Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuciyarsa na tafasa, karo yaci da hamza..

Washe masa hakora yayi sannan yace nasan inda take fa.. Da sauri ya rike shi yana murmushi.. Allah hamza?? Wallahi nasani, tana gidan wanchan tsohon banzan.
Toh ai ni bansan gidan nasa ba hamza ko zaka raka ni??

Eh to zan iya raka ka amma kaima kasan eh yane yane ka gane dae.. Hamza irin yan shaye shayen nan ne.. Tuni kabeer ya fuskanci inda maganar tasa ta dosa.. Hannu yasa a aljihu ya fito da naira hamsin ya mika masa..

Dariya ya saki yace yauwa mutumina ashe dae kaima A ne.. gobe da azahar mu hadu bakin titin gidan nan sae mu wuce kawae.. Bai jira amsa ba ya shige gida..

Yana komawa gida ya sanar da umma. Murna ta shiga yi..

Da daddare safwan yazo suka dade suna tattaunawa da umma..

So yake yaga yanda zasu bullowa al'amarin su kawu.. Nan take brr.sadeeq ya fado masa..
Dole zae nemishi suyi magana.. Lalle yasan zae taimaka masa kwarai.





☆☆☆Harphsart khabeer
[9/13, 3:22 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
7⃣6⃣➡7⃣8⃣

By Harphsart Rano✍


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆


Yana komawa daki ya fada kan gado, Dafe kansa yayi.. Tunani ya shiga yi..

Labarin da umma ta bashi ya tsaya masa rae.. And gaskiya yana suspecting wani abu..

Allah sarki Nurr dinshi ko wanne hali take ciki?? Ba shida amsar tambayar nan..

Ji yayi yana bala'een son ganinta, Amma yasan ba hali.. Zuciyarsa tae masa nauyi..

Wayarsa ce ta shiga kara, dubawa yayi yaga bakuwar number..

Bin wayar yayi da kallo harta katse, after sum minutes sae ga kiran ya kara shigowa.

Tsaki yaja sannan ya daga wayar ya kara a kunnensa..

Daga dayan bangaren yaji ance haba Aboki ina ta kirankw tun last week amma baka piking..

Dan Allah kayi hakuri kila bangani bane ya bashi amsa..

Ba komai ya gida ya aiki, cire wayar yayi a kunne ya dan kalli numbar sannan ya mayar..

Sun dan gaisa sama sama, alamun da sadeeq yaji ya gane sam safwan bai gane waye ba..

Na lura sam baka ma gane waye bako?? Kafin yace komae ya cigaba,, Abokinka ne da kuka hadu a mall..

Lalalala kace naso nayi laifi, dan Allah kayi hakuri amma..

Noo ba komi i understand, nan aka sake sabon gaisuwa..

Kafin su gama wayar sae da sukae exchangin address din juna..

Cikin dare haka yayi ta juyi sam babu alamun barci a tare dashi.. Bayason sama kansa yawan tunani kasancewarsa likita..
Amma bazae iya resisting ba.. Abun da ya sami nurr kamar ya sameshi ne.. Yana sonta sosae and kuma yana jin zae iya komai akanta (Toh fa)..




♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Nurr kuwa Allah sarki, Ni kaina sae dana tausaya mata, kafin dare tasha masifar suwaiba harta godewa Allah..

Kuka kuwa tayishi kamar ba gobe.. Fuskar nan tayi jaaa..

Dadinta daya, kawu ya lallabi suwaiba bayan ya bata kudi akanta barta ta dunga kwana
A falo.

Cikin dare tana kwance a kasan carpet wanda in banda doyi ba abinda yake.. Zurr taji wani abu ya bi mata kafa.. Ta dan saurara taji ko zaa kara yi. Aikuwa taji kamar ala lasar mata kafa.. Innalillahi, wani narkeken bera ne kamar girman skul bag din ayadh🙊..

Ihu ta saki ta mike tana zazzare ido, a tunaninta suwaiba zata fito.. Ina ita bata san ma wainar da ake toyawa ba.. Tana chan ta hangame baki😧

Komawa tayi kan kujera ta dukunkune, suwaiba ta mata warning karta kuskura ta hau mata kujera amma ya ta iya,.. Kasa barcin tayi tana ta tunanin ummanta. sae chan wajen asubah barci mai nauyi ya dauketa..


Wani wawan duka suwaiba ta sakar mata a kafarta.. zambur ta mike tana raba idanu😳..

Uban waya baki izinin hawar min kujera iyeee??? Yau sae kin gane kurenki..

Hakuri ta shiga bata amma kamar kara ingizata take, sae data gaji don kanta sannan tayi shiru..

Mikewa tayi tayo alwala, tana idar da sallah taga suwaiba a tsaye akanta.. Bata jira ma tayi addu' a ba ta fara zayyana mata irin aikin da zatayi mata..

Aikuwa tunda ta fara aikin nan sae data wuni tana yi.. tana gama wannan zata jido mata wannan...

Sae gap da magriba ta samu ta kyaleta.. Wanka kuwa dama baa maganarsa...


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Bayan ya shirya, ya fito.. Kai tsaye dankoli store ya wuce, Kayan abinci ya jidarwa umma da duk wani abu dayasan zata bukata..

A tsakar gida ya tarar da ita tana kokarin shimfida tabarma..

Basuyi wata doguwar magana ba ya mike saboda yana da patients da yawa.. Yara ya samu suka shigo masa da kayan.. Umma kawae gani tayi ana shigo da kaya.. Mamaki ne ya kamata, lallai yaron nan da kokari yake.. Bata kara shiga mamaki ba sae data ga dubu goma a cikin kayan.. Sae data zubar da kwallah..

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Bangaren kabeer kuwa anyi interview sae jiran sakamako.. Ganin yamma tayi yasa alhaji yace ya kara kwana sae ya taho da safe.. haka kuwa akayi.. Safiya nayi ya kamo hanya sae *kano*..

Da farin cikinsa ya shigo, Umma na ganinshi ta shiga murna, Lale da mutan abuja, sannu da dawowa..

Shiru baiji mutuniyar tashi ta fito ba,
umma kanwata fa??
Naji ta shiru ko kin aiketa ne??..

Nan umma ta shiga bashi labarin abunda ya faru.. mikewa yayi ya shiga balaee.. Sae daya gama dan kansa sannan umma ta zaunar dashi..
Ta dan lallabasa sannan ya hakura.. Amma ya kudurce a ransa sae yaje har gida ya dauko kanwarsa.. Gidan baba ja'afaru kawae ya sani shine da suke da zuwa in wani abu ya taso shima tunda nurr taje akae mata wannan wulakncin basu sake komawa ba.. Amma dukda haka sae ya nemo gidan..


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Yau satin nurr biyu gidan kawu..har ta fara sabawa da wahala.. Ba laifi kawu yana dan raga mata.. Amma suwaiba kuwa inaa..

Suwaiba ce ta kwalo mata kira, zokije nan gidan da yake kallon layin nan ki kaimin markaden nna. Kuma saura ki tsaya wasa wlh sae na lahira ya fiki jin dadi..
Fitowa tayi tana tafiya a hankali, kwata kwata ta zama wata lazy..
Mika markadan tayi ta tsaya daka zauren gidan..

Parking yayi daidai kofar gidan, wani matashine hadadde ya fito, kana ganinsa kaga bafulatani..dogo ne sosae.. Kallon unguwar yayi sannan ya shiga danna wayarsa..
Ji nayi yace nafa karaso ina kofar gida.. Owk pls kayi sauri.. Ya katse wayar..

Yananan tsaye yana karewa unguwar kallo, gaskiya unguwar taci sunanta china😂 saboda yawan mutanen unguwar..

Fitowa tayi dauke da markaden a hannunta, hasbunallahu ya furta, Binta yayi da kallo har tazo ta wuce ta gabansa.. Ganin zatayi masa nisa yasa shi saurin binta yana yanmata yanmata.. Kamar daga sama taji ana mata magana..
Karasowa yayi suka jera, baby sannu ko.. Bata tanka masa ba.. Dan Allah ki tsaya ki saurareni.. Kinga bai ma kamata na tsaida ki a hanya ba.. Ni sunana barrister sadeeq kibiya.. Ko zaki fadi min sunanki?? Ganin bazae kyaleta ba gashi tazo kofar gida yasa tace mishi sunanta maryam sannan ta shige gida..

Dariya yayi ya daki kansa.. Komawa yayi ya tarar abokin nasa har ya fto.. A ah kai kuma dga ina?? Hmm mutumina wlh yau zuwana unguwarku na kama babban kifi.. Naga wata beautiful baby.. I jst fall for her.. Wlh lurv at first sight ..




♡♡Harphsart khabeer
[9/13, 3:22 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
1⃣5⃣➡2⃣0⃣

By Harphsart Rano✍


Parking yayi a daedae kofar gidansu ya juyo ya kalli khalil yace oya ku shiga gida i am goin sumwhre..
Owk bro suka amsa gami da bude motan suka fita suna waving nasa, sae daya ga shigarsu sannan ya wuce..

Zaman su da umma ba karamin dadi yake musu ba saboda Allah yayi umma mace mai kirki ga fara a da sakin fuska.. Khalil kua bashi da abokiyar hira sae nurr kullum suna tare. Umma nazuwa kullum da safe ta tafi da laasar,, Shiko dama safwan bae cika zama da rana ba sae dare yake shigowa.

Yau saturday ta kama ba aiki wanda yae daedae da kwanan nurr 3 a gidan amma basu taba haduwa da safwan ba wanda taji khalil na cewa big B.

Islam da iman zaune suna breakfast ya fito sanye da jallabiyya fara yaja kujera ya zauna kusa da islam.. har rige rigen gaisheshi suke..

Morning bro suka fada suna murmushi yace morning an mata momy.. Ina little?? Iman tae charap tace yana gurin anty nurr shi wai da ita zaeci.. Nurr yaeta maimaita sunan a zuciyarshi.. Owk wace nurr ya tambaya?? Islam tace laa bro baka san anty nurr ba?? Ita cefa take zama damu tunda su momy suka tafi.

Owk gud ya furta ba tare da ya fuskanci wace nurr ba.. Ya jawo plate ya zuba chips ya hada tea..

Yana zaune a garden yana duba wani aiki a system dinsa ya jiyo hayaniya.. Ya tsaya da abinda yake ya kura wa hanya ido don ganin meke faruwa..

Gudu yake tana biye dashi yana ihu wooo bata kamani na.. saura kadan ta bige safwan wanda sam bata lura dashi ba..
Wata razananniyar tsawa ya daka mata wanda yasa su saurin dakatawa suka juyo duka a firgice.. " Who d hell d u think u r da zaki shgo kina ma mutane ihu da hauka?? Tae saurin durkusawa ta kama hannunta alamun tana bashi hakuri ,ta runtse idonta.. Siririn hawaye ya gangaro daga idonta.. Ya dan dube ta kadan, ina nasan wannan fuskar?? Ya shiga ayyanawa a zuciyar sa? Ganin bashi da amsa yasa ya tabe baki ya kara dubanta galala.. Get out frm here.. Ta tashi da gudu tae cikin gida tana toshe bakinta don kar kukan da yaci karfinta ya fito

Ya juya ya nuna khalil come here ban hanaka ihu ba?? U kno banason hayaniya shine kake mana ihu ko?? Yai narai narai da ido m sorry bro it was a mistake.. Tsaki yae yace oya shige gida b4 i change ma mind.. Ya wuce da sauri har yana bigewa..

Ta gudu ta fada kan gado ta saki kuka.. me tayi masa zai mata wannan tsawar? Da tana tunanin batada matsala da gidan nan ashe babbar matsala na gaba, dole tae ta katsantsan don ta gane wannan shine big B da khalil kullum yake mata zancen sa.. Khalil ya shigo ya zauna kusa da ita ya kwabe fuska kamr zaeyi kuka.. m sorry anty nurr it was ma fault.. Wannan big B en ya fiya fada ki rabu dashi kinji?? Ta dago tana share hawaye yae maza yasa hannu yana tayata gogewa. Wani abu ya rada mata a kunne Sukae dariya alokaci daya suka mike rike da hannun juna..

Yau ta kama sati biyu da tafiar su momy, Suna zamansu lfy gwanin bn shaaawa, in ka gansu sai ka dauka sun dade da sanin juna, bangare safwan kuwa tun ranar da abun ya faru bata sake sashi a ido ba, wani lokacin Tana jin hirarsu da kannensa wanda yake hanata fitowa har sae sun gama taji alamun ya bar wurin..


Suna zaune a falo around 9 suna kallon cartoon a mbc2 , Nurr ta lura da khalil yana jin barci amma don kar su iman su chanja channel yaki yarda ya kwanta,, Kam kam ya rike remote en ysa tv a gaba kamar me daukar karatu.. Little naga kaman barci kake ji zo muje ka kwanta.. Ya noke kafadansa

Noo ni bazan je ya amsa mata.. Chan ta lura da yanda yake rufe idonsa alamun barci yaci karfinsa..

Ta taso tazo gaban sa ta riko hannunsa zata dga shi yai saurin bude ido, tace oya muje a kwanta..

Ya kwace hannunsa , ni bazanje ba sai dae in a dakinki... Tace olryt Ta daga wa su iman hannun alamun tana zuwa.


Ta zare jikinta a hankali ta mike zata fice taji an riko hannunta, ni bazan kwanta ni kadai ba ba yace..

"Ohh shit" khalil problm ta furta a hankali ta dawo ta kwanta gefensa


Ka idar sa ne duk dare sae yaje ya dubasu yake kwanta wa.. yauma hakan ta kasance ya fto daga shi sae boxer sae singlt fara.. Yana saukowa yaji alamun tv a falo,

Tunani ya fara kardai yaran nan basuyi barci ba?? Ya karasa shigowa falon, iman ya gani kan carpet da remote tana ta sharar barci sae islam akan kujera.. Tuni yaji tausayin kannensa ya kamasa

Mesa baya zama dasu since vasu momy.. Ya shiga tunani, u r always busy en more ever baka son hayaniya wani part en zucianshi ya bashi amsa..

Daukarsu yayi daya bayan daya yakaisu daki.. ya lullubesu ya jawo kofa..

Har ya juya zae tafi ya tuno be duba little ba, Ina ya shiga? Ya juya da sauri ya koma falo, baya nan, ya hau bude bude dakunan duk ba khalil..

Dafe kansa yayi alamun damuwa a fuskarsa.. Nan take ya tuno bae duba dakin kasa ba, ya sauko da ssuri ya bude kofar

Suna kwance cikin kwanciyar hankali, little ya dora kafarsa akan cikin nurr ita kuma ta rungumosa zuwa jikinta..

Karasawa yae bakin gadon ya tsaya yana kallonsu..

Ya durkusa daidai fuskarta yana kare mata kallo,. Wow shes cute zuciyarsa ta gaya masa.. buh shes young ya bawa zuciyarsa amsa..

yayi wani murmushi da baisa na mene ba, sannan ya mika hannunsa ya gyara mata gashinta da ya rufe mata fuska.. Motsawa yaga tayi yae sauri mikewa.. Ya jawo blanket ya rufesu ya juyo a fice..
[9/13, 3:22 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
3⃣1⃣➡3⃣5⃣

By harphsart Rano✍


Daidai kofar gidansu yayi parking, ta fita da sauri, ta tura kyauren.. Ta shiga tana kwala wa umma kira, turus tayi ganin dakin nasu an jawo shi

Alamun babu kowa ya ciki, juyowa tayi da sauri tarar dashi a zaune cikin mota..

Ganin yanayin fuskar ta ya sashi saurin fitowa yana tambayar ta lfy? Tuni hawaye ya wanke mata fuska..

Banga umma ba, ba kowa a gidan.. Wani makocinsu Malam idris ne yaxo wucewa,. Tae saurin karasawa gurinshi, malam ina kwana?? Ta ambata..

Lafiya kalou yan nan.. Ya kuma me jiki?? Dazu na fto ina saurin zan tafi kasuwa, naga yayan naki sun fto da ita dijen zasu tafi asibiti da alamun bata jin dadi..

Allah yasa kaffara ne ya wuce bai jira amsarta ba alamun dai yana da wani uzurin..

Juyowa tayi tana kallonsa hankali tashe..

Wanne asibiti kike tunanin zasuje ya jefa mata tambayar..

Nima ban sani ba ta fada tana share hawaye.. Ta rasa mema zatayi?? Me sami ummanta?? Innalillahi.

Kinga ba kuka zaki tsaya yi ba, In sha Allah umma zata sami sauki.

Da kina da number yayan naki ne ma sae mu kirasa muji,..

Ni kuma kinga zanje aiki though ma dae na makara ya fada yana duba agogo..

Yanzu ki hau adaidaita sahu ki koma gida, anjima sae mu sake dawowa mugaa in sun dawo..

Ji tayi bazata iya masa musu ba, amma harga Allah bataso komawa ba..

Taso ta jira taga dawowarsu, amma ba yanda ta iya.. Ya juya ya shiga mota, daidai bakin titi ya tsaya, ta bude motar ta fito, ya zaro 5k ya mika mata..

Zaro ido tayi ta kasa karba, murmushin nan nasa ya sake sakar mata.. Karbi in wuce ina sauri ya ambata..

Tasa hannu ta karba, kafin tayi magana ya figi motar sa..

Adaidaita sahu ta samo ta shiga sae nassarawa GRA.

Shiko safwan yana tuki yana murmushi, shi kansa yana mamakin yanda yake jin farin ciki, Mesa yake jin wani abu game da ita?

Kodai sonta nake ne, Ya fada a zuciyarsa, a ah wannan ba so bane, ina tausayinta ne kawae.. ya bawa zuciyarsa amsa..
yarinyar tana da innocent face..

Haka dai yaeta tunane tunane har ya karaso
Kofar AKTH..(Aminu kano teaching hospital)

Masu gadin ne suka shga daga masa hannu alamun sun saba dashi..
Yayi saurin sauke glass yana dariya, Sannu da zuwa Dr, fari me farar aniya.. suka shiga yi masa kirari.. Ya saki murmushi ya wuce parkin space..

Fitowa yayi yana tafiya cikin takunsa, direct office ya wuce saboda yasan patient suna nan suna jiransa..

Sae daya zauna ya fara
Duba files din mutane.. Daya bayan daya suka dinga shigowa yana dubasu

Khadija kabir aka kira, yai saurin riko umma saboda jirin da take fama dashi, suka shga dakin likita..

Cikin fara'a ya kalli umma, ya ganeta suna gaisawa sumtyms..

Yae saurin mikewa.. Ya bawa kabir hannu, sannan ya kalli umma ya gaishe ta.. Ta ganeshi itama

Bayan ya dubata, yaga ya dace a dan sa mata drip.. ya kalli kabeer yace zamu dan kwantar da ita saboda jikinta yayi weak..

Kabeer ya dan zaro ido, wannan kudin ma dayaya aka sameshi balle kuma ace zaa kwantar da ita..

Safwan ya danyi nazarinsa, yace baka ce komi ba.. Dr wlh ba kudi yanzu a hannuna amma zanje na nemo in sha Allah..

Sae daya ga an bawa umma daki an jona mata drp sannan ya shaida mata zaeje ya samo kudi..


Safwan kua Bai samu ya gama ba sae wajen 5.. Nurr kuwa kwata kwata hankalinta baa jikinta yake

Su iman har sun dawo daga skul sun tafi islamiyya..

Tana zaune taji karar motar sa, da sauri ta fito har tana tuntube, sae de tana zuwa tsakiyar falo ta tsaya chak,..

Tunani take in taje me zata ce masa, kuma ma don ya taimaketa dazu bashi ne yake nufin ya chanja daka miskilin nan data sanshi ba

Kar taje ma ya wulakanta ta, tana tsaye tana tunani ya turo kofa ya shigo,

Dama yayi tunanin zae ganta tana jiransa, kuma da alamun ma shi taji ta fito..

Kallonta yayi kadan sae kuma ya basar ya haura sama..

Wani kululun bakin ciki taji, jiki ya sabule taja kafarta ta koma daki ta rafka tagumi..

Tuni taji wani zazzafan hawaye ya gangaro a fuskarta..

Lalle talauci baeyi ba, yanzu badan ita tana matsayin yar aiki ba, ai da ba abunda zae zaunar da ita..

Sae taje taji halin da ummanta take ciki..

Sae daya watsa ruwa ya dauro alwala sannan ya sauko..Lokacin an fara kiraye kirayen sallah, Direct masallaci ya wuce..

Sae daya idar da sallah yayi yan adduo insa sannan ya shigo..

Su islam ya samu suna zaune duk kansu ba walwala..

Yane twins en momy na ganku haka.. Khalil nae yae saurin zuwa gareshi yae huggin dinsa.. Big bro ga anty nurr chan tana ta kuka bamu san me akai mata ba..

Kazo muje kaji me yasa ta kuka kaji.. ya shiga jan hannunsa..

Binsa kawae ya shiga yi don ya riga yasan dalilin kukanta..

Sallama yayi ya tsaya a kofar dakin yana kare mata kallo..

Ta dago tana dubansa, sannan ta maida kanta tsakanin cinyoyinta ra cigaba da kuka..

Ki shirya yanzu muje muga umma ya ambata sannan ya juya ya fice..

Tae saurin mikewa har taso ta manta da daukar hijab dinta..

Suka fito gaba dayansu bayn sunyi ma mai gadi sallama

Iman, islam da ita suna baya.. khalil kuma nagaba.

Mamaki ne ya kamata ganin an dauke hanya ba hanyar unguwarsu ba..

Bata kara shiga mamaki ba sae da taga anzo kofar AKTH..

Bayan yayi pakin suka fto ya wuce gaba suka bishi a baya, kasancewarsa likiti baesa sun samu matsala da shga ba duk da ba lokacin ziyara bane..


Suka hau kan barender wanda zae sada ka da aminity..

A hankali ya bude kofar room 3 gami da sallama..

Umma ce kwance hannunta daure da drip, sae ya kabeer a gefenta.. A guje da karasa gaban gadon, saura kadan ta bangaje safwan..

Fashewa tayi da kuka ta riko hannun umma.. Sannu ta shiga yi mata ba kakkautawa..

Yaran suka gaishe da umma da ya kabeer sannan shima safwan ya gaisheta yana kara mata ya jiki.

Sannu dan nan mun gode fa wannan hidimar da kayi damu Allah ya saka da alkhairi umma ta fada taba dubanshi..

Murmushi kawae yayi yaja hannun kabeer suka fita..

Sae bayan sun fta ne take tambayr umma abinda yayi take masa wannan godiyar..

Nan take sanar mata, shine ya biya kudin komae har kudin daki.. kuma shine likitan daya dubata..

Baki bude take kallonsu iman.. Dama big B likita ne?? Wlh ni banma sani ba umma..

Nan itama take bata labarin zuwan da sukae gida nemanta..

Sae 10 suka fto daga asibitin wanda da kyar nurr ta yarda zata bisu don ma umma ta nuna mata rashin kyautwa da zatae idan taki binsu..



Harphsart khabeer
[9/13, 3:22 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
4⃣1⃣➡4⃣5⃣

By harphsart Rano✍


Raba dare yayi yana tunanin nurr.. Haka nan yaji yarinya tana burgeshi.. Yaji lalle yana so ya taimaka ta..
A haka har barci ya daukeshi..


Bangaren nurr kuwa tunda ta koma daki tunanin rayuwarsu ta shiga yi.. Yanda rayuwa ta juya musu.. Daki daki take tuno komae wanda take iya tunawa..


Alhaji Abubakar sumaila shine asalin sunan mahaifinmu.. Yan asalin karamar hukumar sumaila ne dake cikin jihar kano.

Kakanmu malam hamza sumaila yana da mata biyu.. Inna gaje ita ce uwar gida tana da yaya biyar.. Jaafaru shine babba, sae sulaimanu, tukur, lami sai autansu kamalu..

sae baba halima amarya wadda take da da daya Habu..

Baba gaje mace ce sam wacce bata san mutunci ba.. Kwarai ta tsani kishiyarta da tilon danta..

Ba irin makarkashiyar da batai ba don ganin bayansu amma Allah bai bata saa ba..

Su kansu yayanta ta koya musu wannan mummunan akidar..

Sam basa son habu da mahaifiyar sa..

Sam zaman gidan baya wa baba halima dadi da ita da habu.. tsana da kyara suke sha..

Shi kanshi malam hamza baya iyawa da masifar inna gaje.. Haka dae ake rayuwar da dadi ba dadi..


Kasancewar habu shine karaminsu don sa'an kamalu ne.. Sai suka maidashi wani bawa..

Duk wani aikin wahala shi yake musu shi..

Ana haka su jaafaru sukai aure suka tare a cikin gidan kasancewar shi babban gida..

Ba abunda ya chanza na daga tsangwamar da ake musu.. Har matan su jaafaru basa ganin girman baba halima saboda tsoron inna gaje..


Watarana malam hamza kwanta cio me tsanani.. Ya sa aka kira masa gaba daya yayansa da matan.. yae musu nasiha akan zumunci sannan ya rokesu da su kula da baba halima ko bayan ransa..

Suka amsa kamar gaske.. bayan kwana uku da faruwar haka malam hamza yace ga garinku nan..

Mutanen garin sunji mutuwar malam hamza kasancewar shi me son jamaa..

Bayan sati biyu da rasuwar malam inna gaje da yayanta suka fara fito da salo salon wulakanta baba halima..

Kwarai take shan wuya don abinci ma wataran sae an ga dama ake basu..

Ranan dae ta dubi jaafaru yana zaune kan dakalin kofar dakin baba gaje tace "Ya kamata jaafaru a saukewa malam hakki..


Nan danan ya hayayyako mata yana gaya mata bakakin maganganu

Dama ita bata damu da mutuwarsa maalam bq, dan abinda ya bari shi ta sawa ido..

Tou bari kiji in fada miki ba abinda zaa raba a baki nine nan zan cigaba da kula da kadarorin malam..


Baba halima tayi dana sanin dauko wannan maganar wanda akarshe sae data zubar da hawaye..

Cikin dare tana zaune a dakinta ta rafka uban tagumi tana tunanin rayuwa..

Habu yae sallama ya shigo.. guri ya samu yana kallonta yace, baba kiyi hakuri kome ake miki watarana sae labari.. Shikenan Ba komae Allah yayi mana jagora tace

Nan suka shiga hira
Inda yake sanar mata
Dazu yaji mai gari yasa a sanar ,wasu baki sunzo daga gwamnatin jiha suna bukatar yara za asasu a makarantae boko... Ta jinjina kai tana tunani..

Da sanyin safiya jaafaru yazo yana bubbuga wa baba halima daki..

Ta bude da azama a tunaninta ma wani ne ba lafiya.. Ganin jaafaru tsaye fuskar nan ba walwala yasa tasha jinin jikinta.

Ina habu yake ne tun dazo nazo ban sameshi a dakinsu ba..

Ki fito dashi dan yau zasu tafi birni na bada sunanshi..

Kuma ko kiinaso ko bakyaso dole yaje don na gama maganata..

Bae jira amsa ba ya juya fuuu ya wuce..

Kuka ba irin wanda baba halima batae ba ranar da aka tafi da habu...
habaici kuwa ta shashi a tsakar gida har sae data gwammace bata auri malam ba.. A kwana a tashi ba wuya



Assalamu alaikum, ina mutanen gidan ne?? Baba gaje ce ta fito tana gyara dan kwali..

Wanna dan iskanne ke ta mana sallama haka ne.. Turus ta tsaya ganin habu cikin kyakkawar shiga, janye yake da troly yar madaidaiciya..

Baki bude ta ke kallonsa mamaki karara a furkarta..

Shi kuwa murmushi yayi ya tsuguna har kasa yace baba ina wuni, mun sameku lfy..

Ganin bata da niyyar amsawa yasa shi mikewa yaja jakar shi ya

Please Login or Register in order to submit comment