Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fice ismail ya bi bayanta dakinyi shawara dani da baki basu ba.

Nayi dana sani mara misaltuwa tun lokacin da nasamu labarin haihuwar saliha naje nadinga xuga babanta dan sanin yadda sukai da bavana babu ta yaddaxa'ai ya yadda nace kedin yatace burina be cika ba na mutuwarki sedai naji dadin korar saliha da babanta yai sedai mai abinda nake tunani xata rasa matsuguni har muje mu kwaceki kamar yadda hamxa ya tsara be yuwuba.

Batafi watanni da aureba na auri iklima auren da be karar dani komai ba sai dana sani tun da na aurota nake danasi har yau bandena ba .

Watanmu tara da aure ta fara laulayi shekara na xagayowa ta haifi danta yaci sunan babana ismail rashin ta idonta tasa mahaifina yakwace ismail ita kuma yace nasaketa haka kuwa akai duda na saketa bamu rabuba mahaifina da kansa yaban yan kanwarsa ita ta haifi fiddausi gurin haihu ta rasu dan haka yarta ta karba tashayar nakasa rabuwa da iklima kaxalika na kada aure duk yadda namaifina yai yayi nanaki aure duda besan ina tare da iklima ba.

Bansan wanda yaje yasanar masa ba be yarda ba dan haka kuwa ya xo dan tabvatarwa ya yarda aikuwa yana komawa gida akace ya fadi iklima ta hanani xuwa xuwa duda kuwa burina be huce naje na ganshi ya yafe minba.

Ita tasanya na karbo yarana muka sake aure mafarar lalacewr tar biyarsu kenan domin kuwa ita kanta bata da tarbiyar balle tabaima wasu.


Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u




Bawata sana'a nake ba da mahaifina na dogara shima jiki yaki sauki xara bata barin dami komai na kare takai ansayar da komai nasa dan masa magani babu sauki iklima tace babu yadda xa'ai nasaida gidan da muke ciki baxai yiwuba yayata ce tadauki babana wanda matsayinta na mace ba ita yadace ta daukeshi ba duda kuwa banbancin da yake mana kansu matane komai yasamu nine sai gashi sudin sune suka xama gatansa.

Kwata kwata iklima ta daina ganin girmana bama tajin maganata in nai magana tace ai ni ne matar itace mijin abokaina duk sun gujeni yarana sun rainani babu wanda na isa nace yayi yayi.

Bankara danasanin abinda nai abaya ba sai randa na kama iklima da kato adakina nai kuka nai danasani tun daga wannan ranar cuta taki barina nai magana taci mutuncina tabar gidan.

Ahankula duk wani abin anfani na gidannan su fiddausi sun debe sun saida gidanma sai sun gadama nake ganinsu balle insaka ran xasu kula dani dan yayata muhd ne kawai yake xuwa yakula dani duda iyayensa basu sani ba nasan duk sanda suka sani ranar xan dena ganinsa yaron yanasaona katsam iyayensa suka daukeshi suka kaishi waje karatu naci wuya sosai dan banda mai kuladai baufi wata biyu dawowa ba da akwanaki ne baxaki iya shigowaba domin xuwansa yagyaggyara ni.
Yanxuma dan dare yayi ne daxaki ganshi yaxo bankara firgita da hakkin wani ba sai yadda naga hamxa ya koma wanda har gara ni sau dubu daganin irin mutuwar dayai ta wulakacin alokacin na tabvatar lallai hakkin wani ba abin wasa bane ko ya yafe ma balle bai yafeba.

Baba tare nake da mijina shine bakice yashigo ba tai dan murmushi ai yace xe shigo inyaxo daukata to shikena ta mike dakyar tace ina kitchen yake yanuno mata baxai shigaba yadda yake tsami har wani wari wari yake alamar andade ba'a shigesa ba anbar abubuwa sun rube ciki.

Wayarta tasa ta kira jafar inbakai nisa ba dan Allah kaxo ai ina kofar gidan au kace xaka kadawo fasawa nai tai dariya to shigo shi ya tai maka suka sanya shi mota fa'ams special hospital suka kaishi kasantuwar su masana ga kowa basu sha wata wuyaba aka bashi gado satinsa biyu yawar ware har yana tafiya yana iya cin abinci.

Khadija ce taxaunar da fiddausi da ismail tai tamusu nasiha da kwatanta musu abu buwa na rayuwa hartasamu suka dan fiskance ta tadauki fiddausi takaima maman jafar dan tasan ummanta baxa karbeta ba tamata bayanin komai taji dadi ta jin jina kadijar shi kuma ismail shi yake jinyar abban nasu intaxo shi kuma ya rafi gida dan yin wanktaba.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u


Yau khadija ce agurin abban nata burinta yamata bayanin inda yanxu kakansa da sauran danginsa suke dan tanasan ta shiryasu tanasan kakan nata ya yafema abvan nata anman yaki saurararta inta takura masa da maganar saima kuka ko ya rufe idonsa kamar me bacci yanxunma hakance ta kasance ya rufe idon kamar mai bacci baisan taci gaba da maganar da take ms.

Ismail ne yashigo sai wani dake biye dashi bata kula da kowane ba dan kanta asa yake sai ji tai ance khadija ko ba ita vace kamar tasan muryar tai saurin dagowa Abba daman kana duniya yaushe ka dawo ta hada masa tambayar lokaci guda yai dariya kafin ya xauna me yakawoki nan bacin nasan ance ba nursing kikai ba bata bashi amsaba kafin tace kai mai yakawoka opppp duk kun kasa bama juna amsa bara duk na baku inji ismail yana dariya yah kadija kenan yah abba kenan yah kadija yayarmuce taxo jinyar abbanmu kamar yadda yake abbanta kaji amsarka bece komaiba yace yah abba dan gidan auty sadiya ne yayar abbanmu uwa daya uba daya babarsa da abba suke.
Seda khadija tama abba bayani sosai yafiskanta haba ashe mudin jini daya ne shiyasa nake jinki araina narasa mai yasa tai dariya nima haka kasan mai xakamun sekin fada so nake kasharen hanya naje na nemawa abba gafara sai alokacin ya bude ido muhd yaushe kaxo najejje gida bakanan sai yau na tadda ismail yace kn asibiti yai murmushi muhd dan Allah karka kaita kaji ko bansan abbana yakara kullata to Abba baxan kai taba.

Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u


Duk inda khadija xatai da taimakon Allah da tai makon Abba suka samu suka saita abbanta da iyayensa kullum yaxauna shikadai bashi da aiki sai sharar kwalla dan yaga ishara kala kala wai yau ace diyar dayai cikinta dan daukan fansa dan wulakanta uwatta yaso kashe itace ta dauki nauyin komai nasa ta dawo masa darin cikinsa dayake xaton yarasashi rashi na har abada burinsa aduniya yaje ya roki saliha gafara koda baxa yafe masaba.


Tsananin ciwon datakeji yasata kasa daurewa duk kuwa da yadda taso daurewa dole ta tashi jafar agigice ya dauketa saiva sibiti tunda aka shiga da ita labour room yake kai kawo bashi ya xauna ba saida Rahma ta fito dauke da baby oga seka ban tukuci kafin ka karbi baby baisan ko nawa ya bata ba ta mika masa Allah ya raya mana shi tasamu namiji yaron na kirjinsa yana faman kiran waya kafin kace mene dangi sun cika asibitin dakyar ya iya basu yaron danma tsoffi sunfara masa tsiya.

Khadija kam taga gata taji dadi dangi ta ko ina xuwa ake ta bangaren ummanta abbanta babanta yan uwan jafar kawaye da abokan arxiki kowa burinsa yaxo yaga dan dja.

Yau ummam khadija tafi kowa farin ciki wai yau itace dauke da dan khadija ahannunta danta data haifa ta hanyar aure abinda aka sha mata gori akai itakam ko yau ta mutu ta godema Allah ya cika mata burinta aranar aka sallamesu agidanta xasuyi sunan kasantuwar da dama basu san gidanba daga baya se taje wanka gidan mama.

Jafar ne rike da babyn wai wane suna kikeso asamaine duk wanda kaxaba masa kaida tun yana ciki kake nuna iko dashi yai dariya am serious na baki xabi tukuicinkine shike indai nice kasa masa muhd nasir kamar kin shiga raina wallahi sunan naketa Addu'a Allaj yasa kixa ba tai dariya.

Ranar suna yaro yaci sunansa Nasir suke kiransa da sagiree yadda khadija taga yan uwa ta ko ina yafi komai mata dadi dan burinta ya cika ta ko ina sai daya datake san ummanta ta yafema abvanta.


Dakansa yaje har gidan yai sa'a mahrax yana gida ya ganeshi yai mai iso har ciki aiko tana ganininsa ta hau fada me yakawoshi gidanta kuka wiwi yadinga mata yana magiya har saida yabata tausayi abinka da xuciyar mata mai sanyi tuni ta yafe masa.


Khadija tafi kowa farin cikin samin lbrin ummanta tace ta yafema abbanta.

Ita da kanta ta gyara masa gidansa tanaimo masa mata ta bude masa shago anan wanbai ta bashi halak malak.

Yaukam da alhini suka tashi domin kakanta ne Allah yai masa rasuwa na gurin uba tai kuka ba na wasa ba domin yan kwanakinnan sun saba sosai mutunne mai iya xama da jama'a ta ko ina.

Wani abu da yakara baima abban khadija tsoro da saka masa tsoron ubangiji shine yadda bayan wata daya da rasuwar mahaifinsa yana xaune a shago wata almajira taxo bara bema ganeta ba saiji yai tace muktar yadan kalleta vanfa ganeki ba iklima ce matarka babu tayadda xa'ai kace itadince iklima yar kwalliya mai kyau daji da gayu itace ta koma haka babu hannu daya duk tai baki wasu kuraje duk sun fito mata a fuska yabata sadaka yanaji tana magana baice da ita kalaba tabar gurin.
Yaukam hargida taxo tana kuka ta naimi gafararsa dasaka bakin ismail ta ya yafe mata tace ina fiddausi ismail ya kirata taji dadin yadda diyarta ta kintsu gida mai matsakaicin girma aka kama mata suka kaita asibi.
Ashe bayan barinta gidan gurin saurayin nata ta koma suka ci gaba da iskancinsu ashe yanada kanjamau sunje asibiti bata da lpy anan suka gano itama ta kamu aiko tun ahanya suke xabga bala'i kan ya cuceta bai kulaba sukai karo da wata tifa nan take baiko shuraba itama saida tai jinya mai yawa aka yanke hannunta da yarube lokacin data fito daga asibiti babu inda xata dole ta kama bara.


Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u


Abu kamar wasa sai gashi yaxama gaske dan tun ran sunan sagiree Abba da muklisa suka fara soyayya duda cewar ta koma sakkoto dake tana xuwa hutu har gidan khadija take xuwa yanxu andena mata rashin kunya dan ta girma tagano ramine kawai kishir mamarta take jefata dan rabakanta da yan uwanta.

Magana kam tai nisa dan gar manya sun shiga ciki watanni ya rage asha bikin nuklisa da Abba ismail da bintoo me aikin umman khadija da tuni taxama ya dan umman tai mata komi fiddausi da muktar cousin din su jafar.

Khadija kam tayi uwa yadda ta xage da aljihunta da karfinta abikinnan ita tai kayan dakinsu komai akace ana bukata bakyashi ko wani tunani xata bada kowa kagani ita yabonta kawai yake.

Duda kasan tuwarta da tsohon ciki bai hanata xagewa wajen fidda kannen nata kunya va tako ina sudai iyayenta da yan uwanta sai san barka.



Haka nake sanki
Na F.A.Ya'u


Khadija taxama matarsa abarso ga kowa kowa kagani kai har wanda basu wani hada alakaba burinsa a budi baki ace KHADIJA SALIHA YAKASAi yar uwarsa ce.

Kowa cikin dangi yaro da babva inya kwaso matsalarsa kai tsaye gurinta yake xuwa dan sanin vabu kyashi ko wulakanci xatai masa.

Yanxu khadija an na daya daga cikin manyan pharmacist din da ake ji dasu a nageria dan lokacin da jafar yaje waje danyin wani course ya tafi dasu ita da yaranta acan tai PhD dinta kasantuwar tun bayan haihuwar shukra ta kammala masters dinta a zariya kaxalika pharmacy dinta ba wai arewa kawaiba kusan yawanci garuwa ta bude branch dinda yayin da kasama ke alfari da ita bawai iyalinta bama.

Itakam khadija saidai ta godema Allah akalla akarjashinta batasan iyakar wadanda kecin abinci ba kama daga masu PhD,masters,degree bama amaganar masu diploma ko NCE fannin health burinta ace yau tabada gudunmawa a drug discovery tasani balallai ta iyaba hakan yasanya ta dage wajen taimakawa na kasa masu tasowa wanda ko bayan ranta xataso ace yau ga dan nageria shine yagano wani maganin da duk duniya tayadda dashi take kuma amfanarsa burinta ace ta bangarenta wannan wanda ko waccen xasu gano din.

Wata shawara na kawo mana inajinka maixai hana kixama dealer ta magani kiyi register ki bude kamfani kana ganin xan iya xaki iya matsalar ma'aikata babu matsala kinsani kema bata dauki abin da mahin mancin ba ta basar da batun.

Yau suna xaune yakuma xuwa da batun har ya gama komai sunan kanfanin kawai yakeso tasa tai shiru can tace SALIHA pharmaceutical therapy ngl. bai musuba ya sanya basufi wata uku da batunba kanfani ya fara aiki ma'aikata kam harsaida sukai yawa.

Masallatai da fanfuna data gina basa misaltuwa banda makarantun islamiyya waau ta sadaukar ga nasir wasu ummanta wasu kanta wasu family dinsu kai har makarantun gwammnati intaga na bukatar gyara haka take xuwa tayi gabaki daya tanayi ne batare da nuna ita din take ba.


Zaune take tana baima Nawas mama shukra na game yayin da sagiree ke muraja'ar haddarsa mami na na kallo ummi tashigo da gudu ga abba ga abba mts shukra tai tsaki mu dallah malama kimana shiru sekace abban unguwa yaje ina bacci ma yake to bagani nai bai tashi da wuriba momy tunamin nan inji sagiree takarva tana biya masa maman yara ana hirar ne tai dari dadyn yara sarkin bacci har ka tashi natashi xan tafi gurin kanwariki tai dariya to agaishe ace wai ita yaushe xata yadda a aurota ne inganta yai waje yana dariya kayi mantuwa baka dauki gift dinba kingani ko duk na sha'afa santa ya rufen ido yafi minti biyar a tsaye abakin kofa yana kallonta ta gama biyana sagiree mami ta miko mata biro momy rubutamin love wallahi seta fara rubutan agogo inji ummi kinga ummi bansan rigima ta rigaki kibari infara mata ya shigo au har kadawo yai dariya waike dan Allah yaushe xaki fara kishi tai murmushi se randa kadena wannan wasan au kinma gane wasane ko nasan mexanyi sena gano wane irin kishi ne dake hmmm tunda kace haka baxaka ganoba haka kikace eh mana tan shikenan xakisha mamaki ya xauna ya kamo hannun ummi kawo inxana miki agogon ta mika masa yayinda mamin tace bata yadda ba itama dady ne xai mata kaga yaran dady da momy ya rungumosu sagiree da shukra suka maxo muma ahada damu to ai sai a hada da momynko ya hada gaba daya ya rungume kayansa dadi ya ishi kadija yau itace cikin iyayinta gata ga mijinta ga yayanta gashi taxama abae so ga kowa basauran gori Ahankuka ta furta alhamdulillah.




Nima anan nakesan cewa Alhamdulillah ina mai godema Allah da yakawoni karshen wannan littafi fatana a'anfana da abinda aka karanta na rubutane bawai dan cin mutinci ko cin xarafin kowaba sai dan nishadantarwa fadakarwa da ilmantarwa bakuma ya nufin koyi ga rayuwar wani ko waba na kirkira ne kawai.

Wani abu danake san fuskanta game da labarin duk yadda ka tsinci kanka akwai mafita inkai hakuri dayardar Allah xaka ga sauyi da farin cikin da baka xata ba.

Zamantowa maihakuri da yafiya da maida komai bakomai bane wani babban matakine na rayu cikin farin ciki da cigaba duk girman lefin da mutun yama xaka iya yafe masa domin kai bakasan mexaka ma wani a gaba ba.

Duk yanayin da ka tsinci kanka wani yafika walau na farin ciki ko akasinsa kasanto mai godema Allah akoyaushe.

Zamantowar mutun mara uba bashi yake nufin shidin ba mutumin kirki bane bashi ke nufi baxa'a hada auratayya dashi ba.

Karka taba xama mai korafi dan iyayenka sun haifeka suna talakawa sunma gata sun haifeka da aure.

Karka taba korafin iyayenka sun cuceka sun haifeka ba aure kagodema Allah dayaika musulmi hakan baya nufin karshen farin cikinka arayuw dayawa ana kuskure wai dan anhaifeka ba aure sai kace baxaka xama na gariba ai anriga an bata ma rayuwa hakan ba dai dai bane ko kaga uwa ta rike dan inya girma yace bashi da abin ki sai ita bacun ita kanta ba'asan ranta ta haifeka ahakaba takuma jure bata yadda kaiba harka girma kasanta wani yanacan bemasan kowa nasa ba burinsa kuma yaga koda uwattasa ce koda itadin kuturwa ce mahaukaci makauniya duk xai dauka indai xa'ace yau ga mahaifiyarsa.

Duk wani kuskure dake ciki ina fatan amin afuwa dan adam ajixine

GODIYA.
Godiya gami da jinjina gaduk wani ko wata da suka karanta wannan littafi nagode Allah yabar xumunci.
Taku dabance.
Usaina muhd ibrahim
Aisha muhd ibrahim
Zainab shehu umar
Nafisa shu'aib
Fatima Hasan Abbakar

Semun sake haduwa awani littafin mai suna yar'amana.
09028287218



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment