Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na Talatin dan
jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 29
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng PART 30 Na
Isah Bigboy
Hajiya maryam kenan laifin me nayi
kuma da ba'a min magana, idan laifi nayi
ai gwara a fadan dan in gyara laifina ko.
Maryam dan kauda kai tayi gefe cike da
kunya bakayi laifin komai ba.
Yauwa haba har naji zuciyata ta dan
sami sukuni...
Su halema da suke ta kallan su abun ya
bawa Haleema sha'awa, nan ta shiga
tunanin deeni ta Allah sarki.
Anne kuwa hannuwa tasa ta toshe baki
ta bushe da dariya, shima Isah dagowa
yayi cike da kunya yayin da ya tashi ya
nufi kofa, har zai fita kuma sai ya waigo,
ni har na manta ma wallahi kun jani da
hira, baba na kiranku dukaku.
Dukansu sun hallara gaban abban su
isah, Suka kwashi gaisuwa sannan ya
dora da bayani. Ba wani abu bane yasa
na kiraku sai dan in sheda muku cewa
gobe zan hada ku da isa ya maida ku
gida domin bamu san ko wane hali
iyayan ku suke ciki ba a yanzu Kunsan
dai ku ba yara bane. Ya kalli inda su
halleema suke yace fatan kundai ji
abinda nace...
To baba yaushe zasu tafi, kuma dan
Allah baba zan raka su inji anne.
A’a ai gobe da yamma zasu tafi dan
haka kuje ku fara shiri ma tun yanzu
sannan kuma ke aneesa badake za'aje
ba.
Ayya baba dan Allah ka barni inje sai
mu dawo da yaya isah.
In banda abinki aneesah ai ba yanda
za'ayi ki bisu duk da dai kun shaku da
juna amma ai sai ki bari wataran kyaje.
Hakika ita dai bata so haka ba domin
bata jayaya da iyayan nata shi yasa taja
bakin ta tayi shiru.
To mun gode abba, ba abinda zamu iya
cewa sai dai Allah ya saka muku da
alkhairi. To ameen ku tashi kuje sai da
safe ko. Kai kuma isah goben ka shirya
da wuri fa, to abba ya amsa.
Ku tashi ku tafi.
*****************
Yazeed ne yayi shiri tun da safe ya fito a
shirye, a dining ya iske su abba yaje ya
zauna bayan ya gaishe su, a nan yake
fadawa abba zai koma gida amma yana
ga kwana biyu zai yi ya dawo domin ko
kaya bazai dauka ba. Abba yace to ai
shikenan amma jiya ina kaje ne har na
dawo ban iske kaba sai maman haleema
ke gaya min kazo. Yadan sosa kai, eh
wallahi dad abokanaina ne suka tsare ni,
Hmm yazeed kullum in kazo inamaka
warning a kan ka kiyaye abokai marar sa
tarbiya, to dad ai abokan kasuwanci
nane.
Karfe 8;00 tuni sun kammala breakfast,
8:30 yazeed ya tafi.
**************
Deeni kuwa tunanin hanyar tsira yake
yace tabbas dole in bar gidan nan yau ko
ta halin yaya, hannu ya daga yana
addu’a, ga yunwar da take cin sa domin
shi kam yaki yarda yasha ko ruwan
gidan.
Kamar kullum yauma haka aka shigo
karfe 9:00 aka kawowa su deeni
breakfast amma shi ko kallan abincin
baiyi ba. Mai kawo abincin ne yaje yake
gayawa tsohon nan cewa yaran nan fa
yaki yarda yaci abinci kuma a dokar
wannan gidan sai wanda yaci abinci
shine ba zai tsira ba. Ya juya ya kalli
wani dake can tsaye kato ne duk jikin sa
a murmured, baki ne wuluk kamar
gawaye, Kallo daya zakama katan nan
ka tsorata domin indai ta bangaran
girma da murdewa ne to lalai wannan
gardin ya cika. Ya kira shi da wani suna
yace kaje ga daya daga cikin yaran can
yaki cin abinci kuma kasan cewa a
tarihin nan gidan ba wanda ya taba shiga
ya fita in ba yan kungiya ba, maza kaje
ka tsorata shi, kuma banda duka ko ka
tusa mai, domin idan kayi haka ma a
banza dole sai in mutum ne ya dauka
abincin yaci da kansa, to oga kawai
gardin yace, ya juya ya nufi dakin da su
deeni ke ciki.
*****************
9:30 su anne ne ke wanke wanke suna
tadi, to mu da ake cewa mu shirya bayan
ko kaya sai wanda suke na jikin mu, lah
kaji min yarinya to da ace bamu wanke
na jikin mu din jiya ba to da fada min ya
zamuyi yau inji maryam.
Yauwa anne wai ke baki da saurayi ne a
duk fadin garin nan ko dai babu mashin
shini ne, inji maryam. Hhhhh yar sa ido
kawai, Inji haleem. Haleema kyale ta
yau tsokana take ji, kuma maganar
saurayi ke dai tunda kin sami naki kin
zo kin dauki hadadden saurayin garin
nan ai shikenan. Wata kalan harara ta
dakawa anne tace waye? Hmm kedai
kika sani. Lokacin da suke tattara kayan
wanke wankene anne tace yauwa dan
Allah ku taimaka min ku lallabi abba
watakila in kune zaiyi hakuri ya barni in
biku tunda dai yau yaya isah zai dawo.
To mun yarda amma sai kin zagaya
damu wannan rigar taku tinda kinga har
yanzu bamuyi yawo da rana ba, Ai
wannan ba matsala bane yanzu dai kuyi
wanka tukun na, to ke fa yaushe zaki yi
wankan, Tabb to ni da ba dani za'a ba
wankan me zanyi aradu bazanyi ba.
Dariya suka kama yi, Mama wai anne
bazatayi wanka ba sai za'a je unguwa.
Maryam ce ke fadi wa maman.
Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da
daya dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 30
Share This:
RECOMMENDED ARTICLEHmm ai kadan ma kuka gani ko dandali
idan zata kwaskwarima kawai take sai
uban jan baki da take laftawa, wai amma
a hk har samari ke bibiyar ta, Hahaha to
inna amma naga tunda muka zo ba
wanda ke zuwa, inji maryam.
Hmm ai in gaya miki duk wanda yazo
korar shi take, wai ita dan mai gari take
so, Maryam tasa hannuwa biyu ta matse
dariyar da ta taho, ai kuwa inna bari in
taya ki gyaran dakin nan inje inta
tsokanan ta, ah ah maryam da kin bari
ku yan birni ai wannan ba aikin ku bane,
Maryam tayi murmushi lokacin da take
shinfida zanin gadon, lah mama kenan
to wallahi wasu yan birnin ma aikin da
suke in kika gani sai kin rike baki, a’a
maryam ai bazaki hada nan da can ba
kinga mu fa nan ko dakan fura aka barki
da shi ya isheki, balle ace ke zaki jawo
ruwa kuma ki zo kiyi girki kuma fa wani
lokacin ke zaki surfa ki kuma daka ..
Gabanta taji ya dan fadi lokacin da ta
tuno da dan guntun san isah dake
makale a zuciyarta, to shi wannan dan
mutumin idan ya aure ni a nufin shi ina
zai ajiye ni to, al qur'an nidai bazan
zauna a kauyan nan ba, wannan uban
aiki!!!.To da jan ruwa zanji ko dakan ko
girki.
Umman anne din ta danyi murmushi ko
dai abubuwan ne nan uku kadai dana
lissafa sune har suka saki dogon tunani,
ta dan zaro ido mama bayan wannan
harda wasu ayyukan kuma, Sossai ma ai
wannan wai wanda suka zama dole ne
kawai na fada miki amma ai akwai saura
da yawa ma ko in lissafo miki , a’a
barshi wallahi mama karki dada tsorata
ni wllh. Ai sai ynz ma na fahimci matan
birni hutu kawai suke kinga ba kowa
take girki da ice ba wasu cooker gas ma
suke aiki da shi, amma a haka ma sai
shegen korafi, kuma kinga ruwa mai
gida ke siya, haka ma idan kina san fura
shi zai siyo.
Mama tace kwarai kuwa kinsan fa muma
munyi zama a can kusan shekarar 9 a
can. Lah allah mama kuma me ya dawo
daku wannan kauyan.
Mamar tayi shiru kadan sannan tace “kai
maryam gaskiya fa yau kina ji da surutu.
Dama haka kike ashe”, Maryam ta dan
rufe ido wai alamun kunya, tace “mama
kenan”.
****************
1:00 Yanzu
An sallamo maman deeni, Likita ya
rubuta musu magun guna sannan yace
musu su kiyaye, kuma a guji abinda zai
bata mata rai ko kankani ne. Ya sallame
su suka koma gida, gidan kawu kenan,
gidan su aliyu.
Yanzu karfe 2:00
Yazeed ya isa garin Abuja, ya tsaya a
hanya ya danyi sayayya, tsara ba kenan,
sannan ya karasa gida. Yana shiga su
siyama sukayo kansa, wato kannan sa ne
su biyun, dake sun san duk zuwan da
zaiyi sai ya kawo musu tsaraba, saida ya
bawa kowa nashi tukunna ya karasa ya
gaida maman shi. Take tambaya lafiya
yace wallahi lafiya kalau, kawai na
dawo yin wani abune, ina dad, Bai dawo
ba inji hajiya saratu wato mamansa
kenan, “Ok” ya fada sannan ya tashi ya
nufi kan bene.
Su maman anne kuwa da maryam suna
daki sai hira suke abinsu lokacin sallah
har yayi, Maryam ta fito ta tarar da su
anne har sun kusa kammala girki, wato
abincin rana. To uwar surutu kin gaji ko,
ai muna jin surutun ki har nan, halerma
ce ta fada. Cuno baki tayi tace anyi din
yar sa ido kawai. Zanyi maganin ki ai
yarinyar nan wato ina aunty ki amma
kike fadan wannan maganar ko, Eh din
anyi ta harare ta sannan ta juya ga anne
budurwar dan mai gari ina gaisuwa fa,
idan yazo hira yau a mika min
gaisuwata. Anne kuwa daga jin haka ta
gane mama ce ta fada mata, Tashi tayi ta
bita da gudu da kara a hunnu suka hau
zagaya gida, Sallamar da sukaji ita ce ta
tsaida su..............
Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da
biyu dan jin cigaba
ads
BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 31
Share This:
RECOMMENDED ARTICLESAbban su anne ne ya shigo shine yasa su
tsayawa cik daga inda suke suka daina
guje gujen, “Abba ina wuni” kamar
hadin baki duka suka fada, ya amsa “lfy
lau” sannan ya kalli anne ke me yasa
bakya ji ne, ai shi yasa nama hanaki ki
bi su dankarki je ki kama yi musu rashin
jin a can, Kwalla ce ta cika mata idano,
a’a wlh abba zan natsu wallahi abba.
“Abba dan allah ka barta mu tafi tare”
Inji haleema kafin yayi magana maryam
ma tace abba dan Allah ka barta ta bimu
tunda yau yaya isah zai dawo sai su
dawo tare. Jin hakan abba ya danyi jim
kadan sannan yace to shikenan ba komai
zata iya rakaku. Wani kalan murna da
farin ciki ne ya ziyarci zuciyan anne
bata san lokacin da ta daka tsalle ta
kamkame maryam tana dariyar farin ciki
da shewa.
Au kun gani ko kunga abinda nake gaya
muku ko, Ayya abba farin ciki ne fa,
anne ta natsu.
Wai ina yayan naku ne, wallahi har
yanzu dai bai shigo ba abba, Yanzu fa
1:30 kunga kuyi sauri ku shirya sannan
kuyi sallah sai ku tafe can domin kuyi
bankwana da gwaggo, “to abba” suka
fada.
*****************
Bangaran deeni kuwa.
Katan yana shiga deeni yaji gaban sa na
faduwa, gadan gadan kuwa ya nufi inda
deeni ke zaune farantin abinci katan ya
dire a gaban deeni ko magana baiyi wa
deeni ba kawai ya bata rai yana hararan
deeni da jajayan idanonsa. Ganin deeni
ya dake ko dan firgita baiyi ba yasa
katan nan ya kara turo abinci gaban sa,
“Ci dan ubanka” da wata basamudiyar
murya yayi maganar, nan deeni ya fara
tunanin wani abu, tabbas akwai lauje
cikin nadi, to su miye damuwar su dan
naki cin abinci to wallahi bazan ci ba,
haka ya fada a zuciyar sa, bazan ci ba!!
haka kawai ya furta. Katan kuwa ya
fusata ai nin, wata kalan tsawa ya
dakawa deeni wace saida tasa duka
dakin ya rude, sauran police din kuwa su
biyu kan kame juna sukayi hade da sa
hannu suka toshe kunnuwa domin karan
bana wasa bane, deeni kuwa ko kallan sa
baiyi ba saidai kawai rufe kunnan da
yayi.
Kai wallahi badan ance kar in dake kaba
da yau saika dandana azabar da baka
taba ji ba a rayuwar ka, dan iska kawai
wato kai har wani jiji dakai zakawa
mutane ko oya zanje in dawo kuma
wallahi ka tabbatar ka cinye abincin
nan, ya bude kofar in daki ya fita shi
kuwa deeni kallan sa kawai yayi yace ai
kuwa zaka zo ka dauke abinka yanda ka
barshi domin ni azumi nake ma.
Su anne tuni an shirya jin ance za'a da
ita yasa ta yin wanka, nan taje ta fara
kwalliya, duk da ta zauna a birni amma
haka baisa ta daina haukan kwaliya ba.
Ta dan iya kwaliya haka ta zo ta lafta
uwar hoda ja aka zo aka kara da wani
janbaki shima ja kai abindai abin
dariya. Maryam na shigowa ta kwashe
da wata mahaukaciyar dariya sannan ta
shiga kiran haleema wai ta zo ta gani, su
anne anyi kwalliya. Ita kuwa anne
murguda mata baki kawai tayi ta shige,
ina ruwanki yar sa ido kawai, lokacin ne
haleema ta shigo dakin itama dai abin ya
bata dariya amma kawai sai ta basar ta
ce anne kyale waccan yar adawa ce. Nan
haleema ta dan gyagyara mata, “Wow
masha'allah maryam ce ta fadi haka da
tayi tozali da fuskar anne, kinga yanda
kikayi kyau kuwa annesah, ai yanzu ne
kike annesah amma da anne, sukayi
dariya. Haka suka fito suka hau zagaya
gari ko ina sai kallan su ake can suka
hango wani saurayi ya nufo su. Nan take
anne ta wani daure fuska gabaki daya ta
chanja fuska.
Maryam ta fahimci hakan to amma ta
rasa dalilin da yasa anne bata rai haka,
sun danyi gaba maryam ta dawo baya
inda taga wani saurayi wanda zai kai
shekara15 ta tambayeshi wancan waye
ta nuna saurayin da anne ta gani ta bata
rai, “dan mai gari ne mana sunan sa
ado”. Kai amma naji dadi wallahi amma
kaci sa'a bani da ko kwandala amma da
sai nama kyauta. Ta bisu a guje, tana kai
ku tsayani mana duk haukan anne yau
dai kam ta sarawa maryam domin abinda
take yi yau yafi karfin anne ma.
Isah ne a labe ashe yana kallan maryam
yana binsu a baya duk abin da take yana
gani, duk sai yaji ta kara shiga
rayuwarsa yaji santa ya kara shiga
zuciyarsa, da sauri ya bisu domin shi a
yanzu ji yake baya so ya rabu da ita
daidai da na sakan daya.............
Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da uku
dan jin cigabaGida ya bisu saida suka shiga sun dan
jima sannan ya bi bayan su. Maryam ce
sai zuba uban surutu take domin yau yan
haka ne a kan nata. Sallama sukaji anyi.
Sallamar da tasa maryam yin shiru a
dole, isah ne ya shigo, can nesa da su
kadan ya sami wani tsohon tirmi ya
zauna, sanye yake da white t-shirt mai
kyau ta kama jikinsa sai wando black
jeans, ya gyara sumar kansa tayi luf luf
duk da yake shi ko aski ba a kauyan nan
ake mai ba, yasha gyaran fuska abindai
gwanin sha'awa. To ai sai ku gama
bankwanan ku zo ma tafi, ya duba
agogon dake makale a hannunsa.
Oh kunga fa yanzu 3:30 to wallahi minti
10 na baku.
Maryam da take uban surutu daga
shigowar sa taja baki tayi tsit daga eh
sai aa kawai take iya cewa ita gaba daya
kunyarsa take ji, kowa ya fahimci haka
amma duk sai suka kyale.
Isah ne daga can yace haleema wai ni
kam me nawa maryam ne, kinga daga
shigowata taja baki tayi shiru bayan tun
daga waje nake jin sautin ta, Anne tayi
farat Kunyarka take ji..
Ya harare ta, ke kuma ina ruwanki, ah su
anisa anyi wanka ina za'aje ne. Yo ai
dani za'aje, baba bai gayama ba ta
wangale baki. Nifa ince kwaliyar nan
ba'a banza ba. Haleema ce tace kai
gaskiya anne an canfa ki da yawa
wallahi ke kowa yasan bakya wanka.
Kowa ya kama mata dariya ita kuwa ta
wani sha kunu. Maryam dai kadan-
kadan take satar kallan ya isah.
Shima din kallan ta yake daga sun hada
ido kuwa sai ya sakar mata wani
murmushi wanda ke karya mata zuciya.
Nan dai sukayi bankwana da kaka ta
kawo uwar tsaraba irin tasu ta kauye ta
basu sukayi godiya, da maryam har tace
a barshi, ya isah ne yayi magana shine
yasa tayi shiru.
Haka suka koma gidan su anne can ma
aka yo musu tsaraba har makwabtan su
duk sun kawo kayan alheri kunsan dai
tsarabar kauye bata wuce irin
kayayyakin gona su gyada soyaya,
yakuwa, goriba, taura, magarya da
sauransu.
Su haleema Sunyi mamaki matuka ganin
irin karar da yan kauyan nan suka yi
musu gaskiya ko nan sunyi abinda yan
birnin ma baza suyi ba. Tafiya suke sun
nufi hanyar da zata kaisu wajan hawa
mota, Maryam a can gefan take, gefan
dama, Ya isa kuwa yana gefan hagu,
amma saida yayi dabarar da ya koma
can gefan da take. Yau kam Alhmdulilah
sun danyi hira da ita saida ya kasan ce
su anne da halima suna hirar su dabam
itama maryam da ya isah hirar su da ban,
yaji dadi kwarai yanda ta sakar mai
fuska yau, Sun dan yi tafiya mai nisa
tukwunnan suka isa wajan hawa
motar.... Karfe 4:00 daidai suka shiga
Motar kano, Dake dan kauyen nasu ba
mutane saida suka danyi jira akayi lodi
tukwanan...
Bangaran deeni..
Deeni fa ya fara jin maza domin ji yake
kamar ‘ya ‘yan hanjin sa zasu fado dan
yunwa, tsabar yunwar da yake ji tasa ya
fara sallama rayuwarsa ma.
Abuja kuwa..
Yana zaune shida yan kannansa a falo
suna kallo, shi kuwa yana tunanin ya
zaiyi yaja daddy gobe zuwa kano, kuma
inma sunje ya zaiyi ya kaishi gidan tsafi
tunda ya riga yayi kyauta da shi.
Sallamar abba ce ta dawo da shi daga
tunanin da yake yi, cikin fara'a ya tashi
ya tari abban.
Hajiya saratu tazo ta karbi jakar hannun
alhaji, shi kuwa hannun yaran ya kamo
suka zauna yazeed ya durkusa ya
kwashi gaisuwa, sannan ya tashi ya
koma kan kujera.
Kai kuwa yazeed me ya dawo dakai
wannan karan kai da kake yin kwana2
ko 3 wallahi dad na manta wani abu ne
amma gobe zan koma, kuma sannan ina
so goben in ba damuwa mu tafi tare
domin mai gidan mu yace yana san
ganin ka..
To masha'allahu nayi murna sosai kuma
naji dadi domin kuwa na dade ina san in
san aikin ka, wato dayan business din da
kake, kaga kuwa gobe ko inada aiki,
dole na barshi mu tafi tare tunda ba
dadewa zamuyi ba, ai har momyn ka
zamu iya tafiya da ita, ya kalli hajiya
saratu yace ku shirya gobe zamu tafi
kano domin kuwa kinga batan halleema
yau kusan kwana shida bamu je ba
kullum sai faman waya. To alhaji Allah
ya kaimu kawai tace, shi kuwa yazeed
wani irin farin ciki ne ya lullube zuciyar
sa domin kuwa ya sami hanya mafi sauki
da zai ja abban shi gidan sheqewa.....
Karfe 7 su maryan suka iso garin kano,
Alhmdulilah sun zo lafiya......
Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da
hudu dan jin cigaba

A tashar mota suka sauka, a daidaita
suka hai basu zame ko ina ba sai kofar
gidan su haleema. Wani irin farin ciki ne
da azarbabi ke azalzalar haleema tun
kafin su sauko da zata ruga cikin gidan,
yau fa 6 days rabona da gidan nan, zuwa
sukayi suka kwankwasa gidan daga ciki
mai gadin ke tambaya waye, “Haleema
tace nice..” Sautin murayar haleema ne
ya daki dodan kunnan sa amma shi ya
karyata haka domin shine yaga gawar
haleema, wata zuciyar tace mai haleema
ce wata kuma tace mai wannan mai
kalan muryar tace. Kara bubugawan da
akayi ne ya dawo dashi daga tunanin da
yake, su anne kuwa ana tsatsaye sai
waige waige take domin anguwar masu
kudi ne komai a tsare yake a anguwar..
Dan budewa yayi a hankali, ganin
haleema a tsaye tana kallan sa yasa yin
sauri ya tura kyauran ya rufe, da gudu
ya nufi cikin gida yana kiran fatalwa
fatalwa, su ahaji sanusi ne da kuma
maman haleema a falo ya kunna kallo,
wai dan ya dan rage musu damuwa
amma ina, ai duk lokacin da ta tuno yar
tata sai ta fara zubar hawaye alhaji ya
hau lallashi.
Adamu mai gadi ne ya shigo a sukwane
domin masifar gudun da yake abin ya
baci da kyar da alhj ya daka mai tsawa
ya hadawa kansa birki. Kana da hankali
kuwa adamu ya zaka shigo mana gida
haka da gudu kuma ko sallama babu.
Wallahi alhaji abin ne ya tsorata ni,
alhaji fatalwa na gani yau kiri kiri da
ido na.
Kai bana san shirman banza a ina kaga
fatalwar, Alhaji wlh wlh karku je
fatalwa ce tayi shigar yar ku haleema ta
zo gidan nan domin ni nasan ba haleema
bace haleema tuni ta mutu.
Jin an anbaci haleema jikin maman
haleema ya dau rawa duk ta kidime, tana
ina muje ka kaimu, tana fada cikin wata
murya mai gargada.
Alhaji wallahi karku je, yi min shiru
matsoraci kawai, maman haleema tuni ta
fita waje ta nufi gun gate.
Shiru shirun da sukaji ne yasa gaba
daya maryam ta kosa taga mahaifiyarta
dole ta takura musu da ita fa tafiya
zatayi in yaso da safe tazo, Ya isah kuwa
da jin haka yace to yanzu yanda za'ayi
su su tsaya a nan kafin azo a bude, mu
muje gidan naku. Haka aka bar anne da
haleema a gun, su kuwa suka tafi gidan
su maryam da yake unguwar ba nisa a
tsakanin su. Tafiya suke suna hira ya
isah ne keta jaddada soyayyarsa a
gareta, ita kuwa ba abin da take so a
yanzu da ya wuce taga mahaifiyarta.
Tun daga nesa ta hango gidan a rufe
alamu dai ba kowa kenan, basu tabbatar
da hakan ba saida suka karasa suka iske
gidan a garkame da kwado. To ina mum
ta tafi kuma ma ai ya kamata mu iske ya
deeni a gida domin a gida yake yin
sallar maghriba, shidai isah ya tsareta da
kallo sauraran zazzakar muryarta yake,
ji yake kamar karta daina domin kuwa
bazai gaji da jin muryarta ba.
Kallan shi tayi duk da dare ne hakan bai
hanata gane ita kawai yake kallo ba
dake akwai fitulu a layin nasu.
Murmushi tayi “ya isah wannan wane
irin kallo ne haka kamar baka taba gani
naba sai yanzu, a kunyace yace ina wani
tunanine maryam idan na rasaki a
matsayin mata bansan wane hali zan
tsinci kaina a ciki ba, bama wannan ba,
abinda yake kara bani tsoro shine ni fa
dan kauye ne kuma a halin yanzu ma
bansan ya matsayina yake a gunki ba..
Hakika zantukan sa sun sata jin tausayin
sa, “Ya isah kasani cewa tun haduwar
mu ta farko dakai na gane cewa kaine
mijin da zan aura badan komai ba ma ko
dan faduwar gaban da naji a lokacin”,
Ya isah duk abinda ake nema a jikin
namiji ka mallake shi, sannan duk
macan da ta same ka ta wuce gori,
tabbas ina sanka har cikin zuciyata ba
wanda zai rabani dakai da kai ya isah,
kai ne kuma namijin da ya fara furta
kalmar so a gare ni ba shakka ina sanka
ina kuma kaunarka.
Wanni farin ciki ne da baya musaltuwa
ya ziyarci zuciyar ya isah bai san
lokacin da hawayan farin ciki suka zubu
daga idanon sa ba. Sun dade a tsaye
sunawa juna kallan kauna. Sai can
maryam tace yaya isah muje gidan kawu
nasan maman mu bazata wuce tana can
ba, murmushi yayi tare da cewa to muje
Ko...
Da sauri tazo ta kama gate tana kokorin
budewa. Alhaji ne ya karaso wajen
“haba safiya ya zaki zo ki dinga kokarin
bude mana gida bayan baki san ko waye
ba, kisawa zuciyarki natsuwa mana”.
Suna cikin haka ne sukaji an kara buga
gidan tare da cewa ado ka bude mana
nice, haleema ce fa, Jin muryarta ne ya
kara rikita gaba daya iyayan nata sai ya
zama ana rige rigen bude kofar ma. Suna
budewa “haleema ce alhaji wlh ita ce ko
dai gizau take wa idanuna” hajiya ce ke
fadan haka lokacin da take nunawa
alhaji sanusi. Abin tausayi yanda hajiya
safiya ta kidime da ganin yar tata
haleema, itama kukan farin ciki ta fara
da sauri ta zo ta rungume maman nata
tasa kanta cikin jikinta tana kuka tana
cewa mama nice fa. Ta kasa cewa komai
kuka kawai take, Aneesah dake gun ita
kanta saida tayi kwalla shima alhaji hk.
Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da
biyar dan jin cigaba
adsHaka suka shiga gida rungume da juna
sai kukan farin ciki suke yar da aka
fidda rai da ita gashi ta dawo, murna ai
yau a gurin su hajiya safiya bata
faduwa, haka shima alhaji, Anne dai
bayan su tabi kawai wanda su basu
tambaya ko wacece ba haka itama bata
fada musu ba...
Direct su maryam gidan su kawu suka
nufa, ita kam maryam duk da dai tana
cikin zullumin ganin ummanta haka
baisa ta share isah ba, haka suke tafiya a
jire sai hira suke irin ta masoya kamar
dai wanda dama can sun shaku da juna.
Sunzo wuce wa ta wajan wani mai lemu
ne isah yace bari a sayawa umman
tsaraba, Uhmm kawai tace, Lemun 300
ya saya aka zuba a leda. Basu dade suna
tafiya ba suka karaso layin su kawu.
Maman deeni yau jiki yayi sauki zaune
take a kan tabarma a tsakar gida ita dai
yau ta rasa me yasa gaban ta ke faduwa
lokaci zuwa lokaci, haka dai ta wuni yau
tun tana tsammanin wani abu yanzu har
ta daina, ta kammala sallar isha’i tayi
addu'o'I, maman aliyu ce take jira domin
suci abinci karya huce.
Su maryam sun karaso kofar gida, shi isa
yace bari in tsaya ki shiga idan kin sanar
da su sai in shigo ko, tace tom.
Assalamu alaikum, karima wato maman
deeni kafe mai sallamar tayi da ido
lokacin da take kokari tashi, itama
maryam daga inda take ta tsaya cik tana
hawaye dan farin ciki, haka dai sukayi
cirko cirko kowa sai sharar hawaye
yake. Ita dai maman deeni bata gaskata
abinda idanuwanta ke nuna mata ba, shi
yasa ma bata karasa gun maryam ba.
Suna cikin haka ne amina ta fito daga
dakin lokacin da ta gama saller, daga
inda take ta tsaya hade da cewa wa zan
gani haka, maryan kece kuwa, lokacin
ne ma maman deeni ta fahimci
idanuwanta ba karya suke mata ba.
Mama amina nice. Haba a lokaci guda
maman deeni ta taho da gudu ta
rungume maryam tare da fashewa da
wani kuka mai tsuma zuciya tana fadin
“maryam ashe kina raye, maryam ina
kika tafi kika barni” cikin kuka take
maganar, itama maryam kuka take yi
mai tsanani tare da farin ciki, maman
amina ma zuwa tayi ta rungume su, haka
suka kankame juna ba abinda suke sai
kukan farin ciki..
Isah dake kofar gida a tsaye tuni shi
yafara gajiya da tsayuwa ba abinda yake
ji sai sautin kuka dake tashi a gidan, shi
yasa ya yanke shawarar cewa idan yaga
yaro ya aika shi ya kirawo maryam..
Ana cikin hk sai ga aliyu da ya dawo
daga wajan abokansa, ya iske mutum a
kofar gida yayi masa isah sallama
sannan ya mika mar hannu suka gaisa,
har aliyu ya juya zai shiga gida sai isah
yace yauwa dan Allah idan ka shiga
kace anawa maryam magana, cikin
rashin fahimta yace wace maryam kuma,
ai mu bamu da maryam a gidan nan, eh
ba yar nan gidan bace ai zuwa tayi, bai
ce mai komai ba yasa kai ya shiga cikin
gidan, yayi sallama yaji shiru sai sautin
kuka, Ganin halin da suke ciki ne yasa
shi karasawa da sauri, maryam
Alhmdulilah

Please Login or Register in order to submit comment