Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"ganinan fitowa yanzu!." Daga haka yakatse wayar yasata cikin aljihun suit din na ciki yafito daga bedroom din bayan yayi scanning thumb dinsa kofar tabude. Gidan cike yake da securities da soldiers girman gidan zaikai hacter daya manyan plat gudu uku ne wanda yafi sauran biyun girma yanufa securities nata gaidashi. Palo yashiga da sallama wanda girmansa zaikai 100/100 ga manyan Sofa's dakomai na more rayuwa ba'abinda babu ciki. Tana hangosa tatafo da gudu ta rungume sa tana dariya , dagowa tayi ta kallesa sosea tace " kayi kyau yayana, amma matsala daya rashin mata. " sanza fuska yayi zuwa na tausayi yace "baby basune basaso naba matan ...duk sunki aure na." Dukan wasa takai mishi a kirji tace "gaskiya Yaya ban yarda ba, kai ne baka sonsu..amma nasan abin yi.." Takareshi tana kama hanunshi sukayi dining. "To mekike shirin yi.?" Ya tambayeta yana zama. Tsayawa tayi da saving dinshi datake tadaura hnnta saman kirjinta tace "kawata zan hadaka da i'ta tunda kakiyin aure, dama tacemin tana sonka!." ? Wara manyan idonsa yayi yace "kam batada kunya nitakeso?, mezanyi da karamar yarinya yar 18 Allah yakiyaye." Yamaida hankalinsa kan tea din da yake had'awa. "To nidai kayi aure ko infadawa abba cewa wata tace tana sonka kai kuma kace bakaso .." Hararan wasa yay mata yace "kifada!, ai nagirma ..bamemin n dole!."

Kuyi hakuri yau naje unguwa ne shisa kukaji shiru.

Beenaf/beelurv👄
[28/08, 15:02] Habiba Novel Yobe: *💖SAHRA💖*
*Hot Love💋*



11....


Zama tayi kujeran dake gefen nashi tafara feeding dinsa bayan tayi saving nashi. "Wow!..testy.." Yafada yayinda takai mashi spoon daya. "Baby amma ke kikayi breakfast dnn ko?." Yakara fada yana karban second spoon. Dariya baby tayi tace yaa Aliyu ..bani nayiba mami ce tayi sai takoma ta kwanta don tace bcc bai isheta ba." Cikin minti shabiyar yakare breakfast din yatashi yana goge bakinsa da tissue yace "lil sis zanshiga ingaida mami.." Yakare yanayin hanyar bedroom dinta, kamo hnnushi tayi tace "yaa aliyu! Mami tace bcc zatayi inka gama shirinka kawai katafi. Naga a'lama kanaso kamakara ne yau." To shknn zokirakani..yafada yana makaleta one site dinsa suka fice. Wasu manyan motoci kirar Bentley guda hudu aka shirya mashi na tafiya, kai tsayi gurin motar suka nufa ga securities din dazasu tafi tare nn tsatstsaye har an bode mishi wanda zai shiga. Juyo da i'ta gabanshi yayi yay mata kiss a goshinta yace "baby zantafi, mekikeso insayo maki." Murmushi tayi tace "bakomai yayana, amma yau i'nafatan kasamo mana mata yanda kayi kyau dnn kamar ango.." Tai maganar cikin zolaya . jan dogon hancinta yayi yace "kai baby adduan ki bazata ciba, ni bayanzu zanyi aure ba, saina girma!." Yakare maganar yana langwabar da kai kamar karamin yaro. Dariya baby tasa tace "u a now in 33/34 years kacemin saika girma yaya?, koninan 18 nagirma aure zance abba yamin.." Taboye fuskanta a kirjinsa." Dagota yayi yana dariya yaja hancita yace "baby bakida kunya ko?." Girgiza kanta tayi still tana dariya "anyway.. Kikoma ciki zamu wuce." "To yayana ka gaida min da abbey.." Saida yaga shigewar kafin yajuyo wurin motocin walwalan fuskanshi yadauke yadawo ai nahin Aliyun shi snn yashiga back sit yay crossing aka mika mishi news yafara karantawa. Tada motocin sukayi sukafice daga gidan bayan megadi soja yabude masu get sukadau hanyar meduguri. **waye Aliyu?. ALIYU MADU INDABO shine cikekken sunanshi, mahaifin shi Alhj Madu Indabo babban soja ne wanda ayanzu yayi ritaya , mahaifiyar shi Haj Maryam. Aliyu shine dansu na fari wanda yataso cikin gata ba'abinda yanema a rayuwar sa yarasa , saida yayi shekaru 17 kafin aka haifa mashi kanwa Aisha ana kiranta da baby. A US yayi karatunshi 1 degree 2,and3 babban doctor ne haka shine shugaban NGO na African gaba daya. Yakasance yana balain kaunar baby bayason duk wani abinda zai bata mata rea dalilinta nema yasa yabaro US yadawo nig..Sam! Mata basu damesa ba, basa gabanshi ko kallo basu ishe saba. Shekaru uku da suka wuce Alhj Madu ya auri wata mata maisuna Haj Nafisa dalilin makale mashi datayi , tashigo da 'yar budurwa gidan mai suna samha wanda batada burin daya wuce Aliyu ya aureta amma sam bataga fuskaba duk da haka bata zubda maka mantaba tananan tama kanta alkawari harsai burinta yacika. Aliyu miskiline nakin karawa baya taba fara'a i'nkaga dariyarsa to lalle yana tareda baby don ko i'yayensu basu ciki ganin fara'an saba. Mutum ne maison addini don kullum karfe uku yake tashi ya gabartar da nafila harsai yaje masjid yagabatar da sallan asuba snn yazo yayi karatun alqur'an sai gari yayi haske yake komawa bacci, haka duk ranar jumma'a a meduguri yakeyin salla a babban masallacin yayan babanshi duk sallan juma'a a canyakeyi. Wnn kenan. Karfe daya motocinsu sukayi paking a babban haraban gidan Al Sheik, gidan da girmansa yakai unguwa guda ga katon masallacin jumma'a a jikinsa. Al sheik dakansa yazo yakarbi dan nasa ya rungume shi don yana matukar son Aliyu ko cikin 'ya'yansa bawanda yakeyiwa son dayake mishi. Babban falon al sheik suka shiga wanda yaji kayan more rayuwa suka zauna . abinci kala2 aka jerawa Aliyu a dining ..alsheik dakansa yay saving dinshi yasashi gaba yanashi suna taba hira, karfe 1:30 dai2 suka fita masallaci don gabatar da sallan jumma'a. Sauri2 abban sahra yake shiri don yakusa makara sallan jumma'a , dakin sahra yashiga ya hangeta can kuriyar gado tatakuru tahada kai da gwiwa tana kuka. Hankali a tashe yakarasa yadagota ya rungume ta jikinshi yana rarrashin ta. "Meyake damunki habibty..kifada min what's happen to u?." Kamar wanda yazugata takara fashewa da kuka tace "abba wai gobene aure? Taya hakan zata kasance?." Shiru yayi baice komai ba sai rarrashin ta dayakeyi " abba ka taimaka min.. kayi wani abu kai wllh mutuwa zanyi inna auri safwan bana sonsa!." Cigaba yayi da shafa bayanta yace "kikwanta da hankalinki ..insha Allah bazaki aure shiba!." Shiru tayi sai ajiyan hat datake saukewa haka yafita yatafi masallaci .

Yauma zanfita innasamu time zakujini dadare lv u ol.

View wattpad @habiebahlurv

Beenaf/beelurv👄
[29/08, 00:24] Habiba Novel Yobe: *💖SAHRA💖*
*Hot Love💋*



12.....

😍😍

Karfe biyu mutane suka fara shirin fitowa daga masallaci bayan an i'da sallan anyi addua da tunatarwa, tashi abban sahra yayi dakansa yanufi gurin alsheik . guri suka samu a gefe cikin natsuwa abban sahra yashiga kora mishi bayani akan damuwarsa harda dan guntun hawayen sa yak'ara da cewa "ka taimaka kadaura mata aure koma dawaye ne bayan komai ya lafa sai a raba aure, ni wancan yaron ne banaso ta aura ." ajiyan zuciya alsheik ya sauke ya dafa kafadun abba yace" ka kwantar da hankalin ka, insha Allah matsalanka yakau..bari ina zuwa." Yafice bayan yabada umarnin kar kowa yafita sujira shi. Bayan kamar minti talatin yashigo dawasu samari bayanshi hannyensu rike da manyan kwalaye dakuma takardu. Lokaci daya gurin yayi shiru bayan jawabi da alsheik yafara gabatarwa cikin mintu na goma aka daura auren Aliyou Madu Indabo da Sahra Yousuf Aliyou . Razana Aliyu yayi jin sunan da'aka ambata amma alsheik yay masa alamu daya kwanta da hankalinsa. rabon minti da goro akayi daga haka kowa ya watse akabar alsheik.. abban sahra da Aliyu dakuma sadiq autan alsheik mai shekaru 17. Zufane yake ketowa Aliyu ta ko'ina jin bayanin da alsheik yake mishi , bakaramin taba mishi rayuwarsa wnn aure yayi ba , shida baida burin yin aure yauzu ..to wama aka aura masa !?..wace irice!?,,,shin tanada duk qualities din da yake nema gun macan dazai aura ko bata dashi!?. Dafa shoulder dinsa da alsheik yayi ne ya dawo dashi hayyacin sa "Aliyu ka kwantar da hankalinka, kadauki wnn abu amatsayin kaddara.. Kadubi wnn halin da bawan Allah nn yake ciki ka taimaka in bayan abubuwa sun lafa za'a i'ya raba auren ka auri wanda kake so. Kuma zan kira abban ka nai mashi bayani dakaina ." Aliyu bai i'ya cewa komai ba sai wani abu mai daci daya tadiye yafara kokarin mikewa. Rikeshi alsheik yayi yamaidashi ya zauna yace "ka dawo da nutsuwarka mana Aliyu !, kadawo hayyacinka." Dago idonsa dasukayi jajaye saboda tsabar zafin zuciya yayi ya kallesu duka yace "i'na cikin hayyacina!, kawaidai abin yazomin wani kalane,, bantaba tunanin haka zata faru dani a rayuwa ta ba!." Gaba daya sai hausayinsa yakamasu . shafa kansa alsheik yayi yace" nasani Aliyu amma kayi hakuri ..yanzu ga mahaifin yarinyar zaku tafi dashi a yan zunnan i:nzaku koma abuja tareda matarka zaka tafi! Kuje Allah yayi maka albarka!." Daga haka alsheik yatashi yafice daga masjid din yashiga gidansa. Jikin Aliyu har rawa yake yagama kidime wa gaba daya baimasan abinda yakeba . d'agashi sadiq yayi suka fita abban sahra ma yabi bayansu batare da bata lokaci ba securities dinsa suka bude mota sadiq yasashi snn yay mishi sallama suka tada mota suka tafi bayan abban sahra ya zauna gefen driver don yin kwancen gidansa. Suna isowa gidan yafita yashiga da sauri harda bigewa da get , Aliyu baiko daga kanshi ya kalli gidan ba hasalima tunda yashiga motar kansa ke kasa maya bukatar ganin komai a yanzu. Abba yana shiga falon ya sauke ajiyan zuciya ganin momy bata ciki, bedroom dinta yashiga yaji tana wanka dasauri yakoma dakin sahra tana kwance kan gado idonta lumshe. Zama yayi bakin gadon yakira sunanta a hankali tashi tayi ta zauna tace "abba!." Murmushin yak'e yayi yace "tashi kidauki hijabinki kibiyoni." Daga haka yayi gaba jiki a sanyaye tadauki hijab dinta tafito inda taga abba nn falo yakama hannunta suka fita. Tunda taga manyan motocin dake kofar gidan kirjinta yafara bugawa da sauri2 tanajin wani tsoro na shigarta . "SAHRA! Abba Yakira sunanta kai tsaye, kallon shi tayi hawaye na taruwa idonta duk tarasa ma meyake faruwa. " kishiga motarnan kutafi!, daga baya i'nkin samu waya kikirani zan maki baya ni..yanzu ba lokaci!." Kamar sokuwa haka tatsaya tana kallonsa i'ta duk batama san meyake cewa ba. "Kiwuce kije umartarki nakeyi!." Jiki a matukar sanyaye kamar wanda kwai yafashewa a ciki haka take takawa, wani guard ne yafito yabude mata kofa a hankali ta karasa zata shiga Aliyu yadaka wani uban tsawa yace "karki yadda ki shigomin mota..ka rufemin mota nace kasata wata.." Yadakawa guard din tsawa still kanshi a kasa bai kalli kowaba. jikin guard din har rawa yakeyi yarufe motan yabudewa sahra wani tashiga suka tada motar suka tafi. Sosea idon abba yaciko da hawaye baibar gurinba har saida yadena kallon motocin. Hade kai da gwiwa sahra tayi cikin motar tana kuka batare da kowa yajiba. "Meyake faruwa da'ine? , i'na zamuje haka? suwaye wadannan ?.., a i'na abba yasansu?." Kukanta taci gaba dayi tana tausaya wa rayuwarta yanda kaddaranta yazo a haka.

habiebah lurv &anfa novels , jameesha sadnaf novel mom of 12 hat u ol💖

View wattpad @habiebahlurv

Beenaf/beelurv👄


*💖SAHRA💖*
*Hot Love💋*



13......


Wani abu mai daci Alh Madu Indabo ya hadiye Jin abinda yayan nashi yace, "to ..Allah ya sanya alkhairi." kawai yace ya ajiye wayar. Gaba daya hankalin mutanen gurin yatashi so kawai suke suji abinda yake faruwa ,,, kasa jurewa mami tayi ta zauna gefen shi tareda dafa shoulder dinsa tace "dear meyake faruwa wai? , naga gaba daya kashiga damuwa." Still shiru yayi baice komai ba don baima san ta inda zai fara musu bayani ba. Baby dake gefen shi zaune tarushe da kuka harda birgima tace "abba kafadamin abinda ke faruwa, ko wani abu yasamu yayana.." Kuka tarinka yi harda tsalle kamar wata karamar yarinya . kamota abban yayi yazaunar da i'ta kan cinyarsa yace "stop crying baby na, ba abinda yasamu yayanki yana cikin koshin lpy.." "To abba kafad'a min abinda yafaru." Tafada tana kokarin fashewa dawani kukan , saurin rungumo ta yayi yace "karkiyi kuka zan fada maki .." Kollon mami yayi da hankalinta yaba daya ya tattara yakoma kansa haka small mom da samha dasuke tsaye. "Abbey yakirani yacemin ya daurawa Aliyu aure! Yanzu haka yana tafowa tareda matarshi!. Wani uban tsalle baby tayi tasaki ihu tana rawa tana cewa " it's finally over alhmdllh yau yayana yayi aure yeeee..." Tafice da gudu waje tana rawa . samha dake tsaye gagara daukanta kafafunta sukayi tanemi guri ta zauna kanta yana bala'in juya mata " taya haka zata faru!?, wnn wani irin munafurci ne Aliyu zaiyi aure bayan yasan i'rin son datake masa! ...to wama ya aura!?, wace shegiyarce ta!?,,, tabbata asiri akai mishi ya aureta ...to koma waye lalle ta d'ibama kanta .. saitayi dana sanin shigowa rayuwarsu!." Mami dabata ma fahimci abinda abba yafada ba kawai sai kallon shi datakeyi. "Hajiya maryam nace maki Aliyu danki an mishi aure!." Yafada yana dan hura mata iska a ido don irin kallon datake mishi. Ajiyan zuciya ta sauke tace "kace Aliyu yayi aure ko ?." Gyada kai yayi yana tabbatar mata da maganar "to Allah yasanya alkhairi." ..tashi tayi ta wuce bedroom dinta donyin bacci ko Allah zaisa kanta yasaki don tafahimci inda maganar abba ta dosa ..don kamar almara haka take ganin abun. Shima abba tashi yayi yafita yabar small mom da samha i'tama data tashi fuuu kamar zata tashi sama tashige falonsu tareda banging kafo. Bayanta small mom tabi aranta tana cewa " ko wace wnn miskilin ya aura sai Allah. " tadaga kafada tashige. Samha bedroom dinta tashiga tarufe da key ta hautsina gashin kanta tana kaiwa da kawowa zufa nata keto mata gaba daya tagama daukar zafi. "Ni Aliyu zaiwa haka?, watoma don tsabar bura'uba da muna firci ba anan akai auren ba don karmuji ko? saidai akawo mana amarya ... " murmushin dayafi kuka ciwo tayi tace "lallai Aliyu zaka had'u da bala'i dakuma tijara irin tawa..muzuba mugani !..." Daga haka tabude fridge tasha ruwan sanyi amma dukda haka bataji sanyi a ranta ba. Baby tana nan waje ta dasa kujerarta setin get yanda zata hango duk mai shigowa , bayanda abba baiyi da 'itaba amma fir taki shiga ciki tace saitaga dawowan yayanta. Securities da soldiers din gidan sunyi matukar mamaki jin abinda baby tace "wai sir Aliyu got married" kowa da irin tunanin dayake a ransa na mamaki. Har abba yaje masallaci sallan magrib ya dawo baby na nan zaune, girgiza kai kawai yayi yay shigewarsa apartment dinsa. Karfe 8 dai2 motoci suka fara horn megadi yafara kiciniyar bude get... A guje baby ta tafi lokacin data i'sa harsun gama shigowa ko parking basu gama yiba tafara leka motocin tanaga tayadda zata hango amarya . turus tayi ganin wata mace mai katon hijab kanta sunkuye ba'a kallon fuskanta, mamakine yakamata aranta tace "badai wnn ce matar yayana ba?, nayi tunanin zanga big gal wayayya wanda tacika mace ...amma ai wnn bata fini bama..." Saurin katse tunaninta tayi ganin Aliyu yafito yana neman wucewa, dasauri tai gurinshi ta rungume shi tace "yayana barka da dawowa, nd Congratulation!." Kafin yace wani abu gaba daya ma'aikatan gidan sunyo gurinshi suna mishi "congrate!." Ko wanne fuskanshi dauke da faraa , gagara cewa wani abu yayi sai murmushin yak'e da yakeyi yana daga musu hanu. "Yayana warcanne amaryar tamu.." Tafada tana nuna sahra dake can nesa dasu kanta sunkuye kasa. Kallon gurin datake yayi yaga dogon hijab din jikinta amma baiga fuskanta ba , wani kululun bakin cikine yaji ya kamashi "wai wnn abun aka aura min!?." Tsaki yayi cikin ransa azahiri kuwa yayi murmushin yak'e yace "eh!.." Ganin yanda baby takafeshi da i'do ..daga haka yay wucewarsa batareda yabari kowa ya bishi ba. Takawa inda take baby tayi ta rungume ta tace "barka da zuwa amaryar yayana, i'na fatan zakiji dadin zama damu!." Gagara cewa komai sahra tayi sai jikinta dake rawa don kowama rsarinshi take agurin "wannnan wani irin al amari ne!." Tafada cikin ranta. Ganin haka baby tace "kikwanta da hankalinki ,,kisaki jiki damu kinga ba'abinda zamuyi muki. " tai maganar tana kama hanun ta suka shiga ciki.


Duk maison SAHRA daga farko yama wa dannan numbers magana: 08030865816 or
07035668210


View wattpad @habiebahlurv

Beenaf/beelurv👄

*💖SAHRA💖*
*Hot Love💋*


14....


Momy uwar amarya na zaune falo bata jima da dawowa daga unguwa ba ta d'aura kafa daya kan d'aya tana cin apple sai murmushi take zabgawa. Sahra ne tafad'o mata a rea tasaki murmushi tace " Allah sarki daughter na, tun safe ban lekaki ba busy yamin yawa bari i'ndubo lpyr amaryar safwan!. " tashi tayi tashiga dakin sahra. Bata ciki sai tayi tunanin tana bathroom, zama tayi bakin gadon tana ta lissafe2 cikin ranta da yadda za'ayi walima bayan daurin aure dakuma dinner din daza'aje. Harkusan minti talatin ba'alaman zata fito haka yasa momy bude bayin kaitsayi taga bakowa ciki."Ikon rabbi to i'na yarinyar nan? Naga bata zuwa ko'ina gashi kuma bata kitchen." Fita tayi daga dakin da tunanin kotana bayan falonsu inda suke dan zama time2time , zagaye gurin tayi tas bata gantaba bata ga alaman taba , ,,,nan hankakin momy yadan yafara tashi don tasan sahra bata fita saita tambaya . komawa ciki tayi tadau wayarta tai dailing no din abba . bugu biyu yadaga yaji momy nacewa "sahra tace maka zataje wani guri ne?." Murmushi yayi a ransa snn yace "kin ganni tunbayan tafiyata masallaci!?." Tsaki taja tace "dilla i'na tambayarka kana tambayana..toni banga sahra ba, yanzu naje dakinta naga bata nn gashi kana gani dare yayi i'n kasan i'nda taje kace tadawo gida..tunda kasan tanada makiya zasu i'ya saceta." D'aga kafada yayi yace "to i'dan ma sawa kikayi a sacemin 'ya kafin nadawo ki tabbatar kin naimo ta duk inda take.." Daga haka yakatse wayar . tsaki tayi ta wullata wayar tafara zagaye falon " to i'na yarinyar nan taje, kodai safwan ya dauketa..don nasan bai'nda zata je." Daga wayarta tayi takira safwan dake zaune garden shi daya iska mai dadi na kadawa yana jinshi cikin annashuwa gobe i'war haka yana tareda amaryar shi. Yana cikin wnn tunani kiran momy yashiga saurin dagawa yayi yasa a kunnanshi kafin yace komai yaji momy tace "sahra bata gurinka safwan?.. Tun dazu nadawo ban ganta ba nayi tunanin kadauke ta kunje shopping!." Tsaye yamike daga zaunen dayake yace "ban gane mekike cewa ba...kina nufin amaryar tawa ne tab'ata kome?." Cikin momy fara dura ruwa yayi jin sahra bata gurinsa "to taya haka zata faru, guduwa tayi? Saceta akayi kokuma b:uya tayi." Maganar shine tadawo da i'ta hankalin ta yace "kimin bayani yanda zan gane mana.." Yafada da karfin gaske . rawa jikinta yafara tace "wllh ban ganta ba , ba inda ban dubaba amma na rasata." Kashe wayar yayi yafita da sauri yashiga mota yatafi batareda yabari kowa yabishi ba. Ko marfin motar bai rufeba yashiga gidan a hargitse ya daki kofar falon ta bude ya shiga . momy daketa zagaye fasa ihu tayi duk a tunaninta yan fashine suka shigo musu gida saida taga safwan ne snn hankalin ta yadan kwanta amma ba dukaba don tasan shima wani bala'in ne. Irritating look yarinka watsa mata snn yace "salon rainin hankalin dakika fito dashi kenan?,, taya zakice an rasa sahra, yarinyar da za'a dauramin aure da i'ta gabe kike cewa tabata. To wllh i'dan ma wani abun kike shiryawa kiyi gaggawar dakatar dashi . nasan matsalarki kudine kuma i'na baki kuma badaina baki zanyi ba kona auri sahra ,, don haka karki soma cemin tab'ata. nabaki nan da safiya kafin muzo daurin aure ki tabbatar kin samota." Daga haka yafice abunsa. Zama yayi cikin motar yakifa kansa jikin sitiyari yana rasa abunyi "me wnn matar take shirin yine, kodai tasamo wanda yafini kudine shine zata zomin da wnn rainin wayon?, tokuwa lallai indai hakane zata tari March din da batada filin bugawa. Tada motar yayi yafigeta aguje yabar unguwar. Kan momy wani mahaukacin zafi ya dauka tarasa yanda zatayi , taya duka za'a dauki laifi a dora mata, abban sahra yace tanemo mishi 'yarsa ,,,safwan yace ta nemo mishi matar sa to da wanne zataji ? , ko i'ta ta saceta ne?." Fadawa kan kujera tayi tana fidda numfashi kamar tayi gudun tsere. Toru kafar akayi abba yashigo fuskan sa a matukar hade ba alamar walwala. Tashi tsaye momy tayi shikuma yayo gurinta yana jifanta da banzan kallo yace "ina fatan kin samomin 'yata.?" Harara ta watsa masa ta daka tsawa tace "wai ance maka 'yarka tana gurina ne?..can kaje ka naimi'yarka.." Shima tsawan yadaka mata Wanda yasata gigicewa yace "nabaki nanda wayewar gari ki samomin 'yata inba hakaba hukuma ce zata raba ni dake".Daga haka yawuce dakinsa. Fasa ihu momy tayi ta daura hanun ta bisa takanta tazube kasa tana cewa "nashiga uku ni binta yaya sukeso nayi da rayuwata?, ta i'na zanfara nai manta ..i'na kikaje sahra where are u!."

Mekukeci na baka na zubane readers!?, kukwantar da hankalinku yanzu lbrn yafara. Kuma bawai an gamashi bane yanzu ake typing dinsa .

Tnk u Hawee for everything nd u mom of 12💖.

View wattpad @habiebahlurv
Beenaf/beelurv👄

*💖SAHRA💖*
*Hot Love💋*


15......


Abuja..
Samha na mak'ale jikin window tana lekensu sai hada uban zufa take had'awa, bata ankara ba taji shigowan su baby. murmushi ta k'irk'ira tayo gurinsu cikin takunta na higher classic bebe's ta rungume sahra tana cewa "oyoyo amaryan mu..sannun ki da zuwa..." Murmushi baby tayi tace "sis samha kinka amaryar yaya so beautiful kamar wata balarabiya.." Wani kululun bakin cikine ya kamata.. lallai i'tama tagani sahra tafita kyau, amma i'ta kuma tafita aji da wayewa da daukar wanka, lallai tasan hakan zai taimaka mata gurin danne kyau sahra. Murmushi tayi a zahiri tace "hakane sis!, tanada kyua.! Tazo muje dakina mukwana don gaskiya ta burgeni sosea i'na sontaa!." Wara manyan idonta baby tayi tace "sis! Amarya da mijinta zataje ta kwana dakinki?, kinsan ya Aliyu ma bazai yarda ba.. shima yanaso yaji dumin matarsa don haka yanzu tanayin wanka zan rakata dakin mijnta!." Daga haka takama hanun sahra suka wuce falon su suka bar samha nan tsaye kirjinta na tsananin bugawa . wai yau Aliyu ne zai kwana da mace? kuma ba i'ta ba. "To meye zanyi don dakatar da hakan?, i'na bukatar dogon tunani." Juyawa tayi takoma nasu falon tashige dakinta tasa key. Kai tsaye bedroom din mami baby tashiga da i'ta , yayin da mami ke zaune kan praying mat tana ta yima Aliyu addua kan aurenan i'dan alkhairi ne, saboda yanzu ta tabbatar da auren don taga shigowan su ta window. Zaunar da sahra bakin gado tayi tabude karamin fridge din dakin tadauko mata lemo da ruwa tadawo ta zauna gefen ta. Gagara shan komai tayi sai kirjinta daketa bugawa tun sanda suka shigo mota suka tafo har yanzu bataji natsuwa kokadan a ranta ba . bayan kamar minti biyar mami tashafa adduan ta tajuya tana kallon sahra fuskanta dauke da murmushi. Kanta kasa tana wasa da 'yan yatsunta jikinta yabata ana kallonta , a hankali tad'aga idonta sukayi ido hudu da mami. tai saurin maida kanta. Murmushi mami tayi tace " masha Allah 'yata brkn ki dazuwa, i'na fatan Allah yazaunar daku lpy cikin kwanciyar hankali. " "amin" baby tace . "i'na.. yini.." Sahra tacewa mami muryanta na rawa sosea hantar cikinta na kadawa. mami tagama fatimtar halin datake ciki tace "ki kwantar da hankalinki kisaki jiki damu ..muma mutane ne kamar kowa." Gyada kai tayi

1 Comments On SAHRA HOT LOVE
avatar
mariya-4-2

1 year ago

Reply

Muna godiya sosai Allah ya karo basirs

Please Login or Register in order to submit comment