Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

KAZAR KARFI--> 01
.
SHAFI'U DAUDA GIWA
.
AMADU BALIGI" shine shugaban
matasan dake tashar dan
amarya" tun a shekarun baya
kafin siyasa ta kankama shine
saurayin dake fada aji a hanyoyi
da dama
Alal misali Idan aikin gayya ta
taso za'a gyara hanyoyin
kauyensu a fitar da magudanan
ruwa Amadu baligi shine akan
gaba wajen gayyato matasa da
karuwai ako ina da kuma nemo
makada wadanda zasu dinga
gabzar ganguna suna karawa
ma'aikatan kwarin gwiwar kartar
kasa suna ihu da kirari
.
Idan kaka tayi aka kawar da amfanin gona aka kawo gida
Amadu baligi shine yake fita ya
nemo mawaka da 'yan rawa suzo kauyensu su kafa dandali a
wani gidan danni wanda idan dare yayi aka tayar da karamin
jannareto aka fara waka da cashewa samarin dake lardina na nesa dana kusa sukan zo su biya
kudi su shiga suyi kallo da lika
kudi kuma idan aka gama waka
da safe komai aka samu Amadu
baligi yake tarawa ya sallami
mawakin da yaransa" sannan
sauran abinda ya ragu kuma nasa ne
Idan mutane suka fara gajiya da
wake-wake sai Amadu baligi ya
kafa gidan dambe ko kokawa
wanda anfi samun alkairi don
kuwa masu kudin kauyen sukan
sa gasar babura da shanu gaduk
jarumin da yayi kisa mai kyau"
kuma kome aka samu ta hannun
Amadu baligi yake biyowa"
.
Sanin kowa ne cewar duk wata
sabuwar karuwar da tazo tashar
dan amarya" dole ne Amadu
baligi yasan da zuwanta" a
matsayinsa na shugaban matasa"
ko kuma shugaban 'yan iska"
kamar yadda dattawan dake da
mutunci a kauyen suke kiransa"
.
Amadu baligi gwani ne shi kanshi
wajen dambe da kokawa" yasha
fita wasa har xuwa jamhuriyar
nijar kuma yayi kaye da kisa ba
sau daya ko sau biyu ba" Ganin yafi samun alheri a gida wajen
jagorancin duk wani aikin tabara
ya sashi ya kwance wa hannu sa damara ya dawo yana shugabantar matasa duk abinda yace shi akeyi a kauyen"
.
"To amma tun sanda siyasa ta
kankama sai Amadu baligi ya fara samun fada a wajen
shugabannin kauyukka musamman ciyamomi da
kansiloli Idan shugaba yazo
kamfen dole ya fara neman Amadu baligi don kuwa shine
muryar matasa Idan akayi nasara aka kafa gwamnati" Amadu baligi yana samun alheri"
don kuwa yana samun kyautar
kudi da sabbin babura akai-akai
wasu suna cewa duk wata yana
samun kudi a wajen 'yan siyasa fiye da naira dubu dari da
hamsin
mutane idan sukaji haka zasuyi zaton duk a fadin lardin tashar dan amarya babu wani matashi
mai kudin Amadu baligi to amma a zahiri abin ba haka yake ba don kuwa sau da yawa
sutura takan yankewa saurayin
kuma yasha kwana bashi da ko
anini saiya roki na karin kumallo
a wajen mutane
.
Tayaya kuwa kudi zasu zaunawa
Amadu baligi bayan kullum idan
ya zauna a tamfal din caca tun
safe baya tashi sai dare yayi" su
kunna fitila karuwansa shida a
garin" kuma kowacce saiya bata
kudin cefane kullum tunda dai ya hanasu mu'amala da
kowanni namiji shiyasa kudi basa rayuwa a hannunsa kamar yadda wuta bata rayuwa cikin
ruwa
.
Amadu ya samo sunansa na BALIGI ne tun yana yaro dan
shekara sha biyu" wannan ya
samo asali ne a zamanin da yke
shiga cikin manyan kartin dake
zuwa kamun gafiya a kauyen wadanda basa yadda yara suna
binsu sai Baligai tsararrakinsu"
.
Babu irin dukan da Amadu
baisha ba a wajen azzaluman
kartin kauyen wadanda suke
korarshi ya koma gida idan ya
biyo su shi kuma yana sake binsu
A ranar da wani a cikinsu yace
dashi basa zuwa kamun gafiya
tare da yara sai "BALIGAI" sai
Amadu yace dashi-
"Nima ai "BALIGI" Ne!
Fadar hakan ya bawa kowa dariya a cikin kartin kuma tun
daga lokacin suka 'yantashi ya
rika binsu din kamun gafiya yana
yi msu kananan aikace-aikace"
dangin debo ruwa a rafi da
kuma iza wutar gasa nama idan
sunyi sa'ar kama abubuwan da
suka fita nema a ramukan da ke
a bayan garin
Kamar yadda kowanne mutum a
duniya yake da ka'idojin aikinsa
ko sana'arsa haka shima Amadu
baligi yana da tasa dokar wacce
ta dade takai shekara da shekaru a kauyensu babu wanda ya isa ya karyata ko kuma ba'a
riga an samu wanda zai karyata ba har yanxu"
.
Dokar ita ce yana maraba da duk wata karuwa wacce ta sauka a garin komai tsufanta da
muninta" kamar yadda yasha
fada" Amma bai yarda wata
"GILLI" tazo ta zauna ba kuma bai yarda wani yazo da ita garin ya ajiyeta ba"
.
Sau da yawa wadanda basa
cikin harkar bariki dole ne sai nayi musu dogon bayani kafin su iya bambance tsakanin
"KARUWA" da "GILLI"
.
KARUWAI-: Sune wadanda suke
fitowa yawon dandi bayan sun taba yin aure sun fito"
.
GILLI-: Bata taba yin aure ba" yawancinsu yara ne kanana
wadanda shekarunsu ya kama daga goma sha hudu zuwa sha biyar" wadanda suke kangarewa su fito
shalli da sharholiya"
sune yawanci akan samu a rabe
tare da iyayen dakin su mata agidan karuwai saboda idonsu bai riga ya bude sun san yadda
rayuwar bariki take ba da yadda
ake samun kudi a wajen maza ba
.
Sune yawanci suke bin mawaka
sunayi musu rawa" 'yan kallo
suna manna musu kudi a goshi
Idan an tashi wasa a kawo kudin
abinci a basu su kama gabansu
ba tare da sun tsaya tunanin ko
nawa mawakin ya samu a
dalilinsu ba su dai ko ina dare yayi musu nan ne gidan su
kuma anan zasu kwana kamar
kajin turawa ne Idan mai kula
dasu ya mutu kowa nasu ne indai zai basu abinci ya faranta musu rai
.
Sune wadanda yarintar soyayyar
gida bata gama sakinsu ba ko
mutum bashi da kudi sai su like
mishi wani kuma yazo da kudi su zageshi ta uwa da uba irin wannan rashin hankali da rashin sanin mutuncin sana'a yake
yawan hadasu fada da manyan
karuwan dake rike dasu
wadanda suke basu wurin zama idan kaje gidan mata kaga
karuwa ta kama gilli tana lakada
mata duka kamar zata kasheta"
Ko kuma kaga ta debo kayanta ta
watso mata su waje tana zaginta to karka tsaya wahalar
tambayar kowa yadda akayi don
kuwa dalilin bai wuce kuruciyar
da gillolin suke yi ba wajen rashin ba masu kudi hadin kai
suna bin yara kanana wadanda basu da komai sai kodadden
wando da fasashen takalmi"
.
"To amma shi a bangaren Amadu
baligi ba rashin hankali ko yarintar gilla yasa baya son su zo kasarsa ba" haka kawai yaji baya
so yaga karamar yarinya ta fito
dandi duk da lalacewarsa baya
so yaga yara sun lalace" su dai
manya tunda sun riga sun gama
lalacewa to gwara abin ya tsaya a
kansu amma banda yara"
Amadu baligi kakkarfa ne baki
kuma mummuna wanda ko a jajayen idanunsa kawai aka tsaya ya isa ya tsorata duk wata mace
tabi umarninsa indai tana so ta zauna lafiya a kasarsa bai taba rabuwa da singileti ba da ita
yake kwana da ita yake tashi
kuma komai sanyi komai zafi
"To ko a lokacin da akayi bikinsa
a watannin baya tun ranar daurin auren har zuwa tashin
bikin da singileti ya gama angwancinsa ya shiga dakin
amaryarsa ba abinda ya dameshi"
.
Ana kan haka ne a yammacin
wata ranar lahadi yaje 'yar bajau
suna caca shi da mutanensa"
wani yaronsa mai suna "DAMMA"
yazo ya sameshi yace dashi
"Sarki kayi bakuwa fa a kasarka" Amadu baligi ya tambayeshi yana kallon kartar dake a hannunsa ba
tare da ya dago kanshi ba"
"wacece?"
Damma yayi murmushin
takadarancin abinda zai fa" wata GILLI ce" ina jin ba'a dade
da yayeta a nono ba"
Amadi baligi ya dago kanshi ya
kalli Damma yace dashi"
"kaje kace da ita ni sarki nace ta
gaggauta barin kasata tun kafin
inzo in sameta" kace da ita ta koma gida tun kafin muyi ido
biyu" "Damma ya koma ba'a jima ba ya
dawo wajen cacar yace da Amadu baligi sarki tace wai ba inda zataje ko
kasheta za'ayi
tun kafin Damma yakai karshe
Amadu baligi ya watsar da kartar
dake a hannunsa ya tashi cikin
sauri"
"muje inga kowacce 'yar iskar
yarinya ce wannan"
Damma ya takewa sarki baligi
baya suka nufi gidan karuwan
dake gefen garin nesa kadan da
gidajen matan aure"
.
*SUNANTA TALATU*
Sekarunta zasu iya zama kodai tsakanin goma sha hudu zuwa goma sha shida" tana
sanye da kodaddiyar atamfa mai
ruwan toka" wacce zaninta yasha yagewa anayi masa faci daga kasa"
Gajeriya ce" dirarra mai nagari
wacce kai tsaye bazai yiwu mutum ya yanke hukuncin fara
ya cancanta a kirata ko kuma baka ba
A yanayin fatarta fara ce" to amma wani abu da ya lullube
fatarta dake kama da rashin kwanciyar hankali da yunwa
shiya dabirta sakamakon da
mutum zai iya bata a kamaninta to koma dai me yake damunta
bazai yiwu ace da ita mummuna ce ba ko ba komai tana da
faffadar fuska wacce ke dauke da
manyan idanu da kuma dan
madaidaicin bakinta" tana da saurin fara'a da murmushi
bazata iya jure hada ido da mutum tsawon dakika uku ba ba tare data fara yi masa murmushi ba koda kuwa bata
taba ganin mutum ba
tana dauke da leda gari yayi zapi"
kuma ganin yadda ledar ta koshi fal kamar xata yage xa'a
fahimci kayanta ta zubo a ciki"
suturu da kuma 'yan abubuwan
da baza'a rasa ba" koda kuwa
mudubi ne da hoda"
.
"Tun shigowarta garin da dan
acaba ya kawota gidan matan"
saita sami gefe guda tayi tsaye
bata yiwa kowa magana ba" tana
kallon duk abubuwan dake kaiwa da komowa babu wacce
ta kalleta sau biyu a cikin tsofaffin karuwan dake a gidan" don kuwa sun san kowacece da
ganinta GILLI ce kuma ba zama zatayi ba" sunsan da SARKI
BALIGI yayi ido biyu da ita zai
koreta tabar garin kota shirya
kobata shirya ba"
Jefi-jefi mazan da basu nema da
mace a gidan sukanje inda take
suyi mata magana" amma bata
saki jiki da kowa ba" to dama dai
a haka suke zuwa da dan kullin kayansu suyi shiru ayita magana suna ji su wuni a zaune a waje
daya suna jin kunyar magana da
kowa" da an basu kwana uku zasu goge su zama 'yan gari"
wanda ya tafi ya barsu a haka da
sati ya zagayo inyazo zai samesu suna shan taba suna
rawa" don kuwa suna tare da
manyan shaidanu wadanda zasu
bude musu idanu su nuna musu bambancin rayuwar gida da kuma
RAYUWAR BARIKI
.
TALATU...KAZAR KARFI--> 02
.
TALATU tayi shiru taki magana
wannan bashi ne zaisa ace bazata shiga layi ba Da haka
suke farawa su dukkansu sai sun
gama ganin tafiyar ruwan kowa
daya bayan daya sannan zasu
fara yin tasu carar suma talatu tana nan tsaye a jikin
katangar gidan karuwan inda bai
gama rushewa ba ta sauyawa
ledar hannun kenan daga dama zuwa hagu saiga Amadu baligi ya shigo gidan a fusace tare da
Damma
.
Da shigowarsa gidan ya dubi
talatu tana tsaye dauke da
ledarta suka hada ido da ita
dashi tayi masa murmushi don
kuwa halinta ne dazun nan da
Damma yazo yace ta gudu kafin
sarki ya ganta tace bazata tafi
ba don haka yanzu ga sarkin yazo ya sameta Bayan sun gama kallon juna ita
da Baligi ba tare da jin tsoron
jajayen idanunsa ba da kuma
bakar fuskarsa wacce ke cike da
gargada da kwazazzaban duka a
wajen dambe sai yace da ita.
"ke bakiji sakona bane?"
talatu tace dashi cikin ladabi"
"wannan ya fada mini" talatu tace dashi"
"Indai bazaku barni in zauna anan
garin ba gwara ku kasheni in
huta da bakin cikin da ya sameni"
.
Maimakon baligi yaji tausayinta
sai yayi dariya kadan ya girgiza
kai" irin wannan tatsuniyar daba
bakin sabbin shigowa ya dade
yana jin irinsu" to amma karya
suke yi" su dukansu babu wacce zata so a tambayeta ta fadi
gaskiyar abinda ya fito da ita ta baro gida" komai zasu fada idan aka bincika za'a samu ba gaskiya
bane" wata zatazo tace iyayenta
ne suka mutu" marainiya ce babu
wanda yake kulawa da ita don
dai aji tausayinta a amsheta a bata wajen zama"
Wata zatace mijinta ne ya saketa"
kuma yake nemanta zai kasheta"
don haka tazo don buyar masa"
wata zatace auren dole za'ayi
mata kuma bata son wanda za'a
bata shiyasa ta gudu to amma fa zaiyi wahala idan aka bincika labarin ya zama gaskiya shiyasa
ga wanda ya saba da ganinsu indai bakuwar karuwa ce ko "GILLI" komai zasu fada ba abin
yadda bane kuma wanda ya tsaya bata lokacinsa akansu ya
tausaya musu shine babban shashasha a wajensu
.
Baligi ya kebe yarinyar a gepe
guda ya bar Damma a baya suka
koma kusa da wani sabon daki
da ake ginawa a gidan wanda ya
ruguje a kwanakin baya"
Daga inda suke tsaye a faffadan
gidan suna iya jin komai na
surutan da wasu karuwai hudu
suke yi tare da wani mai tsire a
tire wanda ya saba zuwa gidan
talla kullum"
.
"Talatu ta mayar da hankalinta
akan hayaniyar da matan sukeyi
da mai tsiren" tana so tayi
murmushi ga alama rayuwar matan yana birgeta" ganin yadda
suke da 'yancin yin komai babu
mai hanasu" A lokacin da take
kallon nasu ne Amadu baligi ya
fara yi mata magana"
"Ina so ki bude kunnenki da
kyau" kiji abinda zan fada maki"
Ya kara kausasa muryarsa da
yaga kamar bashi take saurare ba"
"Sunana Amadu Baligi"
Yace da ita
"Nasan wata kila kin taba jin labarina a garinku
To idan ma baki taba ji ba yanzun nan zan fada maki don
kisan koni wanene!"
Nine shugaban duk wani takadari dake a wannan gari
namu" An bani wannan sarautar
kuma na Amsheta da hannu bibbiyu"
Baligi ya saurara" sannan yace da
yarinyar
"Nasan abinda ya kawoki wannan garin" bana bukatar
saikin fada min komai" to amma abinda nakeso dake
shine" ki koma gida wajen iyayenki ki rokesu gafara su
yafe miki...
Zaman bariki ba
zaman arxiki bane" muma da
kika ganmu nan a ciki don kawai abin ya zame mana bala'i ne"
amma ba dadi muke ji ba don
haka kiyi sauri ki koma yanzu-yanzun nan tun kafin dare yayi miki" banason ganinki anan!
"Talatu ta juya tana sauraron kalaman wannan kato wanda
batasan koshi wanene ba a gidan"
Amma dai da ganin yadda kowa
yake tsoronsa ga alama shine
sarki kamar yadda ya fada"
batayi masa magana ba tadai
girgiza kanta sau daya alamar ta
gamsu da bayaninshi
.
"Duk wadannan matan da kike
gani anan indai zaki tambayesu
su fada maki gaskiya" na tabbata
wannan magana dana fada maki
irinta suma zamu fada miki duk
lokacin da mace ta gudu tabar
iyayenta cikin fushi da takaici" to
duk inda zata shiga a duniya"
kuma kome zata zama bazata
taba gamawa da duniya lafiya
ba idan kuma kina jin karya
nake yi kiyi tunani a zuciyarki ki
gani" wacce mace ce ta taba yin
yawon dandi da sharholiya tayi
karshe mai kyau ?
Indai ba dainawa tayi ta zama
mutuniyar kirki ba tayi aure toki
zura mara ido kina nan zaki ga
yadda karshenta zaizo a wulakance
kada kiyi la'akari da yadda manyan karuwai suke gina
gidaje suke shiga manyan motoci suke dinka suturun kece
raini suna kashe kudi kiyi zaton
zasu dauwama a haka bazasu
taba dauwama ba wahalar da suke gudu har suka zabi yin karuwanci tana nan biye da su
kuma komai dadewa indai suna a cikin harkar sai sun wulakanta
wannan dole ne muda muke
cikin wannan harka mun san
illolinta ciki da waje shiyasa nake fada miki don ke ma ki
sani ki koma garinku tun kafin
ma ki fara har wani ya bata ki a banza
TO" akwai alamar taurin kai a
muryarta a karshe Amadu baligi
yace da ita
"kada kiyi tunanin idan kinki
komawa gida kin canza gari
bazan sani ba duk inda kika
shiga a fadin kasar nan indai
yawon dandi zakiyi dole ne in
sami labarinki kuma ko ina kika
shiga saina biki na kamaki
saboda haka ki koma gida ni SARKI BALIGI na haramta miki
dandi a duniya kuma dole ne kibi Umarnina ko kina so ko bakya so
.
Bayan Amadu baligi ya gama jan kunnen talatu sai ya tambayeta
"Kina da kudin motar komawa garinku ?
ta girgiza kai ba tare da tayi magana ba alamar bata da
kudin mota
A wanne gari kike ?
talatu tace a sanyaye
A Tsaunin Yalwa
.
Shugaban matasa uban baligai
ya ciro kudi a aljihunsa ya bata
naira dari biyar takarda daya
ki hau babur da mota ki koma
gida kada ki sake fitowa kome
iyayenki zasu miki kiyi hakuri
kada ki sake guduwa zamanki a
gida komai wuya yafi fitowa dandi
Amadu baligi ya tafi ya barta tana
tsaye tana wasi-wasi dauke da ledarta gari yayi zafi
ya samu Damma yana jiranshi a
kusa da kofar gidan wacce ta fadi tuntuni" komai dare idan mutum yazo gidan zai iya
shigowa ba doka" babu birki"
"Nayi mata fada" zata koma
garinsu yanzun nan Damma" na bata kudin mota
.
Damma yace-
"Allah ya taimaki Uban Baligai"
karatan biyu suka fice daga gidan karuwan" suka kama
hanyar komawa dandalin cacar"
suna tafiya suna hira" talatu tana
nan a tsaye tana kallon karuwan"
har zuwa lokacin da wata takadara ta daukarwa mai tsiren
dogon tsinke biyu" ta ruga aguje
ya bita yana kiranta ta dawo
masa da tsirensa bazai bata shi ba"
Karuwar ta shige dakinta ta turo
kofa ta kulle mai tsiren ya
danna kofar da karfinsa da
yaga taki budewa sai ya dawo
yana korafi kamar zai fashe da kuka A karo na farko talatu
bakuwa tayi dariya tun zuwanta garin
.
Duk wannan abu da yake faruwa
Amadu baligi da yaransa basu
sake waiwayar bakuwar yarinyar
ba har dare yayi" zuwa karfe
goma Amadu baligi yana
tsugunne a wajen cacar da suke
wuni suna yi" yayi zufa sharkaf"
yana jiran kartagi yasa mashi
fare ko zuwa daya ne" tunda dai
an cinye dubu ashirin din da ya
tashi dasu a wannan rana" kuma
kuma ko a gida bai ajiye komai ba
Yana cikin wannan fushin ne"
Damma yazo ya tsuguna kusa da
shugaban baligai yace dashi cikin
damuwa!"
"Sarki yarinyar nan fa tana nan a garin bata tafi ba" Ance an ganta
da Baban yara ya dauketa ya kaita dakinsa zata kwana a can Amadu uban Balaigai yayi shiru
kamar abin bai dameshi ba" to
amma a xuciyarsa tuni har ya
fara tunanin irin dukan kawo
wukar da zaiyi mata
.
BABI NA BIYU
"DA karfe takwas Baban yara ya
hadu da talatu dauke da kayanta
a bakin garin da ganinta yafahimci 'yar hannu ce"
Baiwar Allah ya akayi ne.....
Ina zuwa ne ?
talatu tace dashi
"Ni bakuwa ce" ina neman wajen
kwana ne Bban yara yace Kin samu zo muje
ya tayar da babur dinsa yace
"Hau mu tafi
talatu ta haye babur din" wani
tsohon (jingchen) ne" wanda in
ba saurarawa mutum yayi da
kyau ba" sai yayi zaton injin nika
aka tayar a kusa da wajen Baban yara ya murza ya tafi da
talatu zuwa dakinsa"
Da zuwansu ya bude dakin yayi sauri ya shiga ya kunna fitilar
kwai kafin talatu ta shigo ne
yayi saurin gyara shimfidar dake
akan gadonsa na karfe wanda ke dakon wata mukekiyar katifar
ciyawa yar sale
.
Shigo mana ya kika tsaya a waje ?
ya bata umarni yana dariya"
akwai alamar yayi farin cikin
wannan tsuntuwa da yayi don kuwa indai bakuwa tazo a irin
wannan lokaci bata san inda zata
nufa ba ko ina aka kadata zatabi talatu ta shigo dakin ta zauna akan gadon daga gefe
Ki saki jikinki fa nan gida ne yace da ita yana fara'a
"kinci abinci kuwa ?
talatu ta girgiza kai tace
A,a banci komai ba
Baban yara yace
To jirani Ina Zuwa
Ya bazama ya fice daga dakin
cikin gudu-gudu jikinsa yana
rawa" A zahiri bashi da ko kwabo daga wajen gyaran babur
dinsa yake" yau baiyi aikin komai
ba" can ya wuni a gareji akayi
masa garambawul a injin babur din har kudi aka biyoshi"
"to Amma tunda yanzu sha'ani
na bakuwa dole ne ya shiga cikin
gida wajen matar yayansa ya samo rancen kyudi don ya fita kunyar wannan bakuwa tunda
dai hadin kai yake nema
.
Baban taya ya shiga cikin gidansu da sauri bai zame ko
ina ba sai dakin matar yayansa
wacce indai ta ganshi tasan kome ya shigo dashi kodai yazo
neman rancen kudi ko kuma yazo a bashi aron rikoda da
kofikan shan lemu
Idan yayi baki
zaiyi karya yau duka yake so ta
taimakeshi ta bashi da rancen kudin da kuma samira da kofikan tangaran
Baban yara ya marairaice yace da
matar yayansa
Dawowa na kenan daga gari
na sami wani abokina yazo daga
Abuja a wajen acaba muka hadu
dashi acan sanda naje barato nadawo bani da ko kwabo ki
taimakeni salamatu dubu daya kawai nake so ki bani"
Matar tace dashi
"kaga dari biyu nan akan kabet.....KAZAR KARFI--> 03
.
Matar tace dashi
"ka ga dari biyu nan akan kabet"
to wallahi ita kenan dani" ita din
ma kudin adashi ne ban riga na
aika ba Baban yara sai dai kayi
hankuri da ita"
ta miko masa" ya amsa cikin
sanyin jiki" saurayin dan kimanin
shekaru ashirin da uku" gwani
ne wajen kure kai indai akan mace ne
Yace da ita
Bani samira inje in hado masa
abinci Hada min kofikan zuba
lemo ta dauko masa samira a cikin
dakinta a sama ta hado da
cokali da kofikan zuba lemo
biyu" har zai fita sai ya sake tuno
wani abin
"Dan taimaka mini da mafici da rikoda
Da yake ta saba da irin wannan
are-aren kayan sai ta dauko masa rikoda da maficin"
Ban daiyi zubi ba batiran sunyi
sanyi sai ka sayi sababbi
Baban yara ya fice ba tare da ya
tsaya sauraron shawararta ba
ya koma dakinsa dake kofar
gida ya kaiwa talatu maficin ya
ajiye rikodar a kusa da ita ya ce
"wani shashashan kani gareni zuwa yake yi yana daukar mini kaya yana shiga dasu cikin gida"
baya dawo min dasu sai naje na
dauko da kaina na rasa inda ya
kai mani bidiyona da janareton
da nake tayarwa yana ba dakina
wuta har fankata ma ban san inda ya kaita ba
.
Baban yara yayi tsaki" talatu tayi
murmushi a karo na farko tace
"Ai ba komae ko haka ma ya isa
ta daga kanta ta duba ko ina a
cikin dakin bata ga inda turken
kwan lantarki yake ba babu
kuma wani soket a jikin bango"
babu wuta a garin" bata san
yadda wannan saurayi yake ba
dakin nasa wuta da janareta ba
tare da waya ba
Bata yi masa bayani ba ko tambaya a game da haka ta
barshi ya tafi dauke da katon
kwanon da zaije sayo mata abinci"
Ya isa dandalin garin inda masu abinci da masu sayar da
shayi da kwai suke da rumfuna"
ga jama'a nan a zazzaune a ko
ina akan benci" samari da kuma
matasan dattawa"
Baban yara ya sami daya daga
cikin masu sayar da shayin da
kuma indomi" ya kebeshi don
kada mutane suji bayanin da yazo
yayi kafin ya sayi abinda yake so"
su koma bayan rumfar" Da zuwansu baban yara ya mika
masa dari biyun yace dashi
"ka gane Auwalu wata bakuwa
nayi yanzu-yanzun nan to ina son ka hadani sosai dari biyun nan kawai gareni" ka hada mani
indomi guda biyu ka soya kwai biyar ka hada mani shayi dabam a kofi ka zuba madara
gwangwani daya muji nawa ka
biyoni gobe zan baka kudinka...
Ba wasa Auwalu"
.
"Dan siririn mai shayin mai kama
da karas" ya washe baki da
zumudi yace da baban yara
"to kai irin wannan idan ta samu
ai muma ya kamata ku rika
tunawa damu baban yara a ina ka samota ? Baban yara yace a banza na
ganta dazu a bakin gari ina jin
bakuwar gilli ce tazo bata sami daki ba"
Auwalu mai shayi yace
"A to gaskiya nima ina ciki
baban yara" bari in hada mata
komai da komai muje sai in bar yaro ya tsare min shagon kafin mu dawo
Baban yara yaba Auwalu mai
shayi hannu suka tafa faa!!" sukayi dariya"
"kai mutumin nan" ashe kaima
baka barin banza ta wuce ka?
"Ina fa zan bari baban yara ?
Auwalu mai shayi ya koma cikin
rumfar ya fasa kwayaye yana
kadawa" yasa yaronshi ya dora
taliya a wuta baban yara ya zauna a benci yana jiranshi ya
gama su tafi"
Akwai alamar yaji dadin wannan
hadin gwiwa da Auwalu mai
shayi ya nemi su yi Dama bashi
da kudi dari biyu ne da yazo da
ita ta huta itama to amma akwai
bukatar ace sun sayi lemun kwalba ya mance ashe da
sauran cefane gashi kuma Auwalu baya sayar da lemo" to
amma tunda dayyabu mai shago yana dashi" bari yaje su
shawota
Yace da Auwalu"
"kafin ka gama hada indomin da
kwan" bari inje wajen dayyabu in
sayo lemu in dawo"
Auwalu yace dashi
"to, kayi sauri fa" ba dadewa zan gama"
.
Baban
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment