Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can kan wata kujera
ya hakimce ga wani dining table a gaban
sa duk kujeru ne a zagaye da table din,
sannan sai wata kujerar mai kama da
tasa a kusa dashi, kai tsaye yazeed ya
wuce dayar kujerar ya zauna.
Sannan ne suma manyan cikin kungiyar
sun zo duk an zazauna kowa da plate a
gaban sa, abun dake cikine zaisa idan ka
kalla sau daya baza ka kara ba, sasan
jikin mutum ne kala kala a ko wane
plate ba kyan gani, “welcome my son”
inji tsohon juyawa yayi ya kalleshi hade
da cewa :thank you” sannan tsohon ya
tashi yana wasu gwalan gwalantun
tsafinsa sannan yace muna maraba da
babban yaro na kuma shugaba magajin
wannan kungiya wato yazeed (bad man)
ya dora da cewa kun sani cewa a cikin
mu ko jikokin dan kungiya bazasu yi
talauci ba, bazasu taba sanin miye babu
ba kuma baza mu yi sasauci ba ga duk
wanda ya bujirewa umarnin mu, sannan
ku sani dole ku kula da dokokin kungiya
sannan ya juya ga yazeed yace dodon
mu yana bukatar jini kuma daga gareka
wato a cikin dangin ka, dole ka bamu
jininn ka domin tun farko kayi alkawari
cewa a wannan shekarar ne zaka bayar.
Chan kuma cikin dakin ajiya wato inda
aka saka su deeni sun matukar gala baita
yunwa ma ta ishe su gashi anki kawo
musu abinci, wadannan yan sandan biyu
sun sha kuka kamar ransu zai fita
sannan suka hakura sukayi shiru, domin
ba maganin da kukan ke yi musu ba.
Deeni ne ya tashi ya nufi kofar fita
sakamakwon magana da yake ji sama
sama, lekawa yayi ta wata yar kofa, da
sauri ya dago ya dan kama baki alamun
yana so ya tuna wani abu, a ina yasan
waccan fuskar kamar ya taba ganin ta,
kunne ya kafa yana saurare me suke
cewa.. ..
Yazeed ne ya mike yayi gyaran murya,
“a matsayina na mataimakin shugaban
mu kuma babana gashi a zaune ya nuna
wannan tsohon. Inaso in muku bayani
wato dan takaitacan tarihina domin
kusan cewa a harkar nan ba imani idan
kanada imani bazaka ci muriyar mu ba...
Ni dai na kasance fuska biyu ne domin
idan ka ganni a gari bazaka taba cewa ni
mugu bane, yanda nake al'amura na
sakin fuska, kyauta da sauran halaye
masu kyau. Ina so ku sani yan matan da
na kawo nan aka hallaka sun fi a kirga
kuma duk a matsayin saurayi nake gare
su, abinda baku sani ba shine duka ba
wacce mahaifanta suka sanni, hatta
unguwa sai naje nesa da tamu sannan
nake yin budurwa, ku sani cewa yan
matan yanzu ba ruwansu da
SOYAYYAR GASKIYA kawai sudai
abin hannunka suke bukata, laifin iyaye
kuwa da suke barin yaran su wato mata
suna fitowa zance alhalin basu san
saurayin ba.
Ya danyi shiru tukun yace karfa ku zata
wannan nasiha ce, no ni da kuke gani ba
alamun imani ko tausayi tare dani, ni na
hallaka haleema ya fada tare da kawarta
maryam sakamakwan tona min asiri da
suka so suyi.....
Gaban deeni ne yayi mumunar faduwa
sai yanzu ya gane yazeed din
sakamakwon sau daya ya taba ganin sa,
ya dafe kai da yake sara mai da karfi,
“yanzu yana nufin ya hallaka min
maryam dina, no no no, haleema na da
gaske kin mutu kai ban yarda ba karya
kake karya kake” ganin zasuji yayi
saurin control din kansa ya natsu sai
hawaye sharrrr!
Can ya sake kafa kunne dan jin me
yazeed ke cewa...
Sannan ina so in fadawa kungiya cewa
lallai ni mai cika alkawari ne dan haka
naba kungiya babana (mahaifina) ranar
Friday zan kawo shi domin baya garin
nan amma tabbas nasan yanda zanyi in
kawo shi, wannan babbar kyauta ce
nawa kungiya... Gaba daya suka fara
tafi.........................
Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da
bakwai dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 26
Share This:Shi kuwa deeni gaban sa ne yaci gaba da
faduwa wato kawun haleema kenan aka
bawa dodo, hawaye keta kwaranya a
idaniyar deeni, wai an kashe haleeman
shi da kuma kanwarshi shi maryam da
yake matukar ji da ita, bashida burin da
ya wuce ya farantawa ummansa da kuma
yar kanwarsa wato maryam tunda
babansu baya raye, wani xazzabi ne ya
rufe deeni.
Maryam ce zaune kan wani gado na kara
ta dafe kumatu wato tayi tagumi, tunanin
ummanta kawai take, wasu yan siriran
hawaye ne suka kwaranyo, haka
haleema ma da take kwance
kwakwalwarta sai juyawa take cike da
tunani iri iri tama rasa wanne zatayi shin
waye mai neman hallaka mu, shin wane
hali deeni na ke ciki, shin umma da abba
ya zasu ji na rashina bayan basa san yin
nesa dani ko kadan, idanun ta cike da
kwalla ta tashi zaune ganin maryam a
gefan gado ta zuba uban tagumi,
“maryam maryam” inji haleema tunanin
me kike. Tuni maryam ta dago tare da sa
zani tana goge hawayan fuskarta, nan
haleema ta fahimta cewa duk ashe daya
ne halin da suke ciki. Ta dafa kafadar ta
haba my sis ki saka dangana a zuciyar ki
mana mu barwa Allah komai shi zai yi
mana maganin wannan al'amari ba kuka
ne abunyi ba...
Aneesat ce ta shigo, ganin su a wannan
yanayi ta fahimta tunanin gida suke yi,
duk da sun so su boye wa anne amma
saida ta fahimta, “haba yan uwana, nan
fa kamar gidan ku ne ku kwantar da
hankalin ku, dama yanzu daga wajan
maman mu nake shawara muke yi yanda
za'a maida ku gida, ku kwantar da
hankalin ku”...
Tabbas sunji dadi sosai da jin kalaman
anne gaba daya suka ce “hmm anne
kenan haba ba komai amma gaskiya
muna so muga iyayan mu domin basu
san ko wane hali muke ciki ba, kinga in
sun gammu hankalin su zai kwanta.
Yaro ya shigo da salamar sa “anne wai
ana kiran maryam, bata tsaya ko jin
waye ba tace “je kace gata nan”, domin
anne tuni ta kyaro su wato tana lura da
abunda ke faruwa tsakanin maryam da
kuma isa. Ya zaki ce gani nan bayan
baki san kowa ke sallama ba, shin waima
cikin gari nan waya san ni da har zai
aiko kuma wai ace maryam tazo ma.
Anne tayi murmushi ai sai kije ki gano
mana. cikin zolaya haleema tace
“kanwar mu ah gaskiya kinzo kauyan
nan a sa'a kinga shikenan sai mu barki
anan”. Suka sa dariya gaba daya. Bari
inga ko waye tunda kun matsa ta ce,
anne ara min hijab dinki. Ya mata daidai
kuwa kamar dama nata ne..
A tsaye ta iske shi ya harde kafafu da
kara da ya rike a hannun hagu yana
wasa da shi, hannun daman kuma yasa
shi cikin aljihun wando.
“Assalamu alaika” ta fada, wani irin
sauti mai dadi yaji a zuciyarsa yace
dama haka muryar yarinyar nan take
ashe.
Amin wa'alaiki Salam warahmatul lahi
ta’alah wa barakatuhu: sanda ya cika
amsa sallamar cif cif.
Gefe daya ta samu ta tsaya nesa da shi
kadan, ita kam ta kasa dagowa da kanta
domin wannan ne karo na farko nata na
tsayawa da wani da namiji ..
Maryam kenan sarkin kunya shin ko dai
kema yar fulani ce kamar mu, amma ai
ke kunyar taki tayi yawa ma.
Murmushi kawai tayi domin ta gane
yaya Isah ne shi isa taki ma dago kanta
domin tsoran abinda take ji in ta hada
ido da shi wato faduwar gaba.
Ki daure ki dago kanki, ki kalle ni ya
fada yayin da ya dan kara matsowa
kadan kusa da ita.
A hankali ta dago kai “wow” dama haka
wannan bawan allah yake da kyau, ashe
duk ganin da nake mai zaije farauta ne,
amma duk da haka yana da kyau saidai
kayan da yasa sun kara fito da zallan
kyawun sa wanda haka yasa ta kafe shi
da ido shima dai abun ya daure mai kai
ta tsaya sai kallan sa take...
Um dama so nake in gaya miki……
Kuma sai yayi shiru, ka fada mana a
zuciyarta ta fadi hakan, gani tayi ya
kalle ta, tayi saurin sunkuyar da kai ashe
yaji abinda tace...
Maryam ba wani abu bane dama ina so
in gaya miki ina sonki, ina kaunar ki,
tunanin ki ya hanani sukuni ko ina naje
bana jindadi in ban ganki a gunba, idan
na rufe ido ke nake gani, nayi tunanin
cire haka a zuciyata sakama kwan ni dan
kauye ne ke yar birni ce kinga kuwa
auran mu bazai yiwu ba amma dai yanda
sanki ya addabi raina yasa ni dole in
gaya miki ko naji dan sauki...
Farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta hakika
taji dadin kala man sa, wannan ne na
farko da namiji ya taba cewa yana santa
abinda ko da wasa ba'a taba gaya mata
ba, kalmar so kenan yayin fadarta sai
bakin ka ya fara bari duk jarumtakar ka,
bama kamar karo na farko haka duk
macen da aka furtawa a take a waje sai
taji chanji, lalai so halitar Allah ne,
juyawa kawai tayi da niyar tafiya ita
duk kunya ta dabai baye ta..
“Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban
amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata
karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar
mai tattausan murmushi mai dauke da
sako, saidai shi bai iya karanta iri
kalaman din jikin murmushi ba, kawai
cikin gida ta juya ta shige.
Salam Alaikum masu bibiyar wannnan
labari, muna baku hakuri sakamakon
rashin kawo muku cigaban labarin har
na tsahon wasu kwanaki, hakan ya biyo
bayan wasu kalubale da muka fuskanta
amma yanzu insha Allahu zamuci gaba
daga inda muka tsaya.
**************
A baya mun tsaya ne inda
“Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban
amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata
karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar
mai tattausan murmushi mai dauke da
sako, saidai shi bai iya karanta iri
kalaman din jikin murmushi ba, kawai
cikin gida ta juya ta shige.
***************
Cikin rashin gamsuwa isah ya koma gida
yana ta tunane tunane shin me yarinyar
nan ke nufi, ai a so ba’a dole idan bata
so na ba saita fada ba kawai a wuce gun,
Isah ne shi kadai yana tafiya yana
zancan zuci....
Maryam kuwa tana shiga dakin duk suka
gyara zama wato haleema da anne wai
sai ta fada musu waye yazo gunta, ai
kuwa fa fur taki fada, sukayi sukayi
anma tace kawai bata sanshi ba. Anne
tace to ai nasan dole ya fada miki
sunansa, to ya sunansa ai nasan ko wane
saurayi a duk fadin garin nan. Bai fadi
min suna ba... Suka hau dariya wai bata
da gaskiya, haka dai sukai ta zolayar
maryam wacce ita kuwa tunani ne duk
ya addabe ta..
************
“Ina kwana umma” “lfy lau aliyu” a
cewar mamar tasa, sannan ya juya ga
maman deeni suka gaisa.. Wai aliyu har
yanzu ba batun ko daya daga cikin su
ne? Wllh mama babu wani labari a
cewar aliyu haka makarantar su maryam
ma sun ce bata je ba ranar. Maman deeni
ta yi shiru hawaye ne suka fara zarya a
idanonta a bin tausayi, kanta ne ya fara
sarawa da karfi dafe, kanta tayi tana
inalillahi. Kwatsam sai gani sukayi ta
fadi, da sauri sukayi kanta, a kidime
suka kwasa sai asbiti akayi Emergency
da ita, duk a gigice suke sun ma kasa
zama da kyar aka lallashe su da cewa
jinin tane ya hau yanzu tana bukatar
hutu anjima zasu iya shiga domin ganin
ta ....
Bangaran yazeed kuwa
*******************
Naman suka hau ci kallo daya zaka
musu ka fahimci ba imani a tattare da su
gaba daya yanda suke cin abinci da
sassan dan adam a ciki amma su ko a
kansu, tsohon cikin su ne yace gaskiya
badman kayi mana asara kasan fa
dodanmu yafi bukatar jinin yan mata
amma ka bari su mugu suka kashe su.
Dad ba haka bane a duk cikin yaran ba
wanda su mugu suka samu damar
kubutar da su, a inda suka iske su a nan
suke sheqe su. Thats gud, Kasan fa Allah
ne ya kawo mana dakwale har hudu
police 3 da kuma wani 1 dan karamim
cikin su. Dad kace naman police ne shi
isa na ganshi da baki baki. Hahaha
sukayi wata irin dariya tasu ta marasa
imani wacce suka saba. Tashi muje ka
gansu inji tsohon nan, Ya kalli wasu
dake tsaye yace kuje ku kaiwa wadan
can naman abinci mana, ko so kuke sai
sun rame sun zama kashi ne.
Su yazeed ne suka shiga dakin ajiya
wato inda su deeni suke, kallan deeni
yake kamar yasan shi saidai ya rasa a
inane, gaba daya kan yazeed ya daure to
shi a ina yasan wannan. Zuwa yayi
gaban deeni ya tsuguna yana so ya tuna
wani abu amma ya kasa kai kamar na
sanka, denni kuwa kallan sa kawai yake,
“a ina?” Inji deeni. Shiru kawai yazeed
yayi dai dai lokacin ne aka shigo musu
da abinci, plate uku ne aka bawa deeni
daya suma sauran aka jiye musu nasu,
kamar jira suke dama suka fara aika
abincin nan, deeni ne ya yi kokarin da
katar da su “kudaina cin abincin nan” ya
fada. Wata irin harara dan sandan ya
dakawa deeni alamun ya kyale su, deeni
kuwa da ya karewa abincin kallo tsaff
sai ya ga akwai nama mutum da sauri
yasa kafa ya hankadar da abincin ya
zube ..
*************
Assalamu alaikum. Suka amsa mai gaba
ki daya yan majalisar, Zagayawa yayi
bangaran abokinsa da wato salmanu ya
zauna kan dan guntun iccan da yake a
zaune, abokina waya tabo ka ne naga
duk ka wani canja fuska, ya tambayi
isah. hmm abokina zo muja gefe ina san
magana dakai, salmanu ba gardama
kuwa ya tashi suka koma gefe, isah ya
kwashe duk abunda ya faru tsakanin sa
da maryam tun daga farko har karshe,
yace to amma naga alamun yarinyar ba
sona take ba jifa yanda na dame ka a
kanta ko da yaushe tunanina gareta ne
amma kaga fa abinda ta saka min da shi
kenan. Dariya salmanu ya kyakyace da
ita harda su rike ciki, “bana san haka fa
kai wato nazo na fadama damuwata,
wato abinda zaka min kenan ko kasan fa
na tsani dariya” isah ne ke fadan haka.
Salmanu ya dafa kafadar sa yace
kwantar da hankainka abokina nasan
baka fahimta bane kawai, amma a
hakikanin gaskiya ina tayaka murna
abokina domin na tabbata ta amshi
soyayyarka. Wani irin dadi yaji baisan
ma lokacin da ya rungume salmanu ba
dan tsabar murna, “ka tabbata”, eh mana
domin kuwa murmushi ta shine tabbacin
haka sannan ba yanda za'ayi in mace
bata sanka ta maka murmushi a lokacin
da ka furta mata so saidai ma ta bata rai.
“Yaya isah wai ance in kira ka”, Wani
yaro ne dan makwabtan su aka aiko,
“Wake kirana” isah ya tambayi yaran,
“abban ku” inji yaron “jeka ce gani nan
zuwa” yauwa salmanu ina godiya da jin
wannan gagarumin albishir naka sannan
yanzu taya zan gane haka gaskiya ne
idan naje gidan. Kawai abinda zakayi
shine ka mata murmushi in kuka hada
ido sai kaga kalan martanin da zata
dawo maka dashi inji salmanu. Nan
sukayi bankwana, Isah ya nufi gidan
nasu.
Assalami alaikum ya maimaita har sau
uku amma shiru kake ji gidan kamar ba
mutane. Saida ya zo wucewa ta
matattakala sannan ya fahimci akwai
mutum a falo. Ta dora hannuwa biyu,
Haba hajara miye haka ne yasa zaki
dorawa kanki damuwa da yawa bayan
haka allah ya kadarta, haka yayi niyya
ya faru gare mu, kisawa ranki dangana
mana. Sai lokacin ma tayi farat ta dago
alhaji ashe ka dawo, tana goge hawayan
fuskar ta. Haba maman deeni yanzu
dama duk wannan kugin da nake faman
yi bakya jini hakikanin gaskiya ta bashi
tausayi domin yanda take ji da yar ta,
rabuwa da ita dole yasa ta cikin rudu.
Rungumota yayi a jikinsa yana share
mata hawaye kamar yarinya, Ita kuwa
sai shesheka take tana cewa yanzu
shikenan haleema na yanzu shikenan. Ta
kara kakame alhaji tare da kuka mai
tsuma rai, shi kuwa yaci gaba da
lallaban ta yana lallashin ta...........
Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da
Tara dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 28
Share This:Salam Alaikum masu bibiyar wannnan
labari, muna baku hakuri sakamakon
rashin kawo muku cigaban labarin har
na tsahon wasu kwanaki, hakan ya biyo
bayan wasu kalubale da muka fuskanta
amma yanzu insha Allahu zamuci gaba
daga inda muka tsaya.
**************
A baya mun tsaya ne inda
“Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban
amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata
karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar
mai tattausan murmushi mai dauke da
sako, saidai shi bai iya karanta iri
kalaman din jikin murmushi ba, kawai
cikin gida ta juya ta shige.
***************
Cikin rashin gamsuwa isah ya koma gida
yana ta tunane tunane shin me yarinyar
nan ke nufi, ai a so ba’a dole idan bata
so na ba saita fada ba kawai a wuce gun,
Isah ne shi kadai yana tafiya yana
zancan zuci....
Maryam kuwa tana shiga dakin duk suka
gyara zama wato haleema da anne wai
sai ta fada musu waye yazo gunta, ai
kuwa fa fur taki fada, sukayi sukayi
anma tace kawai bata sanshi ba. Anne
tace to ai nasan dole ya fada miki
sunansa, to ya sunansa ai nasan ko wane
saurayi a duk fadin garin nan. Bai fadi
min suna ba... Suka hau dariya wai bata
da gaskiya, haka dai sukai ta zolayar
maryam wacce ita kuwa tunani ne duk
ya addabe ta..
************
“Ina kwana umma” “lfy lau aliyu” a
cewar mamar tasa, sannan ya juya ga
maman deeni suka gaisa.. Wai aliyu har
yanzu ba batun ko daya daga cikin su
ne? Wllh mama babu wani labari a
cewar aliyu haka makarantar su maryam
ma sun ce bata je ba ranar. Maman deeni
ta yi shiru hawaye ne suka fara zarya a
idanonta a bin tausayi, kanta ne ya fara
sarawa da karfi dafe, kanta tayi tana
inalillahi. Kwatsam sai gani sukayi ta
fadi, da sauri sukayi kanta, a kidime
suka kwasa sai asbiti akayi Emergency
da ita, duk a gigice suke sun ma kasa
zama da kyar aka lallashe su da cewa
jinin tane ya hau yanzu tana bukatar
hutu anjima zasu iya shiga domin ganin
ta ....
Bangaran yazeed kuwa
*******************
Naman suka hau ci kallo daya zaka
musu ka fahimci ba imani a tattare da su
gaba daya yanda suke cin abinci da
sassan dan adam a ciki amma su ko a
kansu, tsohon cikin su ne yace gaskiya
badman kayi mana asara kasan fa
dodanmu yafi bukatar jinin yan mata
amma ka bari su mugu suka kashe su.
Dad ba haka bane a duk cikin yaran ba
wanda su mugu suka samu damar
kubutar da su, a inda suka iske su a nan
suke sheqe su. Thats gud, Kasan fa Allah
ne ya kawo mana dakwale har hudu
police 3 da kuma wani 1 dan karamim
cikin su. Dad kace naman police ne shi
isa na ganshi da baki baki. Hahaha
sukayi wata irin dariya tasu ta marasa
imani wacce suka saba. Tashi muje ka
gansu inji tsohon nan, Ya kalli wasu
dake tsaye yace kuje ku kaiwa wadan
can naman abinci mana, ko so kuke sai
sun rame sun zama kashi ne.
Su yazeed ne suka shiga dakin ajiya
wato inda su deeni suke, kallan deeni
yake kamar yasan shi saidai ya rasa a
inane, gaba daya kan yazeed ya daure to
shi a ina yasan wannan. Zuwa yayi
gaban deeni ya tsuguna yana so ya tuna
wani abu amma ya kasa kai kamar na
sanka, denni kuwa kallan sa kawai yake,
“a ina?” Inji deeni. Shiru kawai yazeed
yayi dai dai lokacin ne aka shigo musu
da abinci, plate uku ne aka bawa deeni
daya suma sauran aka jiye musu nasu,
kamar jira suke dama suka fara aika
abincin nan, deeni ne ya yi kokarin da
katar da su “kudaina cin abincin nan” ya
fada. Wata irin harara dan sandan ya
dakawa deeni alamun ya kyale su, deeni
kuwa da ya karewa abincin kallo tsaff
sai ya ga akwai nama mutum da sauri
yasa kafa ya hankadar da abincin ya
zube ..
*************
Assalamu alaikum. Suka amsa mai gaba
ki daya yan majalisar, Zagayawa yayi
bangaran abokinsa da wato salmanu ya
zauna kan dan guntun iccan da yake a
zaune, abokina waya tabo ka ne naga
duk ka wani canja fuska, ya tambayi
isah. hmm abokina zo muja gefe ina san
magana dakai, salmanu ba gardama
kuwa ya tashi suka koma gefe, isah ya
kwashe duk abunda ya faru tsakanin sa
da maryam tun daga farko har karshe,
yace to amma naga alamun yarinyar ba
sona take ba jifa yanda na dame ka a
kanta ko da yaushe tunanina gareta ne
amma kaga fa abinda ta saka min da shi
kenan. Dariya salmanu ya kyakyace da
ita harda su rike ciki, “bana san haka fa
kai wato nazo na fadama damuwata,
wato abinda zaka min kenan ko kasan fa
na tsani dariya” isah ne ke fadan haka.
Salmanu ya dafa kafadar sa yace
kwantar da hankainka abokina nasan
baka fahimta bane kawai, amma a
hakikanin gaskiya ina tayaka murna
abokina domin na tabbata ta amshi
soyayyarka. Wani irin dadi yaji baisan
ma lokacin da ya rungume salmanu ba
dan tsabar murna, “ka tabbata”, eh mana
domin kuwa murmushi ta shine tabbacin
haka sannan ba yanda za'ayi in mace
bata sanka ta maka murmushi a lokacin
da ka furta mata so saidai ma ta bata rai.
“Yaya isah wai ance in kira ka”, Wani
yaro ne dan makwabtan su aka aiko,
“Wake kirana” isah ya tambayi yaran,
“abban ku” inji yaron “jeka ce gani nan
zuwa” yauwa salmanu ina godiya da jin
wannan gagarumin albishir naka sannan
yanzu taya zan gane haka gaskiya ne
idan naje gidan. Kawai abinda zakayi
shine ka mata murmushi in kuka hada
ido sai kaga kalan martanin da zata
dawo maka dashi inji salmanu. Nan
sukayi bankwana, Isah ya nufi gidan
nasu.
Assalami alaikum ya maimaita har sau
uku amma shiru kake ji gidan kamar ba
mutane. Saida ya zo wucewa ta
matattakala sannan ya fahimci akwai
mutum a falo. Ta dora hannuwa biyu,
Haba hajara miye haka ne yasa zaki
dorawa kanki damuwa da yawa bayan
haka allah ya kadarta, haka yayi niyya
ya faru gare mu, kisawa ranki dangana
mana. Sai lokacin ma tayi farat ta dago
alhaji ashe ka dawo, tana goge hawayan
fuskar ta. Haba maman deeni yanzu
dama duk wannan kugin da nake faman
yi bakya jini hakikanin gaskiya ta bashi
tausayi domin yanda take ji da yar ta,
rabuwa da ita dole yasa ta cikin rudu.
Rungumota yayi a jikinsa yana share
mata hawaye kamar yarinya, Ita kuwa
sai shesheka take tana cewa yanzu
shikenan haleema na yanzu shikenan. Ta
kara kakame alhaji tare da kuka mai
tsuma rai, shi kuwa yaci gaba da
lallaban ta yana lallashin ta...........
Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da
Tara dan jin cigaba
adsAliyu ne ya shigo dauke da ledoji guda
biyu a hunnunsa, ya ajiye ledojin tare
da dagowa yace mama ya jikin maman
deeni, da sauki ai, Alhmdulilah saidai
doctor yace ta rage tunani domin duk shi
yake kara zafin ciwan .
Yaja nunfashi tare da cewa to Allah ya
bada lafiya ga abinci nan ai sai ki bata
ko, kema ga naki ya mika mata ledojin
sannan ya mike ya fita, maman deeni
kuwa duk ta wani rame tana jin su duk
abinda suke kuma idan ta a bude amma
bata iya cewa komai ba...
******************
Deeni kuwa tunanin tserewa yake domin
kuwa yaji yazeed yace zai kawo baban
sa. Yace a ransa ai gwara in fita ko ba
komai da zan taimakawa kawun haleema
kuma zan sake ganin ummina ko sau
daya ne kafin a zartar da hukunci a
kaina. Juyawa yayi ya kalli yan sandan
nan yaga sai barci suke abinsu, shi kam
kwana 2 da yayi a gun ko gyan gyan di
baiyi ba.. .
***********************
BAN GARAN ISAH KUWA..
Shiga yayi dakin baban nasu da sallama
abban nasa ya amsa. Bayan sun gaisa
yace mai dama ba wani abu ne yasa nace
a kiraka ba illah in fada maka maganar
da mukayi, dazu muka tatauna da
mahaifiyar ka a kan maganar yaran nan
kaga yau kwana 2 kenan bamu san wane
hali iyayan su ke ciki ba ya kamata mu
maida su ga iyayan su dan haka ina so
zan baka kudi gobe da yamma ka kaisu
gida domin suna cikin hayyacin su, zasu
ganne gida. Isah kuwa gabansa ne ya
fadi ji yake ai shikenan zai rasa maryam
dinsa idan suka koma, domin shi har ya
sakankance ma dan baiji ana maganar
koma war su ba, dan haka sam shi baiji
dadin maganar Abba ba.
“To Abba” yace, Sannan yace baba
kabar kudin ka ai ina da kudi zan sa
yanzu su shirya goben sai mu tafi.
To Allah yamaka albarka, yanzu tashi ka
kira min mahaifiyar ka tare da su yaran.
To baba ya tashi ya nufi dakin umman
nasu ya isar da sako sannan ya nufi
dakin anne, su maryam da suke zaune
sun gama cin abinci sai hirar duniya
suke, maryam ce aka bari a kwano sai
sude kwano take wai miyar tayi dadi
wato taji daudawa.
“Hmm ni wllh wani abu ke ban mamaki”
maryam ta fada, Anne tace miye kuma
wannan maryam, Wai wannan baiwar
Allahr mana ta nuna haleema da yatsa
cewa tayi fa bata cin tuwo miyar kuka in
ba nama. Zumbur haleema ta tashi daga
dan ringisawar da tayi “kiji yarinya da
sharri to waye ya gaya miki? yaushe
mukayi dake?.
Kai haleema kiji tsoran Allah kin manta
ranar da kika zo gidan mu nace in zubo
mana kika ce wai bakya ci, ko dai ranar
a koshe kike.
To ai ni ba wannan yake ban mamaki
bama ji fa yanda kuka ware kuna cin
tuwo, amma fa ni gani nake ba dan Allah
kuke cin abincin garin nan ba sai dan
yunwa inji anne.
Gaba daya suka kwashe da dariya.
Gaban maryam taji ya dan buga shi yasa
ta sasauta dariya, sai suka ji sallama
wannan ya sasu rage dariyar amma duk
da haka a cikin darayi suka amsa
sallama, isah ne ya shigo dakin ya tsaya
yana kallan sarauniyar tasa so yake ta
juyo ya aika mata da sako, amma taki
juyowa sai su anne ne suke gaishe shi...
Ya amsa itama sai daga baya ta gaishe
shi, ina wuni yaya isah a cewar maryam.
Su haleema ne suka hada ido alamun dai
akwai wani abu kenan a kasa. Shima
kam cikin wata sanyayar murya ya amsa
mata tare da cewa anne an sama kawaye
wato ba ko futa dandali, murmushi tayi
tare da cewa yayana kamar ka sani kuwa
domin ni har nama manta da fita zuwa
dandali, zuwairah ma kaga taki biyo
min, ni kwana biyu ma bansan me na
mata ba taki zuwa nan gidan...
Ai ke da ita ba’a san waye mai laifin ba
domin kuwa ke ya kamata ki neme ta
domin kinsan tallah take ko yanzu ma
tana can ta fito tuwo a dandali...
Haleema tace wai me ake a dandalin dan
Allah, yaya isah ka kaimu mu gano, yayi
murmushi, me kike ci na baka na zuba
bayan ga masu dandalin nan a kusa
dake.ya nuna anney.
Ya dan dafe kai, itafa wannan kawar
taku bata magana ne. Tana magana
mana, wannan hmm uwar surutu kenan
inji haleema, watakila kunyar ka take ji
shi isa taki magana. Maryam ce ta
dakawa haleema uwar harara.
Ah ai wallahi gaskiya ta na fada kaji
min yarinya. A cewar Haleema.
Kinga kyale ta bari inzo ni kusa da ita in
tambaye ta me ya hanata magana, zuwa
yayi gab da maryan inda take zaune ya
tsuguna. Yace....................
Sai ku biyo mu a kashi

Please Login or Register in order to submit comment