Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun shekarun baya abinda yake da buqata kenan,tun baikai ga furta mata ba,amma sai tayi tunanin cusa masa ra'ayin karatu tuquru dason maidashi wani madaukaki zaisa ya manta da komai yabi tsarinta,tana ganin a yanzu abdul'azeez tayi quruciya da yawa,yayi qanqanta ace yayi aure,totally bama plan dinta kenan ba,hakan yaci karo da dukkan wani tsarinta,yayin da gefan abdul'azeez zuciyarsa ke cike da fata dakuma burin samun nasara a wannan karon,yanajin cewa indai yayi failing wannan karon to kuma babu wata sauran nasara da zai kuma saka ran samu,hakanan yana tsoron abinda zai biyo baya,bashi da tabbacin ci gaba da wanzuwa a bigiren da yake kai yanzu,komai na iya faruwa dashi,duk da ko sau daya baya yiwa kansa fatan haka
"Abdul'azeez!" Ta kirashi da wani tune dake nuna komai zata fada din daga zuciyarta take gaya masa,magana kaifi guda kamar yadda dabi'arta take!
"Kamar yadda nima na gaya maka a bayane,zancan yi maka aure a yanzu yaci karo da dukkan wani tsari nawa,hakanan zai iya zama silar rugujewar komai,zan maka aure abdul'azeez....amma ba yanzu ba,akwai lokaci,zan maka aure alokacin da duniya tasan waye yarima Abdul'azeez,zan maka aure lokacin daka zama irin mutumin da nakeso,zan maka aure asanda ka qarasa zama cikakken mutum mai raza da firgita zuciyar maqiya abokan gaba da abokan adawa,zan maka auren a lokacin aure na kece raini,irin auren da zai shiga bakunan al'umma,kamar yadda na zaba maka mata wadda tadace takumayi dai dai da yarima abdul'azeez,hakanan idan kayi haquri zan cika maka daya burin naka,amma ayanzu abdul'azeez....a karo na farko ni mahaifiyarka ina mai baka haquri daka dakatar da gudanuwar wannan tunanin a ranka,gaba daya ma abdul'azeez shekararka nawa,25 years fa?,kai kana ganin da wadan nan qananun shekarun naka zaka iya daukan duk wani responsibility na aure?,gefe daya ga goal dinmu da muke son muyi achieving duka at d same time?" Saita kada kai
"Taura biyu ba zata taba taunuwa abaki ba lokaci daya,kayi qoqarin cika dukkan wani buri nawa kagani abdul'azeez,babu abinda zaka nema ka rasa daga nan har zuwa lokacin da zaka bar duniya".


Shuru yakuma biyo baya,cikin qananun mintoci qwaqwalwarsa tayi masa bitar kalamanta,sai kawai yajanyo kwanon dake cike da alkubus yasoma zubawa,saboda yana ganin no way out kuma,abinda yafimishi yaci gaba da azumin tadawwu'i da yakeyi,duk da cewa wani lokaci yakan gamu da tasgaro da wahalhalu,daga lokacin dayayi buda baki zuwa wayewar gari,ci gaba tayi da nazartarsa saidai ta kasa fahimtar kowanne yanayi tattare dashi,hakan yake wasu lokutan idan yaso,duk yadda kaso ga karantarsa sai hakan ya maka wuya,tasauke boyayyar ajiyar zuciya cikin ranta tana fata da saka ran maganar tawuce a wajenshi ne.
"Zaka koma makaranta da zarar hutunka ya qare kamar yadda aka saba,banason mai martaba yasan komai,wannan tsarina,banason kuma yasan da zamansa" kai kawai yasake jinjina mata.


"Auta?,wa nake gani kamar auta?"kubra daya daga cikin amintattun fulani aisha ke fada dai dai sanda take shigowa farfajiyar dake hade da falon da abdul'azeez da mahaifiyarsa ke zaune,cikin waninirin hanzari ta janye kunnuwanta daga laben datayi musu,sannan cikin lokaci qanqani tayi qoqarin yanayinta na masu gaskiya
"Saqo nazo zan kawowa yarima daga sassan fulani adama,to nasamu kuma babu kowa ciknku,kuma ta jaddada min muhimmancin saqon,shi yasa nayi yunqurin neman iso da kaina"
"Saqo?,wanne irin saqo?" Kubra tafada tana jifanta da duban tuhuma,saita miqa mata wani farin yanki dake nannade da wani abu a ciki,kamar ba zata karba ba sai kuma tasa hannu ta amsa tana jifanta da wani kallo
"Kinfi kowa sanin cewa idan fulani na ganawa da yarima,a irin wannan lokacin haramunne ga kowanne cikinmu yarabi wajen sai wanda ta yarjewa,kada ki sake wannan kuskuren ko gangancin,saboda data ganki da kanta kinsan hukuncinki basai na fada ba,a sauka lafiya" tafada tana nuna mata hanya,cikin girmamawa tace
"Godiya nake" kana da hanzari ta wuce kubran,zuciyarta fal farinciki na samun nasarar da tayi kubra bata ganota ba,uwa uba yau tasan tana da gwaggwaban kyauta na iyakacin abinda kunnuwanta sukaji mata,duk da maganar data jin bata zama wata cikakkiya da za'a fahinta ba,amma matuqar akayi dogon nazari ana iya fahimtar wasu abubuwan.


Tsaye tayi tana nazarin yadda tasamu auta a tsaye bakin qofar,bata karanci wani abu ba,amma hakanan taji hankalinta bai kwanta da ita ba,saita jujjuyaa saqon kana taju tafice dashi,don tasan koda an isar dashi ga fulanin abinda zatayi shi zatace nata tayi itama.


Daidai lokacin da wayarta dake saman cinyarta tadauki tsuwwa,tamaida idanu tana kallon kiran uswa babbar diyarta da bata jima da aurarwa ba,wadda ke aure a masarautar kano dake shigowa wayarta,ta dauki wayartata daga saman cinyarta kana tasake cewa
"Maimartaba yana bahrain,dazun kafin isowarka suka tashi,yatafi taron sarakunan arewa,yace ka nemeshi da layinsa nacan" daga haka tadauki wayar uswa din.


"Zaka koma makaranta da zarar hutunka ya qare kamar yadda aka saba,banason mai martaba yasan komai,wannan tsarina,banason kuma yasan da zamansa" fulani adama tasake maimaita maganganun da auta ta gaya mata,ta jujjuyasu tana nazarinsu yafi sau shurin masaki,karo na wajen goma sannan tamiqe tasake tattaki hannayenta goye a bayanta,cikin murya mai amon sauti tafurta
"Nasani wallahi nasani,tabbas akwai wani boyayyen abu da aisha take boyewa,ba shakka nasan da wannan,babu yadda za'ayi ke daya tal kika haifi da namiji wanda babu ko shakka ayau mahaifinsa yarasu ko yayi murabus zai maye gurbinsa,amma ace kin turashi karatu wata uwa duniya,kin zareshi daga dukkan wata harka ta sarauta tamkar shidin agola ne ba jinin gidan ba,tabbas akwai abinda aisha kike shiryawa" saita waiwaya tadubi auta
"Inama ace kin samo gundarin jimlar cikakkiyarta,ba shakka da ayau kin karbi 'yanci" sosai furucin yabugi auta harya sanya jikinta tsuma,tazube gaba daya kan gwiwoyinta tana duban fulani adama
"Indai hakane....namiki alqawarin bankado miki dukkan wani shiri nasu muddin numfashina matuqar zan zama 'ya"
Kai fulani adaman ta jinjina tana fidda murmushi kana tamata nuni da tana iya tafiya.



☀�☀�☀�☀�☀�☀�☀�☀�☀�☀�☀�


Tamkar wadda aka bugewa gwiwoyi haka ta dinga qarasowa gaban gidan nasu idanunta qur kan gidan kamar wadda keson fahimatar yanayin gininsa don zana taswirarsa,duk wata yunwa da gajiyar tafiyar qasa data kwaso daga makarantar zuwa gidan tatafi babu ita,a yanzun fargaba kasala da mutuwar jiki su suka maye gurbin wadan nan.


Masu aikin gini keta kwaso qasa daga ciki suna fiddota waje,wanda kana ganin yawan qasan zakasan cewar wani sashe na gidan aka buge yabada wannan qasar,mahaifinta na coge qofar gidan cikin 'yan aikin yana sake musu bayani da wassafa musu abinda yakeso suyi masa,da gaske ne kenan hasashenta na dab da zama gaskiya?.


Hankalinta yayi matuqar nisa cikin duniyar tunani,har ta manta da cewa tsaye take qofar gidan nasu,saida taji wani hannu dake cike da qasa yana tabata ana cewa
"Yaaya oyoyo" sannan hankalinta yadawo jikinta,saita waiwaya tana duban gefanta,umaimace,jikin nan yayi budu budu da qasa kai kace tayi birgima ne cikin yashi
"Ya haka umaima,meyasaki wasan qasa bayan na hanaku"
"Gini ake mana yaaya a gida,sabon gini,har cikin dakinmu ma" tayi maganar cikin zallar quruciya gamida nuna murnarta a fili,lallai quruci dangin hauka,batasan hakan me yake nufi ba shi yasata take wannan farinciki,to amma kuma mamakinta datace gini har a cikin dakinsu,kada dai ace abinda yatabayi shiya sake maimaitawa,cikin sauri taja hannun umaiman suka shige cikin gidan da saurinta.


Duk da wannan aikin ginin hakan bai hana umna katti sana'arta ba,saidai duba daya zaka yiwa fuskarta kasan yau koma me aka mata a cike take fam,a nutse tabi tsarin ginin da aka soma yiwa kwaskwarima da kallo
"Ina mahaifinta yasamu kudin yin gini?,bayan yau kwanaki biyu baisiyo koda qwayar hatsi ya kawo gidan ba?" Tayiwa kanta wannan tambayar,babu mai bata amsa,hakanan tambayar bata da wani cikakken amfani a wajenta,tunda bayau tasoma gani ba,kusan wannan shine karo na uku a iya girmanta bayan tayi wayo cikin abinda zata iya tunawa,banda abinda yafaru cikin quruciya
"Me kike ne haka akaina,idan zaki gaba gwara kiyi karki fado kaina,don wannan ba abun mamaki bane wajen ubanku mai halin 'yan bunsuraye,wanda bai ganin akuya ya qyale ba tare dayabi ba,tunda kikaga haka ai amsar dayace,yaga wata akuyar ne zaibita" maganganun umma katti masu matuqar muni da kaifi suka katse tunaninta,saita maida kanta ga umma kattin bayan ta janye baya,da alama tun dazun take neman hanyar fidda kalaman bakinta,amma abun yayi muni da yawa,idan bata duba 'ya'yanshi ba da wasunsu a sannan ke cikin gidan a qalla ya kamata ta duba masu siyen abincinta da maginan dake wajen,idan su ba baqi bane game da yadda sukan aibata junansu maginan da masu siyayyar fa?,saita janye hannun duka qannen nata zuwa dakin nasu da tunkafin ta qarasa ta fuskanci aiki yabi ta kansa.


Ilai kuwa an kwakwashe kusan rabin dakin an bar musu dan ragowar filin da take da tabbacin ba qaramin quntata zasuyi ba yayi zamansu,tunda dukkaninsu qara girma sukeyi,wannan ne karo nabiyu daya taba datsar dakin nasu yaqara cikin gininsa duk sa'ilin daya tashi aure,cikin baqinciki take duban yadda kayansu sukayi budu budu da sumunti,tana tuna awanni shida baya kafin ta fita makaranta yadda suka hadu ita da qannen nata suka killace kayan da dakin tsaf gwanin sha'awa,amma idan ka kalleshi a yanzu ba zaka tsammaci haka ba.


Saita nufi akwatinta da sauri tana addu'ar Allah yasa kudinta data adana musu suke jalauta rayuwarsu basu salwanta ba,tajawoshi tabude tahau dubawa.


Nannauyar ajiyar zuciya tasaki harda lumshe idanu lokacin data iskesu yadda suke
"Mai gado!,ke bilki!" Muryar mahaifinta dake kwada mata kiran mafarauta ya ratso dakin,da alama dab yake da isowa,sai tayi hanzarin cusa kudin tsakanin cinyoyinta,daidai lokacin daya qaraso din


"Au,kema baqinciki kike da raya sunnar da mahaifinki zaiyi?" Yajefa mata tambayar da batasan hawanta ba bare saukarta,bata da wata mafita illa girgiza kai alamun a'ah
"Yar nema,sai anyi magana saiki shiga kadawa mutane kai kamar namijin qadangare,to idan ba baqinciki kike ba kina ji ina qwala miki kira ki kasa bude baki ki amsa min?"
"Banji bane baba,kayi haquri" tafada cikin rauni da sanyin murya,yanayin yadda tayi maganar saiya tuna masa da mahaifiyarta maimunatu,sai jikinsa yadanyi sanyi,ya qaraso cikin dakin yana dubanta
"Kiyi haquri maigado,ina nema mana sauqine kinji?" Yafada cikin muryar lallashi,cikin mamaki ta daga kai tana dubanshi,sauqi kuma wanne iri?,bataga wani alamu na neman sauqi daga mahaifinta cikin rayuwar da suke ciki ba,ganin bata fahimta ba saiya sake cewa
"Eh,kinsan annabi yace idan kana cikin talauci kana da mace daya ka ta biyu,idan ka qaro baka rabu dashi ba ka qaro ta uku,idan ka qaro baka rabu dashi ba ka cike ta hudu" tamau kanta ya qulle,duk da tasani babanta yayi dogaro da wannan hadisin qaryar ne tunda dadewa yake aikata dukkan aure aurenshi,hadisin da bashi da tushe balle makama,hadisin da bashi da muhalli ko digo cikin addininmu,hadisin qaryar daya halakar da magidanta da dama,amma tana da yaqinin a yanzun bazai taba fahimtar bayaninta ba idan ma tace zata fahimtar dashi
"Don haka shi yasa naketa wannan abun ko Allah xaisa a dace....nadan ragi dakinku zan mata bandaki a cikin dakinta,saboda balaraba tacemin batason bandakin hadaka,kinsanta gwanar tsafta ce,Allah dai yakawota zaki ganewa idanunki" ya qarashe maganar yana washe baki kamar wanda aka yiwa albishir.


Itadai kanta na duqe a qasa takasa koda dagoshi saboda kunya da nauyi harya gama maganarshi yamiqe tsaye,saiya sanya hannunshi a aljihunsa yafiddo dari
"Ungo wannan ki riqe a hannunki keda qannenki kuci abinci,karki bari wancan baqar kadarar tagani don silaina yau bazai shiga hannunta ba 'yar baqinciki,nasan yadda kiketa dawainiya dasu,kedin diyar albarka ce,kinyo gadon halin uwarki,Allah yaqara miki himma,yabaki miji na aurar dake na huta,ko yaron nan yamiki magana zai fito maigado karki masa halin miskilancin nan naki na banza,ki bashi dama kinjiko?" Bata da wani xabi illa tace masa to,saboda ta qagu ma yafice din yabasu guri.


Ranar bazata fita aiki ba saboda umma luba ta gaya mata zatayi kwana biyu gidan sarki,don haka tazage ita da qannen nata suka gyara ragowar filin dakin daya rage musu suka goge simintin da tsumma.
7/11/21, 4:29 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAƊIN RAYUWATA* 👑


*_wannan littafin na kudine,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina ds buqatar siyan naki kema ki garzaya ki nemi wadan lambobin_*

09032345899

9



Ya jima tsaye gaban mudubi yana qarewa kanshi kallo kai kace wata matashiyar budurwa ce data gama ado tanason tantance meye baiyi ba a jikinta tasauya,saidai shi tsaiwar da yayi sam bata da alaqa da irin wannan,yana tsaye ne yana duban kayan da amminsa ta aiko mishi dasu ayau,wanda yana da tabbacin nuni take masa da cewa ya aje qananun kayansa yakoma irin wannan shigar har zuwa lokacin da zaya koma inda yafito.


Kayane irin nasu na sarakai,wanda suka ji aiki ko ina dake nuna zallar sarauta,wani irin yadine ruwan bula mai turuwa wanda aka yiwa aiki da goldin din zare,sai wasu lausassan takalma rufaffu masu wata iriyar lanqwasa daga gabansu,hakanan an shirya musu duwatsu masu haske da qyalqyali daga samansu,takalma ne masu matuqar kyau daraja da tsada na zallar fatar damisa da gashin jimina,sai rawani da aka nada mishi wanda yadace da shigar tasa da kuma kalar kayanshi,yasan kuma ta sanya rawanin ne saboda umarnin data bashi nayau ya tabbatar yashiga anyi xaman fada dashi.


Sosai shigar tasauya kamanninsa,saidai ta qara masa kwarjini dakyau,tasake maidashi wani mai shekaru ta boye quruciyarsa.


Yana mamakin yadda ammin ke nuna mishi qauna da gata mai yawa amma ta gaza faranta mishi kan abu daya,abu dayan dashi a nashi ganin da kuma wajensa bai daukeshi a wata matsala ba.


Don kanshi ya gaji da tsaiwar,ya daga kanshi a nutse yaduba agogo,lokacin daya kamata ace yashiga yayi,saboda haka yanufi wayarsa da niyyar sanyata a silent yasakata a aljihunsa.


Saidai yana tsaka da qoqarin maidatan kira yashigo wayar tashi,kamar kowanne lokaci sunan Safwa yabayyana kan fuskar wayar,saiya tsaya yana duban sunan kamar baqone a wajensa,baisan iya adadin sau nawa tayi kiranshi ba daga dawowarsa zuwa yanzu,saidai kosau daya bai daga ba bare yabi bayan kiran nata bayan ya tarad da miscal,hasalima wasu lokutan shine da kanshi yake rejecting,don sam baiga amfamin ci gaba da tarayyarsu ba,tamkar ciwone,wanda maimakon azuba mishi magani sai ake bashi guba,saboda haka yasanya hannunshi yayi rejecting da kansa kana yaci gaba da abinda yake.


Kamar hadin baki kiran sufyan yasake shigowa,ya dakata daga qoqarin sakata a aljihu da yakeyi,ya daga kiran yakara akunnenshi
"Mazaaa.....ya mutumina kana gida ne?" Ya fada da alamun nishadi saman fuskarsa,cikin salon maganarshi dake cike da qasaita yace
"Ya akayi?,ina gida....but amma zan shiga wajen maimartaba za'ayi zaman fada dani" wani dan qaramin ihu sufyan yasaki najin dadi
"Kace kawai zaka soma shiga harkoki kaga ya suke?" Qaramin tsaki yaja saboda shi sam a yanzun ba wannan bane babbar damuwar dake neman durqusar da rayuwarsa ba
"Ba wannan ba.....tunda nazo bamu hadu da maimartaba ba yayi tafiya,sai cikin daren jiya yadawo....."
"Ohkey....anjima zan shigo,ina fata nasamu daddadan labari na amincewar ammi?"
"Aside this matter sufyan,saika shigo kawai" daga haka ya datse kiran yana jefa wayar a aljihu,sannan yasoma ficewa daga dakin.


Duk inda ya gifta saiya tsaida zirga zirgar duka wani hadimi ko barori dake kaikawo cikin gidan har sai yawuce,kwarjininsa kadai ya isa yacika maka idanu,kowanne sashe yagifta gaisuwa suke miqa mishi,basu damu da yadda yake wucewa ba tare daya damu dako daga musu hannu ba,saboda sun riga sun kwana sun tashi da tsabar miskilanci irin na abdul'azeez din,wannan ba wani sabon lamari bane a wajensu.


Tun daga nesa ya hangota tana tahowa ita da airah,diyar fulanin masanawa tafarko,wadda duka duka ba zata wuce shekara goma sha biyu ba.


Tunda suka hangoshi kowacce cikinsu tasake shiga nutsuwarta,shikam yi yayi kamar bai gansu ba,saidai yana sane da tahowarsu,saboda komawarshi ta qarshe yaba qwafe da walidan,yasha attempting na koya mata hankali ammi keda dakatar dashi
"Ba abinda bazaka gani ba tattare da yan uwanka...amma abinda bakeso dakai shine,babu ruwanka da ita,kadauke kai da idanu daga dukkan abinda zatayi".


Saidai wani abu guda,tun yana qanqani mutum ne da baison raini,yadda jinin sarauta ke yawo ajijiyarsa haka kusan dukka halaye da dabi'unsa suke,hakan yasanya lamura da dama babu ruwanshi dasu.


Suna gab da iske juna yayiwa dogarawanshi inkiya,tuni suka bace daga farfajiyar,kowanne yasamu saqo da kunnuwanshi bazasu jiyi tattaunawar abdul'azeez da 'yan uwan nashi ba yatsaya qyam yana jiran umarni
"Barka da warhaka hamma yarima"airah ta fada cikin girmamawa yayin da walida ke qoqarin wuceshi tamkar ma bata ganshi ba ko bata sanshi ba,duk da yadda zuciyarta ke tsalle saboda tsaro dakuma kwarjinin abdul'azeez daya cika wajen.


Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata data sanyata tsaiwa cak,take cikinta yajuya fuskarta tasoma hada gumi,amma sai tayi yunqurin saita kanta sanda kalaman mahaifiyarta yafado mata
"Karki sake karki kuskura kici gaba da bashi wata qofa da xaisa ya rainaki,kin bashi kwanaki kusan dari a duniya kafin isowarshi,karki yadda kwarjininsa ya firgitaki koda kinji razani a ranki.....haka halittarsa take,amma dole mukoyi fada da wannan kwarjinin nasa....wanda nake da yaqinin annamimiyar mahaifiyarsa ce ta nema masa....".


Taku uku yayi zuwa gabanta yana duban shigarta sama da qasa,shigace da sam bai dace ace tana ratso cikin gidan da ita ba,gidan dake da tarin hadimai maza da mata,ya mata jan kunne kusan kashi uku akan hakan amma bata sauya zani ba,saboda daurin gindi data samu daga wajen mahaifiyarta.


Dauke kai yayi kana ya gotata kadan kamar zai shige,idanunsa kan airah da take cikin yalwatacciyar doguwar riga da wadataccen mayafi,sam mahaifiyarta bata barinta tayi qazamar shiga tun tana qanqanuwarta
"Saunawa naja miki kunne kan dressing dinki cikin gidan nan?" Cikin tsananin jarumta ba tare data iya juyowa ba sun hada idanu tace
"Gaskiya abdul'azeez kafita daga sabgata.....idan ka manta bari na tuna maka,nidin yayarka ce,gaba nake dakai" tana kaiwa tasauke boyayyar ajiyar zuciya,wani qaramin miskilin murmushi yasaki,yamiqa hannu yariqo airah kana yadawo gabanta yatsaya yana duban qwayar idanunta
"Ko kadan baki taba wani abu dazai nuna cewa gaba kike dani ba,beside ma ayanzun koda bakiso nine gaba dake.....shigar qanwarki bata isheki misali ba?" Saiya daga yatsanshi yanunata dashi
"Wannan shine karo na qarshe dazan sake jan kunnenki game da wannan....ki kiyaye" saiya saki hannun airah yasoma tattaki zuwa gaba,kana ya basu alamar ya kammala da abinda yake,cikin sakanni suka bayyana sukaci gaba dayi masa tattaki har zuwa fadar.


ƙawatacciyar fada ce mai girma da yalwa,wadda tana jerin ɗaya daga cikin fadodi na alfarma cikin jerin fadar da sarki mu'az yake da ita,komai na cikin fadar kama daga shimfidu na alfarma zuwa kujerun zama,adon zanen (dagi) dakuma dardumai dake jikin bangon dukka golden ne da ratsin silver gami da maroon wanda kusan yafi yawa.


Hakimai da yawa sun isa gurin a sannan,harda shi kansa mai martaban,saboda haka yaratsa cikin nutsuwa ya isa gaban mahaifin nashi ya miqa gaisuwa kamar yadda kowa yakeyi sannan ya yiwa kanshi masauki daura da mai martaban.


Sun shafe a qalla awanni biyu cur ana zaman fada kafin daga bisani mai martaban yasoma sauraron shari'u daga talakawansa,abdul'azeez yana zaune daga gefe yana kallon yadda mahaifinsa kebin komai daki daki cikin hikima,kana yayi hukunci bisa adalci,sosai abun yaburgeshi,saiyaji duk a zaman wannan yafi qayatar dashi,zaman yatashi aka rufeshi da addu'a,maimartaba yawuce zuwa sassansa bayan yasa an shaidawa abdul'azeez umarninsa na cewa yasameshi a sassansa.


Su biyune rak cikin falon duk girmanshi,sai tarin kayan abinci da kayan marmari da aka ajiye musu
"Matso abdul'azeez" cewar mai martaba yana duban abdul'azeez din cikin tsantsar qauna da kulawa.


Sau tari abdul'azeez din kanyi mamakin yadda mahaifin nasa ke sakewa dashi sosai,sukanyi hira cikin yanayin da dazaka ganshi kai bakace shine MAIMARTABA SARKIN KAISA BA.


A bayan fage mu'amala yake musu irin ta uba da 'ya'yansa,bama iya abdul'azeez din kadai ba,har duka sauran 'yan uwanshi ma.


Cikin girmamawa yamatso,yasanya hannu kamar yadda shima maimartaban yasanya nashi hannun,duk da abdul'azeez don ba gwanin cin abinci da hannu bane,amma wannan karon abun saiya qawatar dashi.


"Yaya makarantar?,da fatan komai yana tafiya yadda yakamata?" Ya jefa masa tambayar sanda suke tsaka dacin abincin,kaiya jinjina yana qoqarin hadiye abincin bakinsa
"Ina fatan babu wata damuwa?,don na qagu lokacin da zaka kammala karatun yayi kadawo cikin ahalinka" kai yakuma gyadawa kamar wani qadangare yana qoqarin boye abubuwan dake yawo saman fuskarshi,don yasani sarai maimartaban ba baya bane wajen iya karantar mutum shima tamkar amminsa
"Ma sha Allah,Allah ya taimaka"
"Amin Allah ya taimakeka" yabashi amsa a ladabce.


Shuru yasake ratsawa kafin maimartaba yasake magana
"Ga 'yaruwarka nan....ta dage itama so take tafita koda egypt ne ta hada degree dinta" amamakance abdul'azeez yadaga kai yana duban maimartaba,sai akayi arashi shima shi yake kallo,hakan yasa yadan sauke idanunsa qasa yana ci gaba dakai abinci bakinsa,ko kusa ko alama baya yiwa 'yan uwanshi mata sha'awar barin qasarsu zuwa wata uwa duniya neman karatu har wata qasar,saboda su kadai sukasan me idanunsu suke ganemusu,yaran musulmi 'yan arewa hausa amma idan kagansu saika rantse da sarkin daya halicceka basusan wata kalma kota ZO IN KASHEKA da hausa ba,hakanan saika rantse basusan inane alqibla ba bare kayi musu tunanin musulunci,shi a karan kansa yatuna yawan 'yamnatan dake kara kaina da artabu a kanshi,duk da sautari kwarjininsa na taka musu burki,uwa uba bashi da fuska kamar yadda sauran samari keda ita,sakewa da sakin jiki da fuskawa duk wadda ta doshesu.


"Abdul'azeez" kiran damai martaba yamasa yadawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi,saiya dago yana duban mai martaba,dakatar dacin abincin yayi shima kamar yadda yaga mai martaba ya dakatar
"Ka gayamin meye ra'ayinka kan hakan,don ban sake magana ba kan lamarin ba,ba jirayi dawowarka ne,saboda kaidin watan watarana kaine uba a wajensu,koda kuwa akwai wadanda suka girmeka a cikinsu".


Cikin nutsuwa yabude baki yasoma magana
"Inda zai yiwu Allah ya qara maka lafiya....ni a nawa ra'ayin bana sha'awar daya cikinsu tafita wata qasar karatu....koda wacece kuwa a cikinsu.....,zaifi kyau dakuma kwanciyar hankali kowacce tayi karatu a qasarta....koda bazasuyi ba cikin qasar KAISA ba" daga haka yayi shuru yana jiran abinda maimartaba zaice.


Kai yake jinjinawa,shi kansa wannan hukuncin shine hukunci mafi kwanciya cikin ranshi,sai yaji abdul'azeez din nasake samun wani matsayi na musamman a idanunshi,kamar yadda halayensa da dabi'unsa suka banbanta hakama tunaninsa,duk da qananun shekarunsa da basu haura ashirin da biyar ba
"Wannan tunanin naka yayimin abduk'azeez,Allah ya albarkaci rayuwarka kaida sauran 'yan uwanka"
"Amin ya Allah Allah ya taimakeka....godiya nake".


Daga haka suka shiga tattaunawa kan wasu lamuran daban,wasu sun shafi masarauta ne kai tsaye,wasu kuma sun shafi al'amuran da suka dangancin sarki mu'az a karan kanshi.


Saida lokacin sallah yayi sannan suka tashi,yafita yabar maimartaba yana shirye shiryen fitowa don halartar sallar azahar cikin jam'i a masallacin dake mallakin masarautar kamar yadda yasaba duk lokacin da yake qasar matuqar ba tafiya yayi ba,wanda hakan yasake tasiri qwarai a zukatan dukka jama'ar gidan dama sauran al'ummar dake wajen masarautar.


Doka ce cikin gidan naduk wani bawa hadimi ko barori su saki dukkan aikin da suke da zarar lokacin sallah yayi suje suyi,wannan na daya daga cikin sirrika na daukakar masarautar,da samun wani irin kwarjini da haiba na musamman.


Yana gab da isa masallacin saqo ya riskeshi na nemanshi da amminsa take,hakan yasanya suna kammala sallar yawuce sashen nata,duk da yaso yafita yadansha iska yaga garin sosai,don tunda yazo bai samu ya miqe qafa ba,sai yake jinsa duk a takure,sakamakon sabo da yayi da qasar daya fito,wanda take wadace da guraben hutawa dakuma shan iska.


A falo na uku yau yayi burki,jakadiya ta isarwa da ammi saqon zuwan nashi,daidai lokacin tana zaune tana waya da babbar aminiyarta qwaya daya a duniya,wadda take iya raba sirrinta da matsalolinta da ita,kamar yadda itama take raba nata matsalolin da ammin,saboda tsabar shaquwa dakuma dadewa da sukayi tare tun zuwan ammi qasar nijeria,saita yanke kiran tana bawa surayya uzurin zata kirata.


Kamar koda yaushe,cikin shiga ta alfarma dake nuna izza da mulkinta ta tako zuwa falon
"Barka da warhaka ammi" ya furta yana duban yanayin fuskarta,bata amsashi ba har sai data zauna kana ta amsa masa,tare da jefa masa tambaya
"Meya faru tsakaninka da safwa?"
"Takawo qarata kenan as usual?" Ya tambayi kanshi da kansa can qasan zuciyarsa ba tare daya furtawa ammin ba
"Babu komai....takawo qarata ne?" Da idanu ta kafeshi nawasu sakkani sannan ta amsa mishi
"Tabbacin baka da gaskiya kenan,ka gayamin meya faru tsakaninku?.....ta shaidawa jakadiya kadaina daga

Please Login or Register in order to submit comment