Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na yanzu a fakaice,don haka da ci da
zuci
ta ce mat. "Wannan ce hujjarki ta share guri ki
zauna a wannan kejin gidan,kuma don tsabar
zubar da aji tare da wasu mata har biyu
wadanda
ba su wuce 'yan share sharen ki ba a matsayin
kishiyoyinki?"
1 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
29) Sai yanzu ne ma zuciyar fatima ta kuntata
da lamarin Abdullahi,wanda ta tabbatar ba zai
wuce na tuna su sadiya ba, ta kyale baki ta ce.
"Ko daya,ya kankane ni ne,amma kullum ina
iyakar kokarina,yanzu ma da kika ganni asibiti
zani a yunkurina na zubar masa da ciki". Laila
ta
zaro ido gami da dauke numfashi ta dafe
kirji,ta
ce. "Ciki fatima? Da wannan kazamin yaron
kika
yarda kika sami cikin?" Ga mamakin fatima sai
maganar laila ta yi mugum bata mata
rai,musamman ta kiran Abdullahi kazami. Ta
jima
tana kallon laila sannan ta kawar da kai tana
bin
talabijin da kallo cikin tunanwan abdullahi da
suka karade mata kwanya musamman a safiyar
yau. Ta juyo ta dubi laila da bindin ido,ta ce.
"Wai cewa aka yi miki gardi na aura ne?" Laila
ta
tare ta da cewa. "Kwarai da gaske! Ba na ji an
ce
wani dan malam ba ne da ya ki halin malam...
Duk tsiya kuwa na san duk inda gidandanci yake
a nan ya yi gida ya tare...." Fatima ta tareta
da
dariya. "Gaskiya to kin jahilci waye malam,ni
dai
zan iya ba ki shaidar malam ya fi ko wanne
namiji iya soyayya,watakila don shi ya karanta
ya
san wace ce mace,ke nan ko kazami ne zai iya
ribatata masu rikita lissafi kamar
Abdullahi,idan
ban rufe ki ba fa ke nan!" "Ya kamata na
ganshi".
Da kalmar da laila ta fanshe mamakinta ke
nan,fatima ta ce. "Sai ki sami yammaci ki zo,ko
kuma wani week end" Laila ta sauke gwairon
numfashi ta ce. "Shi ke nan,mu ajiye
maganarsa
gefe mu yi ta alh.bayan doguwar jinyar da ya
sha
a dalilin cin amanar da kuka yi masa,jiya ya
dawo da alama kuma ya kasa ganin laifinki,shi
har yanzu sabuwa kike cikin zuciyarsa,ya bukaci
na zo ki sanar da ni bakin zaren idan akwai
hanyar da zai fara warwara bayan nasa
matakin
da yake shirin dauka wai duk dan a samu
wannan
kallagaggen yaron ya sahale miki...." Fatima ta
yi
murmushin yake,ta ce. "Wallahi ni babu wani
mataki da zan iya dauka akan Abdul laila... Ya
fi
karfina,kawai sai. Dai mu taru a bangaren
Alh....,sai dai ina rokonki abu daya,kar ki sanar
da kowa maganar cikin nan shi kuma alh kun
hadu ki sanar masa matakin da yake shirin
dauka
in dai zai fallasar da maganar auren kinsan
wutar
da na yi,to ya canja wani dan ba karamin
hatsari
maganar nan take da shi a kunnen kawu ba....
Kuma bana son abin da kawu zai la'ance ni....
Dan bai taba wulakanta diyancina ba, na
tabbatar
idan ya tsine min sai ta bi ni". A sanyaye laila
ta
ce. "In Allah ya so haka ba zata faru ba, da
kanki
ma zaki iya sanar da Alh,zo na kai ki asibiti ba
sai mu biya gidansa ba idan mun dawo...."
Fatima ta tare cikin zare ido. "Kina da hankali
laila? Idan tsautsayi ya hado ni da abdul ya
ganni fa... Ko kuma ya dawo gidan bai tarar da
ni
ba...." Cikin rashin ko'inkula laila ta ce. "Sai ya
yi miki abin da muke so kawai..." "Tunda ba shi
kadai ne matsalaha a lanurana ba, ina son
hada
dukkan burikana a lokaci daya,sakina da kuma
rufin asirina,da kuma rabuwa da Abdul
salin'alin
ba tare da na tafi da kewarsa ba, na tabbatar
idan na rantse ba zan yi kaffara ba, Abdul ya fi
Alh sadaukar min da rayuwarsa,don shi mai
kadan ne, yake kuma sadaukar min da kadan
din
ya hada min da lokacinsa da KWANJINSA,
sannan
da asarar farin cikinsa ta hanyata batare da ya
nemi fansa ba. Amma Alh fa! Duk kofar kishin
bakuta da yake toshe min da kudi yake toshe
min, wadanda ya mallake su babu adadi,kuma
yana fanshea da abin da ya aure ni
dominsa,wato
kyau na da nunawa duniya da abokansa
kyakkyawar matar da ya aura". Laila ta rasa
abin
da zata ce mata,sai ta dau jaka tana cewa.
"Taso
mu tafi in yaso idan mun dawo asibiti sai mu
biya a sai waya wadda za ku dinga tattaunawa
da Alh,sai kuma ki san hanyar da za ki boye ba
tare da ya kamaki da kokawa ya karbe ba".
Fatima ta san magana ta fada mata, amma sai
ta
kyale ta ta buge fa murmushi kawai ta mike ta
yafa mayafi suka fice ba tare da ta yiwa su
Hindatu sallama ba.
2 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
30)
Bayan laila ta sami wurin ajiye motar,ta fito ta
rufe tana kallon yadda fatima ke waiwaye
waiwaye ta kasa fitowa cike da mamaki laila ta
ce. "Wai wa kike son gani?" Fatima ta balle
murfin motar ta fito tana cewa. "Ko dai waye
bana son gani,ina fargabar kar na ci karo da
Abdul". Laila ta yi dariya ta ce. "Ina mamakin
yadda kike shakkar wannan mutumin wanda ke
yakamata ya yi shakka musamman da yake son
zama da ke karfin hatsi....". Suka jera zuwa
cikin
asibitin fatima na cewa. "Har yau ni ma
wannan
shakkar ke damuna,mutum sai ka ce wanda ya
yi
min sihiri,gaba daya ya mayar da ni wata
kidahuma". A kufule laila ta ce. "To wa ya
sani?"
Sakon zuwan fatima na isa ga likita,kafin ya ba
ta izinin shiga sai da ya kira Abdul a waya.
"Fatinma fa ta iso". Zuciyar Abdul ta buga,ya
ji
labarin kamar wani sabo a kunnensa da
sha'aninsa da fatima A rikice ya ce. "Dr da
gaske
fatima ta ke zata zubar min da ciki?" Likita ya
yi
ajiyar zuciya ya ce. "Ya wuce wai, tunda ga ta
ta
zo...." Suka ja shiru saboda likita ya rasa abin
cewa,Abdullahi kuma yana kokawa numfashinsa
da ke son ya tsaya cak! Har sai da ya sami fitar
da kwalla,sannan ya sami bakin magana.
"Likita
ba za a iya yi mata aikin daure bakin mahaifar
a
yau ba? Tunda kwanaki suka rage ya cika
watanin hudu?" A nutse likita ya amsa. "Za a
iya". Abdullahi ya yi ajiyar zuciya ya ce.$ "to
taimakon da zaka yi min ke nan, yi mata
wannan
aikin a matsayin na zubar da ciki,ku rabu lafiya
in
ta dawo gida sai mu hadu,duk da ina son
shigowa asibitin yanzu".. Da karsashi likita ya
ce.
"Shi ke nan ka kawo shawara mai kyau,Allah
kuma ya saukaka mana al'amuran...ya inganta
abin da aka samu, ya albarkace shi".$
Abdullahi
na nade kwallarsa ya ce. "Amin na gode". Suka
sauke waya,sannan likita ya kira abokin
aikinsa,suka dan yi tattaunawar sirri,kana ya
yiwa fatima izinin shiga. Ko gaisawa ba su yi ba
ya mike yana tattara takarda ya ce mata. "Ina
fatan yau ba ki ci komai ba?" Ta gyada kai cikin
shan kamshi,ya ce. "Kin tabbatar?" Ta gyada
kai,laila ta yi karaf ta ce. "Ai na yi zaton allura
zaka yi mata". Ba tare da ya dube ta ba,ya ce.
"A'a aiki za a yi mata a fitar da shi kawai".
Fatima ta zaro ido cikin dukan zuciya a tsorace
ta ce, "Anya likita babu matsala? Ni da nake so
ka yi min komai yanzu na koma gida,zaka
kinkimo min aiki,ya ya zai zama sirri,
maigidana
yana da matsala fa Dr..." Ya yi mata wani duba
na mamakin zuciya ya kawar da kai tare da
shanye mamakin,ya ce, "Kar ki ji komai za ki
koma gida nan da karfe biyar ko hudu..." Ta
tare.
"Lallai da sake,to ai hudu zuwa biyar din yake
dawowa... Ba ni da wani uzuri da zan iya
gabatar
masa na gamsar da shi". Cikin basarwa likita ya
ce. "Ni kuwa da ina masa kallon wani sassaukan
mutum..." Ta yi karamin tsaki ta ce. "Ganin
kitse
kake wa rogo, tsabar son mulki ke sanya shi
hayaniya,mutum da kafarsa sai ace sai ya nemi
dama kafin ya fito.ita ma sai an ganta za a ba
shi...yanzu dai me ye abin yi?. Ya kada kai ya
ce.
"Babu wani canji,sai dai da yake kina tare da
wannan malamar,karfe uku sai ta mayar da ke
gida ki karasa wartsakewa a can. "Har yanzu
fatima ba ta gamsu ba,da yanayin jimami ta ce.
"Kana ganin mai gidana ba zai fahimci halin da
nake ciki ko wani na kusa da ni ba?" Likita ua
amsa da cewa "Ina ganin ba wannan me mafi
a'ala tare da ke ba, kin sani cikin da ya kai
watanin hudu aka cire shi dole yanayinki ya
canja,sai dai kawai ki san hikimar da zaki yi
wajen sanar da mai gidanki zubewa cikin,ko bai
san da shi ba?" Sai ta gyada kai. Laila kanta sai
da ta ware ido tana kallon fatima, kafin ta
girgiza
kai ta ce. "Sai dai kawai ki ce kun nunke juna
kawai cikin fa ya turo sosai, sai idonsa ya kasa
gani? Ke dai kawai ki zubar komai ta fanjama
fanjam!" Da haka suka rufe tattaunawar aka
fara
shirye shirye shiga da ita dakin tiyata31) Abdullahi
na tsaye kan fatima a dakin da aka turo ta
bayan
kammala tiyata fana baccin nan mai kama da
mutuwa. Ya kurawa fuskarta ido sai zubar da
hawaye yake na ciwon ran yadda fatima ta dage
da sai ta salwantar da musu dan da suka yi
shekaru sun tsumayi daga shi har ita,wannan
wanne irin son zuciya ne? Anya kuwa a duniya
akwai fitiniyar mace irin fatima? Tun yana
karfin
halin dauke hawayen nasa har ya hakura ya bar
shi yana ta zuba. A haka likita ya kama shigowa
ya same shi,ya ce masa. "Hakuri zakayi
Abdullahi,insha'Allah komai zai zo da sauki baby
ciki koshin lafiya cikin mu kuma ya yi nasara.
Abdullahi ya nacewa kallon fuskar fatima
sannan
ya dubi likita yana goge hawaye,ya ce. "Mata
lamarinsu na da wahalar da numfashi. Wallahi!
Musammam kuma irin su fatima,na rasa abin da
yarinyar nan ta ke shiryawa rayuwarta,kina
gidan
mijin ki ki dinga gudun haihuwa,alhalin ba ki da
damar yankar wani tikitin sabuwar wata
rayuwar.ga wadda ke hannunki kuma shekaru
na
shurawa,ko don ta ga ku da zabi kyawunta zai
hana ku ganin munin aikinta in ma kun gani
kun
rabu da ita akwai masu rububinta? Abdullahi bai
musa ba,sai dai ya yi tawili. "Haka ne! Kuma da
taimakom son wanda ke hana ganin aibu. Amma
duk wadannan dalilin biyu ba su hana ni dora da
KWANJI a cikin tarbiyyarta ba, nake kuma
hadawa da addu'a don haka nake ji a
raina,zan
iya toshe duk wata kafar da zata fandare
hanya,wanda ya fi karfinma kuma na san
ubangijina zai min". A sanyaye Dr ya ce. "Na ga
wannan alamar". Yana tuno kalamanta na
dazu.
"...maigidana yana da matsala fa Dr". "..... Ba
ni
da wani uzuri da zan gabatar masa na gamsar
da
shi. "..... Tsabar son mulki ke sanya shi
hayaniya". DuKkan wadannan maganganun
nata
suna bayyana shakkarsa ne,wanda da ba ta yi
ba
karamin cin kashi zata yi akan sa ba. Likita ya yi
ajiyar zuciya,ya ce. "Yakamata ka tafi dan ta
kusa farkowa,me rakota ma na tabbatar ta kusa
dawowa". Abdullahi ya kara zubawa fatina ido,
sannan ya dubi Dr ya ce. "Dr idan ta farko ka
ga
tana cikin wani hali kar ka sallame ta, ka yi
mata
dabara ka ce zaka sanar da ni ta dabara,ya da
za
a barta cikin wani hali ba," Dr ya dafa
kafadarsa
yana cewa. "Kar ka ji komai,in dai hakan ta
faru
wanda ba a fata zaka ji wayata". Suka yi
sallama
ya fice. Bai iya komawa wajen aikinsa ba sai
kawai ya wuce gida cikin bacin rai da tashin
hankali.ya tsaya masallaci ya sallaci la'asar
sannan ya shiga gida. Jin shigowarsa ya sa
sadiya ta ji kamar ta zuba ruwa kasa ta sha
saboda murna. Ta dinga tsaiwa jikin taga don ta
hango shi yana rankwashin dakin fatima,sai ta
ji
shiru ya bata a dakinsa. Ba ita yakamata ta je
dakinsa ba don Hindatu ce mai karbar
girki,amma
kawai sai ta yi shahada ta mike ta tafi dakinsa.
Ta same shi zaune yana karatu kur'ani fuskarsa
a
jagule,don ko kallonta bai yi ba, ya fake da
karatun da yake. Don tsabar tsuguddi abin da ta
jima ba ta yi masa ba sai ga ta tana yi
masa,wato ta tsuguna gabansa ta zare masa
safar kafa,ta kunce masa neck tie ta zare masa
coat sannan ta wuce da su dakinsa ta fito ta
kawo masa lemo da ruwa.ta nemi guri ta zauna
tana jiran ya diga aya.ya gama haka ya ki
tsayawa ya tanka ta,sai da ta zauna sosai sai
murmushi ta ke masa, shi kuma ya yi fuska. Ya
rufe kur'ani yatsunsa na inda yake ya dube ta
yana kokarin hadiye bacin ransa,ya ce. "Kun
wuni
lafiya?" Ta muskuta ,ta ce. "Lafiya kalau.ko
dai
ka ce na wuni lafiya. Tunda Hindatu ba ta nan,
fatima ma haka". Ya yi saurin duban agogo
fuskarsa a bace. "Au Hindatu ba ta shigo ba?
Kamar ban ce kar a dinga fice karfe hudu a
waje
ba?" Ta tari numfashinsa da cewa. "To ai ita ma
fatima ba ta dawo ba" Cikin rashin kulawa ya
dauki wayarsa ya fara dubawa,ya ce. "Mun yi
zan
je na dauko ta,ban sami dama ba amma na yi
waya a kawo ta yanzu. Takaici ya lullube
sadiya,ta zura masa ido da duban tuhuma.
"Tunda idan na je unguwa kana zuwa ka dauko
ni
ko ka dauko Hindatu ko?" Shi ma ya zura mata
ido. Ba tare da fuskarsa ta karbi korafinta
ba,ya
mokade lebe ya ce. "Ko a gadon baya na zanm
daukota bai kamata ranki ya sosa ba,matar da
ta
ke da motocin hawanta na hana ta kawo su
gidan nan ke kin ga yakamata na barta tana
yawan motar haya? Wani lokacin idan kika tashi
korafinki sadiya ba kya hada shi da hankali
wallahi... To kin ga ba na son hayaniya,ki tashi ki
koma dakinki kar ita ma waccan ta shigo ya
zama wani korafin na daban ku da kullum abin
neman masifa ba ya yi muku kankanta. Kafin
ma
ta sami bakin magana ya tashi da alkur'anisa ya
shige daki,n ta fice dakinta.
2 · Like · React · Report · May 17, 2015
Ummee Amina
hmm
Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
32"Dr
wannan wanne irin Abortion ne na ga cikin nata
kurcici?" Tamabayr da laila ta yiwa Dr ke nan
lokacin da ake ta faman cike takardun daukan
fatima zuwa gida,wadda ke kwance tana mayar
da numfashin. Dai dai. Dr ya ki nuna damuwa
da
korafin na laila.,ya ce. "Zai sace nan da
kwanaki
bakwai,illa dai a kiyaye dokokin nan kar ta yi
aiki
mai wahala, ban da shara,ban da daukar ruwan
wanka.ke ban da komai ma sai dai ta ci ta
kwanta,abincin ma kar ta ci me nauyi...kin
gane?"
Ta gyada kai idon ta na kan fatima wanda ke
tambayarta lokaci da hannu,laila ta yi tsaki ta
ce.
"Wai dafa ki zai yi ne kika damu haka? Wannan
ma tsabar zubar da aji ne ki dinga tsoron namiji
haka". Dr ya dinga nazarin laila a fakaice
sannan
ya ce mata. "Malam laila ke nan,ashe zubar da
aji ne don mace ta yi shakkar abin da ran
mijinta
zai sosu.... Ko kin manta abin da ta yi laifi ne
babba?" Ba tare da laila ta dube shi ba, ta ce.
"Mazan ma suna suka tara,in ni ce da wannan
mijin na rantse ki zagina ya yi sai na rama"
Murya a shake fatina ta daga mata hannu,ta
ce.
"Ba na son cin fuska laila". Dr ya dube ta ya
dubi
fatinma,ya ce. "Anya kuwa kin san abdullahi
da
kyau?" Laila ta yi tsaki kawai ta kawar da kai
tana son maganar ta bi ruwa,shi kuma dr ya
nace
a yi ta, ya ce. "Laila kin fin kanwar nan taki
zafin
kai" Ta amsa masa da cewa$ "Ba kanwata ba
ce,kawata ce". Dama abin da yake son sani ke
nan,don kai wa Abdullahi tahoto,wanda ya
tabbatar laila ce ke zuga matarsa. Da haka ya
sallame su da taimakon nurse suka kai fatima
ba
cikin hayyacin ta ke sosai ba,dukkan
sambatunta
na fargabar kar su tara da abdullahi a gida ne,
tare da rokonm Allah kar ya sa ma kar ya san ta
fita. Sai dai kash! Sai ga ta a zaune bayan sun
shiga harabar gidan ta ga motarsa,numfash inta
sama sama ta dafe kirji ta ce. "Na shiga uku
laila,ya dawo wallahi". Laila ta zuba mata iso
cike da takaici. "Kin fara kai ni bangi
wallahi,wai
rufe ki da duka zai yi ne? Iyakacin ya ce ki
koma
nida kika fito,ba shi kenan ba,dawa ta yi
nama...." Fatma ta tareta da cewa. "Zai iya
dukan nawa,ko ma abin da ya fi dukan,in koma
inda na fito din ne kuma na tabbatar ba zai
fada
ba". A kufule laila ta ce. Wannan fargabar ta
kori
jirin da ke damunta,bakin fal addu'ar su shige
suruf ba tare da sun ci karo da abdullahi ba.ta
taka da kafarta suka shiga cikin gidan.
Abdullahi
na tsaye ta taga yana kallonsu har suka bude
dakin fatima suka shiga.ya saki labule ya tafi
gadi da sauri ya zauna lokaci da ya ji shi ma jiri
na kwasarsa,ya ma rasa irin matakin da zai
dauka akan fatima bare laila. Fiye da mintuna
goma yana zuba idon ganin fitowar laila,sai da
ya
ji buruntu kicin din fatima ya san kila ghirki ta
ke
mata. Zuwa wannan lokacin zuciyarsa ta rage
tafasa,ya shawarci kansa yin hukunci a
nutse,ba
da fushi ko gaggawa ba. Har yanzu hankali
fatima bai gama kwanciya ba, tana sha tea a
hankali idonta a kofa, kunnenta a kan juyo
motsin
bude tasa kofar.can ta ji sallamar
Hindatu.lokacin
daya da bude kofar dakin nasa ya fara juyewa
hindati nata sababin da kakkausar murya.
"Duba
agogon hannunki karfe nawa?" A ladabce ta
fara
in ina. "Ka yi hakuri... Wal wallahi go slwo ne ya
rike ni.amma tun uku da kadan na fito". A
zafafe
ya ce mata. "Da ya rike ki ai sai ki kwace ki koma
inmda kika fito tunda na ce in dai an san za a
wuce karfe hudu a waje gara a tambaye kwana.
Ta kuma kwaso wata magiyar. "Don Allah ka yi
hakuri Abu Turab.." Ya kuma tarewa da bala'I.
"Kin ga Hindatu kar ki kara fado min wata
magana, da hakuri da rashin jin maganar tawa
duk ki ci gaba da tanadar min su ai dan inyi ta
fama da su na zo duniyar". Ta yi shiru kanta a
kasa,ya kuma sauke huci,ya ce. "To ki sha
kuruminki idan ma kin yi haka ne don ki bata
min
rai, to tare da naki kika hada wallahi na da
wata
daya da wasa kar inji kin tambaye ni fita".
Gaban
fatina ya ci gaba da dukan uku uku ta yi kasake
da tea a hannu,laila kanta sai da ta ji abin a
jikinta,ta ce. "Fatima,wannan wane irin dan
sababi ne?" Hankali fatima kamar ba ya tare
da
ita ta ce. "Laila rufo mana kofar nan kar ni ma
ya
zo ya sauke min nawa wanda na tabbatar sai ya
fi nata tsauri". "Insha'Allah ba zai shigo ba".
Sai
ga shi kuwa addu'arta ta karbu,don ficewa ya yi
daga gidan sai tashin motarsa suka ji. Fatima ta
sauke ajiyar zuciya kila wa kalanci,wato ko dai
Abdullahi bai san ta fita ba,ko kuma cikin nata
hukuncin ke nan. Laila ta yi ta kwantar mata da
hankali,sannan suka yi sallama da zummar gobe
zata dawo ta dubata kuma zata taho mata da
waya.
2 · Like · React · Report · May 17, 2015
Amierah S-Man
ndalin hausa novels
Zuciya d kwanji 2
33
Sai da bacci ya fara fizgarta a nan falo ta ji
bugun kofa. Ta dubi agogo da sauri cikin bugun
zuciya, agogon ya nuna tara da rabi,ta yi baccin
rabin awa ke nan,domin ta ga tsinken agogon
akan tara dai dai saboda kasa kunneb shigowar
abdullahi bai shigo ba, har baccin ya dauke ta. A
tsorace ta ke, don haka ba ta bude masa ta dawo
falon ta zauna tana jiran tasa karsasowar. Bai
ko
dubi inda ta ke ba, fuskar nan tasa a murtuke!
Ya
dinga shiga da kayan masarufi store dinta, har
ya
gama ya dawo falon ya kwashe kayan tea din da
ta shi da gwangwanayen lemon da suka sha ita
da laila,ya wuce da su kicin. Sannan ya dawo ba
tare da ya dubeta ba ya ce "Me za ki ci?" Ta
dube shi da kyau,sai ta ji shakkarsa ta kara
rufe
ta, tana in 'ina ta ce. "Na ..... Na sha tes ya
gamsar da ni" Ya mokade lbe, idonsa akan
talabijin ya ce. "Kin yi wanka?" Girgiza kai
kawai
ta yi, amma da tasan ba lallai ya san ta yi ba,
tunda ba kallonta yake ba, a hankali sai ta ce.
"A'a Kawai sai ya wuce dakin baccinta zuwa
bandakin ciki, ya tanadar mata ruwan wanka
mai
saukin dumi,sannan ya kirata daga cikin dakin
ya
yi kiranta da murya babu walwala. "Ki shigo ki yi
wankan". Ya kamata ace ta taya shi wannan
danyan kan nasa, amma ita ma sai ta ji a
ranta
gara ta lallaba shi tunda ta riga ta yi
laifin,laifin
da ya sha fada mata hukuncinsa zai iya zama
ba
fallasa sirrinta ga kawu,wadda ta ke jin gara
mutuwa akan haka. Ta mike da kyar ta shiga
dakin a hankali saboda ciwon da dukkan
gabobinta suke babu ma abin da ya fi damunta
irin yadda cikinta ya dameta da watsal
watsal,sai
ka ce akwai dan da ke mata busharara shi ba a
cire shi ba. Ta same shi gaban dressing table
yana feshe kayan baccinta da turare,daga nan
ua
fara ware mata bargon kan gadon yana rage
fulullaka yadda dai zata sami komai cikin sauki,
wannan kyautatawar tasa ce ata sa ta rashin
ganin aibun fushinsa,har tausayin sa ya sata
jin
kwalla ta taru a idanunta. Yadda ta ke jan
numfashi ya sa dole ya dan dora mata ido a
fakaice,ita ma tana satar kallonsa ta yi saurin
daure numfashin ta shige bandakin ko kayan
jikinta ba ta rage ba. Har man wanke baki ta yi
wankan ta gama cikin hawaye don haka har ta
same shi zaune kan stool cikin zurfin
tunani,cikin
dar dar ta wuce ta dauki kayan baccin,ta juya
baya ta saka ba tare da ta nemi ko shafa mai
ba,
ta haye gado ta ja bargo ta lumshe ido. Kamar
daga sama ya jefo mata tambaya muryarsa a
cushe. "Zan iya sanin inda kika je yau?" Ta ji
numfashinta na neman sarkewa saboda fargaba
da neman amsar da zata ba shi don haka suka
kwashi lokaci yana jiran amsarta har ya kuma
cewa. "Wai ba ki ji ba ne?" Rukani ya sa ta tashi
zaune ba tare da ta shirya ba, tana dubansa kai
tsaye ta ce. "Ni babu inda na je". Ya kara tara
gira yana dubanta,ya ce. "Ko? Amma na dawo
ban tarar da ke ba,kuma ina cikin gidan nan
kika
shigo. Ta kawar da kai daga gare shi,ta ce.
"Gaskiya ba in ba ce, don ko kofar daki ban je
ba". Ya sauke nufashin yana girmama karfin
halinta,ya kawar da kai cikin cije lebe,ya ja
fasali
sosai sannan ya kike tsaye ya dubi tsabar idonta
ya ce. "Fatima kai ki mayar da ni dan iska kin
ji!
Kar kuma ki taba tsammanin sonki ya yi min
runtsewar idon da zaki ci kashi a kaina na zuba
miki ido... Na ce dole ya zama da izinina, kuma
dole hakan ce zata kasance wallahi ban fada da
zummar waka ba! Shugabancina a kanki da
matsayin aurenmu kamar sauran aure a
musulumci ba zai taba canja salo da ka'idoji ba
wai do ba kya sona ko ba kya son ki zauna da ni
ni da nake shugaban da KWANJINA nake motsi.
Kamar yadda ba ki da ikon sakin kanki haka
zalika ba ki da ikom canja matsayin biyayyarki
gare ni zuwa yin komai na radin kanki.... Na
rantse miki ba ki isa ba wallahi.... Kin yi na farko
kinyi na biyu, kuma kin yi na karshe,duk ranar
da
kika kuma saka kafa kika bar gidan nan sai na
yi
miki rashin mutumcin da har ki mutu ba zaki
manta da ni ba. Kin fara fitina ta
wallahi,hakurina
ya fara taba bango a lamarinki... Na fada miki
na
kuma har abada babu saki tsakanina da ke,
hakan kuma ba zai sa na laminci abin da raina
ba
ya so a cikin lamarinki ba. Idan ma kin sami
dan
iske ki sanar wa Alh da kike zuwa wajensa...
Kuma idan kun ci amana ta Allah ya saka
min...."
Bai saurare ta ba sai ya fice ya bar ta baki bude
kekkece saboda kuna. Ta yi kuka, ta yi kuka ba
ta da me rarashinta,har sai da zazzabi ya rufe
ta
sannan ta koma ta tasa inda kudundunar tana
faman makyarkata.ina ma daga haka ta
zarce,ta
huta da wahalar wannan rayuwar da mutum na
ya samun abin da yake so. Haka ta kwana tana
makyarkyata,ga dukkan jikinta yana
ciwo,mararta
ma ta kulle tana ciwo, sai ta rasa inda zata
tsoma ranta,Allah Allah ta ke gari ya waye ta
nemi dauki,don haka da ta yi sallah asuba ta
dinga kasa kunnen shigowar Abdullahi har zuwa
lokacin da zai shigo mata.... Amma bai shigo
gidan ba sai da rana ta fito bakwai da
rabi,wanda
wannan lokacin ma ya gama shirin fita ofis.
Yana
shiga dakinsa Hindatu ta cimmasa ta durkusa
har
kasa ta gaishe sji,sannan ta mike a ladabce ta
ce, "Abu Turab wai duk fusjin ne? Don Allah ka
yi
hakuri". Ya girgiza kai da sauri da son ya yi
murmushi,ya ce. "Ya wuce wallahi" Ta ce,"ban
ga
alamar hakan ba,jiya fa baka yi baccin kirki ba,
ka fice sallar asuba ba ka shigo gidan ba sai
yanzu. Ina ganinka ka shigo babu walwala,sai na
ga me ya yi zafi?" Ya share fuska yana kawar
da
kai,ya ce. "Ba wannan matsalar ba ce,akwai
abin
da ke damuna... Ku saka ni cikin addu'a". Cikin
tausayawa ta ce. "To Allah ya warware". Ya
ce,"amin, yi min afuwa na ga fatima ba ta da
lafiya" Ta yi saurin gyada kai tunda tana son
ya
huce,ta ce. "Babu komai". Ya yi mata godiya ya
juya ya fita. Ya same ta kudundune a gado
tana
ta faman kuka da makyarkyata,ya kara daure
fuska don ya yi tsammanin kukan rikicin da ya
yi
mata jiya ta ke, don haka ya yi mata banza ya
fara abin da ya kai shi, wato gyaran dakin,
amma
makyarkayartar da ta ke ya sanya dole ya
sanya
mata ido,murya a cushe ya ce. "Wai wannan
kukan na jin dadi ne ko na me? Ni ya kamata
na
koka don ni kika cutar,me yasa kike son nuna ke
aka cuta?" Ta girgiza kai cikin wahalalliyar
murya,ta ce. "Abdul ba ni da lafiya,zan mutu
wallahi! Da sauri ya yar da sallayar da ke
hannunsa ya isa gabanta,ya ture bargon ya
dago
ta a rikice ya ce. "Me yake damunki?" Ta cije
lebe
cikin sartun hawaye tare da rike hannunsa da
kyau ta ce. "Cikina Abdul zazzabi kaina.." Ya yi
saurin tattarota jikinsa yana rungumewa,cikin
nuna damuwa ya ce. "Ciki kuma fatima...
Wanne
irin ciwon ciki? Sannu.... Ko mu je asibiti?" Da
sauri ta girgiza kai tana kara jankane shi. "Ka
yi
min addu'a kawai... Idan ya yi min sauki ina da
magani zan sha..." Ya ce,"to... To shi ke nan....
Dai dai ina ke miki ciwo a cikin?" A rude ta ce
masa "Ko ina abdul" Ya dagota ya yaye cikin
yana kallo,hankalinsa ya rabu biyu da addu'ar
da
kuma kallon yadda cikin nata ke ta faman
motsi
alamar dai an kuntata shi. Suka kwashe lokaci
mai tsawo a haka,cikin ikon Allah sai ga sauki ya
samu har ta yi bacci a cinyarsa. Ya kara damke
hannunta cikin nasa yana bin fuskarta da
kallo,kwalla ta fara cika

Please Login or Register in order to submit comment