Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sunanki da sunana ba Allah umma ba haka bane to indai ba haka bane yadda banji kunyar hada sunanki da sunanaba kidaure kixauna yadda nasanya miki to umma.

Umma na'am xaki fara tambayarne ko umma dan Allah ki fuskanceni ki daure kibayyana min ni wace koda naji sauki araina na wasu abubuwan da akemin nafara dena yarda da anakirana da sunan mamata ne dan wai kun rabane ke kindaukeni abba ya dauki mubarara ne ke khadija ni kike fadawa haka kina nufin mudin makarya tane xamu maki karya ko haba umma bankaiba bakuma xan taba kaiwaba daxan kiraku da makaryata wannan shine kuskure mafi girma daxanyi ki yafe min ta fada tana kuka tausayin diyar tata ya cika ta shikenan khadija na yafe kamarta


Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Wata sabuwa yan matar baban mahrax ce tace babsnsa ya kamata sumai aure dan xewarta saliha ta mallakeshi dakanta ta fiddo da matar wata yar yarta ce sekawai kiransa akai wai anmai aure kuma so suke yaxauna da ita a garinsu wato sakkoto.


Auren yana shekara guda aka bata yar da saliha ta kuma haifa akai sa'a kuma ita bata haihuwa aikuwa tadau san duniya ta dorama muklisa dan haka yarinyar ta taso asangarce kiyayyar duniya sun sakamata ta khadija dan haka tabi ta rainata.


Wani irin xaxxabi saliha take hartake xaton baxata tashiba hakan yasanya yau tasa khadija gaba tabata labarin samuwar tare da rokarta ko bayan ranta baxata shiga ko tai abin lalaci dan xamtowa ansameta bata halak ba kadija tai kuka ta godema Allah domin ita tanama da uwa tasan danginta koda basa santa ga abbanta da yaxame mata garkuwa wani yananan burinsa ace yanada uwar yasanta koda ita tafi kowa duniyar lalaci anman baisantaba data haifeshi jefarshi tai bai san kowa nasava ita kuwa fa tasan kannenta ta rayu gaban ummanta tai mata tarbiyya ta sata makaranta tana santa tayi duk yadda xatai dan ganin tarayu itako mai xatace ma ummanta banda godiya banda tai mata addu'ar aljanna....tasani duniya bata da kamarta.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u


Kadija na SS1 ta hadu da wani saurayi inda suka kullah soyayayya khadija nasan Abdallah sosai sun shakuwa mai yawa har sunajin rabuwa da juna bamai yiwuwa bace tana ss2 Abdallah ta turo da iyayensa kan tanayin candy xasuyi aure duk wanda yasan khadija yasan abdallah dan makarantarsuma wataran tare suke xuwa ko ina take yana nan.

Ranar asabar ranar dabaxata taba mantawa da itaba ta dawo daga islamiyya ta tun daga farkon lokon ta gango kofar gidansu cike da jama'a da sauri ta karaso abinda idonta da kunnenta suka gani yasata fashewa da kuka yan uwan abdallah ke sirfama ummanta xagi ta uwa ta uba ita kuma tana basu hakuri wai anaso danfari dan uwansu ahadashi da mara asali a hankula ta karasa ta ja hsnnun ummanta umma ki daina basu hakuri daman Allah yai Abdallah ba mijina bane da mijinane ko mai xasuyi sai na aureshi ki kyalesu Allah yana tare damu nasani addu'ar uwa bata faduwa kasa banxa kicigaba damun addu'a takalli daya daga xukinsu kusa aranku ko gawata baxata auri abdallah ba yadda in aka mutu ba'a dawowa haka nabarshi taja ummanta suka shige sukuma suka cigaba da xage xagensu.

Tun daga sannan duk wanda yaxo bama tavashi fuska tasa ma ranta karatu xatai sai Muhammad wanda nacinsa yafi karfin tunanin mai tunani dakyar ta amince suka kulla sosayya aikuwa dai shima rabuwar tsiya akai duda abinda iyayensa sukai baisa yabarta ba dan shi yace ko su yarda ko kar su yarda sai ya aureta ummanta ganin halin data ke ciki cikin dangin mahrax bataso yarta ta zama cikin irin wannan halin yasanya ta kira muhd da kanta tai masa nasiyya dakyar ya hakura karshema sai barin kasar yai.



Duda yadda khadija taci burin dena soyayya segata dumu dumu cikin kogin san nasir wanda takejin invashi baxa iya rayuwaba tanasansa fiye da kowanne saurayi datai yasota lokacin da kowa yakita danginsa sun nuna mata kauna basu taba nuna cewar dan taxama Shegiya mara uba itadin abar kyama bace face maraba da akullum suke da shigowarta family dirakota.

Haka Nake Sanki
Na F.A.Ya'u
Cigaban labarin
A hankula khadija ta bude idonta yayin da ta dorasu kan bilkisu sai ummanta da ke gefe cikin yan dakiku ta tuno da abinda ya faru xumbur ta mike daga kwance yayinda ummanta da bilki sukai kanta umma Nasir tana ina karku fadamin ba mafarki nake ba yi hakuri kixauna umma dan Allah karki fadan dagaske nasir ya mutu be mutuba khadija yana nan da ransa yana samun sauki wata ajiyar xuciya ta saki ta koma ta xauna.

Safiyya ce tashigo suka gaisa da umma ya mai jikin jiki dasauki daxuma ta farka to Allah ya kara sauki daman aunty Aisha ce tace na rakotai mata gaisuwa tamata yajiki uhum har yanxu batasan da rasuwar ba jira nake takuma farkawa sai mu fada mata to gashi sauri take kar aita xuwa mata gai suwa bata nan to shikenan suka koma.

Yau kwanan khadija uku a asibiti tawarware bata da magana sai abarta tage ta dubo nasir umman nasir din tace kar afada mata batun rasuwar sai ta war ware.

Khadija na'am umma ta dago ta kalleta jiyo sosai mgn nakesan muyi ta hankali kinji ko to umma kinyarda da mutuwa ko eh umma inaso kiyadda da kowacce irin kaddara daxata sameki mai kyau ko maras kyau nantai tamata nasiha kafin ta fada mata rasuwar nasir khadija tai kuka bakadanba harta godema Allah.

Washegari da kanta tashirya umma xanje inma maman nasir gaisuwa to maisunan manya saikin dawo tafita tunda fargiyar gidan data hadu da jafar yayan nasir suka gaisa tai masa gaisuwa ya nunata ga sauran dangi maxa mai makon taxama ita take musu gaisuwa sunema suketa mata gaisuwa ba'abinda take sai share hawaye dan ko anan tasam tai rashin dangin miji masu santa kaxalika cikin gida daga masu ya jiki sai masu ya hakuri.

Sati ukunnan da rasuwar nasir inkaga khadija sai ka rantse tayi jinyane nashekaru yadda ta rame ta jeme kullum taxauna bata da tunani sai tunanin nasir dinta.

Tayadda mutuwa gaskiyace in an mutu ba'a dawowa saidai ta kasa yadda nasir dinta baxai dawoba.

Kinsan Allah bilki banasan xuwa islamiyar nan wallahi sabida me kawai na hakura da ita ne itace sanadiyar haduwata da nasir ko uniform din nagani wallahi tunawa nake dashi haba kadija ki yadda da kadda ra kece fa mai fadama mana ur present situation is not ur final destination dan Allah kitaso mutafi ko shi nasir din natabbatar miki wallahi baxaiji da ace sanadiyarsa kinbar neman illiminkiba shikansa xai xamto mai alfahari dake ta dauko mata hijabin dan Allah saka mutafi kin riga kin cuceni kince Allah muje umma mun tafi to Allah ya bada sa'a harga ranta taji dadin yadda tashirya xuwa islamiyya.

Tun daga nesa tahango wata dalleliyar mota a kofar gidansu towa baki mukai ta fada aranta lah yah jafar kune eh nida mamane tana ciki daman gobe xan koma shine nace bara naxo muyi sallama naji mama xataxo nan to aiko ka kyauta nagode suka dan taba fira ta shiga gida mama ta karbeta da farin ciki suka gaisa ta tashi tashiga tabarta ita da umma kafin taji umman ta kwala mata kira taxo taxauna kusa da ita daman gurinki naxo batun admission dinki ya fito shine naxo karbar photo dinki se hawaye haba khadija kixama mai dauriya mana nasani anmiki mutuwa anman karki mantafa nima nasir danane kidaure mu hada kai mu cika masa burinsa yanaso kiyi karatu tun yana da rai yai konai kan makarantar nan taki abinda xakiyi ki anganar dashi shine kimai addu'a kiyi karatunki yadda xaki samu damar anfanar da duniya xai xamo mai alfari gareki to umma bari na dauko hoton.
Yanxu kinga xaki fara xuwa sch of nursing din kafin lokacin jamb kiyi komai xai tafine yadda ya tsara naji safiyya nacewa yanasone kixama pharmacist ko tai shuru insha Allahu xaki xama kinji ko khadija inasan kimin alfarma ki cire damuwa aranki ki daure kiyi karatu ki cire soyayya kinji ko khadija to mama yawwa yarinyata ta mike ni bara na wuce umma dai bata da aiki sai xuba godiya har jikin mota khadija ta rakota.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u
Khadija ta warware tana sabgoginta sai dai wani abu dake damun ummanta shine yadda tafito da wata sabuwar halayya inta dawo daga makaranta sedai ta fita ta shigo da ita dan kuwa xamanta take kan tudun da suka saba xama in nasir yaxo gunta haka kawai ma saita faki idon umma tai waje ada ta xata gidan su Aisha take xuwa daga bisani ra fiskanci xama kawai take tai ta tunani dan wani xubin taddata take tana hawaye wani xubin tana murmushi abin duk yabi ya damu umma tsoronta kar abin yataba kwakwalwae diyar tata.

Khadija anfara makaranta hakan takara dauke mata kewar nasir ta dage sosai tana karatunta intai kamar baxatai ba sai ta tuna da alkawarinta da nasir ta tuna karamcin family dinsu tai karatunta.


Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u


Kharatu kam yai nisa sati daya ya rage khadija su fara introductory examination karatu take ba da wasa va dan yadda taga kowa ya dage burin kowa yaci hakan yasa itama din tadage ba wasa baccima yaxama ragagge gareta.


Kwanci tashi yauce ranar daxasu fara exam hankalunsu duk atashe yake yadda ake tsoratasu game da exam din ga wani irin sanyi da'ake xubawa kowa kagani da'irin addu'ar da yake furtawa bakinsa.

Khadija nadaya daga cikin wanda suka riga kowa gamawa da alama paper din tai mata dadi yadda take ta sakin annuri afuskarta kai tsaye tuka tuka ta wuce tai alwala sannan tai masallaci aiko kafin ta fito har yacika da dalibai wanda suka gama sai faman tsinema malan suke itadai takallesu tai dariya.ta mike Rahma xo mu wuce ko sai kin huta ke ina wani hutu paper din gobema yar kantace hakane fa gara muje itama dai Allah yasa tafi wannan amin khadija yawwa tun dazu nakesan nace miki mubi ta Aminu kano xansayi sako kai rahma wallahi kinfiya san yawo da wahalar da mutun ina daxune kukaje Aminu kano din keda su asiya dabasai kisayoba ke matsalata dake bakya ganewa wadannan kwadayayyun inna sayo aicinyewa xasuyi subarni da wallahi tallahi to shikenan daga nan nasai rake.

Aisaiki shiga ki sayo au baxaki shigaba wallahi baxan shigaba kafin ki fito ai na rage wani abu uhum uwar wayo sauran kuma ki tsaya surutunnaki da wannan dan rainin hankalin owwo nagano ki bukuli kike min dan kar aban kyautako shiyasa baxaki shiga ba ko eh naji komai xaki ce sedai kice baxan shigaba aiko sai nafada masa Allah xakisa nai tafiyata yi hakuri naga alama xancen kike so nabaki minti biyar inbakixoba kyatafi ke kadai tai dariya ta shige.

Kinsan ya mukai da mutumin mtss wallahi Rahma ke matsalace halinku daya da bilkisu kullum haka kike cewa xanso naga bilkinnan taki saka ranki a inuwa xaki ganta af kinga nasha'afa har kwatancen gidanku naimasafa kutt....mai kikace ainasan kinji haba rahma bansan iskanci danme xakimin haka ta bushe da dariya ashe kin iya xagi tai tsaki kinga inaganin mutuncinki meyasa xakimun haka ohooo na fiskanci bakida tausayine shiyasa haka kikace ko fuuuu tai gaba Rahma na binta tana kwala mata kira bata ko jiyo ba dadan karfi tafada dan Allah khadija kitsaya kiji taja tatsaya aibansan gaka kike da xuciyaba wallahi da wasa nake banma ganshiba sai alokacin ta saki murmushi haba harnaji dadi itama tai dariya ayimun hakuri da vata miki rai danai naji na hakura but kussure mafi girma daxakiyi shine ki yi abinda kikace yau kinyi Allah nadena kulaki tai dariya ai vama xanyi ba wai daman hqka kike da fada tai dariya kama take kinsan kowa ya iya iskanci tsoron Allah yake sawa kar ayi Allah ko eh mana dabadan hakaba wani ustax din inyace xai bude babin nasa rashin mutuncin ai sai dan iska ya rike baki dan mamaki.


Komai yai farko xai karshe domin yaushe ranar karshe yauce zasuyi instrumentation paper din karshi jikinsu dik amace yake yan hostal sai hada kaya suke wanda xa'axo dauka anata xuwa diban kaya.

Kai gaskiya yaune mukai intro wannan paper din da wuya take kedai bari rahma ni bama wuyarba karar da ake daka mana tafi komai raxanani uhum ai basa kyautawa aikodai anmanfa muma munada lefi in ance move sau daya bama matsawa ai daman ke haka kike bakya yarda da lefin malaminki anman ko kiyarda ko karki yarda wallahi basu da mutunci malaman sch dinnan nidan Allah bar xancennan muje muyi sallah sukai alwala sai masallace.

Masallacin cike tayake da dalibai masu kwalliya nayi masu hotuna nayi rahma taso mutafi haba khadija kibari muyi sallama da mutane mana bakya ganin daga yau shikenan hakane wani se alahira xamu sake haduwa yawwa ko kefa kinga bari naje muyi sallama da Abba nasan balallai mu kara haduwaba ta fice tabar rahma suna hotuna.

Dan Allah kixo muyi pic ko dayane Allah baxanba toshikenan yanxu sai yaushe sai sanda Allah yaso to shikenan Allah yasadamu da alkairi ya shiga motar da suka lodama kaya yana dago mata hannu Abba kenan xanyi kewarku ta fada ahankula.


Gindin bishiyae mai rake taja taxauna dan yau yatashi tana bin sauran dalibai daketa warkajaminsu da murnar kammala intro da ido batasan sanda hawaye yafara biyo idontaba dan tunawa da nasir dinta yaugashi kamar bai rayu cikin rayuwarta ba gakuma yan ajinsu sunyi xaman mutunci sun rabu suma wadannan din gashi sun rabu ba lallai su kara haduwaba jiyai andafata dasauri ta goge hawayenta haba kadija dan Allah kixo ko hoto dayane ai dake dasu maman baby muje tace dan batasan doguwar magana dan Allah rahma mu tafi magariba ta kawo kai sukai sallama da sauran sukai hanyar fita dan Allah tayani na tsinki magaryar nan Allah baxan tsayaba kinsan xaki tsinka kika tsaya hotuna tai dariya dama wasa nake kimayi da gastasaba


Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u

Yawwa khadija jiya kina islamiyya mama taxo tace yau kije tanasan xakuje kuyi register din jamb to umma bara nagama wanke wanken kuma karki dade kinsan gobe xamu tafi khatsina ko khatsina umma eh ko harkin manta eh umma kiyi sauri karmuyi dare toh umma tafada badan ranta yasoba dan batasan xuwa dangin abbanta.


Yanxu nake cewa safiyya taxo taje ta tawo dake ko umman ta mance bata mantaba aikine yamun yawa toshikenan bari safiyyar tashigo sai kuje nannan ne ba nisa to mama yakuwa batun intron taku bata fitoba har yanxu to Allah yasa muji alkairi amin mama anmanfa duda haka kidage kici jamb dinnan degree yafi diploma kinji ko insha Allahu to wanne course kikeso eh to dadai nafisan pharmacy anman ance va'ayi a kano nasan kuma umma baxata yadda da xuwa xaria ba tokiyi murna anfara ai bara suka fara kinga saikisaka shi inkin samu sai kibar nursing din ko dai kinfi san nursing din a'a wallahi to shikenan Allah ya taimaka tace amin.sai mundawo to sai kun dawo yawwa mama ni xan wuce daga can umma najirana xamuje khatsina a'a kibiyo tanan xan baki gudunmawa kikaima amarya danma danma dai akurarren lokaci nasani aida muje tare tai dariya hakanma mun aiyayi Allah yasaka da alkairi amin kije karsu rufe sutafi sallah.

Tunda suka isa garin gabanta ke baduwa dan tasan xuwa garinnan baya tava xame mata alkairi indai sukaje da bakin ciki take dawowa aikuwa kamar tasani yawdinma da abinda aka fara tararta kenan gaisuwa take anman in dutse ya amsa gwaggwo ta amsa.


Yawwa gashi inji mamar safiyya tace abaima amarya gwaggwo takarva tana yatsina fuska amvulance wanda yan dubu dubu sabbi na dubu hamsinne eyye wace mamar safiyyar umma tai saurin cewa itace wadda da xata auri danta ohoo to angode khadija dake gebe arakube gwaggo wai ina amarenne ta kalleta a kaikaice bansaniba karma kiyi xaton kudinnan xaisanya nafasa halina kimaji da wai yadda basan ganinki nakeba bakuma san xuwanki nakeba karki sake kishiga cikinsu kije kishafa musu tsiya haba gwaggo kanwarta fa akema biki ace baxata shiga sha'anin bikinba eh aishiyasa nace kartaje gunsu balle ta kashe mata aure yaran yanxu da xalinci tunda ita bata samuba haba gwaggo taya xa'ai tai haka kinga saliha inkinga bakyasan abinda ake mata ki maidata gida kema din dabadan karaba kasantuwarki uwar amarya walkahi dabasai kinxoba ah nima abune mai sauki sai intafi ai to kitafi sai mai.
Lah yaya yaushe kukaxo tundaxu inata xuba ido inganka muma jiya mukaxo kinga amaryae kuwa a'a aiko tunjiya take mita bakixoba tai dariya gashi ainaxo kixo na rakaki inda ake mata kitson kema se'a miki a'a ni bakowa kekaman kaiba todai kixo muje kugaisa kaga yanxu mukaxo nagani sosai kavari intaxo ma gaisa.To ai shikenan xokaban labarin makarantarku yai dariya bana xamu shiga ss1 ta budo ido kai dan Allah wallahi gaskiya na tayaka murna jai muhd maye haka sukajiyo muryar muklisa menai banace maka ko khadija taxo karka kulataba ankukata din ba yayarmu bace haka kace eh haka nace to wallahi saina fadama gwaggwo kifadadin kaida mabruka bakuda aiki se wani fadin yaya kadija bacin ance ba yar mu vace kyaji dashi banxa marar hankali ni kake xagi ko anxaga ta biyoshi ya mike aguje yanadari wallahi bakida hankali kina mace kina gudu xan kamakane ta juyo ta gallama khadija harara tai dariya inda sabo tasaba.

Haka Nake Sanki
Na F.A.Ya'u


Lah yaya yaushe kukazo tun dazu aimun dan jima shine bakixo gunaba yi hakuri kanwata gajiye mukaxo to shikenan yanxu taso muje amaki fulawar biki dan baxai yuwu bikina guda ace babbar yaya babu fulawa a bikin kanwarta ba hooo mabaruka ni na isa wahalar da amarya kije ki huta yasir ya rakani haba yaya dan Allah kitaso muje naji xanje kije kici abinci kafin sannan na huta to to shikenan.

Yawwa gwaggo ga yaya mabarukar nan yawwa mara mutunci daman ke nake jira naji ance xaki dau waccan mara mutuncin kikai gun mai fuwala to ahir dinki ta turo baki wallahi sai nakaita ai yayatace yayarki fa kikace a gidan ubanwa taxama yarki kufa kukace ummanmu ta haifeta aiko ba ita ta haifetaba tunda tanasanra tana kuma xaune agunta mutunci yasa ta xama yayata ai gwara da kikace mutunci ita wannan yarinyar daga ita har uwar tata ina sukaga mutunci haba gwaggo bafa nasan abinda kikemana wallahi uwa fa uwace danme xaki dinga cin mutuncin ummanmu gabanmu eyyye ah lallai kin rika todama banda abinki gwaggo yaushe barewa xatai gudu danta yaki aitasha a nono ahto nidai nafada muku yaya khadija yayata ce umma kuma ummata ce inaso kusani ban hanaku abinda kukeba but duk wanda yai agabana yadda baiji kunyata ba baxanji tasa ba fuuu ta fice itadai gwaggo ta rike baki ah lallai kin isa.


Yau ake yini kowa kagani sha'aninsa yake amarya tayi kyau har ba'a fade koya ta juya bataga khadijava nan xatafara nemanta dan batasan abinda xai bata mata rai.

Waya cemiki nan gurin karuwai ne daxaki kwaso tsummokaran kafafunki kixo inna ta fadi dallah matsani kiban guri se anai maki fada kidinga wani sin sin dakai kamar wata tagari da'ace uwarki nada xuciya da tuni ta daina kawo mana ke danginmu yi hakuri kawai tace eh aisai ancuceka ace xa'abaka ni wallahi fatana ma kar itama ta lashema wani cikin yayanmuvkurwa kamar yadda uwarta taima mahrax ya aureta ina aibaxai yuwuba in ita ta auru shegiyar yarta kam kwalelenta da danginmu.


Yawwa yanxu kawar amarya xataxo ta bamu takaitaccen tarihin amarya sukajiyo ta lasifika gaba daya suka bada hankalinsu komawar zainab kawar mubaraka ummi kanwar baban amarya ta amsa nan tafara xubo nata habaicin da duk wanda tasan umman khadija yasan da ita take hakadai sukaita cin mutuncinsu bakin cikine ya ishi kadija da kuka tabar gun bikin gurin.

Yaya yanaga kin fito ba'a tashiba wallahi gajiyanai khanina kinga kuwa nima na gaji inkina da kudin mota xo kawai mutafi tai dariya to shikenan anman jekakafadoma amaryar mun tafi dannasan xata nememu in antashi to angama babbar yaya ya shige gurin tace to su fito ita da yasir suna tafe suna hira abib sha'awa tanasan kannenta duda kadda tasanya basu zauna tare ba dan Allah babbar yaya ki taimaka karmu koma gida muje kidan saimun kayan nakulashe tai dari kai yasir kana namiji kana kwadayi yaya kenan baxaki ganeba aishi dadi kowa yanasansa uhum lallai naka wasane ince dai kana dagewa wajen karatu ta sosa keya sosai aiba dakiki irin yaya muklisa tasanya muginta cikin ranta shiyasa wallahi nai murna lokacin daxan shiga jss da'aka kani Borden na huta da duka ita kuma ta huta da rashin jinkafa Allah baki gane bane ba'abinda nake mata yo yanxu bagashi ta wuce ba hakane kuma sedai ta daki yayanta yasir kenan sarkin shirme hava yaya kinafa maidani baya ss student ne fa af yi hakuti na manta da dan jami'a nake mgn suka saka dariya baki daybanu


Haka Nake Sanki
Na F.A.Ya'u






Yau khadija jinta take cikin annashuwa domin sun kai amarya yau xasu dawo duk ta hada musu komai da nasu umma take jira kawai taxo su tafi duk ta kosa danma batasan tace ta tawone dan tasan yanxu xa'ayo kanta.


Wayyo dadi anya kuwa kece Rahma ashe rai kanga rai yar rainin sense aikya fadi haka ke ko awaya va'ajinki uhum nidai bar wannan batun shigo shigo wayyo nai missing dinki da yawa tai dariya bari na fara gaida umma danni dan ita naxo badan keba dan datakene kisha xamanki to invanda abinki dan wa kikasan umman suka gaisa da umma dayake tasanta asuna bayani kawai tai mata ta ganeta Allah kinmin baxata bantaba xatonki ba kedai bari gajiya nan da xaman gida nace bari na gwada xuwa koxan gane kwatancennaki aikodai kin kyauta sosai wallahi naji dadi suka sha firarsu irin ta jawaye..
Umma xan rakata anman xan biya da ita ta gidansu bilkisu xasu gaisa ta sai kindawo rahma agaida umma ta ta hado kayan da ta hata mata gashi kibata to umma angode suka fice.


Yau gani ga rahma inji biki ai inashan lavarin rahma ta fada tamace halinmu dayane tai dariya nina haka tacemun duda banyarda ba suka saka dariya baki daya.

Ke ban fada mikiba Rahma ta fada har sun tsaida mata da adai daita sahu tace yi hakuri malan ba hawa xamuyiba to aku sarkin magana wacce gulmar kuma aka samo mutuminki ma kadija ta gintse fuska zaki dara ko kinga rahma bani nasha inji bilki ke ai kamu tai gayen ya hadu kullum damuna sch se yaxo guntata taki bada fuska shine naje asibiti amakare naje anman yana ganina ban wani sha wuyaba nida nake dorin dosano bilki tace batta saitaje tana kallon ruwa kwado yai mata kafa kinga insansa kuke seku fadan inmuku hanya suka saka dariya inxaki iya ba kinga rahma kin gama dani wallahi tunda kika fadama wannan sarkin damun ai na banu


Haka Nake Sanki
Na F.A.Ya'u





Cikin ikon Allah exam dinsu khadija tafito inda tai sa'a tana daya daga cikin wanda suka ci farin xiki gunta ba'a kama hannun yaro duda tawani fannin bataji dadi ba kasantuwar vabu rahnanta cikin wadanda suka samu nasara har kwalla tai yadda rahma taci burin xama nurse.

Karatu ya kankama yau satinsu biyu dan har sunfara shirye shiryen tafiya asibiti kadija duk ta damu domin tana kewar rahma sosai kasantuwar duk wadanda suka ci basu wani saba ba wasuma batasan dasuba.

Tunda suka dawo take ganinsa kusan kullum saita ganshi ya shigo cikin makaranta bata taba barin sun haduba dan batasan takura.

Satinsu daya da dawo dawowa daga asibiti aka kafe yan replacement mutum biyar ciki harda Rahma aiko murna gurin khadija ba'a magana

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment