Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[26/09/2021, 00:43] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️


*ANYA BAIWA CE?*

Na

*AMEERA ADAM*


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._


FREE PAGE 1



Tafe take tana ɗan waige dan gudun kar wani ya ganta ko taci karo da wani a hanya, saboda abin da ta gano take san zuwa ta isar da shi ko ta samu ɗan alheri, aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu, kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayinta yasan tabbas akwai abinda ke ƙunshe cikin bakin ta, aɗan diriri ce ta kalle shi ta ce.

"Yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai yayi dare"

Kallanta yayi sai da yayi murmushin gefen baki yana ƙara karantar yanayin ta sannan ya ce, " Tauraruwa mai wutsiya..., Kura kike ga tsoro ga ban tsoro. Ina zaki kike sauri kina ta juye-juye haka? " Sai da ta juya hagu da dama ta kuma leƙa soron ƙarshe tana mai miƙa wuya cikin ƙasa da murya ta ce, " Gobara daga teku maganin ta sai Allah, wata ƙura ce take ƙoƙarin kunno kai a cikin gidan nan amma karka ce kaji daga baki na " ta ƙarasa magana tana kuma duba gabanta da bayanta.

"Jakadiya Kubura kenan, ay harbi ga ɗan jaki gado ne, kuma iya ruwa fidda kai gayamun ina sauraron ki kowa ya biya allon sa ya wanke " ya faɗa cikin son jin labarin.

Sunkuyowa tayi dabda shi sannan ta ce, " Kasan koda girgiza kurna tafi magarya, mai tsoron a mutu shi yake maho " Ƙara gyara tsayuwarta tayi sannan ta ce, " Ƙaramar kyauta tafi babbar rowa " ta ƙarasa faɗa tana miƙa masa hannu alamar ya bata wani abu.

Ya gano abinda Jakadiya ta ke nufi, dan haka ya sa hannu cikin aljihu ya ɗebo mata silallah ya zuba mata akan hannun ta yana faɗin, " Ke dai ciki kike mai manta kyautar jiya, kuma Kura kike mai manta alherin baya"

Juya su tayi cikin jindaɗi ta kunto bakin zaninta ta ɗauresu tana faɗin, " Domin rana ɗaya ba'a ƙin zuguri, kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, buɗe kunnen ka yanzu zaka sha labari, ashe Fulani Zaliha ciki gareta har ya girma, kasanta da shegen nunkufurci ba ta cika bada fuska a shiga sashenta ba " zaro idanu yayi waje shima yana waigen bayansa sannan ya ce, " Lallai tsugunne bata ƙare ba ansai da kare an sayi Mage, naji daɗin wannan albishir naki jeki anjima zan neme ki " ya faɗa yana yin gaba abinsa.

Jakadiya Kubura ta fahimci sarai inda maganar Galadima ta dosa har yaje bakin ƙofa ta ce masa, " Injunan ka sammako wani tafe ya kwana, kuma hargagin ɗan damisa bashi tsorata Namijin zaki, ka taka a sannu kasan Fulani Maryama ba kanwar lasa ba ce " kamar bazai bata amsa ba sai kuma ya juyo ya ce mata, " Tabbas inkaji mutum na tsoron dare ba'a ɗaure shi ya ƙwance bane, Ki bar ganin allura ƙarama itama ƙarfe ce, dan haka bazan ce miki komai ba mu zuba mu gani kowa tasa ta fishsheshi " yana gama faɗa ya sanya kai ya fice daga cikin soron.

Bin bayansa tayi da mugun kallo sannan ta ce, " Mai ƙafa huɗu ma ya faɗi bare mai biyu, ajuri zuwa rafi wata ran tulin zai fashe " tana faɗa ta juya ta cigaba da tafiya, kai tsaye sashen Fulani Maryama ta nufa.

Tana shiga ta zube ƙasa cikin salon kirari ta fara magana, " Barka da hutawa Uwargida na bango madafar bayi, uwar marayu uwar mara gata mai iyayenma kin gamai musu komai, Ƴar sarki jikar sarki Matar Sarki kuma gaki Uwar Sarki, Allah ya ƙara girma ya raya mana Yarima mai jiran gado, Mulki da Sarautar Masarautar Kano gaba ɗaya ta ku ce, Mai Uwa agindin murhu bazai ci miyarsa lami ba... " murmushi Fulani Maryama tayi saboda jin daɗin kirarin da Jakadiya tayi shiyasa ma ta katse ta da faɗin, " Jakadiya anjima zan turo da saƙon maɗi mai ke tafe da ke?? " russunar da kai Jakadiya tayi tana mai sauya yanayin fuskarta cikin damuwa ta ce, " Tuba nake Uwar gijiyata banzo dan isar da mugun labarin nan dan wata manufa ba sai dan ki tashi tsaye ki ɗau mataki kuma asan abin yi, Kaicona da tuntuni ban ankare ba har lamarin ya girmama, amma dukda haka ba za'a rasa abinyi ba dan ba'a rasa nono a riga, ina mai neman gafarar ki saboda labarin bamai daɗi bane ranki shi daɗe "

Tunda Jakadiya ta fara magana Fulani Maryama gabanta ya yanke ya faɗi saboda tasan labarin bazai mata daɗi ba, shiyasa a hargitse ta wurgo mata tambaya, " Jakadiya banasan Kewaye-kewaye tafi kanki tsaye, Me yake faruwa ne?"

Jakadiya kara sauya muryarta tayi ta ce, " Ina neman gafararki da jin kalamai na dama Fulani Zaliha ce ke da juna biyu, kuma ayanayin dana lura har yayi ƙwari..." cikin tsananin tashin hankali Fulani Maryama ta ƙunduma wani ashar sannan ta ce, " Aikin me kike tun tuni baki sanar dani ba tunda wuri? "

Jakadiya ta bata amsa da, " A gafarce ni Uwargijiya ta kinsan Yarinyar da nunk..."

Katseta Fulani tayi cikin tsawa ta na faɗin, " Ya isa haka, Lallai Fulani Zaliha ta ɗebo ruwan dafa kanta, Samun sararin kuturu gaɗa a cikin rama, wato haka ta miƙe ƙafa da yawa? Lallai abinda ya faru a shekarun baya dole ya ƙara faruwa yanzu, tabbatas dole labari ya ƙara maimaita kansa, Aikuwa kowa yaci tuwo dani miya yasha, tashi kije Jakadiya anjima zan neme ki bayan Sallar Isha'i "

Jakadiya najin haka ta kuma rissinawa ta ce, " ALLAH ya huci zuciyar Fulani, Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare yayi hankali, tabbas bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane wace ce Fulani Zaliha da zata iya haɗa sahu da Uwar ɗakina, ni mai bin Umarnin ki ce akowanne lokaci " Jakadiya na gama faɗa ta tashi ta fice zuciyarta fess saboda tasan ba ƙaramin alheri zata samu ba.

Tunda Jakadiya ta fito daga ɗakin, Fulani Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da komawa take, abun duniya gabaɗaya ya isheta, ita kaɗai sai saƙa da warwara ta ke tana san nemarwa kanta mafita, Jaririnta ɗan kimanin wata biyar da ke kwance ta je tasa hannu ta ɗauke shi tana juya shi cikin zuciyarta da shawarar da ta yankewa kanta.

A fili ta fara surutai kamar wata zautacciya, " Yarima yanzu kai ake shirin yiwa kishiya a gidan nan, tabbas bazata yuwu ba tunda ban bari wata ta haifi namiji ba dole na dakatar da cikin Zaliha "

Jakadiya tunda ta fito daga sashen Fulani Maryama kai tsaye sashen su ta wuce tana zumuɗin sauraron kiran da Fulani Maryama ta ce zata yi mata, kamar wacce a ka mintsina tashi tayi ta fito daga sashen bayi wani gida ta faɗa bakin ta ɗauke da sallama, " Balaraba matar Ciroma dake tankaɗe ta amsa mata sallamar tana faɗin.

" Yau kuma Jakadiya ce da doshin magariba haka?? " Kujera Jakadiya ta janyo ta zauna sannan ta ce, " Eh ko bakya maraba da zuwan nawa ne?? " cigaba da tankaɗenta tayi ta bawa Jakadiya amsa, " Ni na isa nace banten Sarki yayi ɓurtu, ai hanyar lafiya abita da shekara, meye labari?? Dan nasan bakin ki baya rasa motsi?? "

Murmushi Jakadiya tayi ta ce, " Ai dama ni kujera ce dole a zauna dani, kuma abokin cin mushe ba'a ɓoye masa wuƙa, wai kuwa kinsan Fulani Zaliha na ɗauke da juna biyu?? Wa ya sani ma itama ko Namijin zata haifo ni zanso ma ta haifo Namijin naga yanda Fulani Maryama zatayi " ta faɗa tana ƙasa-ƙasa da murya.

Da sauri Balaraba ta saki rariyar Hannunta waigawa bakin ƙofa tayi sannan ta cewa Jakadiya, " Da gaske kike wannan maganar?? aikuwa muddin zancen nan yaje gun Fulani Maryama kinsan bazai mata daɗi ba, kuma kinsan dole wani abu ya biyo baya"

Jakadiya ƙara matse bakin zanin ta tayi ta ce, " Ai a bakin wawa akanji magana, wai da kunne yaji muguwar magana wuya ya tsere, kinsan dai ai ciki badan tuwo akayi shi ba, bayan ke babu wanda yasan da wannan maganar "

Tsuke fuska Balaraba tayi da alama bataji daɗin maganar Jakadiya ba dan haka ta maida mata da martani, " Tafasar tukunya bata gefe ɗaya bace, haka nan abinda baki ya ƙulla hannu bashi iya kunce shi, idan kinji makaho ya ce ayi wasan dutse to tabbaci haƙiƙa ya taka dutse, Jakadiya koma dai mene ne daga bakinki wannan maganar ta fito kuma ni nan da kika gani na iya taku na"

Miƙewa tsaye Jakadiya tayi tana gyara ɗaurin zaninta ta fara takawa har sai da taje wajen bakin ƙofa sannan ta juyo ta ce, " Mutum fari ne shi ke rina kansa ya zama baƙi, bakinki dai ƙanin ƙafarki kuma harshenki linzaminki " bata saurari mai Balaraba zata ce ba ta fice daga gidan.


_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[26/09/2021, 01:58] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️


*ANYA BAIWA CE?*

Na

*AMEERA ADAM*


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._


FREE PAGE 2



Da daddare Bayan sallar Isha'i Jakadiya ce tafe tana lalube har ta ƙarasa sashen Fulani Maryama, da sallama ta shiga ta russuna tana cewa, " Barka da hutawa Uwar ɗakina ance kina san ganina yanzun nan "

Fulani Maryama dake tsaye hannunta ɗauke da Salman miƙawa Jakadiya shi tayi ta ce, " Jakadiya inasan muyi tafiyar sirri kamar yanda muka saba da ke a shekarun baya, ayau basai gobe ba zamu kai ziyara ga Boka Marduska, saboda bazan iya kwana da maganar da kika sanar da ni ba, batare na nemi mafita ba "
Riƙe Salman Jakadiya tayi tsam kamar wani zai ƙwace shi sannan ta ce, " Duk abinda kika ce haka za'ayi, bani da ikon bijirewa umarninki, da kai da kaya duk mallakar wuya ne "

Fulani Maryama na gama jin haka ta juya ta shiga cikin ɗakinta, cen ƙasan adakarta ta buɗe ta ɗauko wani kurtu tasa hannu ta ɗebo waɗansu irin wuri guda biyu da wani ɗan ƙaramin zobe, maida kurtun tayi sannan ta dawo gurin da tabar Jakadiya ke tsaye.

Miƙawa Jakadiya Wuri ɗaya tayi sannan ta fara karanta waɗansu irin ɗalasiman tsafi, ba'a ɗauki lokaci ba sai wani haske ya mamaye gurun atake suka ɓace daga cikin ɗakin.

Tsaye suke abakin wani kogon dutsen dake cikin wani surƙuƙin daji mai matuƙar duhun gaske, Fulani Maryama runtse idanunta tayi ta fara ƙwalawa bokan kira har sau uku, " Marduska! Marduska!! Marduska!!! " tana gama faɗa ta buɗe idanunta.

Ji sukayi ankece da wata mahaukaciyar dariya sai da aka ɗan ɗauki lokaci anayi sannan aka tsagaita, sannu a hankali haske ya mamaye gurin, cikin wata irin murya aka fara basu umarni, " Ku sanya ƙafafunku cikin waccen ƴar ƙoramar sannan ku tako ku shigo ciki.

Kamar yanda aka gaya musu haka suka bi umarnin mai magana sannan suka shiga cikin kogon dutsen, daga cen nesa suka hango shi zaune akan buzun damisa, gaba ɗaya jikinsa lulluɓe yake da gashi tamkar ba bil Adam ba, Fulani Maryama na gaba Jakadiya na biye da ita a baya.

Zama sukayi sannan Fulani ta kalli bokan zata fara magana ya ɗaga mata hannu sannan ya kuma kecewa da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana,

" Ai duk wanda ya bamu iska dole kwaɓarsa tai ruwa, Maryama kin ɗauke mana ƙafa na wasu shekaru sai da buƙatarki ta tashi zaki waiwayo mu "

Fulani Maryama ta russunar da kai ta ce, " A gafarceni sarkin bokayen duniya, nayi kuskure awancen lokacin amma yanxu baza'a sake ba "

" Na amshi tubanki kuma nasan abinda yake tafe dake, kalli nan " ya janyo wata ƙwarya mai cike da jini yana nunawa fulani.

Tana leƙawa Fulani Zaliha ta gani kwance akan gadon ta tana baccinta hankali kwance, jinjina kanta tayi ta cewa Murduska, " Ya babban boka sarkin bokayen duniya so nake a salwantar da cikin da ke jikinta inda hali ma akashe su gaba ɗaya, domin bayan Salman bana san kowacce matar sarki ta sake haihuwa acikin su saboda bansan gaba mai zasu haifo ba kuma bansan mai hakan zata haifar ba "

Ƙwala-ƙwalan idanunsa ya kafe ta dasu yana ce, " Daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi, badan kinzo ayanxu ba da tuni sauran damar data rage miki ta ƙare gaba ɗaya " A zabure Fulani Maryama ta ce, " Ban fahimce ka ba Marduska "


Wani mudubin tsafinsa ya ɗauko yasa wata jelar ɓauna dake hannun sa na hagu cikin ƙwaryar ya yarfawa mudubin, inuwar wani ɗan ƙanƙanin Yaro ce ta bayyana na ɗan wani lokaci sannan ta ɓace, maida mudubin yayi gefe sannan ya maida kallonsa ga Fulani Maryama ya ce, " Alƙalami ya riga da ya bushe, duk duniya babu wani ko wata da zai iya dakatar da cikin jikinta har sai ta haifeshi, Zata haifo Ɗa namiji Mai kama sak da Mahaifinsa kuma koda baki ci wannan Alwashin ba haihuwa ta dakatawa Sarki Aminullah, duk wacce kika ga ta kuma haihuwa sai dai in wani ne mahaifinsa ba Aminullah ba "

Cikin damuwa Fulani Maryama ta ce, " Yanxu babu wata mafita da zaka bani ya Shugaba na?? "

Wani Allon jar ƙasa ya ɗauko ya jingine ya na faɗan waɗansu irin kalmomi, yana watsa wani tafasashen jini dake cikin wani ƙoƙon kan Ƙwarangwal, yana cikin haka baiyi aune ba sai gani sukayi Allon jar ƙasa ya ruguje wani irin hayaƙi mai wari na fita daga jikinsa.

A tsorace gaba ɗaya suka ja baya Marduska ba ƙaramin tsorata yayi da ganin faruwar haka, cikin yanayin firgici ya fara magana, " Tabbas Ruhin wasu ababen hallita na katange da shi, idan na matsanta halaka shi ba mu ba hatta Aljanun da suke taya ni aiki sai sun halaka, maganin kar ayi kar afara inba haka ba wanda baiji bari ba yaji woho "

Fulani Maryama jikinta ne ya gama sanyi amma duk da haka zuciyarta bata karaya ba ta ce, " Marduska abar batun Halaka shi tunda ni kaina ganau ce ba jiyau ba, amma bayan haihuwar sa ba damar a aiwatar da wani aiki akansa ko a nakasa shi? "

Matsawa yayi bakin wutar dake ci ya ɗebo wani garin magani mai haɗe da garin naman mage da haƙoran jemage ya zuba aciki, take wutar ta kuma tashi sama sannan wata ƴar ƙaramar ƙorama ta bayyana aciki, daga cikin ƙoramar wasu litafan tsafinsa ya ɗebo guda biyu ja da baƙi, baƙin ya fara jefawa cikin wannan jinin dake cikin ƙwarya sannan ya zura kansa yana karewa Ƙwaryar kallo dake ta zaɓalɓala.

Sai da ya gama kallo tsaf sannan ya ɗago da kansa da yayi gumi sharkaf ya fara mata bayani, " Tabbas cikin biyun za'a iya gudanar da ɗaya amma biyun bazasu iya wanzuwa akanshi ba, zamu iya nakashi ta kowacce siga haka nan zaki iya sawa a fitar dashi daga cikin masaurautar, amma shi ne kuskuren da zaki fara tafkawa a rayuwar ki, domin kuwa ta wannan silar dukkan asiran da kika binne za'a binciko domin kuwa allura ce zata tono garma"

Fulani Maryama harta fara jin daɗi ƙarshen maganarsa ya sa ta shiga damuwa, kallansa tayi cikin rashin fahimta ta ce, " Bangane mai kake nufi ba? " mayar da ƙwaryar yayi cen gefe ya ce, " Abinda na gani kenan zaɓi ya ragewa mai shiga rijiya..., kowanne zaɓi kika ɗauka yana da nashi ƙalubalen da zaki fuskanta ki nutsu da kyau ki saurare ni inba haka ba zakiyi gudun gara ki faɗa gidan zago "

Jakadiya dake gefe tayi tsuru sai raba idanu ta ke cikin zuciyar ta ta ke faɗin, " Lallai Fulani Maryama kema ba ƙaramar makira ba ce, amma ajuri zuwa rafi..., Ay bahaushe ya ce inzaka gina ramin mugunta gina shi gajere, amma lallai wannan Ɗa na Zaliha ya zama kainuwa dashen Allah, wata ƙila shi ne zai zama magajin mulki muga ta tsiya, dama ance kayun Ɗan ƙwarai ya gaji Ubansa "

" Ina sauraren kowacce kalma da zata fito daga bakinka kuma kowacce zan saka ta amazaunin da ta da ce " Fulani Maryama ta faɗa.

Miƙe ƙafafunsa yayi da gaba ɗaya gashi ya rufe su sannan ya fara mata bayani, " Zabi na farko zamu iya baki garin maganin da za'a zuba masa a ruwan wanka ina nufin wankansa na farko a duniya kuma ko yaya ne asamu a bashi wannaa maganin ya sha, sai kuma na turare wanda ita Zaliha tana fara Naƙuda zaki turara mata, karki bari yaro ya faɗo ba tare da kin turara shi ba, to idan kika yi haka bazai iya gani da idanunsa ba, har tafiya da magana ke komai da kika sani sai dai ayi masa, saboda zai kasance a kwance sai dai duk abinda za'a furta zai ji shi babu abinda zai iya wanzarwa "

Murmushin jin daɗi Fulani Maryama tayi ganin haka yasa boka ya ce mata, " Sai dai akwai sharaɗin da zaki kiyaye, akwai ruhin wata da na gani tana jingine da shi, zata shigo cikin gidan masarautar ku tana ƙasƙantacciya muddin kika bari ta shigo cikin gidan sarautar, abubuwa marasa daɗi zasu fara faruwa gareki kuma duk ranar da tayi tozali da shi suka haɗa ido, a ranar aljanun dake riƙe da ƙafafunsa zasu tarwatse alƙadarinsu zai karye, idan kika yi sake ta ɗau wani abun ci ko abin sha ta bashi da hannunta to a ranar suma aljanun da ke riƙe da bakinsa zasu gushe zai fara magana, sai dai aranar zai fara wani irin ciwo kamar zai mutu zai yi ta amai ba ƙyaƙyƙyautawa kamar zai amayar da ƴan hanjinsa, hakan zai ɗaga hankalin Mai martaba har yasa anemo wanda ya bashi wani abu tunda shi zaiyi tunanin guba ce aka bashi, amma ba haka bane amayar da gubar da take jikinsa yake ta tsawon shekaru "



_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉
[26/09/2021, 02:13] Ameera Adam🌚: *FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️


*ANYA BAIWA CE?*

Na

*AMEERA ADAM*


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._


FREE PAGE 3


Ajiyar

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

1 Comments On ANYA BAIWA CE
avatar
kabiru-6

1 year ago

Reply

Uhmm

Please Login or Register in order to submit comment