi kuwa?kinga ramar da
kikai a abinda baifi wata guda ba??tai wani murmushi,kan ta mike tsaye tana
gyara Riga,," wlh na gode da ban tsamu guntu a abunda kika sha na karba ba,da
tuni nima na rako mata duniyar nan,,ki dube ni da kyau,, "wlh nafi karfin gujewa
kishiya,,nafi karfin kishiya ta juyani wlh ko ita wace ce,,da sauri fadeelan ta
taso tana sa hannu a baki halamar tai shiru kar taji,,taja tsaki kan ta suri
jakar ta,," ki same ni a parlour,solomiyo kawai,,duk abinda ake kishiyar tana
ji,,tana fitowa direct kujerar dake facing din kishiyar ta zauna,,ta ajiye jakar
ta a dayar tare da daura kafa daya kan daya,,kishiyar taja tsaki,dai fadeela ta
fito,sai wani rakabe wa take,,Sa'a ta kallo ta,, "meye hakan?a gidan mijin ki
kike sanda?ta kallo kishiyar ta ta,.ta dallah mata harara kan taja wani uban
tsaki,," dama dan talaka haka yake ai,bai oya samun guri ba,,anzo an hau kujera
da babu ita a gidan uba,..ta kara makowa fadeelan harara..a rakabe tazo zata
zauna tuni Sa'a ta amshe,,"dadin ta mun San uwale mun San ubale,,sannan tsinke
ubale bai kawo gidan ba,tsiya kuma ai duk mun ganta har ke,, gwara mu da rufin
asirin Allah,, sannan auran So da kauna aka kula damu,bawai tushe ba..ta nuno ta
da hannu,,"mun San kom ai,,so babu wata rufa rufa..ta dawo kan fadeela.. "Gidan
mijin ki ne nan,,yadda uban ki bai kawo kujera ba haka nata,,so kowa yai zagi a
Kasuwa yasan da wanda yake..tuni ta hazuko ta mike,,"ni zaki gwada wa BARIKIN da
ake fadi,, wlh kije shan kiyi karuwancin ki ba a gida na ba,.yar BARIKI
kawai,,Sa'a ta kallo ta, sai wani huci take kamar tayi gudun fallako,,tai wani
shegen murmushi,, tare da rausayar da kai.." Fadi da ihu ki kara da wayyo
Allah,,. Ta tashi tsaye"BARIKI ba IYAWA ake fada miki,ta na wani yauki tare da
jujjuya wa a hankali..horn suka jiyo,halamar mai gidan ya dawo..ta nuno ta key
din motar ta.."kuma kisha kallo,yau zakiga karuwanci ganin idon ki,,BARIKI ba?
yau zan baki darasi.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/29, 6:22 AM] BARIKI...IYAWA
25_Ta kallo fadeela da har ta fara hawaye,, tai murmushi,,sai da ta dai daici
Alhaji zai shigo ta zauna tare da rukunkumo fadeela,, ta daga murya "Taji ita
yar talakwa ce,masu kwadayin abun Duniya,,Munji mu ya'yan masu da maula
ne,,munji Uban mu baida halin siyan kujera dole ki zage mu,..da sauri Alhajin ya
shigo,," Subhanallah, Sa'a mey ya faru,,tuni ta tashi,,"yauwa,gwara da kazo,,Yau
in kaga na bar gidan nan toh anyi ta ta kare wlh,,Yace"Sa'a meya faru
ne,,fadeela, me ya faru kike kuka?Sa'a ta kallo Matar tashi,kan ta nuno ta da
hannu, "Matar kace,,samun ta nai a kanta tana ta Nada,,dake ita kuma doluwa ce
ta tsaya ana dukan ta kamar jaka,, daga rabiya ta dawo kaina,,Wai mu ya'yan
matsiyata,sai fadeela ta bar mata gida,,Dana tambayi fadeelan sai cewa tayi daga
fitowa zata shiga kitchen ta tare hanya,,Wai ai ba chokalin ta a ciki,,.daga
sake hanya ta hau ta da duka.. Gata nan ta Musa,,tuni ya hau 90,,yayo kanta zai
mare ta ta kauce"Dama na fuskanci Rabi kullum yarinyar nan rama take,,kwata
kwata taki sakewa da gidan nan,, ina tambaye ta baiwar Allah tace ba komai,,
Ashe gori kike mata harda hadawa da duka?a gida na?ta kada kai zatai magana tuni
ya kara tunxuro,, " karya na miki kenan??ta girgiza kai,,ya cigaba"kuma da kike
kiran ba chokalin uban ta,ke da na naki uban,, tuni ta kallo Sa'a, Sa'an ta
kanne mata ido daya,,kan ta kallo Alhaji, "ai zance ya kare,, yau kam zan fadi
komai in naje gida,da sauri ya yo gun Sa'an jiki na bari" aa Qanwata,.kar muyi
haka dake,,kar su dauke ni wanda ban isa da gida na ba,,zan dau mataki ai,,dole
kowa tai hurumin ta,,wlh babu takura a gidana,,saboda haka Rabi ki kiyaye
wlh,,so da kauna yasa na auro fadeela,,dole tai son ranta a gidan nan da itama
nata ne..ta kallo shi "Toh Alhaji ba komai,,ta kallo Rabin,, " Aunty ni zan
tafi,,Allah kiyaye gaba,ta kallo fadeela da Alhaji,, "na wuce,dama zan wuce ne
na shigo mu gaisa,, ya wage baki" Atoh toh kin kyauta,,ya zaro kudi a aljihun
shi,,"gashi Haj Sa'a asha mai,,ta kada kai "Alhaji harda wahala? Ta dan Durkusa"
toh na gode,,Yace"mu rakata man fadeela koh?ta kada kai ya matso ba ko kunya
yana goge mata ido,, Sa'a tai wani murmushin, kai da gani kasan na mugunta ne,ta
kallo Haj Rabi,,tare da daga mata gira,,ta zuge jaka ta dakko wani katon glass

su Alhaji sukai waje,tana kokarin sawa tace"Yato kika ga??ta dau jakar ta tai
hanyar waje"ki gode Allah da yau banyi wanda zaki yi gida ba,,. Ta daga mata
yatsu 2, "sai gani na 2,wlh ki gyara koh na gyara ki,..tai waje..Wai Saida ta
fita tai yunkurin sha kota,sai sai kan ta kai kofa har ta fice,ba abin ta bita
ba Alhaji na waje,..Sai yanxu taji hawaye na zubo mata,, lalle Alhaji, wato
sirrin ta karafkaf ya kwasa ya kaiwa dangin amaryar sa..?
Bayan Sunyi sallama da Alhaji ta kallo ta,zan kira ki,yanxu kibi mijin ki,,saura
ki tsaya wannan Dolan cin naki.. Ta bude kofa ta fita,,fadeela ta bita da
murmushi, dan uwa mai dadi,,Allah yaga tana son mijin ta,duk da badan Allah bai
bashi haihuwa ba da yana da kusan kamar ta.. Ta kada kai, Ashe hakane abun,.kuka
ta samu Haj Rabi nayi reras,dan Alhaji yace in fadeela ta shigo ta bata hakurin
dukan da ta mata..Wai Alhaji yai mata wulakanci DAN bata haihu ba.. Yace" ke
kika ce haka bani ba,abu 1 ne bazan dauka ba,,tuni fadeela tai ciki,.chan Shima
yabi bayan ta ya barta parlour tana ta rasgar kuka,,gashi ba wanda take sakar wa
a dangin mijin hatta Hajiyan shi ba dadin ta take ji ba bare ta kai kara.
5:08 tana gidan Ummi,, da gudu ummin ta rukunkume ta har suna shirin faduwa,,
kan ta dago tare da ture ta kujera,,"Dallah na manta ma munyi fada,, wlh baki m
Sa'a,, ta marai rai ce "yi hakuri, tace" na zata ko lefin ya shafe mu ne na ran
dinner? Tai murmushi, "bar tuna min,ya wuce ai,.da mamaki ta kallo ta,, ta
tashi,meye yake kamshi haka?kai shegiyar qawa,,ke ai bana shakkun ki,,ba kamar
waccan ba,,tai daki," Wai ina angon ne?ta biyo ta, "yanxu zaki gansu,.tace"
inye, qawata komai yaji,Allah sanya alkairi, sannan a dage, yanxu BARIKI zatai
aiki..suka tafa..sun koma parlour taji wayan ta na kuka,, ta dauka,fadeela
ce,."ya akai auntyn tsoro? Tai murmushi, kai wlh Sa'a baki da kyau,tai murmushi
kan tace"kwarai kuwa,ko nai wanka ba..tace"ke kinga yadda yazo yana lallaba
ta,harda Durkusawa fa a kasa, Wai shiga in kara baki hakuri kar ki fada a
gida,,tai kwafa"ai kinga illar nunawa kishiya tsoron ta,, fir ke kenan kullum
akaje gidan ki kina daki,,bazaki ware ki kama mijin ki ba,, bari kiji,idan har
zakina tuna wa da wata a gida bazaki Iya komai ba a gidan Miji,,tukun ina kayan
nan Dana kawo miki?tace"suna nan,"da fatan kina amfani da su?ta kada kai,
gaskiya ban fara ba..ta kada kai "Toh in kin fara mayi maganar,,.dai dai nan
taji hayaniyar su Aminu,,lokacin tana fadin "nidai ina fada miki kishiya ba abar
tsoro bace,atoh u better wake up n shine ur eyes,,.ta tsaya da magana ganin da
wanda Aminu ya shigo,.tace" bari inna je gida zan kira ki,da kallo itama ta
bishi,,yayi kyau cikin kana nan kaya,,sai murmushi yake sakar wa,,fuskar ta ba
yabo ba fallasa,,Aminu yace "Kaga Alalar Gero,, wato BARIKI.. IYAWA,, tuni
fara'ar fuskar Hafeez ta kau.. Maimakon ta kalli Aminun sai ta ke kallon Hafeez
din.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[10/2, 6:06 AM] Feenat Ja'afar: [1/6, 12:34 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
26_Ta maida kallon ta kan Aminu,"Ango kasha kamshi,,ya Dan bata rai,"au,ai munyi
fushi ma Ashe,tai murmushi ta dan sachi kallon Hafeez din,, duk yai kicin
kicin,,tace "ai hakuri dai,gani nazo,,ya kalli Hafeez, ya sake kallon Sa'a,, yai
murmushi, halin su sai su..tashi yai yabi Matar shi daki.. Ya bar kallon wayar
ya kallo ta,.duk ranshi ba dadi, suka hada ido yai mata kirrr,,tana ganin haka
itama ta cinkune fuska,.sun dan jima ba wanda Yace da wani uffan,, chan dai ya
nisa,," Amma kin San BARIKI ba sunan azziki bane ba koh Sa'a?? Ta kallo shi da
mamaki,,baki sake.,yaci gaba,,"Gaskiya Lamarin duk bai dace da ke ba..ta dallah
mishi harara,.kaga karfin hali,Wai Barawo da sallama,."Toh,Abba na,,"meye ruwan
ka da Lamari na toh??ganin ta fara daukar zafi yasa ya sakko.. "No,
Sa'adatu,,BARIKIN ne ban son ana fada miki,ina tsananin jin zafi,..da sauri ta
daga mishi hannu.,"Zafi?sai ta zata ko wani fadan yake nema..cikin fada tace"Ni
dauka ta My professional life was my personal life,,ta hade girar sama da
kasa..da lumana ta karasa fadin" stay out of it..ok?.ta fara kun kuni a
hankali"kaji min mutum da karfin hali..ta daura kafa 1 kan 1,,yai
murmushi,,"Allah ya huci zuciyar ki yan mata,," my mistake..

Tun daga lokacin bai sake ce mata komai ba ya dukufa a wayan shi,,ta dan kallo
shi, jin yai shiru,,kanshi kasa,ta dan harare shi,.kan ta cigaba..lokaci lokaci
tana dan Harar shi,kamar wanda laifin shi ke karuwa..Text taji ya shigo,,tai
kamar karta bude tana chat.. Ta dai sauka,.abinda ta gani yasa ta kalle shi,,wai
"Meye kike harara ta??ta murguda baki..taki reply..Chan wani text din ya shigo,
" mey kuma nai na murguda baki??..ta kallo shi da niyar tace "anyi din,sai kawai
taga Shima ya murguda mata baki,,bata san lokacin da murmushi ya subuce mata
ba,,harda dan dariya mai sauti..ya kallo ta yana murmushi,.haka suke kallon juna
da murmushi, har ta manta da komai,,tunda take,bata taba kallon Hafeez ba irin
na yau,, Hadadden saurayi ne mai barazanar zama tunxuru,fari ne,ba chan ba,yana
da saje, mai taken Razana mata,, kyawun shi na Fulani biyu,yana da kwarjini a
fuska,,da dan gashi wajen gemun shi zuwa sage,anyi aski sai yai mishi dan dass..
Murmushin shi yafi komai tafiya da hankalin mata,dan baiyanar kyawawan farin
hakwaran shi Tass dasu,,dogo ne,Amma ba chan ba,sannan yana da kaurin jiki,a
dire yake,.
Uhmmmm"Aminu ne yai murmushi,, da sauri ta saukar da kanta kasa cike da jin
haushin kanta.,Hafeez ya harari Aminu,, shikwa murmushi yai tare da kada kai,.
Da halamun hasashen shi ya kusa zama gaskiya.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[1/6, 1:01 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
27_Sai bayan magriba ta tashi,.har lokacin Shima yana nan.,tun fitar ta yai musu
sallama,,sai dai da mamakin shi tana ta tada mota taki tashi, sai tsaki take
kamar ta rufe motar da duka,,sai dai ba hali,,yai murmushi kan ya karasa
wajen,,ta dago kai ta kalle shi kan ta cigaba da abinda take, yace"May I?ta
dago,da har zatai gardama, kuma dai sai ta fito..
Shima yai yin Duniya taki fitowa,, ya fito tare da rufe motar,duk ta wani marai
rai ce mata,har magana take mata kamar mai jinta,shi dariya ma take
bashi,,yace"Muje na sauke ki, ta kallo shi,ta girgiza kai taga yana murmushi,sai
ta kule.tace"No tnks,, kan ta kauda kanta gefe..ana haka Aminu ya fito za shi
wani gu ya dawo,,turus ya tsaya kallon su,," Ya na ganku anan?Baku tafi bane?ya
kallo Hafeez daya harde hannu kawai yake kallon ta,, tai dan tsaki"taki tashi
ne,,ga dare nayi,.ya kalli Hafeez, "Toh ka sauke ta man,in yaso gobe na taho
miki da ita in an gyara,,ya kallo ta," ko ya kika ce?sai ta dan sachi kallon
Hafeez din,,"Nifa Aminu da dai..ya katse ta "ki saman a mota,, yai baya kan ya
bude motar, ta kallo Aminu,, ya daga mata kafada halamun bata choice,.
A mota duk ta takura kanta,,ta gyara gyale, ta murza zobe, da sun hada ido tai
saurin dauke nata,,ganin yadda ya wani seta mirrorn yana facing nata,shi dai sai
murmushi,ya dan kallo ta lokacin da yake kwanar wani gu,," zan karbi sako pls,,
ta kalle shi tare da kada kai,,
Ya karbo suka fito da mutumin,, wanda zai bashi kwangilar Zane na gini..ya kallo
shi, "mutumin kace da amarya kake tafe?da sauri ta kallo shi, ya wani kashe mata
ido.. Yace" Madam ina wuni,.da yake ta amsa,.tana nanata amarya a zuciyar ta,,
bari ya shigo,,ta kauda kanta gefe,har ya shigo,.ya kalle ta yana daura
belt,"Muje koh?tai mai banza,, yai murmushi,, ta kallo shi, "Nice amaryar? Ya
kallo ta yai dariya,," no, ta kada kai "yauwa,.ya sake kallo ta" Uwar gida ce
ai,,da sauri ta kallo shi,, ya daga gira,,"yes,.uwar gida ko kinfi son amaryar?
Tuni ta hade rai,. "Malam kaja ni ko ka sauke ni,,uwar gidan wa??Shima ya hade
fuska kamar gaske,,"uwar gida na man,baki ta sake,tama kasa furta komai,ga ya
wani hakimce ya tsare gida,,kawai ta juyar da kanta,,.sun kusa zuwa wayan ta yai
ringing,, ta duba number ne,sai da ta kusa tsinkewa kan ta daga,a gadaran ce
ciki ciki take maganar,," wane Alin?.. Tai Jim,ta kallo Hafeez din, Shima ita
yake kallo yana kallon titi, sai ta waske dan ta bashi haushi"Oh,na gane,ya akai
toh?..wayar ya warce dai dai sunxo kwanar daza ta kaisu gida,,ya kai kunnen shi
a kai kai ce,,"Tana tare da mijin auren ta ne,, kai hakuri ka Adana Tarihin
sunan ka,,ya kashe wayar tare da ajiye wayar bai ko kalle ta ba yai parking,.
Lalle man din nan akwai karfin hali!..baki sake kawai take kallon shi,,wannan
irin tusa kai haka,.jin bata fita ba yasa ya kalle ta, shi take kallo,yace"na
sauya miki ne hala??ta maka mishi harara kan tai waje,.da sauri yace"wayan

ki,.ta warta, zata fita ya dago glass din.."wannan fa?Shima ta warce,kan tace
"ba'a Sani ba,.sai kuma ta manta jakar ta,. Ya kunshe dariya,, tuni ta kara
kuluwa,.zata shiga gida ya fito yace" Sa'ada,.da sauri ta juyo da zummar
masifa,,jakar ya mika mata yana murmushi,. Sai kuma dafe kai"Ya salam,.sai kunya
ta kamata,,toh saurin mey take haka??ta tako zata karba tare da juyar da kai
ganin yana murmushi,. Maimakon ya bata,sai yai baya da ita,ta juyo ta kalle shi,
suna hada ido ta dauke kai,."ban man,.yai shiru,,ta sake kallo jakar ba tare da
ta kalle shi ba,yai murmushi, "Toh yaushe zan dawo?ta sake kallon shi a kai kai
ce,." Kamar ya??da abinda ya rage kuma?ya kada kai, "kwarai,da abunda suka rage
da yawa,. Ta kallo shi da rashin fahimta ,,ya daga mata girar shi,." Ai in kinga
abubuwa sun kare,toh tabbata uwar gida ta tare,.gaba daya kamar an kulle mata
baki taji,. Ta sake mika hannu ya kautar, "in kina son na baki ki fadan yaushe
zan dawo??da kaguwa tace" Gobe,.sai kuma tai shiru,.ta rasa meye dalilin kasa
kallon idon Hafeez da tai,.murmushi yai,kan ya mika mata jaka,.tana karba da
sauri ta arche gida.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary

Posted by Feenat Jaafar on 05:28 AM, 02-Oct-16
  

RECENT POSTS
K'ADDARA CE 1BARIKI IYAWA 7BARIKI IYAWA 6
« PREVIOUS POSTNEXT POST »
COMMENTS
No comments yet. Why not make the first one!
NEW COMMENT
NEW COMMENTS DISABLED FOR THIS POST.
NAVIGATION
HomeAbout MeGuestbookFeedbackFollow This BlogBlogrollFeed: RSS / AtomComment
Feed: RSS / AtomGet a Free Mobile BlogBack to top
© 2016 FEENAT JAAFAR'S MOBILE BLOG.
POWERED BY MYWAPBLOG.COM
REPORT ABUSE
[10/27, 12:08 PM] 💍🛍🍬Salma🍬🛍💍: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afarSalma🍬Salma🍬🛍💍: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar🛍💍: FEENAT JAAFAR'S MOBILE BLOG
JUST ANOTHER BLOG

HOMEABOUT MERSSNAVIGATION
BARIKI IYAWA 4
[10/2, 6:16 AM] Feenat Ja'afar: [1/7, 10:02 AM] Feenat Ja'afar

BARIKI...IYAWA
28_Harta shiga yana Binta da kallo,ya sauke ajiyar zuciya,.Lalle ba makawa a
kamu da ciwo,wanda yake tunanin koh shine So din,.ya sake ajiyar zuciya kan ya
tada motar shi yana ji da nishadi.
A bangaren ta itama haka,kwance take sai juyi take a gadon ta,ta rasa dalilin da
yasa yanzu ta daina jin zafin shi kamar kullum,ga wani dan karan kwarjini da ya
fara mata yanzun da da bata gani,, ta furzar da iska kan ta kara juya wa dayan
gefen, buguwar zuciyar ta ya tsanan ta, lokacin da ta tuno yadda yake mata wani
kallo wanda ta kasa fassara shi,, kai ta girgiza, tana mai rarrashin kwakwalwar
ta da ta daina tunano mata Hafeez,. Tai adu'a tare da gyara kwanciya.
Shima hakan ce ta faru,.sai juyi yake a katifa, sai yayi kamar ya kira ta,sai
kuma yai murmushi, a yau kam,ya rasa nutsuwar shi, ga wani fara'a da yake tamkar
gonar audiga,ya duba agogo,8 da wani abu,ai dare bai ba,. Waya ya dauka ya danna
kiran Aminu,.yana dauka ya fara mishi tsiya,"Tsiyar gauro kenan,bai gane dare
yayi,,yai dan karamin tsaki,"Gargadi zan ma Malam, wallahi BARIKI ya fita a
bakin ka,ka kirata da Sa'adatun ta sak..
Dariyar keta ya fara mishi, har sai da yaga ya fara kuluwa ya dan sarara, "I
knew it,. Dama nasan Biri yai kama da mutum,,kuma ance in kaga Kare na shinshina
Takalmi,toh dauka zai,Lalle Abokina ka afka da yawa,.ya cigaba da dillika
dariya,Hafeez yace" kai fa dan iskan gari ne,mey na afkawa dayawa? Yace"Son Sa'a
kuwa,da sauri yace"So?yace"kwarai kuwa,tun farkon ganin Sa'a nasan ka afka son
ta,amma ka tsaya a haushin ta ne,.
Shidai Hafeez mamaki yake,tunda ya kashe waya yake murmushi, Ashe sone hakan?Toh
amma ya akai bai San So ba shi?abu daya ya Sani yana da muradin auren Sa'a,.
Tuni ya dau waya ya fara tsantsara mata Text,a lokacin da itama bacci ya gagari
idon ta, kwakwalwa ta kasa daina turo mata hoton Hafeez.,Ji shigowar Text yasa
Ta bude ido,takai dube kan wayan,ta mirgina ta dauko,tuni taji bugun zuciyar ta
ya karu, duk da murmushi take yayin karan tawa, "Hafeez.. A hankali ta
furta,,kan tai tsam tana tuna wani abu,.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[1/7, 1:07 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
29_Washegari kowa ya tashi cikin farin ciki,musamman Hafeez, duk da bata mishi
ko reply ba,amma yasan ta ga sakon shi, har Hajiya sai da ta kula da
hakan,binshi da kallo kawai take,, ya zauna a kujera.,lokaci lokaci yana dan
duba waya ko zaiji shigo war amsa.."Ni Hafeez, yau ko mafarkin Aljanna kai ne
haka?Yai murmushi, "ko daya Hajiya,.ta kada kai,.
Ana haka su Zahra suka fito ita da Tasleem,suka gaida shi,ya kallo Zahra,yana
tunanin mey yasa bai jin komai game da Zahra irin na Sa'a??..ya lumshe ido, Sa'a
kam ta daban ce..da sauri ya bude ido jin Tasleem tana ga abincin shi,.Zahra sai
satar kallon shi take,Hajiya na kula dasu,ba tasan mey aibin Zahra ba a gun
Hafeez, duk irin zaman da zatai a gidan bazai taba kallon ta a Wai wacce zai
aura ba sai dai qanwa,kai shi manta wa ma yake da wani batun auren ta,, koda
kuwa zai aure ta, toh gini ma na mata 2 yai,daya a sama da turakar shi,daya a
kasa da dakin yara,kai da kaga gidan kaga na zaman mata 2,.
Hajiyan ta kalli Zuhra tai mata halama da hannu suje daki,.ta yafico Zahra sukai
chan,kan ta kallo Hafeez,." Wai ina zancen mu ya tsaya ne Hafeez??.. Ya kallo ta
da rashin fahimta,. Ganin haka yasa tamai ta gwari gwari,"zancen ka kai da Zahra
man,ko har yanzun baka fahimta ba??tuni yaji gaban shi ya fadi,sarai yasan
Hajiyan su akwai zafi,musamman akan lamarin family, yasan bai isa cewa bazai
auri Zahra ba yanxu,dan yana son Sa'adatu,, sai dai yana tsoron hada Zahra da
Sa'a a matsayin Matan shi,.. "Hafeez,. Tunanin mey kake haka ina magana??..Ya
Sosa keya," Am Hajiya,yana nan, sai dai dama ina da magana..da sauri ta daga
mishi hannu,,"idan har maganar auren nan ne,toh anyi an gama Hafeez,. Ba zaka
maida mu ya'yan ka ba fa,.Yace"Bashi bane Hajiya,.Amm dama wata ce naga,
kuma,.kuma..ya kasa karasa wa, ganin yadda Hajiyan take kwada mai harara,,."kuma
mey?eyeee, nace Kuma mey?kana nufin ka fasa auren Zahra dan kaga wata bare
chan??ko mey kake nufi??.Da sauri ya girgiza kai, "aa ba haka nake nufi ba,,..

Dama,sai yai shiru ganin Abban su ya sakko,ya sunne kai yana gaishe shi, da
fara'a yake kallon shi,."Mey kuma ya faru Kaida Umman taka nake jiyo fadan ta
tun a sama haka??Tai kicin kicin da fuska,,"Ka zo dai ka jiye wa kunnen ka,dama
duk kai ne mai daure mishi ai,,toh wallahi karan nan bai isa kauce wa auren
Zahra ba,,yai murmushi, kan ya kallo Hafeez," Ya akai Hafeez?? Ya kallo Hajiyan
da sai harara take binshi dashi,.ya fada mishi yadda sukai da Hajiyan, "kuma fa
Abba ni duka zan aure su fa,,..A zabure Hajiyan ta tashi," kana nufin mata 2
zakai??!ya sunkuyar da kanshi,,ta kalli Alhajin, "ka dai ji da kunnen ka koh?ta
nuno Hafeez," Toh baka isa ba,babu wacce zaka hada da Zahra,,Abban yai mishi
halamar yai shiru,,ta kallo Alhajin,"kafa sa baki, dan karan nan zamu bata da
Hafeez kwarai..tai sama tana bam bami,.
Zahra da tazo jikin kofa tana zatan zancen auren su zatai mishi Hajiyan ta soma
kuka,, Tasleem ta taso,"lfy Aunty Zahra?Ta zaunar ta akan gado,,"Tasleem mey na
rasa da Ya Hafeez bai sona ne Wai??duk zaman nan dan shi nake yi,amma banda amsa
gaisuwa ba abinda ke shiga tsakanin mu,,shine yanzu zai ce zai hada ni da wata
ya aura dan tsabar rashin so??.,,,, ta barke da kuka abin tausayi,Tasleem
tace"Kut,,wata kuma?ta daga mata kai,. Tasleem ta sake matsowa "Kwantar da
hankalin ki,ni nasan Hajiya bama zata soma yadda ba,,Wai mata 2,,kuma kar ki ji
kom,ya Hafeez na son ki,kawai dai miskili ne na karshe,, ni nasan indai da
Hajiya,toh ke kadai ce Matar shi,. Ta share mata hawaye,.sai lokacin ta dan
sararawa kanta..
Shikwa Bayan Abban yace zai ma Hajiyan magana,yai ta murna,abincin da bai ciba
yai daki,,wata zuciyar tace" Toh kai da kake ta murna, tukun Sa'an ma ka same
son ta ne??sai kuma yai Jim,Toh fa,tanan gizo ke sakar, shifa bai ma San ya ake
cewa a wajen budurwa ba bare in yaje ya tsara ta taso shi,,yai kamar ya kira
Aminu,abokin shi ne ya fado mishi,wani dan Delhi da sukai school a Hyderabad, ya
tuno yadda yake tsara yan mata,duk mai ji da kanta a school din tasan da zaman
Kunal,.tuni ya kira ya kora mai bayani,,yai dariya Shima son ran shi, dan jin
Wai Hafeez ya fada tarkon so,,Yace mishi ai ba'a koya zance,sai dai ya dan bashi
wasu formula,.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[1/7, 2:40 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
30_Dakyar Abba yasha kan Hajiyan,ita sai fadi take batace haramun bane,,kawai
Zahra take so ita daya..sai da ya burkice mata kan suka dai dai ta,,Zahra ai
zabin ta ce,.Da Zahra taji tuni kuka ya karu,,shikenan kuma.
Da Yamma Zahra ta tartara inata ina ta zatai gida,,ta kudiri kuma ba ita ba kara
zama gidan su Hafeez Wai dan shi,,lokacin da suka fito baya nan, kuma sarai
tasan dan su ya bar gidan dan kar ya kaita,,ga Drivern Abba sun fita,kawai suka
je a tsayar da Taxi,,itama da kyar suka samu da mace a ciki.,,Yace zai kaita kan
ya kaisu,,a rashin babu suka shiga,,har akaje unguwar da za'a ajiye wacce suka
tarar a Taxin,sun zo zasu wuce wata a tsaye da wani da yai musu kama da Hafeez a
tsaye sai murmushi yake,,ta motar ta daga wa ta tsayen yatsu tana kiran "BARIKI
Ba..Zahra ta kalli Tasleem," Ba ya Hafeez bane wannan kuwa??..da sauri suka kara
juyawa,akai Sa'a dai dai itama Sa'a ta daga wa ta motar yatsu,ya dan juyo ganin
Taxin da ta wuce,sai dai baiga na ciki ba,,Tasleem tace"La,wallahi shine Aunty
Zahra,, tuni ta cika ta batse dan gane da wa yake tsaye,wato itace wacce zai
gama su tare??mai Taxi na yin kwana ya sauke dayar suma suka sauka,Zahra zatai
kwanar Da sauri Tasleem ta ruko ta,,"mey zakiyi Aunty Zahra?? Ki bari man muji
wacece tukun mu karasa tunda wannan ta San ta,.sai a sannan ta dawo hankalin ta,
mai Taxi Yace in bazasu tafi ba su bashi kudin shi, da sauri suka sallame shi
suka bi bayan Kaltum da zata shiga gida,,.
"Baiwar Allah,, ta juyo da fara'ar ta" Aa,Baku tafi ba?sukai yake, "eh, tambaya
muke pls?ta gyara tsayuwa," toh muje daga ciki,Zahra ta kada kai, "Aa,muyi
anan,." Dan Allah wace wacce muka wuce yanzu da wani a tsaye kika daga mata
hannu?tai murmushi, "au Wai BARIKI?? Yar Duniya ake fada miki,badai saurayin ki
bane ba koh?Tasleem ta kalli Zahra da ke mai maita sunan BARIKI.. Dake uwar

surutu ce tuni ta hau fadi ba'a tambaye ki ba,." Ai in saurayin ki ne toh
wallahi ki hakura dashi,dan ba mai Iya ja da BARIKI a fagen nan,,indai har ya
shiga hannun BARIKI toh sunan saurayin ki "Sorry ",nan ta hau basu labarin irin
kasa wasu da tai da samarin su,Ku harda Matan aure bata bari ba,,campaign na
siyasa tai kadai aka mallaka mata dankareriyar mota da katon gida,tuni suka waro
ido,,.ta cigaba" wallahi ina baki shawara ki ma bar mata,duk da batta gwani
ita..haka tai ta basu karya da gaskiya,tuni Zahra ta tsure,Tasleen kira take
"Shikenan yaya ya hadu da karuwa,.ji yadda yake wage mata baki,.bata Ankara ba
sai gani tai Zahra na hawaye..tai Dede kwanar tana leken su,, a dai lokacin da
Sa'an ta miko wa Hafeez waya,sai wani yauki take irin na yan Duniya.. Yayin da
gogan baki tamkar gonar audiga,,dan ko bata furta ba a formular da Kunal ya
bashi ya gano da son shi a tattare da ita,,dan yau ba hade rai, mai makon haka
ma sai murmushi take mai dan cike
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment