Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

 ____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK 2_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]




Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31


Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
Shaida tanan
+227 97 21 16 15

______________****_______________





Page 🖤1••2🖤



Tafiyah suke Jabeer yana binsu a baya bataresa saninsu ba har suka kai gida.
Kallon ƙofar ya tsaya yi yana nazarin tsarin gidan daga cikin motar.
Wai dama akwai irin waɗannan gidajen a garin abuja?? Kodaga nesa mutum zai gane yanayin rashi da ma'abota gidan suke dashi.
Katangar gidan duk ta zube ta wani wajen saboda rashin ƙarfinta,kuma ya haɗu da yawan ruwan sama dayake kwaranyah a kanta na tsawon lokaci.
Kofar gidan babu wani ishashshen makari,wani langa langane a gefe,da alama dashi ake amfani wajen kare gidan da daddare.
A taiƙacedai gidan na masu ƙaramin ƙarfine sosai.
Numfasawa Jabeer yayi bayan ya gama kallon gidan,inda ba biyota yayi ba yaga tashiga gidan,bazai taba cewa daga nan ta fito ba.
Abinda yafi bashi mamaki shine yanda taƙi karbar taimakonsa,bayan kuma tana rayuwa a gida irin haka.
Fitowa yayi daga cikin motar ya nufi gidan,waigawa yake domin samun wanda zai aikata cikin gidan,idonsa ne ya sauƙa kan wani yaro yana riƙe da kwanon a hannunsa,fuskarsa dama dama da miyar tuwo,da alama tunna jiyane,dan tuwon bayyi kamada wanda aka dafashi sannan ba.
Cikin ɗauke kai daga kallon fuskar yaron ya fara magana.
"Uhm mutumina nace zona aikeka mana,shin nanne gidan su Jaleelah koh?"
"Eh nanne gidan su ina anty hafeezah koh?"
"Eh inaga itace,shiga kace ina sallama da mahaifinta idan yana nan"
"Nawa zaka bani to idan na ƙiramaka shi?"
Mamakin maganar yaron Jabeer yayi,yanzu wannan yaron har yakai bazayyi abuba sai an biyashi?
"Karka damu shiga ka kiramin shi tukunna"
Hanyar gidan yaron ya nufah,bayan wani ɗan lokaci sai gashi sun fito tareda wani farin dattijo mai kamala da dattaku.
Gaisawa sukayi cikin mutunta juna,maganar yaronce ta katsesu da cewa wani abu bayan sun gaisa ɗin.
"Malam baka bani kuɗin ba toh"
Kafin Jabeer yayi magana Dattijon yace.
"Wanne kuɗin za'a baka,har yanzu baku bar wannan ɗabi'a ba koh,ohhh wai yaro baisan a sakashi abu ba sai an bashi kuɗi? Wuce ka tafi gida"
Da sauri yaron ya wuce yana zumbura baki,sai bayan ya tafi tukunna Dattijon ya dawo da kallonsa kan Jabeer.
"Yaro baka faɗamin mai yake tafe dakai ba har yanzu"
"Ehh dama yarinyar gidan na buge da mota a can kan titi,nayi mata magana mutafi asibiti a duba taƙi amincewa,shine nazo naji shin lafiya dai koh?"
"Jaleelah kenan kake nufi,dan itace ta dawo daga makaranta ɗazu,data shigo kuma batace komai ba,babu wanda yasan mai yafaru"
Kasa boye mamakin sa yayi jin wai batace komai ba a gida,kulada hakan da dattijon yayi ne yasashi cewa.
"Yaro karfa ka damu,haka take dama ta saba,kuma tunda har bata nuna ba inaga ba wani abin damuwa bane sosai,kayi tafiyar ka zanje na dubata inna shiga gidan,mungode sosai da kulawarka Allah ya tsare gaba"
Kuɗi Jabeer yafitar ko ƙirgawa bayyi ba ya miƙawa mutumin,tun kafin ya kaishi kusada shi ya ture hannunsa tareda cewa.
"A'ah karma ka ɗorawa kanka nauyi akan wannan,kayi tafiyar ka babu komai kaji yaro"
Daga haka ya shige gida yabar Jabeer a tsaye,dama ana samun irin waɗannan mutanen har yanzu,basuda shi amma kuma sunada wadatar zuci?
Kallon sama yayi ganin rana tayi shirin faɗuwa,gari yafara duhu,yasan zuwa yanzu wataƙila Hajiya zeenah sun dawo.
Wani idan su Hajiya zeenah sun dawo yanzu,toh fah lubna zataji labarin auren da aka ɗaura masa,kuma yasan da gangan Hajiya zeenah zatayi abinda zata san da ɗaurin auren.
Wai yazayyi kenan bai faɗamata ba saidai taji a wani wajen,yasan tashin hankalin dazai tarar ba kaɗan bane.
Saurin dafe kansa yayi,zuwa ɗazu daga haɗuwa da waccar yarinyar har ya manta da damuwar dayake ciki,ya shanye lokacinsa a nan wajen.
Hanyar inda ya ajiye motarsa ya nufah da sauri,yana bata wuta kuwa yanufi gida,a ransa yana addu'ar Allah yasa Hajiya zeenah basu dawo ba tukunna.
Tun kafin ya isa sashen Hajiya zeenah ya hango mutane a wajen,wanda hakan yabashi tabbacin ta dawo kenan.
"Tafaru ta ƙare...."
Yafaɗa cikin kasalalliyar muryah,fita yayi a motar ya nufi sashennata,yasan dole amryar da akayi masan tana sashinta yanzu,tunda baici ace an gama gyara ainihin sashennasa zuwa yanzu.To ma shi baiga wani dalilin komawa wannan sashen ba,kawai dai rigimar Hajiya ce.
Da Maleekah ya haɗu a falon ta ɗauko faranti a hannunta zata shiga ɗakin Hajiyan.
"Ke zo na tambayeki"
Cikeda tsoro da kalleshi,fuskarnan a tamm da ita babu alamar fara'ah.
"Yaushe Mommah ta dawo,tana ina kuma?"
"Uhm batafi minti talatin da isowa bama,tana daƙinta itada amaryar"
"Amarya,kowa yasan da zancen amaryar kenan?"
"Eh mommah tana shigowa ta tara dukkan ma'aikata ta shaida musu cewar kayi sabon Aure yau,kuma dama tana nemanka idan ka dawo"
Dafe kansa yayi ta gefen dama,jin ɗanyen aikin da mahaifiyar tasa ta aikata masa a karo na babu adadi,ko shakka babu yasan da gangan tayi hakan saboda lubna ta sani.
Bai sake kallon inda Maleekah take ba ya wuce ɗakin Hajiya zeenah,itama binsa tayi a baya,dan dama can zata nufah.
A can ƙasan maƙogaronsa yayi salllama kansa yana kallon ƙasa,kana ganin haka kasan yana cikin yanayi marar daɗi.
A ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ya zauna,yaga alamar wata farar mata a zaune gefen Hajiya zeenah suna magana,amma ko kallonta bayyi ba,dan yasan itace matar da aka aura masan.
"Ahh Jabeer kaida nace ka kira su Madeenah ka shaida musu zuwana sai yanxu ka shigo"
"Nasamu wani ɗan ƙaramin hatsari ne a hanya"
"Ohh to Allah ya tsare na gaba,shin an gyara sashennaka ne ko kuwa har yanzu"
"An gyara saidai bansan ko sun gama ba,amma naga wancan ɗinma danake ciki akwai parta empty a ciki"
"Nasan da haka,akwai dalilin daya saka na zabi wancan ɗinne,kuma nasan kaima kasan dalilin. Yanzu dai ba wannan ba,mun taho da baƙi,wannan itace........"
"Please dan Allah mommah kibar wannan bayanin,inkin faɗama ba ganewa zanyi ba,inade part ne,za'a gyara taje da zauna kaman yanda kike buƙata,daga nan kuma fah saime takeda buƙata"
Cikeda bacin rai da ƙosawa yayi maganar,shuru Hajiya zeenah tayi,dan ita kanta tasan takai ɗannata bango,amma shima bazai gane bane,kullum cikin fargaba take da matarsa,gani take da dai da rana dayah idan ta zauna tayi shuru lubna zata cutar mata da ɗa.
"To naji,dare yafara nasan ka gaji,kaje ka huta sannan ka sanarwa matarka cewar yanzu ba ita kaɗai bace,karta sakankance kamar da"
Har yakai bakin ƙofa yasake juyowa ya kalli Hajiya zeenah.
"Amma mommah shin indai yanda kuke faɗan haka take,bakya ganin cewar itama wannan bazata........"
"Kaga ya isa haka kaje saida safe,sannan karka sa damuwar wannan auren cikin ranka,yanada dalilinsa daban wanda bai shafeka ba"
Akwai tambayoyi a cikin kansa kala kala,amma yasan koda yayi su bata lokacinsa kawai zayyi,dan haka yabarsu a zuciyarsa kawai ya fitah.
Jan numfashi Hajiya zeenah tayi bayan ya tafi,maida kallonta tayi kan Hilyaan wacce take zaune hankalin ta kwance akan kujera tana kallon abinda yake faruwa.
"Kiyi haƙuri fah nasan munyi tafiyah kun gaji,shi abokin tafiyar taki ankai shi masauƙin baƙi,ke kuma zaki iya kwana a ɗakin Madeenah,ko kuma a baki ɗaki daban"
"Ahah karki damu Hajiya,duk inda kika bani ma ya wadatar,na kwana ukune ai kawai kafin Anty maryam tazo,sannan ma ba zama mukazo yi ba ai,zamu fita kasuwa ne da khamis gobe"
"Medame kuke buƙata haka,babu ba abinda zaku siyah na kayan gida,gyaran daza'ayiwa part ɗin komai za'a saka shi"
"Eh dama ba wai kayan normal na gidaba,akwai abinda take buƙatar a saka na ra'ayinta ne,......
Uhm wannan shine Angon Antyn?"
Hilyaan tafaɗa,badan komai ba saidan ta kawar da zancen da ake a lokacin.
"Eh fah shine,amma bawani buƙatar ta sanshi ai ko ya santa,kafin tazo zanyimasa bayanin ainihin dalilin auren,karku damu da wannan"
Hmmm ba laifi kyakykyawane kam sosai,kaman yanda itama take mai kyau,ina gujemiki aikinki yajuye ba yanda kike so ba. A fili kuma tace
"Ahh babu wani abin damuwa sosai,naga shima bayada interesting akan auren,ko kallon inda nake bayyi ba,yayi zaton inaga nice amaryar"
Hilyaan tafaɗa ɗauke da ɗan ƙaramin murmushi akan fuskarta.
Kayan marmarin da Maleekah ta kawo ta ajiye tafara ci. Dan ita iyani mai aikace aikacen sashen a gajiye take saboda bidirin da suka sha.
"Hmmm da alama wannnan yarinyar da Hajiya ta auramin batada kunya ko kaɗan,wato tafi ƙarfin gaisheda mutane ma,oh kodayake hakan ma yafiye mata,dan wahala zata sha idan tayi ƙoƙarin shiga rayuwata"
Yana cikin zancen zuci bai sani ba yanayinsa a fili,har ya isa sashen Lubnah.
Bai sameta a falo ba,dan haka ya nufi ɗakinta,a tsaye take tana kallon window da Ƙaramin wando a jikinta,rigar ma iyah rabin cikinta,indai ba sannan tasaka kayan ba yasan dasu tayi yawon a falo babu abinda ya dameta.
Sallama yayi a bakin ƙofar,duk da a hankali yayi yasan tajishi sarai,shurun datayi kaman gunki bata amsa ba ya tabbatar masa da labari ya isa ga kunnenta kenan na auren.
Ajiyar zuciya yasake,zuciyarsa tana tsalle a cikin ƙirjinsa,shikansa yasan tsoron ta dayake bana lafiya bane,saidai babu yanda zayyi da hakan.
"Luban!!!"
Ya ƙira sunanta cikin sanyayyiyar muryah.
Bata amsa ba sannan bata juyo ta kalleshi,shikansa yasan bai isa misalta abinda yake cikin zuciyarta ba a yanzu.
Takawa ya farayi a hankali zuwa inda take tsaye a jikin windown,duk da shareshin datayi baiji daɗiba,amma yasan rabin abinda ya faru larfinsa ne dana mahaifiyar sa,ko mace mai sanyin rai ba kowace zata yarda da irin auren da akayi masa ba,miji bai sanar dakai zayyi aure ba,saidai kawai kaji a bakin masu aiki. Mai yafi haka ciwo,musamman idan aka danganta da zafin kishi irinnata?.
Hannunsa ya saƙala ta ƙasan tumbinta,duk da bawani mai yawa bane amma zaka jishi,saboda ƴar ƙibar datake da itah.
Kansa ya kwantar a kafaɗarta,sunkai kusan minti biyar amma har sannnan yagagara cewa komai .
"Dagaskene kayi aure yau"
"Kinga ba......."
"Kawai tambaya nayi,shin dagaskene yau an daura maka aure ko ahah?"
"Eh da gaskene,amma ba yanda kike tu......."
Buge hannun Jabeer tayi daga jikinta tareda fuskantarsa cikin bacin rai.
"Bana son jin komai bayan gaskiyar danaji,duk ƙoƙarina a koyaushe baka gani sai kayi ta kawomin mata cikin gidana koh,bayan kasan babu abinda na tsana kaman na buɗi ido naga wata halitta wai ita mace a gefen mijina"
"Oh gosh wai lubna yaushe zaki daina irin wannan abinne,eh aure da gaskene an ɗauramin aure yau,amma ki tsaya kiji ni nawa bayanin mana,Nifah banine naje dakaina nayi aurennan ba,Mommah ce ta yimin aurennan ki fuskanta mana"
"Wacce fuskantar zanyi,koma wanene yayi maka auren aidai kai akayi wa,mijina akayiwa ni akayiwa kishiyah,ni wannan kawai nasani ba wai wanda yayi aurenba,akan me akayi shi nasan bazai wuce ace dan ka samu ɗa ba,koba dan haka bane. Ko kace baka santa kaman yanda kayi sauran,kana ganin ta samu ciki shikenan saidai na ganka kana lailayata kaman ka samu ƙwai,koba haka bane?"
"Kaiiii lubna bafah haka bane"
"To idan ba haka bane,yanzunnan kaje ka bata takardarta basai gobeba,shine zan yarda dakai toh nasan babu hannunka a ciki"
"Mee naje na bata takardarta,yakikeso kenan na fuskanci Mommah idan na aikata hakan"
"Ni wannan bai dameni ba,kaita shafah"
"Dan kinsamu ina lallabaki shine kika faɗamin abinda kika ga dama koh,ni bazan iya aikata abinda kike so a yanzu ba,idan har abinda na faɗamiki baki yarda ba shikenan"
"Haka ma zakace aikuwa gidanmu zan tafi bazan zauna ba,inka fitarta daga cikin gidannan saikaje kayi min bayani"
"Fine ga kofa nan,dama konayimiki shamaki da ita bakya daina tsallakata,yanzu ma kuma ƙofarki a buɗe take ki tafi,sanda kika ga dama saiki dawo,dama ba yau kika fara ba ai"
"Zan tafi amma karka damu dakanka zakaxo kana rokona kafin na dawo,itakuma matarka ka faɗamata tashirya dawowa ta bazai mata daɗi ba,saita fuskanci abinda bata taba ganiba a faɗin rayuwarta"
Tana gama faɗin hakan tafara tattara kayanta cikin zuciya,tsayawa yayi yana kallonta,dan shi yanzu ta daina bashi ma mamaki.
Jin ana shirin shiga sallah ne yasashi faɗawa banɗakin dakinnata domin yin alwala.
Lokacin daya fito bata nan itada akwatinta,jan ajiyar zuciya yayi kafin yace.
"Jeki na samu na huta naji da wani abun kafin ki dawo"
A zaune take ta dafe kai tana kallon Haidar yanata yimata kuka,tun yamma take fama dashi yaƙi shan nono kuma yaƙi yin bacci,gashi ta duba jikinsa babu zazzabi.
Sakashi tayi a gaba tana kallonsa har wuntsilawa yake yana shiɗewa saboda kuka.
Ƙarar wayarta ne yasaka ta dauke kanta daga kansa ta mayar kan wayar.
Sunan Hilyaan ne ya bayyana akan screen din,hakanne yasa takai hannunta ta ɗauka a kasalance.
"Hello Hilyaan yaya kun isa koh"
"Eh mun isa anty,yanzunnan ma aka kawoni dakin dazan zauna kafin ki taho"
"Toh ya gidan tsarinsa yayi yanda nakeso,kunga inda zan zauna a gidan"
"Ehh komai yayi sosai,gobe zamuje da khamis muyi order duk abinda kike so a saka...ɗazu naga Mijinnaki gaskiya ya haɗu sosai,saidai da alama fah shima yana ji dakansa,daya shigo wajen mahaifiyar sa ko kallona bayyi ba,yayi zaton nice amaryar"
"Kinga niba damuwa ta ji da kansa ba,inyana so ma yaji da cikinsa ba kansa ba,bai dameni ba danshi zanje garinba daga shi har uwartasa,to ya matar tasa taji labarin auren ko kuwa"
"Eh kaman taji,dan muna zuwa Hajiya zeenah tasaka a shaida mata mun dawo,kaman yadda ta faɗa dagaske bata son ta kam"
"Wannan kuma tsakaninsu,nidai bazan yadda su yimin abinda banaso ba kaff gidan,ita kanta matar tasa ba yanzu zanyi maganinta ba sainazo tafiyah a ƙarshe tukunna,abinda yake raina shizan fara"
"To shikenan Allah yabaki sa'a,yadai naji Haidar sai kuka yake lafiya"
"Hmmm ai Hilyaan kina ƙoƙari sosai da yaronnan,wlh iya yau duk narasa yadda zanyi dashi,ko fita zuwa training na gagara zuwa fah yau,gashi khmis ma bayanan,waɗancan direbobin sai signarsu nake gani a cikin jeji"
"Hhhhhh gwanda ki saba ai,karki manta fah ke uwace, yakamata ki saba da ɗawainiyar danki"
Hilyaan ta karisa maganar cikin dariya.
"Zanyi wanda nayi,in yagaji ai zayyi shuru,gobe zan shiga cikin gari wajen mutanen gidan can,ki tabbatar fah ki tafiyar da komai yanda ya kamata"
"Karki damu anty zamuyi miki yanda angonki yakeso,ni ina ganin ma kina ganinsa ki faɗa soyayyar sa"
Zaro ido tayi jin maganar takaicin da Hilyaan take yi mata,tun kafin tayi magana taji ta ƙatse ƙiran ƙitt,da alama dama tsokanarta tayi.
Duba wayar tayi taga ƙiran ya katse,cije baki tayi tareda cewa.
"Lallai kinga gadon baccina dayawa,na faɗa soyayyar sa,wannan maganar kuwa zata barni nayi bacci yau?"
Bombee tafaɗa cikin cije baki tana dunƙule hannu.
Da safe data tashi har mai aiki tayiwa haidar wanka ta dafa abinci. Wanka ta shiga,bata daɗeba tafito tana tsane ruwan dayake jikinta.
Riga da wando tasaka kaman na pakistan baƙaƙe,da alama irin shigar yana burgeta,kuma yana daukar jikinta dakuma dirinta ba kaɗan ba.
Zama tayi tashi abinci sosai,dan ma yanzu tarage yawan jin yunwar datake kwanaki..
Ɗaure dogon gashinta mai walwali tayi da ribbon,kafin ta yane kanta da mayafin kayan.
Wani baƙin glass ƙato ta toshe dashi a fuskarta. Kallon madubin dake gabanta tayi na dan wasu mintuna,itada kanta tasakawa kanta dariyah ganin shigar datayi.
Belt ta ɗauka na goyon gaba ta ɗaura,kana tasaka haidar a ciki,wanda yake ta daga ƙafa akan gado,shima yasha baƙaƙen kaya masu tsada.
Baƙar motarta tashiga tayi mata key,bayan ta bata wuta yanda ya kamata ta ƙujeta sai cikin gari.
"To mutanen gida dana gari harda maƙwanta,ganinan zuwa muku bankwana kafin na tafi........"
Ta faɗa cikin sautin dariyah mai ɗauke da nishaɗi.
Kaman kullum inna laari ce kawai a tsakar gidan sai innayi tana tayata Gyara ganyen shayi,suna cikin taɗinsu na uwa da ƴa sai ganin Bombee sukayi a kansu carr ta saƙala hannunta na hagun a jikin igiyar belt din abin goyon,dayan hannun kuma tana kakkaɗa key din hannunta,dan jijjiga take da alama tana lallaba ɗanta wanda yake ɗaure a kan ƙirjinsa,hankalinsa kwance bamu mai iya tabashi saidai abinda ido baya iya gani.
"Sannunku iyalan Mlm Ahmadu,nagaban goshinsa abin alfaharinsa,ga baƙuwa tashigo gaisheku"
A tare suka sauke idonsu a kanta,tambayar su daya mai takeyi a wajennan bayan an ɗaura aurenta jiyah.
"Mamakin ganina kuke koh,to ban tafiba bare kusaka ruwa a kasa kusha dan daɗi,uwata nazo gani shin zan samu ganin ta ko ahah banida ikon hakan"
Cikin izzah ta alamar babu wasa take maganar.
Innayi ce ta tashi tareda kallon Bombee tana murmushi.
"Ahh Addah Bombee kawoshi"
Yar dariya Bombee tayi tareda cewa.
"Haka aka koyamiki ki faɗa kuma yanzu,kiyin sakin fuska nabaki ɗana shima ku kasheshi a tsaye koh?"
"Kee wai menene Burinki ne haka,kishigo gida babu sallama babu komai ki hau yiwa mutane tujara,bada sa'nninki ba komai ba,na miki shamaki da cikin gidannan amma kin ƙiji,ki faɗamana mai kikeso ne wai a wajenmu,duk abinda kikayi ta jawo mana a gari na tsawon shekaru bai isheki ba ne"
"Bai isheni ba laari,sai ranar danaci ribar abinda nake,sannan kuma kowa ya tone abinda ya shuka kafin zai saurara,banyi komai bama tukunna,ina jiran lokacin dayafi daidai ne,yanzu gargaɗi kawai nake aikawa kafin sakamakon ya iso.
Bombee zata bar garin gembu amma ba wai ta tafi bane shikenan,kai tsaye zata dawo tasake bayyana,domin akwai aikin data bari bata ida kammalashi,aikin dazanyi a can shine akan layi hakan shikaɗaine sa'arki,kafin sannan ki gama shiri iyah shirin dakike bukata"
Duk wannan maganganun a daidai fuskar laari take faɗansu tana kallonta ido cikin ido.
Wani kallon inna laari tayi mata mai cikeda yarinya baki san komai ba,yayinda itama tayi mata kallon kin sake wuyana yayi kauri yafi ƙarfin yanka.
Muryar mlm Ahmadu sukaji yana cewa.
"Mai kuma wannan halittar takeyimin a gida,duk yanda na kai da ƙin korarki saida kika tilastani na aikata hakan,yanxu kuma mai kike min a gida"
Maimakon Bombee taji haushin abinda ya faɗa,saima murmushi da ta zabga mai armashi da nishaɗi.
Toh mu hadu a page na gaba......


_*SADI-SAKHNA CEH*_




____****🖤🖤****_____


🖤 *BAƘAR AYAH* 🖤


🖤 _BOOK 2_ 🖤



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _Ƴar mutan Jama'are_ ]




Anshiga Sashen na Kuɗi,in kasan baka biya ba karka karantamin littafi,Ka ɗau hakkina bisa kanka tamm!!!

Makarantan Arewabook ku danna zai kaiku cikin littafin

https://arewabooks.com/book?id=62d939a19904b02ce6fa2b31


Masu karatu ta whatsapp kuwa,zaku biyah Naira 300 kacal ne.

3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Shaida tanan
09035784150

Masu saka katin wayah zaku turo katin 300 na MTN tanan layin..
09035784150
No VTU

Mutanen niger kuma zaku biyah kuɗinku tanan
300f
Shaida tanan
+227 97 21 16 15

______________****_______________





Page 🖤3••4🖤




"Karka damu baba dama bakwana kawai nazoyi,hankalin ka zai kwanta sosai,domin a kallah kusan Shekara guda ban juyo ba"
"Hmmm wannan auren ma kenan niyyar kasheshi kikayi koh"
"Ahah baba dama ba aurene irin kowanne ba,na yarjejeniyane akwai ranar mutuwar sa"
"Kai Addah Bombee ko shiyasa wannan matar tazo nemanki ran....."
Kafin tagama magana inna laari ta buge bakinta tareda zabga mata harara.
"Kaga malm ba wannan ba,tazo ta fice daga gidannan,bankwanan ya ishemu haka,kada ta shafa mana tsiyar datake tattareda ita"
Runtse ido Bombee tayi jin abinda inna laari ta faɗa,saidai maimakon hakan yasaka shiga yanayi na baƙin ciki ko kuma karya lagonta,saima tunzurata daya sakeyi,bude shiɗayen idanunta tayi akan inna laari tareda cewa.
"Ke na gama yimiki bankwananki,amma bangamawa wacce tayimin shamaki da ɗaiɗaita birbishinki ba wato innata,dan haka inaga ko kinfi kuturu naci baki isa hanani shiga na ganta ba,kokai kin ƙarisata bansani ba?...... Inaaa bakida wannan ƙarfin gwiwar tukunna,har yanzu dai ina matsayin ƙadangariyar data zauna a miki akan tulunki"
Hanyar dakin innarta tanufa,wacce take zaune kaman koyaushe akan kujera tanajin abinda Bombee takeyi,saidai batada ikon kallonta ko kuma maida mata magana.
A gabanta ta tsugunna tareda daukar hannunta tariƙe akan nata.
"Inna ni zan tafi,amma zan dawo ko domin ke,dan bawai natafi kenan ba,duk yadda zanyi sainayi wajen ganin nagano mai yake damunki,wannan shine kaɗai burina daban cikaba a wannan garin"
Jijjiga kai Danejo tayi da sauri,tareda matse hannun Bombee cikin nata,ma'ana karta dawo kenan kaman yanda take ikirari.
"Ahah inna zan dawo,ko badan aure bama saidan idan lokacinsa ya ƙare,domin ba aurene dama na zama ba,kedai kijira dawowata inna,kafin na tafi zan tabbatar bata isa yimiki komai ba har na dawo,ni banyadda da wannan matar ba sam inna,mutanene ke ganinta ta arziki,amma jikina yana faɗamin sai an bincika garinnan kaf kafin a samu ya ita wajen shu'umanci,tana da baƙin ruhi a tattareda ita,wanda inajinsa idan mutum yana aiki da aljanu,ko kuma akwai shihiri a jikinsa"
Itadai inna Danejo duk abinda Bombee take faɗa tana jinta,amma batada ikon maida mata magana,har tagama sambatunta a cewarta bankwana takeyiwa innar tata.
Saida ta gama kafin ta tashi tafito daga ɗakin,lokacin data fito mlm Ahmadu bayanan ya fita,kokuma ya shiga ɗakinsa. Harara inna laari tasake mata itama ta rama,hadda nunawa da hannunta inta dawo zata yanke mata kai.
Inna laari tana ganin Bombee tafita a gidan tasaki wata ajiyar zuciya.
"Lallai tsugunne bata ƙareba,da sauran rina a kaba"
Ajiye wankin datake tayi tareda tashi tsaye,lelleƙawa tayi ta tabbatar babu kowa a kusada ita kafin tashige ɗakinta da sauri.
Gadonta na ƙarfe ta ɗaga tareda ɗakko wata baƙar tukunyah dakuma wani ƙaton madubi,wanda yayi mutum a tsaye tsayinsa.
Jinginashi tayi a jikin katangar ɗakin,kana ta buɗe jan ƙyallen da aka rufe bakin tukunyar dashi.
Wasu kalmomi tafara karantawa cikin wani yare mai kamada da dalasumai,kafin wani lokaci kuwa tukunyar tafara tafasa shuuuuu wani abu yana fita daga cikinta kaman baƙin hayaƙi.
Shiga madubin dayake gabanta yafarayi,wanda kana gani kasan ba madubine na Allah da annabi ba,domin koda mutum ya tsayah a gabansa baya bada hoto kaman sauran madubai.
Wata mata ce tafara bayyana a jikin madubin,tana ɗauke da jajayen kaya masu kamada na saƙi,ƙyaƙyƙyawace da kana gani kasan ba kyaune na Zahiri ba,sannan fuskarta tana ɗauke da kalar mugunta sosai,wanda baƙin kwallin datayi ado dashi ma yaƙarawa siffartata fitowa da ainihin mungun kallonta bayyana a fili.
Kallon inna laari take wacce take tsugunne a gaban madubin tayi sujjada tamkar taga kashi.
"Meyasa zakiyi ƙirana a yanzu ina tsaka dayin wani aiki?"
"Eh ranki yadaɗe shugabar matsafa ZILIYYAH nabar kowa nabiki ke kaɗai,dama wannan yarinyar ne da kikayi aiki a kanta tsawon lokaci,ta fitine ni kullum barazana takemin idan muka haɗu,wannan dalilinne yasa na saka Mijina korarta,to wani lokacin har a mafarki take zuwamin"
"Hhhhhh laari tun ba'aje ko ina ba harkinyi nadamar
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

3 Comments On BAƘAR AYAH BOOK 2
avatar
ummi-ummi

5 months ago

Reply

My Allah bless you

avatar
taskar

5 months ago

Reply

Replying to ummi-ummi

Ameen

avatar
ummi-ummi

5 months ago

Reply

Ayya next of chapter 4 pls

Please Login or Register in order to submit comment