Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanyi.
Zuwan
maryam din ya yi mata dadi,dan tana da tarin
bukata kamar na dauke kewa,da wata hidima
tata
ta musamman da ta shafi sirri. Dan haka ta
karbi
maryam hannu biyu fiye da zaton
mutum,maryam
kuma ta canji Abdullahi inda ta dinga yi mata
hidima kan jiki kan karfi kusan fiye ma da
Abdullahi tun da ita mace ce. Kwanaki ukun da
abdullahi ya yi yana jinya,kwana daya a dakin
Hindatu,biyu a girkin fatima sai suka zame
masa
wasu kamar na sallah,ya sami hutu kuma ya
sami kusanci da hira tsakaninsa da
fatima,domin
da ta karbi girki sai ya kwashi jinyar tasa ya
tare
a can dakinta,babu halin ta daure masa
fuska,kuma dole ta dinga yi masa sannu tana
nuna masa kulawa saboda idon maryam da ke
tare da su. Da dare ma dole suka kwana daki
duk
da ta takura kanta ne akan sofa. Kwanan
sadiya
daya da karbar girki ya dawo gida da yammaci
ya
ci karo da maryam zata shiga gida,sai ya ji babu
dadi a ransa,dan malam ba ya son fitar su
maryam kamar matan aure yake kullensu,to ina
ta je? Tana yi masa sannu da zuwa yana bata
fuska da tambayarta. "Ina kika je?" Ta daga
masa ledar da ke hannunta mai dauke da
tambarin wani pharmacy,ta ce. "Anty fatima ce
ta
aike ni". Ya bi. Leadar da kallo cikin rashin
fahimta,ya ce. "Kika siyo mata me?" Sai ta yi
dariya kawai tana cewa. "Oho! Rubuta min ta yi
na zaci ma magani ne". Da sauri ya mika hannu
ya karbi ledar ya zazzago abin ciki,sai
numfashinsa ya nemi daukewa,ya zare ido yana
kallon maryam,ya ce. "Me zata yi da pt-strip?"
Fuskar maryama ta bayyana tsoro saboda rikitar
da ta ganshi a ciki. Ta debo in ina tana cewa.
"Ni
.... Ni wallahi ... Ban sa.... Sani ba...... Ban ma
san na me ye ba". Zuciyarsa ta kara saurin
bugu,numfashinsa na son shakewa.da kyar ya
dake ya mika mata tare da murmushin karfin
hali,ya ce. "Ungo! Kai mata". Maryam ta wuce
sukuku shi kuma sai shiga gidan ma ya gagare
shi gaba daya,saboda fargabar yadda zai je wa
sadiya a rikice, kila wannan ya janyo su tashi
dan
karamin yaki saboda rudanin da zuciyarsa ke
ciki.
Fata! Fargaba! Sun hade masa waje daya kawai
sai ya shige cikin motarsa ya dinga fama da
rigimarsu. Sallar magriba ta tashe shi ya wuce
masallaci amsa kiran mahalicci tare da dokin kai
wancan fatan nasa gare shi. Sai karfe tara ya
nemi gida bayan ya sallaci sallar isha,dadewarsa
a wajen bai hana shi shiga gidan a birkice ba,
saboda tsannain kaunar hada ido da fatima da
ya
mamaye ransa,ba kuma hada idon kawai ba har
da kaunar sauke mata tambaya daya kacal
wadda a ma'auni ta fi dutse dala nauyi. "A
kawo
maka abinci?" Da tambayar da sadiya ta kori
shirun da ke tsakaninsu ke nan, bayan ta gama
cikarta da batsewa,shi kuma ya nuna halin
ko'inkula.to a nan ma sai aka kuma
kwatawa,domin girgiza mata kai ya yi alamar
kar
ta kawo,tunda bai ga amfanin tambayar ba.
Sadiya fa ta zo wuta iyaka! Ta hadiye wani
katon
kullin bakin ciki,ta ce. "To wai me yasa ba zaka
sallama ni gaba daya ba? Ka hada mata kawai
da
kwanakin nawa,sai ka bar ni gadin dakinka
kawai,tunda ba zan ce ka barni zaman 'ya'ya
ba". Ya share ta,fuskarsa a hade ya dauki
remote
ya latso tashar kallon kwallo,sannan ya ajiye
remote ya wuce fridge ya dauko fura ya
markada
abarsa cikin matsakaicin jug ya hado da kofi ya
dawo ya zauna ya fara sha hankali kwance
abinsa. Da ta kalle shi sai ranta ya kara mungun
baci,kamar ta mike ta rufe shi da duka,sai ta
zabga wani katon tsaki,ta ce. "Me ye amfanin
zama da makiyi don Allah? Na rantse maka
yadda kake jin ka tsane ni haka nake jin
tsanarka
dan dai kawai ba zan iya sakin kaina ba ne".
Nan
ma ya shanye ya ki tanka mata abin da dama
ya
dinga gudu ke nan,ga shi kuma bai tsira ba, ya
kasa gane wannan bala'in na sadiya wadda ke
neman so da masifa. Har ta karaci maganganun
cin fuskarta bai tanka mata ba, ta fice daga
falon
cikin fushi,shi kuma ta ba shi damar fita ya
tunkari dakin fatima da nufin yi mata
bankwana.ita ma da nata cin kashin ya yi
kwankwasawar duniya ta share shi, dan maryam
ta yi bacci, dole ya kwashi sassanyar gwiwa ya
doshi dakin Hindatu domin yi mata tata asubar
ta
garin. A ranar bai yi bacci kirki ba saboda tsabar
fata da fargaba.ya rasa inda zai aza tunaninsa
akan farin cikin cikin fatima ko kuma a farin
cikin
yadda cikin zai iya matsanta mata zama da shi,
ko kuma idan labarin bai kasance haka ba akan
bakin cikin yadda zata iya masa wasarere da
cikin?
2 · Like · React · Report · May 16, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
.20) Da ya rasa mafita sai ya zabi ta tashi kai
wa ubangiji kokensa na godiya tare da neman
dauki. $ da safe ma bai sami ganinta ba, ya
sami
shiga falon saboda maryam ta tashi har ta fara
hidimominta amma dakin uwar dakin a kulle.
Sai
ya share ya fice kawai dan ya lura da take
takenta idan ya matsa sai ta tsinka shi wajen
maryam. ******************************
******
************************************
'Innalillahi
wa inna ilaihi raji'un! Kawai fatima ke fada
tana
maimaitawa tana ja da baya da jikin jikin din
bayan ta yar da tsinken gwajin da sauri. Tana
bin
kayan gwajin da kallo tare da shafa cikinta
lokacin da ta ke ja da baya kamar su be cikin ta
ke son gudar musu ba wanda ke jikinta ba. Ta
runtse ido ta girgiza kai da karfi tana dokin
abin
da ya faru ya zama mafarki,amma hakan ba ta
samu ba sai cikin nata ne ya yi mata inkiya da
wani karamin motsi da bayar da shaida. Ta
sulale
cikin jiri zuwa kan mat shower ta zauna cikin
kuka da girgiza kai tana hadawa da
ambaton,"A'a,a'a insha'Allahu ba zai kasance
ba!" Fiye da rabin awa tana fama da kuka da
wannan sambatun,can ta mike da wani karfin
hali
kamar na dan daudun da ya kama kadangare
ta
kuma farke wata takardar ta canja tasa ta sake
wani gwajin.tana tsaye a kansa ba ta ko kifta
ido
har lokacin ya cika ta zare tsinken shi ma ta
shiga gadinsa fiye da mintuna biyar sannan ta
daga shi cikin bugun zuciya. Har yau ba ta canja
zani ba,yanzu ya fi dazu fitowa rangadadau ma
kamar ya san shakka ta ke, kawai sai ta kece da
kuka!..21)
Tun kafin biyar ta cika Abdullahi ya dawo gida a
hikimarsa ta neman dalilin da zai sami ganin
fatima,su kebe idan ma da hali ya tambaye ta
sakamakon da gwajin ya bayar. Har biyar da
Rabi
yana zaune a dakinsa sadiya ba ta leko shi ba
bare ya hutar da tata zuciyar har ya sami
damar
tafiya ganin fatima,ga shi kuma yana kyashin
binta ya rarrashe ta tunda bai ga laifin da ya yi
mata ba. A karshe kawai sai ya fada wanka ya
shirya ya zari mukullin mota ya nufi dakin
fatima.ya same ta da maryam suna cin tuwon
shinkafa miyar danyar kubewa kwano daya.
Suna
gaisawa shi kuma yana duban agogo,sannan ya
sauke ganinsa akan fatima wadda kallo daya ya
yi mata ya karanto damuwa a kwayar idonta,ya
ce. "Abincin dare kuke ci ko na rana?" Ta yi
murmushi yake ta kawar da kai,da haka kuma
ta
bar tambayar tasa ta bi ruwa, saboda
makoshinta
ya toshe da haushinsa ba ta ko kaunar bude ido
ta ganshi,sai maryam ce da ta ke zaton jikin da
fatima ke ji ne ya hana mata magana,ita ta
amsa
masa. "Na rana ne, Anti ta kasa cin komai sai
tuwo". Shi ma ya gyara zama a gabansu ya
watsa hannu a kwanon yana cewa. "To Anti
sannu,dama yanzu shigowa nayi mu je asibiti.
Daga nan sai mu mayar da maryam gida tunda
ni
na sami sauki". Sai da ta ji fasali, sannan ta
amsa. "Rashin son cin wani abinci sai wani, ai
ina tsammanin ba cuta ba ce,ra'ayi ne kawai
saboda haka ni ba zani wani asibiti na, maryam
kuma ban shirya ta tafi yau ba". "Ya kai lomar
tuwo uku kafin ya amsa mata ba tare da ya
dube
ta ba. "Na sani,ni 'yar burum burum ce ba na
so.... Sannan malam ba ya son su maryam su yi
nisa da gida, idan muna son gaba a bamu ita ai
dole mu mayar da ita akan kari,amma dai in
ranki
bai so hakan ba ki yi hakuri. Ya kare maganarsa
da tausasa murya dan son ya ragewa zuciyarta
dacin da ta ke ji. Suka yi tsit har suka gama cin
abincin maryam ta nemi wanda zai kara
Abdullahi
ya amsa zai kara,har fatima ta yi musu
shiru,sai
da maryam na dab da shiga kicin ta dan daga
murya. "Shi ma ya koshi dan kadan zaki. Zubo
masa. Sannan ta bishi da harara tana cewa.
"Ban
ga fa dalilin da zaka zo ka cinye min abinci ba,
alhalin ga naka can". Ya kura mata ido tare da
wayon kallon cikinta,dan haka ya kasa damuwa
da ma'anar kyarar da ta ke masa har ta fara
tsarguwa da salon kallon nasa,sai da ya ga
tsarguwar tata ta yi yawa sannan ya basar yana
dariya,ya ce. "Dama kina cin tuwo? Amma
kwanaki can da na yi miki kika ce min ba ki san
shi ba,jiya kin yi tuwo yau tuwo,mene ne
dalilin?"
Sai ta juya masa keya kawai har maryam ta
fito.ya yi mata sannu da kokari,sannan ya ce.
"Ki
shirya mu tafi". Ko daya fatima ba ta so hakan
ba, dan maryam na matukar ji da ita,tana yi
mata
hidima tare da tausayawa,ko motsi ta yi sai ta yi
mata sannu,kuma ga ta da iya girki,da hidimar
yi
mata tuwo kullum ba tare da ta cika ta da
tambaya ba. Sai da maryam ta shige
daki,sannan
ta daga kai ta dan yi masa duban rahma. "Idan
kai ka ji sauki ni naji ne? In dai don ni ka kawo
ta ke nan. Ba tare da ya dube ta ba ya amsa.
"Idan ta zauna ni ne zan kuma kwantawa, dan
na
ga yanzu ne ma kike kan sharafin kina mayar
da
ni aljihun baya. Gara ta koma gidansu ni kuma
na
koma bakin aikina,idan kin ji ciwo sai ki kimtsa
halinki",. Kawai sai ta share shi, ta mike zuwa
dakinta inda ta yiwa maryam sha tara ta arziki
har da kudin dubu goma. Suka yi sallama da
ciwon rabuwa,ya tafi mayar da ita gida. Da ya
ga
take taken fatima na sanyawa kai damuwa da
neman rigima da shi sai ya watsar kai ita kawai
yana jiran ta karbi girki dan su ji dadin yinta
su
wanye. Ranar da zata karbi girki ta samo amsar
lissafinta(-) minu,ma'ana zabar zubar da cikin
kawai tun ma kafin ya fashe ya zame mata
matsala ta ko wanne bangare,wato ta bangaren
Alh da zai san ta ci amanarsa!da kuma ta
bangare Abdullahi da zai iya yi mata karan
tsayen
zubar da cikin,ko kum$a shi da danginsa da za
su hau ta yamadidin ta sami ciki. Cikin shirin
fita
ya shigar mata sanye da fararen kaya
kasancewar juma'a ce. Ya same ta zaune falo
cikin alamun tunani, amma tana ganinsa sai ta
daure fuska,shi ma sai ya dake ya dan bata
fuska
ya ce. "Me zan yi miki na karin kumallo?" Ta
dan
biyo shi da kallo tana so ta fassara
yanayinsa,sai
ya bar mata wajen kawai ya shige dakin
baccinta,har da turo kofa.ya dinga nazarin
dakin
kamar shi zai tabbatar masa da sakamakon
gwajin da ta yiwa kanta,cikin kasala ya hakura
ya hau gyara mata gadon,ya gyara dakin
tsab,sannan ya bude bandaki shi ma ya bi shi da
kallo har idonsa ya fada kan dust bin ya hango
tsinkayen nan. Ganinsu guda biyu ma ya fara ba
shi tabbas din ya yi nasara. Ya hadiye dukkan
murnarsa,ya fito falon ya same ta har yanzu
tana
wajen da ta ke. Ya gimtse fuska ya hau gyara
falon,har sai da ya kammala sannan ya kuma
dubanta. "Har yanzu ba ki yanke shawarar abin
da kike son ki ci ba?" Ta kara daure gira,ta ce.
"Kawai ka dafa min ragowar tuwon nan". Bai
tanka ba, ya wuce kicin din kawai.ta bishi da
kallo ranta na kara yi mata daci. Tana so
tilastawa kanta ganin bakinsa fiye da
yanzu,amma da ta dube shi sai abin da ke
cikinta
ya fado mata a rai.da alama zumuntarsa da
abin
cikin nata ke mata iyaka da kaiwa matakin
karshe
akiyayyarsa. Kamar yasan hakan ya ki yi mata
shisshigi, har ya gama hidimarta ya fice. Karfe
sha daya dai dai ta shirya ta baza hijabi ta
kullop
kofarta,ba ta damu da ta yi wa kowa sallama ba,
ba don suna tsakar gidan ba sun dai gaisa da
Hindatu har ta ce mata a dawo lafiya. Ta dauki
shatar adai daita sahu zuwa asibitinta, inda ta
dakatar da shi ta shige. Dr na jin cewa ita ce,
sai
da ya ji alamun tsoro da fargaba a
ransa,saboda
tausayin Abdullahi wanda ya kwallafa rai akan
samun dan kai. Ya sallami pt da ke gabansa ya
share wadanda ke kan layi.ya ce ta shigo. Suka
gaisa a gajarce kamar yadda suka saba, shi
yana
juya kujerar yana kallonta a nutse tare da
nazarin
cikin dukan ziciya.ita kuma ta yi kicin kicin tana
bin office din da kallo kamar wanda ya canja
mata.
1 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
.Zuciya d kwanji 2
22) Abin mamaki yanzu Abdullahi ya yi min
wauya kuma bai sanar min cewa kina hanya ba".
Ta yi saurin dubarsa kamar a rikice, amma sai
muryarta ta hadiye rikitarta,ta ce. "Ya yi maka
waya akan me?" Sai da ya ja fasali sannan ya
canja gaskiyarsa amsar da ya kamata ya ba ta.
"Ya tambaye ni izinin zuwa ku ganin game da
matsalolinki. Ya sanar da min ba ki da koshin
lafiya". Ta yi shiru tana janye kai a hankali,ta
jima kafin ta tanka,sannan ta nisa. "Sai ga shi
na
kawo kaina, sai dai kuma babu hannunsa ko
yawunsa a ciki, ni ce kawai da na da yunwar
lafiyar zata halaka ni nake son karya a zumin.
Ya
ci gaba da kallonta kawai da alamar tambaya
har
ta gaji da shan kamshinta ta fasa. "Ciki ne da
ni,
amma in so ka fitar min da shi dan ba ni da
bukatarsa, sai dai bana so Abdul ya san da
labarin". Kallon da yake mata ba zata iya
fassara
abin da zuciyarsa ke rayawa ba, amma zuciyar
tasa ta raya manyan abubuwa,ta ga kuma
girman
ta'adancin fatima da zaluncinta,wadda ba ta
san
kowa ba sai kanta.... Me ya yi zafi da ta ke son
mayar da zuciyar mutum mai kirki kamar
Abdullahi dai dai da bakin tunkunya? Da
tambayar da amsar sai ya hada su ya hadiye ,ya
kuma boye abin da ke zuciyarsa,cikin sakewa ya
ce. "Ayya! Me ya yi zafi? Ni kuma gani nake ko
wanne runtsi kika shiga Hajiya barin cikin sai ya
fi zubar da shi alhairi". Ta kyabe baki,ta ce.
"Ban
zo maka da tarihina dan ka yi min gyara ko ka
shawarce ni ba, in wannan ne sai in nemi
malamin falsafa. Na zo maka ne akan aikinka
wanda a kansa kake zaune a wannan kujerar".
Ya
jima yana wasa da biro cikin kada kai, sannan
ya
sauke numfashi ya ce. "Wanne nau'in zamu
yi?"
Cikin farin ciki ta ce. "Mai sauki dai, yadda
wani
ba zai fahimci halin da nake ciki ba". Ya kuma
jan
fasali, sannan ya ce. "Wata nawa ne?" Har
sauri
ta ke,ta ce. "Uku". Nan ma ya jima yana juya
al'amuran cikin ransa,sannan ya janyo takarda
ya
fara rubuce rubucensa, kana ya daga kai ya
dube
ta. "Idan haka ne,ba ma bukatar gaggawa ke
nan,sai mu yi komai cikin dabara,ki yi barinki
hankali kwance, yanzu za ki karbi allura da
magunguna mu jira sati biyu sannan ki dawo mu
dora,kin gane?" Ta kada kai zuciyarta daya. Ya
shirya mata file sannan ya yi kiran nose din da
zata ji da ita. Bayan allura har jininta aka
dauka
da ta nemi ba'asi sai nos din ta ce, mata za'a yi
wani gwajin ne. Sai sha biyu da rabi ta fito
asibitin a gurguje ta shige a dai dai sahun ya ja
suka tafi. Da yake juma'a ce yana tashi aiki
biyun
nan sai ya wuce gida. Sai da ya yi duba ya kara
bincikawa amma bai ganta ba, ya fito ya zagaya
baya sai su hindatu.ya koma yana mao tsoro da
tashin hankali,kar fa fatima ta je ta zubar
masa
da ciki?" Dan dai ya tabbatar din sai ya kuma
zagayawa baya hankali a tashe,ya ce"
"Hindatu,fatima fita ta yi ne?" Cikin shariya
ta ce.
"Eh ba ta dade da fita ba ka shigo". Ya
furta,innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a
hankali,
fuskarsa na kara bayyana damuwa da hasasshen
inda ta tafi. A rikice ya kuma duban hindatu.
"Dama ta taba fita?" Makira sadiya ta yi
saurin
amsawa. "Eh mana". Hindatu kuma ta girgiza
kai.
"Gaskiya ni ban taba ganin ranar da ta fita
ba,idan dai ba tare kuka fita ba". Ya yi kwafa
da
rangaji ya juya.bayan tafiyarsa hindati ta dubi
sadiya ta ce. "Me yasa zaki yi mata karya
sadiya?" Ta yi tsaki ta ce. "To me ye
amfaninta?
Da kin bar ni har da sharri sai na yi mata
wallahi.
Hindatu ta girgiza kai,ta ce. "Kin manta dan
sako
ne sharri, idan ka yi shi ba ka bukatar rufe kofa
dan zai dawo maka da amsa.ba na tsammani
makirci zai yi tasiri a lamarin mutanen nan
wanda
ya wuce addu'a.kina tsammamin duk tabarar
da
ta ke bai ji haushinta ba sai fitarta ba tare da
izininsa ba? Go slow ya hade wa su fatima, ba ta
sami isa gida ba sai daya da kusan rabi,lokacin
Abdullahi ya hakura da lissafinsa ya fita za shi
masallaci,sai suka yi kacibus a tsakar gida. Ya
babbake hanyar da zata wuce ransa bace! Tsoro
ya bayyana karara a idonta, don haka tayi
saurin
kawar da kai daga kallon kwayar idonsa. Ya
daka
mata tsawa ya ce. "Daga ina kike?" Ta dan ja
da
baya dan rage tazarar da ke tsakaninsu,bakinta
na rawa ta amsa masa. "Ina ka aike ni?" Kafin
ma ta dire kawo mata mari, wanda hucinsa ne
ya
sami fuskarta saboda saurin ja da baya da ta yi
hadi da dafe kunci, ta bar shi da marin iska.
Abin
ya ba ta mamaki tare da daure kai, ta dube shi
ta
ce.23)"Abdul lna tsammanin ka kai martabar da
zaka daga hannunka da sunan kai duka a
jikina?"
Ya cije lebe yana bin gidan da kallo,sannan ya
tuna akwai'yan sa ido,kawai sai ya finciki
hannunta ya ja ta dakinsa,yana rike da
hannunta
tana yunkurin kwacewa ya sa makulli ya bude
dakin,ya ja ta ciki sannan ya mayar da kofar
ya
rufe,lokaci daya kuma ya ture ta gefe kamar
dama cizonsa ta ke,sai da ta yi namijin kokari
sannan ta sami tsaywa da kafarta tana binsa da
kallo cikin tashin hankali iri iri. Ya murza hannu
yana kallonta da fuskar gargadi. "Da ace akwai
abin da ya fi duka kaskanci. Na rantse da na yi
miki shi a yau. Na tabbatar kuma ba za a zarge
ni ba dan na kaskantar da wanda ya kaskantar
da
kansa. Ta tare shi da shafakkiyar murya. "Na
yarda ni na kaskantar da kaina na aure ka,sai
dai
kar ka shiga dimunwa wannan bai isheka damar
da zaka daki fatar jikina ka zauna lafiya ba".
Ya
naushi hanunsa yana takawa a hankali ba tare
da
ya juyo ya dube ta ba da kaukkausar murya,ya
ce. "Na rantse miki duk ranar da kika kuma
sanya
kafa kika bar gidan nan sai na yi miki abin da
zaki gamsu kai kake fara kaskantar da kanka
kafin a kaskantar da kai, kawai ki rike a ranki
duk
hakurina da kawaicina ba zai taba shafar
dokata
kulle kafarki ba tare da izinina ba ki ba ni
amsar
inda na aiki ki? An fada miki ni Alh ne? $ sai
kawai ta saki baki tana kallonsa, bai ja maganar
ba ya nufi kofa ya fice bayan ya dubi agogo.
Tana layin ta biyo bayansa,ya fice abinsa ita
kuma ta bude dakinta ta shige cikin hawaye da
takaicin yadda abdullahi ya sami damarta. Babu
abin da ya yi mata ciwo irin kalamar da ya fada
mata. "Ko an fada miki ni Alh ne?" Ta wuni da
takaici da bakin ciki goma da ashirin,ga na cikin
jikinta ga na mai cikin. Hagun wani damar wani
ita kuma sadiya ta wuni da farin cikin da
rabauta
da irinsa tun ranar da aka kawo ta matsayin
amarya.. A yau ta tabbatar duk ma wata rawar
kafa da abu Turab yake akan fatima ta bogi ce,
dan duk tsaurin idon da yake mata kirari bai
taba
gwada dora hannunsa akan fatarta ba. Duk wani
kisinme kisime da sadiya ta san zai shugabantar
da ita a zuciyar abu turab ayau ta yi shi,ciki har
da daukar shawarar kisisina da kawaye suka
dade
suna ba ta tana watsarwa. Ta yi kwalliya ta kai
kala uku,tana baza idon ganin shigowarsa dan
ta
je ta fanshe nata girkin da yake kai wa fatima
idan hargitsi ya hado su. To bai shigo gidan ba
sai bayan sallar isha, kuma abin da ya kusan
buga numfashin sadiya kai tsaye dakin fatima
ya
shige. Ta dinga bulala tuarare tana safa da
marwa a tsakar dakinta,kawai sai ta jefar da
kwalba ta tunkari dakin fatima. Ya sami fuskar
fatima a kode saboda tsabar kuka,sai duk
jikinsa
ya kara sanyi,ya dinga nacin kallonta yana aika
mata sakon ban hakuri da ido,amma ta ki yarda
ta dube shi sai faman cika ta ke tana
batsewa,ya
ajiye jaka ya isa gabanta ya durkushe ya kamo
hannuyanta ya rike da sassauci,da sauti a
makogwaro ya ce. "Ki yi hakuri fadima.... Kin
ji?
Ki yi min uzuri akan yadda na rufe ido na yi
miki
ba dai dai ba. Haka Allah ya yi ni, so ko wani
KYALLI ba ya rufe min ido na kaucewa ra'ayina
wanda ba na kirkirarsa akan son zuciya,ko babu
wata a kasa ba zan iya barinki fita sasakai na
saboda kina da sura mai hatsari.... Bari na sami
ni dan karo ne kawai a cikin rayuwarki, Allah ne
dai ya sallada shugabancinki a hannuna...
Amma
na sani... Ke ma kin tabbatar min ni ba komai ba
ne a cikin rayuwarki.... Sai dai na yi mamaki da
na ji wani matsanancin kishi wanda ban taba
tsammanin an halitar wa wani bil'adama irinsa
ba lokacin da na zo na tarar ba ki cikin gidan
nan
duk kuwa da na san ni ba wata daraja nake da
ita
ba a wajen ki ....." Ya dinga kokarin kallon
fushin
fuskarta, idanunwanta na ga talabijin, ya kai
yatsanta bakinsa ya gatsa a hankali,sannan ya
hura yana son su hada ido, amma ta ki.ya
tausasa murya ya ce. "Kin janyo abin da makota
suka ji tsanainmu ko fatima? Yanzu abin da ya
fi
damuna ke nan, wato samun kofar da za a zaci
gibi a cikin son da nake miki... Kila ke ma ki ji
hakan a ranki.... Amma kamar yadda na fada
miki
laifinki irin wannan ba zan iya hadiyewa ba don
Allah kar ki kuma,kin ji? Ina kika je? Ina
fatan ba
wajen Alh kika je ba". Ta tamke gira rai a bace
ta
juyo ta dube shi, bakinta ya dinga motsi dan
canki cankin abin da zata ce masa... A karshe ta
samu kalamar ta fito da kyar. "Dama mun yi da
kai zaka yanke dangantakar da ke tsakanina
da
shi ne? To ko wajen nasa na je batawa kai lokaci
ne ka nuna damuwa a kai..." Kwankwasa kofar
da ake ya hana ta ci gaba da magana,inda suka
bi kofar da kallo su duka,a hankali abdullahi ya
furta. "Shigo" Sadiya ta shigo kwas kwas tana
taunar cingam ta tsira daurin dankwali daurin
ture
ka ga tsiya,sai zuba yauki ake. Sai da ta karaso
rukunin kujerun sannan abdullahi ya zare
hannayensa daga na fatima ya mike a
hankali,hankalinsa na kan sadiya wadda ta saci
idonsa ta watsa wa fatima harara,sannan shi
kuma ta hau yi masa gwalangwaso. "Abu Turab
talabijina ce ta ki yi, zo ka duba min don
Allah,zaman shiru babu dadi". Yanayin yadda
ta
ke ne ya daura masa kai, don wannan
kwarkwasar ba dabi'arta ba ce,ita banda masifa
ma ba ta iya komai ba, don haka ma ya ga sam
iya yin bai mata kyau ba. Ya saci kallon fatima
wadda ta yi suguri tana kallonsu,a hankali
kuma
sai ta kawar da kai cikin tunani. $ "kin janyo
abin
da makota suka ji kanmu ko fatima...? Wato
samun kofar da za zaci gibi a cikin son da nake
miki..." Yanzu ya gama yi mata wannan karatun
ga sadiya har ta fara biyawa.... Bayan takaici
sadiya har mamaki ta bata,ko ta dauka daga
daji
ta fito don hala ba zata gane wannan
karuwancin
ba? Ita da ta ke da dangi fal! Ko wanne gida da
nasa tsarin wanne irin shakiyanci ne ba ta sani
ba? Bakin abdullahi na rawa yana kuma satar
kallon fatima da ta dauke musu kai,ya ce. "To
ban da abinki sadiya ni gayaran talabijin na
iya?
Kin lalata ta kawai sai ki jita gobe na kira miki
mai gyara". Laraf fatima ta shiga maganar.
"Tun
da ka jiyo ta fadi haka ai ina tsammanain
gyaran
naka ne,sai dai a nan ma ai kana da wani
gyaran
duk da bai taka kara ya karya ba, gama da shi
sai ka yi wanka na rakaka ka duba mata". Tana
rufe baki sadiya ta amsa. "Haka ne,wanda ya
bata dole ya gyara duk da an baro kari tun ran
tubani inji hauswa". Fatima ta yi mata shiru
tana
saka amsar bata,sai dai da ta tuna mai saurin
fushi bai cika cin tiba,sai ta share ta kawai,ta
dauki remote tana latsawa tana sauraron yadda
sadiya ta dage tsakaninta da Allah tana yiwa
abdullahi shagwaba, wai sai ya zo sun tafi. Ya
kuma kasa daukar mataki a kanmta,kirjin
fatima
ya dinga radadi da zogi wanda ta kasa tantance
haushi ne ko kishi? Har sai da ta kasa hadiyewa
ta hade rai ta dubi sadiya ta ce. "Baiwar Allah
nan fa ba club ba ne da za ki ishi mutane da
haninya,shi kuma ba yaron kanti ba ne da za ki
ishe shi da tayi,ina tsammanin da karanki ya
kai
tsaiko ba sai kin batawa kanki lokaci haka ba. Na
ce ki je zai zo ya gyara miki.... Kin nace,ko sai
na janye alfarmar tawa kewar ta lahanta ki?"
Zata yi magana abdullahi ya tare ta. "Kin ga
sadiya ki je don Allah,wanka kawai zan yi in zo.
1 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 24) Takaici ya ishe sadiya duk
da tana ganin
ko yanzu ta yi nasara,ta juya ta fita,shi kuma
ya
rasa da idon da zai dubi fatima wadda ta kara
tamke fuska.ya yi 'yan kame kamensa sannan
ya
shige wanka. Bayan ya shirya ya fara
shashantar
da zuwa wajen sadiya da maganar abinci,har
yana gayyatarta su fita ta sami tuwo ta ci. Ba
don son cin tuwo da ya mamaye ranta ba babu
abin da zai hadata fita da shi, sai ta yarda, sai
dai ba cikin walwalar fuska ba. "Ina maganar
zuwa duba mata talabijin?" Ya dinga nazarinta
yana son gane abin da ke zuciyarta,darare ya
ce.
Ta kara tamke gira,ta ce. "Don me? Idan kuma
kewa ce ta dame ta fa? Ka san dole akwai
ciwo,mace da mijinta mata har biyu su aure
matshi,ban da ta uku me haramar zuwa
maimakon layin kwanaki hudu da ta ke hawa ta
koma na shida.... Ka je ka rage mata kewa
kawai,duk da zan dan yi muku cikas a gabana
za
a yi gyaran, amma na san ko da kallon fuskarka
da

Please Login or Register in order to submit comment