You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
Fita sukayi gaba daya asma'u dafitowar kenan taji abunda yafaru tayi saurin bin bayansu
Waya sarah tadauka takira aysha bugu biyu tadaga cike da takaici sarah tace jiya kunyi accident da AK meyasa baki gayamun ba
Meyafaru ....
Aysha tafada tana yamutsa fuska
Yan sanda sunzo nemanku kina ina ...
Bata karasa ba aysha tayi saurin katse kiran atsorace tama kasheta gaba daya
Suna isa wurin motocin AK yayi saurin nufar motarsa yana kare scratch din dake jikin motar kusa dashi asma'u taje tana fadin jiya kunyi accident ne ?
Girgiza kai yayi baice komaiba
Matsardashi tayi tana kallon scratch din tace to meyasamu motarka
Juyowa yan sandan sukayi suna kallon motar
Dafe kai AK yayi yana fadin ohhhhh chitti bazaki iya yin magana ahankali bane
Janshi tayi gefe cike da damuwa tace jiya da natambayeka meyasa baka gayamun ba kai da waye amotar
Indai bake bace to kinsan aysha ce kidaina mun wawiyar tambaya
Murmushi dan sandan yayi yace yallabai shaidu sun nuna kai kade mutuminnan saboda haka zamu tafi dakai mudawki statement dinka sannan kagayamana wacece tare dakai amotar
Kauda kai yayi yace bakowa atare dani ni kadaine
Kuka grany tafara tana basu hakuri
Riko hannunta yayi yace grany ki kuantar da hankalinki yanzu zan dawo kawai bayanaina zasu dawka
Yana kai nan yashiga motarsa tare da biyu daga cikin yan sandan sukuma suka shiga tasu suka tafi
Cikin gida grany takoma dasauran mutanan gidan
Asma'u kuma nan take tabi bayansu police station
Tana zuwa tayi magana da police din akan yataimaka yahadata da mutumin da aka kade se dakyar yahadata da mutumin
Dafari kin sauraronta yayi seda tahadashi da Allah sannan yatsaya sukayi magana tarokeshi yajanye karar sa base takai ga yan jariduba
Ya yarda zai janye amma setabashi kudi masu yawa
Bayan AK yadawo gida yanemi ganin lawyoyinsa akan maganar
Sunce gaskiya case din yanada girma saboda yahada da tukin ganganci kuma dole se mutumin ya janye kararsa kafin aji da police
Gida asma'u tadawo tadauki sarka da yan kunnanta na zinare da abbanta yataba sayamata
Tazo fita kenan tahadu da AK
Cike da takaici yake kallonta har tafita yana fadin ba ma abunda yadameta yawo kawai tasa agaba
Camun dai ake amma kowa na zillimin abunda zai faru da AK
da rana sega yan sandan sundawo da mutumin da aka kade yasha bandage hannu dakafa
Tunda grany tagansu tafara kuka cike da damuwa sarah tarike AK tana fadin Yaya dan Allah karka bari sutafi dakai
Umma dabatasan abunda yafaru ba tace lafiya mekuma yaka yan sanda
Inna ta katseta tana washe baki tace
Inaga kamun sukazo suma
Juyawa AK yayi yana kallon asma'u dake kan dining tana cin abincinta hankali kuance jiyayi kamar yaje ya shakota dan takaici
Wurin yan sandan yanufa yana fadin muje karna batamuku lokaci
Rikosa dan sandan yayi yana murmushi yace sorry sir bamunzo tafiya dakai bane munzo baka hakuri ne akan shiga lokacinka da mukayi
Da mamaki kowa ke kallonsu
Kamar ya ....
AK yafada yana kallon Wanda yakade
Police din ya nuna mutumin yace wannan ne Wanda ka kade shi yashigar da kara kuma yanzu ya janye
Tukin gangancin dakayi kuma matarka tace bakai bane ke driving din ita tace tana so tayi shine kake koyamata Muncita tara tabiya kuma tabada hakurin hakan bazata kara faruwa ba
Saboda haka zamu tafi se anjima
Tunda yafara magana AK ke kallon sa cike da mamaki yakasa magana har suka fita
Cike da farin ciki grany takalli Wanda aka kade tana mai godiya
Murmushi yayi yace hajiya bani zaki godemawa ba waccan yarinyar zaku godema saboda ita tasa najanye karar
Alama asma'u tamishi da yayi shiru
Murmushi yayi yace a'a yarnan barni nafada kin birgeni matuka da kika tsaya akan matsalar mijinki dan kirufamai asiri najima banga mace kamarki ba
Sarah takatseshi dafadin dallah malam dakata tunda kajanye karar ai sekabar nan da kudin wa tabiya tarar ba kudin gidan nan ba
Bawanda yakulata
Sarkan yanuna ma grany yana fadin kinga abunda tabani akan najanye karar
Da mamki Umma tace asma'u wannan basarkan da babanki yabaki bane shine zaki sayar
Murmushi tayi tace Umma meyasa zan ijiyeta bayan ga anfaninta yazo
Cike da farin ciki grany tace ma mutumin yasaida mata sarkan bada bata lokaci ba ya amince tabashi kudi masu yawa yatafi
Godiya tama asma'u tana samata albarka sannan tabata sarkanta tace kar takara saida sarkan tanada mahinmanci tunda babanta yabata
Bangarensu tanufa dan ijiye sarkan
Aysha ce tashigo gidan adan tsorace dan tahadu da yan sandan suna fita
Kusan AK tamatso cikin rada tace AK naga yan sandan sunfita Allah sa dai baka fadamusu tare Muke ba
Da mamaki yake binta dawani irin kallo yakasa cewa komai
📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KaNWATA_ 👩👧
9⃣0⃣
Sosa kai tayi tana kame kame tace kar kamun wata fassara kawaidai natambaya ne
Ahasale yace meyasa kanki kawai kika damu dashi kina ikrarin kina sona ita wacce bata sona bana sonta ta ysaya mun alokacinda nake Neman taimako
Ke kina ina awannan lokacin kuma inada tabbacin kinsan da zancan amma baki dawo ba seyanzu kuma kina tambayar wai nafadi sunanki
Juyawa yayi ahasale yabar wurin
Hannu tadora akai tace nashiga uku ni aysha
Wurin Asma'u yanufa tana shirin shiga wanka ya iskota
Chitti bansan meyasa kika yi haka ba akan wane dalili amma thank you
Daure fuska tayi tace nagayamaka kadaina kirana chitti kuma karma kayi tunanin nadamu dakaine saboda Umma da grany nayi hakan nasan bazasuji dadi idan aka kamaka ba shiyasa so stop thanking me..
tana kainan tawuce bayi
Murmushi yayi yajuya yafita
Yana sauka kasa yazauna kusa da inna yana tambayarta abba
Fira suka fara yi suna dariya
Kusan sarah aysha tamatsa tana gayamata yanda sukayi da AK takare dafadin
Yanzu zaiga kamar asma'u tafi damuwa dashi ni bandamu ba
Sarah tace to ai dagaskiyansa kema wayakaiki yimai wannan tambayar
Tsaki aysha tayi tana kallon Ali tace ni wallahi guy dincan tunda nashigo yake kallona bai San haushi yake bani ba
Dariya sarah tayi tabar wurin
Kiran kowa tayi akan za'afara rawa sawrayi da budurwa mata da miji
Ai kaman jira Ali yake yazo wurin aysha wai suje suyi rawa Da har taki amma dataga AK na kallonsu tamike suka fara rawa
Inna ameena tace AK yatashi suyi da Asma'u
Dariya yayi yace bata iya rawa ba
Daure fuska tayi tace kamar ya daga ganinta zatayi kyew da rawa kirata kuyi
Murmushi yayi yace kedai kawai kice tabirgeki amma wane kyew da rawa yarinya kullun alullube
To ai shine kyen ni duk nan wajan banga yarinyar da lullubi yakema kyew ba kamar Asma'u
Dariya yayi yace akwaisu dayawa ma
Ina suke
Waige waige yafara can yahango wata yarinya atsaye ta juya baya tana magana dawata
Nuna ta yayi dayatsa yace gawata can
To tashi kirata muganta
Gyara kuanciyar sa yayi kan 3siter yana fadin dan Allah kibarni ba inda zani
Jan kafanshi tafara tana fadin tashi dai ka kira ta inkasan da gaske kake ni ban yarda ba se naganta
Tashi yayi yana yarfa hannu yanufi yarinyar
Bayanta yatsaya yace hello !!!
tana juyowa yaga asma'u tana murmushi tace hi!!!
How me I help u
Juyowa yayi yakalli inna ameena tana kwasan dariya
Sannan yakalli asma'u da mamaki yace meyasa zaki canza kayan jikinki
Murmushi tayi tace saboda nayi wanka idan abunda kazo tambayata kenan sekatafi ....
tana kai nan tayi gaba abunta
Juyawa yayi yana kallon su aysha dake rawa haushi yaji yabar wurin
Murmushi tayi dan ganin AK yana kishinta
tana ganin yatafi tadaina rawan takoma tazauna
Kusa da ita sarah tazo tazauna tana mata magana akunne suna kallon fa'iz da yadage yana daukan khadeeja photo
Ita kwa se daure fuska take tana kauda kai
Dariya sukayi suka tafa hannu sannan sarah tace je kifito da jakan kidora kan gado bari nakirashi
Aysha natafiya sarah takira fa'iz tace yaje dakinta ya dawkomata jakanta yaso yaki tace zata gayama Umma hakanan yatafi yana gunaguni
Aysha nashiga dakin AK yaturo kofar atsorace ta jiyo tana kallonsa
Kusa da ita yamatso yana fadin rawa kike dawani agabana ko ??
Murmushi tayi tace to ai nadauka kadaina sona ne tunda kayi aure
Ashe kana kishina
Rungumota yayi yace ina sonki amma kishindai ban saniba dan banji komai ba lokacinda naganko
Tunowa tayi da plan dinsu tafara kokarin turesa tana fadin AK katafi kar wani yaganmu bata gama rufe baki ba sukaji anturo kofar
Atsorace yasaketa sukajiyo atare dan ganin Wanda yashigo
Fa'iz suka gani atsaye yana kallonsu idonsa cike da hawaye
Me kake anan....
AK yafada yana daka mai tsawa
Shuru yayi yakasa magana yana binsu da kallon tuhuma
Janshi AK yayi dakarfi yafito dashi Waje
Damamaki kowa ke kallonsu
Ahasale grany tace kai abidi sakeshi mana meyamaka
Aysha tayi saurin fadin grany lekani yake ina canza kaya
Juyowa fa'iz yayi yana kallonta da jajayen idanuwansa
Zaiyi magana kenan AK ya wankesa da mari yana fadin me ya kaika dakinta
Zai karamishi kenan asma'u tarike hannunsa tana kallon fa'iz tace dagaske kaje dakinta
Zai yi magana AK yarigashi dafadin tambayarsa ma kike kenan karya zan masa kome
Inna ameena tace yo kai AK ya akayi kasan yaje dakin kana daga ciki kodaga waje
fa'iz zaiyi magana AK yakara katseshi dafadin wallahi idan nakara ganinka kanufi dakinta sena tattaka ka
Kwaceshi asma'u tayi daga hannun AK tanuna mai hanyar fita tana fadin wuce gida
Cikin rawar murya yace ammah listen
I said out ....
Saurin barin wurin yayi khadeeja tabi bayansa
Hakuri AK yaba su inna akan abunda yafaru
Murmushi tayi tace ba komai abidi ai fa'iz kaninka ne zaka iya hukuntashi idan yayi badaidai ba
Fita asma'u tayi tabi bayan khadeeja akarkashin bishiyar kofar gida ta iskosu yasa kai aguywa yana kuka khadeeja na zugunne kusa dashi tana lallashi
Asma'u nakarasowa yamike zai bar wurin tayi saurin rikosa tana bashi hakuri
Cikin sheshshekar kuka yace yanzu amma kema kinyarda na aikata abunda tace wallahi karya takemun
Rikoshi tayi tana murmushi tace nasan ba halinka bane fa'iz amma bayanda zanyi inkareka
Kauda kai yayi yana share kwalla yace amma meyasa kika auri AK Sam bai dace dake ba ba mutumin kwarai bane kuma wacece wannan yarinyar danagansu tare
Murmushin dole tayi tace haba fa'iz meyasa zaka ce haka kaifa kake yabon AK hausawee kuma yau kana kushisa wannan yarinyar kanwarsa ce shiyasa kaga yamaka haka akanta amma ba halinsa bane yanada kirki kuma yanada hakuri bayada saurin fushi kuma ko yayi nantake yake mantawa
Da kyar tasamu ta lallasheshi suka wuce gida da khadeeja ita kuma tadawo ciki
Karo sukaci dasu inna zasu fita hakuri tabasu kuma taroki kar su gayama Ummi da abba abunda yafaru sannan sukayi sallama suka tafi
AK natsaye yana kallon sarah da aysha dake dariya karasawa yayi wurinsu fuska ahade yace inafata dai Baku kuka shirya wannan wasan kwaikwayon ba
Kame kame suka fara suna kallon kallon zai yi magana kenan ahmad yakirasa awaya yana tambayar ya yake yaji wai police sunzo Neman sa
Murmushi yayi yace I am fine friend yanzuma nakeso nazo company
Dariya ahmad yayi yace har kagama cin amarcin ne
Katse kiran yayi batare dayace komai ba
yana dubawa yaga harsun bar wurin girgiza kai yayi
Yajuya zai fita sukaci karo da asma'u tazo wucewa dafe goshi sukayi atare cike ahasale yace wai meyake damunki ne
Murmushin yake tayi tana mai alama da grany tana kallonsu
Shima kalan murmushin yayi yana taba goshinta yace meyasa ba kya kula dakanki ne kinfiso kiyita jima kanki ciwo kina bani aiki
Inna ameena dake kallonsu tayi dariya tace ai kakanninmu sunce in mata da miji sukayi karo sau uku to ba mai rabasu sai Allah saboda haka kunyi daya saura biyu
Kan asma'u Yakama yahada danasa da karfi saida taji zafi seda yayi har sau biyu sannan yawuce yana shafa goshinsa ....
Da daddare yana kuance kan gado yayi rub daciki yana kallon TV ga bowl din gyada ahannunsa yana ciki
Asma'u tashigo dakin rike da mug din coffee dinsa kusa dashi ta ijiye batace komai ba da alamun damuwa afuskanta
Binta yayi da kallo yana fadin fushi kike ne dan nadaki kaninki
Juyowa tayi tana kallonsa tace meyasa zanyi fushi dan yayi laifi ka hukuntashi
Sedai inaso nasan meyasa kamareshi
dan yashiga dakin
Kodan yaganka tare da aysha
Shuru yayi baice komai ba yaci gaba da cin gyadarsa
Bathroom tanufa tana fadin kunasaka familyna amatsala saboda makauniyar soyayyarku
Dakallo yabita har tashiga sannan yadauki coffee dinsa yanasha
Can anjima tafito sanye da doguwar rigan baccinta ga towel akanta tana tsane gashinta
Remote din kusa dashi tadauka takashe AC tanufi dressing mirror tana gyara gashinta
Da mamaki yake kallon dogon gashinta dan Sam bai San tanada gashi haka ba
Remote din yadauka yakunna AC
Juyowa tayi takallesa yayi saurin kauda kai yana kallon TV
Zuwa tayi tashiga gaban TV tahanashi kallo
Kashe AC din yayi takoma wurin dressing mirror
Kara kunna AC din yayi yana murmushi
Juyowa tayi tana yarfa hannu tace wai miye haka kakeyi
Gyana nakeci....
Yafada batare da yakalleta ba
Kusa dashi tamatso dan ita se alokacin ma ta lura da gyadan hadiye yawu tayi tana murmushi tace tsammun gyadan
Make kafada yayi yace naki kije wurin grany tabaki
Grany tayi bacci
To kijira dasafe tabaki
Dawke bowl din tayi daga gabansa tana fadin Allah senaci
Dirowa yayi daga kan gadon yana fadin to kikawo na tsammiki da kaina
Guduwa tafarayi tana cin gyadar shikuma yana kokarin kamata seda suka zagaye dakin kap sannan takara cika hannu da gyadan ta mika mai tana fadin to tsaya gashi Allah kadan naci
Kin karba yayi yana kokarin kuace na hannunta suka fada kan gado shi Asama ita akasa
Kallon juna sukafarayi alokaci guda suna tuna lokacinda suka fara haduwa da zamansu awuri guda
Asma'u ce ta tuna lokacinda AK kecemata gobe ana daura auren sarah zata bar gidan
Tureshi tayi tatashi tana gyara balanket dinta dake kasa ta kuanta tana hawaye
AK ma shiru yayi yaci gaba da kallon TV har bacci yadaukesu
Washegari dasafe ....
Khadeeja nazaune adaki tun jiya take kuka har yau tana tuna shikenan yau ahmad zaizam nawata shikenan zata rabu dashi
Umma ce tashigo dakin cike da tausayi take kallonta tace khadeeja kiyi hakuri shi aure nufi ne na Allah tunda kikaga bai aureki ba Allah yayi ke ba matarsa bace
Shuru khadeeja tayi tan sharan kwalla
Cikin sassanyar murya Umma tace zaki samu zuwa bikin kuwa
Girgiza kai tayi batace komai ba se hawayen ta dasuka karu
Abangaren ahmad ma haka Zaune yake atakure ga idonshi yayi ja da alama kuka yasha bakadan ba Momy batayi wani taron biki ba dan tasan ahmad ba son aurennan yakeba dafashi tayi da damuwa afuskanta tace ahmad kaifa namiji ne za a iyama mace auren dole tazauna amma ba namiji ba idan har kasan baka son sarah to karkayi kuskuren aurenta
Namiji shine ginshikin aure idan har bazaka iya jan ragamarsa ba to baida wani anfani
Girgiza kai yayi yace Momy banason sarah amma zan aureta saboda wani dalaili
Tashi yayi yafita yana fadin Bari nashirya natafi AK yana jirana
Asma'u na bangaren grany bayan tagama hada breakfast ta fito tana kallon grany tace
Grany har kinshirya lalle kin kosa sarah tayi aure
Dariya grany tayi tace eh mana asma'u ai rana tafarayi gashi har mutane sunfara taruwa jeki kema kishirya
Zama asma'u tayi tana fadin bari har nacika tumbina grany
Ina wani tumbi anan Abu kaman faranti
Wai ina abidi banganshiba yau
Yana bacci ....
Oh to nidai yau Allah sa yasa manyan kaya wallahi natsani kananun kayannan daurin aure guda amma kagansu da kananun kaya kamar wasu turawa
Dariya tayi tace karki damu grany tunda ba kyaso bazai saka ba
Wa ya isa ya hanasa asma'u mutumin da kika ga ko juma'a kananin kaya yake sakawa
Tashi tayi tafita tana fadin
Grany idan kasan halin mutum zaka ita sashi yayi abunda kakeso
Tana isa bangarensu ta iskoshi kwance yana bacci murmushi tayi tanufi bayi tayi wanka kayanta taduba taciro wata doguwar riga mai kyew da dogon wandonta kamar na India se gyalen kayan
Datasakasu ita kanta sunbirgeta mai kawai tashafa sedan kunne datasaka kalan kayan
Drowan AK taduba taciro mashi kananun kaya masu kyew sannan tafito
Azaune ta iskoshi bakin gado tunda tafito yake kallonta seyaga tayi kyew yau
Murmushi tayi tadawra kayan kan gado tana fadin ABI....bata karasa ba yawatsamata harara tayi shuru tana kunshe dariyarta
Can kuma tace to ai ban fada duka ba tunda ka kirani da chitti ai nima zan iya kiranka da ABIDI amma sunan yamun yawa shiyasa na rageshi
Daure fuska yayi yace to kikirani da AK ko ABID mana
Miye nawani ABIDI
Dariya tayi tace ashe ba dadi idan bakaso nakiraka ABI to nima kadaina kirana chitti
Shuru yayi yana kallon kayan da ta ijiye kan gadon murmushi tayi tadauko kayan tana nuna mai tace ga kaya nazaba maka kasa zasuma kyew
Kauda kai yayi yace karki manta matsayinki awurina so stop acting like my wife
Dariya tayi tace banmanta ba amma ai duk dahaka ni matarka ce kuma kananun kaya suna maka kyew inason ganinka acikinsu shiyasa nakeso yau kasa
Kwace kayan yayi ahannunta yanufi dressing room yana fadin tunda kinaso kwa bazan saka ba kuma kidaina tabamun kayana daga yau
Murmushi tayi tana kallonsa har yashiga sannan tafara gyara gadon
Can anjima yafito sanye da manyan kaya sunmasa kyew bakadan ba
Dariya takusa kwacemata ganin yanda yake tattare rigar ga hular akarkace
Daure fuska yayi yanufi dressing mirror yana fesa turare
Kallonsa tayi tana dariya tace yallabai hularka akarkace
Banza yayi da ita yana gyara zaman wandonsa
Dagowa yayi yana kallonta tana dariya yace ai gwara ni koba komai ansan nayi kyew ke kuma fa dako janbaki baki iya sakawa ba kin wani yafa gyale kamar dillaliya ...
Fita tayi tana dariya tace wani gwara kai dawata hularka har tarufe girarka Allah sama kana gani da kyew
Bin bayanta yayi suka fito tare yana rike da rigar da yakeji tamai dabaibayi
Tasashi agaba se dariya takemai tun yana daure fuska har yabiyemata suna dariyar
tunda aysha ta tsinkayesu taji kamar andaba mata wuka suna sakkowa aka hau yima AK dariya bashir ne yagyara masa hularsa kowa nafadin yau ya canza kamar bashiba grany tace manyan kaya sunfi yimasa kyew
Matsowa aysha tayi taja asma'u gefe ahasale tace ke wai meyake faruwa ne
Bige hannunta asma'u tayi tana murmushi tace abunda idonki yaganemaki
Firan me kuke da AK dazu dakuka sakko
Barin wurin asma'u tayi tana fadin sirrin ma'aurata ne baizama dole ke kiji ba
Da kallo tabita tanaji kamar ta kurma ihu
Gyada kai tayi tana cije lebe tace dole nadau mataki naga alama ina sake dabaki zan jini asalansa ....
Shigowar Ahmad da sauran abokanansu ne yakatsemata tunaninta nan take aka hau shewa ana murna banda ango dakana ganinsa kasan yana cikin damuwa
Tunda yashigo sarah takasa dauke idonta akansa tana ji ba macan da takaita Sa'a saboda ahmad daban ne yahadu iya haduwa
Dining suka nufa gaba daya suka fara cin abinci suna fira
Kitchen aysha taja sarah tana fadin amarsu zo mu dakko masu dambun naman da grany tace aba abokanan ango gift idan sunzo
Da kallo asma'u tabisu dan tasan wata gulmar zasuyi
Tashi ahmad yayi yanufi bangaren grany yazo wucewa kenan yaji suna magana
Aysha tace wallahi yau senakeji nafiki farin ciki mun kusa rabuwa da annoba
Dariya sarah tayi tace ai jira kawai nake adaura aure muyi waje da ita
Dariya sukayi suka tafa ...
Girgiza kai yayi yana fadin kai inaaaaa bazai yuwu ba bazan yi biyu babu ba
Narasa khadeeja kuma bukata bata biyaba auren asma'u yamutu
Wayanshi yaciro yana kiran khadeeja amma bata dauka
Fita yazoyi yahadu da asma'u zataje wurin khadeeja taga yatake
Shan gabansa tayi ta tareshi tana fadin ina kuma zakaje bayan lokaci yayi idan ma kana tunanin khadeeja ne to koma wurinta zanje yanzu
Zaiyi magana yaga sarah atsaye tana kallonsu
Runtse ido yayi yana cije lebe yajuya Yakoma ciki """"
Ur's.......
*MHD*
[18/07, 15:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na ( *Maryam Mhd* )
( _nasadaukar dawannan page din gareki Aisha(anna) da kuma Dr Aisha tnx for ur support
Sa'ata da xee Allah yabar zumunci )_
9⃣5⃣
Bayan anci ansha AK yafara Neman ahmad amma bai gansa ba yakira wayarsa yafi akirga amma baidaga ba daga karshema ya kashe wayar baiyi tunanin wani Abu ba yaje yatambayi sarah ko yagayamata Inda zaije
tace bata ganshiba nan fa aka fara nemansa gashi kowa yataru amasallaci ana jiransu adaura aure
Hankali tashe yake kiran wayar ahmad amma akashe
Sarah dake gefenshi tana rusa kuka ta mike zunbur tana fadin ina asma'u
Juyowa sukayi shida aysha suna kallonta
Aysha tace kina nufin tasan inda yake
Bata bata amsa ba tafita aguje tasauka kasa tana kwalama asma'u kira
Amma bata ganta ba
Jan hannunta AK yayi yamaidata sama ganin yanda mutane ke kallonsu
Dakinsa yakaita yana fadin ki kuantar da hankalinki sarah nasan bai yi nisa ba kila wani uzuri ne yafitar dashi
Tureshi tayi tafada kan gado tana kuka tace Yaya duk laifinka ne kai kaja haka tafaru kasake mata dayawa ka aureta ne dan kahukunta ta amma kabiyemata kana mata wasa kana mata dariya kana fira da ita shiyasa tasamu damar yin haka yanzu gashi tarusa mun farin cikina kuma naganta tana ma ahmad magana dazu nasan ita tacanza mai ra'ayi yafasa aurena wallahi bazan barta ba sena kasheta
Ahasale yafita daga dakin yana banko kofar dakarfi
Aysha tazo binsa kenan tahango wata farar takarda akan dressing mirror har tawuce se kuma tadawo tadauki takardar ganin ansa
from ahmad to AK
Yasa tafaki idon sarah tafara karantawa kamar haka
Nasan lokacinda zakaga wannan takardar kana nemana friend
kayi hakuri naso na sadaukar da soyayyata na auri sarah amma daga baya na fuskanci hakan bashida wani anfani
Nadauka idan nahakura da wacce nakeso na aureta komai zai wuce amma naji da kunnena tana cewa zaka saki asma'u idan na aureta
Friend kayi hakuri naboye maka gaskiyar lamarin amma ni ba asma'u nakeso ba
KHADEEJA kanwarta ita ce budurwata da ita muke soyayya baku fahimci abun yanda yadace bane
I am really sorry amma bazan iya gyara daya nabata goma ba
Bazan iya auren sarah narabu da khadeeja ba
Kai kuma daga karshe karabu da asma'u
Nasan zaka ji haushi amma kayi hakuri
I am sorry but i can't
Ur friend ....ahmad
Zufa ce taji tana karyomata lokacinda tagama karanta wasikar cike da tashin hankali take fadin na shiga uku ni aysha yanzu dama ba asma'u bace budurwan ahmad
boye takardar tayi aranta tana fadin ai wallahi bazan bari kusan da wannan zancan ba dama can naga takeken asma'u tafara jan hankalin AK inaga inyaji gaskiyar maganar nasan bazai saketa ba
AK na sauka kasa ita kuma tashigo hannunta yaja dakarfi yanufi sama da ita
Yanayin da taganshi aciki ya tsoratata tana magana amma yayi banza da ita se fizganta yake da karfi har tana neman faduwa
Sadiya takalli ladidi tana fadin wai meyake faruwa ne
Dariya ladidi tayi tace ango ne ya gudu annemesa anrasa
Tashi tayi tanufi bangaren grany tana murmushin mugunta tace bari naje nagayama tsohuwar can Allah sa ma hawan jininta yatashi tamutu muhuta
Tana isa bangaren grany tafara kukan munafunci tana fadin grany munshiga uku za'akunyataki gaban baki
Daure fuska grany tayi tace kunya takare akanki meyafaru
Ahmad ya gudu yace yafasa auren sarah
Jiri ne yadibi grany inna ameena ta tarota tazaunar da ita kan kujera
Bayan wani dan lokaci tasauke ajiyar tana salati tace shikenan haka Allah yakaddara amma ahmad bai kyewta ba yasan bazaiyi auren nan ba meyasa bai fada tun wuri ba gashi yanzu muntara mutane mezamuce masu
Cike da takaici sadiya ke kallonta ahasale tace wai grany bakiji komai ba
Inna ameena tamaka mata harara tace to munafuka mai bakin labari me kike so taji
Juyawa tayi tana jan tsaki tabar wurin
AK na shiga daki ya wurga asma'u kan gado kusa da sarah cikin kakkausar murya yace daga ina kike ina ahmad
Cikin rawar murya tace meyafaru ...
Shako wuyanta sarah tayi tabaya tana fadin
Book Chapters
Chapter 13
Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35