Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai
ce zai shiga, saboda ganin abin da ya faru gareta, shi kuwa
Zuhairu cikin karfin zuciya da jarumta sai ya amsa da cewa
"Ni zan shiga kogon dutsen na dauko wannan sako, sanar
dani inda sakon yake na je na dauko."
Buniyatu ta ce da shi "Sakon yana rubuce ne jikin
wata fatar bauna dake cikin akwatin bakin karfe da ke ajiye
a Karshen wannan kogon dutse, idan ka shiga cikin kogon
dutsen kada ka sake ka taba komai sai wannan akwati, kada
ka sake ka ji tsoro ko ka razana akan duk abinda za ka ga ya
tunkaroka idan ka shiga kogon dutsen, haka kuma kada ka
yi magana ko ka yi waiwaye ka Juyo baya har ka isa inda
akwatin take, idan ka isa gareta sai ka dauko akwatin ka
fito da ita, ni kuma zan bude mu dauki wannan rubutaccen
sakon dake cikinta."
Da Zuhairu ya gama jin wannan bayani na Buniyatu
sai ya tashi ya nufi kofar wannan kogon dutse ba tare da
wani tsoro ko fargaba ba, yana zuwa ya shiga cikinsa da
Shigarsa wuta ce ta fara tasowa kansa tana wani irin huci da
ruri irin na azaba, Zuhairu ya daga hannu zai kare fuskarsa
don kada wutar ta konashi, amma sai ya tuna da maganar
Buniyatu cewa duk abin da ya gani kada ya ji tsoro ko ya
razana, don haka ya ci gaba da tafiya har wutar ta karaso
gareshi ya ji ta wuce ta jikinsa ba tare da ya ji zafinta ko
Kuma ta konashı ba.
Ya sake ganin wani katon dutse ya taho daga sama
zai fado kansa ya halakashi .zunairu bai razana har
dutsen ya kusa kansa amma sai ya bace babu shi ya
sake jin kamar muryar kakansa Marwan ya kira sunansa ta
baya, Zuhairu bai juya ba ya cigaba da tafiya.
Haka ya yi ta ganin abubuwa na ban tsoro da
razanarwa iri daban-daban, amma Zuhairu bai razana ba har
ya isa inda wannan akwatin bakin karfe take ajiye a
karshen kogon dutsen, ya dubi akwatin ya ga tana da
matukar girma yadda idan mutum ba sadauki bane ba zai
iya daukarta daga inda take ba, ya matsa gare ta ya sa
hannu ya ciccibeta da kyar ya rabata da kasa ya dora a
kansa saboda tsananin nauyi, Sannan ya juyo ya kama
hanyar fitowa daga kogon dutseen
Bayan Zuhairu ya fito ya nufi inda su Buniyatu da
sauran jarumai da suke tare da su suke tsaye suna jiran
fitowarsa, ya sauke akwatin a gabansu, Buniyatu ta yi
matukar farin ciki da samun nasarar dauko akwatin da ya
yi, sannan ta sa hannu ta bude murfin akwatin, wani haske
mai tsananin karfi tamkar walkiya ya tashi sama bayan da
ta bude, baradan dake tare da su suka ji tsoro suka ja da
baya, yayin fitar wannan haske. Bayan lafawar hasken
Buniyatu ta sanya hannu a cikin akwatin ta dauko wata
bakar fatar bauna dake nannade da bakin zare wadda ita
kadaice a cikin akwatin, sannan ta dubi Zuhairu ta ce da
shi.
"Tunda har mun samu wannan rubutaccen sako na
sirri, to kuwa mun samu damar samun nasara akan matsafi
Bahalu yanzu zamu tafi ga tsohuwa DIYANNUWA don ta
karanta mana wannan rubutaccen sako, ta kuma sanar damu
yadda zamu iya zuwa wannan fada ta Darul Sabar da
matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima, don babu
wanda zal iya karanta wannan rubutaccen sako a fadin
duniyar nan idan ba ita ba."
Zuhairu ya dubeta cikin mamaki ya ce da ita "Wacece
kuma tsobuwa Diyanuwa da zamu tafi gareta don ta karanta
mana wannan sako kuma menene alakarta da wannan
rubutu da ke jikin wannan fata da babu wanda zai iya
karantawa sai ita?"
Buniyatu ta ce da shi "Ita wannan tsohuwa Diyanuwa
kakata ce ta wajen uwa, kuma a hannunta na girma tun
tasowata, bayan mahaifiyata ta rasu, tana matukar kaunata
fiye da yadda ta ke son komai a duniya don babu abin da
Zan nema a gareta ta gaza mallaka min matukar tana da
ikon bani shi, sai dai kuma ba ta kaunar dan uwana Bahalu
tare da mahaifinmu Kauwas a rayuwarta ta duniya, ta
tsanesu da mafi munin tsana saboda kasancewar halinsu iri
daya na tsananin mugunta da zalunci, wannan ne dailin da
ya sa mahaifina ya karbeni daga hannunta ya dawo dani
gareshi, a halin yanzu ta makance ba ta gani kuma
mahaifinmu ne sanadin makancewarta, sakamakon jifanta
da alkaluman sihirin sa da ya yi.
"Babu wanda zai iya karanta wannan rubutaccen
sakon sai ita duk da cewa makauniya ce ba ta gani, kuma
idanunta ba zasu warke daga wannan makaranta ta aikin
sihiri ba har sai an debo mata ruwan dake cikin rijiyar dake
tsakiyar fadar Darul Sabar ta wanke idanunta da shi, idan
muka isa gareta muka sanar da ita bukatarmu babu shakka
za ta taimaka mana ta kuma sanar damu bayanan da bamu
Sani ba, game da ita wannan fada, ko don mu debo mata
ruwan dake cikin wannan rijiya ta tsakiyar fadar ta warke
daga halin makanta ta aikin sihiri da ke tare da ita."
Zuhairu ya sake cika da mamaki ya dubeta ya ce da
ita "To ita da take cikin halin makanta ta ya ya za ta iya
Karanta wannan rubutaccen sako dake jikin wannan fata?"
Buniyatu ta yi murmushi sannan ta ce da shi "Idan
muka isa gareta za ka gani har ma da wasu abubuwan ban
mamaki da al'ajabi daga gareta, don Allah ya yi mata
baiwar gane duk abinda ya kusanceta, koda kuwa tsuntsu ne
ya wuce a sama ba tare da ya yi kuka ba, idan ta ji hucin
iskarsa za ta fada maka sunansa kuma babu kuskure ka ga
shi ne ya wuce."
Zuhairu bai sake cewa komai ba ya ci gaba da
mamakin wannan al'amari da ta fada masa, daga nan suka
tashi suka kama dawakansu suka hau suka ci gaba da tafiya,
inda zasu yi tafiyar kwanaki goma sha biyu akan hanyarsu
ta zuwa lardin Ashtar kafin su isa inda tsohuwa Diyanuwa
take zaune
Ita kuwa Gimbiya Hasima tun daga ranar da matsafi
Bahalu ya kawota wannan fada ta Darul Sabar ta kasance
cikin halin tsananin damuwa da bakin ciki mara misaltuwa
babu abin da ta rasa na daga sutura, abinci ko abin sha, a
wannan fada bar ma da hadimai masu yi mata hidima, sai
dai ba ta iya cin abinci sosai kullum tana cikin tunani da
damuwa da bakin cikin rabota da mahaifanta da matsafi
Bahalu ya yi, cikin kwanaki kadan ta rame ta yi baki
tamkar wadda ta shekara a halin rashin lafiya, ba ta da aiki
sai yawaita ibada don ta rika samun nutsuwa, tun da
Gimbiya Hasima take a cikin wannan fada ba ta taba fita
dąga cikin dakin da matsafi Bahalu ya ajiyeta ba, duk da ya
bata damar ta fita ta zagaya cikin wannan fada duk inda
take so, wata rana da yanma ta yi tunani ta fita waje don ta
dan zaga a harabar fadar ko ta ga wani abin nishadi da zai
debe mata kewa.
Ta tashi, ta fita daga dakin ya zuwa waje ta ga an
zagaye harabar fadar da shuke-shuke masu matukar
kayatarwa, ga furanni da ya'yan itatuwa na ababen marmari
iri daban-daban. Ta ci gaba da tafiya a cikin harabar fadar
tana zagayawa har ta iso wani dan karamin lungu da duhun
itatuwa da furanni sulka lullubeshi tana shiga sai ta riski
wata kuyanga daga cikin kuyangin dake hidima a wannan fada tana sallah, Gimbiya Hasima ta cika da matukar
mamaki don ba ta yi zaton akwai ma'abocin addinin
Musulunci a cikin wannan fada ba, ta tsaya daga bayanta
har sai da ta idar da sallah ta zauna ta yi addu'a ta shafa,
sannan Gimbiya Hasima ta matsa gareta ta yi mata sallama.
Kuyangar nan ta dago kai da sauri ta dubi me yi mata
sallama da ta ga Gimbiya Hasima ce ta amsa mata cikin
mamaki don ba ta yi zaton cewa itama ma'abociyar addinin
Musulunci ba ce ba.
Gimbiya Hasima ta zo kusa da ita ta zauna sannan ta
ce da ita, Ya ke wannan baiwar Allah ina labarinki kuma
me ya kawoki wannan waje na ganki a halin yin hidima
karkashin wannan shu'unmin matsafi, ma'abocin shirka da
sihiri bayan kin kasance Musulma mai bauta ga Allah
(SWT)."
Kuyangar nan ta sunkuyar da kai hawaye ya zubo
daga idanunta sannan ta dago ta dubi Gimbiya Hasima ta ce
da ita.
"Sunana SANAWIYATUL ASSAD BIN ABDUL
NAS mahaifina sarki ne dake sarautar birnin KUBAIRU
Gabas da kogin Haisa, kuma jarumi ne da ya shahara a
fagen yaki da rundunar mayaka, wanda hakan ta sa sauran
sarakunan kasashen kafirai ma'abota bautar gumaka da tsafi
suke matukar shakka da tsoron kai hari akan birninsa, ya yi
yake-yake da dama na jahadi dan daukaka addinin
Musulunci har sai da ya kafa daular Musulunci a wannan
yanki, na taso cikin gata da kulawa tare da tarbiyya irin ta
addinin Musulunci har na kai girmana.
"Wata rana daga cikin ranakun rayuwata wani dan
Sarki daga cikin 'ya'yan sarakunan yamma ma'abota bautar
gumaka, ya ganni ya ce yana sona ya tafi ya sanar da
mahaifinsa bukatarsa ta san a nema masa aurena, da yake yana da gata a wurin mahaifibaa saboda shi kadai ya haifa a
duniya, tun a wannan rana sai mahaifinsa ya taso yan aike daga fadarsa zuwa fadar mahaifina akan neman aurena ga
dansa, 'yan aike suka iso fadar mahaifina suka nemi iso aka
basu damar su shiga bayan sun shiga suka kai gaisuwa
sannan suka sanar da mahaifina sakon sarkinsu na neman
aurena ga dansa.
"Da mahaifina ya ji bayanin dake tafe da su sai ya
basu amsa da cewa, su koma Su sanar da sarkin su cewa
babu auratayya tsakanin dansa ma'abocin bautar gumaka da
'yarsa Musulma, sai dai idan ya amince zai karbi addinin
Musulunci daga shi har jama'ar birninsa su daina bautar
gumaka da tsafi, to kuwa zai bada aurena ga dansa.
Yan aike suka tashi suka kama hanya suka koma
birninsu, da suka isa birnin suke sanar da sarkinsu abinda
mahaifina ya ce sai ran sarkin ya baci, ya yi fushi da
harzuka mai tsanani ya dauki alkawarin sai ya yaki
mahaifina ya rushe birninmu ya daukeni ya tafi dani fadarsa
ya aurar dani ga dansa, tun daga sannan suka shiga shirin
yaki, sun kawo hari har sau uku birninmu amma ba su taba
samun nasarar shiga birnin ba, bare su samu nasarar abinda
suke nufin aikatawa kuma a duk sanda suka zo sukan koma
ne cikin tsananin rauni da tagayyara, yawan rundunar
baradansu ya kan karanta jarumai daga cikinsu su zama
raunana, madaukaka daga cikinsu su zama makaskanta.
"Bayan da suka dawo daga yaki na uku ne da suka je
kai hari birinmu, wannan dan sarki ya fusata da ganin
baradan mahaifinsa sun kasa samun nasara akan jama'ar
birninmu, ya tafi ya dauki guba ya sha ya halaka da mafi
munin mutuwa saboda ni, sarkin nan ya yi matukar bakin
ciki mara misaltuwa, saboda hallakar dansa saboda ni
wanda shi kadai ya mallaka a duniya.
Tun daga wannan lokaci ya sake daukar alwashi
akan sai ya halakani ya halaka mahaifina don daukar fansar
salwantar dan sa, ko ta wane irinhali don haka ya koma
neman taimako daga manyan matsafa da hamshakan bokaye don a samu wanda zai je fadar mahaifina ya
halakashi ni kuma ya daukoni ya kai masa fadarsa, amma
cikin hukuncin Ubangiji babu wanda ya samu nasara
kaina ko kan mahaifina daga cikin jama'ar da yake turowa
har zuwa sanda ya hadu da boka Kauwas, wanda shi ne
mahaifin matsafi Bahalu wanda ya daukoki ya kawoki
wannan waje, shi ne ya daukoni daga fadar mahaifina ya
kawoni wannan waje duk da bai samu nasarar halaka
mahaifina ba, kuma bai kaini fadar wancan sarki da ya yiwa
alkawarin zai daukoni ya kawo ni ba, sai ya taho dani
wannan waje ya ajiye ni,
"Yadda al'amarin ya faru kuwa shi ne wata rana da
yammaci muna zaune a dakina tare da sauran kuyangina
muna hira, sai muka ji wata irin tsawa mai tsananin karfi
daban firgici ta gauraye dakin, karfin tsawar- kamar
faduwar aradu muka razana matuka daga ni har kuyangin
da suke tare dani, muka tashi zamu fice daga dakin a figice
sai muka ga wata bakar guguwa ta turnuke ta rufe kofofin fita
daga dakin, nan take kuma ta gauraye ko ina dakin ya yi
duhu mafi tsanani daga yankin duhun dare, sannan sai na ji
an wafceni an yi sama dani cikin iska, na yi karaji da
kururuwar neman taimako daga sauran kuyangin da suke
tare dani amma babu wanda take ganina saboda tsananin
duhu da ya rufe dakin kamar yadda bana ganin kowa, daga
nan sai na ji kaina ya juye na fita daga hayyacina ban sake
sanin abinda yake faruwa gareni ba.
"San da na dawo hayyacina sai na ganini a cikin
wannan waje da kuma wanda ya kawoni wato boka Kauws
mahaifin matsafi Bahalu da ya daukoki, ni ce mace ta farko
da aka fara kawowa wannan waje dukkanin sauran daga
baya ne aka kawosu. Kuma duk wadda ki ka gani a cikin
wannan fada 'yar wani sarki ce ko kuma yar attajiri aka
daukota daga hannun mahaifanta aka kawota nan, yau
Shekaruna uku kenan rabona da mahaifana da sauran dangina, na yi kukan bakin CikI da takaici mara misaltuwa
har na hakura na mika lamarina ga Allah ina mai rokon sa
ya kubutar dani daga wannan hali da nake ciki, wannan shi
ne labarina da abinda ya faru a gareni."
Da Gimbiya Hasima ta ji wannan labari nata sai ta yi
matukar tausayawa wannan kuyanga, itama ta bata nata
labarin da abinda ya faru tsakaninta da matsafi Bahalu ya
daukota ya kawota wannan waje, suka taya juna jimami
tare da addu'ar Allah ya kubutar da su daga halin da suke
ciki, daga nan suka ci gaba da hira har zuwa faduwar rana,
suka yi sallar magariba sannan suka yi sallama Gimbiya
Hasima ta tashi ta koma dakinta.
Tun daga wannan rana Gimbiya Hasima ta kan
ziyarci wannan kuyanga su yi hira, ko kuma ita kuyangar ta
je dakinta da haka har suka yi matukar shakuwa da juna
***
Su kuwa su Zuhairu bayan da suka ci gaba da tafiya a
cikin wannan daji suka shafe tsawon kwanakin shida
sannan suka iso inda wata bukka take ita kadai a tsakiyar
daji, Buniyatu dake gaba ta dubi Zuhairu ta ce da shi
"Wannan shi ne bigiren da Kakata tsohuwa Diyanuwa take
zaune, don haka bari mu isa gareta ka ga abin mamaki da
al'ajabi cikin hikima da baiwar da Allah ya hore mata.
Kuma kada wanda ya yi Magana daga cikinku ku yi saurare
ku ga abinda zai faru tsakanina da ita danku zama shaidu
da tabbatar da abin da na ambata.
Suka tunkari inda wannan bukka take, kafin su isa
gareta sai suka hanngi wata tsohuwa ta fito daga cikin
bukkar da ta ji takun sahun tafiyar dawakansu sanye da
bakaken tufafi hannunta rike da sanda tana dogarawa, ta
tunkaro inda take jin motsin tafiyarsu ta tsaya har suka
karaso gabanta suka ja linzamin dawakansu suka tsaya,
gaba daya babu wanda ya yi magana daga cikinsu, ita kuma
idanunta a rufe irin na halin makanta ta ce da su. "Su wanene wadannan jama'a da ku ka zo gareni
hafika na ji cewar akwai jikata Buniyatul Hajari a tare da
ku.
Buniyatu ba ta yi magana ba ta karbi kwari da baka
daga hannun wani jarumi daga cilkin jaruman da suke tafee
tare da su, ta sanya kibiya a cikin bakar ta ja ta sakar mata
kibiyar a saitin kirjinta, kibiyar ta tafi gareta da karfi kafin
ta kai jikinta tsohuwa Diyanuwa ta ji hucin tahowarta, ta
sanya sandar dake hannunta ta kade kibiyar ta tafi jikin
wata bishiya ta cake a jikinta, sannan ta sake yin magana ta
ce da su.
"Babu shakka wannan harbin kibiyar na jikata ne
Buniyatu, marhabin da zuwanki gareni kuma ke da su wa
ku ke tafe har ku adadin mutum arba'in da biyu kuma ke
kadai ce mace a cikinsu?
Su Zuhairu da sauran baradan dake tare da shi suka
cika da mamakin abinda ya faru tare da maganar da
tsobuwa Diyanuwa ta ambata, wadda babu kuskure a
cikinta tamkar idanunta a bude suke tana ganin adadin
yawanSu.
Buniyatu ta amsa mata da cewa "Babu shakka ni ce
jikarki Buniyatul Hajari, na ziyarceki tare da wadansu
jarumai da muke tafe tare dasu cikin wata bukata da ta
kawomu gareki, amma ya aka yi kika san adadin yawan
mu cewa mu arba'in da biyu ne muka zo wannan waje
kuma ni kadaice mace a cikinsu?
Tsohuwa Diyanuwa ta yi murmushi sannan ta ce da ita "Jikata mantawa ki ka yi dani shi yasa ki ka yi min
Wannan tambaya, amma ki sani ina da hikimar gane mace a
cikin taron maza komai tsananin yawansu kuma koda ba tai
magana ba, ta hanyar hucin numfashi da bil adama suke
wanda kunnena yake ji, kuma na gane adadin yawanku
tun daga takun sahun dawakanku da na ji sanda ku ka tunkaro inda nake, ta juya ta nufi wajen bukkarta tana dogara da sanda tare da yi musu izinin su karaso, su
Zuhairu da Buniyatu suka saki linzamin dawakansu suka
karasa bakin wannan bukka suka sauka suka daure
dawakansu, tsohuwa Diyanuwa ta gabato musu da abinci da
abin sha na daga 'ya'yan itatuwa suka ci suka sha har sai da
ya ishesu gaba daya duk da yawansu."
Bayan sun huta Sun nutsu tsohuwa Diyanuwa ta
tambayesu me ke tafe da su gareta, kamar yadda Buniyatu
ta fara sanar da ita da farko.
Buniyatu ta kwashe labarin duk abin da ya faru
tsalkaninta da Zuhairu da kuma yayanta matsafi Bahalu ta
sanar da ita, ta kuma yi mata bayanin abinda ya kawosu
gareta, don ta karanta musu wannan rubutaccen sako na
sirri da mahaifinsu ya bari kafin ya rasu, saboda su sami
damar zuwa wannan fada da matsafi Bahalu ya tafi da
Gimbiya Hasima su karbota daga gareshi, su kuma debo
ruwan da yake çikin rijiyar tsakiyar fadar, don samun
waraka daga aikin sihirin da aka yiwa Zuhairu su kuma
kawo mata don karya sihirin dake tare da ita, ta warke daga
halin makanta da take ciki.
Da tsohuwa Diyanuwa ta ji wannan bayani sai ta ce
da Buniyatu "Hakika zan taimaka muku ko don na samu
waraka daga halin makantar da nake ciki, idan kun cimma
nasara, kuma bana kaunar zalunci ba kuma zan taba goyan
bayan azzalumi ba a duk inda yake a fadin duniya." Tajuya
ga Buniyatu ta ce da ita "Ina rubutaccen sakon yake?"
Buniyatu ta dauko wannan fata ta mika mata,
tsohuwa Diyanuwa ta karba ta warware fatar, ta shafi
rubutun dake jikinta da tafin hannunta, ta sanya dan
yatsanta tana shafar tsawon rubutun sannan ta soma
karantawa tana sanar da su ma'anar rubutun kamar haka:
Darul Sabar wata shahararriyar fada ce da aka ginata
a lardin Ashtar tsakanin wasu manyan tsaunuka guda uku,




BAKAR GUGUWA
littafi na biyu 2
Na Shehu Usman Muhd
typing by Shuraih Usman
post by Shuraih 99%
Part E
.
.
tana da matukar kariya da tsaro na dalasumai na aikin tsafi
da sihiri dake zagaye da fadar, kuma kafin ku isa inda
wannan fada take da zarar kun shiga lardin Ashtar za ku
fara gamuwa da fitintinu iri daban-daban, na abubuwan
cutarwa da zasu taso gareku da nufin halakaku, sai kun yi
da gaske waje samun nasara a kan su, don shi kansa lardin
Ashtar yanayinsa ya bambanta da sauran yanayin da ku ka
saba ji a cikin wannan duniya, akwai masifu da wahalhalu
masu tsananı a cikinsa, wanda zai yi wahala ace wani bil
Adama ya shiga cikinsa ya fito ba tare da ya halaka ba."
Idan kun shiga lardin Ashtar kafin ku isa inda wannan
fada take, za ku fara tarar da wasu manya-manyan
sansasanin barada kuma jarumai ma'abota aikin sihiri har
guda uku, mahaifinki boka Kauwas ne ya samar da wannan
sansanin baradan, kuma sai da ya shafe shekaru uku cur
yana tattaro manyan sadaukai da suka shahara a fagen
jarumta, sannan ya kafa wadannan sansanoni karkarkashin
alkaluman sihirinsa, don su zama masu bada kariya da tsaro
ga dukkan wanda zai kawo farmaki akan fadarsa, ya
sanyawa kowane sansani shugaba daga cikinsu da kuma
Sunan da yake kiran sansanin da shi, sansani na farko
sunansa DARUL UKUB, sai na biyu DARuL MUSIBA naa
karshe shi ne DARUL MAUTU babu abinda wadannan
barada suke aikatawa a kowane sansani illa bauta ga wasu
manyan gumaka dake kusa da tsaunukan nan guda uku da
Suka zagaye fadar, tun daga farkon hudowar ranar har
faduwarta, kuma sukan ci su sha ne daga abinci da abin sha
da yake zubowa daga saman wannan tsaunuka da zarar sun
fara bauta ga gumaka da suke kUsa da su, wannan wata
hikima ce ta zubowar abincin daga saman tsaunukan dága
mahaifinku da ya tara wadannan jarumai, cikin alkaluman
Sihirinsa don su kara karfin imaninsu ga gumakan da suke
bautawa.
Babu wata halitta mai rai da zata gifta ta wannan waje baradan basu farmaketa sun halakata ba, koda kuwa tsuntsu
ne dake shawagi a sararin samaniya, don haka babu wani
mutum da zai wuce ta wajen ba su farmakeshi da nufin
halakashi ba, don haka ya zama dole kenan sai kun yi yakk da
wadannan sansanonin barada guda uku, kun halakasu kafin
Ku samu damar zuwa fadar.
Idan kun samu nasarar halaka wadannan barada ku ka
isa inda fadar take, za ku tadda tana kewaye da manyan
kofofi guda uku, ban san yadda za ku iya bude kofofin ku
shiga cikin fadar ba, saboda ba a rubuta a jikin wannan
sako na sirrin zuwa fadar ba, sai dai na yi sani da cewa
kofofin suna tare da tsaro na dalasuman aikin sihiri, wanda
ba za ku iya tunkarar kofar kai tsaye ku bude ku shiga
cikinta ba, ku yi kokarin neman hanyar da zaku bude kofar
da kanku, idan kun samu nasarar shiga cikin fadar shi
kenan babu wani aikin sihiri da zai yi tasiri a kanku, daga
nan kuma ya rage tsakaninku da shi wanda yake zaune a
fadar ku yakeshi don samun nasara a kansa."
Da ta gama karanta wannan rubutaccen sako da suka
kawo mata tare da yi musu bayanin abin da sakon ya kunsa
ta kara da cewa "Kada abin da na sanar daku na daga
wahalhalu da musibar dake tare da wannan tafiya da zaku
yi ta sa ku karaya ko ku zama masu rauni da fargaba, ku yi
imani da cewa za ku iya samun nasara akan abinda ku ka sa
gaba a ukatanku, za ku ga nasarar tana tare da ku ku kai ga
Cimma kudirinku akan duk abin da ku ka sa gaba."
Su zuhairu suka yi mata godiya a bisa wannan
shawara da ta basu, da kuma karanta musu rubutaccen
sakon da ta yi ta sanar da su yadda za su iya zuwa Darul
Sabar fadar da matsafi Bahalu ya tafi da (Gimbiya Hasima da yake yamma ta yi sai suka yada zango a yannan
waje suka kwana, da gari ya waye suka yi shiri suka yi
bankwana da tsohuwa Diyanuwa suka kama hanya suka ci
gaba da lafiya, suka tunkari inda da zai kai su lardin AShtar inda wannan fada ta matsafi Bahalu take
Bayan Su Zuhairu sun bar inda tsohuwa Diyanuwa
take zaune ita kadai a cikin daji suka ci gaba da tafiya
har suka shafe tsawon kwanaki takwas, sannan sulka iso
bakin wani katon kogi ma'abocin girma da fadi, ruwan
cikinsa na kadawa daga gabas zuwa yama, iska na
turashi da karfi yana ambaliva da toroko ya yi tsiri sama,
daga gefen kogun suka ga wani katon jirgin ruwa a tsaye
tamkar ana jiran isowarsu su shiga dan ketare ruwan,
suka ja linzamin dawakansu suka tsaya a bakin wannan
kogi Buniyatu ta dubi Zuhairu ta ce da shi.
"Wannan shi ne ruwan da zamu ketare mu shiga
lardin Ashtar da mun wuce wannan kogi tatiyar kwana
biyu zamu yi mu shiga cikin lardin, kuma mun yi sa'a
jirgin ruwa a bakin kogin da zamu iya shiga ciki ya
ketare, anan zamu bar dawakanmu har zuwa sadda zamu
dawo, don dukkanin tafiyar da zamu yi a cikin lárdin
Ashtar zamu yi ta ne da kafarmu."
Da Buniyatu ta yi musu wannan bayani sai Zuhairu
da sauran baradan suka sauka daga kan dawakansu suka
daure su a bakin wannan kogi, sulka tunkari jirgin ruwan
Za su hau, sai Zuhairu ya dakatar da su, ya zare takobinsa
ya nufi wajen da jirgin ruwan yake don ya tabbatar da
cewa babu wani abin cutarwa a cikinsa kafin su shiga
yana zuwa ya shiga cikinsa tun daga farko ya fara ganin
jini face-face a jikin jirgin ruwan ko ina, ya rika tafiya a
hankali yana kara shiga ciki, sai ya soma ganin kasusuwa
da gawarwakin bil Adam birjik a cikin jirgin, ya ci gaba
da tafiya yana dube-dube ko zai ga abin da ya halaka
Wannan jama'a sai ya soma jiyo wani gunji da huci
tamkar na wata halitta da ke da rai Cikin karshen jirgin ruwan
Zuhairu ya gyara rikon takobinsa ya ci gaba da
tunkarar inda yake jin wannan gunji da huci don ya ga
abinda yake yin sa, har ya isa karshen jirgin ruwan, da
zuwansa sai ya tarar da wata katuwar macijiya a nannade
ta fasa kai tana wannan huci, girmanta kamar wani
karamin dutse za ta iya hadiye mutum ya halaka lokaci
guda, a gabanta ga gawarwakin mutane nan da ta halaka
take hadiya a matsayin abinci, nan take Zuhairu ya
fahimci. Macijiyar nan ce ta halaka jama'ar dake cikin
jirgin rowan gaba ki daya.
Da ganin Zuhairu sai macijiyar nan ta yi wani huci
mai karfi ta taso kansa ta kawo masa sara, Zuhairu ya
kauce ta samu jikin itacen jirgin ruwan ya daga takobinsa
ya kai mata sara ya samu jikin ta amma sai ya ji kamar
ya sari dutse takobinsa ta tashi sama ba tare da ta yanki
jikinta ba,
Macijiyar ta sake kawo masa sara Zuhairu ya goce,
ta sake kai masa sura za ta hadiye shi, Zuhairu ya kai
mata sara ya samu bakinta, macijiyar ta yi gunji da
girgiza saboda azabar saran da ya yi mata, jirgin ruwan
ya yi tangal-tangal kamar zai kife, sauran baradan da ke
bakin kogin suka ja da baya saboda jin wannan gunji. Shi
kuwa Zuhairu ya sake jan daga don tunkarar ta, da ya
lura sosai sai ya ga ya ji mata rauni a inda ya sareta a
baki, don haka ya kara azama da kai sara a wannan waje
don ya halakata:
Macijiyar ta sake taso masa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

2 Comments On BAKAR GUGUWA book 2
avatar
auwal-6-7

1 year ago

Reply

Littafine hadadde wanda Na dade ina nema

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to auwal-6-7

Ga shi kuwa yanzu ka sameshi

Please Login or Register in order to submit comment