Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke ciki, da duk abubuwan da ke da amfani, ya raba, ya ke wa kowane mutum da ake yi wa makirci ya fada ramin nan. Amma shi ko allura bai dauka ba. Ya kuma watsa duk 'yam matan dake cikin gidan, ya sa wa gidan wuta ya kone. Ya kama dokinsa ya hau ya koma wurm dutsen nan na mararraba ya sake rubuta: "Ni Iliya-dam-mai-Karfi, na bi hanyar da ta nufi hagu amma ban sami mace ba." Daga nan ya tsaya lokaci. mai tsawo, sa'an nan ya ce, "Duk na bi hanyoyin nan biyu, amma ban sam! abubuwan nan da aka ce ana samu ba, bari kuma in nufi wadde ta nufi wajen dama, ko kila na sami abin da aka ce." ya kama hanyar da ta nufi wajen dama ya yi ta tafiya har ya iske wani kurmi. Bayan shi kuma ya ketare wani kwari mai zurfi. Da ya wuce wannan kwarin, sai ya iske wadansu ramuka manya manya kamar rijiya wajen guda dari, duk ciccike da zinari da azurfa da jauhari da lu'ulu'u, sai daukar ido su ke yi, tal, tal, tal! Daga gefe guda sai ya ga an rubuta: "Wannan dukiya duk ta iliya ce." Shi ke nan sai ya sauka ya bi ramun nan da dai dai ya ga irin tarin dukiyar da ke cikin ko wanne, ya yi mamaki matuka, ya kuma rasa yadda zai yi da ita. Ya ga ko mutum dubu suka kwana dubu suna aiki a wurin, ba za su iya debe rabin dukiyar ba. Ya tsaya ya yi tunanin abin da zai yi, sa'an nan ya hau dokinsa ya koma Birnin Kib, ya fada wa Waldima. Ya ce kuma yana son mutane dubu wadanda za su yi aikin tonon wannan dukiya. Nan da nan aka shirya masa su, suka tafi wurin suka kama tona dukiya. Suka yi ta aiki ba dare ba rana har kamar wata uku, amma ko rabin rabi ba su debe ba. Iliya ya sake komawa wurin Waldima ya samo wadansu mutum dubu, suka hadu suka shiga aiki. Da suka kwana kamar hamsin gaba daya suna aikin ba su kare ba, sai suka kwashe iyakar abin da suka hako, suka kai Birnin Kib. Iliya ya danka duk dukiyar ga Waldima, ya ce ga ta nan a diba a yi masallaci, sauran kuma a raba wa gajiyayyu, shi ba shi bukatar ko da allura daga ciki.

DINAR SARKI WALDIMA TA UKUILYA ƊAN MAI KARFI-08

WALDIMA ya sake shirya wata dina wadda ta fi duk wadda ya taba yi a baya saboda murnar dawowar Iliya, da kuma irin taimakon da ya bayar ga gajiyayyu da mutanen gari Sarki ya aikawa manyan mutanen kasar da tajirai da sarakuna duk suka taru. Ya yi shagali, har ya rika raba kyautar kaya da kansa. Don murna, a rannan duk ya'yan sarakunan da suka halarci wannan taro sai da Waldima ya ba ko wannensu sarautar wani gari, ko wani kauye. Tajirai kuma ya ba su manyan riguna, jarumai kuwa ya ba su dawaki da sulkuna da kayan fada. Da ya zo kan lliya, saboda ya san ba wani abin da zai ba shi ya biya shi, sai ya kawo wata riga mai kama da alkyabba ta fatar zaki, wadda aka yi wa ado da fatar damisa ya ba shi. Wannan ita ce shaidar shi ne babba daga dukan jarumai.

Iliya ya sunkuyar da kai ya amsa, ya yi godiya da murna. Bayan an jima, sai Iliya ya tashi tsam, ya tafi wajen masu dafa abinci, yana rike da kyautar da Sarki ya yi masa. Ya cira ta sama ya ce, "Yadda na dauki wannan alkyabba da Waldima ya ba ni don girmamawa, haka zan dauki babban makiyin nan nasa in kashe shi in kama dukan ahalinsa. In Allah ya so, sai ya zama karkashin mulkin Waldima."

To, cikin madafan abincin nan akwai wata mace makira, nan da nan sai ta ruga wurin Waldima ta ce masa, "Ga jarumin nan can a madafi yana cewa sai ya kashe ka, ya kashe dukan zuriyarka." A lokacin kuwa giya ta riga ta ratsa shi, sai tangadi ya ke yi. Ya ce wa jaruman da ke wurin su tafi su kamo Iliya, su tafi da shi kurkuku. Irin kurkukunsu kuwa rami a kan haka mai zurfi kamar rijiya, fadinsa kamar daki, ciki a ke saka mutum a rufe, kamar kabari.

Iliya ya dubi jaruman nan ya yi murmushi kamar wanda ya ga 'ya'yansa. Suka durkusa duk gaba daya suka ce suna rokonsa arziki ya taimake su ya fid da su daga hushin Sarki, kada ya kashe su. Suka roke shi ya yarda su tafi da kansa har wurin da Sarki ya yi umurni, amma daga can su bar shi ya yi tafiyarsa. Su kuma sai su koma su ce wa Waldima sun aikata abin da ya umarce su. Iliya ya yi dariya ya ce, "Haba yara, ai na fi gaban haka. Amma saboda rokona da kuka yi, zan yi kamar yadda ku ke so." Ya shige gaba suka bi har wurin da Sarki ya ce. Amma da suka ce ilya ya yi tafiyarsa, sai ya ce shi ba zai tafi ko ina ba, sai dai su haka rami su rufe shi, kamar yadda, aka umurce su. Suka yi, suka yi, ya ce lalle sai dai su haka rami ya shiga su rufe. Da suka ga ba yadda za su yi, sai suka haka rami, ya shiga suka mai da itatuwa da kasa suka rufe bakin rif. Suka tafi wurin Sarki suka fada masa sun gama aikinsa. Waldima ya yi ta gode musu, har ya kawo kyauta mai yawa ya ba su.

Bayan da aka watse, sai matar Waldima ta tafi ta fada wa wadansu amintattun bayinta, wadanda ba su saba mata balle su tona asirinta. Ta nuna musu wani wuri ta ce su yi ta hakar wurin daidai yadda mutum zai shiga har su kai daidai inda ramin da Iliya yake su. Suka shiga hakar rami, suka kare. Ta shiga wurin Iliya tana kuka, ta gaishe shi. Iliya ya rarrashe ta ya ce ta bar kuka wannan duk babu kome. Ya bayyana mata da bai yarda ba, in duk duniya za ta taru, ba mai iya kawo shi nan. Har ya ce, "Na zo wannan wuri saboda dalili biyu. Na farko, saboda mutanen nan da aka sawo sun roke ni, na ji tausayinsu, kada hushin Sarki ya shafe su, ya kashe su. Na biyu kuwa, na yi tunani tun ran da Allah ya hada ni da Waldima ban taba tunawa ko a raina in cuce shi ba. Na kuma dubi irin alherin da ya shiga tsakanimmu, amma ya ce a yi mini haka. Su ne abubuwan da suka sa har na hakura na zo wannan wuri Sarauniya ta ce, "Ba kome. Kullum zan kawo maka abinci da abin sha da kaina. Akwai ranar da Waldima zai neme ka. Zai yi kuka da hawaye don rashinka, ba kuwa da dadewa ba." Suka yi ban kwana ta tafi gida. Daga ran nan a kullum da dare sai ta kawo masa abinci da abin sha irin wanda ko Waldima ba ya cin irinsu Ta kuma kai masa shimfidu da gado, da dukan abubuwan sha'awa.

To, Sarki Waldima yana da wani abokin gaba, Sarkin wani gari ne wanda ya fi shi mayaka. Kwanan bayan kamar wata uku da rufe Iliya, sai Sarkin nan ya aiko wa Waldima da manzo cewa ga shi nan tafe. Ya shirya ko da karfin hatsi ko da yawan mayaka, kai, ko sama da kasa za su hadu, sai ya kama Waldima da hannunsa. Zai kuwa washe gidansa, ya kame ahalinsa duka, ya kone garin. Da dai sauran maganganu iri iri bakake.

Waldima ya shiga gida, ya kira Sarauniya ya fada mata duk abin da a ke ciki. Ba ta nuna masa kamar Iliya na da rai ba, ta ce, "To, yaya ke nan? Ka ga da Iliya na nan da da sauki." Waldima ya kara rudewa, ya rasa inda zai sa kansa, abinci ma ya gagare shi ci. Da dare ya yi ya shiga dakinsa ya yi lamo, ya kasa barci. Can tsakar dare ya tashi ya zauna, ya yi ta rusa kuka. Da Sarauniya ta ji, ta shiga wajensa, ta ce, "Ba kuka za ka yi ba, kamata ya yi ka aika wurin da aka rufe Iliya, watakila har yanzu bai mutu ba. Ka sa a rarraso shi, kila ya hakura ya taimake ka."

Sarki ya dube ta da fushi ya ce, "Ke, tashi ki ba ni wuri! In ba sakarcinku na mata ba, kin taba ganin an rufe mutum cikin rami, wata uku ba ci, ba sha, ba iska, sa'an nan ki ce a same shi da rai ?" Ta ce wa Waldima, "Ka sani fa Iliya ba kamar sauran mutane ya ke ba. Kai dai aika a gani." Da kyar dai ta ciwo kansa, ya tashida kansa, tare da ita suka tall, aka tone ramin, sai ga Iliya kwance lafiyarsa kalau, ya yi kiba, ya huta. Ga kuma abinci ri iri a ajiye. Waldima ya cika da mamaki. Ya durusa ya nemi gafara wurin Iliya. Ya fada masa duk irin abin da ya gudana. Saboda alherin Sarauniyan nan sai lliya ya gafarci Waldima, suka dunguma sai gidan Sarki. Gari kuma ya rude da murna, Iliya ya komo. Sarki ya tara mutane fiye da yadda ya tabayi, aka shirya gagarumar dina. Aka yi shagali. Da aka kusa karewa, Sarki ya tashi ya yi wa Iliya godiya gaban mutane, ya kuma bayyana musu yadda abin ya faru har ya sa aka rufe Iliya. Mutane kowa ya mike ya gaida Iliya Shi kuma zuwa can ya tashi ya yi godiya, sa annan ya dauki alkawari zai yi yaki sosai ya taimaki Waldima da mutanensa. Sa'an nan kowa ya tafi gida cike da murna. Can da tsakar dare, sai Iliya ya ji ana gugar dakinsa, da ya fita ya duba, sai ya ga ashe dokinsa ne Kwalele. Iliya ya duka gabansa yana shafa shi yana kuka don murna, shi kuma dokin yana kuka. Ya kama shi ya daure.

YAKIN ILIYA NA KARSHE
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment