Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba. Mutum ka tsufa amma ba ka san ka tsufa ba? Ka taho da hanci duk majina, ga tsumma, ka ce kana son giya? To, ba a sayar maka!" Sai Iliya ya Zara marairaicewa ya rarrashi mutumin, amma ya hana shi. Sai liiva ya fadi ya lunshe ido ya yi kamar ya suma. Mutanen da ke wurin suka ce wa mai giyan nan, "Idan ba ka ba shi ba, zai mutu, ka ga ka jawo wata rigima ke nan." Aka debo giya aka sa wa Iliya a baki, nan da nan ya farfado. Aka karo masa mai yawa ya sha ya koshi, har ya bugu. Shi ke nan sai ya shiga kantin giya ya yi kwanciyarsa, ya yi ta sharar barci. Da dare ya yi kwarai masu kantin suka ta da shi, ya ki tashi, sai suka rufe kantin da shi ciki. da asuba Iliya ya tashi, ya sa kafa ya buge kyauren kantin. A cikin kantin akwai wadansu gangunan giya manya manya, wadanda kome karfin kato ba zai ya daga ganga guda ba, balle ya yi tafiya da ita. Iliya ya kwashi guda uku, ya makale ko wace daya a hammata, ya rika tura daya da kafarsa, yana tafe yana cewa, "Duk wanda ke so ya sha giya ya zo nan, har wanda ba ya sha ma in yana so ya zo." Daga can masu giya suka ji, suka biyo shi, suka yi, suka yi, su kwace gangunan giyarsu, abu ya faskara. Sai suka tafi suka kai kara wurin Alkali. Alkali ya aika aka rarraso Iliya. Da jin labarin, sai Waldima ya tsargu, ya tabbata ba mai ya yin haka sai Iliya. Don haka da zuwansa sai ya ce, "Haba Iliya, da ma ka komo cikin kamar ka sosai." Sai Iliya ya bushe da dariya, ya komo kamar yadda kowa ya san shi, Ya biya masu giya kudinsu, ya ba su sauran giyar.

Da dare ya yi, bayan an gama hira, duk fadawa sun watse, sai Waldima kadai da Iliya, Waldima ya ce masa, "Ina so ka taimake mu, ka kubutar da mu daga sharrin wani rikakken dan hari, maridi, wanda a ke kira Falalu. Ko ina ya ratsa cikin kasar nan sai ya rika kwace, yana raba mutane da dukiyarsu, ya kuma ba su kashi. Ya dame mu kwarai, ba mu kuwa da wani wanda zai iya tararsa, sai kai kadai.

Iliya ya yi murmushi, ya gyara zama, ya murza gashin baki, ya san ranarsa ta zo, ya ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara, an gama. Allah dai ya ba mu sa'a. Ina so daga cikin jarumanka, da ka ke takama da su kazabo mini shida mu tafi tare." Amma mutanen nan guda shida ba don komai Iliya ya ke bukatarsu ba, sai don ya jarraba jaruntakarsu. Waldima ya umurci jarumai shida su shirya subi Iliya.
Da lokacin ya yi, jaruman nan suka shirya, Iliya na gaba suna biye da shi, suka nufi hanyar da Falalu ke wucewa.

ILYA YA HADU DA FALALU.ILYA ƊAN MAI KARFI-06

ILYA YA HADU DA FALALU.

CAN wajen asuba, sai sukaji motsin Falalu tafe, yana keta itatuwa kamar toron giwa. Yana tafe yana shan iska abinsa, don ya san ba mai iya tarensa da fada. Ya zo ya wuce ta kusa da inda su Iliya su ke Boye, bai gansu ba. Sai Iliya ya ce da jaruman nan, "Waye zai iya binsa ya ga inda ya nufa? In kuma ya ga da hali ya tone shi da fada ?"

Duka sai suka yi shiru, aka rasa wanda zai ce zai bi shi. Sai wannan ya dubi wannan, wancan ya dubi wancan. Iliya ya dubi babban su ya ce ya tafi. Jarumin nan bai yi gardama ba, ya tashi ya kara jan majayin dokinsa, ya hau, ya bi sawun Falalu. Amma duk zuciyarsa tana dar dar, yana tafe yana kulle kullen yadda zai yi, a zuci. Ya dai tabbata idan suka yi ido da ido da Falalu, shi ba zai kwana ba. Ya yi ta tafiya har ya fara hangen Falalu. Can sai ya hangi Falalu ya tsaya ya dubi kansa ya dubi kayan fadansa, ya, dubi dokinsa, ya yi dariya, ya zaburi dokinsa kadan, ya yi tabi, ya jefa mashinsa sama, ya bi ya cafe, yana kirari yana cewa, "Yau ko da Iliya ta hada mu ma kara! Yau ina zan gamu da Iliya.?

Sa'ad da jarumin nan ya ji Falalu ya ambaci Iliya sai ya tuna shi ma jarumi ne, nan da nan zuciyarsa ta motsa. Daga can nesa, ya ce, "FALALU! Karyar ka ta sha karya, maza bisa kanka. Idan ka sake kuka yi arba da Iliya, sai dai wani ba kai ba!"

Falalu fa ya juyo a fusace ya ga mai magana. Ya yi. wata irin kururuwa mai ban firgici, kamar aradu ta fadi Sai hayaki ya rika. fita daga bakinsa, har da wata irin walkiya kamar hadari ya taso. Akwai wata korama ku sa da shi, nan da nan sai ruwanta ya kada yana kumfa. Ya nufi jarumin nan a sukwane, shi kuma ya juya a guje ya koma wurin su Iliya. Saboda sauri har dokinsa ya yi sassarfa ya fadi. Ya tashi da rawar jiki ya hau ya ci gaba da sukuwa har ya kai wurin Iliya, yana haki kamar ransa zai fita. Da ya farfado kadan, ya fada wa Iliya abin da ya. faru.

Duk abin nan lliya zaune ya ke. Ko da ya ji labarin kuwa sai ya yi murmushi, ya kara kishingiɗa, ya rika wasa da kafarsa. Ya dubi jaruman nan ya ga duk sun rude kowa ido ya fito. Ya ce, "Allah Sarki, tsufa ya zo mana ga shi kuwa ba mu da magada." Sai ya yi wuf ya tashi ya tafi wurin Kwalele, ya shafe shi ya yi masa Kirari.
KWALELE DOKIN ILIYA, KWALELE DOKIN YAKI BANI SAISHE KA, BANI KUWA BADA ARONKA!

Kwalele ya yi haniniya kamar ya san abinda Iliya ke fada. Daga nan Iliya ya gyara, ya dauko sirdi ya aza ya daura, tamau, Ya sabi kulki ya rataya takobin Wargaji, ya dau mashi da kwari da baka, ya zabura ya nufi wajen Falalu.

Da suka kusa haduwa sai Iliya ya fara hargowa, yana cewa, "Kai lalataccen maridi, Barawo. Don me ka shigo kasarmu ba da iznimmu ba!" Falalu ya fara harzuka, ya cika da haushi. Ya zaburi dokinsa, Iliya kuma ya kwarari Kwalele, za a yi karon battar karfe. Suka hadu suka ja baya, ko wannensu ya jawo kulkinsa, suka yi ta rusawa juna. Kowane aka buga sai ka ji kamar ana fasa dutse da nakiya. Dajin wurin duk ya rude da amon duka, da rurin mazaje. Itatuwa kewayen wurin duk aka tattake su. Suka yi ta yi har duk kulaken suka karye, babu wanda aka yi wa rauni, Kana suka jawo takubba. ji kake kakas, kakas, sune sarar juna. Idan takubba, suka gamu sai tartsatsin wuta ya tashi ya yi sama kamar walkiya. Kafin a jima takubba suka lalace. Ko wannensu kuma ya sunkuci mashi suka yi ta sukar juna, har masun suka karairaye. Daga nan sai suka yi tsaye cirko cirko, suna kallon juna kamar zakaru. Da suka huta, sai suka kama fada hannu da hannu, suka yi ta yi har da ya yi, gari ya waye, rana ta fito ba su rabu ba. Suka sake wuni suna ta dambe da kokawa, har dare ya yi, ba su rabu ba, sai da suka kwana uku.

Can Falau ya tuna shi yaro ne, ya kwashi Iliya ya yi sama da shi, ya fyada da kasa ya bi ya danne, ya zaro wani gajeren gatari ya kirɓa masa a kirji. Saboda zafin naman Iliya da iya yaki ya goce, gatarin ya sari kasa. Ya yi wuf ya rike hannuwan Falalu da kyau, ya dube shi ya yi dariya ya ce, "Kai, yaro manya gabanka! Kura ba farkar kare ba ce. Rubutaccen al'amari ba shi canjuwa. Samari daga ina ka fito, mutumin wace kasa ne kai, Wa ya haife ka!"

Falalu ya ce, "Yaro yana bayan uwarsa. Kuma ba ruwanka da kasarmu, ko iyayena !" Wohoho, ai sai ka ce ya watsawa Iliya wuta, Ya fusata, ya sunkuci Falalu ya wujijjiga, ya kwala da kasa, ya bi ya take. Tsofo mai daka wa yaro kashi. Ya ce, "Manya ke magana da kai yaro. Ka fada mini abin da na tambaye ka ka huta! "Falalu ya cira kai ya dubi Iliya ya ce, "Kai dattijo ko giwa ta san zaki! Ai ba kamata ke magana biyu ba.
Abin da na fada maka da farko, shi ne."

Iliya ya kara fusata. Ya tallabo kan Falalu zai yi masa fashin albasa da wani irin. mulmulallen karfe, wanda aka yi don irin wannan rana. Falalu fa ya ga halaka a fili, sai ya ce, "TSAYA! Ka yi mini rai, zam fada maka." Sa'an nan Iliya ya saki kan Falalu Tilas ba hakuri ba. Bugu mai kashe kura! Baban Falalu sai dubu ta taru.

Muryar Falalu na rawa, ya ce, "Uwata Sarauniya ce, amma ubana wani mayaki ne shahararre, ya kuwa mutu. Da na girma ni kuma na ce sai dai in mutu wurin yaki kamarsa. Lokacin da zan fito daga gida, ta yi mini addu'a, ta kuma yi mini wasiyya cewa duk inda na gamu da wani da ke kira ILIYA-DAN-MAI KARFI In roke shi gafara in wuce, kada in yi fada da shi. Wai shi kadai zai iya halaka ni cikin duniya. Wannan shi ne iyakar abin da zan iya fada maka game da labarina."

Da jin haka sai jikin Iliya ya yi sanyi, ya gane lalle Falalu dansa ne. Sai ya tasa shi, ya rungume shi yana kuka. Ya sumbace shi, ya ce, "ɗana, Allah ya ba mu hakuri mu duka. Wannan abu rashin sani ne. Na gafarceka duniya da lahira. Na kuma yi murna kwarai tun da na sami mai gadona." Sa'annan kuma ya fada masa yadda aka yi Sarauniya da irin halin da har ya aure ta ya bar ta, ya shigo duniya. Daga nan ya ce, "To, yanzu saikayi shiri ka tafi gida Ka gaishe ta kwarai. Ka ce idan Allah yayarda wata rana zamu hadu da ita."Falalu tashi ya kakkabe kura, ya durusa ya yi ban kwana da ubansa, ya hau dokinsa ya tafi.

To, abin da Sarauniya ke gudu ya faru. Da ma bata son Falafu ya gane Iliya ne ubansa, ba wani Sarki ba. Ga shi kuwa yanzu ya gano da isar sa is a kofar gidansu, ko sauka bai yi ba, sai ya yi kira da karfi ya ce, "Ya ke wannan tsohuwar banza, munafuka, ashe wani matsiyacin talaka kika aura aka same ni, ba Sarki ba? To, fito, asirinki ya tonu yau !" Ta fito da rawar jiki, tana kuka, ta durkusa gabansa ta ce, "Gani." Falalu bai yi wata-wata ba, sai ya dauke kanta da takobi..

Duk abin nan bai sa zuciyar Falalu ta yi taushi ba, balle ya ji tausayi. Sai ma ya juya ya ce, "Bari kuma in koma inda Iliya shi kuma daya munafikin." Ya juya linzami ya kama hanyar da ya fito, ya yi ta tafiya kwana da kwanaki har ya isa garin da Iliya ya ke. A lokacin ya tarad da Iliya yana kwance yana barci. Sai ya shiga ya dubi kirjin Iliya ya kafta masa gatari.

Fadi zanen dutse, ba shi shafuwa! Manya maganin karakar kasa ! ko da Falalu ya sari Iliya, sai ya sami wata damara ta karfe dake kirjinsa daure, kamar gaba-gaba. Gatarin ya yi tsalle sama kamar an sari dutse.

Iliya ya farka daga barci, ya ga Falalu ne tsaye yana rike da gatari. Ya yi wuf ya kama kafadarsa guda, ya yi hajijiya da shi ya fyada shi da bangon daki, kwam! Nan take Falalu ya mutu ko shurawa bai yi ba. Shi kuma iyakarsa kenan.

Da ya ke mutanen kasar ba su san Falalu dan lliya ba ne sai suka yi ta murna suka kara daukaka shi saboda ya kashe shi. Nan ta Falalu ta kare, Iliya kuwa ya ci gaba da yaki da gwagwarmaya cikin duniya.

ILYA DA YAN FASHI....ILYA ƊAN MAI KARFI-07

ILYA DA YAN FASHI.

Watarana Iliya na zaune yana shan iska a wani katon lambu a bakin kogi, yana kallon yadda kwale-kwale ke ta yawo bisa ruwa, ga tsuntsaye iri iri suna kiwo, sai ya tuna da yaki. Ya tuna irin hadarin da ya shiga, da kuma wanda zai shiga. Yace, "Allah Sarki, tsufa ne. Na tsufa, dokina kuma ya tsufa, amma ga shi zuciyata ba ta gaza ba." Ya yi farat ya tashi ya ce. "Zama wuri daya tsautsayi inji kifi. Ya kamata mu shiga duniya mu ga abin da ta ke ciki."

Da isarsa gida, sai ya jefa wa Kwalele sirdi, ya yi shiri ya kama hanya ya yi ta tafiya. Tun yana ganin alamar karkara, har ya zama ba ya ganin kome sai daji. Ya yi ta tafiya har ya tarad da wani wuri inda hanya ta kasu uku. 'Daya ta nufi dama, daya hagu, dayar kuwa ta mike gaba ɗoɗar. "A daidai wurin da hanyoyin nan suka hadu, an yi rubutu bisa wani dutse mai fadi ance

"WANDA YABI HANYAR HANNUN DAMA, ZAI SAMU ISASSHIYAR DUKIYA.

WANDA YABI HANYAR HAGU, ZAI SAMI MATA WACCE BA KAMAR TA.

WANDA YA MIKE ƊOƊAR KUWA ZAI GAMU DA MUTUWAR SA.

Iliya ya tsaya, ya karanta ya yi shiru yana tunani, sa'annan ya ce, "Ni da na ke tsoho, me zan yi da dukiya? Me kuma zan yi da mace? Bari na bi hanyar da zan gamu da mutuwar tawa in gani. Na sani dai kushewar badi sai badi. Mai rabon ganin badi kuwa sai ya gani!"

Iliya ya sakar wa Kwalele linzami, ya zarce sosai ya tafi. Can ya shiga cikin wani surkukin daji mai duhu. Ba zato sai ga shi gaban taron 'yan fashi, mutum dubu hudu, da babbansu, guda. Ko wanne yana rike da kayan fada iri iri. Suna jira ne kawai wani ya fado, ya bakunci lahira. Basu ankara ba sai ga Iliya gab da su. Suka yi mamaki, don sun tabbata ba mahalukin da ke iya shiga dajin nan. Suka daka masa tsawa suka ce, "Kai mai dokin nan tsaya!" Iliya ya tsaya cif, har suka zo wurin da ya ke. Suka ga dokin ba irinsa duk cikin yankin kasar. Suka ce, "Ina za ka? Me ya kawo ka nan wurin ?" Iliya ya ce, "Na biyo hanya ne zan wuce, ban san zan gamu da ku ba." Sai babbansu ya ce, "Ba ku gani har wani kallon hadarin kaji ya ke yi mana? Kila yana wani dan gani-gani ne gare mu ko?"

Iliya kuwa lalle a kaikaice ba'a ya ke yi musu. Ya sunkuyar da kansa ya ce, "Haba samari, tsofai-tsofai da ni, gani-ganin me zan yi muku? Ba ni da kome sai 'yan kudin guzuri fam dari. Wannan damarar ta zinariya da ku ke gani, duka duka kudinta bai fi fam dari biyar ba. Rigata kuwa tsohuwa ce, kudinta ba zai shige fam dubu uku ba, takalmana da hulata kudinsu da kyar zai yi fam goma. Wadannan likkafun da ku ke kallo tsohuwar azurfa ce, jauharin da aka lillika musu shi ke sa ku ke ganinsu kamar wani abin kwarai, kuɗinsu fam dubu ne kawai. Sirdina, ko da ya ke na karfe ne, ba zai wuce fam metan ba. Dutsen nan da ke bisa kan dokina kuwa, kun dai san darajarsa. Ba shi da wani amfani, sai don ya kara wa dokin gani idan dare ya yi. Dokin kuwa ba shí da wani amfani in ba wurina ba. To, me zai sa ku tare ni? Ni ba ni da kome, ina rokonku ku kyale ni in wuce."

'Yam fashi suka ce wa Iliya, "Tun da mu ke tare mutane, ba mu taba samun sakarai, mahaukaci, kamarka ba." Babbansu yace su kama Iliya. To, a kusa da wani katon itace kuwa su ke tsaye, wanda ba kamarsa duk wurin. Da ganin jama'an nan ta yunkura zasu kama shi, sai ya yi wuf ya zaro, Kibiya ya dubi katon icen nan ya sakam masa, Itacen nan ya ratattake ya fadi ricaa!
Kamar dai tsawa ce ta fada masa. Karfin iskar faduwar itacen nan da karar faduwarsa, ta sa 'yam fashin nan duk suka fadi kasa somammu. Da suka farka, sai babbansu ya ce wa Iliya, "Mun yarda kai ne shugabammu. Muna rokonka, ka zauna tare da mu, ka zama babammu. Muna da dukiya, zinari da azurfa da lu'ulu'u da jauhari da tufafi iri iri, ga kuma dabbobi. Duk yawammu in muka taru ko mun shekara goma ba za mu iya gama kidayar zinarin da ke gare mu ba Mun yarda ka debi duk abin da ka ke bukata, mu dai ka zama Shugabammu."

Iliya ya yi dariya, ya yi wakar nasara, irin ta mayaka. Sa'an nan ya ce, "Yan'uwana, ba ni so in wahalar da kaina don tsaron dukiya, ko kiwon dabbobi. Ni bukatata in yi yawo cikin duniya, in yi yaki. Dukiya kuma da dabbobi, tajirai da makiyaya su tsare. Na gode muku kwarai, sai wata rana." Suka yi ban kwana, ya karya linzami ya koma da baya, ya zo wurin dutsen nan na mararraba mai rubutu.
Daga gefen inda aka rubuta, "Wanda ya bi hanyar da ta mike totar zai hadu da mutuwarsa," sai ya rubuta: "Ni Iliya-dam-mai- Karfi, na bi hanyan nan da ta mike, amma ban gamu da mutuwa ba."

Daga nan ya karya linzami y bi hanyar da ta nufi hagu inda aka rubuta za a sami mace, ya yi ta tafiya, Bayan kamar kwana biyu yana tafiya, ran nan sai gashi ya tunkari wani irin gida mai ban mamaki. Shi dai ya fi girman gida, amma bai kai gari ba. Ginin gidan duk an yi shi ne da wani irin farin karfe, sai kyalli ya ke kamar madubi. Rufin gidan kuma kansa da zinari aka yi, ga tagogi kuma na madubi, ko. wacce an sa mata labule iri daban. Akwai. furanni iri iri kewaye da gidan, akwai kuma lambu cike da kayan marmari. Iliya bai tsaya ba, sai ya tasam ma kofar gidan. Tun kafin ya kai, sai ga 'yam mata arba'in, ko wacce ta ci ado, daga kayan gwal, sai talafin farin siliki, sai alharini, sun fito tarbarsa Suka kewaye shi suna yi masa maraba, har suka iso kofar Sarauniya. Yam matan nan su suka rike masa sirdi ya sauka. Aka fada wa Sarauniya

Jim kadan sai ga Sarauniya ta fito, iliya ya dube ta da kyau yaga tun da ya ke yawo cikin duniya bai taba ganin mai cikakkar kyaun halitta kamar ta ba. Irin tufafin da ke jikinta sai wanda ya gani. 'Yam mata biyu suna biye da ita daga baya suna gyara mata tufafinta da ke jan kasa. Gashin kanta kuwa har bisa duga duganta. Da zuwanta sai ta rungume Iliya da murna ta sumbace shi. Ta kama hannunsa suka nufi cikin gida, sai ka ce wadda ta ga wani tsohon masoyinta.

Aka kai Iliya cikin wani irin daki na shafaffe da zinari, kowace kusurwa kuma an kafa mata shama. Kasa kuwa ambi duk an shimfida dardumu da kilissi iri iri, ga kujeru wadanda in ka zauna su zauna, Idan kuma ka kwanta su kwanta. Akwai tebur a tsakar dakin na farin karfe, an rufe shi da zane na farin siliki, an jera abinci, da na sha iri iri. Waje daya kuma ga wurin wanke hannu, ga sabulu da tawul a rataye. Suka zauna kan kujeru, ga teburi a gabansu. Suka shiga shaye-shaye da ciye-ciye wadanda Iliya bai taba saninsu ba.

Ilya yafara tunanin watakila wannan matar da irin abin da ta ke nufin kulla masa. Gaskiyar Iliya, ashe matar hila ta ke yi masa don ta zambace shi. 'Yam fashin nan ne suka ajiye ta, suka gina mata wannan katafaren gida, suka samo 'yam mata don su rika yi mata aike-aike, suna kuma taya ta zama. Duk fadin gidan kuwa ba namiji ko daya. An shirya shi sosai yadda duk wanda ya zo gidan nan, ko Sarki, ko tajiri, ko malami, ko waye, lale zai halaka Abin da ya bari kuma ya zama na matar, da yan fashin.

Akwa wani daki wanda aka shirya musamman duk wanda aka ajiye a dakin toh kwanansa yakare akwai kayan kawa iri iri wayanda aka kawata da zinariya ko ina an cika dakin da su. Matasan kai kuwa ko ina an jingine. Akwal kwalaban turaren wardi daga kololuwar dakin a rataye, an hudar bakinta, tana diga kadan kadan kan gadon. Kuma ga fitilu masu haske a kowace kusurwa. Gadon nan yana bisa wani katon shisshike ne na karfe wanda ke juya shi ko ina, ga zannuwan gado masu tsada an rufe shisshiken yadda ba za a ganshi ba

To, dabarar kashe mutanen duk a wurin gadon ta ke. Akwai katuwar rijiya daga karkashinsa, kamar girman daki, daga can ciki, zurfinta kuma ya fi gaba dari uku. An rufe bakinta rif da shimfidu. An shirya gadon yadda idan mutum ya kwanta, har gadon ya rabu da bangon dakin, to, sai ya kife, mutum ya fada cikin rijiyar. Sa'annan kuma gadon ya koma yadda ya ke. Duk abin nan Ilya kamar ya sani.

Da su lliya suka kare cin abinci suka shiga hira, tana ba shi labarin duniya, shi kuma yana fada mata wadansu labaru irin wadanda ya kamata ya fada mata. Sai ya rika yin gyangyadi da gangan, kamar yana jin barci. Sai ta ce da Iliya ya kamata su tafi ya kwanta don ga alama ya gaji Iliya ya ce, "To, da kuwa na so." Ta shige gaba ya bi ta har suka shiga dakin nan inda Rijiyar take. Ta ce masa, "Ga gado kwanta ka huta, ai ka wahala." Har za ta fita sai ta ce masa, "Af, yau kuwa ana sanyi-sanyi. Sai ka matsa daga can kusa da bango, akwai murhun wuta daga cikin wancan dakin da ke game da wannan, za ka ji dumin wutar, ka gasa jikinka, don ka ji dadin barci!"

Iliya ya ce, "Ai ba na so in cika barci, saboda kullum dare na kan fita waje in duba dokina." Kafin ta juya sai ya yi wuf ya fizgo ta, ya jefa bisa gadon, ya danna waje bangon, inda ta ce shi ya kwanta. Ko kafin ta yi kara gadon ya bintsire ya kifar da ita, ta fada cikin rijiyar. Shi kuwa sai ya yi tsalle waje daya, gadon ya koma inda ya ke. Da ya ga haka sai ya koma waje daya ya kwanta, ya yi ta sharar barcinsa.

Da gari ya waye Iliya ya fito ya kira 'yam matan nan da fuska murtuke, ya ce, "Ku kawo mini makullan dakin nan na kasa." Saboda tsoro da rudewa ba su tsaya wata-wata ba, sai suka kawo masa. Ya ce su nuna masa wurin da a ke budewa, suka nuna masa. Ya ga ashe wadansu irin manyan karafa ne kamar azeru da su aka yi kyauren. Ya fusata ya watser da makullan, ya sa kafa ya balle kyauren ya shiga. Ya tarar da mutane jingim suna zaune a cikin rijiyar babu ko shimfida. Wadansu suna kuka, wadansu suna ta salati. Wadanda suka dade a wurin suka saba, suna ta wake-wake.
Kuma kusa da su ga gawar wadanda suka mutu, wadansu sun bishe wadansu kuna danyu suna ta wari. Iliya ya daka musu tsawa, yace kowa ya san inda ya yi nan da nan sai wurin ya rude suka tashi a gigice da rawar jki, wannan ya ture wannan wannan ya ture watan sunga ta fita. Ko wanne ya fta waje ya ga hasken rana, ko waiwayawa ba shi yi, balle ya tsaya ya dubi inda zai nufa Sai ya bazama kawai, ya nafi inda ya sa gaba. Sai ka ga Sarki ya tattara buje ya soke, ya sheka gudu bai san ko wajen da ya ke nufa ba. Jarumai rannan babu ko ta da hannu, belle a tuna da kayan fada.

Daga nan sai lliya ya samo wadansu kosassun dawaki guda uku, basu kome a turke sai harbin iska, ya kamo matar nan, ya sa sarka ya daure hannayenta, ya daurawa doki guda. Ya kuma daure ko wacce kafa da sarka, ya daura ga doki guda, kana ya buge su suka watse gaba daya ko wane ya nufi waje daban Shi kuwa sai ya kau da kansa don kada yaga irin mutuwar da za tayi.

Sa'an nan ya shiga gidan ya kwashe duk dukiyar da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment