Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dauketa tana karaji da kururuwar
neman taimako har ta daina hangensu saboda nisa da
suka yi da wajen, sannan matsafi Bahalu ya turo wani farin hayaki daga bakinsa ya bugi fuskarta, nan take
Idanunta suka daina ganin komai, barci mai nauyi ya
dauketa, ta fita daga hayyacinta daga nan ba ta sake sanin
abinda yake faruwa a gareta ba.
Matsafi Bahalu ya ci gaba da tafiya da ita cikin
alkaluman sihirin rage nisan tafiya, sai da ya shafe
tsawon kwanaki goma yana tafiya ba tare da yada zango ya
huta ba sannan ya isa lardin Ashtar inda wannan fada ta
Darul Sabar take, ya wuce cikin fadar dake tsakanin
wasu manyan tsaunuka guda biyu a tsakiyar daji
Fadace da aka ginata da kananan duwatsu abin
yiwa ado da jauhari, an zagayeta da manyan katangu
masu matukar girma da tsayi tare da kariya ta alkaluman
sihiri da babu wani mahaluki da ya isa shiga cikinta
matukar ba da izinin wanda ya mallaketa ba. Akwai
itatuwa da furanni masu matukar kyau da suka kayata
wajen tamkar lambu, ga rafuka da koramu masu
gudanawa a tsakiyar wajen kana zuwa inda fadar take za
ka tabbatar da cewa ka zo wata kasaitacciyar fada, irin ta
manyan sarakuna da suka shahara a fagen tarin dukiya da
karfin iko.
A cikin fadar akwai hadimai mata kyawawa wanda
dukkaninsu an daukosu ne daga hannun iyayensu aka
kawo su wannan fada aka ajiyesu don yin hidima ga
wanda ya mallaketa, kuma da yawansu 'ya'yan sarakuna
ne da manyan attajirai, sai dai daga cikinsu babu wadda
matsafi Bahalu yake ganin ta dace ya zauna da ita a
matsayin matarsa ban da Gimbiya Hasima, don haka
dukkanin matan da ya tarar an tara a fadar suna zaman
kuyangi ne don yin hidima a gare ta.
Matsafi Bahalu yana shiga cikin fadar ya wuce da
Gimbiya Hasima wani daki mafi kyawun ado daga cikinya'yana da nake fatan su gajeni a fagen tsafi da sihiri, za
ki kasance a karkashin ikona kuma mai yin biyayya a
gareni har karshen rayuwar ki."
Hasima ta ce da shi "Allah ya yi mini tsari da
dukkanin sharri da mugun nufinka a kaina, ya kuma
kubutar da ni daga wannan hali don shi mai karfin iko da
isa ne Cikin buwayarsa akan kowane tasirin tsafi da sihiri
da kake dagawa da shi, kuma kiyayata na tare da kai har
Karshen rayuwata ba zan taba kaunarka ba, bare na yi
biyayya a gareka."
Bahalu ya sake bushewa da dariya sannan ya ce da
ita "Ai lamarina ya yi nisa a gareki daga fita daga
wannan fada, kuma bakin alkalami ya riga ya bushe
tunda har na riga na kawoki cikinta, ki sani cewa babu
wani mahaluki da ya isa shigowa wannan lardi komai
jarumta da sadaukantakarsa bare ya kubutar da ke daga
hannuna." Ya tafi jikin wata karamar kofa dake saman
dakin ya budeta sararin samaniya ya bayyana, a lokacin
dare ne kuma babu hasken farin wata sai tsananin duhu
sannan akwai wasu taurari masu matukar haske guda
biyu daga daidai kofar da ya bude, ya dubi Gimbiya
Hasima ya ci gaba da cewa.
"Ki yi duba ya zuwa wadannan taurari guda biyu
dake sararin samaniya, sune taurarin da na dade ina jiran
bayyanarsu, don samun nasarar daukoki daga birninku na
kawoki wannan fada, kuma da suka bayyana na samu
nasarar aikata hakan. Saboda haka ki ci gaba da duba ya
Zuwa wannan taurari tsawon kowane dare, a duk sanda ki
ka ga taurarin sun taho sun hade da juna sun zama daya,
to wannan rana ce da take bayyana kasancewarki matata
da tabbatar aure a tsakaninmu, kamar yadda bayyanar
taurarin ta tabbatar da samun nasarar daukoki daga birnin ku.
Ya sake bushewa da dariya irin ta mugunta da
zalunci kamar yadda ya saba sannan ya juya ya fice daga
dakin ya bar ta.
Gimbiya Hasima ta sake fashewa da kuka saboda
bakin ciki da takaicin halin da matsafi Bahalu ya sanya
rayuwarta a ciki, ta dade tana wannan kuka don
tausayawa kanta har kusan asubahi, sannan ta hakura ta
mika lamarinta ga Ubangiji, ta duba hannunta ta ga
zoben nan na Zuhairu yana tare da ita ba ta jefar da shi
ba, ta daukeshi ta saka a dan yatsanta ta sumbaci zoben
kuka
don
sannan ta daga hannunta sama ta yi addu'a don neman
Allah ya kubutar da ita daga hannun wannan shu'umin
matsafi da ya daukota daga birninsu ya rabota da 'yan
uwanta ya kawota wannan waje.
Shi kuwa Zuhairu cikin kwanaki biyar ya gama
shirinsa na tafiya lardin Ashtar don 'yanto Gimbiya Hasima
daga hannun matsafi Bahalu tare da neman makarin aikin
sihirin da Bahalu ya yi masa ya maida siffarsa irin ta tsoho
mai tarin shekaru.
A ranar da Zuhairu zai tafi ya fito cikin shiri na
sulken yaki, ya yiwa dokinsa damara da shiri na sosai, haka
itama Buniyatu an bata doki tare da sauran kayan yaki daga
fadar Sarki Shaiban, ta gama nata shirin cikin sulken yaki ta
fito idan ka ganta za ka yi zaton wani hamshakin jarumi ne
sadauki da ya shahara a fagen fama ba mace ba ce ba, kafin
su tafi suka yi bankwana da dattijo Marwan kakan Zuhairu
ya yi musu addu'a ta tatan samun nasara sannan suka yi
sallama suka kama hanyar birnin Bahazum.
Da isar su Birnin suka wuce fadar Sarki Shaiban, suka
tarar da an shirya wasu manyan jarumai cikin shirin yaki,
su kimanın mutum arba'in da zasu yi musu rakiya cikin



BAKAR GUGUWA
littafi na biyu 2
Na Shehu Usman Muhd
typing by Shuraih Usman
post by Shuraih 99%
Part C
.
.
tafiyar da za su yi, Zuhairu ya sauka daga kan dokinsa ya
tafi gaban Sarki ya kai gaisuwa, sarki ya amsa masa sannan
ya ce da shi "Allah ya baka nasara na gama shiri dan yin
tafiya bisa ga alkawarin da na dauka, na neman Gimbiya
Hasima duk inda take a fadin duniya."
Sarki Shaiban ya ce da shi "Na shirya wasu jarumai
da zasu yi maka rakiya adadin mutum arba'in, daga cikinsu
akwai mutum goma kwararru a fagen iya harbi da kibiya,
sannan akwai wasu mutum goma da suka kware a fagen iya
fada da mashi, sai kuma mutum goma masu iya jifa da
majaujawa, sauran mutum goma na karshe sune kwararru a
fagen iya fada da takobi, wadannan sune adadin mutumn
arba'in da zasu yi maka rakiya, don haka za ku tafi tare dasu
su taimaka maka, ni kuma zan sanya malamai su ci gaba da
addu'a Allah ya baku nasara cikin tafiyar da za ku yi."
Zuhairu ya yi godiya sannan Sarki Shaiban ya sa aka
yi musu addu'a ta fatan samun nasara ya kuma umarci
baradan da zasu yiwa Zuhairu rakiya su kasance masu yi
masa biyayya a matsayin shugabansu har su je su dawo,
daga nan suka yi sallama da sarki, aka yi musu rakiya zuwa
bayan gari suka kama hanya suka ci gaba da tafiya.
Buniyatu tana gaba don yi musu jagora zuwa bigiren da
suke zaune tare da yayanta matsafí Bahalu, don dauko
rubutaccen sako wanda zai shiryar da su hanyar da za ta
kaisu lardin Ashtar inda fadar da matsafi Bahalu ya tafi da
Gimbiya Hasima take.
Kwanci tashi suna tafiya a cikin wannan daji tun daga
ranar da suka baro gida, har suka shafe kwanaki ashirin
daga cikin kwanaki arba'in da za su yi kafin su isa bigiren
da Buniyatu suke zaune a cikinsa, sukan yi tafiya daga
bayan ketowar alfijir har zuwa faduwar rana sallah da cin
abinci ne kawai yake 'tsayar da su sai dare ya yi su yada
zango don su kwana kafin gari ya waye su ci gaba da tafiya.
A rana ta ashirin da daya daga cikin ranakun tafiyarsu da La'asar sakaliya, suna tsakiyar tafiya sai suka hangi wasu
rundunar mahaya cikin shirin yaki, suna dauke da tutoci na mabiya addinin bautar rana, su Zuhairu suka yi nufin
Su ratse musu su ci gaba da tafiya, don kada baradan su
tsayar da su su bata musu lokaci cikin tafiyar da suke yi,
amma sai wadannan ayarin baradan suka hangesu suka sha
kansu suka tsayar da su, daya daga cikin baradan wanda
kuma shi ne babbansu ya dubi su Zuhairu ya ce da su.
"Kai wadannan matafiya daga ina ku ke kuma ku
jama'ar wane birnine da inda ku ka nufa? Sannan ina
labarin dukiya da guzirin da ku ke tare da shi. Ku yi
gaggawar mikoshi garemu don a yanzu kun zama ribatattu
a garemu ababen tafiya da ku ya zuwa birninmu don kaiwa
sarkinmu ku zama bayi, kamar yadda mukan yi ga duk
jama'ar da muka hadu da su a wannan daji cikin tafiyar da
muke yi."
Zuhairu ya ce da shi "Ba ma tare da wata dukiya ko
guziri da zamu baku bisa ga bukatarku, cewa dai mu mun
kasance matafiya ne cikin wata bukata da take tare damu,
kuma bamu fito dan yin fada da kowa ba sai don tunkarar
abin da muka sa a gaba saboda haka muna neman afuwa a
gareku, ku bamu hanya mu wuce ya zuwa inda muka nufa."
Wanda ya fara magana ya dubi Zuhairu ya ce da shi
"Kai dattijo ma'abocin rauni da gazawa ka sani cewa ba
zaku kubuta daga hannunmu ba har sai kun zama ribatattu a
garemu, don na ga alama kun kasance daga cikin mabiya
addinin Musulunci ba masu bauta ga rana ba. Za mu tafi
daku ya zuwa biminmu don mu bautar da ku kamar yadda
muke bautar da duk wanda bai zamo daga jinsinmu ba.
Kuma baya bauta ga rana abar bautawa da gaskiya, to kuwa
Sunansa bawa a garemu kuma ya halatta mu bautar da shi
ko
ko mu halakashi mu shayar da jininsa ga rana abar
bautarmu bisa ga tsarin addininmu"
Zuhairu ya fusata da jin maganar wannan mutum ya ce da shi, kaicon rayuwarka da abin da ka ke ambatawa
cikin zantukanka masu munin ambato, wadai da miyagun
kalamanka na zalunci da ke bayyana tsantsar shirka da bata
mabayyani na bauta, gara na abar halitta, da shayar da
jinanan Musulmi a gareta da nufin yin bauta don
girmamata, ka sani cewa halaka ta gabata gare ka da
rundunar baradan da kake jagoranta sababin abin da kake
aikatawa na zalunci a doron kasa, don sha fe ruhinka daga
bayan kasa shi ne mafi alkairi ga sauran jama'ar Musulmi."
Barden nan ya bushe da dariya saboda jin abin da
Zuhairu ya ce sannan ya dubeshi ya ce da shi "Kai dattijo
ma'aboCin rauni da gazawa saurara ga ambaton wadannan
kalamai naka da ka ke ambatawa, ka bari natasa masu
ragowar jini a jiki da jarumta su yi magana, ba kai dattıjo
raunanne ka yi magana ba, don haka ko dai ku mika wuya a
garemu ko kuma mu tursasaku ga aikata abin da muka
umarceku ta hanyar karfi da tsananin yawanmu."
Zuhairu ya zare takobinsa ya fita gaban rundunar
baradan ya ce da su Ba zamu zama masu soro ko karaya da
ganin yawan rundunarku da ku ke alfahari da ita ba, don
Allah da muka yi imani da shi muke bauta masa zai iya
bamu nasara a kanku koda kun fi yawan adadin kasa, don
haka idan da mai karar kwana ya fara fitowa gareni ya ga
yadda zan aika da ruhinsa barzahu, idan kuma kun ki fitowa
ni na gabata cikinku na hau ku da sara da kisa irin na kare
dangi, har sai na tarwatsa rundunarku na sanyaku nadamar
halittarku a bayan kasa da abinda ku ke aikatawa."
Jarumin nan ya sake fashewa da dariya lokaci guda
kuma sai ya turbune fuska, irin na mugunta da zalunci ya
dubi Zuhairu ya ce da shi.
"Ban zamo daga cikin mutane masu imani da zan ji
tausayin tsufanka na kyaleka ba, tunda har kana jin ka isa
jarumi bari ni na halakaka da kaina, don ya zama izina ga
Sauran jama'ar da ke tare da kai." Ya zare takobinsa ya taho ga Zuhairu sai kuma yasa ke shawara ya maida takobin
yana mai fadin cewa "Ai halaka ka da takobi ma nuna
rashin jarumta ne, da gazawa, don kuwa iskar gudun dokina
kadai ta isa waftoka daga kan dokinka ka fado ka halaka."
Kafin ya gama maganar Zuhairu ya fusata ya daga
takobinsa ya kai masa sara, Jarumin ya yi sauri ya sanya
wata garkuwa ta bakin karfe ya kare saran, kaifin takobin
Zuhairu ya keta garkuwa gida biyu ta tarwatse, jarumin ya
yi baya taga-taga kamar zasu fadi daga shi har dokinsa da
kyar dokin ya tirje ya tsaya saboda karfin saran da Zuhairu
ya kai masa irin na sadaukantaka, jarumin nan ya dubi
Zuhairu cikin tsananin mamaki kafin ya kare mamakinsa
Zuhairu ya sake kai masa wani saran cikin karfin zuciya da
zafin nama, jarumin ya yi sauri ya zare takobinsa ya kare
saran, a wannan karon ma sai da ya sake yin baya kamar zai
fado daga kan dokinsa saboda karfin saran.
Zuhairu bai saurara masa ba ya ci gaba da kai masa
sara a fusace, barden nan ya yi kokarin ya kare amma tuni
ya makara kaifin takobin Zubairu ya sari tirken dokin
wuyansa, kansa ya fita daga gangar jikinsa, ya yi tsalle
sama ya tafi ya fadi a gaban sauran baradan da ke tare da
wannan jarumi.
Da ganin haka sai ragowar baradan dake tare da
wannan jarumi suka harzuka suka taso kan Zuhairu cikin
karaji da gunjin fusatuwa, suka far masa da sara da suka
kamar zasu halakashi, Zuhairu ya shiga karewa da maida
martani yana saransu da halakasu, suma ragowar jarumai da
suke tare da shi tare da Buniyatu suka zare makamansu
suka farwa baradan nan da sara, nan take waje ya yamutse
kura ta turnuke ta tokare sararin samaniya, karar haduwar
takubba
ta cika wajen kururuwar mazaje da haniniyar
dawakai ta yawaita.
Kafin wani lokaci su Zuhairu sun ragargaza rundunar
baradan nan da suka taso kansu, suka tarwatsa su, madaukaka daga cikinsu suka zama makaskanta, manyan
jarumai da ke ji da kansu suka zama masu rauni, da
yawansu suka halaka sai 'yan kalilan daga cikin su ne suka
arce don su tsira daga halaka, a sanda ake tsakiyar gabza
yaki
Bayan su Zuhairu sun tarwatsa rundunar baradan nan
suka yi godiya ga Allah a bisa nasarar da suka samu cikin
iko da kiyayewarsa, kuma babu wanda ya halaka daga
cikinsu, daga nan suka kada linzamin dawakansu suka ci
gaba da tafiya ya zuwa inda suka nufa.
Al'amarin matsafi Bahalu kuwa bayan da ya fice daga
dakin da ya ajiye Gimbiya Hasima ya tafi ya zuwa nasa
dakin cikin murna da farin cikin samun nasarar dauko
Gimbiya Hasima, tare da mallakar wannan fada ta
mahaifinsa da ya gada, hankalinsa ya kwanta don a yanzu
babu abinda ya ke jira illa bayyanar hadewar wannan
taurari na alkaluman sihiri da zasu tabbatar da kasancewar
Gimbiya Hasima matarsa ya samu damar kusantar ta, ya yi
sani da cewa mahaifin Gimbiya Hasima zai tura wanda za
su shiga duniya neman ta, saboda irin kaunar da yake yiwa
yar tasa, amma ya san babu wanda zai iya shigowa lardin
Ashtar bare ya samu nasarar shiga fadarsa, ko ya karbi
Gimbiya Hasima daga hannunsa, saboda ma'abota tsaro da
kariya dake tare da fadar.
A kowace rana ya kan ziyarci dakin da Gimbiya
Hasima take, don ya ganta ya ji sanyi a ransa saboda kaunar
da yake yi mata, sai dai bashi da ikon kusantarta ko ya
tabata, saboda alkaluman sihiri da ya yi imani da su basu
bashi damar aikata haka ba, har sai ranar da wannan taurari
na aikin sihiri suka hade da juna suka zama daya, saboda
haka a kowane dare ya kan zauna a daidai kofar da taurarin
suke ya zira ido yana dubansu da sauraron ya ga sun hade
da juna har zuwa wayewar gari, sai ranar ta fito ya tashi ya koma dakinsa, haka yake yi a cikin kowanne dare tun daga
ranar da ya kawo Gimbiya Hasima wannan fadar
Bayan wasu kwanaki matsafi Bahalu ya yi tunanin va
yi bincike don ganin halin da 'yar uwarsa Buniyatu ta ke
ciki, ya tashi ya tafi ga tarkacen kayan bokancinsa na aikin
sihiri, ya zauna a gaban wani kasko na lu'u-lu'u a cikinsa
akwai farin rairayi, ya sa hannu ya yi zance akan farin
rairayi sannan ya rufe idanunsa yana karanta wasu
dalasumai na aikin sihiri, bayan wani lokaci bayanai suka
bayyana gareshi, a saman farin rairayin sai ga siffar
kanwarsa Buniyatu tare da Zuhairu da sauran baradan dake
tare da su sun bayyana tafe akan dawakansu kan hanyarsu
ta zuwa bigiren da suka zauna tare da mahaifinsu kafin ya
rasu.
Matsafi Bahalu ya yi mamaki da ganin wannan
al'amari, ya sake share rairayi ya yi wani zanen a kansa,
bayanai suka sake bayyana a gareshi cikin alkaluman
sihirinsa ya ga cewa za su je wannan kogon dutse ne don
dauko wani rubutaccen sako na sirri da zasu samu damar
sanin inda wannan fada take, hankalinsa yayi matukar tashi
nan take ya tashi cikin sauri ya shiga shiri, dan tafiya
wannan kogon dutse ya rigasu zuwa ya dauke wannan
rubutaccen sako da zasu je daukowa a cikinsa.
Bayan ya gama shiri ya fice daga fadar ya kama
hanya, ya yi tafiya har ta tsawon kwanaki shida cikin
alkaluman sihirin rage nisan atfiya, sannan ya isa inda
wannan kogon dutse yake, da zuwansa ya shiga cikin kogon
dutsen ya soma duba da binciken inda wannan rubutaccen
sako yake, amma ya rasa inda aka ajiyeshi, babu abin da
matsafi Bahalu bai duba ba ko bincika cikinsa a cikin
kogon dutsen amma ya rasa inda rubutaccen sakon yake, ya
yi bincike cikin alkaluman sihirinsa baya nan suka tabbatar
masa da cewa babu shakka rubutaccen sakon yana cikin
wannan kogon dutse amma ya yi duk binciken da zai yi ya
kasa gano inda rubutaccen sakon yake.
Da matsafi Bahalu ya gaji da nema sai ya hakura ya
fita daga kogon dutsen, sannan ya yi wani aikin sihiri akan
kogon dutsen yadda Buniyatu ba za ta iya samun damar
shiga cikinsa ba, bayan ya kammala ya yi dariyarsa da ya
saba yi irin ta mugunta da zalunci sannan ya bace ya bar
wajen.
Su Zuhairu suka ci gaba da tafiya har suka shafe
sauran kwanaki goma sha tara da suka rage musu, kafin su
iso inda wannan kogon dutse yake, a ranar da suka iso
wajen da sanyin safiya suka tunkari inda kogon dutsen
yake.
Da isarsu wajen kafin su kai ga shiga cikin kogon
dutsen, sai suka ji wata irin tsawa mai tsananin karfi da ban
firgici ta gauraye wajen tamkar faduwar aradu, kasa ta
soma girgiza tana raurawa tamkar za ta tsage, Zuhairu da
sauran jaruman da suke tare da shi su afka cikinta su nutse,
can daga nesa sai suka hangi iska mai tsananin karfi tare da
bakar guguwa sun keto daga bangaren yamma, aka sake yin
tsawa da rugugi mai matukar ban firgici kamar sau uku,
gaba daya dajin ya yi bakikkirin sararin samaniya ya yi
duhu mafi tsanani daga yankin duhun dare.
Baradan da suke tare da su Zuhairu suka yi matukar
razana da ganin wannan yanayi da kuma al'amarin da yake
faruwa mai matukar firgitarwa shi kuwa Zuhairu ko a
jikinsa don ya saba da ganin irin wannan yanayi a duk
sanda matsafi Bahalu zai bayyana, kuma ya san wannan ba
komai ba ne face aikin tsafi da sihiri irin na ma'abota shirka
da tabewa Wa iyazu billahi ya ce a zuciyarsa yana duban
wannan bakar guguwa da ta tunkaro inda suke cikin
jarumta da karfin zuciya har ta karaso ta tsaya a gaban su ta
sauka.
Da tsayawar iskar sai ga matsafi Bahalu ya bayyana Cikin bakar guguwar a wannan karon ya sha babban da
yadda suka saba ganinsa a baya, a yanzu yana sanye ne da
sutura irin ta alfarma ta manyan sarakuna da suke ji da
kansu a duniya suke sanyawa, hannunsa na hagu yana rike
da kurtunsa na sihiri a dama kuma yana rike da sandarsa ta
tsafi, ya dubi su Zuhairu ya yi magana da murya irinta
nuna kaskanci a garesu ya ce da su.
"Ban yi zato ga samun nasara cikin abinda ku ke
nufin aikatawa ba, don kuwa a yanzu lamarina ya ta'azzara
akan wani abin halitta ya samu nasara a kaina komai karfin
tasirin tsafi da sihirinsa, na san za ka fito neman Gimbiva
Hasima da nufin zuwa fadata ku karbota daga hannuna, sai
dai ina mai sanar da ku cewa abune da ba za ku taba samun
nasara a kansa ba ne ku riski inda fadata take, bare ku karbi
Gimbiya Hasima daga hannuna, kuma halaka ta tabbata ga
duk wanda ya shiga lardin Ashtar da nufin zuwa fadata
saboda ma'abota tsaro da masu bada kariya dake tare dani,
babu wata jarumta ko aikin sihiri da zai yi tasiri a kaina,
kuma babu wani masani na ilimin bokanci da zai iya sanar
da ku yadda za ku samu nasarar zuwa fadata.
Ya dubi 'yar uwarsa Buniyatu ya ce da ita "Ke kuma
kin yi zabi ga abinda zai kai ki ga halaka, kasancewar ki
tare da wannan jarumi da ki ke son taimaka masa idan har
ba ki rabu da shi ba, don kuwa ba za ku taba samun nasara
ba, kuma hallaka ta kusanta ta gabata gare ki matukar kina
tare da shi cikin wannan tafiya da ku ke yi, ki zama mai
neman afuwarm a gareni tare da yin rantsuwa da alkaluman
Sihiri masu gima akan za ki rabu da wannan jarumi ki
dawo gareni, ni kuma na yi miki alkawarin zan maida miki
alkaluman sihirin da na kwace daga gare ki, na tafi da ke
fadar mahaifinmu da na mallaka a yanzu, mu zauna tare da
ke cikin salama da aminci kamar yadda mahaifinmu ya so
mu kasance kafin ya rasu.
Buniyatu ta amsa masa da cewa "Ai babu juya baya ga abin da na tabbata a kansa, na taimakawa abin begena da
kasancewa tare da shi har abada, kamar yadda mahaifinmu
ya bar duniya abadan ba zai sake dawowa cikinta ba, haka
na inganta rabuwa da kai abadan ba zan sake komawa
gareka ba, kuma ka sani a yanzu na karbi addinin
Musulunci tare da yin imani da Allah mahaliccin kowa da
komai, don haka ba zan sake komawa ga alkaluman sihiri
da bautar gumaka da tsafi ba, wanda a yanzu na yi sani da
cewa aikata hakan shirka ce da bata mabayyani, Allah ya
kiyashemu da sake afkawa a cikinsa.
Matsafi Bahalu ya ce da ita "Ke dai kina cikin
fagamniya da bata saboda makancewar zuciyarki akan
begen wannan jarumi, kin zabi kasancewa da shi cikin halin
wahala da kunci wanda karshensa halaka. Fiye da
kasancewa dani dan uwanki cikin salama da tasirin aikata
abin da ki ke so na alkaluman sihiri, to kuwa za ki kasance
abar yiwa kaico da danasani mara misaltuwa ckin wannan
hali kuma ba za ka taba samun nasara a kaina ba, cikin
kudirinku, idan ma kina da wani sirri da ki ke son dauka a
cikin wannan kogon dutse kamar yadda bayanai suka
tabbatar mini to kuwa ba za ki samu nasarar shiga cikinsa
ba, bare ki dauka, don na daure kogon dutsen da dalasumai
na aikin sihiri da ba za ki iya shiga ba, tun da ba kya tare da
alkaluman sihiri a yanzu.
Zuhairu ya zare takobinsa cikin fushi yana mai maida
masa raddi da cewa "Mu mun yi sani da cewa samun nasara
ko rashinta daga Allah ne, kuma a gareshi muke neman
taimako don haka muka yi imani da cewa zai bamu nasara a
kanka, ko don ya tabbatar da karfin iko da buwayarsa akan
duk wani aikin sihiri da ya sa ka ke inkarin samun nasara a
kanka, kuma bari na fara tabbatar maka da cewa kai ba
komai ba ne a cikin rayuwar duniya, na hallaka ruhinka da
Salwantar da rayuwarka, wata kila san da zamu isa fadarka
mu dauko Gimbiya Hasima kai ka dade da tafiya barzahu. Ya saki linzamin dokinsa a sukwane ya iso gare shi,
ya kai masa sara a fusace da dukkanin karfinsa, matsafi
Bahalu ya bace saran ya wuce shi kuma ya bayyana a baya,
zuhairu ya sake juyowa gareshi ya kai masa wani saran,
Bahalu ya sake bacewa bai sake bayyana ba sai da ya yi
nisa da inda Zuhairu yake sannan suka hangeshi ya bayyana
akan wani karamin dutse dake gabansa, ya dubi Zuhairu ya
ce dashi.
"Ai yanzu girman matsayina ya fi gaban na yi
arangama da kai dan fafatawa, ka sani a yanzu ni ne
shugaba na duk wani ma'abocin aikin bokanci da sihiri da
ke wannan yanki a duniya, don haka yin mubazara da kai
nuna kaskancine a gareni, kuma idan na halaka ka da kaina
zaj zama nuna gajiyawata cikin aikin shihirina, don haka
zan bar ka ka halaka ne cikin wannan tafiya da ku ke yi
daga kai har sauran jarumai da ku ke tare da su."
Yana gama fadar maganar sai bakar guguwar nan ta
sake turnukewa ta gauraye wajen, iska mai karfin ta taso ta
yi sama da guguwar ta nufi bangaren yamma inda bakar
guguwar ta bullo tunda farko, suka rika duban wannaan
bakar guguwa har ta bacewa ganinsu sannan sai suka ga
wajen ya washe duhun da ya lullube sararin samaniya ya
yaye, komai ya koma yadda yake alamar matsafi Bahalu ya
tafi yi.
Bayan tafiyar matsafi Bahalu sai Buniyatu ta sauka
daga kan dokinta, ta nufi kofar kogon dutsen za ta shiga
cikinsa, da zuwanta bakin kofar kogon sai suka ga wata irin
iska mai tsananin karfi ta fizgeta ta yi sama da ita ta makata
da jikin wani karamin dutse dake kusa da wajen, Buniyatu
ta yi kara a firgice sannan ta zube a kasa sumammiya
sulken jikinta ya kama da wuta za ta ta halaka.
Zuhairu da sauran jaruman da suke tare da shi suka
diro daga kan dawakansu cikin sauri suka tafi gareta don
kai mata dauki kada ta halaka, suka yi kokarin kashe wutar


BAKAR GUGUWA
littafi na biyu 2
Na Shehu Usman Muhd
typing by Shuraih Usman
post by Shuraih 99%
Part D
.
.
da ta kama jikinta har ta mutu. kafin ta fara konata, daga
nan Zuhairu ya ci gaba da shafa mata ruwa a goshinta yana
yi mata addu'a har ta farfado daga suman da ta yi, bayan ta
dawo hayyacinta ta tashi ta dubi Zuhairu ta ce da shi
"Hakika ba zan iya samun nasarar shiga wannan
kogon dutse ba, saboda aikin sihiri da yayana matsafii
Bahalu ya aikata akan sa, don haka sai dai wani daga
cikinku ya shiga saboda ni bani da damar shiga cikinsa.
Da jin haka sai ragowar baradan dake tare da su suka
yi shiru, babu wanda ya yi magana bare a samu wanda

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

2 Comments On BAKAR GUGUWA book 2
avatar
auwal-6-7

1 year ago

Reply

Littafine hadadde wanda Na dade ina nema

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to auwal-6-7

Ga shi kuwa yanzu ka sameshi

Please Login or Register in order to submit comment