Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

gaisheshi. 
  "Malam gani gabanka, ka yankemin dukkan hukuncin da kaga ya dace, na yi babban laifi, na manta da dukkan hakkinku da ya wajaba a kaina na kula da shi, ka gafartamin Malam, na tabbatar har da k'in jin maganarku da na yi na auri son raina."
  Malam ya damk'i hannunsa cikin rawar murya ya ke fadin.
"Ba ka da laifi Abdullah, na jima da fahimtar hakan, shiyasa ban ta6a rik'eka ba a raina. Gareni, na yafemaka, tashi mu shiga ciki Abdullah mahaifiyarka ta sanyaka a ido ka nemi gafararta." Da taimakon Malam Balaraben Mahaifinnasa ya mike, suka yi ciki, yana dogara sandarsa. 
  Ummi wacce Haruna ya gama ja da hira yana fadamata irin matukar kamar da sukayi da mahaifiyarta, itama tasan hakan sakamakon hotonta da mahaifinnata ya bata. Suka mara musu baya suna mai daukar jakankunan wadanda uku ne kacal. 
   Saida suka shiga ta fahimci ashe dai ginin nada dan girma, irin ginin nan na gidan yawa, yara suka yita binsu da kallo, Abida mata ga Usman wato Baffa ta dubi Haruna bayan shigewar su Malam Balarabe da Malam. 
  "Waye wannan?"
  Yana murmushi mai bayyana hakora ya amsa.
"Har kin mance da Balarabe? Ai shine da iyalinsa."
Ta zaro ido tana mai dafe kirji, yayinda ta ke bin su Ummi da kallo, Ummi ta gaisheta sannan itama Mariya ganin haka ta gaidata. 
Dada na zaune a rumfarta tana gyaran wake, tsohuwa mai ran karfe, idan ka ganta ba ka ce yara bakwai sun fito daga jikinta ba don kuwa da kuzarinta. 
   Ta ajiye waken gefe ta yi sakato tana duban wanda ke rike da mijinta. Ko shekara nawa Malam Balarabe zai yi ita din mahaifiyarsa ce da ba zata ta6a mance fuskarsa ba. Kafin su kai ga karasawa gareta ta mike da sauri ta shige dakinta. Suka karasa suka isketa zaune saman gadonta na karfe tana faman sauke ajiyar zuciya. .  Bayan zamansu ne ta dubeshi kamar ta tashi ta makureshi.
"Me ka zo yi mana?! Ka zo ka ga ko mutuwa muka yi ka ci gado ne?!!!"
Tana maganar a zuciye, hakan ya karyawa Malam Balarabe zuciya ya hau zubda ruwan hawaye. 
   "Haba Fatima, ban sanki da zuciya ba, kada fushi yasa ki aikata abinda za ki nadamarsa nan gaba."
  Cewar Malam cikin harshen fulatanci. 
  "Nadamar..."
Sai kuma ta kasa magana sai kawai ta fashe da kuka sosai don kuwa ita bata ta6a takawa ta je inda suke ba, hakazalika tun zuwan da ya yi sau daya bayan aurensa ya wuce da Hasiya bai k'ara takowa garesu ba don ko mutuwar Hasiya sai Jar Kwami ta je musu gaisuwa.  Har da wannan zafin ta ke ji na dumbin shekaru har goma sha takwas da aka kwashe ba tare da ta sanya dannata a ido ba. 
    Duk iyakar lalla6awa da ban hakuri da Malam da Malam Balarabe suka bata, babu alamar saukowarta haka suka tattara suka fita inda Malam ya ba wa dansa shawara akan ya yi hakuri har ta huce don a yanzun tana cikin zafi ne. 
   Ko bayan fitarsu, dakin Malam din suka nufa har Haruna don Baffa yaba can kasuwa har lokacin bai dawo ba, nan Malam Balarabe ya yi sallar la'asar sannan ya yi zaman hira da mahaifinsa. Acan suma su Ummi sun samu tarba kwarai daga matan gidan da yan uwansu, daidai da Dada ta ja su jiki musamman Ummi wacce ke tunano mata Hasiya yarinya mai shiga rai da sanin ya kamata don shekaru biyun da ta yi a nan wajensu kafin zuwan mijinta sun saba kwarai da ita. 
   Haruna ya hau ba shi labarin bayan rabuwa, Malam na sauraronsu, anan ne Malam Balarabe ya dubeshi.
"Ni kuwa Malam ya labarin Kanwata Aisha? Har yanzu suna can Adamawan? Yaranta nawa da Yakubun?"
  Shiru ya biyo baya kafin Malam ya yi dauriyar ba shi amsa.
"Sai hakuri Abdullah, Allahn da Ya fimu son Aisha ya kar6i abarsa, yanzun ta shekara da rasuwa."
"Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun!" Cewar Malam Balarabe kafin ya soma kuka har da sheshsheka, kanwarsa ma ciki daya ta rasu ba tare da ya sanyata a idanu ba? Rabonsa da ita tun kafin tafiyarsa Ringim. 
   "Addu'a za mu yi mata, ciwon koda ta ke fama da shi har da abin ya gagara Yakubun suka dawo nan tare da ita don ta yi jinya, saidai takan yawaita tambayarka, har Yakubun yaso zuwa wajenka ya kira mata kai amman Allah baiyi ba, har ta rasu. Yaransu uku, babbar wacce ta ci sunan Hasiya, shekarunta sha shida, tana can Jar Kwami hannun Lamido kakanta, Yusuf da Aminatu kuwa suna can Adamawa hannun mahaifiyar ubannasu. 
   Malam Balarabe ya jima kwarai cikin jimami don kuwa bayan mutuwar Hasiya, wannan ce mutuwa ta biyu da ta girgizashi. Rayuwa kenan. 
   "Allah Ya ji kan Aishatu, Yasa ta huta. Zuwa jibi sai naje Jar Kwami mu gaisa da su."
"Ku tafi gobe, Manu ya jima yana son ganin jikarsa." Cewar Malam kenan, ya amsa da toh.
    Garin ya yiwa Ummi dadi matuka, har hawaye ta yi ganin irin gatanta, ashe daman tana da gata har haka? Kwanon abinci kuwa sai wanda ta za6a ta ke ci, don daga matar Baffa har Halima matar Haruna kowacce saida ta aiko, aka yanka kaji aka soyamusu. Dada sai nan nan take yi da su, acewarta su basu da laifin komai awajenta.......
   
 DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  Wannan naku ne.. 
SallyMoh
Sadia maman ashraf
  AB Kura
  95

Malam Balarabe da Ummi saida suka yi kwanaki uku kafin su bar Ringim zuwa Gombe don kuwa saida aka yi shari'a a babban kotun jaha dake birnin Jigawa a karshe aka yankewa Habiba hukuncin daurin rai da rai. Ita kuwa Saude bayan an tabbatar dagaske ta haukace kai tsaye aka mik'ata asibiti, cikin danginsu babu daya da ya zo banda Malam Yahuza. 
   A motar suna tafe har Mariya saidai ran kowannensu babu dadi suna cike da tunani, shi Malam Balarabe tunaninsa bai wuce na irin kar6ar da danginsa za su yi gareshi ba sakamakon watsi da su da ya yi, yayinda a 6angaren Ummi ta ke tunanin rayuwa ta DAN ADAM mai cike da kalabule, ga jarabta kala-kala. Shi dan Adam kwata-kwata a rayuwa ba shi da wani jin dadi da hutu face na idan ya kyautata mu'amalarsa da Mahaliccinsa, wannan kadai zai tsira da shi har mutuwarsa. Abin sai godiyar Allah, kaga dai duk mutum mutum ne amman a halayya da dabi'u an bambanta, wani sai ka rikeshi da gaskiya ya ci amanarka, wani sai ka dunga yi mishi kallon mak'iyinka, batare da sanin shi din mai sonka domin Allah bane, DAN ADAM ne zai fidda makudan kudade, ya aikata dukkan wani nau'i na sa6on Allah don kawai ya k'untatawa dan uwansa DAN ADAM rayuwa, haka kawai sai ya tsaneshi, ya hana kansa sukuni idan ya ganshi cikin jin dadin rayuwa batare da shi din ya yi mishi laifin komai ba, dan uwa sai ya cuci dan uwansa, ya kasheshi.
  Ta sanya hannu ta share hawayen da suka zubomata tana mai k'ara rungume Mariya wacce ta yi filo da cinyarta tana bacci. 
  'Ya Allah, mu bayinKa ne masu yawan zunubai, Ya Allah ka gafartamana, Ka barmu kan tafarki na gaskiya. Ya Allah ka sa mufi karfin zuk'atanmu. Mun shaida babu abinda bautawa sai Kai, mun yi imani Annabi Muhammad(s.a.w) ManzonKa ne. Allah Ka jik'an wadanda suka rigamu gidan gaskiya.'
Tana maganar a zuciyarta, sannan ta k'ara goge hawayenta, kwantar da kanta ta yi saman kujera ta lumshe idanu tana tunanin rayuwarta har zuwa yau, tamkar rana makamanciyar yau ba zata zo ba, ranar da komai zai zo karshe.
  Haka ta yi ta tunane-tunane har suka iso cikin Gombe bayan sun ci awa kusan biyar akan hanya. Kai tsaye Gombe Motor Park suka shiga sannan kowa ya soma saukowa. 
  Malam Balarabe ya tarar musu taxi.
"Tudun Wada zaka kaimu."
((Pls manage...dare ya yi sai da safe zan dora in sha Allah))
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  Kin cancanta....
Sis Aisha Kalli...Allah Ya bar zumunci duniya da lahira...ameen.

97
  
  Washegari Dada da kanta ta yafa mayafi ta shigar da Ummi makwafta suka yita ganinta tana nunamusu jikarta diyar Hasiya. Ummi har ta rasa inda za ta saka kanta don murna, fararen hakorannan nata sun kasa rufuwa, a karshe suka dawo gida.  Batun Mariya kuwa, Dada har mancewa ta ke yi da ita don dagaske jininta yafi haduwa da diyar Hasiyarta.
   Koda suka dawo anan waje suka tarar da Malam Balarabe da mahaifinsa suna hira. Ta daure fuska tamau kamar bata ta6a dariya ba, ko sannu da zuwan Malam Balarabe bata amsa ba. Ta gaida mijinta ta yi gaba. Haka ya sauke ajiyar zuciya ransa duk ba dadi. Malam ya girgiza kai. 
"Kar ka gajiya, ka cigaba da rok'onta gafara, Fatima mace ce mai hakuri saidai tana da zafi idan an ta6ota, ni nasan tana kaunarka matuka, na sha kamata tana kuka duk akanka, yanzun kuma da ka zo sai ta yi fushi? Karka damu zata sauko."
  Wannan magana ta karfafawa Malam Balarabe gwuiwa, ya saki fuskarsa sosai.
"Ai ni na yi mata laifi, dole na bita a sannu."
  Murmushi kawai Malam ya yi. 
"Ina matarka ne?"
Gaban Malam Balarabe saida ya fadi, cike da damuwa ya labartamishi dukkan abinda ya faru tun bayan mutuwar Hasiya kawowa yanzu da Saude ta haukace da irin tone-tonen da ta yiwa kanta.
  Malam banda ambaton Innalillahi babu abinda ya ke yi, tausayi matuka na Ummi da dannasa ya mamayeshi.
"Yanzu Hasiya saida ta yi aikatau? Allah Mai Yanda Ya so da bayinSa."
  Shima Malam Balarabe da jikinsa ya yi sanyi ya amsa da eh. Kafin ya sanyomishi batun maneman auren Ummin. Da kuma irin taimako da suka yiwa Ummin a rayuwa.
  Malam ya danyi jim sannan ya numfasa.
"To, shi lamari na aure ai na Allah ne, kwarai sunyi mana halaccin da suka cancanci mu dauki diyarmu mu basu. Allah Ya za6amata abinda ya fi alheri."
Malam Balarabe ya amsa da amin.  Haka sukayita hirarsu abin sha'awa.
  
Bayan Magriba suna zaune suna hira a tsakar gida har Dada, Ummi na kwance ta yi matashi da cinyarta ita kuwa tana aikin tsefemata kai tana fadan tabar kai kitso ya tsufa. 
  Ita dai banda murmushi babu abinda ta ke yi, ta lumshe idanunta, gatan kawai ta ke gani tamkar a mafarki. Wayarta ta dauki k'ara, ta bude idanunta da sauri, tun dazu ya ke kiranta a hanya saidai ganin tana cikin mutane ne yasa ta jin kunyar dagawa, ta janyo wayar a sanyaye ta ce.
"Dada tsaya na amsa waya."
Dada ta saki kannata, ta dan dubi Dada, ita din kuwa ta zubawa ido, kawai sai ta mike a guje ta fada daki tana murmushi daidai lokacin da ta ke amsawa da sallama. 
  Wata nannauyar ajiyar zuciya ta ji ya saki wanda ta ji shi har cikin ranta. A sanyaye ya amsa sallamar gami da fad'in.
  "Ki yi hakuri kin ji don Allah."
Ta kasa gane inda maganarsa ta dosa, ta yi hakuri fa? Yaya Faruk ke bata hakuri?
"Hakuri kuma? Akan me?"
"Ba ki ji yanda hankalina ya tashi jin shiru ba ki amsa wayata ba Ummi, har ina niyyar biyo bayanki Gombe."
Ta numfasa sannan ta murmusa, duk a zatonta wani abin ne daban ko kuma cewa zai yi ya fasa aurenta.
  "Kai zan bawa hakuri Yaya Faruk, wallahi muna tare da su Dada ne ni kuma kunyar daukar wayar na ke yi."
  Ya yi murmushi mai sauti.
"Karki damu, ya wuce, saidai dagaske ina jin zan shigo Gombe karshen satinnan, nisan ya na takurani, na soma gajiya da rashin ganinki."
Ta kasa cewa komai sai murmushi, a haka Dada ta shigo daukar damammiyar furarta a kwanon sha ta ganta, duk sai ta diririce, Dada murmushi kawai ta yi ta fice.
"Kin yi shiru, dagaske za ki iya ganina."
  "Ba ka kunyar su Daddy?"
Ta fada cikin sanyin muryarta. Ya dan yi dariya. 
   "Haba Ummi, Daddy fa ki ka ce? Kar ki damu, sunsan irin kaunar da nake miki wacce sai na daure matuka na ke iya 6oyonsa, bansan wace irin addua ki ke min na har kullum kaunarki ke k'aruwa cikin raina."
Ta girgiza kai tana dan dariya kawai. 
Sun dan jima suna hira sannan suka yi sallama.
  Koda suka kammala sai ta kasa fita ta yi zamanta a dakin ta kwanta saman gadon karfen Dada tana game. Can jimawa kadan Dada ta shigo tana fadin.
"Wai 'yarnan ba ki gama wa..." Ganin da ta yi mata kwance tana wasa da waya yasa ta rike ha6a.
"Au, tsifar kenan? Shi ne ki ka yi kwanciyarki anan? To kin kyauta ai daman dare ya yi nima hannuna ya gaji, taso ki sha fura ga farfesu can Abida ta aikomiki."
   Ta mike tana mai kokarin rufe kanta da dankwali don sam bata mance tsifar ake mata ba, kawai nauyinsu ne ya hanata fita. 
   "Allah Yasa ba sukari sosai a ciki irin na dazu."
   Dada ta murmusa.
"Kema bakya son sukari sosai? Allah Ya jik'an Boddo, itama haka ta ke ko kadan bata son sukari. Komai naku dai daya."
  Jin haka yasa Ummi zamowa daga gadon bayan ta amsa da amin.
"Ni kuwa Dada wai da wa Ummana ta yi kama tsakanin kakana da kakata."
   Jin haka yasa Dada zama gefenta gami da dubanta fuska a sake.
  "Mahaifiyarki ta dauko kamannin Kakanki Usmanu Lamido, wanda suke kama sosai shi da yan uwansa, musamman babbar yayarsu Bintu dake aure garin Adamawa da yaranta uku, danta namiji guda ne Allah Ya azurta mata shi, a hannunta Karamar uwarki (Zahra) wacce suke kira da Inno ta girma, ana shirin aurenta ta rasu.  Idan da zaki ganta itama marigayiya Zahra, sai ki rantse mahaifiyarki ce don kamannin da kuma jini.
  Ta jinjina kai kafin ta k'ara da fadin.
"Wai akwai yan uwanmu ne a Adamawan nan sosai? Naga har kanwar Baba itama can aka ce ta yi aure har ta rasu."
"Dangantaka mai karfi kuwa da Adamawa, duk kuwa da asalinmu Kwami da Jar Kwami, saidai mazajenmu da iyayenmu sun yi tafiye-tafiye, wasu suka yada zango Adamawa har suka tara iyali. Ba acan ne shi Lamido Shuaibun ya auro mahaifiyar Yakubu mijin marigayiya Aishatu kafin kuma su rabu ta koma can, a hannunta Yakubun ya girma ai wani zuwansa nan ya ga Inna Boddo a Jar Kwami ya nuna yana so, sai mutuwa ta rabasu."
Ummi zata k'ara magana saidai bata samu dama ba, don Dada mikewa ta yi.
  "Kinga, tashi mu je ki sha fura sai mu zo ki ban mijinnawa a waya mu gaisa don na lura sai kumbiya-kumbiya ki ke kada ya ji muryata ya fasa da ke."
Jin haka Ummi ta yi dariya tana rufe fuskarta, Dada ta fice itama tana yar dariyar.
   Washegari....
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
   
   DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

98

Washegari misalin takwas bayan sun gama karyawa suka yi shirin tafiya, kamar kullum, yau ma  Malam Balarabe ya shigo har dakin Dada don gaisheta, saidai ko kallo bai isheta ba, Ummi tana duban mahaifinta cike da tausayi har ya gaji ya kara da fadin.
"Za mu wuce." Uffan ba ta ce ba sai ma mikewa da ta yi ta fita, ya dan bita da kallo jiki a sanyaye kafin ya dubi Ummi.
"Idan kun gama sai ku fito, bari na je nan makwafta wata gaisuwa na dawo."
Ta amsa da to, bayan fitarsa ta ja bakin mayafinta mai adon jajayen fulawa ta rufa akan riga da siket din dake jikinta na wani fari da jan yadi, ta ci kwalliya don ta fi so suna ganinta cikin lumana koda suna fushi da mahaifinta su huce. Idan ka ga Ummi ba zaka ce itace ba, ta yi kyau kwarai hakanan ta ciko a kwana ukun da sukayi kacal, babu damuwa babu mai tsangwamarta ko kuma jifanta da kallon banza balle uwa uba gorin gida. Shigowar Dada ne ya katse tunaninta, ta rataye bakar jakarta.
"Kaga 'yata ta fito."
Ta dan tamke fuska don har zuciyarta bata jin dadin abinda Dada ke yiwa mahaifinta. Ganin haka yasa Dada ta rude.
"Ke meyafaru? Ko wani abin ya ce miki?" 
Ummi ta dan karyar da wuya sa'ilin da ta ke zura takalmi kamar bata so ta ce.
"Don Allah Dada ki daina yiwa Babana haka ba dadi, don girman Allah ki yafemishi. Ya yi muku laifi saidai shima ba laifinsa ba ne, da kanta Saude ta tona dukkan mugun ayyukan da ta yi ciki har da.."
Zata fadi na kashe Ummanta da ta yi sai kuma ta yi shiru don batasan zafin da zata kara dauka ba.
  "Bari ki ji kadan daga abinda ya faru."
Ta soma koro mata bayani a gajarce, da kadan cikin zaman da suka yi da Saude bayan mutuwar Hasiya da aikatau da ta yi da irin karamcin mutanen da suka dauketa aikin har zuwa komawarta Ringim da yanda abubuwa suka kasance har da haukacewar Saude da kai Habiba gidan yari. Ta dubeta.
"Naso 6oyemiki cewa kashe Ummana sukayi saidai naga kamar ba amfani. Komai da ya faru babu laifin Baba, idan hakane nima zan iya yin fushi ai tunda babu wani cikin yan uwan Ummana da ya nemeni, amma na yi hakuri da na fahimci ba ku da laifi kusan laifin na Saude ne tunda Baba ba cikin hayyacinsa ya ke ba. Ko don wannan don Allah ki yafemasa."
  Dada ta dan daure fuska.
"Jeki suna jiranki, Allah Ya saukeku lafiya, ki gaidamin Inna Boddo."
  Ummi ta dan yi murmushi a sanyaye kafin ta amsa da toh sannan ta juya ta fita. Dada ta bita da kallo, kafin bayan fitarta ta zauna da6as a saman gado. Kawai sai ta soma shar6ar kuka tana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Ashe haka lamuran suka afku? Ko jiya Malam ya yi niyyar fadamata saidai bata ba shi dama ba asalima tashi ta yi ta bar wajen. Ta tausayawa dannata ainun amman daman wanda bai ji bari ba zai ji hoho, illar rashin jin maganar iyaye kenan, sai gashinan ya janyowa kansa bala'i. 
  "Allah Ya jikanki Boddona, Allah Ya yi miki rahma." Ta fada a hankali. 
    Acan kuwa su Ummi suka gama sallama da kowa suka kama hanyar Jar Kwami har Haruna wanda shi ya yi musu rakiya.
    Bayan sun isa kai tsaye gidan Lamido Shu'aibu yaya awajen Manu kakan Ummi. 
  Ummi ta dubi gidan, gidan gargajiya, saidai babba ne, suka shiga ciki. Anan kofar gidan k'asan 'yar rumfa, Lamido Shu'aibu ne kishingide saman wata darduma akan tabarma, ga wasu dattijai su biyar zaune gefensa ana hira, saidai ganinsu ne yasa su maida hankali garesu. Ummi ta lura da mutum uku masu kamanni farare ne saidai tsufa ya dakusar da haskensu. Malam Balarabe da Haruna ne suka karasa suka durkusa wajensu, yayinda Ummi da Mariya suka durkusawa a gefe suma. Bayan an gaisa, Lamido Shuaibu  cikin harshen fulatanci ya ke tambayar ko su waye. 
  Shima ya ba shi amsa da fillancin ai tuni waje ya karade da murna, Malam Balarabe ya karasa suna dafashi baki a washe, wani har da goge kwallar farin ciki. Tsoho Mai ran karfe Usmanu Lamido ya dubi Malam Balarabe da harshen fulatanci ya ce.
"Ashe da rabon na kara sanyaka a ido kafin na mutu Abdullahi?"
  Kunya ta bi ta cika Malam Balarabe ya hau bada hakuri yana nuna ba laifinsa bane. Ya waiwaya ga su Ummi. 
"Ku karaso nan." Suka taho, Ummi ta durkusa ta gaishesu, suka zubamata idanu. 
"Wannan itace diyar wajen Hasiya, itama Hasiyar sunanta, Ummi."
   Suka yi kabbara.
"Ai ko baka fada ba na ga kamanni, matso gareni Boddo." Cewar Dattijo Usmanu. Ummi ta matsa gareshi tana jin hawayen farin ciki na kokarin zubomata. Ya rungumeta ya fashe da kuka, itama kasa jurewa ta yi ta sanya kukan, bawan Allah jikinsa har rawa ya ke yi. Saida aka basu baki sannan ya yi shiru. Ya dagota yana shafa fuskarta kamar Boddonsa. 
   Ta karasa ga Lamido Shuaibu shima ya dafa kanta yana murmushi mai bayyana hakora, duk girma ya kamashi dakyar ya ke gane mutane. 
"Allah Ya yi miki albarka. Ya ji kan Mammarki."
  Ta amsa da amin. Bayan duk an gama gaisawa sukayi cikin gidan inda tuni labari ya je musu ga diyar Hasina ta zo daga burrni. (Lol).
   Nan aka zubawa Ummi ido ana kallonta baki sake, wasu dakyar suke samun karfin gwuiwar gaishe da su sakamakon ganin tsantsar kamanninta da mutan gidan. Kai tsaye Haruna ya nufi da su 6angaren Inna Boddo wacce tuni labari ya iso gareta saidai babu mai kaita ta ganota. Inna Boddo wacce ko tashi bata iya yi saida wanda sakamakon ciwon kafa da ta ke fama da shi, tana zaune a tsakar gida cikin rumfa saman gadonta na karfe don koyaushe nan ne wajen zamanta saidai yaran gidan su zo nan tayata hira. 
  Shigowarsu ce ta katse tunaninta, ta zubamusu ido, tana hada ido da Ummi ta zaro ido.
"Boddona!" Sai kuma ta soma kuka tana mikamata hannu, a guje Ummi ta karasa ga kakarta don ta gane wacece daga sunan da ta ambata, suka rungume juna. Fuskar kowannensu cike da farinciki. 
  Bayan an gaggaisa, ta ke tambayar Malam Balarabe sadda ya dawo, a kunyace ya bata amsa ya kara da neman gafara. Ta yi kamar bata ji ba don kuwa kokusa bata da rikeshi ba. Mariya dai an zama yan kallo sai rarraba idanu kamar shege a rabon gado. 
   Ranar Ummi dai ra rasa inda zata sanya kanta don dadi, haka ta wuni cikin yan uwa, dangi sai zuwa akeyi rututu ganinta. Wasu sunfi danganta kamanni da yanayinta da Inno Zahra data rasu saidai ita tana da yawan barkwanci da dariya, wasu kuwa sun fi karkata ga Hasiya. 
  Ranar fura da nono har saida ta ture, ga cima kala-kala da aka kawo musu. Mariya tana samun yaran abokan wasa shikenan kuma ta saki jiki har ta fice tare da su. 
  Ranar Ummi ta mance dukkan wasu bakkan cikinta. Kwanan Malam Balarabe biyu suka juya tare da Dan uwansa da kuma Mariya wacce itama ya ke son kaita ganin dangin mahaifinta wadanda bata sani ba, ba kuma yaso nan gaba azo baya raye ta tambaya ba wanda ya sani. 
   Ummi ta zama 'yar lele, kullum cikin hira, idan ta jima wajen Inna Boddo, nan kakanta zai nemeta, nan ma ba jimawa sauran matan musamman uwa ga Inno da Binta, Danejo itama zata shiga nemanta, don tunda ta ga Ummi ta ji kamar Innonta ce ta dawo. Rayuwa kenan, bayan wuya sai dadi idan har mutum zai jure ya yi hakuri da dukkan lamura, Allahu Ya bamu ikon juriya da hakuri ba don isarmu ba, Amin.
    Ranar talata da misalin biyar na yamma, Ummi da wata yar uwarta Abu wacce itama jika ce a gidan suna tafe a hanyarsu ta zuwa gona kaiwa baban Abun abinci. Ummi na sanye da doguwar riga bulu mai adon fulawoyi bakake, ta tufke gashinta wanda tun tsifar da Dada ta yi mata bata yi kitso ba, fuskarta fayau, ta yafa mayafi akanta bata ko daura dankwali aciki ba, sai gashin ya yi tudu a tsakiya kadan, tana wasa da karar dake a hannunta. Suka tsinci muryar yayan Abu, Gidado yana kwalamusu kira ta bayansu. Tsayawa sukayi gami da juyawa, gaban Ummi ya yi wani mugun faduwa ganin wanda ke tare da Gidado. Murmushi tattausa ya ke jifanta da shi da kallon dama na fadamiki...
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  99

Kasa kwakkwarar motsi Ummi ta yi, ya hade cikin farin yadi wanda ake ganin farar singiletinsa ya dora bak'ar hula hakanan takalminsa bak'i ne. Ya yi kyau kwarai duk ya chanjamata. Abu  ke tambayar Gidado abinda ya faru. Daidai lokacin da suka karaso wajensu ya kasa dauke idanunsa daga Ummi. 
  "Bak'o ki ka yi, tare da Mai sunan Baffa(Usman kanin Malam Balarabe) ya zo, bayan an gaisa kuma ya ce bazai jira ku dawo ba na yi mishi rakiya." Duk wannan dogon bayanin da Gidado ke yi gareta ita gaba daya jikinta ya yi sanyi, Yaya Faruk? Ina ya baro aikinnasa? Yanzu babu kunya ya cewa su Daddy zai zo wajenta? Wayyo, wannan abu akwai kunya. Saida ta ji Abu ta gaisheshi da hausa ne ya amsamata da fulatanci har Abu na dariyar mamaki, itama ta dawo hankalinta, ta tuna ashe fa shima bafulatanin ne. 
  Ta durkusa ta gaisheshi da girmamawa kamar yanda ta saba. Ya amsa, Gidado ya dubesu.
"To, za ku juya ne ko mu
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment