You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ya kwace yafara shafa ma kansa
bathroom tawuce tayi shirin kwanciya cikin kayan baccinta wando da riga mai dogon hannu
Bayan tagama tafito yana kuance kan gado yarufa da bargo
Tsaye tayi daga gefe tana kallonsa idonsa arufe amma da alamun damuwa afuskansa kamar daga sama taji yace
Malama idan abun kallo kike nema ga TV can ki kunna stop staring at me
Saurin barin wurin tayi tanufi bookshelf( drowan litattafai) din dake jikin bangon dakin daga gefe tana fadin
ina ai ni bana kallo da daddare sedai nayi karatu
Wani storybook tadauko tadawo kan stool tazauna tafara karantawa afili sedaga baya tagane tatsuniyoyin naban tsoro ne
Shiru AK yayi yana kara cusa kansa cikin bargo
Kallonsa take tana kunshe dariyarta tacigaba da karantawa cikin muryan ban tsoro tace
Dazaran yamma tayi se kowa ya kulle kofarsa saboda wannan aljanan tana yawo cikin dare duk Wanda tahadu dashi to yagama yawo
Wannan tsohon yana kuance cikin dakinsa yalulluba dabargo yana karkarwa gashi garin ana wata irin iska mai karfi kamar daga sama yaji ana bugamasa kofa dakarfi .....
Daidai nan grany ta aiko Rebeka da wayan asma'u takamata kawai sukaji bugun kofa
atsorace AK yafito dakansa daga cikin bargo yana kallon asma'u itama adan tsoracen take kallonsa
atare suka juya suna kallon kofa
Dariya asma'u tayi tana kallon AK tace wai yanaga kamar katsorata ne to bari na aje
Daure fuska yayi yana gyara kuanciyarsa yace tsoron me zanji awannen shirmen
cigaba tayi dakarantawa ...
atsorace tsohon nan yatashi zaune jikinshi narawa jin ba akara buga kofan ba yasa yakoma yakuanta can anjima yakara jin anbuga kofar dakarfi ....
daidai nan Rebeka takara kuankuasa kofar
Wannan karon gaba dayan su sunkasa boye tsoronsu
kallon AK tayi tana hadiye yawu tace ABI kaima kaji buga kofar koni kadai keji
tashi zaune yayi yana fadin naji mana to amma waye zaizo awannan Daren
Jin shiru ba abude ba yasa rabeka tatura kofar ahankali ta ijiye wayar kusan TV tafita
ai sunaji anbude kofa asma'u tadaka tsalle tafada kan AK atsorace yaja bargon yarufesu tana kankame dashi har suna musayar nunfashi
cikin rada yace inajin motsi anan dakin
Itama cikin rada tace banan dakin bane Palo ne kuma kamar anfita muje muduba
Ahankali yafito dakansa daga cikin bargon yana bin dakin dakallo ganin bakowa yasa ya sauko ahankali daga kan gadon
Itama tasauko suka nufi kofa
turata yayi gaba yakoma baya yana fadin lady first
Saurin dawowa baya tayi tana fadin to ai kai namiji ne kamata yayi ma kace inzauna kaje kaduba
Wata wahalalliyar dariya yana kara turata gaba yace
to ai saboda naga yawanci nabaya akafi fara cabkewa shiyasa nasaki gaba
wata zungureriyar kwalba tadauka tarike ahannunta dayan kuma tana bude kofar dashi
seda suka dudduba ko ina bakowa sannan taga wayarta akan table
Ijiye kwalban tayi tadauki wayarta tana kallon AK tace kamar wayata aka kawofa
Murmushin yake yayi yana waskewa yace dama ai nasan ba komai kawai ina gwadaki ne naga ko kinada tsoro ashe ke matsoraciya ce
kallon ka rainamun hankali take mai seda yagama sannan tasaki yar kara atsorace tana nuna bayansa
Haba lokaci guda yadaka tsalle se gashi agabanta
Dariya tafara mishi harda rike ciki tawuce daki
Binbayanta yayi yana murmushi
Suna shiga daki yadauke blanket dinta daga kasa yadora kan gado
daukan blanket din tayi tana fadin miye haka malan
kwace blanket din yayi yadora kan gado yace nan zaki kuana yau kina tare mun hanya idan natashi dasafe
buga kafa tafarayi dakasa tana fadin ni gaskiya ban yardaba daacan bakace haka ba seyau dakake jin tsoro
pilulluka yajera atsakiyar gadon ya kuanta yana fadin ga wurinkinan ki kuanta idan ma kina tunanin wuri daya nakeso mukuana
Kuma kika ki allah gobe zan gayama grany gaskiya akan aurenmu
zagayawa tayi takuanta tana zunbura baki
Murmushi yayi yana Jan bargo yajiyo yana kallonta yace chitti
Kyaleni.....
Tafada tana juya baya
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣1⃣5⃣
Gyara zamansa yayi yana kallonta dakyew yace aysha ni nakasa gane wannan lamari abun yadaina bani mamaki yafara bani tsoro tunda naga AK ya yima sarah haka akan yarinyarnan to tabbas akwai wani Abu atsakaninsu
sadiya tace nima dai haka nagani Abba aysha halin da namiji ne bakisani ba yarinya kar azo garin kallon ruwa kwado yamana kafa tanadin da mukayi shekara da shekaru yazo yaruguje mana muzama yan kallo
Dariya aysha tayi tana tafa hannu tace kai wallahi kun ban dariya ai wallahi ba Wanda zaishiga tsakanina da AK koda kuwa grany ce dakanta bare wata banza wai asma'u
Ku kwantar da hankalinku dady insha allahu wannan dukiyar tamuce mu kadai bawanda zaicita se mu
dariya jamilu yayi harda kyajyatawa yace ai nasanki ya'ta bakya wasa kunsan me duk lokacinda narufe idona kawai jina nake natashi daga jamilu nadawo jamil hausawee
Dariya sadiya tayi tace ni kuma Mr's jamil hausawee
Mikewa aysha tayi tafita tana fadin ni kuma Mr's AK hausawee
ladidi da bashir ne zaune adaki suna fira
ladidi tace wai kai bashir har yanzu ba'abaka albashinka bane
Murmushin gefe yayi yace to in anbani meza'ayi dashi badai inbaki ba
Daure fuska tayi tace kai kar kamun rashin kunya kaji ko wai kai kodan ciwa ciwa da babakere dinnan ma duk baka iya ba company nan fa nakune kabude aljihunka kadiba kudi amma katsaya wasa
Girgiza kai yayi yace a'a mama nifa ba abunda yakaini wurin ba kenan nayarad idan ina son kudi intambayi AK yabani amma bawai insata ba
" yo wayace kayi sata kai kowafa daka gani agidannan tasa ce takawosa kowa soyake yakwasa na kwasa kafin ayi waje dashi
saboda haka kaima kasan nayi gaka jamilu da wannan kinibabbar matar tasa allah kadai yasan abunda aysha ke kwaso masu a aljihun AK
amma kai katsaya wasa to tsaya kaji dazaran AK ya auri aysha to tamu takare agidannan dan wallahi gaba daya kawye zasu maidamu daga ita se iyayanta ne zasu muri wannan dukiyar
yashi yayi yana fadin insha allahu ma bazai aureta ba dan da ace matar nan tasa ta kile irin yan duniyan nan ne to wallahi ko kallon aysha bazai yi ba
tsaki tayi tana binsa da kallo har yafita sannan tace aikin banza ana ga maciji kana ga tsutsa dadin ya'mace kenan wallahi da ameena na nan dayanzu ta taimaka mun ga salma tayi Karama bata San komai ba ...
sarah na kuance kan gado da photon ahmad ahannunta tana kallo idonta sunyi ja sun kunbura tun hawaye nazuba har sun kafe
Tunowa tayi da AK kefadin wai tahakura da ahmad tunda khadeeja zai aura
Wurgi tayi da photon tafara wawwatsa kayan dakin tana fadin ina bazai yuwu ba sedai idan bana raye bawacce ta isa ta auri ahmad seni
Kwalba tadauka tarusa madubin dressing mirror tasulale akasa cikin dasashshiyar muryanta tana fadin
nawa ne nikadai ....ni kadai nake sonshi...kuma ni zan aureshi...inba haka ba zan mutu
Wayarta ta dauka takira numban khadeeja
bugu biyu tadaga tare da sallama
Shiru tayi nadan lokaci sannan cikin dasashshiyar murya tace
sarah ce nakira namiki barka ina tayaki murnan samun ahmad amatsayin mijinki amma ni kuma zanbaku wedding gift din sekun mutu baku manta dani ba kigayama ahmad idan har bashi arayuwata to batada wani anfani
tana kainan takatse kiran
mamaki ne Yakama khadeeja tana maimaita wedding gift
saurin kiran asma'u tayi tana dauka tagayamata yanda sukayi da sarah
atsorace asma'u tamike tana fadin me sarah zata aikata
ohh my god ....tafada tana fitowa dagudu daga dakin
aguje tanufi dakin sarah tana bugamata kofa amma shiru
aysha ce yazo wucewa tadawo tana fadin malama lafiya what is ur problem
Banza tayi da ita takwala ma nura kira yazo suka fara balla kofar
aguje tafada dakin sedai cak tatsaya tana kallon sarah dake kuance ga hannunta duk jni alamun yanka awurin
Durkushewa tayi akusa da ita tana kuka aysha ma hannu tadora akai tafashe da kuka
ganin jinin baitsayaba yasa asma'u tayi saurin yaga gualenta tadaure wurin sannan aysha ta taimaka mata suka kaita mota se asibiti
Suna zuwa aysha takira AK awaya seda takusa katsewa yadaga yana fadin baby I am busy zan kiraki anjima
Cikin rawar murya tace AK sarah ta kashe kanta kayi sawri kazo asibiti
Dariya yayi yakatse kiran yana kallon ahmad dake kusa dashi yace kaji wani shirme wai sarah takashe kanta
azabure ahmad yamike yana salati yace AK yana yiwa dagaske ne kasan sarah fa bata iya shiga damuwa ba
"No wasa ne nasan aysha tana mun irin wannan wasan in tanason ganina
Girgiza kai ahmad yayi yace a'a AK nifa tsoro nakeji kar azo dagaskene kakira grany ko asma'u mana
Wayansa yadauka ya lalubo numban asma'u dayayi saving da chitti yakira
yana fara ringing tadaga tana fadin ABI ina kashiga ina kiranka bana samu
kazo asibiti sarah bata jin dadi
Azabure yamike yana fadin meyasami sarah kina nufin dagaske tamutu
cikin rawar murya tace a'a bata mutu ba ABI kaidai kawai kazo
aguje yafita daga office ahmad nabinsa abaya
Cikin minti 30 suka iso asibiti yana isa doctor nafitowa wurinsa suka nufa atare suna tambayar ya jikinta
Kallonsu yayi daya bayan daya sannan yace dafari dai inaso insan wa yadaure mata hannu da kyalle
baigama rufe baki ba aysha tayi saurin nuna asma'u dayatsa tana fadin wannan ce
juyawa sukayi atare suna kallonta sanan suka maida kallonsu kan doctor
itama asma'u kallonsa take dafargaban abunda zaifada
Murmushi yayi yana kallonta yace gaskiya kinyi dubara mai kyew saboda badan kinyi hakan ba da kafin kuzonan tarasa jni mai yawa kuma jijiyarta zata ita bushewa ko iska yakai ga zuciyarta hakan kuma shi zaisa tarasa ranta amma yanzu alhamdulillah taji sauki zaku iya shiga kuganta sedai akula irin haka kar takara faruwa
Sannan yakalli AK yace muje office ina son ganinka
gaba yayi AK da ahmad suka bisa abaya aysha kuma tashiga dakin da sarah take
Nuance take tana kallon sama hawaye nazuba a idonta ga igiyar Karin jini ana mata
se hannunta da aka ma bandage
Kusa da ita aysha tazauna tana fadin sannu sarah gaskiya AK bai kyewta miki ba koda yake ba laifinsa bane wannan munafukar yarinyar ce tasashi wayasan metagayamasa ...
Muryan asma'u tajiyo tana fadin tashi kifita
Juyowa tayi tana hararenta tace dawa kike kehar kin isa kice nafita
dan karamin table din da ake dora magunguna ta rarumo tanufota dashi bashiri tayi waje aguje har tana bigewa da kofa
ijiye table din asma'u tayi takarasa kusan gadon tana duba hannun sarah
Kwace hannunta tayi tana fadin wayace ki kawoni asibiti meyasa baki bari namutu ba tunda natabbata abunda kike so kenan
Kusa da ita asma'u tazauna tana fadin sarah kina bani mamaki idan kikayi wani abun kamar wacce batayi karatu ba yanzu idan kika kashe kanki riban me zakici Wanda kikayi danshi zai danyi jimamin lokaci kadan daga baya kuma yamanta yayi aurensa yacigaba da rayuwar farinciki
Yanzu dazan tambayeki da allah da ahmad wakika fiso zakice allah amma kuma kinyi kokarin aikata laifin da allah bazai yafemaki ba saboda ahmad
Akan rayuwar duniya kikayi kokarin ruguza ta lahirarki
Miye laifin AK dazaki daga mai hankali yana matukar kokari wurin faranta miki amma ke kanki kawai kika sani bakya tunanin halin dazai shiga idan kika aikata wannan kazamin aiki
Sarah kefa macece mata ansansu da juriya da danne soyayya aransu saboda gudun wulakanci amma ke kinkasa yin hakan shiyasa kike wahala
Ki godewa allah dayabarki da ranki yana sonki shiyasa baidauki rankiba yabaki dama akaro nabiyu dan kyallen danasa maki bashi yahanaki mutuwa ba lokacinkine baiyiba
Bakowa yakesamun irin damar dakika samu ba yau da kin mutu da zaki dawwama kina nadama har abada
ina gayamiki hakane ba amatsayin asma'un dakika tsana ba
Ina gayamikine amatsayin musulma kuma mace yar uwarki
Ga glass nan da wukake kina iya dauka kikara yanka hannunki ko wuyanki amma kisani ba kyada hujjar dazata hana allah yakonaki
tana kainan ta tashi ta fita daga dakin
Tana fita AK da ahmad nashigowa aguje AK yakarasa bakin gadon yana kallonta cikin rawar murya yake fadin
sarah why!! Why sarh!! Why!!
yakasa cigaba da maganarsa se hawaye dake zuba daga idonsa
Itama kukan take tana fadin yaya i am sorry
dafasa ahmad yayi yace friend kaje waje zanyi magana da ita
fita AK yayi yana sharan kwalla gefe guda yaje yazauna hade da dafe kai
AK nafita ahmad yadawo kusan sarah yazauna cikin sassanyar murya yace
Sarah base kinfadamun dalilin dayasa kika aikata hakan ba nasan saboda kinji zanyi aure shiyasa
Na fahimci halin da kike ciki saboda nima nashiga wannan yanayin abaya
sarah nasan kina sona kuma nagode da kaunarki agareni amma bayanda na iya sarah
Ina miki kallon kanwata ne kuma kawata idan kika hakura kika manta dakomai zanci gaba da kallonki ahakan amma idan kika kara aikata wani abun to zaki rasa wannan matsayin awurina
Shiru tayi tana kallonsa takasa cewa komai
tashi asma'u tayi tanufi inda AK kezaune tazauan kusa dashi
Dagowa yayi yakalleta yakara maida kansa kasa
ahankali takai hannunta tadafa kafadansa cikin sigar lallashi tace
kar kadamu kaji she will be fine
dagowa yayi yana kallonta da jajayen idanuwasa cikin rawar murya yace chitti meyasa sarah zatayi abunda ko jahili bazai yiba meyasa zata zabi tarabu dakowa nata tahadu da fushin ubangiji akan tarasa ahmad
bazatayi tunanin halin da zan shiga ba bana kewar iyayenmu saboda ita da grany aduk lokacinda nakalleta fuskan ummarmu nake gani atata
hawayene suka zubo daga idanuwansa yacigaba dafadin
Chitti nasan zakiyi tunanin nabata sarah dayawa ko duk abunda takeso ina mata kinsan dalili ?
Girgiza kai tayi hawayen datake makalewa suka zubo
cije lebensa nakasa yayi yana saita muryansa yace
Tun ina karami nataso ina son yima iyayena hidima inaso naga sunkawo bukatrsu namusu kodan naga murmushi afuskansu ta dalilina
Naci burin yi musu hidima na kyewtata musu in sungirma amma allah bai kaddara ba
Kinga sarah to yadda take haka ummana take ita kuma grany sak yanda take haka abbana yake
daga ranar da suka rasu daga ranar duk wani son danake masu da burin kyewtata masun danake yakoma kan sarah da grany haka nataso har kawo wannan lokacin banason ganin abunda yabata musu rai ko sun nemi Abu sun rasa amma gashi yau nakasa wurin farantama kanwata ...muryanshi ne yakarye yakasa cigaba damagana
Hannu takai tana share mai hawaye cikin muryan kuka tace
ABI kai ba allah bane mutum ne duk yanda kaso ka kyewtata musu dole wata rana sunemi wani abunda su rasa kuma dama haka rayuwa take kowa kaduba akwai abunda yakeso yakasa samu
ABI u are not just a brother but u are a real hero
kayi ita kokarinka sauran kuma sekabarma allah amma please stop blaming ur self
Gyara zamanta tayi tana kallonsa cikin sigar tsokana tace
Yanaga kayi saurin karayane ko kamanta maganr damukayi jiya idan bazaka iya samomata ba ni kabani dama nasamo mata handsome guy
Murmushi yayi yace a'a nizan zaba dakaina ke kinsan handsome ne
haka kawai kije kidaukomata dan jagaliya murasa yazamuyi dashi
Kwaikwayon yadda aysha tashigo jiya tayi tana fadin
wai me kadaukeni ne naga fa kana nema karaina mun class dina
Dariya yayi yace to ya isa masoyiyar tawa kike kwaikwayo komai abunki dai bazaki kaita haduwa ba
"Allah sedai in banyi niyya ba abun ai ba wuya ne dashiba nidai kawai banda lokacinsa ne
tashi yayi suka nufi dakin sarah
Rungumeshi tayi tana kuka tace
Yaya na amince nahakura ahmad ya auri khadeeja
Dagota yayi da mamki yace dagaske kin amince amma abunda da mamaki da zaki kashe kanki yanzu kuma kin amince kodai kin hango malakal mauti ne
kara rungumesa tayi tana murmushi tace Yaya kabari banaso
dariya sukasa gaba dayansu banda aysha dake jifan sarah da kallon tuhuma
Dagowa tayi tana kallon asma'u tace sister nagode dakika ganar dani abunda nakasa ganewa tun tuni
Gaskiya ke tadabance thank u once again
Juyowa AK yayi yana kallon asma'u da murmushi afuskansa
Sunkuy dakanta tayi itama tana murmushin
Da yamma aka sallemesu suka dawo gida dakin sarah suka fara zuwa seda ta kwanta sannan suka fita akabari daga ita se aysha
Bayan kowa yafita aysha tazo tarufe kofar da key takoma kusan sarah da mamaki tace sarah what is ur plan?
kauda kai sarah tayi tace kamar ya ?
"Hahaha sarah kar kirainamun hankali nafasanki kamar yunwar cikina u won't give up easily
Ya akayi haka
Share hawayenta tayi tace to aysha yazanyi ahmad yariga yazama na khadeeja Dana tsaya inaba kaina wahala ba gara nafita hanyarsu ba nima nayi addu'ar allah yabani mijinagari
Hanyar fita aysha tanufa tana fadin kin bani mamaki sarah Ashe bama son Ahmad kike ba kawai cika baki ne
Dakallo sarah tabita har tafita sannan tarufe idonta ahankali hawaye nagangarowa gefen fuskarta
Aysha nafita wurin AK tanufa yana zaune apalo ta iskosa kusa dashi tazauan tana shagwabe fuska tace darling wai mekake jira da yarinyar nan ne naga bakada niyyar korarta daga gidannan
Gefen fuskanta yashafo yana murmushi yace aysha kifahimci halin da grany take ciki kinsan tana son asma'u dayawa to kafin in rabu da ita ina bukatar hujja ko dalilin dazan kare kaina dashi awurin grany idan bahaka ba gaskiya bazan iya sakinta haka kawai ba
to mezan gayama iyayenta idan ita tasan dalilin dayasa na aureta su basu saniba
Murmushi tayi tace OK I understand amma dan allah kadaina shishshige mata dazu fa ina ganin lokacinda kuke dariya a asibiti
Nidai gaskiya kadaina sake mata fuska kaga tafara raina mutane tun ba'aje ko inaba
kauda kai yayi yana fadin nasan menakeyi base kin gayamun yadda zan zauna da ita ba
Yana kainan yamike yanufi masallaci
Dakallo tabisa har yafita sannan ta tashi ahasale tawuce dakinta
dakarfi ta tura kofar dakin tashiga tana fadin ina bazai yuwu ba wallahi wannan ai shirmene
dolema nasan abinyi ina ganin abun kamar wasa gashi yafara zama babbar barazana wa farin cikina """"
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣2⃣0⃣
Da yamma aysha taraka sarah gidansu asma'u taje Neman khadeeja
Bayan sungaisa dasu Umma khadeeja tarakosu har waje
Juyowa sarah tayi tana kallonta da murmushi afuskanta tace to deeja nizan tafi se kinzo gobe
kauda kai tayi tana daure fuska tace allah ya kaimu
ahasale aysha taja hannun sarah tana fadin wai sarah meyake damunki ne kintsaya karamar yarinya tana daddaure maki fuska kar allah sa tazo
Kwace hannunta tayi tana daka mata tsawa tace aysha ya isa haka karkimanta matsayinta awurina so behave ur self
Dariya khadeeja tayi tadawo gaban aysha tatsaya tana fadin
malama dafarko dai inaso kisan bani nagayyace Ku gidanmu ba so dole zaku Bini aduk yadda nakarbeku ku idan kinga bazaki iya ba hanya abude take
Sannan tajuyo wurin sarah tace ke kuma sarah ina so kisan cewa koda gaba daya mutanen duniya zasu yarda da canzawarki to ni khadeeja bazan fada tarkonki ba
Saboda nasan people like u won't change easily
nasan kina da wata buyayyar manufa akan wannan fuskar mutuncin dakika ara
nunata tayi dayatsa tace
let me worn u sarah if u dare do something terrible to me or my sister I will make ur life a living hell that's my promise
tana kainan tajuya tabarsu atsaye suna binta da kallo har tashige ciki sannan sarah tajuya jiki asanyaye tashiga mota aysha tabita tana jan dogon tsaki
AK na zaune apalo asma'u tashigo tana kwasan gyalenta tawuce takusan shi zata shiga daki hannunta yakamo yajuyo da ita gabansa yana fadin zo nan hajajju ina so in tambayeki wani abu
zaunawa tayi daga kasa suna fuskantar juna takure shi da ido batace komai ba kallon kallon suka farayi nadan lokaci kana yaja nunfashi yana Sosa kai yace mema zan tambayeki ?
tashi tayi tana fadin bari natafi inada abun yi idan katuna seka kirani
Janyota yayi yazaunar da ita yana fadin a'a dawo natuna nace wai me kika gayama sarah ne har tayi saurin gane abunda najima ina kuatanta mata
murmushi tayi tace ni nama manta abunda nagayamata kawai dai magana namata kuma banmasan zata dauki abunda nafada ba
kankance ido yayi yana kallonta yace um um chitti a iya sanina sarah ta tsaneki bata sonki amma ya akayi lokaci guda tafadi magana mai dadi akanki anya kwa ba magic dinnan naki kika mata ba kuwa ni kikoyamun yanda ake nama grany tafarayin duk abunda nakeso
Dariya tayi tace wane magic kuma nidai bawannan ba gaskiya ABI bai kamata ayi bikin khadeeja anan gidan ba duk da sarah tahakura amma bazataji dadi ba
zaiyi magana kenan sukaji sarah nafadin
Ba abunda zanji sister anan zamuyi bikin kanwarmu kamar yadda Yaya yafada
Juyawa sukayi suna kallonta da murmushi afuskansu
Karasowa tayi kusa da AK tazauna tana kallon asma'u tace bama wannan ba sis kushirya gobe da daddare nahada dan kwarya kwayan party wa ahmad da khadeeja saboda inaso musanar da abokanansa da kawayanta zancan bikinsu kuma natayasu murnan cimma burinsu
kallonta AK yayi cike da tausayi yace kintabbata ba wata matsala sarah can u bear it ?
Dafashi tayi tana dariya tace Yaya come on I am not a kid ko kuma Baku yarda nahakura bane
murmushi sukayi suna kallonta basuce komai ba
da daddare har Sarah ta kuanta aysha ta iskota rai bace tace sarah ni nakasa ganeki wai ina sarahn da nasani wacce bata hakura da abunda takeso bare abunda nasan kinfi sonshi fiye da komai aduniya yaushe kika dawo hakane ko kema sallon yaudarar asma'u yayi tasiri akanki ne
Daure fuska tayi tana kallonta tace aysha waini wacece dabazan gyara rayuwata ba ko kafiri yakan musulunta yazama nagari bare ni me kika daukeni ne to nagaji da abunda kike mun kar ki kara mun wannan banzar tambayar kinji nafadamiki
ahasale tafita tana banko kofar dakarfi
washegari dasafe AK d nabangaren grany yana breakfast kan dining asma'u nagefensa azaune tana kokarin zuba kunu akofi amma takasa saboda hannunta da yayanke wurin girki
inna ameena nazaune daga gefe tana kallonsu
karasowa tayi wurinsa tana murmushi tace AK kaga asma'u tayanke dazu ahannunta kazubamata kunun mana kabata
kwarewa yayi yayi saurin daukan ruwa yakora yana kallonta da mamaki yace inna me ...mekikace ....nabata kunu fa
daure fuska tayi tace yo miye ba matarka bace kai gaka ahaka kamar zakayi soyayya amma ashe ko wayewar ma bakayi ba
Harara yajefa ma asma'u yana fadin to dabana nan waye zaibata kunun ko dolene ma setasha kunu
tafa hannu inna ameena tayi tana salati tace oh ni ameenatu menakeji haka kamar gwaranci abakin AK
amma wallahi kabani kunya se anyi magana kuce mana yan zamanin da to mudai bahaka mazan mu ke mana ba
Kallon asma'u tayi tana fadin baiwar allah shiyasa da daddare sena koreki kike tafiya allah kadai yasan me yake miki
labace baki asma'u tayi kamar zatayi kuka tace inna infadamiki wani Abu
Zaunawa inna ameena tayi kan kujera tana fadin inajinki asma'u menene
"Jiya ma haka ya.....
bata karasa ba yayi saurin fadin
OK fine....zan bata abar zancan
gyada kai inna ameena tayi tana fadin dadai yafi maka inba haka ba yanzu nakira grany asma'u tafadi komai agabanta
Kofin kunun ya fizge ahnnun asma'u yana ji kamar yarusa mata shi abaki seda yafaki idonsu ya ciko cokali da barkono ya zuba cikin kunun ya juya yana murmushin mugunta yakai kofin bakin asma'u yana fadin enjoy ur self baby !!!
Kurban farko taji kunnanta ya amsa saboda yaji
saurin janye bakinta tayi tana kallonsa
Murmushi yayi yakara kai kofin bakinta yana fadin drink it badai kunu kike soba
kallon inna ameena yayi yace kinga ai halin matan kenan tace kunu yanzu kuma nafara bata tana nuna bataso
hannunsa asma'u takama takai kofin bakinta tana shan kunun kamar ba komai aciki
Da mamaki yake kallonta seda tayi rabi sannan takai kofin bakinsa tana lashe baki tace to kaima kasha darling!!
zaro ido yayi yana kokarin kauce bakinsa inna ameena tace kai kasha mana yau naga sakaran yaro
asma'u zatayi magana kenan yayi saurin kama hannunta ya kai kunun bakinsa ya kurba
saurin hadiyewa yayi ya kauda kai gefe yana huddo harshe
Kallonsa inna ameena tayi da mamaki tace wai yanaga kana Abu kamar dayaji akunun ne
dariya asma'u tayi tace inna yaji ya....
bata karasa ba yayi saurin katseta dafadin kaji inna kuma mezai kawo yaji cikin kunu waima banaji grany nakiranki ba kitashi kije mana zamu
Book Chapters
Chapter 16
Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35