Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita..

Sati guda kabeer yana zaryar gidan baba ja'afaru amma babu wani chanji..

πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“Ώ

πŸŽ€Guguwar SoπŸŽ€
7⃣9βƒ£βž‘8⃣0⃣

By harphsart Rano✍


Dafa shi kamal yayi yace haba abokina calm down.. Kasan yadda ka hadunnan ba yarinyar da zaka nema bata soka ba..

Ka fada min inane gidansu nikuma nayi ma alkawarin sae tasoka..

Hannu yasa ya nuna masa gidan da ta shiga, a rasane kamal ya maida dubansa gareshi.. Ganin sadeeq yana masa kallon tuhuma yasa ya dan wayance..

Lalle mutumina, toh karka damu zan bincika naji ko wacece duk da dae nasan yaran gidan yara ne.. Manyan duk an aurar dasu. Kila bakuwa ce tazo amma kabar komi hannuna..

Haka sukae sallama ya kama hanya yanata tunanin maryama😘.

Har ya dau hanyar gida sae kuma ya fasa, waya ya ciro ya shiga kiran safwan.. Shi dae haka nan yaji safwan yayi masa kuma. Yana son suyi abota..

Jin an daga wayar yasa ya katse tunanin.. Likita bokan turai, ya gida ya aiki.. Daga dayan bangaren safwan yayi dariya yace babban barister ka fiya tsokana wlh gida lfy wlh..
Sun dan taba hira sannan yace masa ya jira sa a gida yau zae shigo bayan magriba..


Haka kuwa akayi bayan sallar magriba sadeeq ya shirya sae nassarawa g.r.a

A daedae gate en gidan ya tsaya ya kirawo safwan.. Nan ya shaida masa ya karaso..

Fitowa yayi, yae masa iso zuwa falon baki.. Nan suka shiga hira kamar sun dade da sanin hira.. Tun safwan na baya baya har shima ya ware..

Yau fa nayi babban kamu aboki.. Dan Allah?? Wallahi kuwa. Nn ya bashi labari.

Tafawa sukayi safwan yace gaskiya ne yallabai.. Ba sanya wato har binta kayi..
Ai abokina wanann harkar ba'a sanya.. Gobe goben nan zan koma. Babe din ta hadu over.

Nurr ce ta fadowa safwan.. Allah sarki ko tana wanne hali.. Ganin yayi shiru yasa sadeeq kiran sunan sa.. Yadai aboki?? Ko dae ka tuno babe dinka neπŸ˜‚..


Dariya yayi sannan ya dan harare sa.. Sae kace wani kai.. Suka tafa.

Sadeeq bai bar gidan nan ba sae wajen tara na dare, sae daya shiga ya gaida mommy. Ai tuni su khaleel suka manne masa.. Ya dinga jansu da magana suna dane masa jiki..


β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘

Kabeer ne ya kalli umma, sannan yace
Umma gobe zanje gidan baba ja'afaru. Inaso naji wani abu game da kanwata.. Dole su bani ita na taho da ita don wlh hakuri na ya kare..
Jin umma tayi shiru yasa yace umma baki ce komai ba.

Me zance abba? Ni abun nan ya ishe ni.. Kaje kaji yanda ake ciki.. Yawwa umma dama amincewarki nake nema..

Washegari ya shirya sae gidan baba ja'afaru .. A kofar gida ya tarar da hamza dan gidan baba ja'afaru.. Suka gaisa sannan ya shiga ciki.. Baba ja'afaru na ganinsa ya damke fuska.. Mara kunya me ya kawo ka gidana?? Ko yau ma kazo kamin rashin kunya ne?? Har zae tanka sae ya tuno umma tace karya kuskura ya tanka masa. Batason rashin kunya.

Dukar da kansa yayi ya shiga gaisheshi.. A dakile ya amsa sannan ya dora.. Kayi gaggawar sanar dani abunda ya kawo ka.

Dama zuwa nayi naga nurr.. Ka bani ajiyarta?? Toh bansan inda take ba. Tashi ka bani wuri..

Haka ya dawo gida batare da wani kwakkwaran bayani ba



β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†
Nurr durkuce tana wanke wanke, suwaiba kuwa tana zaune a kofar falo tana yan wake wakenta.. Duniya tayi mata dadi.. Ita fa yanzu bata wani aiki tun zuwan nurr.. Yaranta ne suka jeho mata ball daedae goshinta..

Kyalkyalewa sukayi da dariya, ganin ta taso zata kamasu yasa suka fice da gudu suna mata ihu..

Yana tsaye kofar gidan yaga yara sun fito, daya daga ciki ya kira yace ya shiga ya kira masa maryam..Kasancewar kawu tukur maryam yake cewa nurr yasa yaron ya gane wayake nufi.. makale kafada yayi yace masa bazan kirata ba sae ka bani kudi.. dariya yayi ya zaro sabuwar dari biyu ya mika masa.
Aikuwa da gudu ya shiga gida yana kwala mata kira.. Suwaiba ce ta ganshi ya shigo rike da kudi yana kiran nurr..

Tasowa tayi da sauri ta rike shi, kallon kudin hannunsa take tana masa dariya.. Yawwa yaron kirki aina ka samo wannan kudin haka?? Wani ne a waje yace na kiramai maryam shine ya bani..


Washe baki suwaiba tayi..
Maza maza wanke hannunki kizo kije ana kiranki a waje, ta juyo ta sauri tana mamaki.

Wani lafiyayyen murmushi ta kara sakar mata.. Taso mana karya gaji da jira kinji yar nan..

Zuwa tayi ta dauko hijab dinta, sae data zo zata fita sannan suwaiba tace karki yarda ki dawo min cikin gidan nan bako kwandala kingane ai..

Yake tayi ta wuce tana mamakin irin halin suwaiba..

Tana ftowa taga wannan na jiyan daya biyota.. gefe ta samu ta tsaya..

bae jira komae ba ya shiga zuba mata surutu.. Tambayoyi kuwa ta shasu.. Tana amsa masa wasu wasu kuma tayi masa banza..

Amma ba laifi yana da abun dariya ga saurin sabo.. yanda ya sake da ita.. Kwata kwta bai mata maganar soyayya ba..

Dazae tafi ya ciro kudi ya mika mata.. kin karba tayi ta shige..

Yaro ya kira ya bawa yace yaje ya kaimata. sannan ya tafi..

Aikuwa suwaiba bakinta kamar gonar auduga.. Nan nan ta shiga yi da ita ranar bata sake yin wani aiki ba..


β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†
Satin kabeer daya yana sunturin gidan baba ja'afaru amma ba wani sauyi..

Fitowa yayi zuciyarsa na tafasa, karo yaci da hamza..

Washe masa hakora yayi sannan yace nasan inda take fa.. Da sauri ya rike shi yana murmushi.. Allah hamza?? Wallahi nasani, tana gidan wanchan tsohon banzan.
Toh ai ni bansan gidan nasa ba hamza ko zaka raka ni??

Eh to zan iya raka ka amma kaima kasan eh yane yane ka gane dae.. Hamza irin yan shaye shayen nan ne.. Tuni kabeer ya fuskanci inda maganar tasa ta dosa.. Hannu yasa a aljihu ya fito da naira hamsin ya mika masa..

Dariya ya saki yace yauwa mutumina ashe dae kaima A ne.. gobe da azahar mu hadu bakin titin gidan nan sae mu wuce kawae.. Bai jira amsa ba ya shige gida..

Yana komawa gida ya sanar da umma. Murna ta shiga yi..

Da daddare safwan yazo suka dade suna tattaunawa da umma..

So yake yaga yanda zasu bullowa al'amarin su kawu.. Nan take brr.sadeeq ya fado masa..
Dole zae nemishi suyi magana.. Lalle yasan zae taimaka masa kwarai.





β˜†β˜†β˜†Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“Ώ

πŸŽ€Guguwar SoπŸŽ€
8⃣7βƒ£βž‘9⃣0⃣

By harphsart Rano✍

Shirya wa yayi tsaf sannan ya fto, bayan ya kukkule ko ina ya fto zuwa mota.

Wani mutum ya gani a tsaye alamun yana jiransa..

Mika masa hannu yayi suka gaisa. Gabatar masa da kansa yayi. Sannan suka koma cikin falo.

Sun dade suna hira kafin su fito su shiga motar sadeeq

Direct police station suka wuce bayan ya dauko detective salim. Nan sadeeq ya shigar da report inda wannan mutumin ya sake maimaita abunda ya fada wa sadeeq a gida..

Godiya yayi masa sannan yace ya zama cikin shiri ko wanne lokaci zasu iya nemansa.

Dalilin zuwan wannan mutumin yasa dole ya hakura da zuwa wurin nurr.. bayan ya sauke mutumin suka wuce kai tsaye gidan detective salim

Sun kara tattaunawa akan yanda abubuwan zasu kasance..


Ya kira safwan ya kara sanar dashi abunda ya faru. Mamaki ya shiga yi ya gode ma sadeeq.

Kasancewar yana gidan umma yasa ya kwashe komae ya sanar da umma.

Tayi farin ciki sannan ta kara yi musu fatan alkhairi..

Wai umma ya maganar nurr kuwa?? Har yanzu ya kabeer din bae samu zuwa ba??

Wallahi Dr. Amma yau ya tafi ganin ko yaron da zae rakashi ya samu sauki.. Muna dae zuba ido naga shiru bae dawo ba..

Shikenan umma ni zan wuce Allah yasa muji alkhairi..


β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†
Lokacin da khabeer ya karasa gidan baba ja'afaru, hamza da abokansa na zaune a kofar gida..

Hamza na ganinsa ya taso, tafawa sukayi sannan yayi masa ya jiki..

Basu bata lokaci ba suka kama hanya sae dorayi..

Akan layin kabeer ya tsaya , shiko hamza sae ya wuce bayan sunyi plannin yanda komae zae kasance.

Shiga yayi cikin gidan kai tsaye ko sallama babu..

Suwaiba bata nan, tana makofta inda suke dasa dandalin gulmarsu. Kowa a unguwar ya riga yasan halinsu.

A kofar kitchen ya tararda ita tana tsintar shinkafa.

Kwana biyu da sadeeq bae zo ba ta shiga takura a wajen suwaiba.

Shi kanshi kawun sae daya chanza mata. Ita kanta ta damu da rashin zuwansa, ba don wani abu ba sae don ta saba dashi.. Kuma dae bata ji dadin yanda suka rabu ba ranar ko ba komae sadeeq mutum ne..

Kallonsa tayi taga ya jawo kujera ya zauna, yan mata ya fda ya dan kashe mata ido irin na yan duniya.

Kawar da kanta tayi dalilin tasan halin hamza sarai lokacin da take sunturin zuwa gidan baba ja'afaru.

Ganin bata da niyyar kulashi yasa ya dan rage murya.. Ke kinga fa ba jan aji zaki tsaya yimin ba..

Tare muke da kabeeru yana kan layi yana jirana..

In zaki dauko hijab dinki mu wuce in kuma ba zaki dauko ba nayi tafiyata..

Bata san sanda ta saki farantin shinkafar ba, aikuwa ta tarwatse a tsakar gidan.

Bata bi ta kai ba ta jawo hijab dinta akan igiya ta zura..

Shi kam dariya ma ta bashi.. Tsayawa tayi a gabansa ganin bashida niyyar tafiya yasa ta kafe shi da ido..

Karki cinyeni wuce muje. Yana gaba tana binsa a baya. Tsoronta daya kar suwaiba ta fito daga makota..

Har suka kusa barin layin jikinta bari yake..
Suna zuwa kaarshen layi ta hango yayanta ya tsaye alamun jiransu yake.

Da gudu ta karasa ta rungumeshi ta saki kuka.

Ganin mutane sun fara kallonsu yasa shi janyeta.. Ki nutsu mu wuce gida kinga mutane na kallonmu..

Kamal na kofar gidansu yana kallonsu.. Wannan ai ita ce yarinyar da sadeeq ke so. Toh me ya samesu haka??
Oho ya bawa kansa amsa.

Suna tafe cikin adaidaita sahu ta makale yaya kabeer kamar wani zae raba su.

Hamza kuwa sae kallonsu yake, sun dan bashi tausayi.

Shi kansan ya tsani kawu tukur kasancewar ya taba jin wata hirarsu da baba ja'afaru.

Ba shida kirki ko kadan kuma duk wani abu shi yake sa baba ja'afaru yinsa.

Sunxo inda zasu sauke hamza, kabeer ya zaro dari biyu ya mika masa.
Kallonsa yayi sannan yace ba komae dan uwa ka barshi kawae
Ya juya ya tafi. Baki bude kabeer ya bishi da kallo.
Hamza ne yaki karbar kudi?? Lalle tou ko rashin lafiyar da yayi ne ya sashi haka.


Bata jira adaidaita sahun ta tsaya ba ta fito tana kwala ma umma kira.

Kamar daga sama umma taji muryar nurr..
A firgice ta fto suka ci karo a tsakar gida..

Rungume umma tayi ta saki wani kuka me cio. Umman ma kukantake.. Shikuwa kabeer harde hannunsa yayi yana kallonsu gwanin tausayi. (Ni kaina bansan sanda na saki kuka ba😭)

Da kyar suka samu sukayi shiru. Kin barin jikin umma tayi, a haka suka zauna suna manne da juna.

Umma sae shafa mata kai take. Hira suka fara ta yaushe gamo.


Kabeer ne yayi gyaran murya yace shikenan umma an manta dani nurr ta dawo ko??

Dariya umma tayi tace ba haka bane abbana kaima kasan kaine na karfen.
Duka suka kyalkyale da dariya.

Nan yake sanar da umma visar sa ta fito in two weeks zasu tashi.

Kusan hantsulowa nurr tayi, kallon su umma ta shiga yi alamun tana neman karin bayani..

Dariya umma tayi tace bakyanan yayanki ya samu tafiyar nan zuwa kasar waje.

An gama komae ma yanzu kinji ma nan da sati biyu zasu tashi..

Tsalle ta shiga yi tana ihu. Dama sun san zaa rina..


β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘

Suwaiba kuwa bayan ta gama zaman gulmar tata ta nufo gida don ganin ko nurr ta gama girki..

Tun daga waje ta fara kwala mata kira. Tattabaru ta gani sun cika tsakar gidan, shinkafar data zube duk sun kara barbazata.

Kashi kuwa ko ina sunyi shi kacha kacha. Wata uwar ashariya ta saki ta shiga kiran nurr kamar zata fasa gidan..

Shiru ba alamun akwae mutum a gidan, dama yaran gidan basa zama a gida kullum suna unguwa suna daukar magana.

Kan balaee ta furta, lallai yau yarinyar nan sae ta gane kuranta. Ko gidan ubanwa ta tafi.

Tana tsaye tana jarabar data saba kawu ya shigo. Ganin ta tsaye ga shinkafa baja baja yasa shi kundumo asharπŸ™Š

Shinkafar tashi ce haka a zube, lalle ma an raina masa hankali..

A wulakance ta kalle shi sannan tace, da zakazo kana wannan sababin nima haka nazo na tarar.

Nabar yarinyar nan a gidan, kafin na dawo nazo na tarar da wannan aika aikar.

Kuma abin haushin ma bata gidan kwata kwata.

Sae kuma ya rude, ina ta shiga? Dama tana fita ne?? Kardae ace yarinyar nan ta gudu.

Aikuwa yanzu zan bita in gani, bata isa ta ja dani ba wallahi.

Gashi na karbi kudin alhaji mudi akan zan bashi aurenta.

Kudin kuwa ma na riga na bawa Alhaji wada akan kwangilar da zamuyi..


Duk ya zauce ya rasa inda zaeyi.. buguzun buguzun ya juya, kicibis sukayi da yan sanda har guda biyar..

Ja da baya ya shiga yi, ganin zae juya yasa wani dan sanda ya damko shi.

Ihu ya shiga yi wanda yasa suwaiba fitowa ba shiri. Turus tayi ganin kawu a hannun yan sanda.

Kuka ta shiga yi tana hauka. Ita a lallai sae an saki mijinta.

Angiza keyarsa sukayi sae police station.. Suna isa suka ga baba ja'afaru. An riga an kamo shi tuni..

Kallon kallon suka shiga yi. Bayan an kwace komae na jikinsu aga tisa keyarsu zuwa cell.. Hamza ne tsaye cikin station din sae kai kawo yake..

Wani dan sanda ne ya dube shi sannan yace ba wani abu zaai musu ba yan tambayoyi zasu amsa indae kuwa sun amsa daidai zaa sakesu.

Haka ya juya jiki a sanyaye..

β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†

Mommy zaune da yaranta safwan ya fito fuskar nan fal farin ciki.

Guri ya samu ya zauna yana kallon mommynsa.
Mommy anjima idan na dawo zamuyi wata magana..

Yanzu zanje wata yar unguwa. Tom shikenan ka gaishe min da ita in kaje.

Dariya ya saki ganin mommy ta ganosa. Har ya kae kofar fta khalil ya taso da gudu..

Big bro kafa ce min zaka dawo mna da anty nurr amma har yanzu.

Kallon mommy yayi sannan ya jawo khalil.

Karka damu little kwanan nan zanje har gidansu nace ta dawo. Dnt worry owk?? Daga kai yayi ya koma shi kuma ya fice..

Tunda ya dauki hanya yake ganin kamar baya sauri. Allah Allah yake ya ganshi a hotoro. Kabeer ne ya kirashi ya sanar dashi dawowar nurr.

Umma ce ta sata a gaba tayi wanka. Doguwar rigar da ya bata ta dauko mata.

Light make up tayi.. bayan tasa rigar ta rollin kanta da gyale pink.

Tsaf rigar ta fto mata da figure 8 enta.. Kallon kanta tayi, ita kanta tasan tana da kyau..

Tsaya wa yiwa mai karatu bayanin yanda nurr tayi kyau kamar ma bata lokaci ne.

Kasancewar umma irin fulanin gomben nan ne, kuma duk yaran nata ita suka yo...

Tana tsaye tana karewa kanta kallo ta jiyo sallamar shi. Gabanta ne ya fadi.

Sama sama take jiyo hirarsu da umma har ta daena ji. Hakan ke nuna mata ya fta kenan.

Umma ce ta shiga kwala mata kira. A kasalance ta fto. Maza kije yana waje yana jiranki.

A hankali take tafiya gabanta na tsananta faduwa. Tayi tsammanin zata ganshi a zauren gidan.

Ganin baya xauren yasata karasawa waje..

Tunda ta fito ya kafe ta da ido.. Bae taba ganin ta cikin irin wannan shigar ba. Ganin tana dan dube dube yasa shi sauke glass din motar.

Karaso yan mata ya fada fuskar nan tasa dauke da murmushi.

A hankali ta taka har wajen motar. Bude mata yayi ta shiga ta zauna.

Wani sanyi taji yana bin ilahirin jikinta.
Shima hakan ce ta kasance dashi.

Sunkuyar da kanta tayi ganin kallon da yake mata tana wasa da zoben hannunta..

Kinyi kyau taji ya ambata, yana kallonta.

Kasa dagowa tayi sae kawae tace masa nagode.

Matsowa yayi daf da kunnenta sannan ya furta.

Anya nurr kinyi missin dina kuwa??

Dagowa tayi suka hada ido, murmushi ta sakar masa sannan tace Nayi missin dinka sosae ma.

Gaskiya ni banga alama ba, ko kallona fa kin kasa yi balle kiga yanda na rame saboda rashinki.

Ke kuwa ma kibar ki kikayi abinki alamun bakiyi missin nawa ba..

Zaro ido tayi ta kama baki, ina kiba anan? Ni dana rame ma.

Ka ganka kuwa yanda ka kara kyau.. Dariya yayi sannan suka cigaba da hirarsu cikin so da kauna.

Sae da yaga kiran sadeeq sannan ya tuna fa sunyi zasu hadu.

Kwata kwata ganin nurr ya mantar dashi komae.

Dan dole ba dan yaso ba sukayi sallama ya nufi wurin sadeeq.

β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†

Police station suka nufa, a hanya safwan yake bawa sadeeq labarin dawowar nurr dinsa.

Nan yake gaya masa yanzu haka ma daga chan yake.

Allah aboki?? Gaskiya nayi maka murna sosae. Shisa naga bakin yaki rufuwa ya fada a wasance.. Dakar kafadarsa safwan yayi yana dariya.

Ina sonta ne sadeeq, komai nata is unique. Duk wannan abunda nake akanta nakeyi.

Kaga kuwa nayi ma alkawari in mukayi aure, duk sanda nurr ta haifi namiji sadeeq zan sa masa saboda kokarin ka akanmu.

Dadi ne ya rufe sadeeq, aboki ka gama min komae wlh.

Nan shima safwan yake tambayarsa yanda sukayi da maryam.

Aboki bari kawae ban samu naje ba har yanzu. Wannan case dinne ya ke delyin dina.

Aikuwa babu wani police station da zamu je yanzu sae mun fara zuwa na shirya ku.

Da kyar sadeeq ya yarda suka juya akalar motar zuwa dorayi..

Sun dade a kofar gida kafin su sami dan aike.
Yaron ne ya dawo yace musu wai ance batanan taje kauye.

Sam basu ji dadi ba amma ba yanda suka iya dole suka ja motarsu suka wuce p.station.

Lokacin da suka karasa an tsare su kawo da tambayoyi, basu nemi ganinsu ba, direct wurin D.P.O suka wuce..

Nan yake shaida musu kwata kwata sunki yarda su fadi gaskiya akan tuhumar da ake musu akan dukiyar marayun.

Daya daga ciki yana da taurin kai, amma ba komae zuwa gobe in basu fadi komae ba sae mu aika su zuwa kotu.

Shikenan D.P.O, Sae naji daga gareka. Har sadeeq zae shiga inda su kawu suke sae kuma ya fasa.

Baya jin dadin jikinsa, so yake yaje gida ya huta..

Gidan sadeeq din suka zarce kasncewar motar safwan din tana chan..

Sae daya san jima a gidan sannan ya wuce gida..

Wanka yayi sannan ya nufi dakin mommy.

Jin motsin ruwa a toilet yasa shi komawa, kitchn ya shiga ya hado coffee sannan ya dawo falo ya zauna yana kallon t.v


Fitowar mommy tayi daidai da gama shan coffee dinsa.
Kitchen ya mayarda mug din sannan ya dawo ya zauna.

sae daya fuskanci mommy sannan ya fara bata labari.. Tun zaman nurr a gidan da irin abubuwan da suka faru har zuwu yanzu da kamen su kawu da akayi.

Kallonsa ta shiga yi da mamaki, ashe safwan zae iya duk wadannan abubuwan ba tare da ya sanar da ita ba.

Mommy kiyi hakuri nasan banyi daedae ba, ya kamata na nemi shawararki kafin na aiwatr da komae.

Mommy mace ce mai fahimta, nan take ta nuna masa ba komae ita bata ji haushi ba..
Kuma tana farin ciki da kasancewar nurr a matsayin wadda yake so.
Fatan alkhairi tayi masa sannan ta mike ta shige daki.

β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†
Nurr da umma zaune suna hira, nan take bawa umma labarin sadeeq.. Da irin rabuwar da sukayi.

Tana so ta sake ganinsa, tana jinsa har cikin ranta.

Fara'arsa , barkwancinsa duk take tunawa.

Allah sarki, gaskiya ya taimaka miki. A dalilinsa kin samu rangwamen zama a gidan kawu cewar umma.

Amma ba komai wataran zaku hadu. Sae kiyi masa godiya.



Harphsart khabeer
[9/13, 3:23 PM] Fati Novel: πŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“ΏπŸ“Ώ

πŸŽ€Guguwar SoπŸŽ€
9⃣1βƒ£βž‘9⃣5⃣

By harphsart Rano✍

β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†

A nutse yake tuki, kana kallonsa zakasan ba shida walwala..

Asibiti ya fara biyawa don su wuce da safwan, ganin aiki yasha kansa yasa shi tafiya shi kadae.

Station ya nufa don jin inda zance ya kwana..

Bayan sun gama magana da dpo ya tabbatar masa da an riga an tura karar kotu. Saura kowa ya dauki lawyer..

Shikenan dpo ko zan iya zuwa nagansu?? Eh zaka iya zuwa ya fada gami da kwala wa sargent kira.

Har ciki ya jagorance shi.. Gabansa ne ya fadi ganin kawu maryam, me hakan ke nufi?? Kardai ace...
No bama haka bane, maryam da nurr ai its a differnt name. Lalle kenan dey are related..

Kwata kwata idonsa ya rufe, yama manta a labarin da safwan ya bashi..

Bae karasa inda suke ba sae kawae ya juya..

β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘
Yau kwana uku ya rage a shiga kotu, kabeer kuma tafiyarsa saura 5days..

Nurr da safwan kullum suna jone.. Sunje ta gaida mommy, khaleel kamar zae yi hauka don murna.
Sae dare suka dawo..

Chan bangaren su kawu kuwa suma sun dauki lawyer...

Ana ta shirye shiryen shiga kotu, duk bangaren biyu sun gama shiryawa. Kowa yana ganin shi zaeyi nasara..

Umma kuwa kwata kwata bata ciki hayyacinta, tana jin tsoro. Tasan indae su kawu sukayi nasara toh kashinsu ya bushe.

Kullum cikin addu'a take, kabeer da safwan ke kwantar mata da hankali..

Karta ji tsoron komae.. Ranar da yamma sadeeq yazo, ranar kuwa nurr bata nan.

Tun Dawowarta daga gidan kawu, safwan ya maida ta islamiyya.

Har suka gama zamansu bata dawo ba..

Sae da suka fto safwan yace masa gashi har zamu tafi ba ku gaisa da ma wife ba..

Noo ba komae ai ana tare, nxt tym xamu hadu ai..

Sadeeq kamar ya tambaye safwan akan kawu, sae kuma ya fasa.



β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†β˜†

Yau ta kama zaa shiga kotu, da sassafe safwan ya shirya.

Dakin mommy ya nufa don sanar da ita.

Addu'a tayi masa sosae da fatan nasara.

Sae daya fto ya kira sadeeq donjin yanda tafiar zata kasance..

Kazo gida mu karasa shirye shiryen kafin tym en a cewar sadeeq, Shikenan to ganinan..

A gidan sadeeq suka hadu duka harda salim..

Duk wani information da suke son hadawa sun gama hadawa..
Sae dae matsalar daya akwae babban hujjar da zata warware wannan shari'ar..

Rashin zuwan wannan hujjar zae iya jan shari'ar.. sadeeq ya damu kwarai amma bae sanar da safwan komae ba.

Ganin lokacin shiga kotun ya kusa yasa safwan tafiya don dauko su umma..

Yana zuwa ya tarar duk sun shirya amma kaf basa cikin walwala.

Fargaba ce fall cikin zuciyarsu. Kowa da irin nasa tunanin..
Suna tsoron sharrin su kawu..

β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘
Lokacin da suka zo harabar kotun makil take da mutane. Daga gani kasan akwai babbar shari'ar da zaa gudanar..

Bayan an gama sauraron shari'ar mutanen nan alkali ya bukaci jin shari'a ta gaba..

Nan aka gabatar da shari'ar su kawu.. Shari'a ce tsakanin wasu marayu da suke tuhumar yan uwan mahaifinsu akan danne musu dukiyar da suka gada wajen mahaifinsu.

Sunana
Barrister *zubair malunfashi* nine lawyen da ke kare wa anda ake tuhuma.

Ni kuma sunana barrister *Sadeeq Kibiya* lawyen dake kare masu kara.

Bayan yan tambayoyin da barister sadeeq yayi wa su kawu.. Sun bashi amsa daedae gwargwado..

Barrister zubair ne ya bukaci ganin umma, bayan ta tsaya ya shiga jero mata tambayoyi.

Bayan ta gama basu labarin abubuwan da suka faru har zuwa mutuwar mijinta.

Barister zubair ya kalle ta sannan yace, a baya kin nuna wa kotu mijinki sun sami matsala da yan uwansa a baya chan.. Amma daga baya kuma sunxo sun shirya.

Sannan kin nuna ma kotu irin kaunar dake tsakanin mijinki da yanuwansa ko?? Haka ne ta bashi amsa.

Murmushi yayi sannan ya cigaba, ya mai girma mai shari'a ni a ganina mutanen da suke son danuwansu sosae ba zasu iya cutar dashi ba

Bayan haka ya mai girma mai shari'a, wa dannan sune takardun kadarorin marigayi, ina so kotu da duba da kyau, ga sa hannun marigayin nan wanda yake nuna ya mallakawa yan uwansa duk wani kadarorinsa,..

Umma ya nuna wa takardun don ta tabbatr da sa hannun mijinta.

Bayan mai girma mai shari'a ya duba ya kalli umma sannan yace

Kin yarda wannan rubutun mijinki ne ko kina da ja??

Bani da jaa ya mai girma mai shari' a..

Barrister Zubair ne yayi murmushi ganin akwae alamun nasara sannan ya dora.

Ko hajiya zata iya gaya mana dalilin da yasa batayi aure ba har wannan lokacin??

Objection ya mai girma mai shari'a a cewar sadeeq..

Bai kamata bartister zubair ya dinga neman shiga personal affairs ba..

korafi ya karbu barister a kiyaye.. cewar alkali..

Murmushi ya kara yi sannan ya umarci umma data koma ta zauna..

Mamaki sadeeq yake ganin shari'ar na neman juya musu..

Barrister zubair ne ya cigaba: ya mai girma mai shari'ai ina son ka duba wannan shari'a, bata da wani sarkakiya.

Alkali ya kallk sadeeq yace ko barrister sadeeq yana da abun cewa??..

Eh inada shi ya mai girma mai shari'a..

Ina bukatar ganin tukur da ja'afaru domin su sake amsa min wasu yan tambayoyi..

Bayan sun fto, kawu

Please Login or Register in order to submit comment