Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fad'a cikin kwallar furar datake damawa kamun sume da k'ofar surufe gammm😂


Eggo kuwada tinda ta hangi mama da wayannan zakunan hankalinta yatashi Kuma duk abunda suke itada aminan nata eggo na kallo hakan bakaramin Kara daga Mata hankali yayiba sanadin hakan yasa tashiga wani mugun shock Wanda yahanata Koda kwakkwaran motsi seda yanzuda kowa yawatse mama tarink'ata tana fad'ar eggo mike faruwa ne tashi muje gida kowa Babu agun...arazane eggo tajuyo tana kallan mama kamun tajanyo da k'arfi tarungume tana dudduba jikinta kamar mene man wani abun..can Kuma tamik'e dasauri takama hannunta suka nufi gida itadai mama tana biye da eggo tana mamakin wannan Al,amarin..!


Dubai


Yau jumu,a Kuma kowa a part d'in habibbty zeyi breakfast dinner dakuma lunch...cike parlourn habibbty yake da zaratan samarin jikonkin nata da yammata se iyayensu Wanda idanda perlon bayada girma to baze tab'a daukarsuba...Yaya suhaif ne yashigo Yana turo kujerar da ammy ke kai yayin da kannenshi ke takemai baya sallama sukayi kowa ya ,amsa kana yasamu wuri kusada iyayen nasu Mata ya,ajiye ammynshi kana yaje gun habibbty yaringoneta Yana gaidata suma duka su Al,Hassan hakan sukayi kana suka shiga kaida iyayen nasu abbu suka fara gaisarwa sa,annan Abba se dady da uncle A kana iyayen mata..daganan Yan uwansu suka shiga gaisawa da juna...seda kowa yanutsu bayan anga gaishe gaishen kana suka fara cin abunci in da suhaif ya fara bawa mahaifiyarsu Amma hajiya suhaima tahana tahanyar karbar abuncin daga hannunshi ta shiga bata hakan kuwa bakaramin dad'i yayi musuba duk da in da sabo sun saba, muddin akazo cin abuncin nan part d'in habibbty to d'aya daga cikin iyayen nasu matane zata Bata...bayan angama cin abuncin ne masu aiki suka gyara wurin kamar yadda aka Saba d'aya daga cikin samarinne yamik'e me suna muhufas yashiga had'a wata katuwar computer dakenan perlon habibbty seda yagama had'a komai kana yamik'e yakoma wurinshi tareda d'aukar wayar habibbty yashiga contact d'inta yadannwa wata nomber Kira ta WhatsApp seda tayanke aka sake Kira kana Wanda ake Kiran yad'aga d'auke da sallama abakinshi yayinda Kuma ya bayyana awannan katuwar computer mekamar Rabin bagon perlon... murmushi yayi kamun yayi magana habibbty tace jalaludeen kana lpy? Cikin far,a da farin cikin ganin ahalinshi jalaludeen yace lpy qalau habibbty kana ya gaisar da iyayen nasu sake wurin bayan kowa ya,amsa cikin farin ciki k'anen nashi suka shiga fad'ar Yaya jalal barka da safiya duk acikin larabci suke maganar Yana amsa musu seda duk suka gama gaisawa kana yadubi alhusain yace little bro yajikin ammy? Amma d'auki Yaya jalal...to allah yabata lpy...duk suka ammasa da ameen kana yammata suka shiga zuba mishi tab'ara Yaya jalal kasiyomun Yaya jalal kayimun kaza hakan sukayita seda iyayen suka gaji kana sukayimashi sallama aka riwani...jalaludeen duka shine babba acikin ahalin gidan Kuma shima sojane sedai Shi Yana aikine a Nigeria acikin garin Abuja.

Bayan ankashe aka Kira Zaid shima hakan akayita yi mishi duk da be cika sakewa kamar Yaya jalal ba bayan anshene aka Kira wata number, Amma me wannan number seda akayi masi Kira hud'u kana yad'aga, Yana zaune cikin office d'inshi atake kyakkyawar fuskarshi tabayyana sedai ad'aure take tamau ba wani walwala atare dashi kallanshi habibbty tayi nadan lokaci kum tace *ALYASAT* kana lpy? Lumshe kyakkyawan idanuwanshi yayi kamun yasake bud'esu cikin so da k'aunar kakar tashi yace lpy qalau habibbty ya k'arfin jikinki? "" Alhmdllh alyasat y aikin? Shiru yayi kamar bejitaba kamun yabud'e baki kamar bayaso yace alhmdllh sa,annan ya shiga gaishe da iyayen nasu dakyar domin jinyakeyi gabaki d'aya ya wahala wannan Yar maganar dayayi danshi baya k'aunar Friday d'innan tazo sabida kiraye2 Nan

Nan shima kannenshi suka shiga gaidashi Amma hankalinshi na kan ammy daketa dokamai murmushi..seda duk suka gama wayar harzeyanke domin yagaji wlh sekawai yaji ance yaya sat I miss you..atake duk anunrin fuskarshi tad'auke yak'ara take fuskarnan sosai kamun yakashe wayarshi kawai...itako muhibbat dataga yayi Mata hakan se kawai tasaka kuka cikin Jin haushi mama Billy tabige Mata Baki karma wani yaji bayasan Kuma ta makaraba domin d'ay d'ayku ne kawai Basu ganiba.

kamun asake Kiran wani hakan akayita Kiran yaran gidan d'aya bayan d'aya duk akagaisa da way'anda basa gari kana akayanke wayar kowa ya fito zuwa wurin aikinshi bayan Al, Hassan ya maida ammy part d'inta tareda damk'arta hannun anty ayame.

Ahakan motocinsu sukabar gidan ajere kamar yadda suka Saba.



Ba,afayikomaiba yanzune asalin cankalen zefara💃



*SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500 kacal ka duk me buk'atar complete kuma 700 Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub'ar wannan number 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 👉 08107819124






Autar Alheri ✍️

🚀 *SOLDIERS FAMILY*🚀
(Romantic novel)


*By Dr Yasmeen Ahmed*


Autar alheri ✍️

Page 7&8

__"sunyi nisa cikin tafiyar mejo sadam yadubi suhaif yace, "bro wai yamaganar zuwanmu India ne?" Numfasawa suhaif yayi kana yace, "miye anfanin zuwa India bro abunda ba,ayiwa ammy ananba India za,ayinshine?"

"Aa gaskiya sedai kasan yadace familyn ta Susan halinda take ciki kokuwa?"

"Hakane Amma kasan ya alyasat ba yadda zeyiba domin yatsani Al,adunnan nasu Kuma abunda kasanine..."

"eh to Amma bazamu saka su dady suyi magana dashiba?"

"humm mejo kenan sekace bakasan waye ya alyasat ba..."


"Gaskiya ne Kuma nasani abunne me wahala ya amince, Amma Bakomai muyi magana da ya Yusuf nasan shi zai saurareshi.."shiru suhaif yayi kamar bazai yi magana ba sai kuma yace, "bakomai bro Allah yasa ya, amince"
"ameen dai" cewar sadam kana sukaci gabada firarsu.

Acan gida kuwa suna fita habibbty tafara k'wallah tana addu,ar Allah yabayyana Mata yaronta abun soyuwa agareta aduk inda yake afad'in duniya..da kyar su Abba suka lallaɓata tayi shiru suna fatar Allah yabayyana Dan uwan nasu.!


Shinkafi

Su mama nashiga gida eggo tashiga had'o kayanta Dana mama ba tare da ta cewa mama ko mai ba, ita ko da kallo kawai take bin mahaifiyar tata, sai da eggo ta had'a komai da suke buk'ata kana tajawo mama tare da rufe gidan suka fita tafiya sukeyi sosai da k'afa sai da mama tagaji tadubi mahaifiyar tata tace "eggo Wai Ina zamujene hakan?

Sokoto eggo tafad'a atak'aice...Ido mama tazaro kamun tace sokoto fa kikace eggo da wannan yammacin Kuma ak'afa? Shiru eggo tayi kamar bataji mitaceba sai da mama tasaka Mata kuka kana tadubeta tace, "yanzu zamu shiga cikin garine musamu motar dazata shiga sokoto saboda hakan wlh kiyimun suru kafin na faffala miki mari anan..." shiru mama tayi bata karayin magana ba har suka iso cikin gari suka ko yi sa,a motar sokoto tacika saura mutin d'aya...shiga sukayi inda eggo tad'ora mama akan kafafunta suka d'auki hanya sai da suka baro cikin garin zamfara sai kawai motarsu tatsaya ahanya ashewai Yan bindiga ne sukayiwa motar kawanya ...cikin tashin hankali kowa dake wurin yakama salati kamun duk akafito dasu waje..gabaki d'aya akasetasu da binda za,afata farfesun kanunsu se kawai wani daga cikinsu yace, "Ku da kata karda mu kashe way'annan kawai mu,ajiyesu Idan ansaki kud'i musakesu....angama oga cewar yaranshi kana aka tasa k'eyar dukan mutanen dake cikin motar izuwa cikin surƙurmin jejeji...hankalin eggo in yayi dubu to ya tashi, Dan ganin wannan taddancin amma mama ko akwalar rigarta sai da sukayi tafiya mai nisa kana suka cinma mafakarsu anan duk aka ajiyesu kana suko sukashigayin abin gabansu.!


London

"Zaune yake acikin kantamemen office d'inshi Yana duba wasu peril kawai akaturo k'ofar akashigi..shiru yayi name cigaba da abunda yakeyi domin tasan ko ba a fad'a ba, ba mai shigo masa office kai tsaye in ba lateep ba, kujera ya samu ya zauna Yana fad'ar big man wani abunda ya taso anturamu Dubai yin wani aikin Kuma hadda sunanka aciki...d'aukowa alyasat yayi Yana kallan lateep din kamun yace banada ra,ayida hakan big man saboda hakan kawai kuje....shiru lateep yayi nadan wani lokaci yasan tinda yace bayada ra,atabbas bazejeba domin alyasat bayabin umurnin kowa shike bawa kansa umurni Kuma haryabawa manyan nasu saboda yadda suke tsananin ji dashi, domin yasan aikinshi Kuma jarimine na bugawa ajarida...okay badamuwa Naga mutuniyar na nemanka koka ganta? Shiru yayi mashi kamar bejiba... "kana fa jina Dan renin hankali kawani shareni ☹️"

Nan ma ko kallanshi Alyasat beyiba..ganin hakan yadaka lateep dariya yafita Yana fad'ar "Allah yashiryeka big man inda akebibiyar mutum ana sonshi shikenan yana wulakanta mutane..."

Shidai alyasat banza yayi mishi kamar baiji me yace ba?, yaci gabada aikinshi..!


Dubai


"Wai miyake damunkine muhibbat? Tayaya zakice bazaki iya boye sonda kikeyiwa Alyasat ba yanzu har kinjawo yana wulakantaki abanza nace kibar komai ahannuna amma kink'i indai inaraye kisani alyasat bayada wata Mata datafiki aduniya anty Billy keta wannan banbamin domin bataji dad'in yadda alyasat yayiwa Yar tata ba ɗazun agaban kowa...""wlh anty inasanshi ne narasa yazanyida zuciyata anty in Sha,awar yaya sat Ina sanshi anty Ko da baze aure ni ba ya mayardani dadironsa Allah inaso....wani dogon tsaki anty Billy tayi kamun tabbema aurenki zeyi bawani dadiro Allah natuba uwarsama tayi kad'an balleshi...cikin sauri muhibbat tarungumi mahaifiyar tata tana fad'ar I love you so much my anty nasan tabbas Zaki iya inanan inajiranki antyna kimallakamun zuciyar Yaya sat ahannuna...itama rungumarta tayi tana fad'ar angama my sweet baby.!"


*Asalin labarin*


Wannan family na alhaji shuraim ne shikeda wannan stet d'in Yana Mata d'aya ruk'ayya wadda yaranta kekirada habibbty Alhaji shuraim attajirin me kud'inne acikin garin Dubai Allah ya arzittashi da samu zuri,a y'ay'a maza domin yaranshi 9 Kuma dukkansu mazane mace d'aya kawai acikinsu ukku daga cikinsu Allah yakarb'i abunshi akabar mace d'aya maza 5 tin tadowar yaranshi Allah yasaka mishi son su zama sojoji Amma dukkanku suka botsare se mutin d'aya ne ya yadda wato danshi na ukku habeeb shine kawai yayi karatun soja ganin hakan Alhaji shuraim ya mallakawa habeeb dukiya mayyawa Amma bada sanin Yan uwanshiba Kuma yad'oki son duniya yad'orawa habeeb hakan kuwa bakaramin bakantawa Yan uwanshi yakeba dudda Basu tab'a nuna waba.

Ana hakan har sukayi munzilin aure inda Alhaji shuraim yace, "dukkansu anan zasu zauna tare dashi ya siya wani katon fili yak'arawa wurin girma bana wasa ba acewarshi duk Wanda yataso cikin zuri arshi baze fita wajeba anan cikin stet d'in zezauna...hakan yayiwa yaranshi dukkansu aure naseer Marwan Jameel Imran da Kuma habeeb kowanne daga cikinsu balarabiya ya aura se habeeb ne kawai yace ba india yake so duk da cewar hajiya ruk'ayya bataji dad'in hakan ba Amma bayadda ta,iya tinda mujinta ya amince ahakan akayi biki kowanne yatare da amaryarshi.


Bayan wasu shekaru kowannensu Allah ya albarkaceshi dasamun zuria Kuma suna zaune lafiya da dukan matansu ba wadda zakace tanada wani mugun Hali aciki sedai ma,isha dabata shiga sabgar kowa Kuma inkasakata bazata kiyimaba tanada kirki sosai domin sedaga baya Habibbty taji dad'in barin d'anta datayi ya aureta....zama sukeyi medadi tsakaninsu ba zaka tab'a cewa akwai wani mummunan abuba acikin ransu ko kad'an.


Alhaji Marwan yana da Yara 5 hasheen nusaiba Ibrahim shuraim mesunan babansu sekuma sadam.

Alhaji habeeb kuwa yaranshi hud'u alyasat suhaif sekuma twins Al,Hassan da alhusain.

Alhaji Jameel nada Yara 6 jalaludeen yusif basheer sulaiman suheil sekuma najeeb.


Alhaji naseer nada Yara 4 Hakeem Walid domin sunan mahaifin mamansu ne dashi..se Fahad se Kuma muhibbat.

Alhaji Imran yanada Yara 7 dukkansu maza sufiyan shareef sadeeq sultan Zaid haisam dakuma Ameer.


Se autar hajiya suhaima tanada Yara 4 nafeesat mardia Mansoor dakuma lateep duk shine babba acikin yaranta.


Tin tasowar yaran gabaki d'aya da habibbty suke kiran hajiya ruk'ayya kamar yadda sukaji iyayensu nafad'a.... dukkansu yaran sutaso cikinso da k'aunar junansu sedai kowanne daga cikinsu hallayyarshi daban...bayan sunfara girmane sungama makaranta abbee dakanshi yanema musu form na makarantar sojoji dake Nan cikin kasar Dubai wasu Kuma a London kabaki d'aya yaran maza Kuma iyayensu Basu hanaba domin sunsan abunda mahaifinsu keso kenan... dukkansu abbe yad'auki nauyin karantunsu har suka kammala wato alhaji habeeb shi suke kirada abbe.

Gabaki d'aya yasama musu aiki kowanne yafitoda saka mako me kyau Kuma aka dorashi ababban matsayi acikin aikinshi inda alyasat da Yusuf sekuma lateep suke aiki a London domin suna kaga training d'insu sukace bazasu Bari suyi musu nisa ba.

Alyasat Yusuf da Kuma lateep sunshak'u sosai da junansu inda d'aya baya iyayin Abu seda sanin d'ayan Kuma hakan bakaramin dad'i yayiwa iyayensuba sedaifa dudda hakan alyasat yanada wuyar Sha,ani da murɗadɗan hali...shekaru sunja suna zaune lafiya dajin dad'i acikin ahalinsu se kwatsam wata Rana aka wayi gari Babu alhaji habeeb Babu dalilinsa anyi neman duniya ba,asameshiba Kuma anrasa Ina yaje tin ana kallon abun amatsayin almara arbu yazama gaske domin yanzu kusan shekara 7 kenan babushi Babu labarinshi....Kuma bayan b'atansa da wata 2 ammy takwanta ciwo Wanda sunyi yawo asibitin duniya anafad'ar ba,agakomaiba Bata iya magana Kuma Bata iya motsi ba,abunda ke aiki atareda ita se fuskarta wannan lamarin bakaramin Kara daga hankalin wannan family yayiba inda alyasat yak'ara komawa kurman k'arfi da yaji dakuma rashin son sakewada mutane Dana ya lafiyar Kura🤔


Mukoma cikin lbr kaitsaye


Bayan fitar lateep wayarsa yad'auka tareda Kiran wani yaronsa bayab yad'auka yace yafitoda mota zasu fita..ok Sir kawai maskurr yace kana shiko gogan yayanke wayar tareda kwasar wayoyinshi yafita.!


Zamfara


Yau kusan kwanan su mama 4 acikin wannan jeji Kuma baci Basha sedan abunda ba,arasaba zaune suke jugum 2 inda wasu ke kuka wasuko sunata Kiran Allah....ahakan Yan bindigarnan sukazo suna masu kallo wulakanci kamun Sununa wata yarinya dabazata wuce da,ar mama ba yace tazo bamusu yarinyar tafita..abum mmki cikin tashin hankali wannan mutumin ya tuɓe yarinyarnan agaban kowa ya duk'a ze kwanta da ita tana kuka tana karkarwa.

Cikin tashin hankali eggo yace innalillahi wa innailaihhiraji un kayi human Allah da zatinsa karka cutarda wannan baiwar Allah k'aramar yarinya ce it....kobaki bebari eggo tarufeba yaketa alfarman wannan yarinyar tana ihu tana k'arawa cikin tashin hankali duk Wanda ke wurin yashiga rusa kuka suna neman mafita awurin Allah...seda yayiwa yarinyar fata2 daga baya har gaba kana yad'agata kamun wannan lokacin tuni yarinyar tamutu😥


Wani daga cikinsu ne yanuna mama daketa rusar kuka domin mama akwai tausayi gashi Kuma tabaro shinkafi balle tayi tinanin ganin aminanta sutemaka musu...kin tashi mama tayi se harara datake ballamai shiko gani Taki tasowa tanason renamai hankali kawai seya Mika hannu ya fincikita tareda wullarda ita yabita ze danne arazane eggo yad'ago tana dubanshi tareda rikeshi tana girgizamai Kai Tama kasa magana...shiko cikin rashin Imani darashin sanin darajar furfura kawai ya hankad'e eggo seda tabugu akan wani dutse sebata k'ara motsiba....Ido mama tazaro tana me.....!





*SOLDIERS FAMILY* na kud'i ne nera 500 kacal 👌 ga duk me buk'atar complete 700 Idan kinshirya siya Zaki iya tuntub'ar wannan number 👉 07037092176 on WhatsApp kokuma kikira wannan number 👉 08107819124





Autar Alheri ✍️

🚀 *SOLDIERS FAMILY*🚀
(Romantic novel)


*By Dr Yasmeen Ahmed*


Autar alheri ✍️

Page 9&10


__"tana me hantsilowa daga k'asa kamar wata aljana hakan tadira gunda eggo tafad'i juyo da ita tayi, tana kallon yadda jini ya b'atawa tsohuwar fuska cikin tashin hankali, ta shiga girgizata tana fad'ar sunanta Amma ko gezau eggo batayiba...abunda mama Bata saniba tuni eggo takarb'i Kiran mahaliccinmu....

Shiko wannan banzan mutumin wurinta yadawo tare da zabga mata marin da saida ta ga wasu taurari, Babu Imani balle tausayin ganin ya kashe mata mahaifiya hakan yak'ara fisgarta tareda wullarda ita awurin....Amma ni k'ememe mama taki kai k'asa gata dai ta tafi kad'an ya rage bayanta ya tab'i kasan tinda jefata yayi Amma be tab'a ba Kuma bata ta soba....duk Wanda kewurin kallonsu yakeyi cikin mamkin wannan abun ciki kuwa hadda sauran Y'an ta,addan Yan uwanshi.

Kuma yazo zai turata dak'arfi...kamun hannunshi yakai jikinta yayi Bala,in Jada baya saka makon idonta data bud'e hawanyen jini nafita bako k'ak'k'au tawa sun wani birkice kamar ba nata ba....duk Ido suka zaro suna kallonta...itako ahakan ta taso tana mik'ewa tsaye kamar ana turo icce ko saƙaho.

Baya sukaja dukkansu suna Kara kallonta amutukar tsorace suna neman fecewa...itako mama cikin k'ank'anin lokaci kamannin ya sauya kamar aljana.

Wani daga cikinsu ne ya yarda bindigar hannunshi, tare da rugawa aguje domin ya gama sadak'arwa yau aljana ce suka ƙwamuso ba mutum ba....ai beyi aune ba yaji anfin cikoshi tare da makashi akan wani dutse atake kansa yatarwatse ko shurawa beyiba yace, "Ga garinku nan"



Ihun sauran suka saka ganin mama ko daga inda take bata motsa ba Amma Tamik'arda hannunta tacimma wannan mutumin harta kamoshi....ba,iya Yan ta addaba duk da sauran mutanen da aka kamosu tare ahalin yanzu amugun tsorace suke fiyeda Wanda sukeji daga farko.....tsayetake kawai tana k'arewa duk Wanda ke wurin kalllo kamun tashiga d'aukarsu d'aya bayan d'aya tana makasu afuk inda tasamu wasu akan dutse wasu akan manyan bishiyun dake wurin wasu Kuma kasa seta tabbatarda ta karairayawa mutin kasusuwan jiki kana tayi masa d'aya Wanda baze Kara numfashi ba.....iya tashin hankali yan ta,addan Nan sunshiga domin izuwa wannan lokacin sun riga da sun yadda da aljana ce suka sato domin duk ya wansu gashi tana neman karardasu Kuma Kara Yar Loma figigiya da ita.

Ahakan mama tayitayin tamaula dasu seda taga bayansu Wanda yakashe yarinya kuwa biyu tarabashi domin kafawanshi tarik'a tareda yageshi gida biyu duk Wanda ke wurin seda yarufe idonshi....datazo kan Wanda yakashe eggo kuwa kisan wulakanci tayi masa domin seda tagama ragargaza kasusuwan jikinshi kana tashiga ɓallahsu gab'a gab'a tana jefarwa seda taga yagama nakassa da galabaita yasuma Babu adad'i azaba na farfad'o dashi kana ta cire mashi kai tawulgar.....dubawa tashigayi ko Ina tananeman taga ko akwai Wanda yarage Amma ba ko d'aya...suko sauran bayin Allah da,asatosu tare gabaki d'aya sun cure wuri d'aya wasu duk sun suma sabida firgita wasu kuwa kamar zukatansu subuga saboda razana....ganin Babu saura b'atagari awurin sekawai tasamu gefen bishiya tazauna tareda rufe idanuwanta.

Ganin hakan yasa sauran bayin Allah sukad'an samu natsuwa acikin ransu domin sunyi tunanin daga ta gama da Yan bindigar gunsu tayo.....sund'au tsawon lokaci ahakan kamun wani daga dattijuwan wurin yayi k'arfin halin nufar wurinda gawar eggo take seda yaduk'a Yana kallanta yaga tabbas Bata numfashi d'agowar dazeyi yaga mama tabud'e idanuwanta da har yanzu basu sauyaba tana kallanshi seda yad'an zabura da kallon datayi nasa domin ya razana sosai sekawai yaga tamayarda idonta ta lumshe ajiyar zuciya ya sauke mek'arfi kana sauran Mata dake wurin sukazo suka d'auketa daganan kana wani dattijo Daban yaje kusan mama cikin tsoro da fargabar abunda zuwan nashi ze haifar yafa fad'ar y'ata Dan Allah kiyi hak'uri kitashe muje cikin gari kekaigun dankinku akai gawar baiwar allarnan...shru mama tayi kamar bazayi maganaba sekuma tabud'e Baki dakyar cikin wani voice me ban tsoro tace bansan inda danginta sukeba kawai kuyimata sitira kamar yadda addini yatanadar.

Cikin sauri tsohonnan yace, "to shikenan yarnan tashimuje cikin gari ayimata suturar"...."kuje zanzo ta fad'a atak'aice"... Tun Bata rufe baki ba yace, "to shikenan sekin k'araso" Yana gama fad'ar hakan yabar wurin domin shikanshi da basin mama yayi ba Adan zaman da sukayi yasan ba muryartace ba tunda yanaji tana yiwa mamarta magana wani lokacin.!

Yana zuwa tasanarda Yan uwanshi Aiko suka d'auki eggo akayi cikin gari da ita duk da sunci bak'ar wuya kafin sufita saboda nisanda kenan...bayan sunfitone Allah yakawo musu wata mota babba kamar boss duk sukashi bayan sunyiwa memotar bayanin inda zekaisu..

Basu tsaya ko ina ba seki dan wani daga cikin dattijuwan suna Isa ba suka Sami mama zaune ak'ofar gidan ba wanda yayi mmkin ganinta Idan sukayi duba da abunda ya faru b'ata lokaci akashiga yiwa eggo sutura domin sadata da gidanta na gaskiya...sai da duk aka gama yimata komai za,afitada ita kana d'aya daga cikinsu yazo domin ya kira mama taganta kafin su fita da ita...Amma seya samu tana bacci mamaki sosai abun yabashi harzetafi yabarta sekuma sekuma wata zuciyar tace yatadata hakan yashiga tadata yad'an jima Yana Dan buga k'afarta kamun tayi firgigit tamik'e zaune tana rarraba Ido tareda doba inda take atake atake abunda yafaru yashiga dawo mata tun inda wannan mutumin yafincikota har hankad'e eggo dayayi wani irin zaro Ido mama tayi tareda mik'ewa tana fad'ar, "eggo eggo kina inane Ina mahaifiyata? Me mukeyi anan? Misuka Mata? Dan Allah Ina sukaimun eggo ta?" K'wallah wannan bawan Allah yashare kamun ya janyo hannunta izuwa inda gawar eggo take kwance..Yana zuwa wani ya bud'ewa mama fuskar eggo daketa fitadda anuri cikin suturarta kamarba matacciyaba...wani irin jaa baya mama tayi tana k'walalo duka idanuwanta kafin ta k'wall k'ara tana Kiran eggoooooo innalillahi wa innailaihhiraji un nashiga ukku 🙆 Ni mama sunkashemun mahaifiyata ba tare da takaini garinsu ba sun rabani da farin ciki na na shiga ukku Ni mama.... kuka takeyi sosai akan gawar eggo dakyar aka d'aga ta wata mata tayi cikin gida da ita kana aka tafi kai eggo gidanta na gaskiya....ansha fama da mama awannan wunin domin in banda kuka ba abunda takeyi ahakan har dare yayi duk me Imani Idan yakalli mama dolene ya tausaya mama Inka duba karancin shekarunta Babu uwa Babu uba bawani takamme ko jigo arayuwarta😥....cikin dare Mama nazaune tana rusar kuka kowa yayi bacci itace kawai Ido biyu...dafata taji anyi Koda tad'ago taga wata mata tayi shigar fararen Kaya da murmushi kwance a fuskarta...cikin kuka tafad'a jikinta tareda cewa k'awata Ina kikaje sunkashemun eggo ta sunkashet....kasa K'arasawa tayi saboda kukan da yaci karfinta be hanata ba sai da tayime isarta kana yad'ago ta tana share Mata hawaye kamun tace ba k'awarki bace mama yayartace k'awarki da bibibo basanan sunyi tafiya me Nisan gaske domin cika umurnin me martaba nikaina bansan abunda kefaruwa dakeba sai da abokin bibibo d'inki yasanar dani kiyi hak'uri mama munkasa Baki farin ciki kamar yadda muka d'auke alkawari munkasa tare Miki faruwar wannan abunda yasameki Amma kiyi hak'uri komai na duniya me wucewa ne watarana sai labari, ki d'auka wannan abunda yasameki k'addara ce daga ubangiji insha Allah komai zai zo ya wuce kinji.

*ZARAAH* d'agowa mama tayi dasauri tana kallan matar Jin ta fad'i asalin sunanta...itako murmushi kawai tayimata tare da shafa kanta tace nizan tafi kinji kirika yiwa mamarki addu,a kidena wannan kinjiko? Kai mama tad'aga cikin sauri kana tace zanbiki kikaini gun bibibo na bazan iya zama ananba Idan narufe Ido eggo nake gani kamar zata dawo tak'arasa zancen ciki kuka..."shikenan ya,Isa mama zanjeda ke Amma bibibo bayanan sedai Idan yadawo Zaki ganshi Zaki iya zama,inda nake? Daga matakai mama tayi cikin sauri..tace to shikenan rufe idonki...ba musu mama tarufe idanuwanta wannan matar ta b'ace b'at daga ita har mama kamar Basu tab'a wanzuwa awurinba..!


Tofa 🤔 wayannan bayin Allah wasukayiwa alkawarin zasu bawa mama farin ciki? Shin meyema had'inta dasu? Dasuka kasance wani gefe na rayuwarta?


Koda safiya tawaye mutanen gidan suka nemi mama sama da k'asa suka rasa abun kamar wasa har dare Babu mama abubu Alamarta megidanne yace sukwantarda hankalinsu kila mutanen datake taredasune suka d'auke ta tindadai ba wanda yashigo gidan balle ayi wani tunanin daban....sai a lokacin hankalinsu yad'an kwanta dudda basuji dad'iba Sam domin sunso rike mama tsakanida Allah domin tabasu tausayi matuk'a sai dai ba yadda za suyi da k'addarar rayuwarta..!


London


Wata baturiyace tsaye bakin k'ofar office d'in alyasat tana rike da wani abun ahannuta me kama da babyn roba (y'ar tsana) sedai kallo d'aya zakama abun kasan ba alkhairi a tare dashi duk'awa tayi wurin tana k'ok'arin daga carpet d'inda ke wurin sekawai muyar lateep Yana fad'ar leamtair mikijeyi ananne? Cikin sauri tatura abun cikin kasan wandonta tashiga k'ok'arin zuge igiyar takallminta tana fad'ar takalmanane yakwance Sr shine Zan d'ora.... kallonta yatsayayi kamar me nazarin wani abun domin Sam be yadda da itaba Kuma lateep be,iya b'oyoba Kuma nuk'u2 shiyasa yace ba gaskiya bane leamtair akwai dai wani abun Amma kasani ko miye nagani atare da brother na hummm....Yana gama fad'ar hakan yashige nashi office d'in...da kallo tabishi tana tinanin Hali irin nashi cikin ranta kuwa fad'ar takeyi koza,a mutu saita samu abunda takeso atareda alyasat..


Yau Thursday tun safe alyasat ke kiran k'annenshi domin suhashi da mahaifiyarsu Amma besamu ba kum. Ya tashi da k'ulafucin San yaganta domin hakan kawai gabanshi ke fad'uwa....wayarsa yajanyo tareda Kiran yusif Yana d'auka yace ""bro I will go to Dubai now? "What happened Satt?" Cewar Yusuf... nothing just I love see my mom...."ok wait I'm coming now....okay kawai yace tare da yanke wayar yatashi yashiga wanka bayan minti 15 yafito d'aure da towel akugunshi d'aya Kuma ahanunshi Yana tsane kanshi wurin mirror yanufa yashafa mayukanshi masu kamshin dad'i kana yafesa titare wurin kala ukku kamun yad'auko kayanahi yasaka kananun kayane wando blue Riga Marron gaskiya bakaramin kyau suka mishiba sufitida asalin kyawun farar fatarshi wayoyinshi yakwasa da jakar computer d'inshi kana yafita aperlo yaci karo da Yusuf da lateep suma duk cikin shigar kananun kayane ajikinsu Masha Allah

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3

2 Comments On SOLDIERS FAMILY
avatar
fatima-9-4-7

1 year ago

Reply

Tnx

avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete document

Please Login or Register in order to submit comment