Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉*








MALLAKIN


*©FATEEMAH RABI'U*
*(ZAHRAH ROYAL STAR)*


















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




Marubuciyar :


*1-RAYUWA*


*2-WATA RANA SAI LABARI*


*3-SA'ADHATU*


*4-ASMA'U (MA'U)*


*5-YAZDAD*


*6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI*


*7-RUHI BIYU*
*NOW*


*FANSAR MACIJIYA*






*GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.*








*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*


PAGE1️⃣➡️2️⃣




_________________✍️ Dandazon mutune ne a k'ofar Wani maidaidaicin gida k'ofar gidan a kulle take gam k'ok'ari suke su bud'e ta amma sun k'asa kai daka kalle fusk'okinsu wadda suka fi koya shiga tashin hankali samari ne kusan su *SHADDA 6* sunfi koya shiga tashin hankali d'aya daga cikin su wadda yafi shuru-shuru da gyar ya bud'e baki saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki ya kira sunayansu gaba d'aya *"JAMIL!!, SULAIMAN!!, ABUBAKAR!!, KAMAL!!, MUSTAPHA!!"* amsawa sukai a tare cike da tashin hankali Kamal yace "ya dai ALIYU da magana a bakinka ya zamuyi mu shiga cikin gidan nan ace mutum tun jiya da dare amma gashi har yamma tayi ba labarin sa ga gidansa a kulle kodai karya k'ofar zamuyi ne?"


Sauke ajiyar zuciya sukai jin Kamal ya kawo sha wara bud'awa sukai mutanan dake wajan suka kama bugun k'ofar da iya k'arfin su ai ko sunsha wuya kamin su b'alla k'ofar




Ko wanne daga cikinsu k'asa shiga sukai zuciyar su na wata mahaukaciyar bugawa ALIYU ne yayi k'arfin kutsa kansa cikin tangamemen porlon wani irin jan birki yayi ganin Abokinsu kuma mafi soyiwa a garesu yashe a k'asa babu alamar rai a tare dashi




Jikinsa yayi fari fat kamar an tsotse mai jini kalar jikinsa ta chanza ta koma bulu bikinsa na fitar da wani kunfa fari fat dashi jikinsa duk ya saddare,




Wani irin uban ihu ya kwalla yana zubewa a k'asa sumamme da sauri sauran Abokan suka shigo ba shiri zan birki sukai ganin abinda Aliyu ya gani ya sashi sumewa suma dai zuciyar su kamar zata faso k'irjin su saboda tashin hankali


Cikin wajan gari wani irin jeji ne tafe take tana b'ab'b'ak'a dariya iya k'arfin ta tana wata rausaya kai daka ga yadda take tafiya k'ugunta na jujjuyawa dukkan jikinta na launkwasa daka kalleta kasan ba cikakkiyar mutum bace zaunawa tayi jikin wani dutse kanta a duk'e d'ago wa tayi ta wani irin sauri (ni kaina sai da razana da tsananin kyawunta da kalar idanuwanta bulu shar dasu ga gashi ya sakko har yana so ya tab'a k'asa dariya ta k'ara shek'ewa da ita sai kuma ta fara wasu irin hawaye na jini jikinta ya fara sab'ulewa ya fara kumawa na maciji rabin jikinta ne daga k'asa ya koma na maciji wata irin uwar k'ara ta kwallah "inahhhh wllhy sai naga bayanku ku duka tunda kukai sana diyar shigata cikin k'unci kun jama kanku masifa da bala'i bazan barku ku zauna lafiya bahhhhh" ta ida maganar da murya mai k'arfi wadda har yasa dajin da tsintsayan dake rayuwa cikin dajin girgiza tsintsaya suka watse sama kasar dajin har wani tartsatsi take kamar zata rabe gida biyu.........






***************** Wani k'asur gumin boka ne zaune a wani k'aton kogo wasu macizzai ne durk'ushe a gabansa wadda ya kasance rabin jikinsu daga k'asa na maciya ne sai daga sama kuma na mutum ne kuka suke suna buga kansu a k'asa suna magiya da sauri cike da fushi bokan ya d'aga masu hannu da cewa "Matarka Alina tayi babban kuskure dole ne tabar wannan duniyar" yana nunata da yatsa d'ago fuskar tayi da duk ta b'aci da jini ga hawayen jini na shatata a idonta na tsananin tashin hankali da sauri na mijin wadda ya kasance mijinta zai bud'e baki domin magana bokan ya dakatar dashi "Bijay kasan cewa doka ce ba'a lamince muku shiga cikin bil Adam ba sai nan da shekara dubu biyar wadda zasu gaba shid'ewar zamanin nika amma Alina ta sab'a dole ne ta mutu"




Kuka yake kamin yayi aune Alina ta fad'i a numfashi babu a jikinta da sauri ya tallafo ta yana kuka bokan ya shima cike da tausayin wannan masoya yace "nima ba yadda zanyi ne dole tunda ta k'arya doka amma karka damu nayi duba zamanin da zaka fito daga wannan kogo bayan shud'ewar zamanin nika za'ayo wata irin Alina sak babu banbanci sai dai za'ayo ta ne a jinsin d'an Adam" da sauri Bijay ya d'ago da kansa yana kallon boka "kware kuwa zata dawo gareka amma ba'a jinsinka ba kuma za'ayota ne a musulma wannan kogon da zaka shiga har sai zamanin da za'ayota zata bayyana a kusa da wannan kogon za'a gina wata makaranta wadda chan zamanin suna kiranta da jami'a ne zata zo cikinta dumin yin karatu a wannan lokacin ne zaka fito daga kogon kaje gareta".........✍️








*To Masoyana sai naga yanayin comment d'in ku zan cigaba da typing yayi kukaji salon book d'in*




Nice taku


*FATEEMAH RABI'U Ce (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️✍️✍️✍️




Comment and share Fisabilillahi🥰🙏🙏




























*🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉*








MALLAKIN


*©FATEEMAH RABI'U*
*(ZAHRAH ROYAL STAR)*


















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




Marubuciyar :


*1-RAYUWA*

*2-WATA RANA SAI LABARI*


*3-SA'ADAHTU*


*4-ASMA'U (MA'U)*


*5-YAZDAD*


*6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI*


*7-RUHI BIYU*
*NOW*


*FANSAR MACIJIYA*






*GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.*








*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*




PAGE3️⃣➡️4️⃣






__________________✍️ Durk'ushewa sukai gaban gawar Abokinsu da Aliyu dake a Sume su duka hawaye suke mai cike da kunci da kuma rad'ad'in rashin dan uwansu da kyar mutane suka b'anb'b'are su daga gawar aka shiryasa aka kaisa gidansa na gsky,




Koda Aliyu ya farfad'o a gigice ya farka yana kuka mai tab'a zuciya yana tabbayar shin ina HAIDAR (wadda ya mutu kenan) da kyar aka samu aka kwantar mai da hankali tunani ya fad'a,


Sun kasance tare tsawon shekaru sun kasance basuda kowa su *TAKWAS* sun tasu a gidan Marayu sun gida kansu tabbas sunsha wahalar rayuwa amma kuskure d'aya yasa duk rayauwar jin dad'i da suke buri zata ruguje wadda ya kasance tsananin Abotarsu har gidajensu a jere suke inda Jamal yana da aure amma bashi da yara, sai Mustapha yana d'a d'aya namiji mai Suna *Al'ameen* k'arami ne wadda bai wuce shekara biyar 5 ba Matarsa ta mutu wajan haihuwar Al'ameen , Sai Sulaiman Shima yana Aure amma kamar dai Kamal basu da yara, Sai Abubakar bashida Aure, sai Aliyu wadda ya fisu yarinta shima baiyi aure ba, sai kuma Haidar daya mutu shima bai tara iyali ba.


Wannan kenan


Sai da aka kwana biyu da rasuwar wadda kwata-kwata zuciyar su bata kawo wai abinda suka aikata chan baya bane yake bibiyar su ba,




Bayan kwana bakwai wadda da yawonsu sun dawo normal amma banda Aliyu dan har yanzu mutuwar bata bar jikinsa ba,




Dare ne sosai wadda kowa ya kasance yana muhallinsa hadari ne sosai iska na kad'a wa mai k'arfin gaske ga wata irin walk'iya,


Zaune Abubakar yake a gidansa yana d'an daddana computer windows gidan na kad'a wa da d'an k'arfi tashi yayi yana yatsine baki saboda duk a gajiye yake duk sai da ya rufe ko ina zai juya ya zaune kenan ya fara jin ana buga k'ofa da d'an k'arfi baiji wani tsoro ko fargaba ba ya nufi k'ofar,




Bud'ewa yayi macece tsaye ta juye baya da sauri yace "wace a nan?" da sauri ta waigo tana Durk'ushewa k'asa cike da kuka da makyarkyata sanyi sanye take da kayan fulani tace "dan Allah ka taimaka min dare yayi ina tallar nono ga hadari", da kuka bai ban tausayi,




Cike da tausayi da kuma dama Abubakar akwai san mata har wani d'an lashi baki yake yace "Ahh haba ba komai shigo" har wani rik'o hannunta yake da sauri ta fisge bayan ta shigo rufe k'ofar yayi juyowar da zaiyi yaga ta juya baya da sauri yakai hannunsa yana juyowa da ita da sauri ya sake ta cikin razana yana ja da baya yana nunata da yatsa bakinsa na kyarma,


B'ab'b'ak'ewa da dariyar tayi mai amsa kuwwa runtse idanuwanta tayi sai kuma ta bud'e su sun rine sun koma bulu shar jikinta ne ya fara wani girgiza yana wani chanza kala daga k'asan ta ya koma maciji shar b'eb'e dashi,




Da sauri Abubakar ya buga wata uwar k'ara yana zubewa k'asa da sauri kuma ya tashi da gudu yayi hanyar waje yana shirin bud'e k'ofa,


Da saurin daya wuce misali tasa jelarta ta maciji ta yarb'er da k'afafunsa ya fad'i nannad'osa tayi tsakiyar cikinsa ta matso dashi kusa ta d'aga shi sama tana kallonsa cike da mugunta ta k'ara shek'ewa da wata mahaukaciyar dariya tana cewa "hhhhhhhhh ka shigo hannu kai har wani mai wayo ne da zaka iya tsallake kaidi na ne kunyi babban kuskure shigowarku rayuwa tahh" shi kuwa ya kasa magana sai mutsu-mutsu yake saboda ta matseshi tam bai aune ba yaji sara akan d'an yatsan sa babba ta sare shi sakinsa tayi ya zube a k'asa abinda bai wuce sakon d'aya ba jikinsa ya fara wata irin kyarma da chanza launi dafin macijin ya fara shigarsa jikinsa ne ya fara sandarewa bakinsa na aman wani farin kunfa na dafin da tana sa mai,


Cike da jin dad'i ta bace bat daga gidan kamar ba'ai wanzuwarta a wajanba tabar gawar Abubakar yashe a k'asa.......






****************** Da gama maganar sa bokan ya bace da sauri Bijay ya tashi yana shafa kasan sa ya koma kamar mutum gaba d'aya kogon ya shiga wadda ya kasan kamar kukar aljanu k'atuwar gaske.


*BAYAN SHEKARU ARU-ARU*




Zaune take sai shagwaba take zubawa Momy "please ki barni nida Aamah mu cigaba da karatu mana tunda kina da hali kinji Momynah" cike da lallashin take lallab'a Momy tana turo d'an k'ara min bakinta mai d'auke da jan leb'e fuskarta doguwa ce tana da siririn hanci dogo har baka ga idanuwanta manya dasu,


Cike da rashin son suyi karatu Momy ta kira sunan ta da cewa " RAYHA bank'i ba am
hankali na bai kwanta ba sam" da sauri Rayha tace "inshallahu Momy ba abinda zai faru damu kedai kiyi mana Addu'a shine Momy" sauke ajiyar zuciya tayi dai-dai nan Aamah ta shigo tana cewa "ai nasani Momy zata barmu ne inshallah ko Momy?" Tana lek'a fuskar ta murmushin k'arfin hali ta sauke tana rungume su su kad'ai Allah ya bata Babansu ya dad'e da rasuwa tace "Allah ya albarkaci rayuwarku dama tuni an samar muku makarantar kawai dai hankali ne ya kasa kwanciya ji nake kamar wani abu zai faru da kune" ta ida maganar cike da sanyin murya suma duk jikinsu yayi sanyi cike da kwantar mata da hankali Aamah tace "babu wani abu Momy Addu'arki muke nema babu abinda zai faru sai alkhairi" sauke ajiyar zuciya tayi tace "inshallah tuni kun fara lecture inshallah zuwa gobe ko jibi sai ku tafi koh?" Cike da tsananin murna suka rungume Momyn........✍️








*Shin wai mi su Aliyu suka aikata ne yake bibiyar rayuwarsu ne yake san k'arar dasu?🤔* *Miye Momy taji game da yarinta shin wacce rayuwa zasuyi a jami'ar mi zai faru da Rayha ne,🤔 kudai ku kasance dani sannu a hankali zan warware muku chakwakiyar*






*FATEEMAH RABI'U Ce (ZAHRA ROYAL STAR)*🥰✍️✍️✍️✍️






Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
































*🐍🐉 FANSAR MACIJIYA🐍🐉*








MALLAKIN


*©FATEEMAH RABI'U*
*(ZAHRAH ROYAL STAR)*


















*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*




Marubuciyar :


*1-RAYUWA*


*2-WATA RANA SAI LABARI*


*3-SA'ADAHTU*


*4-ASMA'U (MA'U)*


*5-YAZDAD*


*6-MAHAIFINA NE SILAR KOMAI*


*7-RUHI BIYU*
*NOW*


*FANSAR MACIJIYA*






*GA MASU BUK'ATAR NAH TALLAH TA MASU HAJAR SU A BOOK D'IN NAH ZASU BIYA ₦500 . KACAL KU TUNTUB'I WANNAN NUMBER NAWA 08130479973.*








*بسم الله الرحمن الرحيم*
*وصلى الله عل النبي الکريم*








PAGE 5️⃣➡️6️⃣






__________________✍️ Washe sun tashi da sabon tashin hankali wadda fad'ar shi ma b'ata lokaci ne bare Aliyu dabai gama farfad'owa ba,




Bayan akai gawar Abubakar zaune suke sunyi jigum-jigum wani mutum ne yayi masu sallama amsawa sukai hankalin su kwata-kwata jikinsu gyran murya yayi tukun yace "Gaskiya wannan aikin dana ga gawar Abubakar tabbas da akwai dafin maciji a jikinsa" da sauri suka waigo suna kallonsa cike da tsananin tsoro da kuma abinda suka aikata baya ya shiga tariyo masu, mutum ya cigaba da cewa "tabbas hakane amma zan had'aku da wani masanin macijzai zai iya taimaka muku inshallahu" da sauri su duka suka amince amma banda Kamal dake wani sham k'amshi dan shi kwata-kwata bai yarda da wannan abobuwan ba sam,




Inda basu bata wani lokaci ba mutunan yayi masu jagora har wajan sarkin macijzain wadda mutane suke mai lak'ani da *D'AN MACIJIYA*






Kamal kuwa yadai biyo su ne amma baya jin zai iya bin abinda za'a ce wajan da isarsu wani kogon dutse ne shiga sukai wajan cike yake da wasu layoyi da wasu y'an kwanduna kamar na saka dukansu macijzai ne ciki,


Zaune yake duk layoyi cike da wiyansa da wasu irin abu irin na maciji a damtsan hannunsa da wasu kalar zobina masu zanan maciji,


Tsaye suke a jere mutunan yayi masa mayanin mike faruwa da sauri D'an maciji yakai dubunsu a kan samarin su biyar a jere yace "tabbas kun shiga kaidin MACIJIYA wadda kwata-kwata ba imani a ziciyarta a yanzu tabbas ganin bayan macijiyar nan akwai jan aiki amma zan baku kariya tabbas indai kuna tare da wannan a d'aure a damtsen hannunku tabbas bazata iya koda tab'a ku ba" ya idasa maganar da d'akko wasu irin y'an hannu kamar laya ya bisu a jere yana sa musu dai-dai yazo wajan Kamal zai samai cike da rashin yarda da abin ya dakatar dashi ta hanyar d'aga mai hannu yana cewa "karka sake ka samin wannan shirmen babu abinda zai min" ya idasa maganar da iya gskyr sa su duka cike da kid'ima suke kallonsa dama duk cikinsu shine mai taurin kai da sauri Aliyu ya matso yana kama hannun Kamal yana cewa "haba Kamal kasan cewa muna cikin had'ari shin mi yasa zaka k'i ne please ka sa" yana amsar abin ya kamo hannunsa nufin ya samai,




Kamal kuwa fisge hannunsa yayi bai ce komai ba ya juya ya fice daga wajan, cike da tashin hankali suka bisa da kallo,




Da sauri D'an macijiya yace "lallai abokinku yana cikin hatsari" ya ida maganar cike da d'an b'acin rai yadda ya disga sa ya tsani mutum irin su Kamal sauke ajiyar zuciya sukai Jamil yace "yanzu dan Allah babu abinda zaka iya?" D'an macijiya yace "bari inada wani maciji mai fad'a dafinsa shima yana da had'ari sosai zan tura mata shi koh za'a samu nasara ya kashe mana itah" cike da gamsuwa




Sukai godiya da mutunan daya kawosu ko wannan su gida ya wuce Mustapha yana shiga gidan sa da sauri Al'ameen d'ansa da dawowarsa school yahau cinyarsa yana cewa "Abbee" jin shuru bai amsa ba yasa Al'ameen d'an lek'a fuskar sa cike da damuwa shima yaron ya k'ara cewa "Abbee baka lafiya ne?" Da sauri Mustapha ya sawo d'ansa ya rungume sa yana tsoron rasa sa gara shi ya rasa tashi rayuwar,




A wajan sauran ma Jamin da Sulaiman Matansu sun k'asa gane kansu saboda damuwar da suke ciki,




A wajan Kamal kuwa yana shiga gidan sa yaga matarsa cike da mamaki yace "ba cewa kikai kwana zakiyi ba ya akai naga kin dawo?"


Cike da wata irin rangwad'a ta tasu ta zauna a kan cinyarsa tana mai wani irin mayan kallo, cike da d'an mamaki yake dubanta matarsa bata saba mai haka ba anya kuwa kawar da zanchan yayi,




Cike da kissa zata kai bakinta cikin nasa da sauri ya kawutar da fuskarsa cike da shagwaba da kissa tace "haba Honey" tana turo baki hannunta dake d'auke da wasu zak'o-zak'on farci tana shafa fuskar sa d'an karsar sa tayi, da sauri ya dafe wajan kanne mai hannu d'aya tayi cike da jan hankali ta fara gogamai mazau nanta da k'irjin ta hankalin sa ne ya fara tashi,




Lura da haka yasa ta tashi zunbur da sauri ya rok'o hannunta bata juyo ba jawota yayi amma kamar dutse ya tsaye take wajan da d'an k'arfi ya sake jawota amma ina a tsaye take dai ta juya mai baya, cike da d'an tsoro daya fara d'arsar mai a zuciya




Yasha gabanta da sauri da tashin hankali da bugawar zuciya yaja da baya, wata irin dariya ta kece da ita tana mai hiddo harshanta zungurere kalar na macijzai sai kuma ta tsaya da dariyar suffar tace ta koma asalin tata, shi kuwa Kamal kalar jikinsa ce ta fara chanza launi dafin maciji ya fara shigarsa dan kuwa ta rika ta samai tafin tuni wajan data karceshi fad'uwa yayi kasa yana shure-shure na zafin fitar rai,




Ita kuwa wata dariyar ce ta sake yi tana cewa "kayi babban kuskure kai gaka mai taurin kai ko kayi kuskure kayi kuskureeeee rashin amsar wannan d'an hannun da aka baka suma kuma bawai tsallake kaidi na sukai ba daga su har wadda ya basu abin bai san wace ni bahhhh" ta ida maganar ta razananniyar tsawa wadda tasa gidan da duk wani gilassa dake cikin gidan faffashewa,




Kamal kuwa kunfa ke fita ta bakinsa ga jini na shatata ta hancin sa kamin kace mi jikinsa ya saki dariya tayi tana sa jelarta ta maciji tana bubbuga fuskar sa ganin rai yayi halinsa cike da farin-ciki ta tashi sama kamar kububuwa ta bace bat


Bata sauka a ko ina ba sai dajin da take rayuwa tana zubar da hawaye na rad'ad'in abinda akai mata da sauri kuma ta juyo jin kamar wani abu na bibiyar ta wani bakin maciji ta gani tsaye a gabanta wata irin dariya ta shek'e da ita tana cewa "lallai D'an macijiya kayi kuskure shigowarka cikin wannan sha'anin ni zaka turowa wannan k'aramin alhakin tabbas kayi kuskureeeee duk wadda yace zai dakatar Dani to zan d'au mummunan mataki a kansa........












****************** Da gyar suka rabo da Momy kuka kam sun shashi ita kanta kasa daurewa tayi sai da tayi kukan tabbas tana ji a jikinta wata k'addara na shirin faruwa d'aya daga cikin yaran nata tabbas ita zata kaisu wannan makarantar ba yadda zatayi ne in k'addara tazo kai bawa baka isa dakatar ta ita ba fatan ta ko wacce iri ce ta zo masi da sauk'i, sun baro garin *gwambe* cike da kewa,




Sun sha tafiya kana suka iso garin *RUMAN* mai cike da ni'ima da yawan shuke-shuke mai cike da kyawawan mutane wadda duk sun kasance fulani ne na Asali garin ya tara k'abilu da dama, school ce wadda ta amsa sunan ta wadda duk garin ba irinta sai d'an wane da wane keyita kai tsaye school d'in aka sauke su Rayha d'aga kanta Aamah tayi tana karanta sunan school d'in *UNIVERSITY OF RUMAN* kai tsaye school suka shiga babbar makaranta ce girmanta har ya wuce misali cike take da d'alibai Maza da kuma Mata kowa yana ji da kansa sunzo wuce d'akin da aka basu number d'akin tunda akai masu komai na school d'in ake baka number d'akin ku d'aki mutum Uku so yanzu mace d'aya ce a d'akin sai su sunzo gimta su maza ne sun kusan su biyar ko wanne sanye da k'ananun kaya sunsha askin y'an iska sai dizga y'an matan dake wuce suke su Rayha zasu gimta wajan kenan wani daga cikinsu yasha gabansu yana cewa "kai friend ga wasu zafafa" yana wani lumshi ido cike da shak'iyanci,


Tsaki Aamah da Rayha suka ja suna mai ra
rab'a ta gefe zasu wuce cike da jin haushin tsakin da sukai masu wadda yasha gabansu yasa hannunsa yajawo gyalan Rayha har yana zamowa kafad'arta cike da wani irin fushi ta waigo tana d'aukesa da mari lafiyayye tana nunasa da yatsa "shashasha kawai mararsa tarbiyya" su duka samarin tashi tsaye sukai cike da mamakin abinda tayi anya tasan shi waye kuwa? Shi kuwa huce yake cike da bakin kudiri a ransa lallai saya wargaza ma wannan yariyar rayuwa shi zatam mara kamar shi wacece ita,


Da sauri Ikilima wadda d'akinsu d'aya ta shaidasu ta k'arasu wajan cike da tashin hankali ta kama hannunsu tana cewa "kai Rayha kunsan shi waye kuwa d'an gidan wani ne a cikin garin nan babansa babbane kwata-kwata Abdallah baya jin magana an sansa a cikin school d'in nan miya za maku tsayawa wajansu?" Tsaki Rayha taja tana cewa "yo saimi ko ma d'an gidan wane kinga mi yayi mana ne kwata-kwata basu da d'abi'a wallahi" Aamah kuwa har d'an tsoro ya fara shigarta ta kasa cewa komai Ikilima ta katseta da cewa "ai duk wadda zai shigo school d'in nan sai sunmai haka in kayi banza dasu zasu rabo dakai ne" "hmm lallai kuwa wa'innan sun kai to wallahi nidai indai sukai min saina rama" cewar Rayha da sauri Ikilima ta d'od'e mata baki tana cewa "ke Rayha ki rufa mana asiri" bige hannunta tayi tana turo baki, shi kuwa bayanta yabi da kallo yadda k'ugunta ke juyawa duk da tasa babban mayafi amma hakan baisa halittun jikinta rikita d'a namiji ba idonsa ne yayi jawur har wani lashe baki yake da sauri friend d'in sa suka
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment