Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kuma mahaifina Malam Buba(Abubakar) aminan juna ne wanda amintarsu ta samo asali tun kan iyayensu wanda tarihi ya nuna suma haka suka taso kansu a hade. 
   Malam Buba  bayan aure ya koma cikin birnin Gombe da zama Unguwar Tudun wada tare da mahaifiyata Fatima wacce muke kiranta Dada. Yaransu bakwai, uku sun rasu, ya yi saura daga  Haruna, Baffa(wanda ya ci sunan Usman baban Hasiya) sannan ni Abdullah wanda hasken fatata yasa suke kirana da Balarabe sannan kuma kanwarmu Aisha. 
    Gaba daya danginmu bamu da yawa sosai don bamu kai yawan dangin mahaifiyarki. Mahaifinta d'a ne ga Muhammadu Lamido, tsohon Sarkinmu na kauyen Jar Kwami, kafin ya mutu yana da mata har hudu banda uku da suka ta6a rabuwa duk kuma sun ajiye mishi yara, mata sunfi yawa cikin yaransa, bayan mutuwarsa aka dora wani kan karagar mulkin don alokacin yaransa maza su uku duk basu kai minzalin rike mulki ba. 
   Koda lokacin ya yi, babban yayansa ne kawai  ke shaawar mulkin sam kakanki Malam Manu(dansa na biyu) ba ya so.  
    Gaba daya a gidan sarautar su ke zaune, manyansu da yaransu. Sai kuwa matan da aure ke rabasu da gidan, wasu cikinsu ma auren gida ake musu da yaran yan uwa. 
   Duk cikin yaran Malam Manu, mahaifiyarki ce k'aramarsu, babban dansa namiji ne, Ado sai Bilkisu, Safiya, Asma'u sannan Mahaifiyarki Hasiya saidai Boddo suke kiranta, wato mai kyau. Don Masha Allah duk cikin yaran Malam Manu babu mai kyawunta.  Innarsu Aisha da suke kira da Inna tun bayan haihuwar Hasiya suka koma kiranta da Inna Boddo. 
     Tun farko anso yi mana auren zumunci da mahaifiyarki tun ma bata isa aure ba, amma fir na k'i sakamakon soyayyar da muke yi da Saude diya a wajen wata mai siyar da abinci a tsohuwar kasuwa inda nan nake zuwa siye da siyarwa. Asalinsu yan Kano ne can kauyen Ringim, saidai aure ne yasa Atine uwa ga Saude  baro garinsu zuwa nan Gomben, bayan rasuwar mijinta ne ta fad'a harkar siyarda abinci. Saude kadai ce diyarta, nakan yawaita zuwa shagonnasu daga shagon yayana dake zuwa Kano saro yadikan maza,  haka har muka saba da Saude kafin kuma soyayya mai karfi ta shiga tsakaninmu. Kullum kwanon abincina na rana anan ya ke. 
   Ranar da na zo wa mahaifinmu da maganar auren Saude, sam bai aminta ba don kuwa ya ce shi fa ba ni da mata sai Hasiya, lokacin idanuna sun rufe na ce bana sonta, nan duniya  Saude kadai ce abar sona. 
   Akan wannan saida ran Malam ya 6aci ainun, ya budemin wuta sosai. Har ya yanke shawarar zuwa Jar Kwami don ayi wacce zaayi, hankalina ya tashi, ina gani babu wanda ya goyi bayan na auri Saude. Karshe kuwa da ni aka je Jar Kwami, koda Malam ya gama magana akan aurena da Hasiya, Malam Manu ya aminta kuma ya ji dadi sosai, saidai ya bawa Mahaifina hakuri inda ya nunamishi har lokacin Hasiya bata kai munzalin aure ba saidai ko ta zo a ta biyu. Malam fir ya k'i amincewa, ya jajirce akan lallai a daura aurenmu da Hasiya. 
  Koda na sanarwa Saude halin da ake ciki, ta shiga tashin hankali matsananci ga shi a wannan lokacin mahaifiyarta na shirin zuwa ganin gida can Ringim.  Ana gobe za'a daura aurena da Hasiya na bi Saude da babarta zuwa Ringim don kuwa a wannan lokacin ji mu ke yi idan ba mu auri juna ba to fa za mu iya rasa ranmu. A hanyarmu muka yi hatsari mahaifiyar Saude ta rasa ranta, har suma saida Saude ta yi don tashin hankali, inda ma aka ci sa'a Sauden tasan garin tana zuwa. Da taimakon jamaar gari da kuma kwatancen Saude, Allah Ya yi isarmu gidan Kawunta Isah, anan aka yiwa mahaifiyarta jana'iza bayan nan Saude ta gabatar da ni matsayin wanda za'a auramata, ta sanarmusu wannan ne musabbabin zuwanmu garin. Koda aka nemi sanin tarihina, muka rufe komai muka nuna cewar ni din maraya ne, dangi kuwa sun sakoni gaba, babu mai kaunar ya ra6eni. Kawu Isah bai so aurennan ba don yana ganin kamar mun 6oye wani abu bayan wannan, saidai ganin yanda Saude ta tada hankali ga kuma maraicinta da ya duba hakanan itama bata samu wani sukuni daga dangin ubanta ba, ya amince ya daura aurenmu, gidannan da ki ke gani nawa ne, a farkon zuwanmu gidan Kawu Isah muka zauna har na tsawon shekaru biyu kafin na samu abin hannuna ta hanyar sana'o'i daban-daban na gina wannan gidan ginin k'asa. Wannan na sumuntin duk na yanzu ne. (Ya yi nuni da bangon gidan sannan ya dora). Tun zamanmu tsawon shekarun nan Yahuza mijin Habiba makwatanmu ne, yanda na saba da Yahuza haka Saude ta saba da unguwar zoma Habiba kusan ma da ya ke su mata ne shakuwarsu ta fi namu.
   Ashe su kuwa acan da na tafi sun daura aurena da Hasiya, saida watarana tunanin gida ya addabeni tashi guda na ji inason komawa Gombe. Zuwana na ji labarin rasuwar mahaifiyarmu da kuma auren kanwata Aisha. Na yi kuka kwarai, Malam kuwa ko kallon inda nake baiyi ba. Gwara ma yayyuna sun saurareni, Haruna da kansa ya bani shawarar zuwa ga Malam Manu don shi kadai ne zai iya shawomin kan mahaifina ya yafemin. Banyi kasa a gwuiwa ba washegari na wuce Jar Kwami. Malam Manu kusan ya yi murna kwarai da ganina, yanda ya kar6eni har kunya na ji don ban ta6a daukar an daura aurena da diyarsa Boddo ba. Ya bini doguwar nasiha, karshe washegari muka wuce cikin Gombe. 
Malam ya tabbatar ya hakura muddin zan ba shi takardar Hasiya, ashe ma tun bayan auren aka kawota gidanmu saboda gudun maganar mutan gari.
  Malam Manu kuwa ya ce bai isa ba, babu mai kunce aurennan, ni kaina ba zanso hakan ba. Dakyar da sidin goshi Malam ya hakura saidai ya ce nan zan zauna da Hasiya. Nan ma ansha artabu kan ya amince da tafiyarmu Ringim da ita. Saida na yi sati uku kafin na taho da Hasiya da yayyunta da wasu cikin dangi duk don a ga waje. 
  Ina cike da tsoron irin kallon da Saude za ta yiwa lamarin, saidai ga mamakina ta nuna ta fini farin ciki, har da durkusawa ta yi ta nemi gafarar yan uwana acewarta itama ta yi musu laifi na rabasu da ni. Wannan abu ya k'aramata k'ima a wajena, haka suma yan uwana suka cika da farinciki fad'i su ke, "Balarabe ka yi dacen mace ta gari." Har suna kwatantawa Hasiya da ta yi koyi da Saude. Ko bayan tafiyarsu na barwa Hasiya dakina, daman dakuna uku ne a baya, daya a zaure sai biyun nan kafin yanzu da aka yi ciki da falo.  
  Zaman lafiya suka gudanar, hakurin Hasiya da kyawawan dabi'unta su suka sanya ni cikin shaukin so da kaunarta ainun, abin Allah sai Ya doromin so da kaunarta fiye da irin wanda na yiwa Saude. Dakyar nake kokarin kwatanta adalci atsakaninsu. 
  Alokacin ne kuma Saude ta soma nunamin damuwarta kwarai akan rashin samun ciki. Kullum cikin yi mata nasiha nake, saidai takan yawaita tambayata kudi na zuwa wajen wata mai maganin gargajiya da aminiyarta Habiba ta bata labari na wai tana bada maganin samun ciki. Duk yanda na so fahimtar da ita cewar haihuwa lokaci gareshi, bata fahimta ba. 
   Haka har Hasiya ta samu ciki, kusan Saude ta fimu nuna murnarta, har kuma ta raineshi Saude har ayyuka ta ke kar6amata, magungunan gargajiya duk da tasan zai amfaneta takan kawo, haka itama Habiba ta kyautatawa Mahafiyarki, Allah kadai yasan zuciyoyinsu, ko tun wancan lokacin da gaske suke nunawa Hasiya kauna, ko kuwa dai da biyu su ke yi? Ba zan ce komai akai ba don bani da tabbas. 
  Cikin ikon Allah cikin Hasiya ya kai wata tara, tana haihuwarki kuma sai Allah Ya dauki ranta."
  
Malam Balarabe yana kaiwa nan ya dubi Ummi ya na mai haska wayarsa sakamakon wutar da tuni aka dauketa. Ummi hawaye ta ke yi don ita tasan duk ba don Allah suka yi ba, ta sha ji suna hirar, Allah ne kadai ya yi itama za'a haifeta don tun tana ciki aka so cikin ya zube, cewar Saude kenan duk sadda ta ke goranta mata da zaginta a baya.
  "Hasiya ki gafarceni, bansan dukkan abinda ya biyo baya ba bayan mutuwar mahaifiyarki, don lokacin gaba daya tsanarki ce ta dirar min, su kansu yan uwana sai suka fita hanyata haka kema daga dangin mahaifiyarki babu mai zuwa su ganki. Sun aminta da Saude fiye da zatonki, kamar yanda nima na aminta da ita ta yimin halin DAN ADAM na butulci."
Ya karashe yana mai share hawaye. Murmushi Ummi ta yi gami da kamo hannun mahaifinta....
  ((Inda gyara kofa a bude ta ke [email protected] ko fcbk.. Rufaida Omar))
DAN ADAM

@RUFAIDA OMAR

    94

"Idan kana bani hakuri bana jin dadi wallahi Baba, ni na hakura komai ya wuce awajena. Abinda ya faru kaddara ce, kuma Allah Ya yi ba makawa sai ya faru. Ka daina damuwa kada wani ciwon ya kamaka."
  Ya jinjina kai yana murmushi can kasan ransa kuwa, yabawa ya ke da kaifin basira irin na 'yartasa. Damuwa dole ce a wajensa, ko don ma rashin sanin irin kallon da danginnasu zasu yi gareshi. A fili kuwa ya nunamata komai ya wuce. Wayarta da ke(ringing) ne ya katsesu, ta sa hannu ta janyo jakarta ta ciro don ita ta mance da ita ma, ganin mai kiran yasa ta ajiye wayar don kunyar dauka ta ke ji gaban Babannata, lura da hakan yasa shi yin murmushi sannan ya mike.
"Bari dai na lek'a wajen abokan hirata yau sun ji shiru, daga nan na saka kati na kira su Yalla6ai na ji yanda suka isa. Wannan ki kaita ga daki nan akwai katifa ku kwanta anan." Ya karashe yana nuni da Mariya. 
   Ta amsa da to, bayan fitarsa ta janyo wayar da sauri saidai kafin ta kai ga amsawa har ta yanke, ta bi wayar da kallo cike da shauki anan take ta kira ya kuma shigowa. Ta d'aga da sallama. 
   Faruk da ke kwance saman gadonsa rungume da filo ya lumshe ido jin muryarta ya amsa sallamar ciki-ciki. 
  Jin yanayin muryarsa ne yasa ta fadin.
"Kun isa lafiya? Ya mura?"
"Alhamdulillah, kin samu Baba kin mance da mijinki ko?"
  Ta ji kunyar maganar, har lokacin bata gamsu da yanayinsa ba, kamar dai akwai damuwar da ya ke 6oyemata.
  "Ummina." Ta kasa amsawa sakamakon jin kiran sunannata da ya yi yana zaga dukkan ga66an jikinta, ta lumshe ido gami da jingina kai da bango tana kallon sararin samaniya wanda ke cike da taurari. 
    "Ba za ki amsa ba?"
Ta daure ta amsa.
"Um." Murmushi ya yi mai sauti kafin ya ce.
"Ina kewarki. Ina matukar kewarki Ummina, ban gane hakan ba saida muka dawo gida, duk sai ya yimin fad'i."
   Murmushi ta ke yi saidai ta kasa cewa komai don ita kunya ma ya bata, ga kaunarsa da ke k'aruwa sosai a ranta. Ita kanta ta yi kewarsa fiye da tsammaninta.
  "Ba magana ko? Wannan kunyar fa ta gulma ce akwai ranar da zan kaudata don na gaji da ita tana cutata."
   Ta rufe idanunta da hannu tamkar yana ganinta, banda "Um" ba abinda ta ce. 
   "Banso aka k'i tsayar da maganarmu ba yanzu ba, saidai Baba yana da gaskiya, ni kaina zanfi so kiga danginki ko burinki zai cika tukunna. Ina kara tayaki murnar sasantawa da mahaifinki, Allah Ya k'ara kauna tsakaninku."
  "Amin Yaya Faruk, nagode."
"Na gaji fa da Yaya yayannan, ki chanjamin suna."
   Ta danyi dariya kawai. 
"Dagaske nake, ana muku ruwa?"
Ta girgiza kai.
"A'a."
  "Ayya, mukam ruwa sosai ake yi."
Murmushi ta yi.
"Alhamdulillah, kun ji dadi."
"Ina wani dadi, babu Ummina a gida?"
Kamar ta nutse don kunya ta kasa magana can kuma ta ce.
"Saida safe."
  Ga mamakinta ta ji ya saka dariya sosai, sai itama yasa ta murmushi. Bayan ya tsagaita ya ce.
"Allah Sarki Ummina, ina son wannan kunyartaki saidai please ta kasance iyakar yanzu kafin mu kai ga aure kin ji ko?"
   Murmushin dai ta ke yi ba ta ce komai ba. Atishawa ya saki har uku a jere, ya karashe da fadin Alhamdulillah, ta amsa da YarhamukAllah sannan ya amsa mata da 
"Yahdikumullahuwa wa yuslihu balakum."
   Shiru ya biyo baya kafin kuma ta daure ta ce.
"Don Allah ka sha maganin mura."
Ya ji dadi ainun na kulawar da ta nuna gareshi. 
   "Banason magani, sau daya na sha ya sanyani bacci ban k'ara sha ba."
  "Haka za ka daure ka..."
Sai kuma ta ji nauyi ta yi shiru.
"Kin damu da ni har haka Ummina?"
Wasa ta hau yi kawai da jelar dankwalinta batare da ta ce uffan ba. Ya sauke ajiyar zuciya.
"Zan sha tunda ba kya sona da mura."
  Ta murmusa.
"Ka turomin lambar Hajiya don Allah."
   "Me za ki ce mata?"
"Gaisawa za mu yi."
"Shikenan zan aikomiki."
Daga haka suka yi sallama, ta mike ta shiga dakin da Baba ya yi mata nuni da makwancinsu, ta gyara shimfidar, dakin katifa ce kawai sai shirgin kaya a gefe. Da taimakon wayarta ta haska ta dauko Mariya bayan ta kai ta ta yi fitsari ta shimfideta. Ita kuwa kayan jikinta ta rage ta d'ebi ruwa ta zagaya kewaye don garin akwai zafi, bayan ta yi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga na bacci cikin wadanda Faruk ya siyamata. Ta feshe jikinta da turare mai sanyin kamshi sannan ta zauna gefen katifar tana tunanin ko ina mahaifinta ya wuce? Sallamar Saude ta ji wanda ya sanyata jin wani mugun faduwar gaba, kafin ta amsa, ta tsinci muryar Babanta wanda daman ba nisa ya yi ba yana zaune kofa. 
  "Me ki ka zo yi a gidana?"
Saude ta dubeshi, daman a k'ule ta ke don acan Kawunta Isah ci mata mutunci ya yi ya nuna babu inda zaije daman tuni ta bar ganinsa da daraja. Da ta gaji da zama ta ga dai babu wanda ya kulata an barta a tsakar gida yashe yasa ta taho ko tayin abincin da akayimata bata ci ba don ta rantse gidanta za ta kwan. 
   "Ka manta inada 'ya? To babu inda zanje sai na yi idda."
"Idda a gidan wa? Wallahi ba ki isa ba Saude, ke ba irin matar da zan yi marmarin na komawa aurenta bace, tun muna mu kadai ki tattara ki barmin gida kafin na jibgeki na tara miki jama'a!"
  Ummi dai tana daga daki tana lek'ensu don tsakani da Allah har yanzu tana jin tsoronta sosai. 
   Saude ta yi shewa.
"Ahayye! Lallai Abdullahi wuyanka ya isa yanka! Har ni Saude ka ke gayawa haka? To ni kuwa yau babu inda zanje, anan gidan zan kwana don uban mutum!"
   Tana maganar kamar ta6a66iya, daidai da su Habiba da sauran makwafta mafi kusa suna ji, ko daga majalisar su Malam Balarabe suma suna jiyo ihunta da maganarta. Zagin da ta yi ya firgita dukkan masu sauraro, ai Malam Balarabe baisan lokacin da ya janyo igiyarsu ta shanya ba nan take ta tsinke, ya soma tsulamata yana fadin.
"Kinyi kadan, karyarki ta yi karya ki zagi ubana! Kin yi kadan Saude."
Ihunta yasa mutane suka shigo, itama Ummi fitowa ta yi tana rokon mahaifinta da ya kyaleta. 
"Haba Malam Balarabe da girmanka? Wannan ba girma bane, dukan mace don Allah ka yi hakuri." Cewar Malam Yahuza kenan, Saude wacce ta ci duka ta hayayyako mishi.
"Kai dalla can rufewa mutane baki, solo6iyon banza da wofi, duka-duka yaushe ka samu kwato kanka a hannun Habiba?"
  Hakan ya harzuka Malam Balarabe ganin bakar maganar da ta ke fadawa abokinsa, ya k'ara tunzura zai kai mata duka, gam! Ummi ta rike igiyar gami da durkusawa tana fadin.
"Don Allah Baba ka yi hakuri, ka kyaleta."
Saude ta mike tana gyara zaninta tana ihun kuka, Malam Yahuza da sauran mazan suka rasa bakin magana, suna shirin fita ai kuwa ta cakumo wuyan Ummi ta baya tana fadin.
"Kema sai kin bar duniya yadda Hasiya ta barshi, sai na kasheki!"
  Ummi da ta ji shak'a ta soma kwatar kanta saidai ta kasa, cikin zafin nama mutanen suka yo kanta, dakyar aka yi nasarar kwatar Ummi daga hannunta, kuka sosai Ummi ke yi tana shafa wuya tana tari don ba kadan ba, ta ji shak'ar. Mari lafiyayye Malam Balarabe ya wanke fuskar Saude da shi, ai kuwa ta hau tsalle tana zage-zage, ya finciki hannunta tana tsalle tana ihu tana zagin iyayensa da Ummi har tana fadin "Da nasan haka za ki zama da tun kina jaririyar kema mun kasheki!!" Haka har ya watsar da ita a kofar gidan ya kulle ta waje. 
Mutane sai hakuri suke bata daidai da mata fitowa sukayi kallon wannan abin al'ajabin. Bata jira komai ba ta nufi kofar gidan Malam Yahuza. Hannuwanta a k'ugu tana karkad'a jiki.
"Ina ki ke shegiya bak'ar munafuka? Ki fito! Ki fito nace!!!"
Tana shirin shiga gidan Malam Yahuza ya tureta daman cike ya ke da haushinta.
"Karki sake ki shiga gidana, kada na k'ara ganin kafarki wallahi."
  Dariya ta shiga kyakyatawa ga hawaye jage-jage saman fuskarta kamar mahaukaciya sabuwar kamu tana nunashi daga sama har k'asa kafin ta rangad'a bud'a. 
  "Ayyiririii! Eh babu shakka akuyar daure ta samu sake! Yahuza kai ne ka samu iko haka? To wallahil azim yanda aurena ya mutu kema Habiba yau naki zai mutu!"
    "Idan ke ce da shikan a hannu sai ki zo ki rabamu!"
  Cewar Habiba sa'ilin da ta leko kanta, Malam Yahuza na kokarin tsawatarmata akan ta koma ciki saidai maganar Saude ya dakatar da shi, duk jama'a na kallo, Malam Balarabe kuwa jira ya ke yi ta gama haukanta ta bar wajen ba zata shigar mishi gida ba. 
   "Keda ki ka kashe rai! Wallahi jama'ar gari ku shaida Habiba da hannunta ta kashe Hasiya!!!"
    
   Can na hango Bokanya tana faman kyakyata dariya tana kara jijjiga abin tsafinta a hannu, cikin ihu da kururuwa ta dauki wata kwarya ta fasa tana fadin.
  "Kadan ku ka gani shegu! Kadan ku ka gani!! Na soma karya dukkan mugun aikin da na k'ullamuku!  Daman kwa yarda da wani bayan Allah? Hahaha! Mu daman ta6a66u ne mun yarda!!! Hahahaha!!!" Wannan furucin Bokanya kenan sa'ilin da ta ke kallon dukkan abinda ke faruwa ta cikin wata k'atuwar kwaryar sihiri. (Wa'iyazubillah).

Mutanen wajen suka yi sak, Ummi a guje ta fito daga gidansu kanta babu ko kallabi ta zubawa Saude ido jin abinda ta fad'a. Habiba fitsari ta soma saki a wando don kuwa bata ta6a tsammanin akwai ranar da Saude za ta yi mata haka ba! 
   Gaba daya waje ya dauki salati. Wuf Habiba ta fito bayan ta ture hannun Malam Yahuza wanda ya tokare kada Saude ta shigar mishi gida.
"K'arya ta ke yi! Ta haukace! Kada ku yarda karya ta ke min!!"
  Saude wacce bata bar kyakyata dariya ba ta ce.
"Ina rantsuwa da Allah ita ta kasheta amman da sa hannuna!"
  Ta karashe tana soshe-soshen jiki don haka kawai ta soma jin wani k'aik'ayi a fatar jikinta. Kafin wani ya yi yunkurin karasawa gareta Ummi cikin zafin nama ta k'arasa, ta rik'e kafadunta tana kuka cikin daga murya ta ce.
"Ki gayamin, dagaske kune ku ka kashe Ummana?"
Dariyar dai ta ke yi itama cikin kwaikwayon daga murya ta Ummi ta amsa.
"Eh! Ni da Habiba muka kasheta! Kema na so a kasheki saidai Habiba ta bada shawara a kyaleki nan gaba jari za ki zamarmana! Kuma kin zama." Ta karashe cikin dariya. Sai kuma tiryan-tiryan ta shiga bada labarin yanda komai ya faru. 
Ummi batasan sadda ta fidda hannu a zafafe ta dauketa da mari hagu da dama ba, tana yi tana kuka da fadin.
"Ban yafemiki ba Saude(ta fada gatsal don girman ya fadi)! Ban yafemiki ba!!" Sai kuma ta durkushe tana kuka sosai, nan aka ankara Habiba ta gudu. Ai kuwa wasu matasa suka rufamata baya. 
  Ita kuwa Saude wacce bata ji marin Ummi ba asalima dariya kawai ta ke yi, ta karasa ga Malam Balarabe wanda ke kuka har da sheshsheka saidai ya kasa samun karfin zuwa ya rarrashi Ummi sai wasu matan makwafta ne suka zo suka dagata. 
  "Abdullahi kai mutumin kirki ne, ka so ni sosai, saidai ni tun daga ranar da ka yimin kishiya na tsaneka."
Ta cigaba da dariya sannan ta dora.
"Habiba kawata ta ban shawarar 6oye kishina kuma na bi, babu irin maganin da ban barbada muku ba a abinci kai da ita, sai kuma duk da haka ka fifita ta a kaina!"
Ta karashe ciki daga murya a fusace sannan ta dara.
"Kuma ta zo ta samu ciki." Fadin haka yasa Saude soma kuka duk mutane na kallonta cike da takaici har lokacin wadanda suka bi bayan Habiba basu dawo ba, Malam Balarabe da ya rasa ta cewa tagumi kawai ya yi yana hawaye yana dubanta, can kuma ta dora tana soshe-soshenta.
  "Na sha gwada kashe Hasiya da dan cikinta ta hanyar duramata magunguna ina fakewa da fadin na gargajiya ne na kara lafiya, saidai banga wata illa da ya yi mata ba har zuwa sadda cikinta ya shiga wata tara ta soma nakuda muka kasheta muka bar jaririyar. A karshe na asirceka ka daina kaunarta, na saka dangin uwarta da danginka suka daina zuwa inda ku ke, amma Abdullahi duk wannan kaunar da na nunamaka bai hana ka sakeni ba?!!!"
Ta karashe tana mai dibar k'asa ta watsamishi ya rufe fuskarsa. Nan kuma ta hau tsalle da soshe-soshe, baiyi wata-wata ba ya soma yunkurin dukanta dattijan suka hana. Malam Sule makwafcinsa ya ce. "Ai dukanta yanzu kuma 6ata lokaci ne Malam Balarabe, ba ka ganin ma bata cikin hayyacinta?"
  Malam Balarabe kawai sai ya juya ya shiga gidansa yana kuka, Ummi ta bi bayansa da sauri itama. 
  Habiba cikin sa'a aka cafkota, ana zuwa Malam Yahuza ya tsinke igiyar aurensa da ita, nan ta hau kuka da neman gafara, Malam Balarabe ya fito aka hada kansu sai ofishin yan sanda. Habiba da kanta ta yi bayani don Saude hauka ta ke yi tuburan tana faman kyakyata dariya. 
    Aka gark'amesu da zummar sai washegari a k'arasa maganar. 
    Ummi da mahaifinta wannan ranar kasa bacci suka yi ga ciwon kai mai tsanani da Malam Balarabe ya kwana da shi, ita kanta Ummin da shi ta kwana sakamakon kuka da ta sha. Nafila kuwa a wannan daren ta yi shi hakanan addu'o'i. Babu wanda cikinsu ya ta6a kawo hakan, kowannensu tunaninsa bai wuce mutuwa Hasiya ta yi ba kawai ashe azzaluman ne suka kasheta.
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  96
    "Ina a Tudun Wada?" Cewar matuk'in.
"Bayan gidan Sarki."
  Suna tafe Malam Balarabe na nunawa Ummi wurare gaba daya ya kasa ma rufe bakinsa, itama saita tsinci kanta da farinciki, Mariya ma kalle-kallen ta ke yi bakinta washe har suka iso unguwar. Wayar Ummi ta yi k'ara ta amsa. Hajiya Babba ce don kuwa ta yi kiranta kwanakin, suka gaisa kafin ta tambayi ko sun isa, ta amsa mata da eh. Ta ce ta gaishe da mutanen gidan. Daga haka suka yi sallama alokacin da kuma ta ga sun tsaya daidai wani gida karami ya sha fenti ruwan madara, wanda a kusa da shi wani gidan ne shima shigensa don hatta da fentin iri guda ne. Zaune a kofar gidan, wani dattijo ne kishingide saman tabarma, a gefensa kuwa wani ne da bai wuce shekaru hamsin ba suna hira da dariya saidai tsayuwar tasi din a kofar gidannasu yasa hankalinsu ya dan koma gareta. 
Jikin Malam Balarabe har rawa ya ke don ko shekaru nawa ya yi ba fa zai mance wadannan fuskokin ba, Haruna yayansa ne sai kuwa Mahaifinsa. 
   Shima Harunan mik'ewa ya yi da sauri.
"Abdullah!" Jin sunan da ya ambata yasa Dattijo Malam Buba mikewa zaune daga kishingidar da ya yi yana mai gyara zaman gilas dinsa na masu ciwon ido gami da k'urawa wanda aka kira da sunan Abdullah dansa idanu. 
  Tuni Malam Balarabe ya karaso da sauri suka rungume juna shi da yayannasa. Kawai sai suka fashe da kuka, Ummi ganin haka itama ta soma hawayen tausayamusu. Duk a silar kaddara sun rabu da juna. Ganin mai tasi ya gama sauko kayansu daga boot, ta tambayeshi ko nawa ne kudin sannan ta zaro a jakarta ta biyashi ya wuce. 
"Abdullah ashe za mu k'ara sanyaka a idanunmu?" Cewar Harunan kenan cikin zubar hawaye. 
  Malam Balarabe ya na sharar hawaye ya karasa ga mahaifinsa wanda ya yi shiru yana ta faman jera hamdala a zuciyarsa ganin addu'arsa ta shekara da shekaru ta kar6u a yau.        Ya riko hannuwan mahaifinsa shi kuwa Haruna ya nufi wajen su Ummi wadanda ke

Please Login or Register in order to submit comment