Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aisha itace tauraruwar maimartaba ko ace giwarsa,tun asali bawai sai zuwa yanzu ba,badon komai ba saboda dukka cikin matanshi babu tamkarta wajen damuwa da lamuransa gamida nuna mishi qauna kulawa da soyayya,hakanan halinta dabanne cikin matanshi,duk da tana da kafiya jajircewa kan dukka abinda tasa gaba.


Idan taso abu tana sonshi ne da dukka zuciyarta,hakanan idan taqi abu tana qinsa ne da dukka zuciyarta,kaifi daya ce ita,ba'a fiya sauketa daga ra'ayinta ko sauya mata al'amura ba.


Baya ga mijinta da iyaye 'ya'yanta sune abu nabiyu da take so sosai a rayuwarta,cikin 'ya'yan kuma sai abdul'azeez tashi qaunar tafi takowa,tun lokacin da aka taba samun galabar cutar dashi sau biyu ta fidda duk wani qasaita izza da isarta,ta sake qaro rashin yarda da tsaron lafiyar yaran nata.


Sosai aka samun nasarar kwantar dashi kwanciyar da ba'aso har abada yatashi ba,saidai zakaran da Allah yanufa da cara,aishan macace data yarda da malamai wadanda zata biya kudi ayi mata sauka duk wata ko sati da addu'o'i kan tsaronta dana yaranta,duk da itadin bata damu can da saitayi da kanta ba,wannan shi yakawo sassaucin lamarin Allah yayanke masa ya tasheshi da wuri.


Tun a sannan tadaura dambar dukkan wanda bayason ganin abdul 'azeez a matsayin yarima saita hanashi bacci
Ta dora buri sosai bisa rayuwarshi
Tana qaunarshi da bashi kulawa fiye da kowa cikin yaranta
Zaka iya taba kowa ta daga maka qafa amma banda abdul'azeez
Zata iya daukan komai sabodashi,hakanan zata iya haqura da komai saboda abdul'azeez
Tayima rayuwarshi babban tanadi
Taci buri da alwashin saiya zama wani shima tamkar yadda mahaifinsa yazama kafin zamantowarshi sarki
Duk wanda yakwana yatashi cikin gidan yasan zallar qaunar da take masa
Saidai duk da wannan yasan wacece mahaifiyarshi sarai,yasan tsarinta yasan halayyarta ta kaifi daya ce!


A yanzu burinta nafarko shine abdul'azeez yayi karatu mai zurfi bakin rai bakin fama,wanda take hasashen shine mataki nafarko da zai soma zama wani haske mai kaifi a gareshi dazai nunawa duniya shi,sunansa yayi fice,yakuma shiga loko da saqo na duniya fiye da sunan mahaifinsa.


Yana da wannan ra'ayin,yana da burin haka,sai akwai abu guda daya tak daya kawo sauyawar ra'ayinsa da nata,burinta guda daya daya zama tarnaqi a rayuwar abdul'azeez,buri guda daya daya kawo sabanin ra'ayi tsakaninsa da ita,abu guda daya dayake neman dagula rayuwa da nutsuwarsa,duk da takan gaya masa
"Abd'azeez,kada kace zakaja da dukkan abinda na shimfida maka,dukkan abinda nakeyi inayine saboda kai,saboda 'yan uwanka,saboda kare suna da matsayi na masarautarku data mahaifina,ka ajiye naka da ra'ayin da burin,na maka alqawarin cewa AKWAI LOKACI!".


Dukkan wani qoqari da juriyarshi ya tattarata waje daya don ganin sun tafi doro daya bisa tsari da ra'ayin mahaifiyarsa,saidai koda yaushe qoqarin nasa yana neman gazawa,akaran kanshi bashi da yadda zaiyi da kanshi,da da akwai da babu makawa zai kasance kamar yadda takeso dinne,saboda babu abinda yake qauna a duniya sama da mahaifiyarsa shima,yadda tabashi qauna haka yake qaunarta koma fiye da hakan,zallar soyayya irin ta d'a da uwa.


Wannan shine taqaitaccen tarihi kan masarautar kaisa,duka sauran abubuwan da basu bayyana ba zasu bayyana kansu a nan gaba,muje zuwa.......🤙�🤙�
7/11/21, 4:29 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAƊIN RAYUWATA*👑


*_wannan littafin na kudine,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina buqatar siya ki tuntubi wannan number_*


0903 234 5899
Ko
09033181070




7




A hankali tasauke labulen harabar tata wadda take iya ganin dukkan abinda ke kaikawo cikin gidan,duk data sauke labulen amma saitaci gaba da tsaiwa gabanshi duk kuwa da cewa bata iya hango abinda ke ci gaba da gudana saboda kauri da nuyin labulen,amma kuma kunnuwanta naci gaba da jiye mata bushe bushe da tashin algaita data mamaye ilahirin gidan gaba daya.


"Tuba nake ranki ya dade,Idan da sabo yaci ace kun saba da ire iren wadan nan abubuwan dake faruwa cikin gidan nan" saita sauke hannayenta daga goya kana ta waiwayo tana duban wadda ke tsaye a bayanta kanta na kallon qasa cikin nuna girmamawa
"Ko jikina bazai taba sabawa da wadan nan al'amuran ba bare zuciyata,mansura...ni kadai nasan yaya nakeji a zuciyata duk sadda yaran nan yadawo hutu gidan nan,idan yatafi kan cika da fata da burin yatafi kenan,ko duriyarsa banson a sake ji,amma.....kullum jiya iyau,komai ya faskara,aisha bansan da wadanne iri bokaye da matsafa take aiki ba" takai qarshen maganar tana dafe goshinta da hannu kana ta yarfar dashi
"Allah ya huci zuciyarki,tabbas wataran haqanmu zata cimma ruwa,tunda dukkan mai nema yana tare da samu" kai kawai ta kada,ba tare data amsa maganar tata ba tace
"An gama shirya dukka kyaututtukan da kayan ciye ciyen?"
"An gama ranki yadade" ta amsa mata tana rusunawa
"Shikenan.....kije,bayan wasu lokuta akai ace injini,ina masa barka da dawowa,sannan ina nan tafe in duba lafiyar dana" tafadi maganar tana jin dacinta har qasan zuciyarta,duk wannan abun tana yine saboda babu yadda zatayi,tana yine saboda tacimma wani buri nata wanda tasoma aiki akai,amma aysha ta dakatar da tafiyar lamarin ta hanyar turashi wata qasa uwa duniya waida sunan karatu,sai taja qwafa tana neman daya daga cikin kujerun alfarma dake mamaye da qaton falon tazauna.


_fulani saratu_


Babbar haraba ce da aka qawatata da shuke shuke masu sanyaya rai da debe kewa,kashingide take saman wani tafkeken kilishi wanda aka qawata zamanshi da tuntu masu zanen gidan sarautar kaisa da wani yadi mai taushi,wanda duk da taushinsa zanen sarautar da rubutun jiki bai hanashi fitowa ba.


Ita daya ce zaune a wajen kamar yadda ta buqata takuma shaidawa barorinta bata buqatar kowa kadaici takeso tsahon mintuna talatin,saidai duk yadda taso tasamu hutu takuma katange kunnuwa da idanunta wajen jin duk wani sauti alama ko shaida na shigowar abdul'azeez cikin gidan ta gaza cimma gaci,sarewa da algaitar dake tashi saika rantse daura da itane bawai nesa da inda take ba.


Sake gyara kashingidar da har yanzu batajin dadinta tayi gamida jan wani dogon tsaki,bayan tadire tafurta a hankali
"Wannan wacce irin masifa ce!" Idanunta da zuciyarta taf da wasu al'amura da sukayi shekara da shekaru suna sukan ranta.


A hankali take takowa farfajiyar da mahaifiyartata take,duk da idan kadubi fuskarta zaka karanci damuwa qarara a cikinta,jin takunta yasanya fulani saratu daga kai tana duban inda take jiyo takun,ganin walida ce yasanyata maida kanta tana dakon isowarta
"Barka da warhaka mama" walida tafada bayan tazauna gefan kilishin da haj saratu ke zaune akai,bata amsata ba sai data koma tazauna sosai tasauke ajiyar zuciya idanunta kan walidan
"Barka kadai....ya akayi?" Kai tadan rausayar cikin nuna alhini kana ta hadiye wani abu sannan tace
"Mama....dama yau yarima zai daw....."hannu tadaga mata cikin katseta
"Dakata,bansan wani da irin wannan sunan ba,ki kirashi da sunan da mahaifinsa ya rada masa" kaitadan jinjina,tajima da sanin cewa mahaifiyarta bataso ko qaunar taji ankira abdul'azeez da wannan sunan ko misaqala zarratin
"Afuwa....abdul'azeez"shuru yaratsa nadan sakanni,tamkar ba zatace komai ba kana ta ƙuta tace
"Gashi kuwa idanunki sun ganemiki?" Wani busasheshen murmushi da babu armashi ko farinciki a cikinsa ko misƙala zarratin tasaki sannan taɗora
"Akullum aikin mahaifiyarsa kenan,rufe dawowarshi harsai ana yagobe ko randa zai dawo,koda yaushe aisha gani take itadin me wayo ce,bayan duk wayonta babu ruwan ƙaddara da wannan,hmmmm".


Sam walida bata bi takan zancanta,don ita duka waÉ—annan salon maganar tasu bata cika fahimtarsu ba,asalima basa gabanta
"Mama....kaman yadawo a lokacin da bamu shirya masa ba,yadawo a lokacin dabai dace ba" sosai tasanya ƙwayar idanunta cikin ta walidan,tana karantar rudewa ƙarara cikin idanun nata
"Me kike tsoro?"
"Makarantata,kada mai martaba yaqi yarda da maganar tafiyata karatu"
"Akan wanne dalili?" Ta jefa mata tambayar data sanyata ƙara zama
"Mama,kinsan kome maimartaba zaiyi wanda yashafemu sai yayi shawara da abdul'azeez,akowanne lokaci yakance idan babu shi nan gaba shine ubanmu,kuma kinfi kowa sanin yadda bayason wata cikinmu tafita wata ƙasa karatu,afnan kawai ta ishemu misali.....".


Kalaman walidan tamkar wani tuni ne ko fami a zuciyar haj saratu,saboda haka ta tsaida walidan
"Saboda shi abdul'azeez din shine uban kowa?,ko zamansa muke?,ko a ƙarƙashinsa muke?,wai tsoron ma me kikewa ƙaninki?,yaron da kika baiwa kwana hamsin harda doriya....to wannan karon kuwa bazan lamunta ba,abarmin yarana suyi karatu a duk inda sukeso kuma sukaga dama,saboda shima babu uban daya takurashi,asalima shida kansa ya zabi ƙasar dayafiso sannan yatafi,don haka zuwanki makaranta babu fashi indai ina raye,banason ma nasake jin wata magana kan wannan batun" sosai walidan taji dadi,cikin farinciki tadan rungume hajia saratun
"Allah ya qara miki lafiya da nisan kwana"
"Amin" ta amsa ciki ciki saboda bacin ran dake damunta,walidan tabude baki zata sake cewa wani abu wayarta dake saman cinyarta wadda ke jone da erpiece dake cikin kunnenta tadauki kida,saita saki mahaifiyar tata tahau duba kiran,kana tamiqe zumbur tana zura takalmanta
"Ki gayawa mabaruka akawomin ruwa da lemo" kaita gyada mata tayi gaba data amsa wayar.


A hankali jeron gwanon motocin suka dinga fakawa illa qwara daya data ci gaba da kutsa kai zuwa cikin gidan masarautar,wata iriyar mulmulallaiyar mota ce mai ruwan gold,'yar qarama ce wadda dududu bata da wani girman arziqi amma sai azabar kyau da tsada dakuma daukan hankalin mutane.


Bata tsaya ba harsai data isa qofar sassan fulani aisha kana ta tsaha cak,kamar qiftawar ido wani hadimi dake zaune gaban motar yayi wuf yafito,ya tsaya bakin qofar motar yayi qyam yana jira a bashi umarnin bude murfin motar.


Tsahon minti daya kafin ataba glass din motar wanda ya fidda sautin qwas sau daya,sautin na gama direwa a kunnensa yayi maza yabude yana cewa
"Gaba salamun baya salamun magaji ga mahaifinsa,taka lafiya cikin amincin Allah da kiyayewarsa,Allah ya kare mana kai,ya zamar maka jagora kuma majingina yarima kuma sarkin gobe"


Sautin kirarinsa yaqare daidai sanda yasanyo qafafunshi dake saye cikin takalmi half cover shoe irin na maza na zallar fata qirar qasar italy mai dan banzan kyau da daukar idanu,kafin wasu sakanni gangar jikinsa tabiyo bayan qafafun nashi,wasu shegun suit ne suka bayyana ash colour masu madaukakin kyau da jan hankali,sun zauna masa a jikinsa tamkar saboda shi aka qirqiresu,fuskarsa da hannayensa dake daure da wani tsadden agogon gwal sune abu na qarshe da suka fito,hasken ranar dake kwance saman sararin subhana ya haska kwantacciya kuma lafiyayyar fatarsa wankan tarwada,wani irin choculet colour skin wanda ko cikin wankan tarwadan ma bakowanw ke dace da irin nau'inta ba,nau'in fatar dake tsada wanda tsantsar hutu dajin dadi suka hadu suka qara mata ado da qawa da wani irin launi mai daukar idanu.


ƙawatacciyar fuska wadda komai nata ke bisa tsari mai qayatarwa,cikakken gashin idanu da madaidaicin gashin gira wanda qasansa wasu irin madaidaitan idanune wanda basu cika girma ba,hakanan sunfi gaban qananu,saidai wani irin shape ne dasu dake dake cike da kwarjini da maganadisu dakan narkar da zuciyar duk wanda ya zubawa su,musamman 'yammata da yaken dilmiyasu cikin kogin soyayyarsa cikin daqiqu qalilan,kyakkyawan hancinsa mai matsaho da tudu wanda ya ta qasanshi ya qawatu da gashin daya zagaye fuskarshi zuwa habarshi,wanda yasha gyara da wani irin salon aski mai qayatarwa,yakuma fidda kyawawan labbansa,wadanda suke Da surkin ja,daga cikin jerarrun haqora farare tas sun sake qawata fuskar tashi,sai dimple qwaya daga daga kumatunsa na hannun dama.


Miƙewa yayi sosai bayan yafito daga motar yana duban sassan mahaifiyar tasa,tsaiwar tasa ita ta bayyana yanayin tsari na jikinsa,yana da tsaho da murjajjen jiki,wanda murjewarsa yasake tasiri wajen boye adadin tsahonsa,faffadan qirji da kakkauran damtse duk da ya boye cikin rigarshi amma dukkan alamun qarfi da samartakarsa sun bayyana qarara a zahiri,duk kuwa da cewa bazai wuce shekara ashirin da biyar ba
(Lol,masu karatu zasuce wai wannan kyau haka,yawanci ko baka qimanta jarumin littafinka da wannan siffar ba kuda kanku haka kuke hasasoshi,beside ma novel din dukka yakan tafine bisa tafarki biyu,ilimantarwa da kuma nishadi).


A hankali yasoma takawa kai tsaye zuwa sassan fulani aisha,wanda a duba daya kacal da zaka masa ka tantance yadda jinin sarauta daga tsatso biyu na uwa da uba ke zagaya jininsa,yazauna masa kuma ya zame masa jiki,duk inda zaya gifta sai barori da hadiman dake sashen da wadanda wata sabga tashigo dasu dama 'yan ganin ƙwaƙwaf sun zube suna miƙa gaisuwa,kamar yadda yake a tsarinsa yakan ɗaga musu hannu ne kawai yawuce,a haka yadinga kutsa kai har zuwa cikin ainihin ginin dazai sadashi da falo nafarko na mahaifyar tashi.


Kyakkyawar macace hakimce saman ɗaya daga cikin kujerun alfarma royal dake kewaye da falon,ta zarta munzalin ƙuruciya hakanan batakai shekarun da za'a kirata da dattijuwa ba,duk da cewa ta tasamma shekara hamsin babu uku amma baka isa kace tana da waɗannan shekarun ba,mulki da tsananin hutu gamida jin daɗi sun wawashe kaso mai yawa na dukka hasashen da zaka iya yi mata na shekaru yaboye,saika tsammaci tana cikin shekararta ta talatin ko talatin da ɗaya zuwa da biyu ne.


Wankan tarwada ce itama amma saboda hutu yasa fatarta ke nemam juyewa zuwa fara irin farin nan mara haske sosai,duba daya zaka mata kaga izza mulki dakuma qasaita shimfide saman fuskarta.


Sanye take da wani lace na alfarma wanda aka yiwa dinki na manyan mata,wuyanta kunne hannuwa da yatsunta dukka kowanne akwai abun ado,fuskarta wadace take da fara'a,tun sanda kunnwanta suka jiyo mata sautin algaita na isowar shalelen nata fara'a taƙi barin fuskar tata,farincikinta ya gaza ɓuya.


"Salamu alaikum....Allah ya taimakeki,yabaki yawan rai,ina iya ƙarasowa?" Dayake cikin farinciki take ayau din dakanta ta amsa mata
"Bismillah lubabatu" cikin nutsuwa da girmamawa ta ƙaraso falon,wanda ba kowa ne yataba ƙetarashi ba,face ire irensu makusanta,kuma amintattun fulanin,fuskarta fadade da fara'a tazube a gabanta
"Allah ya qara miki lafiya tauraruwar mai martaba,hasken masarautar kaisa,uwa a wajen yariman kaisa....sarkin gobe da ikon Allah,Allah yayi,yarima ya qaraso lafiya,yana gab da shigowa nan,yana neman izini" murmushi yasube ma fulani aisha har saman lebanta,wanda ba kasafai suka fiya ganin hakan ba
"Albishir dinki lubabatu yayimin dadi,ko yaushe saqonki mai dadi ne,kije a bude miki store,kidauki dukkan abinda kikaga kinaso,ladan wannan albishir din naki...yarima kuma basai an masa iso ba,yana iya shigowa duk lokacin dayake da buqatar hakan,kice ina masa maraba" sosai tasake duqawa cikin madaukakin farinciki,tana ayyana iya abinda yau zata diba a store din
"Kinfi gaban haka Allah ya taimakeki,gado kikai ai ba taka haye bace,saqonki yanzun nan zai isa ga kunnen magajin mai martaba,godiya nake...godiya nake...." Hannu ta daga mata,don zuwa yanzu ta qagu kawai taga yaron nata,don haka umma luba tamiqe ta hanzari tafice.


"Assalamu alaikum warahmatullah" ya ambata cikin Muryarshi mai taushi,mai kuma cike da samartaka irin ta matashin da ilimi da mulki suke aiki a jikinsa,miqewa tayi tana murmushi idanunta bisa kanshi,tana jin qaunar yaron nata har cikin ranta
"Wa'alaikumussalam warahmatullah,maraba da yarima" murmushi yasake shima wanda yafidda ainihin kyansa,murmushi na daya daga cikin abubuwan dake masa kyau a dabi'unsa,saudai kash,shidin ba ma'abocin fara'a bane bare murmushin kansa,duk inda kaga murmushinsa to tabbas wajene mai muhimmanci,ko kuma wani muhimmin abune yafaru
"Allah ya qara miki lafiya da nisan kwana Ammi" yafada sanda yake isowa gabanta ya duqa saman gwiwoyinsa tamkar qaramin yaro,hannunta tasanya saman lallausar sumarshi tana cewa
"Alhmdlh,na godewa Allah daya sake kawomin kai gida hutu cikin qoshin lafiya,Allah yaci gaba da albarkatar rayuwarka"
"Amin ummina" ya amsa mata cike dajin dadi sannan tabashi umarnin tashi,yasamu daya daga cikin kujerun yayiwa kansa mazauni bayan tazauna.


Gaisawa suka sakeyi,tana karance dashi,yadda suka saba dai,saidai ta lura akwai dan sauyin yanayi tattare dashi,maganar da suka tabayi watannin baya tadawo mata akai,sai take fatan ba lamarin bane har yanzu cikin ranshi ya kasa barinsa ba kamar yadda ta umarceshi,saidai koma meye zata tabbatar data sake cire masa batun cikin ransa har zuwa lokacin data tanada.


"Kaje ka huta,bani kadai ba har 'yan uwanka na marmarin ganinka,muna da isashshen lokacin zama mu gana,har wata nawa?...." Ta tambayeshi tana dubanshi fuskarta na fidda murmushi,yana tsaye hannunshi guda cikin aljihunsa,saiyadan rusunar da idanunsa zuwa duban wani sashen kana ya amsa mata cikin sanyi
"Ba wata ba ba satittika ba ammi,i forever came back" yanayin fuskarta saiya soma sauyawa daga murmushi zuwa hade rai,wani kallo take masa wanda dama ya tsammaci sama da haka daga gareta
"Me kake cewa azeez?,kadawo kamar yaya?,bayan aqalla akwai shekara daya da wasu watanni a gabanka kafin kagama,kuma kafi kowa sani koda ka gama din bawai zaka dawomin bane yanzu,zaka dora da masters dinka har zuwa inda nake ganin lokaci yayi da zaka dawo kaci gaba da rayuwa cikinmu,karka soma,kada ka yarda kayi abinda zai bata tsarina koya batamin rai,kafin kowa sanina,kafi kuma kowa sanin tsarikana akanka,saboda haka karka soma yin duk wani abu da kasan zai wargatsa tsarina" dukkanin idanunshi yazuba mata da wani irin duba dayake nuna zallar buqatar a tausaya masa a fuskanceshi da nashi buqatun,saita dauke kanta daga dubanshi,saboda ita kanta tasan da idanunshi kadai yana iya karya lagonta,saboda wata baiwa ta musamman da Allah yayi masa cikin idanun,murya a narke hakanan a sanyaye yace
"Please ammi...listen tome"
"Kawuce ka huta,koma meye daga baya ka sanar dani,amma kasani,bazan yadda da dukkan abinda zaici karo da tsarina ba" daga haka ta baiwa kubra daya daga cikin amintattunta umarnin shigowa
"Allah yabaki nasara....aikene daga sassan fulanin masanawa...."
"A hada da nata da nasu duka ayi yadda aka saba" ta katseta ba tare data bari ta qarashe bayanin nata ba.


Shuru ya ratsa falon har kubran tafice,sannan shima yasoma takawa a hankali yabi sawayenta yana furta
"Na barki lafiya",da ido tabishi harya gama ficewar,tasauke ajiyar zuciya tana lalubar kujera tazauna bayan tadauki wayarta dake daura da ita tasoma neman wani layi,tana jin tausayinsa yana ratsata,amma tilas takauda kai saboda anata ganin tsarinta shine tsari,kuma ko meye tanayi ne don ci gabansa da alfanunsa.


A hankali yatura qofar qawataccen falon nasa cikin wata iriyar kasala ta zuci da gangar jiki,falone na qarshe wanda daga shi sai dakin baccinsa,yalwatacce kuma qawataccen falo wanda komai dake cikinsa kalolin milk ne da gold,komai qanqantar abun kuwa,komai dake cikinsa yana alamta maka gidan da kake kuma sashen wanda kake ba tare daka bata baki wajen tambaya ba,sarauta zalla,komai nadauke da tambarin masarautar,hatta kuwa da kujerun dake falon,falone wanda yake gaba gaba cikin jerin manya kuma tsararrun faluka dake kafatanin gidan,wannan shine qiyasi da wadanda suka samu katarin taba shiga falon sukayi.


Iska yafesar mai zafi daga bakinsa yana kallon manya manyan hotunan dake maqale a falo,wanda bana kowa bane face nashi maimartaba da mahaifiyarsa fulani aisha,wani shi kadai,wani shida ita,wani shida mai martaba wani su ukun,hotunane da sukayi bala'in kyau suka kuma dace da yadda aka shiryasu,hatta da frames nasu suma milk ne da gold.
7/11/21, 4:29 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAƊIN RAYUWATA*👑


*wannan littafin na siyarwa ne,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar siya ki tuntubi wannan numbers din*


0903 234 5899
Ko
09033181070


8



Gaban daya daga cikin hotunan ammin dake saqale ya qarasa ya isa gabanshi,sosai yazuba mishi yana kallonshi kai kace itace tsaye yana fatan ta karanci tsantsar gaskiyarsa takuma tausaya masa,ya rasa da wanne irin yare zai mata bayani tagane,duk daya fahimci ta gane inda yasa gaba,saidai bata da sha'awa ko niyyar yi masa abinda yake da muradi.


A qalla yashafe kusan mintuna goma ahaka,kana da kanshi ya lumshe kyawawan idanunshi sannan yabudesu,dai dai lokacin daya sauke ajiyar zuciya yasanya hannunshi yana sassauta daurin tie dinshi,kana ya zareshi ya jefar,yasoma rage duk wani kaya da yasan zai takura masa dake jikinsa,a haka ya isa bedroom dinsa yatura yashiga yazauna bakin zagayyen gadonshi yana cire sauran kayan da suka rage.


Sai daya gama cire sauran kayan da sukayi saura a jikinsa sannan yawuce toilet dinsa dake manne da dakin gadon.


Ya shafe a qalla kusan minti talatin sannan yabude qofar toilet din yafito daure da towel,gargasar jikinsa tayi luf saboda ruwa datasha sai sauran ruwan dake diga tun daga sumarshi zuwa qafarsa,a maimakon yazauna shafa mai saiya koma gefan gadon yasake zama,ya jawo locker dake manne da gadon yasoma laluben wani abu.


Mintina qalilan ya debo layukansa na qasar nan yasoma qoqarin cire nakan wayarshi ya sanyasu,bai kammala ba wani abu dake daga saman gadonshi yadanyi wuta gamida 'yar qararrawa,kai kawai ya daga ya kalli abun yamaida kansa ga abinda yakeyi,yasan wani ne ke falon farko yana jiransa,hakanan yakejin baison doguwar magana duk da dama haka halittarshi take,hakanan baison ganin kowa.


Yana gama hadawa yakunnata ya sanyata saman gadon yatafi gaban madubi yasoma shiryawa,nikam tsaiwa nayi ina kallon ikon Allah,kowacce gaba da irin nata man da turaren tamkar macen dake tashen budurci haka yadinga shafa kowanne a muhallinsa,yana cikin fesa body spray wayarshi tadauki tsuwwa,saiya dakata yana komawa da baya don ya duba waye yakirashin.


'Safwa' da manyan baqi shine sunan daya bayyana saman screen din wayar,saiya dauke kanshi yaci gaba da abinda yakeyi din ba tare daya daga ba,saboda yasani tariga da tasan tsarinshi,idan ta katse din ba zata sake kiranshi ba.


Saidai a wannan karon sabanin baya kiranne yasake shigowa,cikin mamaki yasake dubawa,ba ita bace sufyan ne,mutumin da yakeso ya kammala shiryawa yakirashi,babu bata lokaci yadaga wayar yakara a kunnenshi
"Thank god,yauna taki sa'a,ringing biyu kayi picking,'yan iskan yau basa kusa hala?" Yasan me yake nufi,kuma yaudin baijin wani jokes a kanshi irin wanda sukanyi lokaci lokaci a tsakaninsu,murya can qasa yace
"Kana ina?"
"Bansan wannan taqamar taka prince,ka dawo zaka fara kenan,nine maganinka,any way ina dab da shiga garin abuja ne yanzu"
"Oh shit!" Yafadi yana runtse idanunsa
"Hey friend,yaya dai?"
"Baida amfani tunda baka nan,see you later" daga haka ya katse kiran,ya cusa hannunsa guda saman sumar kanshi yana yamutsata,yana buqatar taimako,yana buqatar tallafi,yazama lallai yayi dukkan mai yiwuwa ammi ta fusakanci,ta gane matsalarshi,bayaso yakai ga fadawa ga halaka,yana qyamatar hakan matuqa da gaske,saiya nufi wardrobe dinsa yasoma binciken kayan da zai sanya da hanzari.


Falon dake manne da bedroom dinshi yadawo yazauna hannunshi riqe da wayarshi,yashafe aqalla awanni kan wayar da alama akwai abinda yakeyi kafin alamun dake bayyana anason ganinsa sushiga kadawa,karo na wajen biyar yana basarwa kafin daga bisani yatashi ya isa gaban cctv camera din dake nuna mishi duk wani sashe na gidan,ya fuskanci daga falo na uku ne,saiya shiga inda camera din falo na uku take,afnan ce tsaye bakin madannin qofar,fuskarta na nuna alamun qosawa,sanye take da doguwar riga wadda tabude daga qasa sosai tarufe har qafafunta,kanta yane da mayafi wanda iyakarsa wuyanta,tadan bubbuga qafa alamun gajiya da tsaiwar,saiya daga yabata izinin shigowa.


"Yaaya....barka da warhaka" tafada cikin nuna farincikin ganinshi
"Ammi tace zaka shigo,amma shuru munata jira,an kawo maka abinci kace a dakatar,shine ta aikoni in gaya maka,ka qaraso sassanta acan xamuci abincin rana tare" kai ya kada mata kawai,wanda hakan yasa tadan bata rai
"Yaaya,har yanzu baka daina ba?,baka bani amsa bafa"
"Am coming" ya amsata a taqaice,idan dasabo sun saba da halin miskilancinsa,wanda tun usuli haka yake,duk da kuwa yadda ammi taso ta sauyashi,koda qannenshi ne yadinga sakewa dasu suna hira amma abun yaci tura,ba kowanne lokaci magana take damunsa ba,tasan ci gaba da tsaiwarta bashi da wani amfani saboda haka tajuya tafice cikin ranta tana mita
"Shi mutum Allahn daya yishi koyaushe kaman wani kurma ko bebe,bakinsa ko tsami bayayi,saikace mai ciwon kunne wanda bayajin me mutane ke fada bare ya amsa su" da wannan qananun mitocin tafice takoma zuwa nasu sassan.


Zaune yake yana fuskantar ammin tashi cikin shigar qananun kaya da suka sake haska quruciya da kyansa,tazarar dake tsakaninsu dukka kayan abincine da abunsha nau'i daban daban
"Abdul'azeez" muryar amminsa ta ratsa dodon kunnenshi,wanda hakan yasa ya dakata daga shan tataccen ruwan inibi zalla da yaketa faman yi tun dazun,gaba daya jin cikinsa yake a cunkushe,bayajin sha'awar cin komai,saboda matsalar dake barazana da rayuwarsa yana jin tafi qarfin komai
"Ammi" ya amsa mata muryarsa a tausashe
"Matsalar dake gareka har tayi girman da zaka gaza cin abinci?" Ta qarshe maganar tana kafeshi da idanunta cikin son sake karantarsa,saiya ajjiye kofin hannunshi ya hade hannayen nasa waje daya,yana matuqar jin kunyar yin maganar da ita akoda yaushe,abu babu wani wanda zai masa maganin damuwar indai bai tsaya yabude baki yayi magana da itaba yadda yadace
"Hakan nada alaqa da cemin bazaka koma karatu ba?" Tasake jeho masa tambayar.


Wani nauyi yaji yahau kanshi sosai yadda ta tsareshi da idanu,irin wannan maganar banda abokai ba zaka iya yinta da kowa ba,to amma ci gaba da shurunshi na nufin fadawarshi halaka,saboda duk duniya ita kadaice zata lamunce mishi yasamu mafita
"Kiyimin afuwa ammi,nayi qoqarin nabi tsarinki kamar yadda kika umarceni amma hakan yaci tura,kiyi haquri ammi ki fuskanceni,idan na aikata wani abu da yake ba dai dai ba tamkar na zubar da mutunci da qimar masarautar nan dama taku masarautar,sa'annan bamusan ta wacce fuska abokan adawa zasu bibiyemu ba,wala'alla dukka abinda zan aikata din yazama sun tonoshi,yazama wani makami da zasuyi amfani dashi,wanda zai ruguza duk wani shiri naki akaina ammi,ammi....kiyimin afuwa,kamar yadda nataba gaya miki a baya" saiya sake sadda kanshi yana jin nauyi
"Ina da buqatar aure ammi,idan kikayimin,na miki alqawari bazai dauke hankalina koda ya kadeni daga dukkan qudurin da kika tsara ba,komai zai tafi yadda kike muradi ammi na miki alqawari".


Shuru ne ya ratsa ilahirin falon kai kace babu wani sauran me rai sai na'urori,kowanne tsakaninshi da ita akwai abinda ke kaikawo cikin zuciyarsa,tasani tabbas abdul'azeez

Please Login or Register in order to submit comment